Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 4
da nake yi akanka. Bakin cikina shi ne, zan rasa mijina uban 'yata. Ita kuwa 'yata za ta zamo marainiya. Ka je ka yi duk irin shirin da za ka yi don fuskantar makiyanka amma ina tabbatar maka da cewa abinda kake tsoron kada ya faru sai ya tabbata". Koda gama fadin hakan sai Sabirat ta fashe da kuka sannan ta mike tsayc zumbur ta ruga wajc da gudu. Nan fa Sarki Huraisu ya kama tsuma kuma ya sake fusata ainun ya yi duru-duru ya rasa ma abinda zai yi. Daga can sai ya fita da sauri ya nufi bangaren masaukin Sarki Imras, yana tafiya bugzum-buguzum kamar zai tashi sama saboda sauri. Duk inda ya gifta sai ka ga Dakaru sun tsorata sun rakabe suna masu sunkuyar da kansu kas don kada fishin Sarki ya hau kansu. Kai tsaye Sarki Huraisu ya kunna kai izuwa cikin turakar dakin da Sarki Imras yake. Yana shiga kuwa ya iske Sarki Imras zaune a tsakiyar dakin ya harde kafatu ya tankwashesu kuma idanunsa a rufe suke yana karanta wadansu dalasimai na tsafi Koda Sarki Huraisu ya durfafoshi kai tsaye sai kawai ya daga masa hannu ya tsaida shi. Bisa dole Sarki Huraisu ya tsaya cak yana huci kamar bakin kumurci, har sai da Imras ya gama laziminsa na tsafi sannan ya bude idanunsa ya mike tsaye fuskarsa cike da alamar tsananin damuwa ya dubi Sarki Huraisu ya ce, "Ya kai abokina ka yi sani cewa duk abinda matarka ta gaya maka yanzu gaskiya ne kuma zai faru a gaske muddin bamu dauki matakin gaggawa ba. Nima a cikin bincikena na ga cewa 'yar uwata Husnaila za ta kasheni da hannunta kai kuma Murisu dan Muraisu zai kasheka, wato yaro mai kahon BUSA A MUTU". Lokacin da Sarki Imras ya zO nana zanccnsa sai hankalin Sarki Huraisu ya dugunzurma ainun ya rasa abinda ke masa dadi a duniya ya dubi Imras cikin firgici ya ce, "Ya kai abokina yanzu wanne mataki ya kamata mu dauka domin mu kubuta daga sharrin wadannan makiya namu? Sarki Imras yai ajiyar Zuciya sannan ya ce, "A cikin binciken da na yi yanzu na ga cewa su Gimbiya Suzaila sun sadu da Jarumi Imran kuma ya amince zai yi musu jagora izuwa dajin Kirzula domin ya kamo Muraisu a raye azo da shi har nan Birninka amma bisa sharadin su Gimbiya za su karbi addinin Musulunci, amma sai bayan sun shafe kwana arba'in a wani kauye Ya zama dole yanzu mu yi shiri ni da kai mu bi bayan su Gimbiya ya zamana cewa muna tare da su amma basu sani ba har su shiga dajin Kirzufa su yi yaki da su Muraisu bayan sun sami nasarar kama Jarumi Muraisu da 'yar uwata Husnaila sun fito daga cikin dajin Kirzufa mu kuma sai mu shammaccsu mu sace Muraisu da Husnaila daga wajensu mu kaisu can wani wajen mu kashesu. Ka ga kenan Kura da shan bugu gardi da kwashe kudk Ma'ana ba tare da mun sha wahalar komai ba zamu kama makiyanmu a ruwan sanyi". AA Misau ke Magana Lokacin da Sarki Imras yazo nan a jawabinsa sai Sarki Huraisu ya cika da tsananin farinciki ya rungume Sarki Imnras yana mai cewa, "Ya kai abokina hakika ka yí tunani mai kyau kuma ka z0 mana da shawara wacce za ta fisshemu. Daga can kuma sai