Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 3
fita filin gasa inda ya sanya kayansa na yaki kuma ya daukil takobinsa da garkuwarsa ya fice da sauri. Shi kuwa sarki Taryan ba komai ne ya hanashi fitowa ba da wuri izuwa filin gasa face rashin jin sakamakon abin da ya faru tsakanin bokayen birninsa da sarki Gurzalu. Al'amarin da ya yi matukar dugunzuma hankalinsa kenan ya kasa zaune ko tsaye kuma ya rinka kai kawo a cikin turakarsa yana jiran dawowar sarkin yakinsa Zamaru wanda ya turashi yaje ya yi leken asiri don ya gano duk abin da sarki Gurzalu ke kullawa a sirrance. Ba don komai yake son ya gano wannan sirri ba sai don ya ts erar da rayuwar "yarsa gimbiya Sbumaira don kada ta rasa saurayin da ta kamu da tsananin Sonsa fiye da komai rayuwarta. Sarki Taryan ya san cewa tabbas idan aka kashe jarumi Imhal a wannan gasa za ta iya rasa hankalinta koma ta rasa rayuwar ta ta gaba daya. Sarki Taryan na cikin wannan hali na damuwa sai ga gimbiya Shumaira ta shigo a gigice tana kuka. Cikin sauri sarki Taryan ya tareta yana mai rike hannayenta ya dubeta cikin firgici ya ce, yake 'yata wai shin me ke faruwa ne naga har kina yin kuka haka? Shumaira ta rungurne sarki Taryan ta sake fashewa da matsanancin kuka sannan ta ce, ya ya ba zan yi kuka ba ya Kkai abbana alhalina yau ne masoyina zai yi wasa mafi hadari a cikin wannan gAsa. Ka yi sani cewa yau fa kowa yana tsoron wannan gurnurzu da za a yi tsakanin jarumi Imhai da sarki Gurzalu Saboda babu wanda ake da yakinin cewar shi ne zai lashe gasar. Matsafa sun yi iya yinSu kan su gano wanda Zai yi nasara, atlajirab Caca sun Zuba Gaba dayan dukiyarau akan wannan Wasa kuma na san cewa kai ne Wanda ya zuba dukiyarsa mafi tsoka daga cikinsu tabbas idan jarumi Imhal ya fadi ba kararmar mummunar asara Zaka yi ba Yanzu ta yaya zasu iya kubutar da rayuwar Inhal daga sharrin sarki Gurzalu? Ko da jin wannan tambaya sai sarki Taryan ya rasa abin da zai gaya mata, ya dan juya mata baya sannan ya waigo ya dubeta Cikin tsananin damuwa ya ce, yake yata kin sani cewa duk yadda zan yi naga rayuwarki ba a salwanta ba zan yi don haka ki kwanta da hankalinki dan jirani akwai abin da nake jira kafin mu fita izuwa can filin gasa.. Nima kuma AA Misau kudan jirani abu Kadan nake jira naa cigaba muku da typing...... WhatsApp group https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30Q Facebook page https://www.facebook.com/profile.php?id=100063661782295 Facebook page https://www.facebook.com/AlaminGuyson?mibextid=3amO3DAFELuS4Abp Saikunzo Admin AA Misau ke MaganaRIJIYA GABA DUBU 💕 Littafi Na Shida (6)🩸 Part C. 💎 Na Abdulaziz Sani M Gini 🤴 AA Misau ke Magana ✍️⭐⭐⭐ (Kamar yadda mukayi korafi akan kuna son litattafan da muke dorawa amma bakwa Nuna Kuna so a Yanzu Nake Ga Kamar kun gyara Ta hanyar maida hankali Akan goya mana baya SABODA HAKA idan yau kun Samar mana da LIKES SOSAI gobe ma zamu dora cigaban) 🥰 Labari Ya Isowa Shagala Cewa Marubucin Yaci gaba da cewa... Kafin sarki Taryan ya gama rufe bakiisa sai ga sarkin yaki zamaru ya shigo cikin dakin da gudu. Yana isowa gaban sarki Taryan sai ya yi masa rada a kunne. Nan take sarki Taryan ya cika da tsananin mamaki kuma ya