Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 4
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels BUSA A MUTU Littafi Na Shida (6) Part A Na Abdulaziz Sani M Gini AA Misau ke Magana WANNAN muguwar dabi'a ta Sarki ta addabi Wannan mutanen kauyensu da sauran mutanen da ke zaune a garuruwan makoftaka kuma ya zame musu alakakat, domin ya shafe shekaru talatin yana yi musu wannan mulkin zalunci. An sha hada Dakaru azo a yakcshi domin a kawar da shi a kashe Dodon nasa, amma abu ya faskara. Bisa dole mutane suka rungumi kaddara suka zuba Ido suna jiran ranar da mutuwa za ta riski Sarki Labarazu domin su huta da wannan abin takaici. Da isar Sarkin kasuwa Rubiyan izuwa cikin fadar Sarki Labaruza sai ya zubc kasa ya kwashi gaisuwa sannan ya dago kai ya dubeshi cikin tsananin damuwa da fargaba ya ce, "Ya Shugabana yau fa wadansu bakin mutane sun shigo garin nan wadanda ga dukkan alamu sun shigo da cikakken shirinsu kuma tamkar sun san sirrin garin namu. Abu na farko dai sun ki su ci ko su sha komai na cikin garin nan, bare mu sami damar da zamu kamasu a hannu mu kaisu can kogon Dodo. Abu na biyu shi ne, basu yarda sun sauka a ko ina ba sai a kasuwa inda suka bukaci na basu hanyar gida. Nan takc na tsuga musu kudi a tunanina za su hakura su koma cikin gari inda zamu gama da su nan da nan amma sai suka ki yarda suka biya kudin da na iuula musu. Bayan an kaisu masaukin nasu sai na bukaci su bani kwangilar kai musu abinda za su rinka ci da sha nan ma suka ki amincewa. Koda Rubiyan yazo nan a zancensa sai Sarki LabaraZu ya daga musu hannu yana mai dakatar da shi. Ribiyan ya tsuke bakinsa yai shiru, a sannan ne Sarkı Labarazu ya dauko wani farin kyalle ya shafeshi da hannun hagu yana mai karanta wadunsu dalasiman tsali. Nan take hoton su Gimbiya Suzaila ya baiyana akan kyallen, boka Labarazu ya yi arba da su gaba dayansu. Koda ya ga jaruma Suzaila a cikin tawagar sai ransa ya baci ya takarkare ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa wanda yasa Rubiyan ya firgita, ya dimauce bai san sa'adda ya saki fitsari ba a wando. Sarki Labarazu ya kasance narkeken kato mai kirar Sadaukai da siffa irin ta mutanen farko. Kallo daya zaka yi masa ka san cewa sadauki nc mai dakawa maza gumba a hannu. Cikin tsananin fishi Sarki Labarazu ya cakumi kwalar rigar Rubiyan ya dagashi sama da hannu daya tamkar sillan kara ya ce, "Saboda me tun da farko baka aiko da gaggawa an gaya mini zuwan wadannan baki ba?" Cikin tsananin tsoro da kyarmar jiki Rubiyan ya ce, "Ka gafarceni ya Shugabana na yi zaton zan iya kamasu nc a hannuna ba sai na zo na sanar da kai ba." Labarazu yai wurgi da Rubiyan ya fadi can gefe daya tamkar ya yi wurgi da tsumma sannan ya ce, "Hakika wadannan baki su ne mafi hadari daga cikin dukkan bakin da suke zuwa mana. Idan ba mu yi da gaske ba su nc za su kawo karshen mulkinmnu anan garin". Yanzu dai muna da mutanen da zamu yankawa Dodo har na tsawon kwana shida, dole ne kafin rana ta bakwai mu fara sato wasu daga cikin wadannan baki wadanda zamu yankawa Dodon namu". Koda jin wannan batu sai tsoro ya kama Rubiyan ya ce, "Ya Shugabana ta ya ya zamnu iya