Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 4
da matukar jarumtaka haka? Duk sa'adda Sarki Labarazu ya gabza masa naushi a kirji ko a fuska sai ka ga ya shanye dukan. Amma da zarar shi tsohon ya gabzawa Sarki Labarazu naushi daya sai ka ga har faduwa kasa yake. Nan da nan cikin kankanin lokaci tsohon ya hadawa Sarki Labarazu jini da majina. AA Misau ke Magana Koda Sarki Labarazu ya ga va fara jigata sai ya ci gabu da anfani da karfin sihiri ya rinka watsawa tsohon wula, kibbau da sauran mugayen abubuwa domin sun ki su yi tasiri a jikin tsohon. Ana cikin haka ne tsohon ya zage iya karfinsa ya gabzawa Sarki Labarazu wawan naushi a fuska. Take hakoran Sarki Labarazu guda biyu suka yi fitar burgu daga cikin bakinsa ya sulale kasa daga tsaye ya yi faduwar manya a sume. Nan take Dakarun Sarki Labarazu suka ruga izuwa kansa suak watsa masa ruwa. Faruwar hakan ke da wuya sai Sarki Labarazu ya farfado a lokacin da kansa ya kumbura yai suntum! Yana bude idanunsa da kyar a lokacin da yake gani dishi-dishi sai ya ga wannan Jarumin tsohon ya durfafoshi da nufin ya karasa kashe shi. Koda tahowar tsohon sai gaba dayan Dakarun Sarki Labarazu suka watse suka gudu izuwa can gefe daya suka zube kasa suna tsuma. Shi kuwa Sarki Labarazu sai ya mike zaune zumbur va kama rokon tsohon yana mai cewa, "Ya kai wannan tsoho ka yi mini rai na yi alkawari yanzu zan bar wannan gari kuma idan na tafi ba zan sakc dawowa ba." Koda jin wannan batu sai tsohon ya dakawa Sarki Iabarazu tsawa ya ce, "Kai tsohon azzalumi kuma munafukin Allah, shin ka manta ne cewa sau biyu muna fafatawa ni da kai kuma na yì maka kashcdi akan cewa idan har baka tuba ba ka daina shayar da Dodonka jini sai na hallakaka sa'adda muka yi karo na uku? Tabbas ni mai cika alkawari nc domin rayuwarka ba ta da wani amfani a wannan nahiya gaba daya. Lallai yau Allah Ya kawo Rarshenka, don haka da izinin Ubangijina yanzu za ka bar duniya". Kafin Sarki Labarazu ya budc baki ya ce wani abu sai tsokon ya daka tsallc sama tamkar an cilloshi daga cikin baka. A lokacin Sarki Labarazu ya. wangame bakinsa da nufin ya ce wani abu, amma sai tsohon ya soka masa wannan sanda tasa a cikin bakin. Take sandar tá nutse a cikin bakin ta faso ta cikin keyarsa sannan ya zare sandarsa. Sarki Labarazu ya kana kakarin mutuwa, cikin karfin hali ya zaro wani karanin kahon tsafi daga jikinsa ya busashi. gawa. Yana gama busa kahon kansa ya langabe ya zama A dai-dai wannan lokaci nc gaba dayan kauycn ya kama girgiza kasa ta fara tsagcwa, mutane da gidaje suka rinka ruftawa cikinta. Nan take wannan tsohon Jarumi ya yiwa su Gimbiya Suzaila inkiya da su biyoshi a baya. Nan take kuwa dukkaninsu suka bishi a baya a guje. Inda tsohon ya bi ne kadai baya tsagewa. Haka dai su Suzaila suka ci gaba da bin Wannan tsoho suna waigawa haya suna ganin abin tausayi da abin mamaki, domin kiri-kiri suka rinka iiyo ihun mutanc a lokacin da suke nutsewa a cikin Kasa. Gidaje kuwa suka rinka rugujewa suna bajcwa a kasa. A takaice dai gaba davan mutanen wannan kauye sai da suka hallaka, kuma babu gida daya wanda bai dagargaje ba. Sai