Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 3
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels RIJIYA GABA DUBU Littafi Na Shida (6) Part A. Na Abdulaziz Sani M Gini AA Misau ke Magana Labari Ya Isowa Shagala Cewa Marubucin Yaci gaba da cewa..... Badakaren ya kawo gwauron numfadhi ya ajiye sannan yace ai muna rabuwa da kai na taho iZuwa nan dakina domin na yi shiri na tafi izuwa cikin gari don cika umarninka. Na juya baya ina sa tufafina sai na ji an turo kofar dakin nan an shigo. Katin na waigo naga mai shigowa sai ji nayi an gabza mini naushi a kan kunnena na hagu. Daga nan ban san abin da ya faru ba sai farkawa nayi na ganni a kwance da rub da ciki kuma a daure. Kafin badakare ya gama rufe bakinsa tuni Zamaru ya nike tsaye ya ruga waje da gudu. Wannan shi ne abin da ya faru a cikin gidani sarautar sarki Taryan bayan dare ya raba a ranar da jaruni imhal ya lashe gasar lambun jarumta a zagaye na hudu, Al'amarin jarumi Imhal kuwa sa da ya shafe kwana biyu a kwance yana cikin natsananciyar rashin lafiya da jinya ba tare da ya ma san wanda ke kansa ba. A tsawon wadannan kwanaki babu mai shiga cikin dakin da aka ajiyeshi face sarki Taryan da likitansa. Ita kanta gimbiya Shumaira babu yadda bata yi ba akan sarki Taryan ya amince mata ta shiga taje ta ga lafiyar Imhal amma ya ki. Babban abin da ya dada dugunzuna hankalinta shi ne gaba daya ta daina ganin Muzaira a tsawon kwanakin biyu bare ta toketa ta shigar da ita inda aka 6oye jarumi Imhal kuma bata san dalilin bacewar Muzaira ba. A wannan dare na biyu ne kafin daren ya raba jarumi Imhal ya dawo cikin haiyacinsa har ya bude idanunsa. Yana bude idanun nasa ya yi arba da sarkí Taryan da likitansa zaune a gabansa kawai sai ya yunkura ya mike Zaune, yana shirin mikewa tsaye kenan sarki Taryan ya ce, kada kayi Kwakkwaran motsi domin dinkin da na yiwa raunikan jikinka zai iya farkewa kuma kaga raunikan basu gama warkewa ba. Ko da jin wannan batu sai kwallar takaici ta zubowa jarumi Imhal ya du ikitan sannan ya dubi sarki Taryan ya ce, na gaji da wannan gasa haka kuma na gaji da irin bakar wahalar da nake sha don baka lallai gobe da safe nake son na yi wasan karshe da sarki Gurzalu domi na kawo karshen komai, ko ni ko shi Ina son na sami'yancin kaina haka na gaji da ganin jinina na zuba. Ko da gama fadin haka sai jarumi Imhal ya yunkura cikin zafin nama va hankade sarki Taryan da likitansa daga gabansa suka zube kasa sannan takarkare ya kwarara uban ihu wanda ya sannan ya Cika gidan sarautar gaba daya da amsa kuwa. Hatta sarki Gurzalu dake tsaye a Can cikin turakarsa sai da zucivarsa ta buga da karfi sakamakon jiyo wannan sautin ihu domin ya gane muryar mai ihun ba ta wani bace face ta jarumi Imhal. nan take ya cika da tsananin mamaki bisa yadda akayi jarumi Imhal ya Sami lafiyar da har zai iya yin Wannsn uban ihu a vanzu Saboda ihun da jarumi Imhal ke yi sai dinkin raunikan jikinsa suka rinka farkewa amma kuma sai gashi raunikan sun warke babu inda jini ya tsattsafo. Al'amarin da ya yi matukar baivwa sarki Taryan da ikitansa mamaki kenan Imhal ya ci gaba da kwarara ihu yana zarya. a cikin dakin tankar mahaukacin tsohon