Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 5
nimbras irin be Santa din Nan ba yace"wanan ai tayi kankanta a aiki saidai gyaran dakin yarima, dama kuwa nafeesat tace"Bata son wanan kattin suna zuwa me d'aki itace dai'dai" Ummi ta kalli nimbras tace"wani Aiki Kika iya?ya kuma na ganki da goyo?" Mama ladi tace"ayya ai Bata Jin hausa shuwa ce" Ummi tace"tunda Sudan ne ai zata ji larabci " Ummi ta Mata larabci Nimbras harda murmushi ta sauke ajiyar zuciya ta Bata amsa sai da ta d'aga hanun kawu ya gan zoben yarima a hanunta besan ya akayi yayi Mata ashe inne ce ta Kai aka rage mata Wani numfashi yayi be son ummi ta gani itako Bata Lura ba ummi tace"mashaallah yariya tayi kawai ki Fara koya Mata aikin daya dace da ita Ummi ta mike da larabci tace",kawo shi"Dan ji tayi tana son ta amshi A'med Dake kuka"Bata shi nimbras tayi....ummi ta kurawa yaron Ido tana Jin wani feelings Da sauri Mama ladi tace"kaninta ne" Jinjina Kai tayi shima dai kawu kallon Amed yake,ummi tace"zaku iya tafiya ku barshi nan Nimbras ko Taki tafiya...kawu yace"ikon Allah yaron Nan da shiga Rai yake kammaninsu daya da Ahmed da Yana yaro " Ummi dai Bata ce komai ba Kuma Taki bawa nimbras BΓ yan kwana uku Mama ladi ce a b'angaren yarima da ummi ta Basu makulli tana nunawa nimbras inda zata dinga gyara b'angaren dukda basa fahimta yaren juna nimbras natsuwa tayi tana kallo a kwana biyar kacal ta gane komai har mamaki mama ladi take...Bata San wahalar rayuwa yasa ta iya aikin manya ba yawanci aikin ta iya Da asuba yau ta fito da goyon A'med zata b'agaren yarima sai sauri take a hanya ta had'u da yarima aliyu ya bita da kallo yana mamakin ita wacece Itako gaidashi tayi inda ta gan sauran bayin nayi tayi wucewarta Tana zuwa ta sauke A'med a gadon yarima ta tFara goge gaban mirrow tanayi tana Hira dashi tana magana harda kyakyatawa shiko sai kiriniya yake Yana gwarancinsa Jingina tayi da mirrow tana me tafi sai gashi Yana rarrafowa taje da gudu ta fad'a saman gadon ta kyalkyale da dariya tana ja me kumatu Wasa Suka farayi tanawa A'med cakulkuli Yana kyalkyale dariya sai ta Haye gadon tana tsalle Dan Bata da buri kamar ta gan shi cikin farin ciki Tana cikin tsalle A'med da ko tashi ba yayi sai kokarin tashi yake idanunta ya sauka Kan mutum jingine da kofar ya rungume hanun idanunsa a kanta Dai'dai nan aka turo kofa Gimbiya nafeesat ce ta tsaya tanawa nimbras kallon raini bala'i na cinta Nimbras ta duro daga gadon kallon da suke Mata yasa ta Maman Nur [8/21, 11:28 PM] MAMAN NOORUL HUDAH Writer: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„ *_YARIMA AHMED_* πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹ _By maman noorul_ _Hudah_ _Paid book_ πŸ…Ώ1️⃣7️⃣-1️⃣8️⃣ Bismillahir Rahmanir Rahim Nafeesat tace"what? Baby who is this har cikin bedroom dinka" Shiko a bangarenshi he was shock but bazaka gane ba a tunaninshi mafalkin daya saba ne because this is the girl with a baby that always appear in his dream Tsawar da nafeesat ta dakawa nimbras da ke rude yasa ya gane abinda ke faruwa ba mafalki bane Rikicewa yasa nimbras jiki na rawa ta Fara kokarin daukar A'med da ya birkice Yana tsala ihu sai dai kafin ta daukeshi nafeesa da zuciya ya dibeta ta je gadan-gadan zata Kai Mata duka jikinta duk rawa yake nimbras tayi hanzarin kaucewa sai karkawa take Jiki na rawa ta dauki A'med ta rungume tunda take ta gan tashin hankali but Bata tab'a Shiga irin wanan ba Cikin yare