yi shiru yana tunani har izuwa tsawon yan dakiku sannan shima ya yiwa Zamaru radar a kunne sai Zumaru ya sake ficewa da gudu shi kuwa sarki Taryan sai ya karma hannun gimbiya Shumaira ya jata da sauri yana mai cewa, zo mu karasa filin gasar domin lokaci na neman kurewa. Da isowar sarki Taryan da gimbiya Shumaira cikin filin gasar sai jama'a suka rude da shewa gami da tafi da murna saboda sanin cewa nan ba da dadewa ba za a fara wannan babban wasa na manyan giwayen da ake shakka da tsoro. Bayan sarki da gimbiya sun je sun zauna a inda suka saba zama sai aka buga tambari sannan mai gabatar da gasar ya fito tsakiyar- fili ya fara jawabi, bayan ya yi gaisuwa da bayanin barka da zuwa ga manyan baki sai ya ce, ya ku jama'a ku yi sani cewa a yau din nan wani bakon jaruni ya zo kuma ya bukaci shiga wannan gasa duk da cewar a yau ne za a yi wasa na karshe wato ya amince ya fafata da jarumin da ya lashe gasar ta yau a gobe ko a lokacin da ya kama. Wannan bakon jarumi ya biya harajin da ake biya kuma ya cika duk gasa bisa ka'idojin shiga wannan wanda shima wakilcin maigidansa bakon attajiri ne mai yawo da jarumai izuwa kasa don halattar irin wadannan wasanni. Bisa dalili ne yanzu wannan bakon jarumi zai fito yayi wasa don mu ga irin jarumtakarsa kuma ya amince a hadashi fada da jarumai ashirin Duk attajiran da suke da sha'awar yin caca akan wannan bakon jarurni da jarumai ashirin da zai fafata da su sai su kai kudadensu ga wakilin caca. Ko da jin wannan sanarwa sai filin gasar ya dada kaurewa da shewa gami da tafi da hayaniya. Attajiran cacar da suke da sauran 'yan kudi a jikinsu suka shiga wannan sabuwar caca. Bayan jama'a sun dan sami yar nutsuwa ne aka kirawo wadansu zaratan jarumai su ashirin suka shigo cikin filin sanye cikin kayan yaki. Komai jarumtakar mutum idan ya ga wadannan jarumai sai ya tsorata saboda irin kirar da Allah ya yi musu ta mutanen farko. Sun kasance dogaye kuma kaurara kuma gaba dayan jikinsu a murde yake cike da jijiyoyi da kwanji, kai da ganinsu kasan babu tambaya dole ne su kasance sadaukai. Ko da "yan kallo suka ga wadannan manyan sadaukai ashirin sai suka firgice guda suka firgice suka kama sumbatu wasu na cewa shi kuma wannan bakon jarumi wane irin ne haka mara hankali har da yake tunanin cewa shi kadai zai iya da wadannan samudawan mutane. wawa Wasu kuma sai suka rinka cewa ai karar kwana ce kawai ta kaishi ga yin wannan furuci. Abin da ya kara daurewa mutarne kai shine yanzu ashe akwai sauran irin wadannan mutane dama a duniya amma ba a ganinsu? Menene dalilin da ya sa tuntuni ba a sasu cikin wanann gasa ba Ana cikin wannan kace kace ne aka kirawo bakon jarumi Salmanu bin Usmanu. Nan fa filin agsar ya yi tsit kowa ya zuba idanu izuwa kofar da jaruman gasa ke fitowa. Wata rigar fata ce da wandontaa jikinsa. Rigar mai yankakken hannu ec iya hammata don haka ta baiyana surar kwanjinsa da murdewarsa, Salmanu ya bar fuskarsa a bude bai rufe ta ba don haka yana shigowa cikin filin gasar sai tsananin kyawunsa da kyawun surar jikinsa suka dauke hanklain kowa maza da mata, musamman ma matan domin dìmaucewa suka yi saboda babu wata ya mace da zata ga jarumi Salmanu ba la ji tana sonsa