da su Gimbiya Suzaila suka shafe sa'a guda Suna gudu sannan suka tsira daga sharrin wannan girgižar kasa kuma dawakansu ma gaba daya sai da suka hallaka. Lokacin da girgizar kasar ta daukc nc cif su Gimbiya Suzaila suka waigo suka ga kauycn gaba daya ya nutsc izuwa cikin karkashin kasa sai nan take suka dawo cikin haiyacinsu suka tuno da sauran abokan tafiyarsu wato Dakaru, bayi da kuyangi wadanda suka barosu a gidan da Sarkin kasuwa ya saukesu. Nan take hankalinsu ya dugunzuma suka fara tunanin su koma da baya domin su jc su tona gawarwakin su. Ilar sun yunkura za su koma da baya sai wannan Jarumin tsoho ya tsaida su ya dubi Suzaila da Sarkin yakinta ya ce, "Ku kwantar da hankalinku da izinin Ubangiji na za ku sadu da 'yan uwanku wadanda kuka baro a cikin wancan kauye da ya baje. Ina so ku gane cewa yanzu haka sauran yan Uwanku mutum uku da kuka fito nema suna can kogon Dodo da ke gabanmu tafiyar sa'a uku. Tabbas rayuwarsu tana cikin hadari saboda haka su va kamata mu je mu ccci rayuwarsu katin wannan Dodo ya hallakasu". Koda jin wannan batu sai Gimbiya Suzaila ta taho gaban tsohon ta tsaya daf da shi ta dubeshi cikin murmushi la ce "Ya kai wannan dattijo mai jarumtaka ta ban al'ajabi kayí sani cewa ko a tarihi ban taba jin labarin mutum mai irin jarumtakarka ba wanda ya kai shekarunka haka. Da farko dai ina mai mika godiya ta musamman a gareka bisa ccton rayuwarmu da ka yi gaba dayanmu nan domin in ba don kaiba da tuni yanzu wannan azzalumin Sarki ya hallakamu tunda ya fimu karfin damtse da karfin sihiri. Alfarmar da nake nema a wajenka yanzu ita ce, ina son ka bamu labarinka kuma ka sanar da mu irin addinin da kake yi domin mun ji duk abinda za ka yi kana ambaton Ubangijinka". Lokacin da Suzaila ke wannan jawabi Gimbiya Lushair ta fara matsowa gaba tana mai kurawa Dattijon idanu saboda ta ga idanun nasa sun yi ma ta kama da na almajiri Sarumi Imran. Koda dattijon ya ga Lushaira tana matsowa kusa da shi kuma ta kura masa idanu sai ya juyawa Suzaila baya AA Misau ke Magana ya ce, "Yanzu bamu da lokacin da zan tsaya baku wani labari don haka sai ku z0 mu hanzarta tafiya iZUWa kogon Dodo." Yana gama fadin hakan ya juya ya ci gaba da taliya yana mai dogara sandarsa. Cikin hanzari Suzaila, Lushaira, Sarkin yaki suka Kamar yadda tsoho ya fadi haka al'amarin ya kasance, wato sai da suka shafe sa'a uku cur suna ratsa daji sannan suka iso kofar kogon Dodo. Abinda yai matukar baiwa su Gimbiya Suzaila mamaki shi ne, tunda aka fara wannan tafiya tsohon bai gaji ba kuma shi ne akan gaba yana ta tsala sauri kamar zai tashi sama, duk da cewa sai ya dogara sanda yake taliyar. Su kuwa su Giimbiya Suzaila dukkaninsu babu wảnda bai gaji ba har mna suna hada kafa suna sassarfa kamar za su fadi kasa. Shi dai wannan kogo wanda Dodo ke ciki ya kasance mai girma da tsawo, sannan wani katon gungumcn dutse ne ya rufe kofar kogon wanda koda mutum dubu sun taru basu isa su iya matsar da shi ba. Shi kansa Sarki Labarazu da karfin sihirin tsafi yake daga dutsen sama, idan za a shigar da mutancn da aka kamo ciki. Da isowar su Gimbiya Suzaila bakin