take Basu hakuri Nafeesa ta Kai hanun ta shaketa tace"how dare you Zaki Shiga bedroom din mijina waye ya turo ki?" Nimbras ta shaku idanunta sun firfito Amma Taki sakin Amed D'auke Kai yarima yayi baka gane yanayinsa ya Zo gaban mirrow ya zauna as if the 2 of them don't exist ya shafa cream sanan ta koma toilet be Jima ba ta fito da jallabiya ya gan har yanzu nafeesa Bata saki nimbras ba duk karfinta ya Kare ta Fara slum Rintse Ido yayi badan ya so ba yace"feena you are disgusting gaskiya yau kin zubda kimarki a idona you are fighting with a servant for what exactly? " Maganarshi yasa nafeesa sakin nimbras tayi Baya sai jikin mirrow takarcen sama Suka watse...a'med da har ta sadakar zaiyi kasa yarima yayi saurin kamoshi,ya rungume Mari ya saukewa nafeesa yace"how dare you meyasa baki da human feeling what do you have against this poor girl?* Kallonshi tayi da shock tace"baby you slap me saboda wanan slave din??"she can't believe Prince slap her face because of a slave Shiko be sake kallonta ba ya cigaba da lallashin Amed Yana Jin son yaron na shigarsa A fusace nafeesa ta bar bedroom din nimbras da duk ta galabaita ta fi minti goma tsaye a gu d'aya kafin ta d'aga Kai ta kalleshi daga sama har idanunta ya sauka yatsunsa dake sheki alaman Hutu ta gan babban yatsarsa yayi stain da wani syrup dake saman mirrow duk ya b'ata wuri alamun da aka turo ta kayan Suka wargaze ne ya same sa Zaro Ido tayi a tsorace ta mike da k'yar tana Jan kafa ta karasa gabansa sai yanzu ya kalleta yayi Mata kallo daya ya d'auke Kai Dukawa tayi da guiwowinta ta saka hanun a hullanta ta zaro dogon sumanta data kisa bakin ta duka kamar wacce zatayi sujjada be Ankara ba yaji tana goge stain din da sumanta tana hawaye Ji yayi kamar an kwara me ruwan sanyi ya rasa kuzarin shi so yake ya janye kafarsa ya kasa sai ya zuba mata Ido this is the highest respect,by this act tana nufin ta kaskanta da kanta a gabanshi ta yarda shine master Wani numfashi ya ja ana girmamasa but ba a tab'a Masa irin wanan ba duk sai yaji b'acin ransa ya ragu D'agowa tayi ta kalleshi ta had'a hanunwanta alamun ban hakuri Besan sanda ya lumshe idanunsa ba ya bude su akanta ta mike ta Kai hannu zata amshi A'med yayi Mata banza kamar be Gane me take nufi ba itako mamaki ne ya kamata inda A'med din ya sake Masa Yarima yayi hanyar fita falo dashi a zaton ta zaije ya hukunta ta ne through yaron sai ta fashe da kuka Amma Kuma Bata bisa ba Saida ta ci kukanta ta koshi ta mike jiki ba kwari ta gyara d'akin ta d'au lokaci kafin ta Gama gyaran dakin ta Shiga ta wanke toilet ta fashe ko Ina da freshener ta fito falo Gabanta ne ya fadi ganinshi kwance a kujera A'med a cikinsa yayi bacci shima da alamu baccin yake Ta karasa ta tsaya a kansa ta rasa ya zatayi ta d'au A'med din kartayi laifi Amma gaskiya bazata iya barinsa ba dashi zata tafi Ta Kai hanun zata d'aukesa sai ta janye da wuri,tayi haka yafi kusan so biyar kafin tayi karfin halin daukarsa ta Kama hanunsa kenan Yarima ya bude Ido a rike ce ta janye jikinta na rawa Cikin yare tace"na Gama aiki ne Zan tafi?" Kallonta yake a tsanake ya Gane she is in pain tare da ganin karfin halinta Abinda yayi shocking dinta shine da yace"toh tafi Mana"cikin halshen larabcinsa me kyau ba nata broking ba Ta zaro Ido Amma ko kallo Bata ishesa ba ya mike rike da A'med ya shige ciki Binshi tayi Amma Yana Shiga ya turo kofa sai ta fashe da kuka ta zauna a laulausan carpet din