Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 3
na nan tsaye a kansa suna aiki. Ko da jin wannan batu sai gimbiya Shumaira ta fashe da matsanancin kuka tana cewa, ya kai abbana kayi sani cewa ba zan iya yin rayuwa ba muddin ban sami soyayyar jarumi Imhal ba. Ko da jin haka sai tausayin Shumaira ya kama sarki taryan ya rungumeta a kijinsa kuma ya shiga rarrashinta yana mai kwantar mata da hankali kuma yana nuna mata cewar lallai zai yi iya ko karinsa wajen ganin cewar ta mallaki Imhal. Haka dai ya ci gaba da lallabata har likita ya bata. maganin barci ta sha. Sarki Taryan na rungume da ita a kirjinsa yana shafar gashin kanta barci ya sace bata sani ba. Sarki Taryan ya shimfideta akan gadon sannan ya kirawo wata babbar kuyangarta ya ce ta kula da ita sosai Nan take suka fice daga cikin Turakar ta gimbiya shi da likitan nasa. Suna isowa kofar harabar turakar ta gimbiya sai ya dubi likitan ya ce, tsawon sa'a nawa gimbiya zata yi tana barci? Likita ya ce a kalla sai ta shafe sa'a shida tana wannan barci. Ko da jin haka sai sarki Taryan ya yi ajiyar numfashi ya ce, dole ne na nemo jarumi Imhal a duk inda yake kafin gimbiya ta farka daga wannan barci in dai ba so nake ta rasa rayuwarta ba gaba daya. Ya zama dole nayi shiri da kaina na tafi farautar wadanda suka saceshi tunda Cimmasu.Sun kasa dakaına Nan take sarki Taryan ya sallami likita ya tafi sannan ya aika aje a kirawo masa sarkin yakinsa Zamaru. A daidai wannan lokacin ne alkalan gasar kambun jaruntar suka rugo da gudu izuwa gaban sarki Taryan suka zube kasa suka kwashi gaisuwa sannan suka mike tsaye suna masu sunkui da kawunansu Kas. Babban cikinsu ya risina ya ce ya shugabana yanzu menene abin yi, wane hukunci zamu yanke akan wannan gasa? Ko da jin wannan tambaya sai sarki Taryan ya bushe da dariyar mugunta, al'armarin da ya yi matukar baiwa alkalna gasar mamaki kenan. Daga can sai sarki Taryan ya murtuke fuskarsa ya dubi shugaban alkalan ya ce, ku kwantar da hankalinku ku sani cewa sarki Gurzalu da jarumi Imhal ba su mutu ba yanzu nema za a fara wannan gasa, duk abin da akayi a baya somin tabi ne. yanzu ne8 a sarmi kazaman kudade a cacar da akeyi saboda ma zuwan bakon jarumin da yake son fafatawa da wanda ya yi nasara tsakanin Gurzalu da Imhal. Yanzu na gano wadanda suka tura a kashe jarumi mhal har cikin dakin da muke tsaresh ida amma ba zan baiyana su ba yanzu har sai an gama wannan gasa. Ko da jin wannan batu sai mamaki da tsoro ya kara turnuke alkalan gasar, shugaban nasu ya sake dubna sarki Taryan ya ce, ya shugabana shin yanzu ba ka tsoon cewa wadanda suka kaiwa Imhal hari a wancan karon su ne suka saceshi a yanzu? Ko da jin wannan tambaya sai sarki Taryan ya sake bushewa da dariya a lkaro na biyu sannan ya ce, ko kadan ba su bane su ka sace jarumi Imnal ba amma nasan ko su waye. Abin da zan gaya muku yanzu shi ne daga yau na sauya jarumin gasata. Wannan sabon jarumin da ya shigo gasar shi zan zuba dukkan kudin cacata a kansa. Ko da jin wannan bat sau mamaki ya dada kama alkalan gasar