wannan kogo sai suka yi cirk0-cirko aka zubawa dutsen idanu cikin karayar zuciya. Shi kuwa wannan tsohon Jarumi sai ya koma gefe daya ya zauna yana kallon su domnin ya ga abinda Zả su yi. Gimbiva Suzaila ta dubi Sarkin yaki sanann ta dubi Lushaira da Hasnalu ta cc, 'Shin a cikinku akwai wanda yake da dabarar da vake ganin zamu iya janye wannan katon dutse mu shiga cikin wannan kogo? Koda jin wannan batu sai Sarkin yaki ya ce, "Ya Shugabata ai ina ganin cewa mu jarraba tureshi tukunna ni da ke idan muka kasa sai kuma mu jarraba karlin Lsafinmu". Gimbiya Suzaila ta ce, "Tabbas ka z0 da shaw ara mai kyau". Ba tare da bata wani lokai ba gimbiya Suzaila da Sarkin yaki suka je gaban katon dutsen suka dora hatavensu bibbiyu akai suka tara karlinsu gaba daya suha tura amma sai dutsen ya ki motsawa ko kadan. Nan take duk su bivun suka fara amfani da kartin sihirinsu don su ture dutscn. Sai da suka jina suna lalatawa har ya 7amana cewa Nn jike sharkal da gumi amma abu ya faskara. Duk wannan abu da ke faruwa Gimbiva Lushaira na tsaye a can gefe daya ta kurawa Jarumin tsohon nan idanu tana ta kokarin ta kwatanta kamannin idanunsa da Jarumi Imran, shi kuma tsohon duk sa'adda ya dago kai ya hada idanu da ita sai ya yi sauri ya sunkui da kansa kas. Bayan su Suzaila sun yi iya yinsu sun kasa turc wannan dutse sai suka koma gefe daya suka zauna. A sannan nc Gimbiya Suzaila ta dubi wannan Jarumin Isoho sannan ta dubi Sarkin yaki ta ce, "Ai kuwa mun yi garaje. Bai kamata mu jarraba kawar da wannan dutse ba tun da farko tunda muna tare da wannan sadaukin Sadaukai domin masu iya magana sun ce ta inda aka hau ta nan ake sauka,'" Hasnalu da ke tsaye daf da su sai ya dubi Gimbiya Suzaila ya ce, "Ai shima wannan Jarumin tsoho yana sane ya zuba muku ido domin ya ga iya gudun ruwanku saboda na ga yana ta yi muku dariya a lokacin da kuke ta kokarin kawar da dutscn". Suzaila tayi ajiyar zuciya sannan ta dubi Hasnalu cikin murmushi ta ce, "IHakika abinda ka fadi gaskiya ne. Ya kai Ilasnalu ka yi sani cewa ina godiya a garcka bisa yunkurin ceton rayuwata a dazu sa'adda Sarki Labarazu ke kokarin hallakani. Tabbas kauna ce tasa ka yi ganguncin taimakona tunda ka san ccwa ba za ka iya ba". Sa'adda Hasnalu yaji wannan batu dapa bakin Gimbiya Suzaila sai ya kamu da tsananin farın ciki domin a zatonsa ta karaya ne ta sauya shawara akan ka'idar da ta shimfida masa cewar sai ya kamo Jarumi za ta karbi mai kahon BSUA A MUTU sannan soyayyarsa amma kuma sai kawai ya ga ta dauke kai ga barin kallonsa ta juya ta nufi inda Jarumin tsohon yake. Koda ta iso daf da shi sai ta risina a gareshi cikin biyayya ta ce, "Ya kai wannan dattijo mai ban al'ajabi ashe baka taimakcmu ba ka bude mana kofar wannan kogo tunda mu mun kasa?" Sa'adda dattijon yaji wannan batu sai murmushi ga Gimbiya Suzaila ya ce, "Ai nima ba ture wannan dutsc ba face da taimakon Ubangijina. ya yi iya Zaman da kika ga na yi anan addu'a nake yi ina rokon Ubangijin nawa domin Ya bamu sa'ar kawar da dutscn. A hálin yanzu bani da tababcin Ubangijin nawa Ya amsa addu'ata amma kije ki sake jarraba ture dutsen