tun tana jiransa har baccin wahala ya d'auketa Nafeesa ce ta It a paid book 300 for regular,vip 500 via 2378022567 Aisha Mohammed Zeinith bank Wanda Basu da account kuma zasu iya turo mtn card for more information 09090112846 Maman Nur [8/21, 11:28 PM] MAMAN NOORUL HUDAH Writer: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„ *_YARIMA AHMED_* πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹ _By maman noorul_ _Hudah_ _Paid book_ Yau dai bari in kokarta inyi so biyu anty shamsiyya tace littafin ya Kai Mata linta πŸ…Ώ2️⃣1️⃣-2️⃣2️⃣ Bismillahir Rahmanir Rahim Washe gari Da k'yar ta iya tashi tayi sallah asuba saboda idanuwanta da sukayi Mata nauyi ga Kuma ciwo da take ji na Mara Wanda yau kwana uku kenan yakan zo ya sake ta ga bacci da ciwon Kai Sai dai Bata dade da komawa ba mama ladi ta tashe ta cikin tausayawa domin tasan Bata samu bacci kirki ba jiya ta bude idanunta da suke kumbure saboda rashin bacci,ta rigada tasan aiki ne Ta mike zaune ta gan har mama tayiwa A'med wanka ta shiryashi sai kamshi yake ta same turarukar da inne ta had'a musu har ta so yayi me karfi yayi ta atishawa Da k'yar ta tashi mama ladi tace"kiyi hakuri Yar nan kije ki Gama aiki ki dawo sai kihuta kinji " Bata ce komai ba ta shige bayi tayi wanka ta fito ta gogawa jikinta humra da inne ta Bata irin tasu ta Sudan ta saka doguwar Riga ta d'auki A'med dake nuna Mata hanun ta daukeshi ta Goya ta saka hijabi ta fita tana sauri Mama ta bita da kallon tausayi Koda ta fito ta gan mutan gidan sunyi busy ma'aikatan sai Kai komo suke masu decoration nayi hakan ya tabbatar mata akwai wani bikin da za ayi sai Kuma zancen jiya ya dawo Mata Rai Ta zo dai'dai zata wuce maid quarters din masu abinci ta juyo ana yarensu abin ya Bata mamaki ta koma ta hango wata budurwa ce tsaye tana sanye cikin uniform tana waya Murmushi nimbras tayi ta wuce Dan Bata tab'a tunanin za a samu masu Jin yarensu ba a nan dukda tasan ana samun masu Jin larabci but pure shuwa yana wahala Tana kokarin Hawa stairs din daya banbanta katafaren b'agaren yarima Aliyu dana Ahmed domin na ahmed na hagu ne na yarima Aliyu na dama sai taji ta bige mutum A tsorace ta janye ta duka tana gaida shi cikin ladabi Ya washe Baki yana mamakin ita din wacece Yana kokarin yin magana amaryarsa ta sauko hakan yasa ya d'auke Kai daga gareta itako tayi ciki yabita da kallo a sace Yarima Aliyu girman turai ne Rabin rayuwrsa a can yayi ba tarbiyya ne dashi ba balle da gimbiya Zenabu ke nuna Masa shi dan sarkine Yana da ikon take kowa yayi duk inda yake so,Yana da d'abi'ar bin Mata mussaman kananun Yara Duk abinda ya faru yarima Ahmed na daga dakinsa Yana kallo ta window Da sallama nimbras ta tura kofa babu kowa falo sai kamshin da sanyi a/c dake tashi Sanyi da d'akin ya d'auka yasa Bata sauke Amed Ba ta Fara aikinta harta gama ta nimi wuri ta zauna tana jira ya fito falo ita ta Shiga bedroom saidai shiru a zaune ta Fara gyangyandin Shigowar feena tare da wata maid na biye da ita da had'adiyar basket a hanun yasa ta bude Ido ta gaida nafeesat da ko kallonta batayi ba suka karasa dining area aka jera breakfast din sanan nafeesat ta Shiga bedroom ba a Jima ba sai gashi sun fito tare rike da hanun juna Fuskar Nan tashi murtuke yake ya karasa dining " Ta mike ta karasa cikin ladabi da dukar da Kai irin na Yan sarauta tace"Ina kwana" Be kalleta ba hakan yasa ta juya ta Shiga bedroom din Nafeesat ta bita da kallon tsana tace"I