domin gani suke yi kamar sarki ya saki reshe ne ya kama ganye tunda ba a san irin sa'ar ba, jarfin wannan sabon jarumi damtsensa kawai aka sani. Nan dai sarki Taryan ya sallami alkalan gasar sannan shima ya tafi izuwa cikin turakarsa da sauri ya kimtsa sannan ya fito ya hau doki shi kadai jal ya fice daga cikin gidani sarautar ya nausa cikin daji ba tare da wani ya shaida shi ba saboda yayi badda kama yayi shiga irin ta dakarunsa. Al' amarin su jarumi Salmanu kuwa lokacin da suka bacewa dakarun da suka biyosu bayan sun dauke jarumi Imhal sai suka ruga izuwa cikin wani dogon dutse mai tsawo da duhun gaske suka shimfide jarumi mhal a kasa. Har izuwa wannan laokaci yana kakarin mutuwa. Nan fa Lamrita ta dada dimaucewa ta shiga kokarin zare takobin dake cikinsa tana kuka. Cikin hanzari jarumi Salmanu ya rike hannunta ya hanata zare takobin har sai da ya yi wata addu'a ya tofa akan raunin sannan ya sa hannunsa ya zare takobin. Nanfa Lamrita ta cika da tsananin mamaki saboda take jini ya daina zuba duk da cewar ramin raunin mai Zurfi ne SOsai. Salmanu ya bude jakarsa ya debo wani garin magani ya zuba akan raunin sannan ya kawo wani farin dogon kyalle ya daure raunin da shi tamau. Faruwar hakan ke da wuya sai Imhal ya daina kakarin mutuwa kuma barci ya daukeshi. Nan take Salmanu ya sake karanta wadansu addu'o'in ya tofawa Imhal sannan ya dubi Lamrita cikin murmushi ya ce, da izinin ubangijina wannan rauni na Imhal za warke a cikin kwankai kadan kuma zai sami lafiya sosai ya ci gaba da wasansa. Ko da jin wannan batu sai Lamrita ta kamu da tsananin farin ciki ta kuma yiwa jarumi Salmanu tana mai goge hawayen idanunta sannan ta dubeshi ta ce, ya kai Salmanu kayi sani cewa ka yi mini taimakon da ba zan iya biyanka ba tunda ka ceto rayuwar masoyina wanda nake kaunarsa fiye da komai a wannan duniya a yanzu. Ko da jin wannan batu sai jarumi Salmanu ya yi murmushi ya ce, ai ba ni ne na ceto rayuwarsa ba, ubangijin musulunci ne ya ceci rayuwarsa tunda ni ba likita ba ne kuma ni ba matsafi ba ne. ubangijin nawa na roka ya bashi lafiya. Amma fa yau saura kiris asirinki ya tonu kuma a hakan ma ina zargin cewa sarki Taryan ya ganeki. Kafin Lamrita ta bude baki tace wani abu sai kawai suka ji motsi bayansu. Cikin hanzari da firgici suka waiga da sauri. Ba wani suka gani ba tsaye bayansu face sarki Taryan a cikin gagarumar shigar yaki yana murmushi. Kawai sai ya dubi Lamrita ya ce, ki dena zaton ban san duk abin da kike kullawa ba dangane da mahaifinki. Ko da jin haka sai Lamrita da jarumi Salmanu suka mike tsaye suna masu kurawa sarki Taryan idanu cikin tsananin mamaki. ME ZAI FARUYANZU TSAKANIN SU JARUMI SALMANU DA SARKI TARYAN? YAUSHE NE ZA A CI GABA DA WANNAN GASA TA KAMBUN JARUMTA, KUMA WAYE ZAI SAMI NASARAR LASHE GASAR A KARSHE? Mu hadu a litafi na gaba don jin yadda za ta kasance. Marubucin littafin Abdulaziz Sani M Gini Typing by AA Misau WhatsApp group Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30Q An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 3 of 3