sato wadannan mutanc alhalin ko yaushe suna tare a waje daya. Duk hanyar da zamu bi mun bi, amima mnun kasa samun nasara". Labarazu ya ce, "Kar ka damu a daren yau zan san abinda zan yi. Yanzu ka tashi ka tafi na sallameka". Nan take Rubiyan ya mike tsaye ya fice daga cikin fadar da sauri. Shi kuma Sarki Labarazu ya sake kurawa wannan farin kyalle da ke hannunsa idanu ya shiga nazari yana karanta wadansu dalasimai na tsafi. A CAN masaukin su Gimbiya Suzails kuwa da Yarima Hasralu da Ginsbiva Lushaira suka shig cikin dakin su sai suka zauna suka yi shiru kowannensu ya fada cikin kogn tunani. Abinda Hasnalu yake ta tunowa da shi shi niu, lokacin da ya gana da Gimbiva SulaiZa a cikin lambun gidan sarautar mahaifinta, lokacin da ta gindaya masa yana son ya sami soyayyata dole ne dokar cewar in dai yana yaje dajin Kirzufa ya kamo Jarumi nai kahon BUSA A MUTU yuzo ma ta da shi." Koda Hasnalu yzo dai-dai nan a tunaninsa sai kwallar takaici a cika masa idanu, domin ya san cewa tabbas wutsiyar rakumi layi nesa da kasa. Idan har Jarumi Imran ne ya kamo Muraisu mai kahon Busa a mutu shŁi ke nan dama ta wuceshi. A bangaren Gimbiya Suzaila kuwa, ba wani abu ta fara tunowa da shi ba face lokacin da ta kaiwa Ainiirin nan abinci. Nan take ta tuna cewa abincin da ta kai masa kala biyu ne. Daya gasasshen nama ne, daya kuma 'ya'yan itatuwa ne na tuffa da ayaba, sai kuma ruwa a tulu. Ita dai ta ga ya dauki tuffar ya gutsura sau biyu ya ci, sannan ya ajiye ya dauki Ayaba ya gutsureta sau daya ya ci, sannan ya dauki tulun ruwan ya yi masa kur6a uku. A dai-dai wannan lokaci nc ta tuno da kalar fatar Almajirin wacce ta kasance wankan tarwada. Duk da cewa fuskarsa ta cika da gashi akwai alamun ccwa kyakkyawa ne shi na gaban kwatance domin idanunsa dara-dara nw masu tsananin fari da haske kuma hancinsa dogo ne siriri, a kasansa akwai dan karamin baki tamkar yankan wuka. Lushaira ta tuna cewa yadda ta ga kamannin wannan Almajiri haka boka Kirishna ya siffanta Jarumi Imran. Nan take taji ta gamsu a cikin zuciyarta dari bisa dari cewar wannan almajiri shi ne Jarumi Imran. Kawai sai kuma taji ta kamu da tsananin sonsa a cikin zuciyarta yadda babu abinda take so sama da ta sake saduwa da shi. Nan take itama ta dilmiya a cikin kogin tunaninsa da begensa, al'amarin da ya sanya lakaici ke nan a cikin zuciyarta saboda bata taba tsintar kanta a cikin irin wannan yanayi ba. A dai-dai wannan lokaci ne Yarima Hasnalu ya dawo cikin haiyacinsa, koda ya dubi Lushara ya ga ta shiga cikin irin halin da ya tsinci kansa a ciki, al'amarin da yai matukar bashi mamaki ke nan ya dubeta cikin damuwa ya ce, "Ya ke yar uwata, tunanin me kike yi ne AA Misau ke Magana Madakin Gint haka wanda har Va dauke miki hankali kika manta cewa muna tare?" Koda jin wannan lambaya sai Lushaira ta bushe da dariya ta ci gaba da dariyar kamar ba za ta daina ba. Al'amarin da yai matukar baiwa Hasnalu mamaki ke nan ya zuba ma ta idanu kawai. Daga can sai Lushaira ta nutsu ta ce, "Ya kai dan uwana kayi sani cewa ba wani abu bane yasa ka ga ina yin wannan dariya ba face yanin nima na shiga irin halin da ka tsinci kanka a ciki. Abinda