ba. Nan fa aka rude da yi masa tafi da jinjina tamkar dama can an sanshi kuma ana kaunarshi fiye da fima. Ko da gimbiyahumaira ta yi arba da jarumi Salmanu shima ya hada idanu da ita sai duk su biyun suka ji zukatansu sun bugad a karfi kuma suka kasa gane dalilin faruwar hakan. Jarumi salmanu ya nufi tsakiyar filin mai gidansa na take masa baya wanda ya yi shiga irin ta manyan attajirai ababan kwatance, domin alkyabbar da take jikinbsa da rawaninsa da takalminsa sun isa su gina fadar wan AA Misau ke Magana sarkin, fuskarsa cike take da kasumba. gashin baki da gemu. Ba wani ba ne wannan mutum ba face gimbiya Lamrita wacce tayi 6ad da kama. Sai da ta raka jaurmi Salmanu har izuwa tsakiyar filin gasar sannan ta juyo ta barshi tsaye cikin tsakiyar wadannan samudawan jarumai guda ashirin. A daidai wannan lokaci ne filin gasar ya yi tsit tamkar mutuwa ta gifta. Mutnae suka bude idanuwansu sosai suna kallon tsakiyar filin, domin su ga yadda wannan bakon jarumi shi kadai jal zai fafata da jaruman guda ashirin. Ai kuwa nan take aka buga gangar fara yaki, sai jaruman guda ashirin suka zare takubbansu suka afkawa jarumi Salmanu suka haushi da sara da suka ta ko ina da dukkan karfinsu. Nan fa jarumi Salmanu ya rinka kare duk hare haren nasu ta duk inda suka kawo ya zama kamar mazari a sakiyarsu ya rinka yin wata irin cstantawa a Kasa da sama wacce tasa ya zame musu alakakai kuma ta burge gaba dayan yan kalon har sai da kowa ya Kama yi masa tafi, filin ya dada rudewa da shewa fiye da koyaushe saboda ba a Taba ganin jarumin da ya taba yin irin Wannan gwaninta ba. Jarumi Salmanu ya ci gaba da kare kansa kawai ba tare da ya maida martanin sara ko suka ba amma sai ya Rinka naushinsu da hannu da kafa Nan fa ya fara hada musu jini da majina a hanci da baki. (Kai nima fa abin ya fara bani mamaki AA Misau ke Magana) Al'amarin da ya fusta jaruman kenan surma suka fara kai masa wawan duka gami da wawan saran amma duk sa Suka zamo na banza saboda tsananin Zafin narmansa ya wuce tunanin mai Tutani kai kace jkinsa na karfe ne bana Jini da tsoka ba. Sai da aka shafe kusan rabin sa'a ana wannan bakin artabu amma jaruman ashirin sun kasa ko da kwarzanar jikin jarumi Salmanu shi kuma sai ya kasa kai mutum daya kasa a cikinsu duk da cewar shi ne yake yi musu lugudan duka saboda tsananin juriyarsu da nacinsu. Ko da jaruman suka fusata ainun kuma suka rasa yadda zasu yi da shi sai kawai suka ja da baya gaba dayansu a lokaci guda suka rabu izuwa kaso biyu wato suka rabu mutum goma goma Lokaci guda suka rugu da gudu cikin tsananin zafin nama da shammace goman farko suka danki hannayen Salmanu, ragowar goman kuma suka kama kafafunsa suka kana ja suna tale shi da nufin su tsinkashi. Saboda tsananin azabar da Salmanu ya ji bai san sa'adda ya kumma uban ihu ba tunda shammatarsa suka yi bai san manufarsu Amma da yake shammatarsa suka yí bai san manufarsu kenan ba, amma da yake Allah ya bashi karfin Allah ya isa sai shima ya dage ya hanasu samun damar tsirkashi. Nan fa kwanjin Salmanu ya fara kumbura, rigarsa ta fara yayyagewa sai gashi yana janyo jaruman ashirin gabansa wato ya zamana cewa kartin damtsnsa ya fara rinjayar nasu. Nan fa filin