mean meyasa sai itace zatayi maka aiki" Yace"what is your problem nafeesat?? yariyar Nan dai yariya ce Wanda babu ko nono kirjinta in Zan bi mata kina tunanin Zan bita ne, this act of your is a insult to me haba,Ni ban gan matsalantar ba tunda she is doing her job perfectly fiye da previous once" Tace"you are even praising her prince wallahi bana sonta I don't have a good feeling about her kawai a koreta"be sake kulata ba yayi breakfast dinsh Nafeesat ta tashi tana duba wayarta dake ringing tace"bari in je in dawo zanyi magana da dad Dina" Ya jinjina Mata kai,Yana fita ya Shiga bedroom din Bude kofar yasa nimbras juyawa da sauri ta karasa ta d'auki A'med dake zaune ta ajiye me wani kwali Yana Wasa Zata sakashi a baya yayi hanzarin zuwa ya amshe shi ta kura me Ido cikin Sanyi murya cikin yare tace"ka bani in Goya shi karya b'ata maka Kaya ranka dade"be nuna ya fahimci abinda ta fad'a ba saima daga rigar Ahmed da yayi yace" he has a fever me kuka bashi ya Sha?? " Girgiza Kai tayi Dan Bata fahimce me yace ba,tsaki yayi yace"you are useless wallahi I wonder who gave you yaron Nan kike wahalar dashi I need to Called a doctor "ya Kare magana Yana latse waya itako ta kasa cigaba da aikinta ta tsaya tana kallonshi kamar tv,ganin kallon yayi me yawa yasa ya gwalo Mata Ido sai tayi murmushi tana b'oye fuska Shima murmushi yayi but be Bari ta gani ba...zama Tayi a kasa ta tankwashe kafa kanta a duke yayi ta kallon kafafuwarta da yatsun kafar ya lumshe Ido Itako tana son fad'a me maganar da ta ji jiya Amma ta rasa taya Bata manta maganar inne akan babu ruwanta da abinda ya shafi gidan sarauta gidane da ba a musu shishigi Ba a Jima ba wani young Dr ya shigo yarima ya kwanta da A'med ya kalli Dr Fahad cikin French yace"yaron nan zaka duba" Dr Fahad ya kalli nimbras yace"ranka dade Bakuwa mukayi Ne?"wani kallo yarima yayi me da sauri ya karasa ya duba shi yace"Zan Aiko da magani malaria ne"duk maganar Nan da yikeyi idanunshi na Kan nimbras Yace"ko Kuma yariyar ta bini ta amso maganarnin gidan yau a cike yake zatayi saurin dawowa" Ko kallonshi yarima beyi ba ya gaji ya fita Yana waigen nimbras da Bata San ma ko wani Abu nafaruwa ba karanta ke murd'awa hawaye ya wanke Mata fuska so take ta koma ta huta kila ya d'an saketa Cikin yare tadubeshi shima Ido ya zuba Mata ganin tana kuka tace Maman Nur [8/21, 11:28 PM] MAMAN NOORUL HUDAH Writer: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„ *_YARIMA AHMED_* πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹ _By maman noorul_ _Hudah_ _Paid book_ πŸ…Ώ1️⃣9️⃣-2️⃣0️⃣ Bismillahir Rahmanir Rahim Nafeesa ce ta shigo ta Zo ta bashi hakuri saboda inda ta gan fushi abinda tayi a kwayar idanunshi saidai zatayi maganin yariyar nan cikin ruwan sanyi akanta har prince zai mareta hmmm abinda be tab'a faruwa ba Ganin nimbras zaune tana bacci yasa ta d'anyi turus da mamaki a ranta tace"Wai wacece wanan mayya"ta karasa zatayi ball da ita ko me ta tuna oho sai kawai tayi bedroom din Gabanta ne yayi mugun fadiwa ganin yarima kwance A'med na samanshi Yana Wasa Ta kurawa d'an Ido tana Jin wani yanayi,soyyayar yaron ke niman wuri a zuciyarta Amma kishi da bakin Hali ya rufe Mata Ido ta girgiza Kai zuciyarta na Raya Mata mugun abu A fusace ta karasa ta fisgi yaron zatayi wurgi dashi sai ta kasa,shiko A'med ya firgita sai ya fashe da kuka Kukanshi ne ya tashe yarima har nimbras dake falo ta mike da wuri ta Shiga d'akin Yayi