nake nufi shi ne., nima yanzu na fada tarkon soyayya kamar yadda kaima ka tsinci kanka a ciki". Koda jin haka sai Yarima Hasnalu ya gyara ZaIma cikin firgici ya dubcta ya ce, "Ya ke 'yar uwata ni a sanina da ke ban taba ganin kin so wani da narriji ba, kuma ba kya sauraron 'ya'yan Sarakai da Attajirai masu ZUwa neman aurenki ba. Wane nc wannan gawurtaccen saurayi mai sa'ar gaske wanda har ya sami matsugunni a cikin zucivarki farat daya haka?" Sa'adda Gimbiva Iushaira laji wannan tambaya sai tayi ajivar numfashi sannan ta cc, "Ya kai fan uwana ka yi sani cewa a iya rayuwata da duk irin tafiyc-tafiyen da na yi ban laba ganin da namiji mai kwarjini, haiba da kyau ba kamar wannanAImajir da ya Z0 mana heman laimako aka wulakantashi." Koda jin wannan batu sai Yarima Hasnrlu ya kara irgita ainun ya ce, "Haba kanwala wanc tsautsatyI ne ya kaiki son Jarumi Imran alhalin kin san cewa Gimbiya Suzaila ma tana sonsa?" Lushaira lavi murmushi sannan ta ce, "Ai da ni da Suzaila duk muna son mutumin da bai ma san halin da muke ciki ba ne. Duk da cewa ita ta fara sonsa ne tun daga ranar da ta fara jin labarinsa ni kuwa sai da na fara ganinshi ido da ido sannan na kamu da sonsa, tawa soyayyar lafi ta ta karfi. Dalilina anan ita ce, tana sonsa nw kawai saboda jarumtakarsa ni kuwa ina sonsa ne saboda ganin irin mu'arnalarsa da halayyarsa ba wai kyansa ko jarumtakarsa ce ba ta fauke mini hankali tunda sa'adda ma na ganshi.bai yi wata jarumtaka ba sannan kuma ban ga kyawunsa ba s(isai kasancewar gashi ya cika fuskarsa gaba daya kuma bai yi wata shiga mai kyau ba wacCe za ta bayyana kyansa ba". Koda jin wannan batu sai Lushaira ta yi murmushi ta ce, "Ai konai na rayuwa akwai sa'a da rabo. LLokaci zai bambance konmai". Koda gaina fadin hakan sai Gimbiya ILushaira ta mike tsaye ta tafi izuwa kan shimfidarta ta kishingida domin ta huta a lokacin ne kuyanginsa suka shigo dauke da farantan ahinci da 'ya'yan itatuwa suka zube a gaban Yarima da gaban Lushaira sannan babbar cikinsu ta dubi Lushaira cikin biyayya ta ce, "Ya Shuabata shin akwat Wani aiki da kike buralar mu yi muku a yanzu?" Lushaira ta ce, "A'a babu komai. idan akwai bukatar hakan zamu sanar da ku, ku tashi ku tafi na sallamcku". Nan take kuwa kuyangin suka mikc tsaye suka ficc daga cikin dakin. Lokacin da yamma tayi ya Zamana cewa babu sauran zalın rana sai Gimbiva Suzaila ta fito cikin harabar gidan ta kama kewaye tana Zagaya gidan tana nishadi. ne sauran abokan taliyara la suka rinka A lokacin wajcn Swaila firlitowa daga cikin dakunarsu suna zuwa suna gaishcta a lokacin da ta zauna a cikin lambun gidan. A wannan lokaci ne, Suzaila ta lura ccwa ba la ga lawarcn Sadaukai ba Jarumi Shalaru da Jarumi Halaru, sannan kuma a cikin kuyangin su Gimbiya Lushaira ba la ga wala baiwa ha mai suna IKILIMA. Nan take hankalinta ya dugunzuma ta dubi Sarkin yakin mahaifinta ta ce, "Ya kai Sarkin yaki shin ko ka san inda tagwayen Sadaukai suka talī?" Koda jin wannan tambaya sai hankalin Sarkin yaki ya dugunzuma ya kama kalle-kalle da waige-waige ya shiga binciken ko wani ya ga sa'adda su Jarumi Ililaru suka fita amma sai kowa ya ce bai