ya janyc jikinsa daga cikin na Imras ya dubeshi cikin tsananin damuwa da sanyin jiki ya ce, "To yanzu ta ya ya zamu iya riskar su Gimbiya Suzaila cikin kankanin loakci tunda na san cewa yanzu suna nesa damu?" Koda jin wannan tambaya sai Sarki Imras ya yi murmushi ya ce, "Kada ka damu ya kai abokina, kai dai kawai ka je ka yi shirin wannan tafiya gobe da sassafe zamu tafi" Cikin murna Sarki Huraisu ya juya da sauri ya fice daga cikin turakar domin yaje ya fara shirin wannan gagarumar tafiya. Kashe gari kuwa tun da duku-dukun safiya Sarki Huraisu ya gama kimtsawa ya yi gagarumar shigar yaki. Dama tun a daren jiya ya tara fadawansa ya sanar da su cewa zai yi tafiya don haka ya bar musu ajiyar gari a hannunsu kuma ba zai wuce wata biyu ba zai dawo. Bayan Sarki Huraisu ya gama kimtsawa sai ya fito daga cikin turakarsa ya nufi kofar fita daga gidan sarautar gaba daya. Yana cikin tafiya ne ya yi kicibis da matarsa Sabirat tsaye a gabansa, hawaye na zuba daga cikin idanunta daki-daki. Nan take jikin Sarki Huraisu ya yi sanyi kuma ya Ji tausayinta ya shigeshi a karon farko a iya zamansa da ita, A haukali ya karasa daf da ita ya dubcta ya ce, "Ya ke matata ina dalilin zubar wannan hawaye naki?" Koda jin wannan tambaya sai Sabirat la rungume Sarki Huraisu ta fashe da matsanaicin kuka ta ce, Ya Kui mijina za ka yi tafiya amma ko yi mini sallama ba ka yi ba Menene tabbacinka cewar zamu sake saduwa? Ka yi sani cewa a tarihin Sarakunan kasar nan gaba dayansu suna bacewa ne su shude a lokacin da tafiya ta riskesu, walau suna kan han yar tafiya ko ta dawowa. Dan uwanka Muraisu ne kadai ya mutu a cikin garin nan a kofar gari sa'adda ku ka yakeshi kai da su Sarki Imras. Yanzu shi ke nan haka duk za ku tafi ku barni ni kadai a cikin gidan sarautar nan? Suzaila ta tafi har yau ba ta dawo ba, kaima kuma gashi yanzu za ka tafi ban san ranar daWowarka ba? Na zama ni kadai babu 'ya, kuma babu miji". Koda jin wannan batu sai Sarki Huraisu ya janye jikinsa daga cikin na Sabirat suka fuskanci juna ya dubeta cikin alanun tausayawa yà ce, "Ya ke matata ki yI sani Cewa ba a san raina zan tafi na barki ba, kuma in ba don wannan tafiya ta kasance mai hadari ba da tare da ke zan tafi. Ina so ki sani cewar faduwar gaba asarar namiji ce. Da dai azo a cini da yaki har gida gwara na fita na tari abokan gaba. Ina mnai tabbatar miki da cewa ni da 'yarki zamu dawo gida a raye cikin koshiiin lafiya nan da cikar wata biyu". Koda gama fadin hakan sai ya sumbaci goshinta sannan ya juya ya yi tafiyarsa ba tare da ya sake waigowa ba amma tuni idanunsa sun ciko da kwallah baya so ta gani ne, ita kuwa Sabirat sai ta bishi da kallo kawia tana mai ci gaba da zubar da hawayc kurma ta ji kamar ta bishi. ruga da gudu ta Wannan shi ne abinda ya faru a Birnin Lairuftsakanin Sarki Huraisu da matarsa Sabirat mahaifiyar Gimbiya Suzaila. A CAN bangaren su Jarumi Imran kuwa, lokacin da suka iso wannan kauye tare da tsirarurn yan garin wadanda suka rayu sai suka kama aikin gyaran garin aka shiga