ta bin nafeesat da wani kallo hakan yasa jikinta sanyi ta ajiye Ahmed a kasa da sauri nimbras ta karasa ta daukeshi Bata yarda ta kalli kowa ba ta juya ta Kai kofa ta ji yace"dawo dashi?"ba hausar take ji ba dan Haka Bata tsaya ba tayi wucewarta tana hade kafafunta " Nafeesat ta kalli yarima bala'i na cinta tace"what is happening yarima is there something you are not telling me,miye had'in ka da slave da har zaka Dake ni akanta " Kamar bazai amsata ba yace"are you high?who are you to question me" Cikin tsawa tace"your wife prince ahmed,iam your wife I have the right to question abinda na gani ban gane ba' Zuba Mata Ido yayi sai Kuma ya bar wurin zai shiga toilet ta Sha gabanshi tace"wallahi sai ka bani amsa aure kayi ne ban sani ba ko kuwa wa'yanan kauyawar kakaninka na kasar Nigeria have succeeded in getting you marry to a village......"ratsata yayi ya shige toilet ba tare da yace Mata komai ba dan magangnunta be dame shi ba kamar inda nimbras tayi disrespecting dinshi yace ta tsaya har tana da gut din wucewa who is she by the way,he will sure deal with her wallahi Zama nafeesat tayi ta dinga durzan kuka har ya fito Yace"nafeesat kina tuna Azhan kuwa?" Tace"Ni uwa ce Taya Zan mance d'ana Wanda aka rabani dashi" Ya karaso ya duka gabanta ya d'ago hab'arta yace"I don't think so, inda kina tuna shi you will have compassion for baby's may be through kaunar da Zaki nunawa d'an wani Allah ya tausaya Miki ya bayyana naki feena,our child could be alive someone,he could be close to us and seeing this girl with this baby wallahi I felt as if he is my Azhan" Tace"this dirty boy could never and will not be my Azhan baby what are you saying Azhan with this dirty girl please don't said that " Ya mike ya tafi gaban mirrow yace"it useless talking to you" Mikewa tayi ta rungumeshi ta Baya tace"baby I don't like her a kore ta" Da murmushi a fuskarshi yace"ai bani na kawo ta ba ai"dawowa gabanshi tayi zatayi magana yace"please nafeesat I need re....."Bata Bari ya karasa ba tayi kissing dinshi Kamar jira yake ya cafke bakin Nimbras na komawa d'akin mama ladi ta shiga tana maida numfashi ta dama kunu ta bawa A'med ya Sha ya koshi Mama ladi ta Zo zata daukeshi taki Bata...mama ladi dai na mamaki a tare bacci ya daukesu Da yamma kin komawa tayi ta zauna abinta mama ladi na son ce Mata bazata koma tayi aiki ba Amma ta rasa taya zata fad'a Mata Zuwa karfe bakwai jikin Amed yayi zafi alaman zazzabi sai kuka yake Mama ladi ta amshe shi ta Goya ganin duk jikin nimbras ya mutu da rashin lafiyarshi Magani mama ladi ta samo paracetamol ta bashi sai yayi bacci Sai kusan 10pm ya tashi jiki a mace wanka nimbras tayi ko kunu be Sha ba ya kwanta kawai sai ta hade Kai da guiwa tayi ta dirzan kuka Mama ce dai ta Goya shi jikin tsam ba Dadi Cikin dare wajajen 1am A'med ya tashi yayi ta kuka ga gidan tsit sai lallashin shi ake yaki shiru Mama tace"ko cikin shi na ciwo ne??" Itadai nimbras duk tayi wuri wuri yaki zuwa wajen mama tun mama na zaune har bacci yayi awon gaba da ita Nimbras ta goyashi ta rasa me zatayi me yayi shiru sai jijjjigashi take tana dukan bayanshi sai gyangyadin take Shiru ta ji alamun ya Fara bacci jira take yayi nisa ta kwantar dashi BΓ yan wasu mintuna ta kwantar dashi tana bugun bayanshi ajiyar zuciya ta sauke ganin baccinshi yayi nisa,iska ne ke shigowa ta window ta mike Dan ta kulle tana kaiwa ta gan shadow din mutane Tsoro ya kamata abinda ya Bata