rikakken zalki wanda ya fusata ainun a cikin daji. Sai da sarki Taryan ya taso da sauri ya kama jarumi Imhal da karfin tsiya ya zaunar da shi kasa sannan ya shiga rarrashinsa yana bashi baki amma Imhal bai nutsu ba sai da sarki Taryan ya amince da batun cewar gaba da gasar kambun jarumta gobe da safe. A cikin wannan dare kuwa aka yada labarin ci gaba da gasar kamnbun jarumta gobe da safe. Ai kuwa nan da nan labari ya bazu a ko ina birni da kauye, mutane suka rinka cewa lallai jarumi Imhal ba mutum ba ne, aljani ne shi don babu yadda za a yi ace mutum ya warke daga iin mugayen raunikan da ke jikinsa guda shida. Al'amarin gimbiya Lamrita kuwa tun daga lokacin da ta sami nasara kufcewa daga hanun su sarkin yalki acan birnin Kisra ta fada cikin daji. bata saurara ba da gudu akan doki don gudun kada su sarkin yaki su biyo bayanta su cimmata saboda ta san cewa sarkin yawa yafi sarkin karfi. idan suka yi mata rubdugu zasu iya cafketa su je su jefataa cikin kurkukun da ba za ta iya guduwa ba. Lamrita bata yada zango ba sai da ta ga dokinta ya gaji likis kuma itama ta gajin kuma yunwa da kishirwa sun fara galabaitar da ita sannan ta tsaya a bakin wata korama ta sauko daga kan dokin suka kama shan wannan ruwa ita da dokin nata. Da yake tana tsoron kada cikinta ya kulle sakamakon yunwar da take ji sai ta sha ruwan dan kadan. Ita dai wannan korama tana da zurfi amma bata da fadi sosai kuma mahada ce ta ruwan wani katon kogi da ke can gaba a cikin daji. Kash rashin sani yafi dare duhu.a she dai dai wurin da gimbiya Lamrita ta tsuguna tana shan ruwa akwai wata murtukekiyar macijiya mai kauri da tsawon gaske wacce ta yi lambo a AA Misau ke Magana Karkashin ruwan, kawai jira take Allah ya kawvo wata dabbar mai tsautsayi shan ruwa ta yi kalaci da ita saboda tana cikin matsananciyar yunwa. Ko do Lamrita ta gama shan ruwa ta mike zata kama dokinta su bar wajen sai kawai taji an fincikota izuwa cikin ruwan da Karfin tsiya, kafin tayi wani yunkuri macijiyar ta fara kanannade kafafunta ta kasa zuwa kugunta ne ta sa hannayenta ta tokare macijiyar. Nan fa suka kama kokowa suna nutsewa izuwa kasan ruwan Suna dagowa sama Suna ta birgima, Sakamakon nutsewar da suke yi izuwa kasan ruwan sai Lamrita ta fara galabaita saboda daukewar numfashinta, gashi dai suna ta fafatawa ita macijiyar ta kasa karasa kanannadeta ita kuma ta kasa samun damar zare wuka ko takobinta ta cutar da ita. A daidai wannan lokaci hankalin gimbiya Lamrita ya dugunzuma ainun domin karfinta ya fara karewa ta san cewa da zarar macijiyar ta karasa kanannadeta zata karya gaba dayan kasasuwan jikinta ta hadiye ta. Nan take Lamrita ta cire kai ga samun tsira ta saddakar da cewa lokacin mutuwarta ya yi. Kwatsam sai ga wani matafiyi bisa wani dogon rakumi sanye da fararen tufafi ya zo giftawa. Matafiyin ya rufe fuskarsa, idnaunsa ne kadai ake gani. Ko da ya ga abin da ke faruwa sai ya dako tsalle sama daga kan rakumin, tun kan ya fado kan macijiyar ya zaro wata sharbebiyar wuka kawai sai ya sokawa macijiyar wuka a idonta guda Take idon ya fashe, macijiyar ta yi wani uban ruri saboda tsananin zafi da zogin da taji a sa'adda iini ya kama