gani ba. A dai dai wannan lokaci ne Yarima Hasnalu da Gimbiya lushaira ma suka fito daga cikin dakinsu. Koda suka hango laro an yi cincirindo an zagaye Gimbiya Suzaila sai hankalinsu ya dugunzuma suka karaso wajcn da gudu. Da zuwansu sai Suzaila ta dubcsu cikin damuwa ta ce, "Dakaruna guda biyu da baiwarku daya sun karya dokarmu ta cewar kada kowa ya fita daga cikin gidan nan, lallai sun sulale sun fice daga cikin gidan, saboda haka bamu da sauran kwanciyar hankali dole nc yanzu mu lafi neman wadannan 'yan uwa namu, amma ni kadai nake so na fita bana son kowa ya bini domin ina ji a jikina cewar akwai mugun tanadi da mutancn kauycn nan suka yi mana mai hadarin gaske". Koda gama fadin hakan sai Gimbiya Suzaila ta mike tsaye da sauri ta juya za ta nufi inda dokinta kc daure cikin hanzari Sarkin yakinta ya sha gabanta ya ce, "Ranki ya dade ba zan iya barinki ki tafi ke kadai ba domin idan wani abu ya samcki ba tare da na gani ba, idan na koma Birnin Lairuf ban san abinda zan gayawa mahaifinki ba. Zai iya fusata ma ya sa a hallakani saboda ya gargadeni kafin mu baro gida ccwar duk inda za ki fuskanci wata masifa na tabbatar da cewa ina tare da ke." Lokacin da Gimbiya Suzaila taji wannan batu sai jikinta ya yi sanyi domin ba ta da ikon ta hana Sarkın yaki binta. shi kansa Yarima Hasnalu hankalinsa ya dugunzuma ainun da yaji ccwa Suzaila za ta fita neman Dakarunta nan take yaji cewar ba zai iya zama ba ya jira lokacin da zata dawo ba, saboda zai kasance a cikin fargaba da zullumi saboda rashin sanin balin da takc ciki Kawai sai ya budi baki ya cc, "Ai ina ya kamata na bika mu tafi tare tunda baiwarmu guda daya ta bace." Koda jin wannan batu sai Suzaila ta dubcshi tayi murmushi ta ce, "Shin kara son ka fita farautar ajalinka ne? Ka sani cewa kai ba Jarumi banc saboda me za ka siyar da rayuwarka a banza?" Hasnalu ya maidawa Suzaila nartanin murmushia muguntar da tayI Inasa yà cc, "Dalilin da ya sa ita baro gida na biyoku iZuwa wannan taliva mai hadari shi ne zai sa na biku a yarzu tunda duk a cikin aiki muke". Koda jin wannan batu sai Gimbiya Suzaia ta kyalkyale da dariya ta ce, "Hakika duk abinda ka fada gaskiya ne don haka duk wanda ma yake ganin zai ya binmu ya biyomu ban hana kowa ba". Nan take Suzaila ta ruga izuwa irida dokinta yake ta kwanceshi ta hau. A guje Sarkin yakinta, Hasnalu da Lushaira ma suka ruga izuwa inda nasu dawakan sukc suka hau. Nan da nan aka bude musu kofar gidan suka fice cikin azababben gudu tamkar za su tashi sama. Abin tambayar anan shi ne, "Ina suka dosa, ina za su Je sU ga tagwayen Sadaukai su Jarumi Shalaru da baiwar da ta bata " AA Misau ke Magana Da yake Suzaila ce akan gaba kawai sai ta zamo 'yar Jagorarsu duk inda dokinta ya dauke Sanya nasu. dauke sawu anan suke Kamar Suzaila ta san înda ya kamata su je kawai sai Ta durfafi hanyar fadar Sarki Labarazu duk da cewar bata taba zuwa ba kuma ba, kuma bata san a inda takc ba. Abinka da wanda ya taso a cikin gidan saraua, Suzaila tana la'akari ne da irin yanayin alamomi na hanyar da zata kaisu izuwa fada. Ai kuwa suna cikin tsala gudu ne suka hango gidan sarautar. Tun daga ncsa suka