mu gani, wata kila Ubangijin nawa Ya amsa rokona bamu sani ba," Ba tare da wata gardama ba kuwa Gimbiya Suzaila ta durfafí bakin kogon cikin karayar zuciya domin ko kadan bata sa ran cewa abin zai faru. Tana zIwa gaban wannan dutse sai ta fara sa hannunta gaba daya ta dafashi. Ai kuwa kafin ma ta tura dutscn sai dutscn ya mirgina da kansa sau uku ya bar bakin kogon sai ga kofa Zururu izuwa cikin kogon ta baiyana. Nima kuma AA Misau ganin wannan hanya zururu yasa zan dakata anan sai wani lokaci kuma idan Allah ya kaimu Singn Admin AA Misau ke Magana BUSA A MUTU Littafi Na Shida (6) Part C Na Abdulaziz Sani M Gini Typing AA Misau ke Magana (Rashin Sakin Litattafan da muke kawo muku akan lokaci daga gareku ne domin muddin zaku dinga nuna kuna so a cigaba ta hanyar LIKES & COMMENTS bamuki kullum mu kawo muku cigaban ba) Labari ya isowa Shagala cewa Marubucin yaci gaba da cewa.... saboda tsananin mamaki Ginbrya Suzaila ba ta san sa'adda ta bude baki ba kuma ta durkusa kusa bisa guiwoyinta tana juyowa tana kallon wannan dattjo kyma tana kallon kofar kogon dutsen wanda aka rataye fitilun itatun wuta a cikinsa saboda duhunsa. Suma su Sarkin yaki sai suka cika da tsananin mamaki gaba dayansu. Nan take Jarurnin dattijon ya Wuce gaba izuwa cikín kogon dutsen , sai Gimbiya Suzaila ta bishí a baya sannan Sarkin yaki sai kuma Hasnalu da Lushaira. . Sai da suka yí doguwar tafiya a cikin kogon dutsen basu hadu da komai ba kuma basu ga kowa ba amma duk inda suka wuce suna ganin fitilun itatuwan wuta a rataye a saman dutse. Kwatsam! Ba zato ba tsammaní sai suka iso wani babban fili a cikin kogon dutsen inda suka yí arba da waní katon keji. A cikin kejin akwai tagwaycn Sadaukai Shalaru da Halaru da kuma kuyangar su Gimbiya Lushaira su uku kacal A gefe daya kuma gawarwaki ne na mutane dubunnai ba adadi wata kan wata sn yi tsiri, wadansu gawarwakin ma har sun rube, wari da doyi ya cika kogon dutsen gaba daya. Ba shiri su jaruma Suzaila suka toshe hancinsu da rigunansu. Su kuwa su Shalaru saboda warin gawar da ya cika musu ciki ma tuni sun kama amai sun galabaita ainun har suna kokarin sumewa. Koda isowar su Jarumin tsoho daf da kejin da su Shalaru ke ciki sai wani irin haske na musamman ya baiyana ya haskake kogon gaba daya yadda ko allura ce ta fadi a wajen za a iya ganinta. Faruwar hakan ke da wuya kuma sai suka ji wani irin gurnani mai matukar ban tsoro ya cika Dodon kunnensu. Kafin wani daga cikinsu ya yi wani yunkuri sai kawai suka ga wani gabjejen Dodo ya fito daga cikin wani sako na kogon. Girman wannan Dodo ya ninka girman Sarki Labarazu sau bakwai. Kai inda za a yanke kansa a ajiye shi a kasa da sai yafi wannan dutse na kofar shigowa kogon girma da nauyi. Dodon yana da wawakcken baki tamkar rijiva hakar mutanen da. Wadansu irin manyan hakora ne da shi masu fika kuma a wargatse suke ba kyan gani wadanda koda karfe suka tauna sai sun ruburbusheshi. Girman idonsa guda daya ya kai na katon tulun debo ruwa a rafi. Lokacin da Dodon ya yi arba da su Gimbiya Suzaila ncsa kadan da inda sukc sai ya takarkare ya kwarara uban ihu har tartsatsin