kwaba kasa ana yin bululluka wasu kuma suka rinka shiga daji suna saro itatuwa wadanda za Yi rufin sama da su. Haka dai aka wanzu ana ta yin wannan aiki har Tsawon kwana goma sha tara, a sannan ne sabon Birnin ya dawo sabo ya yi kyau matuka fiye da yadda yake a da can. A tsawon wadannan kwanaki kuma an fita bayan gari an fitar da gonakai an vi shuka. Nan da nan gonakin suka yi yabanya abin gwanin ban sha'awa. Haka kuma kullum Jarumi Imran yana koyar da mutanan garin yadda ake ibada, kai har ma sai da aka gina masallaci a tsakiyar Birnin, Jarumi Imran ne yake limanci. Nan da nan mutanan garin suka sami ilimi mai yawa kuma suka tsinci kansu a cikin rayuwa mafi dadi gami da samun nutsuwa da kwanciyar hankali. Duk abinda yake faruwa a Birnin su jaruma Suzaila suna gani kuma abin yana matukar burgesu da basu sha'awa amma kullum a cikin yin shawara suke akan su karbi addinin Jarumi Imran ko kada su kar6a sun kasa yanke hukunci. A koda yaushe idan Suzaila ta ga Lushaira tana kusanutar Jarumi Imran sai kishi ya kamata itamna ta kusanceshi ya zamana cewa ta hanasu samin damar da za su yi wata magana wacce ta shafi soyayya. Al'amarin da ya rinka kona zuciyar Lushaira ke nan ta inka kamuwa da tsananin bakin ciki kumna ta rasa yzdda za ta yi ta shawo kan matsalar. Ana cikin wannan hali ne wata rana Jarumi Imran ya tara mutanan kauyen a tsakiyar gari ya hau mumbari yana yi musu wa'azi ya sanar da su irin abubuwan da Allah Ya tanada na azaba ga wadanda AA Misau ke Magana suka bijire masa da kuma abubuwan da ya tanada na jin dadi ga wadanda suka bishi sai ga su jaruma Suzaila sun zo wucewa ta wajen domin su fita daji yin farauta tamkar yadda suka saba yi kullum da safe. Jaruma Suzaila ce mai jagorantar wannan farauta kuma idan aka tafi farautar ba a dawowa sai yamma. Sanadiyyar fatocin dabbobin da suke zuwa da su ne aka kafa sabuwar kasuwa a kauyen ta cinikin fata. Cikin kwanaki kadan kasuwar ta bunkasa ya zamana cewa mutanan da ke zaune a sauran kauyukan da ke makofataka suka rinka zuwa cin kasuwa, daga nan kuma masu zuwa cin kasuwar suka rinka karbar addinin Musulunci. A kan wannan dalili ne Jarumi Imran yake tsananin farinciki da wannan farauta ta su jaruma Suzaila saboda ta kawo ci gaban Rauycn ta fannin arziki da yaduwar addinin ALLAH. Lokacin da su Suzaila suka zo giftawa ta gaban Jarumi Imran a lokacin daya ke gabatar da wannan wa'azi sai maganganunsa suka ratsa zuciyar Lushaira. Nan take taji kaunar addinin Musulunci ta shiga ranta, ba ta san sa'adda ta noke ba ta tsaya a inda ake yin wa'azin. har su Suzaila suka nausa cikin daji suka yi nisa basu ankara ba cewar babu ita a cikin zugar. Sai da Jarumi Imran ya. shafe sa'a hudu yana wa'azi sannan ya kammala. A sannan ne mutane suka watse kowa ya kama gabansa ya zamana cewa babu wanda ya rage a filin wa'azin face Gimbiya Lushaira a tsayc, hawaye na zuba a idanunta. Ko kadan Jarumi Imran bai kula da cewar Lushaira na tsaye a wajen ba sai da ya sauko daga kan mumbari sannan kawai ya ganta a tsaye