hango Dakaru sama da mutum dubu zaratan mazaje a tsaitsaye. rike da muggan makamai suna gadin gidan. Nan take Lushaira da Yarima Hasnalu suka firgicc suka tsorata ainun da ganin wadannan zaratan Dakaru masu kwarjini da ban tsoro. Suzaila da Sarkin yakinta kuwa ko gezau ba su yi ba. Maimakon ma su rage karfin gudun dokinsu sai suka kara kaimi. Koda ya rage saura bai fi taku goma ba tsakanin su da kofar gidan sai wasu daga cikin Dakarun da ke tsaron gidan suka taso rikc da dogaycn masu suka tare hanya. Bisa dole su jaruma Suzaila suka ja linzamin dawakansu suka yi turjiya. A sannan ne Shugaban Dakarun gidan sarautar ya ratso ta cikin 'yan uwansa yazo gaban su jaruma Suzaila Ya yi tsayuwar takama irin ta manyan jarumat ya đubesu va ce, "Su waye ku? Mene ne yake tafe da ku ga Sark i aihalin ba a san da zuwanku ba?" Koda jin wannan tambaya sai Suzaila ta dubi Shugaban Dakarun ta ce, "Ka jc ka gayawa Sarkinku cewar ya bani mutanena guda uku da suka bace Ka shaida masa cewa ni ce jarurma Suzaila Sarkin yakın Bimin Lairuf. Idan bai bani mutancia ba ty va sani cewa ran dayansu dai-da: yake da ran gaba dayan jama'arsa. Idan daya daga cikin mutanen ya rasa rayuwarsa to sai na share mulkinsa daga doron kasa". Koda jin wannan batu sai gaba dayan Dakarun gidan sarautär suka fusata ainun suka yunkuro za su afkawa su Jaruma Suzaila da vaki amma sai Shugaban nasu ya daka Imusu tsawa suka fasa. dubi Dakarun ya Shugaban Suzaila cikin girmamawa ya ce, "Ya ke wannan 'yar Sarki ki saurara na jc na shaidawa Sarki wannan sako naki" Koda garma fadin hakan sai ya juya ya koma da baya ya shige izuwa cikin gidan sarautar. Jim kadán bavan shudewar wadansu 'yan dakiku nasu yawa sai kawai suka ji kasa ta kama girgiza, nan take kuma suka ji wani irin takun sawu mai karfi da kara mai ban tsoro tamkar giwa ce ke tahowa. Cikin hanzari Dakarun gidansarautar gaba daya suka dare suka samar da hanya. Koda jaruma Suzaila tayi arba da abinda ke shirin tunkarOSu sai tà razana ainun duk da ccwa ta kasancc gawurtacciyar jaruma waccc ta yaki bakar macijiya ta kogo da kuma sihirtacciyar halittar kogi sai da zuciyarta ta buga da karfi ta razana ainun saboda tayi arba ne da wani irin mutumn mai kira ta matukar ban tsoro. Mutumin ya kasance dogo zan kalele tamkar bishiyar dabino, sannan kaurin hannayensa tamkar na katon reshen bishiyarr kuka ne, kuma gaba dayan jikinsa a murde yake kamar dutse Gashi ya kasance mummunan gaske tamkar an yi kumalloa kasa. Ko riga babu a jikinsa, kirjinsa a cike yake da gashi tamkar na Zaki, babu komai a jikin nasa face wani walkin tsafi kuma ya rataya wata zabgegiyar takobi a bayansa sai muzurai yake da jajaycn idanunsa tamkar an gasa dan buda a cikin wuta. Nan fa aka yi kallon-kallo tsakanin wannan shirgcgen mutum da Gimbiya Suzaila na tsawon 'yan dakiku sannan mutumin ya takarkarc ya bushe da mahaukaciyar dariya mai kama da amon tafasasshen dutse ya dakawa Suzaila tsawa ya ce, "Ke karamar tsagera ki yi sani cewa yau sa'arki ta kare donin kin shigo cikin ramin da bashi da kofar 6ullewa face ta kushewa. Yau za ki dandana ruwa mai mugunyar dacin da baya kashe kishirwa. Topa