gasar ya sake rudewa da shewa aka shiga yiwa jarumi Salmanu kirari da jinjina, kawai sai gani akayi ya janyosu su duka da karfin tsiya ya gwara fuskokinsu. Cikin bakin zafin nama ya mike tsaye zumbur ya rinka naushin Hannayensu da kafafunsu ya rinka kakkaryasu suka rinka yin ihu suna zubewa kasa. A cikin abin da bai wuce dakika ashirin ba ya zubar da su kasa su duka suna iface-iface aka rasa dayansu da zai iya mikewa tsaye. Ko da ganin haka sai filin gasar ya kaure da tsananin ihu da shewa Attajiran cacar da suka zabi Salmanu kuwa rawa da tsalle suka kama wasunsu kuwa suka kamna zuba ruwa a kasa suna sha su ma suna birgima a Rasan tamkar wadanda suka zautu. Al'amarin gimbiya Lamrita kuwa saboda tsananin farin ciki da kidimewa bata san sa'adda ta mike tsaye ba zumbur daga cikin yan kallo ta ruga izuwa cikin filin gasar ta daka tsalle ta rungume jarumi salmabu. Saura Riris rawanin kanta ya kwance a ga gashin kanta sai jarumi Salmanu ya yi sauri ya gyara mata rawanin. A lokacin ne sulka hada idanu taji ta kamu da tsananin kunya amma sai ta wayance ta ci gaba da tsallen murna don kada jama' a su gano wani abu Yan kallo da yawa suka fado flin gasar suka daga jarumi Salnanu sama suna tayi masa jinjina har Sai da dakaru suka rugo suka tarwatsa su Aka fitar da jarumi Salmanu daga cikin flin kuma aka kwashe wacannan Karyayyun jarumai sannan wuri yayi daidai jamna'a suka utsu. Ba tare da bata wani lokaci ba aka Sake buga tambarin ci gaba da gasar in da alkalin gasar ya fara kirawo jarumi mhal ya fito daga cikin dakin jaruman Yan kallo na ganinsa sai aka rude ihu gami da shewa, tafi, jinjina da A daidai wannan lokaci ne sarki Taryan ya dubi gimbiya Shumaira ya ce yke yata yanzu ke a ganinki tsakanin Jarmi Imhal da wannan bakon jarumi Waye ya fi kyau da jarumtaka? Sa'adda Shumaira ta ji wannan tambaya sai ta yi ajiyar numfashi sannan ta ce, ai ni kaina ma ya juye. Ya kai abbana kayi sani cwa babu wanda zai iya tantancewa tsakanin Imhal da wannan sabon jarumi face kawai idani sun fafata a zahiri an gani. Sarki Taryan ya yi murmushi ya ce, hakika zancenki dutse ne 'yata. Gama fadin hakan ke da wuya sai suka ji an kirawo sunan sarki Gurzalu, ai kuwa sai filin ya sake yamutsewa da ihu da hargowar mutane fiye da koyaushe har sai da aka rinka toshe kunnuwva da tafin hannaye don ji zaka yi kamar kunnenka zai dode saboda karfin ihun mutane. Sarki Gurzalu ya nufi cikin filin gasar yana tafiya cikin takama da izza irin ta manyan sadaukai kuma nanyan sarakai masu ji da kansu. Nan fa murokansa suka shiga yi masa kida da kirari irin wanda suka saba yI masa na musamman. A wannan lokaci jarumi Salmanu da gimbiya Lamrita na zaune a waje guda tare a inda manyan attahirai ke zama. Ko da sarki Gurzalu ya taho zai gifta ta gabansu sai Lamrita tayi sauri ta a sunkui da kanta kas saboda tasan cewa a da zarar sun hada idanu ita da sarki Gurzalu sai ya shaidata, Shi kuwa Jarumi Salmanu sai ya kurawa sarki a Gurzalu idanu, ai kuwa shima yana ganinsa sai ya kura masa idannun har yana waigensa. Duk su biyun sai sukayi ta kokarin su tuno da inda suka taba haduwa arnma sai abin ya gagara har dai sarki Gurzalu ya isa tsakiyar filin ya