wuta ya rinka zuba daga bakinsa ya haddasa karamar gobara a cikin kogon dutsen, sautin ihun kuwa ya sa dutsen kogon ya kama Sagewa, duwatsu suka rinka fadowa kasa suna fashewa. Al'amarin da yasa kowa va firgita ke nan suka dimauce amma banda Jarumin tsohon nan. Ita kanta jaruma Suzaila ba ta san sa'adda ta koma bayan Jarumin tsohon ba ta rakabe Su Sarkin yaki kuwa rugawa suka yi da baya suna neman ficewa daga cikin kogon. Koda Jarumin tsohon ya ga wannan Dodo ya durfafosu sai shima ya ruga gareshi da gudu yana mai karanta wata addu'a a cikin zuciyarsa yana mai rike da wannan sanda ta hannunsa wacce yake dogarawa ya yın da yake tafiya. Ai kuwa suna zuwa daf da juna sai Dodon ya kawo masa wawan mangari da hannu daya. Cikin bakin zafin nama ya gocewa mangarin. Koda hannun Dodon ya bugi dutscn kogon sai inda ya buga din ya rugurguje ya zube kasa. Nan fa Dodon ya ci gaba da kaiwa tsohon mangari, bugu da taku da hannayensa da kafafunsa, shi kuma ya rinka gocewa cikin tsananin zafin nama yana tsalle Isalle da shawagi akan sassan jikin Dodon yana dukansa da wannan sanda ta hannunsa. Duk inda ya doka a jikin Dodon sai ka ga wajen ya dare jini na zuba tamkar da takobi ya sareshi sai dai kaji Dodon ya kurma ihu amma saboda na ci, taurin rai. da Karfin Allah Ya isa Dodon ya ki faduwa kasa sai daima Al Amin Ahmed Misau AA Misau ke Magana ka ga ya dada haukacewa da kara, kaimi wajen kokarin hallaka tsohon. Sai da suka shafe sa'a biyu da rabi suna wannan bakın gumurzu ya zamana cewa jikin Dodon yai fata-fata da jini amma tsohon ya kasa kasheshi. Ana cikin hakane tsohon ya fusata ainun ya daka wawan tsalle sama ya shallake tsohon Dodon gaba daya yana mai kwalla kabbara da karfi ya kwadawa Dodon sanda a tsakiyar kansa. Take kan Dodon ya 6are gida biyu tamkar an bare gyada sai ga kwakwalwarsa tayi fallatsi ta kwararo kasa. Nan take Dodon ya sulale kasa ji kake tim! Kamar giwa ta fadi. Cikin tsananin farin ciki su Sarkin yaki suka ruga suka 6alle wannan keji suka fito da su Jarumi Salaru. A dia-dai wannan lokaci ne kogon dutsen gaba daya ya kama girgiza ya ci gaba da rushewa yana faduwa kasa. Da kyar da sidin goshi suka samu suka fiice daga cikin kogon dutsen ba tare da dayansu ya hallaka ba ko ya raunana. Suna gama fitowa daga cikin kogon ya baje gaba daya ya nuke izuwa cikin karkashin kasa tamkar bai taba wanzuwa ba a wajen. Kamar a mafarki sai su Gimbiya Suzaila suka yi arba da sauran 'yan uwansu da suka baro a cikin Kauyen nan tsaitsaye a gabansu cikin koshin lafiya kuma suna tare da wadansu tsirarun mutanan kauyen maza da mata yara da tsofaffi wasunsu da yawa sun sami raunika sakamakon wannan girgizar kasa da aka yi musu. Nan fa su jaruma Suzaila suka ske kamuwa da matukar farin ciki. Bayan kowa ya nutsu sai wannan Jarumin tsohon ya dubi wadannan mutanen kauyeya ce "Ya ku jama'ar wannan gari kun sani cewa shekara da shekaru Sarkinku Labarazu yana zaluntarku yana yi muku mulkin murdiya da danniya.. Ya debi iyayenku, 'ya'yanku, yayyenku da kannanku ya bayar da jininsu ga Dodon da yakc bautawa a matsayin Ubangijinsa. Yau gashi rana daya na