mamaki sai taji ana yarensu shuwa,Daman jiya taji wata Mata dattijuwa nayi Wanda ya saka riga me hula baka ganin fuskarsa yace"ki yarda Dani bana aiki da Wasa ko na farkon anyi nasara dan Saida na Kai yaron har garin mu Sudan sanan nayi creating accident a gabana motar ta tashi wanan shima ai har wani kauye naje na samu wani hatsabibi dan ayi nasara,ya tabbatar min in har tayi inda aka ce macijin ya same sa toh bazai rayu ba is a dangerous snake but turasa ake ranan da za a sake sa, ta fad'a me sunansa da kuma abinda take so yayi mata" Nimbras tayi kamar zata bar wajen sai Kuma ta sake lekawa iskan dake kad'awa ya sauke mayafin Kan jakkadiyar gimbiya Zenabu har nimbras ta gan fuskarta tana amsar basket din da ake Bata Gayen da Bata ganin fuskarsa ya bude basket din katotuwar maciji ne lafe jakkadiyar itama ta tsorata zata saki basket din yayi saurin kamawa Jakkadiya tace"kenan ranan zata sakesa? kasan taron jibi ne zata Kira sunan Yarima Ahmed din kenan so uku Kan ta turasa" Yace"kwarai kuwa ko mutane dubu ne a wurin wajensa zashi Kuma ya aiwatar da abinda aka sashi in Kuma aka nimi dakatar dashi toh fah zai halaka ko wanene so a kiyaye sai ta shirya zata sake sa" Nimbras ta dawo ta zauna bakin gado cike da tsoro jikinta har rawa take tasan macijin a garinsu inko shine toh akwai babban matsala sosai toh waye yarima Ahmed?meyasa ake niman ganin bayansa.... Nimbras Bata rintsa ba ta rasa waye xata fad'awa maganar Washe gari Maman Nur [8/21, 11:28 PM] MAMAN NOORUL HUDAH Writer: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„ *_YARIMA AHMED_* πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹ _By maman noorul_ _Hudah_ _Paid book_ Ga Mai bukatar biya is 300regular vip 500 via 2378022567 Aisha mohammed Zeinith bank for more information:09090112846 Last free page πŸ…Ώ2️⃣9️⃣-3️⃣0️⃣ Bismillahir Rahmanir Rahim Tuni tana kwance flat ko numfashi batayi sai kumfa dake fita a bakinta ga jinin dake fita a gun da aka halbeta Mutuwar tsaye yarima Ahmed yayi ya Kura Mata Ido,with shock Ummi ta hauro da gudu ta saki ihu ta duka gabanta,tana cewa,Wai babu masu taimako ne ku taimaka karta mutu please Wani tashin hankali me Kama da hauka ya shiga jakkadiya domin suman tsaye tayi ta kasa motsawa sai girgiza Kai take irin tana ganin kamar a mafalkin abin ya faru Jamila kawai ta mallaka a duniya duk duniya Bata da kamarta duk abubuwan Nan da take tanayi ne Dan ta tara dukiya su koma Sudan tayiwa yar'ta aure shine zata mutu?' Situation din yarima aliyu is very bad domin shi ko motsawa bayayi halbin a kirji ya samesa gimbiya Zenabu ta saki ihu Mai rikitarwa Yarima ya karasa gaban nimbras ya zube akan guiwowinsa be tab'a shiga tashin hankali irin na yau ba fuskarta da yayi fayau yayi ta kallo ya kalli kafafunta,tunanin abinda ya faru da ta zo aiki na dawo Masa ganinta yake in slow motion ji yake kamar zatayi magana ya rintse idanunsa Ummi ta girgiza Kai tace"Bata numfashi yariyar Nan . Mama ta karaso tace"Bata numfashi?kenan ta mutu kike nuf....."itama a rude tayi maganar" Yarima Ahmed ya kama hanunta Yana murzuwa shi da ka kallesa zaka San hankalinsa baya jikinsa ya Kai bakinsa goshinta yayi kissing ya Kama bakin rigarshi ya goge kumfa me hade da jini a bakinta maganar mama na ta mutu na dawo me kwakwalwa yace"yanzu sai ta mutu ummi?akan me zata mutu?me mama take nufi da mutu tana nufin ta mutu kenan?" Ummi tace"sai hakuri ai". Mai martaba

Chapter 3 of 5