kusanci jarumi Imhal ainun yadda suna Ajin mum fashin juna. AA Misau ke Magana A daidai wannan lokaci ne zuciyar gimbiya Lamrita ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda tsananin bakin ciki da kuma jin kiyayyar mahaifinta a cikin ranta a sa'adda ta ganshi daf da Imbal. rinka Nan fa ta tuno da maganganun da sarkin yaki ya gaya mata bisa irin cin amanar da sarki Gurzalu ya yi ya kashe mahaifin Imhal dan uwansa kuma jininsa da yadda ya kashe matarsa da duk zuri'arta. Nan take jikin Lamrita ya kama tsuma ta yunkura zata mike tsaye ta ruga izuwa cikin filin domin taje ta gayawa jarumi Imhal, Salmanu ya riko hannunta a karon farko tun da suka hadu. Cikin sanyin jiki ta koma ta zauna. Cikin rada Salmanu ya ce da ita, me za ki je ki yi a cilin flin gasar wanda ba ki sanar da ni ba tun kafin mu iso nan? Ko da jin wannan tambaya sai Lamrita ta wayance ta kama yake ta ce babu komai. Sarki Gurzalu ya dubi jarumi Imbal ido da ido ya ce, to Imhal yau ne fa ranar karshen numfashinka a doron Rasa. ldan kana da wata wasiya ka bar mini ita nayi alkawari zan cika maka ita bayan mutuwarka. Sa'adda jarumi Imhal ya ji wannan batu na sarki Gurzalu sai ya yi murmushi ya ce ko kadan bana ji a jikina cewar zain mutu a wannan gasa da za mu yi ni da kai. Idan har ban vi nasara kanka ba sai dai mu yi ragas amma kasan cewa da hannuna ba zan iya kasheka ba saboda ina yi maka kallon ubana mahaifi a matsayinka na uban masoyiyata wacce na kamu da tsananin sonta, son da ba zan iya kankareshi ba daga cikin zuciyata Ko da jin wannan batu sai jikin sarki Gurzalu ya yi sanyi har ya ji Kwalla na neman zubO masa sai ya yi sauri ya sunkui da kansa kas ya juya da baya yayi taku bakwai sannan ya zare takobinsa ya gyara tsayuwarsa. Ko da ganin haka sai shima jarumi Imhal ya zare tasa takobin kuma ya gyara tsayuwa suka fara kallon kallo. Ba wani abu bane ya sa kwalla ta zOwa sarki Gurzalu ba face sanin cewa a badini fa shi uba ne ga jarumi Imhal mutane ne basu sani ba amma kuma gashi a zahiri ba shi da makiyin da ya fishi a doron kasa. Nan take sarki Gurzalu ya ji ya tsani jarumi Imhal fiye da koyaushe don haka ba shi da wani burin da ya fi ya gaggauta kasheshi domin ya daina tuno da cin amanar da ya yi a baya. A wannan lokaci gimbiya Lamrita na zaune na cikin van kallo cikin shigarta ta attajiri kuma jarumi Salmanu na zaune a gefan damanta daf da daf Ko da jarumi Salmanu ya karewa sarki Gurzalu da jarumi Imbal kallo na natsuwa sai ya dubi Lamrita ya ce, haikka wadannan jarumai ne na gaske, samun nasara a kansu sai sa'a da rabo ba wai tsagwaron karfin damtse ba da 1ya yaki. Ko da jin wannan batu sai nankalin Lamrita ya sake dugunzuma ainur fiye da koyaushe ta sake rudewa har shi kansa jarumi Salmanu ya fahimci cewar lallai Lamrita ba ia son wannan gum urzu da za a yi tsakanin mahaifinta da jarumi imhal kuma nan take ya gane cewa lallai akwai soyayya tsakaain ta da jaruni Imhal. Salmanu na cikin wannan tunani Ne ya lura da cewa ashe gaba dayan matan dake cikin filin gasar hankalinsu kansa suke, kai hatta matan aure ma sun kasa kau da idanunsu a kansa, al'amarin da ya sa yaji gaba daya ya tsani filin gasar kenan, har ya janyo rawaninsa