shatatowa kasa, ba ta san sa'adda ta saki Lamrita ba saboda dimaucewa, ai kuwa sai ta koma kan wannan bakon matafiyi shima ta fara kanannadeshi amma sai ya yi wuf ya kama jelarta da hannu guda kuma ya wuyanta da daya hannun ya warware nadewar da tayi masa a hankali da karfin tsiya. Nan take kwanjin hannayensa suka kumburo har hannun rigarsa ya yayyage saboda tsabar karfin damtse nasa. Tuni a wannan lokaci gimbiya Lamrita ta fito daga cikin koramar da kyar tana jan ciki saboda tsananin galabaitar da tayi. tana numfarfashi Ko da ta ga irin tsananin karfin wannan matafiyi da ya kawo mata dauki sai ta ci gaba da kura masa idanu tana kallon gumurzun da yakeyi da wannan katuwar macijiya a cikin ruwa. Tun da gimbiya Lamrita ta zo duniya bata taba ganin mutum mai kirar sadaukai ba da tsananin karfi kamarsa domin duk girman macijiyar sai ga ta hannunsa ta kasa kufcewa. Ana cikin wannan artabu ne taga jarumjin ya daga macijiyar sama ya tabe hannayensa yana mai kwala kabbara. Nan take ya tsinke macijiyar ta dare gida biyu ya yi jifa da gawarta a cikin ruwan. Saboda tsananin mamaki gimbiya Lamrita ta sandare kamar gunki, baki a bude, idanu a kafe ta kura masa idanu ko kiftawa ba ta yi har ya fito daga cikin koramar ya zo daf da ita ya tsuguna sannan ya kwaye rawanin da ya rufe fuskarsa da shi suka yi arba da juna yana mai yi mata murmushi. sai Ko da gimbiya Lamrita ta ga irin tsananin kyawun fuskar saurayin sai ta sake dimaucewa har yayi mata kwarjini ainun ta kasa ci gaba da kallonsa ta dan sunkui da kanta kas, a sannan ne ya dubeta ya ce, ina fatan dai babu wani rauni a jikinki? Ko da jin wannan tambaya sai gimbiya Lamrita ta mike tsaye ta duba ko ina a jikinta ta tabbatar da cewar babu wani rauni sannan ta dubi saurayin ta ce, ina godiya a gareka mara adadi bisa ceton rayuwata da ka yi daga sharrin wannan katuwar macijiya. Sunana gimbiya Lamrita 'ya ga sarki Gurzalu na birnin Kisra kuma ina kan hanyata ne ta zuwa bimin Misra don hallarar gasar kambun jarumta, wanene kai, daga ina ka fito kuma ina ka dosa yanzu? Sa'adda kyakkyawan saurayin ya ji wannan tambaya sai ya cika da mamaki amma sai ya dubi gimbiya Lamrita cikin murmushi ya ce, ni sunana Salman bin Usman kuma na fito daga wata kasa da ake kira Madinatul Ansar dake kudancin nahiyarku. Babu inda na nufa face birnin Misra inda ake wannan gasa ta kambun jarumta domin nima n AA Misau Ke Magana shiga gasar amnma da wata manufa. Na dade ina jin labarin wannan gasa da yanayinta irin yadda ake fafatawa da manyan jarumai na duniya ana yi musu kisan gilla. Lallai idanuna sun kagu da su ga yadda ake wannan bakin gumurzu. Yake yar sarki ki yi sani cewa kafin anzo nan na sauka a cikin birninku na Kisra har na kwana biyu kuma na sami labarin cewa mahaifinki sarki Gurzalu shi ne zakaran wannan gasa ta kambun jarumta kuma yanzu haka yana can birnin Misra yana yin gasar. Menene dalilin da ya sa baki bishi kun tafi tare ba izuwa birnin na Misra, kuma ta yaya kina matsayin 'yar sarki guda za ki shigo cikin wannan daji mai hadarin gaske ke kadai? Ko da jin wannan tambaya sai kunya ta kama gimbiya Lamrita ta dabarbarce ta kama in ina, shi kuwa jarumi