Nima AA Misau Jin Wannan Bayani Yasa zan dakata a nan sbd kar Nima nasha wannan ruwa hhhh Karku Manta Da bibiyarmu ta wannan shafukan WhatsApp https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30Q Facebook page https://www.facebook.com/profile.php?id=100063661782295 Facebook page https://www.facebook.com/AlaminGuyson?mibextid=3amO3DAFELuS4Abp Saikuma Shafin Matashin Marubuci Yusuf imam https://www.facebook.com/profile.php?id=61553596297488 Saimunzo Singn Admin AA Misau ke MaganaBUSA A MUTU Littafi Na Shida (6) Part B Na Abdulaziz Sani M Gini AA Misau ke Magana Labari Ya Isowa Shagala Cewa Marubucin Yaci gaba Da Cewa. . Ni ne turbuya mai rubar da yaro da babba, bana barin kashi da tsoka bare fata mai saukin da-ya Ni ne ruwa maganin wuta wanda bashi da adadi. Ni ne beri wanda ba a kwasheshi dai-dai, kuma ni ne santsi mai kada kato komai girmansa. Ya ke wannan karamar shu'uma tun da har kika tako da kafalfunki kika zo mana nan da rashin kunyarki, to ba ba zamu boye miki komai ba Tabbas 'yan uwanki mutum uku suna hannunmu a tsare kuma ba za mu baku su ba face mun shayar da jininsu ga Dodo abin bautarmu. Kuma da ku ka kawo kanku nan duk rabon Dodo za ku zama. Kafin Sarki labarazu ya gama rufe bakinsa tuni Suzaila ta zare takobinta ta daka tsalic a sama, ta kuwowa Sarki Labarazu mummunan sara a wuya da nufin ta sare masa kai. Cikin zalin nama Sarki Labarazu ya sunkuya takobin la ta ta sari iska, kalin Suzaila ta dirgo kasa a bayansa tuni ya zare sharbebiyar takobin da ke bavansa ya kai ma ta wawan sara. Duk da cewa Suzaila ta wurkila jikinta ta kauccwa saran ai da kaifin takobin tasa ta dara suiken yakin da ke jikinta tamkar an sa wuka an yanka tuffa ta rabe gida biyu. Hakan ma bai rabu da ita ba sai da shima ya daka tsalle ya tareta a sama ya gabza ma ta naushi a fuska. Saboda karfin naushin sai da tayi katan tanwa sau uku a lokacin da wani gudan jini yai fitar burgu daga cikin bakinta ta fadi kasa a matukar galabaice. Koda Sarkin yaki, da su Yarima Hasnalu suka ga abinda ya faru ga Gimbiya Suzaila wacce suke takama da jarumtakarta sai hankalinsu ya dugunzuma ainun. Yarima Hasnalu dai bai san sa'adda ya zare takobinsa ba ya diro daga kan dokinsa ya ruga da gudu izuwa kan Sarki Labarazu domin ya kare rayuwar Suzaila saboda a lokacin Sarki Labarazu ya nufi inda take kwance tana numfashi sama-sama yana rike da takobi a sama da nufin ya yi ma ta kisan gilla. Koda Gimbiya Lushaira ma ta ga dan uwanta ya sai la rayuwarsa don ya ceto ta Suzaila sai itama ta sauko daga kan na ta dokin ta ruga inda ya ruga domin ba za ta iya kallon mutuwarsa ba. A wannan lokaci ne shina Sarkin yakin Suzaila ya yi Rundunbala ya kai musudauki. Saura kiris! Sarki Labarazu ya sa takobinsa ya tsarge Suzaila gida biyu sai kawai yaji gudun takun sawu a bayansa. Koda ya waigo ya ga ashc mutum uku ne suka durfafoshi maza biyu mace daya, sai ya juyo garesu yana mai murmushin mugunta shima ya falfalo da matsanarcin gudu izuwa kansu cikin mugun nufi. Tabbas ya san cewa yana riskarsu zai yi musu kisan gillah a lokaci guda su duka, daga sama aka cilloshi ya baiyana a sama dal dai sarki Labarazu