zai rufe fuskarsa kuma sai ya hada idanu da gimbiya Shumaira, yana yin arba da ita yaji nan take ya kamu da tsananin sonta kuma itace kadai bata kallonsa a filin, idanun ta suna kan jarumi Imhal kuma kwalla ta ciko mata, hawayen na shirin zubowa. Kawai sai ji akayi an buga gangar fara gumurzu, ai kuwa sai jaruman biyu suka rugo izuwa kan juna suka kacame da azababben yaki suna masu kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama, juriya da bajinta ta ban al'ajabi. Nan fa yan kallo suka rude da shewa, tafi, kowa na yiwa gwaninsa kirari, makada da mawaka ma suka kama aikinsu. Sai da jaruman biyu suka shafe sa'a daya da rabi suna wannan bakin artabu suka tashi hankalin kowa a filin gasar amma dayansu bai sami nasarar ko da kwarzanar jikin daya ba. Al'amarin da ya sa 'yan kallo suka kagauta kenan. Bisa dole jaruman biyu suka ja da baya suka yi cirko cirko suna kallon juna suna haki. Ba komai ne ya sa suka ja bayan ba sai domin su baiwa kansu dan hutu kuma su yi nazari akan irin salon fadan da ya kamata su sauya don samun lago. Ai kuwa sai da suka shafe kusan dakika dari a tsaye sun kurawa junansu idanu sannan suka sake tasowa da gudu iZuwa kan juna. Ko da ya rage saura baifi taku hudu ba su hadu sai kowannansu ya daka tsalle sama tamkar kibiyoyi, kowannansu ya kaiwa dan uwansa mugun hari cikin shammnace. Cikin nasara sarki Gurzalu ya yanki Inhal akan damtse hannunsa na dama.... Topah nima AA Misau ganin wannan galaba da. Sarki Gurzalu ya samu yasa zan dakata anan sai wani lokaci kuma Admin AA Misau Ke Magana WhatsApp group Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30QRIJIYA GABA DUBU 💕 Littafi Na Shida (6)🩸 Part D💎 Na Abdulaziz Sani M Gini 🤴 AA Misau ke Magana ✍️⭐⭐⭐ (HAKIKA KUN NUNA MANA KUNA SON LITTAFIN NAN SABODA HAKA GA ALKAWARI NA NAN NA CIKA😎 kucigaba da nuna mana goyon baya kusha LABARAI) Labari Ya Isowa Shagala Cewa Marubucin Yaci gaba Da cewa... Sarki Gurzalu ya samu nasarar yankar imhal a damtsen sa na dama shi kuma Imhal sai ya sami nasarar yankasarsa akan cinyar kafarsa ta hagu. A tare su biyun suka kwala ibu sakamakon tsananin zafi da zogin da sukaji suka rikito kasa, jini na diga a jikinsu kowannansu na dafe raunin kuma suna hararar juna. Kai da ganin wannan abu da ya faru akasan cewar karfi ya zo daya. Hakan ce ta sa gimbiya Lamrita tayi murmushin farin ciki ta sami nutsuwa da kwanciyar hankali, bisa ganin cewa abu ne mawuyaci sarki Gurzalu ya sami nasarar kashe Imhal. Da zarar dayansu ya sami nasarar saran dayan ko yankansa sai kaga shima dayan ya samu. Nan fa jini ya rinka zuba a jikinsu a wurare da dama har jiri na dibarsu amma saboda bakin naci da juriyar bala'i sun ki faduwa kasa kuma basu daina yakin ba. A haka ne kuma suka hada da gabzawaunansu j naushi da bugu. Nan fa fiuskokinsu da idanuwansu kumbura suka yi suntum. suka Haka dai suka ci gaba da wannan bakin artabu suna layi kamar zasu fadi Kasa, kai hatta 'yan kallo sai da suka kamu da tausayinsu amma ko kadan su jaruman basa tausayawa kansu. Tun suna tsaye sai da suka tsugune kasa a sannan ne kuma suka kama komowa, wannan ya shake wancan wancan ya shake wannan suka yi ta birgima a kasa kuma suka ci gaba