kashe wannan Sarki naku kuma na kashc Ubangijin nasa Wannan ita ce shaidar cewa Sarkinku yana kan addinin karya kuma yana bautawa Ubangijin da bai cancanta a bauta masa ba tunda ya kasa kare kansa daga mutuwa. Ku saní cewa babu wani Ubangiji da ya cancanci a bautawa facc Ubangijin Musulunci wanda Ya halicci sammai da kassai da duk abinda ke cikinsu. Shi ne Ubangijin da Ya bani karfi da sa'ar har na kashe Sarkinku da abin bautarsa. Shi ne Ubangijin da nake bautawa dare da rana. Shin yanzu za ku bayar da gaskiya ga Ubangijin Musulunci?" Koda jin wannan tambaya sai gaba dayan wadannan mutancn kauye suka hada baki suka ce mun bayar da gaskiya ga Ubangijin Musulunci". Cikin tsananin farinciki tsohon ya biyawa mutanen kauyen kalmar shahada suka maimaita sannan ya dubesu ya ce, "Yanzu zamu koma izuwa tsobon kauyen naku mu sake rayashi. Ma'ana mu sake gina gidajenku, kuma zan zauna tare da ku har izuwa tsawon dan lokaci domin na koyar da ku yadda ake bautar Ubangijina, " Koda gama fadin hakan sai tsohon ya juya kuma ya fuskanci su Gimbiya Suzaila ya ce, "Ya ku wadannan baki shin kuma ba za ku bada gaskiya ga Ubangijina ba tunda kun ga karfin Sa da ikonSa da idanunku?" Har Suzaila ta budi baki za ta ce wani abu sai Lushaira ta tari numfashinta ta dubi tsohon ta ce, Tabbas zamu iya karbar addininka yanzu take anan, amma sai idan ka bani amsar tanbayar da zan yi maka yanzu" Koda jin wannan batu sai tsohon yadubi Lushaira cikin mamaki ya ce, "Ke kuwa wacce irin tambaya ce haka kike son a ki yi mini?" Lushaira ta dubeshi cikin nutsuwa ta ce, "Ina son ka dubi girman UbangijiniKa ka fada mini iyakar gaskiya bisa abinda zan tambayeka. Shin wanann kamanni da kake ciki a yanzu shi ne kamanninka na gaskiya? Me ka sani dangane da wani Almajiri wanda muka hadu da shi a baya cikin wannan tafiya tamu wanda ya zo mana a jigace cikin yunwa da kishirwa har na taimakeshi, shi kuma ya bani labarin dokokin da zamu kiyaye idan muka shigo wannan gari na Sarki Labarazu?" Lokacin da Jarumin tsohon yaji wadannan tambayoyi guda biyu sai jikinsa ya yi sanyi ya sunkui da kansa kas yana mai ajIyar zuciya sanann sai kawai ya karanta wata addu'a ya tofa akan tafin hannaycnsa biyu ya sha fa akan fuskarsa. Nan take kamanninsa ya juye izuwa kyakkyawan saurayi ma'abocin haiba da kwarjini. Nan fa kowa ya kamu da tsananin mamaki aka bude baki ana kallonsa. Ita kuwa Gimbiya Suzaila yanke jiki tayi ta fadi kasa surmanmiya sai da aka Zuba ma ta ruwa sannan ta farfado. AA Misau ke Magana Koda ta bude idanunta tayi arba da saurayin sai ta kura kawai. idanu.masa tana murmushi A sannar ne dattijon ya dubi Lushaira ya ce, "Sunana Jaruni lMRAN BIN HUZEIR. Na kasance ma'abocin addinin Musulunci wanda ya sallama rayuwarsa akan tafarkin yada addinin Allah. Kaso tamanin na rayuwata ina gudanar da ita ne a cikin daji don yin bautar Allah da kuma yin sana'ar farauta. Bani da wani abinci face dan itaciya. Bana shiga cikin gari sai a lokacin sanyi ko zafi da damina. Babu abinda na tsana sama da zalunći kuma bana taimakon mutum face na jarrabashi na ga yana da gaskiya, amana da jin