Salman sai ya tari numfashinsa ya ce, bana son karya a rayuwata kuma bana tafiya tare da makaryaci. Kawai ki fito fili ki gaya mini gaskiyar tambayoyin da na yi miki, idan kuma kin san cewa ba za ki iya gaya mini gaskiyarki ba to ki yi shiru da bakinki ina ganin cewa zai fi alheri a garem ubaki daya. Ko da gama fadin hakan sai jarumi Salman ya mike tsaye ya je inda rakuminsa ke tsaye ya dauko wata jaka tasa ta guzuri gami da battar shan ruwa ya dawo wajen Lamrita ya baje jakar guzurin ya fiddoa gasasshen namna tsuntsu nannade a cikin wani ganye ya ajiye a gaban Lamnrita ya yagi cinyar tsuntsun guda daya sannan ya dubeta ya ce, ki cinye wannan naman duka don naga akwai alamun matsananciyar yunwa a tare da ke. Dan wannan da na yaga ya isheni. Yana gama fadin hakan sai ya koma can inda rakumin nasa yake ya shimfida buzu a kasa ya zauna a kansa yana mai juya mata baya ya cinye dan guntun naman dake hannunsa sannan ya mike tsaye ya fuskanci alkibla ya kama sallar nafila. Al'amarin Lamrita kuwa ko da jarumi Salmanu ya ajiye wannan gasasshen tsuntsu a gabanta sai ta cika da murna, Nan take ta kama Cin nanan har sai da ta ci ta koshi ta taune kashin duka sannan ta dauki battar ruwan shan nasa ta kwankwada har sai da taji tayi Byatsa. Tana ajiye battar ruwan ne ta hango jarumi Salman yana sallar nafila, a sannan ne ta gane cewar lallai shi ma'abocin addinin musulunci ne addinin da yake da tsananin bakin jini a nahiyarsu gaba daya. Nan dai ta ci gaba da kallonsa tana mamakin irin yanayin aikin bautar da yake yi har sai da ya kammala ya shafa addu'a sannan ya juyo ya dubeta ya ce, ina neman alfarma a wajenki guda daya. Ina son ki nema nini damar shiga wannan gasa ta kambun jarumta idan mun isa birnin Misra. Ko da jin wannan tabaya sai mamaki ya kama gimbiya Lamrita ta dubeshi ta ce, tabbas kai bako ne baka san dokokin wannan gasa ba. To ka sani cewa yanzu saura zagaye daya kacal a yi gumurzun karshe na wannan gasa a wannan shekara, babu mamaki ma a yi fafatawar ta karshe a cikin wannan sati da muke ciki. ldan har kana son ka fafata da jarumin da ya lashe gasar dole ne ka fara kafsawa da wadansu manyan jaruman guda hudu kuma sai ka biya dinare dubu dari biyu da hamsin sannan za a yarda ka kafsa da jaruman dake rike da kambun gasar. Sa'adda jarumi Salman ya ji wannan jawabi na bimbiya Lamrita sai ya yi murmushi ya ce idan da mutum dari zan kafsa kafin na hadu da mai kambun jarumta babu matsala kuma batun kudin ba matsala ta ba ce ko dinare miliyan daya ake bukata zan biya. Ko da jin wannan batu sai gimbiya Lamrita ta karewa jarumi Salmanu kallo daga sama har Raş cikin raini domin bata ga alamar yana da ko dinare dubu ba bare miliyan daya. Ko da jarumi Salnanu ya fahimci cewar kallon rauni take yi masa sai ya dauko wata katuwar jakar fata a kan rakuminsa ya ajiye a gaban Lamrita ya budeta sai ga dinare cike fal. Take gimbiya Lamrita ta dimauce ta kidime saboda mamakin ganin wannan dukiya Ni kaina AA Misau saida naa dimauce har na kasa cigaba da wannan rubutun kuma na dakata anan Saikuma wani lokaciRIJIYA GABA DUBU Littafi Na Shida (6) Part B. Na Abdulaziz Sani M Gini Typing By AA Misau ke