da naushi da bugun juna a lokacin da takubban hannayensu suka subuce daga bannayensu. Babu abin da ya dada baiwa 'yan kallo mamaki face ganin yadda da zarar dayansu ya cutar da dayan sai shima dayan ya rama yayi masa irin abin da yayi masa. Tun da aka fara Wannan gasa ba a taba yin jaruman da suka yi irin wannan dadewa ba suna gumurzu a cikin filin gasa ba tare da daya ya samni nasara ba. A daidai wannan lokaci ne hankalin atajiran caca ya dugunzuma ainun saboda kowa yana ganin cewa za a iya cinye jaruminsa. Lokacin da jaruman biyu suka kwamarzu sosai kuma suka galabaita ainun sai suka saki juna suka zube kasa wanwar suna haki da numfashi sama Sama. Da kyar da sidin goshi suka mike tsaye suka skae daukar takubbansu suka ja da baya taku biyar biyar suka dada kurawa juna idanu suna tunanin karshe na samun nasarar lashe gasar. Tsawon 'yan dakiku suna tsaye kikam, a lokacin ne filin gasar ya yi tsit kamar mutuwa ta gifta saboda kowa ya zuba idanu ya ga yadda wannan haduwa Ta karshe zata kasance. Kawai sai aka ga jaruman biyu sun taso da gudu izuwa kan juna suna ihu da kururuwa mai tsananin firgitarwa wacce ta razana kowa, mutane suka mimmike tsaye daga zaune ana dafe kai da bude baki, kawai jira ake a ga jarumin da zai fadi kasa idan aka yi wannan mugun gamo. Ba zato ba tsammani sai aka ga jaruman biyu sun daka tsalle sama, kafafunsu sun rabu da kasa tamkar an barbosu daga cikin baka suka luluka can sama tamkar kawunansu zasu tabohadari Ai kuwa suna haduwa kowannasnu ya sami nasarar sokar dan uwansa da takobi da gefen ciki. Kowace takobi sai da ta hudo ta gadon baya. Take suka rikito kasa suka baje wanwar suna kakarin mutuwa. Ko da ganin ahin da ya faru sai gimbiya Shumaira da gimbiya Lamrita suka dimauce suka kwala ihu. Take Shumaira ta sulale kasa daga kan kujerar da take zaune ta sume, ita kuwa gimbiya Lamrita bata san sa'adda ta mike tsaye ba zumbur har rawanin dake kanta ya tuje sai gashi gashin kanta na ya mace ya zubo kasa. Kawai sai ta ruga izuwa cikin filin gasar. Maimnakon ta wuce zuwa kan sarki Gurzalu wanda shi ne mahaifinta sai ta wuce zuwa kan jarumi Imhal. A daidai wannan lokaci ne alkalan gasa da dakaru suka ruga izuwa kan jaruman gasar domin a gane halin da suke ciki, idan basu mutu ba a basu agajin gaggawa. Da yake fuskar gimbiya Lamrita cike take da gashi ba a shaida kowacece ba ammna kuma da aka ga gashin mace ne da ita sai rashin yadda ya fado dakaru suka sha gabanta domin su hanata isa inda jarumi Imbal yake, ai kuwa sai ta tarwatsasu da Rarifn tsiya inda ta zarc takobinta ta hau kare harinsu tana makesu suna faduwa kasa. Nan fa filin gasar ya yamutse, 'yan kallo suka kama iface-iface da guje guje. A lokacin ne aka yi sauri aka đauke sarki Gurzalu aka shige da shi cikin gidan sarautar likitocinsa na biye da shi da gudu babu tabbacin cewar za a iya ceto rayuwarsa. Gimbiya Lamrita ta isa har inda jarumi Imhal ke kwance cikin jini male male yana ta kakarin mutuwa amna sai ta kasa daukeshi saboda dakarun dake tare ta kara yawa suke kuma sarkin yawa yafi sarkin karfi. Ko da jarumi Salmanu ya ga cewa lallai gimbiva Lamrita ba za ta iya dauko jarumi Imhal ba kuma in dai ta ci gaba da kokarin