ita kadđai a filin tana zubar da hawaye . Cikin tsananin mamaki Imras ya matso kusa da ita ya dubcta ya ce, "Ya ke Lushaira ina dalilin zubar wannan hawaye a idanunki?" Sa'adda Lushaira taji wannan tambaya daga bakin jaruma Imran sai tayi ajiyar zuciya sannan ta dubcshi cikin nutsuwa ta ce, "Ya kại wannan Jarumi ma'abocin kyau da sadaukantaka ta ban mamaki ka yi sani cewa ba wani abu bane ya sani zubar da wannan hawaye ba facc tsananin jin dadin yadda kalmomin da na ji daga bakinka a wannan wa'azi da ka gama yanzu. Ka yi sani cewa tun da na zo duniya ban taba jin irin wadannan kalmomi ba wadanda babu mahaluRin la rai iya tsarasu komai iya zancensa. Babu wani bil'adama ko aljani mai irin wannan basira da hikima. Lallai wanda yai wannan zance shi ne mafificin komaí da kowa don haka na yi imani da shi kuma na gamsu cewa shi ne Ubangijin da ya fi cancanta a bauta masa," Koda Lushaira tazo nan a zanccnta sai Jarumi Imran ya kamu da tsananin farinciki mara misaltuwa kuma yaji nan take a karon farko a rayuwarsa ya kamu da soyayyar 'ya mace. Cikin muraa ya dubeta ya ce, "Shin yanzu kina nufin kin amince ki karbi addinin gaskiya?" Lushaira ta yi murmushi mai taushi ta ce, "Kwarai kuwa na amince da raina, zuciyata da gangar jikina gaba daya. Nan take Imran ya daga kansa sama ya yiwa Allah godiya sannan ya dubi Gimbiya Suzaila ya biya ma ta kalmar Shahada ta maimaita. Lushaira ta ce, "Ya kai sadaukin Sadaukai, ina rokonka alfarma guda daya. Alfarmar kuwa ita ce, na boyewa sauran yan uwana wannan addini da na karba kuma ina son ka koyar da ni addinin a sirrance ba tare da sun sani ba." Da jin wannan batu sai Jarumi Imran yai murmushi sannan ya dubi Lushaira cikin nutsuwa ya ce, "Ya ke wannan ma'abociyar kyau ki yi sani cewa ba a yin addinin Allah da tsoro, sannan kuma bana son na rinka koya miki wannan addini a sirrancc saboda bai kamata mu rinka kebanta ba ni da ke tunda baki kasance muharramata ba. Koda jin wannan batu sai hankalin Lushaira ya dugunzuma ta ce, "Ai kuwa in dai haka ne sai dai mu yi abu da daya, domin ka cetoni daga irin tsangwamar yan uwana za su vi mini. Lallai za su ji haushina su kyamaccni saboda na kar6i addininka ba tare da shawararsu ba. Abinda za ka yi ka kubutar da ni shi ne, kawai ka aureni na zama matarka". Koda jin wannan batu sai Jarumi Imran yaji zuciyarsa ta buga da karfi ya yi shiru yana tunani, daga can sai ya dubi Lushaira ya ce, "Ya ke ma'abociyar kyawu ki yi sani cewa shi aure a Musulunci yana bukatar walicci na dangi ko iyaye ko kuma wadanda suka dace. Anan garin ni da ke duk bamu da wanann walacci, saboda haka ki ajiye wannan magana a gefe daya. Ki tuna cewa fa akwai babban aiki a gabanmu na zuwa dajin Kirzufa don gabatar da yaki da Jarumi mai kahon BUSA A MUTU. Abinda nake so da ke shi nc, ki saki jikinki kuma ki kwantar da hankalinki domin zan zame miki garkuwa mai kareki daga dukkan kyamatar abokan tafiyarki. Lallai ba zamu 6oye musu karbar addininki ba. Yanzu ki je ki sami daya daga cikin matan garin nan