Magana (Rashin Sakin Litattafan da muke kawo muku akan lokaci daga gareku ne domin muddin zaku dinga nuna kuna so a cigaba ta hanyar LIKES & COMMENTS bamuki kullum mu kawo muku cigaban ba) Labari Ya Isowa Shagala Cewa Marubucin Yaci gaba da cewa.... tsananin mamakin wannan dukiya mai yawan gaske a hannun mutum daya mugayen kuma matafiyi mai ratsa dazuzuka haka. Nan fa ta fara aiyanawa a ranta cewar anya kuwa wannan saurayin ba dan sarki bane ko wani mashahurin attahiri? Amsar da ta kasa baiwa kanta kenan. Ko da jarumi Salmanu ya ga gimbiya Lamrita ta tsaya tana tunani sai ya katse mata tunanin ya ce, ai sai ki tashi mu hanzarta zuwa birnin Misra don ka da a yi wannan fafatawa ta karshe ba ma nan. Lamrita ta yi ajiyar zuciya ta ce, na yarda zan taimaka maka ka shiga wannan gasa amma bisa sharadi biyu. Sharadi na farko shi ne dole ne ka zama kamar yarona, ma'ana za mu shiga cikin birnin Misra kana matsayin sabon jarumina wanda na kawo na shigar da shi gasar kuma ina matsayin bakon attajiri daga wata nahiyar, kaga kenan babu abin da zaka yi sai bisa umarnina. Ko da įin wannan batu sai mamaki ya kama jarumi Salmanu ya ce yanzu kina nufin kice za ki boye siffarki ta 'ya mace kenan ki yi shigar mata, sannan kuma ni na zauna a matsayin bawanki • alhalin na fiki ma arziki? Ko da jin wannan tambaya sai gimbiya Lamrinta ta yi murmushi ta ce kwarai kuwa abin da nake nufi kenan kuma in dai baka bi wannan umarni nawa ba ina tabbatar maka da cewar ba zaka taba samun damnar shiga wannan gasa ba. Sa'adda Lamita ta z0 nan jawabinta sai hankalin jarumi Salmanu ya dugunzuma ya dubeta cikin matukar damuwa ya ce haramun ne a addinina mace ta yi shiga irin ta maza ko kuma namiji ya yi shigar mata. Kafin ya gama rufe bakinsa sai ta ce, ai ana iya hakuri da wata dolen bisa lalura, kuma a kowane addini akwai lalura. Ko da jin haka sai jikin jarumi Salmanu ya yi sanyi ya yi shinu yana tunani da nazari daga can sai ya numfasa ya ce, shi kenan na yarda da duk sharadin da kika zo mini da shi. Cikin tsananin farin ciki gimbiya Lamrita ta mike tsaye ta kimtsa kayanta ta hau dokinta shima jarumi Salmanu sai ya hau kan rakuminsa, har ya yunkura zai wuce gaba sai ta sha gabansa ta ce, saboda me zaka wuce kan gaba alhlain ni ce na san banya fiye da kai? Salmanu ya yi murmushi ya ce, ai dole ne na wuce kan gaba ke ki tsaya a baya saboda haka dokar addinina ta ce, in ya so idan na kauce hanyar sai ki saitani. Lamirat ta jinjina kai ta ce, shi kenan amma ka sani cewa dole ne ka Boye addininka idan mun shiga birnin Misra, in ba haka ba kuwa duk shirinka sai ya wargaje. Salmanu ya sake yin shiru yayi dan guntun tunani da nazari sannan ya saki rakuminsa ya yi gaba itama Lamrita sai ta sakarwa dokinta linzami ta bishi a baya dá sauri suka nausa cikin daji. A can birnin Misra kuwa kafin gari ya waye filin gasa ya cika ya batse, duk inda mutum ya hanga sai dai yaga kawunan bil adama rututu babu masakar tsinke. Kai ba ma akan katanga ba hatta akan benayen gidajen birnin mutnae ne maza da mata suna kallo tsakiyar filin gasar domin su ga yadda wannan gagarumin wasa na karshe zai kasance saboda an san cewa wasa ne wanda babu