daukoshi sai asirinta ya AA Misau ke Magana tuno sai ya yi sauirI ya batar da kamanninsa ya ruga izuwa inda take ya taimaka mata suka bazar da duk dakarun dake gabanta suka dauke jarumi Imhal suka hau doki da shi suka fice daga cikin birnin gaba daya da karfin tsiya. Ai kuwa sai dakaru sama da mutum dubu uku suka hau dawakai suka bi sawunsu. Ko da jarumi Salmanu ya waigo yaga dumbin dakarun da suka biyo su kuma suna kokarin cimmasu sai ya shiga addu'a yana mai neman taimalkon Allah. Faruwar hakan ke da wuya sai yaga sun baiwa dakarun tazara mai yawa, kafin a jima kuma sun bace musu da gani. Su kansu dakarun sai suka cika da tsananin al'ajabi bisa ganin bacewar barayi biyun da suka sace jarumi Imhal tunda da suna hangensu daf da daf. Bisa dole dakarun suka yi turjiya suka kama kalle kalle da ddawakansu suka waige waige suna kallon kudu da arewa ko zasu gansu amma ko duriyarsu babu., gabas da yamma Nan take suka kada linzamin dawakansu suka koma da baya domin su kai labari. A can cikin birnin Misra kuwa gari ya hautsine hankalin kowa a tashe yake. Shi sarki Taryan hankalinsa na kan "yarsa gimbiya Shumaira. Dama yana ganin ta suma ya kwalawa likitansa kira suka dauketa suka shige da ita cikib gidan sarautar a dimauce amma har tsawon sama da sa'a guda ba ta farfado ba, al'amarin da ya kara razana sarki Taryan kenan ya kama kai kawO a lokacin da kwalla ta cika masa idnau., shi kuna likitan yana ta aikinsa. Bayan jama'a Sun gama tarwatsewa daga filin gasar ya zamana cewa filin yayi wayam tamkar dama dan adam bai taba wanzuwa ba a cikinsa sai mutane suka ruga izuwa cikin gidajensu a cikin gari suka kukkulle kofafi domin gani suke yi kamar yaki ne ya barke a garin. Sai da aka dan jima ba a ji hayaniya ta ci gaba ba sannan hankalin mutane ya fara kwantawa har suka fara bude kofofin gidajensu suna lekawa waje don suga abin da ke gudana. Babu abin da suka gani face dakarun sarki Taryan suna ta kai kawo alamar cewar suna neman wani abu. A wannan lokaci ne mutane suka sami damar tattaunawa akan abin da ya faru. Nan fa kowa ya rinka fadan albarkacin bakinsa. Wasu su ce ai sarki Gurzalu da jarumi Imhal sun mutu wasu kuma suce ai basu mutu ba, zama su iya idan likitoci suka yi gaggawar cetonsu, yanzu menene To wai shin matsayin wannan gasa? Tsakanin sarki Gurzalu da jarumi Imhal wanene kenan zqi lashe wannan gasa? Shin sunyi ragas kenan ko kuwa zasu sake fafatawa ne jdan har sun rayu basu mutu ba sannan a tantnace zakaran gasar? To ai ga shi ma an sace jarumi Imhal kuma ba a ma san wadanda suka sace shi ba, don haka babu tabbacin ma za a sake ganinsa. Haka dai mutane suka yi ta kace nace ba tare da an san takamaiman halin da ake ciki ba. Sai bayan sa'a daya da rabi sannan gimbiya Shumaira ta dawo cikin haiyacinta ta farfado. Tana bude idanu sai ta mike zaune zumbur tana mkai anbaton sunan jarumi Imhal kuma ta yunkura zata sauka daga kan gadon da take zaune sai sarki Taryan ya yi sauri ya riketa ya ce, ki yi hakuri yake 'yata ba za ki iya ganin Imhal ba a yanzu domin yana cikin wani irin nugun yanayi wanda in kika gani kema za ki iya komawa cikin halin da muka cetoki da kyar. A yanzu haka likitoci

Chapter 2 of 3