domin ta koyar da ke yadda ake wankan tsarki, alwala da sallah, sannan sai ki ci gaba da daukar karatu na samun ilimin wannan addini mai TSarki". Koda gama wannan jawabi sai Jarumi Imran ya juya ya nufi hanyar da za ta kaishi izuwa masallacin garin, Dama tunda aka gina garin, wannan masallaci shi ne makwancinsa kuma shi ne makarantarsa inda yake koyar da ilimin addini. Ba tare da bata wani lokaci ba kuwa Lushaira ta nufi daya daga cikin gidajcn garin domin ta koyar da ita abubuwan da Jarumi Imran ya lissafa ma ta. Al'amarin su Gimbiya Suzaila kuwa, lokacin da suka yi nisa a cikin dajin don gabatar da farauta sai kawai Suzaila ta tuno da Lushaira. ta waigo baya ta dubi gaba dayan abokan tafiyar, Koda ta ga babu Lushaira a cikinsu sai hankalinta ya dugunzuma ta ji wani irin bakin kishi ya turnuketa tayi zargin cewa lallai Lushaira ta ki tahowa wannan farauta nc domin ta sami damar da za ta gabatar da soyayyarta ga Jarumi Imran, Nan take Suvaila ta jí kamar ta bayar da umarnin a koma da baya a fasa yin farautar amma da tayí tunanin cewa sauran abokan tafryar Za su gano cewar saboda kishi ne tayí hakan sai ta fasa, aka ci gaba da kutsawa cikin daji. Nima AA Misau ganin wannan kishin nata yasa zan dakata anan🥰 Zamu dakata anan saikuma wani lokaci zamu cigaba insha Allah Admin AA Misau ke Magana WhatsApp group Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30Q BUSA A MUTU!!! 💕 Littafi Na Shida (6)🩸 Part E. 💎 Takun Karshe😍 Na Abdulaziz Sani M Gini 🤴 Typing AA Misau ke Magana✍️⭐⭐⭐ (HAKIKA KUN NUNA MANA KUNA SON LITTAFIN NAN SABODA HAKA GA ALKAWARI NA NAN NA CIKA 😎 kucigaba da nuna mana goyon baya kusha LABARAI) Labari ya isowa Shagala cewa Marubucin yaci gaba da cewa.. TUNANIN CEWA SAURAN ABOKAN TAFRYAR ZA SU GANO CEWAR SABODA KISHI NE TAYÍ HAKAN SAI TA FASA, AKA CI GABA DA KUTSAWA CIKIN DAJI. Aikuwa ashe a sa a Suka fito domin sai da Suka kama damisa guda ukü gamida manyan. Macizai guda bakwai a lokacin ne rana ta fadi Bayan sun yada zango an gasa maciji guda daya kowa ya ci ya koshi sai suka tashi, suka kimtsa, aka taho gida. Suj auma Suzaila, basu shigo cikin gari, ba, sai daf da magariba lokacin da ake yin sallah. Koda su Suzaila suka zo giftawa ta gaban Masallaci sai suka yi kicibis, da Gimbiya lushaira tayi shigan fararen tufafii ta rufe jikinta ruf da mayafi za ta shiga masallacin bangarèn mata Nan take su duka suka tsaya cak suna kallonta cikin tsananin takaici da mamaki. Saboda fishi ma, sai su duká suka wuce basu ce da ita kala ba. Dan uwantai Yarima lHasnalu.ne kadai ya tsaya ya dubeta cikin alamun tsananin darmuwa kamar zai yi kaka yace, Yake yar,uwata mene ne dalilinda ya sa kika kar6i wannan addini ba, tare da shawarar mu ba?" koda jin Wannann tambaya sai:Lushaira tayi rmurmushi taoe, Na karbi wannan addini ne saboda shine na gaskiya kuma naga hujjoji a Zahiri da idanuna;wadanda suka sä na gamsu da haka Kuma kun ga wadannan hujjoji da idanunku kawai dai kun tsaya yin taurin kai ne da yin shawarwari na banza wadanda basu da