kai'". Imran ya dubi su Gimbiya Suzaila gaba dayansu daya bayan daya, sannan ya ce, "Ya ku wadannan matafiya ku yi sani cewa na taimakcku ne albarkacin wannan yar uwa taku wacce ta taimakeni sa'ada na zo gareku a galabaice. In ba don ta tainakeni ba da ko kadan ba zan ceci rayuwarku ba daga sharrin Sarki Labarazu da Dodonsa. Na kan batar da kamannina ta hanyar rokon Ubangijina domin na shiga cikin mutane a kaskance na jarraba halaycnsu. Ina mai sanar da ku cewa tun kafin na hadu da ku Ubangijina Ya sanar da ni cewa kun fito nemana ruwa ruwa a jallo, ba don komai ba sai domin na yi muku jagora izuwa dajin Kirzuta na Kawar muku da Jarumi mai Gahon BUSA A MUTU. Shin abinda na fada gaskiya ne?" Cikin hanzari su jaruma Suzaila suka hada baki suka ce, "Wannan gaskiya ne". Jarumi Imras ya yi murmushi ya ce, "Tabbas na amince zan yi muku jagora izuwa dajin Kirzufa amma bisa sharadi biyu. Sharadi na farko shi ne. za ku karbi addinina gaba dayanku bayan na kama MURAISU DAN MURAISU mai kahon BUSA A MUTU na dajin KIRZUFA. Sharadi na biyu kuma shi ne, ba zamu tafi izuwa dajin Kirzufa ba sai bayan mun zauna da mutanen wannan kauye tsawon kwana arba'in na koyar da su yadda ake bautar Ubangijin Musulunci'. Sa'adda Jarumi Imran yazo nan a zancensa sai jikin su Gimbiya Suzaila yai sanyi suka shiga kallon junansu aka rasa wanda zai ce kala. Daga can sai jarụma ta dubi Jarumi Imran cikin murmushi da wani irin kallo mai nuna tsantsar SO ta ce, "Ya kai sadaukin Sadaukai, ka yi sani cewa kazo mana da babban al'amari wanda ba zamu iya yanke hukunci akansa ba kai tsaye don haka lallai muna da bukatar đan lokaci da zamu yi shawara saboda haka yanzu zamu zauna tare da kai a cikin kauyen wadannan mutane na marigayi Sarki Labarazu. Lallai kafin cikar kwanakin da za ka yi tare da su muma zamu gama shawara mu sanar da kai hukuncin da muka yanke." Koda Gimbiya Suzaila tazo nan a zancenta sai Jarumi Imran ya yi murmushi ya ce, "Shi ke nan ai rana bata karya sai dai uwar 'ya taji kunya. Yanzu sai ku zo mu koma da baya izuwa kauyen wadannan mutane ." Koda gama fadin hakan sai Jarumi Imran ya juya da baya ya kama tafiya, take ragowar mutanen wannan kauye suka bishi a baya duu!Tamkar kaza da 'ya'yanta, suka durfafi hanyar da za ta mayar da su izuwa wannan rusasshen kauyce Kawai sai Suzaila ta dubi su Sarkin yaki ta ce, "Ai bamu da wani zabi wanda yafi mu bi bayan mutancn wannan kauyc." Babban abinda yafi daga musu hankali a yanzu shi nc, sun san cewa sun rasa gaba dayan guzurinsu da kayayyakin su wadanda suka nutse a cikin karkashin kasa. Hatta dawakansu na hawa yanzu babu bare su ci gaba da tafiya izuwa dajin Kirzufa cikin kwanciyar hankali. Wannan shi ne abinda ya faru ga su jaruma Suzaila bayan sun dace sun hadu da Jarumi lmras, Jarumin da suka fito nema ruwa a jallo. AA Misau ke Magana A CAN Birnin Lairuf kuwa, tunda aka tura su jaruma Suzaila ncman Jarumi Imran, Sarki Imras bai koma kasarsa ba kuma kullum yana cikin bincike a cikin hallarar tsafi domin ya gano yadda karshen tafiyar su Suzaila zai kasance walau akwai sa'a ko rashinta. Wata rana da rana tsaka Sarki Huraisu na zaune a turakarsa tare da mahaifiyar Suzaila suna cin abinci cikin nishadi sai kawai ya ga ta daina cin abincin ta sunkui da kanta kas tana tunani. Daga can sai idanunta suka ciko da kwallah har hawaye ya zubo ma ta. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin Sarki Huraisu ke nan ya dubcta cikin tsananin damuwa ya ce, "Ya ke matata ina dalilin zubar wannan hawaye naki?" Koda jin wannan tambaya sai Sabirat ta dago kai ta dubeshi ta ce, "Ya kai mijina ka yi sani cewa tun daga ranar da 'yarmu Suzaila ta yi wannan tafiya kullum sai na yi wani mugun mafarki a cikin barcina. Abinda nake gani shi ne, mumnunan yaki ya barke a tsakanin Birnin nan namu an kashe mutane babu adadi, jini ya malala a ko ina ba kyan gani kuma a gaban idanun 'yar tamu, wani Jarumin saurayi yake sa takobinsa ya sare maka kai ba tar da ta ceci rayuwarka ba." Kafin Sabirat ta gama rufe bakinta tuni Sarki Huraisu ya zabga ma ta mari. Nan take bakinta ya fashe har jini ya fito, ta zubawa Sarki Huraisu idanu kawai tana mamaki da takaicin yadda yasa hannu ya mareta. Cikin tsananin fishi Sarki Huraisu ya mikc tsaye zumbur ya dakawa Sabirat tsawa yana mai cewa, "Wannan mafarki na kì karya ne, har abada ba zai taba faruwa ba. Ni murucin kan dutse ne ban fito ba sai da na shirya. Babu wani makiyina wanda ya isa ya sami nasaraa kaina " Koda Sarki Huraisu yazo nan a zancensa sai yaji Sabirat ta bushe da dariya. Al'amarin da yai matukar girgizashi ke nan ya zuba ma ta idanu kawai ya fara zargin ko ta sami tabin hankali ne. Daga can kuma sai ya ga ta murtuke fuskarta ta dubeshi a fusace ta ce, "Ya kai mijina ka yi sani cewa tun da ka kashe đan uwanka Muraisu ka kar6i karagar mulki kake zalunci a Birnin nan naka. Babu mai jin dadi a kasar nan face wanda ya kasance azzalumi irinka kuma mai biyayya a gareka Topa Nima kuma AA Misau zance sai wani jikon Zamu dakata anan saikuma wani lokaci zamu cigaba Admin AA Misau ke Magana Whatsp group https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30Q Facebook Fage https://www.facebook.com/profile.php?id=100063661782295 Facebook page https://www.facebook.com/AlaminGuyson?mibextid=3amO3DAFELuS4Abp SaikunzoBUSA A MUTU 💕 Littafi Na Shida (6)🩸 Part D. 💎 Na Abdulaziz Sani M Gini 🤴 Typing AA Misau ke Magana ✍️⭐⭐⭐ Labari ya isowa Shagala cewa Marubucin yaci gaba da cewa.... (Kamar Yadda Mukayi Korafi Kan Kuna Son Litattafan Da Muke Dorawa Amma Bakwa Nuna Kuna So A Yanzu Nake Ga Kamar Kun Gyara Ta Hanyar Maida Hankali Akan Giya Mana Baya SABODA HAKA idan yau kun Samar mana da LIKES SOSAI gobe Ma Zamu Dora Cigabansa) 🥰 WANDA YA KASANCE AZZALUMI IRINKA KUMA MAI BIYAYYA A GAREKA sai da Gimbiya Suzaila ta girma ta tas0 da gagarumar Jarumtaka sai mutane suka fara samun Saukın zaluncinka domin sau da yawa ita ce take matsa maka kake yiwa talakawanka adalci. yanzu Gimbiya Suzaila bata nan ka dawo da mulkinka na zalunci da cutar da talakawa. To ka sani cewa mulki da zalunci baya dorewa, komai daren dadđewa sai ka rasa wannan matsayı naka. Bisa wannan dalili ne naji na yi imani da wannan mugun mafarki

Chapter 2 of 4