mai kyansa da hadarinsa tunda za a fafata ne tsakanin tsohon jarumin dake rike da kambun gasar da kuma sabon jarumin da babu kamarsa. Bayan filin gasar ya gama cika, ga alkalin gasa su duka sun gama hallara kuma ga attajiran caca sun taru su da yawa kuma sun zuba kudade mafiya yawa a duk kwanakin gasar da akayi sai kuri da cacar baki suke. Makada da mawaka kuwa tuni sun fara aikinsu tun kafin ma a fito da jaruman gasar. Nan fa mutane suka kagu su ga fitowar sarki Taryan domin dole sai ya fito sannan za a fara gasar kuma a ka rinka mamakin abin da ya sa ake ta bata lokaci haka. A can cikin gidan sarautar kuwa sarki Gurzalu bai fara shirin fitowa filin gasar ba sai da ya gama kimtsawa a hankali cikin nutsuwa. Abin da ya fara yi bayan ya tashi da safe shi ne wasa jini ta hanyar yin wasa da takobinsa. Sai da ya shafe kusan sa'a guda yana wannan wasa jini sannan ya je ya yi wanka ya zauna yana buda baki cikin janjani tamkar ba shi da wani uzuri a gabansa. Yana cikin wannan hali ne ya tuno da batun 'yarsa gimbiya lamrita, nan take takaici ya turnuke shi saboda ganin yadda rashin jituwa ke neman shiga tsakaninta da shi kuma bai san hanyar da zai bi ba ya shawo kanta ba tunda ba shi da amsar tambayoyin da ta yi masa akan zafafa kiyayyarsa da yayi akan jarumi Imhal. Ko da sarki Gurzalu ya zo nan a zancensa sai hawayen bakin ciki ya zubo masa gami da nadamar abin da ya aikata a baya wanda bai taba zaton cewar zai yi nadamarsa ba kuma ba wani abu bane face nadamar kashe dan uwansa wato mahaifin jarumi Imhal da dukkan iyalansa saboda kawai ya karbi karagar mulki. AA Misau ke Magana Yanzu dai gashi ya sami mulki. daukaka da dukiya mara adadi kuma ya yi suna a duniya amma ya rasa abu daya wanda har abada ba zai sameshi ba. wato rashin dan uwa na jini. A halin yanzu sarki Gurzalu ba shi da sauran dan uwa a duniya ko guda daya face jarumni Imhal wanda ya kasance dan uwan dan uwansa da suke uba daya. Babban abin da zai rasa kuma anan gaba shi ne soyayyar 'yarsa gimbiya Lamrita a duk ranar da ta gano cewar shi ne ya kashe mahaifin Imhal kuma ta gano cewar Imhal dan uwanta ne na jini Ko da sarki Gurzalu ya zo nan a zancensa sai hawvayen bakin cikı va sake subuto masa. A daidai wannan lokaci ne yaji an kyalkyale da dariyar mugunta. Dariyar ta cika cikin dakin nasa da amsa kuwa Take ya shaida muryar mti cdariyar, ba ta kowa baee face ta Muzaira. Ko motsawa sarki Gurzalu bai yi ba sai ya gyara zama akan kujorar da yake zaune ya dauki kofin ruwan inibi ya kai bakinsa zai kurba, Caraf sani yaji an karbe kofin daga hannunaa sai ga Muzaitn ta baynna tsulum a gefe daya kusa da shi ta sa kofin a bakinta ta kwank wacde ruwan inibin dake ciki kuna tayi jifa da kofin Sannan taje ta zauna akan kujerar da ke fuakantar ta sarki Gurzalu wacce tazarar dake tsakaninsu bata wuce taku bakwai ba ta dubeshi cikin mumushi ta ce hakika sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba a je ba, Yau kusan shekaru ashirin da biyar kenan da cin amanar da ka yiwa dan uwanka wanda a sanadiyar haka ne ka kashe yar uwata da duk zuri ar mu Ni kadai ne na tsira ka jeda rayuwata a Cikin kunci da rashin 'yanci da sakewa tunda