wani amfani. Koda gama fadin hakan sai Lushaira ta juya ta shige izuwa cikin masallacin ta bar Yarima Hasnalu a tsaye cikin tunani da wasi-wasi. Nan take shima yaji zuciyarsa tayi na'am da addinin Musulunci. Daga wannan rana Lushaira ta ci gaba da yin addininta a fili a gaban su Suzaila ba tare da shakkar komai ba har ta sami ilimi mai yawa na addini. haka kuma ita da Jarumi Imran suka ci gaba da soyayya a boye har ma soyayyar ta fito fili kowa ya fahimta. A sannan ne Suzaila taji ta tsani Lushaira ainun kamar ta kasheshi ta huta saboda kishi amma ta hakura ta danne abin a cikin ranta. A ranar da suka cika kwanaki arba'in ne dai-dai a wannan gari su Suzaila suka taru gaba dayansu suka Z0 gaban Jarumi Imran suka durkusa kasa sannan Swzaila ta dubeshi ta ce, "Ya kai sadaukin sadaukan duniya ka yi sani cewa mun ZO ne mu sanar da kai cewa wa'adin da ka dibar mana na Zama a wannan gari ya cika, kuma yanzu mun amince da sharadin da ka gindaya mana cewar za mu karbi addininka bayan mun je dajin Kirzufa ka kamo mai kahon BUSA A MUTU." Koda jin wannan batu sai Jarumi Imran ya cika da tsananin farinciki ya dubi Suzaita cikin murmushi mai taushi ya ce, "Ai shi ke nan Sai ku je ku fara yı mana shirye-shiryen tafiya. Kuma lallai a kammala shirin kafin rana tayi domin mu sarni nutsuwar tafiyar. Ba tare da gardamar komai ba kuwa su Suzaila suka tashi suka ruga izuwa kasuwa suka sayi dawakai da sauran kayan guzuri suka dawo cikin gari. Sai da aka gama kimtsawa sannan aka je aka sanar da Jarumi Imran cewa an gama shirin komai shi ake jira. A wannan lokaci gaba daya mutanen garin taru a masallacin domin su yi bankwana da shi. Koda jama'a suka ji ccwar Jarumi Imran zai tafi sai kowa ya fashe da kuka mazansu da matansu, yara da manya saboda tsananin sabon da suka yi da shi da kuma matukar kaunar da suke yi masa. Kai ba ma shi ba, hatta L.ushaira da ta ja su a jiki sa'adda ta kar6i addinin Musulunci sai sukai ta yin kukan rabuwa da ita. Nan fa zuciyar Imran da ta Lushaira ta karaya suma suka kana kuka suka ji kamar su fasa yin tafiyar. Da kyar su Yarima Hasnalu suka janyesu daga cikin jama'a aka basu dawakai suka hau sanann suka tafi suna waigen mutancn garin suna zubar da hawaye. AA Misau ke Magana Su kuwa jama'ar garin sai suka barke da kuka wadansu manyan tamkar wadanda makusantansu. suka rasa Komai taurin zuciyar mutum a wannan lokaci ne dole ne tausayi ya kamashi domin su Gimbiya Suzaila ma sai da suka rinka zubar da hawayensu. Lokacin da wannan tawaga ta su Jarumi Imran suka yi nisa da barin wannan kauye, suna cikin tafiya sai suka ga wata inuwar wata katuwar halitta ta gifta ta mansu cikin tsananin azababben gudu tamkar tauraruwa mai wutsiya. Kafin su daga kansu sama su ga ko mene ne tuni halittar ta bace a cikin gajimare. Kawai sai suka ga Jarumi Imran ya kalli sama yai murmushi. Cikin alamun mamaki jaruma Suzaila ta dubeshi ta ce. "Ya kai sadaukin sadaukan duniya, menene dalilin da ya sa ka kalli sama ka yi murmushi?" Koda jin wannan tambaya sai