Nan. take mutumin yasa kafarsa guda, ya doki kiriin Sarki Labarazu. Saboda karfin dukan sai da sarki Labarazu yai sama ya gwàru da ginin katangar gidan sannan ya fado kasa yana aman jini kasa sai gaba dayan, Dakarun Sarki Labaràzu suka ja da baya cikin tsananim tsoro aka rasa wanda zai tari mutumin.Babban abinda ya, daurewa su Hasnalu kaishi wannan mutum da ya kawo musu, đauki tsoho ne saboda tsufa ma ya rankwafa yai doro kuma habu wan makania hannunsar face wata 'yari gajeiyar sanda da ya dogara bisa kasa. Gaba dayan gashin kan tsohon gemunsa da gushin bakinsa duk fari ne fat saboda tsufa. Fatar jikinsa gaba daya ta yamutse, kallo daya, za ka yi masa ká san cewa ya. Tsufa ainun Lokacin da SarkiLabarazuyasagokai ya yi arba laiwannan tsohorsa'adda yake yin aman jini sai ya mike Tsaye zumbur cikin tsananin fusata ya kwarara wani uban ihu ai stsananin firgitärwa wanda ya: haddasa, karamar girgizar Rasa Gaba dayan mutanen da sarkl suka, tsugunna kasa suka dunkule jikinsu saboda razanar da Maatakin Gini Y amma banda wannan tsobo. kawai Byara Isayuwarsa ma ya yi suka ci gaba da kallon-kallo tsakaninsa da Sarki Labarazu. Kamar hadin baki sai Sarki Labarazu da wannan Isoho suka rugo da gudu izuwa ga junansu suka kacame da azababben yaki. b a Wohoho! Nan fa Gimbiva Suzaila da ke zaunc a kasa magashiyan bakinta na yoyon jini ta dago kai ta Zubawa Jaruman biyu idanu tana kallon abin al'ajabi abinda ya fi burgcta a rayuwarta wato zarton Jarumi. Sarki Labarazu ya wanzu yana mai kaiwa tsohon sara da suka cikin tsananin zafin nama, kuma da dukkan karfinsu sai gushi tsohon yana karewa da wannan sanda ta hannunsa. Abinda ya iara baiwa kowa mamaki a Wajen shi ne, sandar da ke hannun tsohon ta ice ce amma gashi takobin Labarazu ta kasa datsata. To wai shin ma shi wannan tsohon Jarumi mutum ne kuwa? Tambayar da Gimbiya Suzaila ta yiwa kanta ke nan a cikin zuciyarta kuma ta kasa baiwa kanta amsa, Sai da aka shafe kusan rabin sa'a ana wannan artabu Sarki Laburazu bai sami nasarar koda lakutar jikin Tsohon ba, kuma a sannan ne takobin hannunsa duk ta dakushe, gaba dayan kaifinta ya disashe saboda yawan goguwa da sandar tsohon. Cikin fishi Sarki LabaraZu ya ja da baya takobinsa sannan ya yi nuni da hannunsa Tsohon. yai jifa da izuwa ga Take wata irin guguwa mai karfi ta fito daga cikin hannun Labarazu ta nufi kan tsohon. Koda guguwar ta isa daf da tsohon sai ta tsava cak ta kasa cutar da shi sakamakon wani abu da yake karantrawa a cikin bakinsa. Nan take guguwar ta koma kan wanda ya turota la dagashi sama tayi wurgi da shi ya maku a jikin ginin gidansa. Saboda karfin makuwar sai da ginin katangar gidan ya rushe Shi da ginin suka zube kasa. Amma saboda tsananin karfi da juriya irin ta Sarki Labarazu sai ya sakc mikcwa tsayc zumbur ya kwarara uban ihu a karo na biyu ya rugo izuwa kan tsohon suka kacame da sabon masifaffan fada ya zanana ccwa suna kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama, juriya da bajinta. Ita dai Gimbiya Suzaila bata san sa'adda la gyara zama ba tana kallon abin manmaki. Abinda yafi bata mamaki shi ne, ya ya aka yi wannan tsoho yake

Chapter 1 of 4