koyaushe a cikin buya nake don gudun sharrinka. Yau gashi ranar daukar fansa ta zo. A gaban idanuna dana zai yi maka kisan gilla. Babban bakin ciki na shine ba zan iya gayawa dana sirrinka ba a yanzu ya san cewa kai ne ka kashe masa mahaifi. ldan har na gaya masa hakan jikinsa ne zai yi sanyi ya kasa yin yakin da kai da kwarin guiwa saboda sanin cewa kai dan uwansa ne na jini kurna uban macen da ya kamu da tsananin sonta. AA Misau ke Magana Ko da Muzaina ta Z0 nan zancenta sai sarki Gurzalu ya bushe da dariya, al 'amarin da ya baiwa Muzaira mamaki kenan domin a tunaninta maganganun da ta gaya masa zasu sa zuciyarsa ta karaya. Lokaci guda kuma sai ya turbune fuskarsa ya daka mata tsawa ya ce, ke yarinya ki yi sani cewa kafin giwa taje kasa sai anyi da gaske. Kuma mushen zaki, kuda ma baya binsa bare tsuntsaye da sauran dabbobi. Ni a rayuwata duk abin da na sashi a gabana sai naga bayansa kuma makiyina bai taba samun nasara ba a kaina. Ina so ki sani cewa bukatata tana gaba da komai nawa. Kar ki taba zaton cewa soyayyata ga 'yata zata iya zama lagon da za a iya sarmun galaba a kaina. Ki bar ganin cewa kina tare da guurun sihirina ki yi zaton cewa hakan zai sa ku sami nasara a kaina. Muzaira ta yi murmushi ta ce, ai ni ban sa ce gurun sihirinka don na cutar da kai ba sai don na tserar da rayuwar dana daga sharrinsa tunda kaima kasan cewa ban san yadda zan iya sarrafa gurun na ka ba har na yi amfani da shi. Kafin Muzaira ta gama rufe bakinta tuni sarki Gurzalu ya yunkura cikin tsananin zafin nama ya daka tsalle sama ya zaro takobi daga cikin wani kufe dake rataye a jikin bangon dakin a sama ya taho shu... sama ya sokawa Muzaira takobin a kirjinta, ya duro kasa bisa kafafunsa ya kura mata idanu. Kawai sai yaga ashe gaba dayan jikin Muzaira na haske ne don haka takobin bata yi mata illar komai ba duk da cewar ta lume a cikin kirjinta ta faso gadon bayanta. Muzaira ta kyalkyale da dariya sannan ta zare takobin daga cikin kirjin nata tamkar ta zare silin gashi daga cikin tandun mai ko alamar kwarza ne babu akan kirjin nata, (topah ni kaina AA Misau abin ya bani mamaki) tayi jifa da takobin can gefe daya ta sake bushewa da dariya ta ce, wai shin so kake ka kasheni ka dauke gurun sihirinka ne? To idan ma mafarki kake yi ka farka. Idan kaga wannan gurin sihiri ya dawo hannunka tabbas ka sami nasarar kashe jarumi Imhal a filin gasa. ldan kuwa shi ne ya kashe ka to fa gurin sihirinka zai koma kogonsa a ranar da ya hau karagar mulkinka. Ko da jin wannan batu sai jikin sarki Gurzalu ya kama tsuma saboda tsananin fishi, fuskarsa ta kama gatsine kamar zata zazzago ta zabtare kasa. Kawai sai ya sake yunkurawa cikin shammace a karo na biyu ya watsowa Muzaira wutar sihiri daga cikin tafin hannunsa. Kafin wutar ta zuba a kanta tuni ta 6ace 6at tana mai kyalkyala masa dariyar mugunta gami cewa, mu hadu a filin gasa zan gani idan sauran sihirin tsafin naka da ya rage zaisa ka sami nasarar kashe dana. Nan take muryar Muzaira ta dauke dif tamkar bata taba wanzuwa ba a wajen kuma bai Rara jin wani motsi ba a cikin dakin. Cikin tsananin fishi sarki Gurzalu ya mike tsaye ya fara shirin

Chapter 1 of 3