Jarumi Imran ya yi murmushi ya ce, "Kar ki damu nan gaba za ki san dalilin yin wannan murmnushi nawa'". Suzaila ta gyada kai sannan tayi dogon tunani ta sake dubansu ta ce, "Ya kai Imran ka yi sani cewa daga nan fa zuwa dajin Kirzufa tafiya ce ta a kalla kwana arba'in da daya kuma akwai muggan aljanu da muggan dabbobin daji da 'yan fashi wadanda za su iya Keaa bata mana lokaci kuma za su zama sanadıyyar ajalin wadansu daga cikinmu." Imran ya numfasa ya ce, "Ai duk na san da wadannan abubuwa amma da izinin Ubangijina babu abinda zai taba lafiyar daya daga cikinmu har mu isa dajin Kirzufa kurna wannan tafiya ta kwana arba'in da daya Ailah zai gajarce mana ita ta koma ta kwana goma sha daya". Koda gama fadin hakan sai Jarumi Imran yai shiru bai kara cewa uffan ba har aka yini ana tafiya. Kamar yadda Jarumi Imran ya fada haka al'amuran suka kasance wato duk dajin da suka ratsa da zarar 'yan fashi ko muggan aljanu ko dabbobi sun hangosu sai ka ga suni ratsawa suna basu hanya ko matsowa ma kusa da su basa yi, kai ka ce ajalinsu suka gani. Ba komnai ne ya hadadsa hakan ba face karfin addu'ar da Jarumin Imran ke ta karantawa a cikin zuciyarsa ta neman tsarin Allah akan dukkan abu. Wani abu da ya daurewa su Gimbiya Suzaila kai shi ne, ganin yadda suka rinka shafe doguwar tafiya mai nisan tsiya a cikin kankanin lokaci tamkar masu daurin kasa. A takaice dai a cikin kwana goma sha daya kacal suka shafe tafiyar kwana arba'in da daya suka iso bakin dajin Kirzufa suna isowa wajen ne Jarumi Imran ya daga hannunsa sama kowa ya tsaya a bayansa sannan sai ya karanta wadansu addu'o'i na musamman. Kawai sai ya dubi su Gimbiya Suzaila ya ce, "Kowa ya biyoni a baya kada wanda ya kuskura ya wuce gabana". Yana gama fadin hakan ya sakarwa dokinsa linzami ya kunna kai cikin dajin. Lushaira ce ta fara bin bayansa saboda tayi imani da Allah cewa babu abinda zai sameta. Suzaila, Sarkin yaki, tagwayen Sadaukai da sauran bayi da kuyangi kuwa sai suka dan noke cikin alamun tsoro-tsoro. Sai da suka ga Imran da Lushaira sun yi dan nisa a cikin dajin sannan Suzaila ta bi bayansu a guje suma sauran tawagar suka bita. A dai-dai wannan lokacin nc Muraisu ya kamata ya busa kahon BUSA A MUTU, saboda haka tuni ya dauko kahon ya zo tsakiyar dajin na Kirzufa ya tsaya. Koda ya daga kahon sama ya busa sai yaji kahon ya ki busuwa. A zatonsa ya yi ne ya shiga cikin kofar kahon ya tosheshi don haka sai ya zarzageshi a kasa amma bai gu komai ya fado daga cikinsa ba. Ya zura hannunsa cikin kahon nanma yaji babu komai a cikinsa kawai sai ya sake daga kahon ya kafa a bakinsa ya busa a karo na biyu. Ai kuwa sai yaji dai kahon ya ki busuwa. Al'amarin da yai matukar dugunzuma har alimsa Ke nan ya rasa abinda ke masa dadi Kawai sai ya sa6a kahon a bayansa ya juya da nufin ya koma inda mahaifiyarsa take ya sanar da ita abinda ke faruwa. Yana juyawa sai yaji takun sawun dawakai a bayansa. Cikin hanzari ya juyo. Take ya yi arba da su Jarumi Imran sun durfafo inda yake. Koda Muraisu ya ga su Imran sai ya daga kansa sama ya takarkare ya kwarara uban ihu. Faruwar hakan ke da wuya sai ga dabbobin dajin suna fitowa daga kowanne bangare suna falfalowa da gudun tsiya suna taruwa a bayan Muraisu. Ana cikin haka ne sai ga Husnaila ma rike da mashinta ta falfalo da azababben gudu. Tana isowa daf da Muraisu sai ta tsaya cak tayi tirjiya tana haki. A dai-dai lokacin ne su Imran suka kara kusantosu ya zanmana cewa tsakaninsu bại wụce taku goma ba. Kawai sai Imran ya ce da su Suzaila su sauko daga kan dawakansu suka tsaya cak aka fara kallon-kallon. Koda Muraisu da Husnaila suka kyallara ido suka ga Lashaira sai suka icka da tsananin mamaki saboda AA Misau ke Magana Lushaira da Husnaila kamanninsu iri daya ne sak tamkar an tsaga kara. Daga can sai HuSnaila ta dubi Lushaira ta daka masa tawa ta ce, "Ya ke wannan budurwa mai kama da ni, wace ce ke kuma mene ne ya kawoku nan cikin dajin Kizufa?" Har Lushaira ta budi baki za ta bata amsa sai Jarumi lmran yai sauri ya numfashinta ya cc, "Wannan ita ce Gimbiya Lushaira 'ya ga dan uwanki Sarki Imras. Ni kuam sunana Jarumi Imran ma'abocin addinin Musulunci. Wannan jaruma da ke bayanmu kuwa ita ce Gimbiya Suzaila 'ya ga Sarki IHuraisu dan uwan mijinki marigayi Sarki Muraisu. Ku yi sani cewa bamu shigo nan dajin domin mu yakcku ba mu kasheku sai domin mu tsaidaku akan barnar da kuke yi ta salwantar da rayukan 'ya'yan Sarakan duniya. Kamar yadda danki Muraisu ya ga zahiri a yanzu, wato a daga kahon domin ya busa amma sai kahon ya ki busuwa. To fa wannan ta faru ne da taimakon Ubangijin Musulunci, ba wai taimakon tsafi ba. Duk irin zaluncin da aka yi muku ke da danki aka jefaku a cikin rayuwar kunci anan daji duk 'ubangijina ya nuna mini a cikin barcina. Abinda nake so da ku shi ne, ku ajiye makamanku ku karbi addinina in yaso sai na tafi da ku izuwa Birhin Lairuf inda za a kirawo 'yan uwanku Sarki Huraisu da Sarki Imras suma su kar6i addinin gaskiya sannan mu yafi juna a fara sabuwar rayuwa ta bin Allah". Kafin Jarumi Inran ya gama rufe bakinsa tuni Jarumi Muraisu ya daka masa tsawa yna mai cewa, "Ya kai wannan ma'abocin addinin Musulunci ka yi sani ccwa tunda ka Zo mana da batun yin sulhu tsakanin mu da abokan gabainu ba zamu ta ba yarda da kai ba don haka kaima kana sahun makiyanmu tsakaninmu da kai sai yakı" Muraisu na gama fadin hakan sai ya zare takobinsa ya ruga izuwa kan Jarumi Imran yana kururuwa irin ta manyan mazaje wacce ke firgita dandazon mayaka. Itama Iusnaila sai ta biyo bayansa a guje haka ma gaba dayan sauran dabbobin dajin duk suka yiyo kan Imran. Har su jaruma Suzaila sun yunkura za su taimakawa Jarumni Imran sai ya daka musu tsawa ya hanasu. Nan take yaja dogon layi a gaban su Suzaila ya karta kasa da takobinsa sannan ya faifala da gudu ya tari su Muraisu suka ruguntsume da azababbci yaki Duk dabbar da ta iso dai-dai wannan layi wanda Imran ya ja a gaban su Suzaila sai ta kasa ketare layin ta kai nusu hari domin ji take tamkar ana huro ma ta wuta mai mugun zafi. Nan

Chapter 3 of 4