Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 5
ta ce To dana yau fa ita ce ranar da za ka shiga wajen amaryarka, don haka ina yi maku addu'ar Zahlu ta albarkance ku da iyali. To amma fa ka kiyaye da wannan allo naka, domin ka san mai tsarki ne kuma rike shi sai mai sarki." Malukussaifi ya yi mumushi ya shiga dakin da Shamatu take, ita kuma Kamriyya ta koma ta zauna tana ta tunanin yadda za ta yi ta raba shi da wannan allo nasa. Jim kadan bayan rabuwarsu da danta, sai Kamriyya ta bi shi dakin da yake, ta same shi tare da Shamatu suna hira irin ta mata da miji. Da shigarta sai ta ce, Ya dana, ni dai iná dada gaya maka ka kiyaye da wannan allon domin kada najasa ta same ka yana jikinka." Malukussaifi sai ya ce da ita, I, ai zan kiyaye Unmma, amma dai bari in ba ki shi ki ajiye mini." Ya dauka kaunarsa take. Kamriyya ta karbi allo daga hannunsa ta fice tana murna da farin ciki. Kamriyya ta dabi allon nan ta yi dariya ta ce, "Wai shi yanzu ya dauka fa duk kaunarsa nake yi, wai shi ga mai uwa, ya dauki allonsa ya ba ni To ni kuwa na rantse da zahlu, sai na halaka shi da wannan allon nasa. Yayin da Kamriyya ta koma dakinta sai ta goga wannan allo, nan da nan sai lluru ya zo gabanta ya tsaya, ya ce, "Gani ya shugabata, me kike so na aikata miki." Kamriyya ta dube shi ta ce, Kai ne iluru?" ya amsa mata ya ce NI ne ya shugabata." Sai ta tambaye shi, "Wadanne birane ne suka fi nisa da abin tsoro daga wannan birni namu?" lluru ya amsa mata, ya yi ta lissafa mata birane daban-daban, har ya zo kan birnin Gailanu da birnin Daudanu. Sai ta tsai da shi a nan, ta tambaye shi-ta ce, Shi wannan birnin Gailanu a ina yake, kuma mene ne hadarinsa?" Ya ce, "Shi birnin Gailanu yana can gabas da wannan kasa, kuma Fatalwoyi ne masu cin mutane a wannan birni." Sai ta sake tambayar sa ta ce, To shi kuma birnin Daudanu fa? Ya kuma amsa mata ya ce, "Shi kuma wannan birni yana can ku dancin Kasar nan, kuma mutanensa halittarsu sun fi ku girma da tsayi kwarai da gaske." Da ta ji wannan bayani na lluru, sai ta ce da shi, To yanzu ina so ka dauki Malukussaifi tare da matarsa Shamatu, shi ka jefa shi birnin Gailanu, ita kuma ka jefa ta birnin Daudanu. ka dawo nan ka same ni." Ko da lluru ya ji haka sai ya ce, Ya shugabata, wannan fa danki ne na cikinki wannan kuma matarsa ce, don haka ita ma yarki ce. Wane laifi sukai miki da za ki sa ni na aikata musu haka? Kamriyya ta daka masa tsawa ta ce, Ni dai na ba ka umarni kawai ka je ka aikata. ai ko cikin wannan dane lluru ya shiga dakin da Malulkussaifi da Shamatu su ke. ya tarad da su suna kwance suna barci ya dauke su ya tashi sama da su ya kama hanyar sa ta zuwa bimin Daudanu. Yana cikin tafiya, saboda iska sai su ka farka daga barcinsu gabadaya suna mamaki da tunanin cewa wai shin a ina ma suke ne. Can Malukussaifi ya waratsake daga magagin barcinsa ya gane a wa ya dauko su sai ya tambaye shi. MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN Littafi na biyu 2 Fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi rubutawa Shuraihu Usman Part 10. Malukussaifi ya ce,"To kai kuwa lluru ina kake nufin za ka kai mu iluru ya amsa masa, "Ka sani fa yanzu ba kai kake iko da ni ba domin ka yi sakaci ka rabuda allonka, saboda rashin sanin amfanina Ka manta duk wahalar da ka sha ka samu allon nan, amma duk kamanta ka rabu da wannan allo. To yanzu wanda ya mallaki wannen allon shi ya umarce ni da na dauko ku na yadda ku. Da Malukussaifi ya ji haka, sai ya tambayi lluru, "Shin yanzu waye ya mallaki wannan allon kuma ya umarce ka da ka aikata mana haka?" Ya amsa masa ya ce, "Waye kuwa in banda uwarka wadda ka baiwa allon. Ita ce ta umarce ni da na aikata muku wannan, kuma ka sani ba ni da ikon saba umarnin wanda duk ya mallaki wannan allo. Saboda haka kada ka zarge ni sai dai ka zargi kanka da yin sakaci da allonka da ka yi." Da ya ji wannan bayani na Iluru, sai ya yi nadama da rabuwa da allonsa ya kuma nemi iluru da ya ajiye su wuri daya tare da Shamatu, amma ina, ya ce ai ba shi da ikon yin hakan. Bayan wani dan lokaci sai su ka iso birmin Daudanu, nan sai Iluru ya sauko kasa ya ajiye Shamatu ya kuma tashi da Malukussaifi ya nufi birnin Gailanu da shi. Alokacin da ya sauke Shamatu, sai ta zauna tana kukan bakin cikin rabuwa da mijinta da iyayenta. Haka ta kasance cikin wannan hali har gari ya waye, da ta ga gari ya waye sai ta tashi ta fara tafiya ba ta san inda za ta ba. Ta yi ta tafiya har rana ta take, kafarta ta rika konewa da zafin rana ga kishirwa ga yunwa, sai ta fara kuka tana cewa,"Ya Ubangiji kai ka shigar da ni wannan hali saboda haka ka kubutar da nı daga wannan bala'i da na abka cikinsa. Tana cikin wannan hali sai ta hango wasu dogwayen gutane manya manya su arba'in bisa dawaki sun nufo ta, su kuwa mutanen wannan birni na Daudanu ne. Yayin da suka karaso wurin Shamatu sai suka tsaya suna kalonta, daya daga cikinsu sai ya ce da sauran," Kun ga wata 'yar karamar halitta mai ban mamaki, ai sai mu dauke ta mu kai ma Sarki ita." Sai ya mika hanmu ya dauki Shamatu kamar wanda ya dauki takalmi. Suka koma izuwa cikin birni suka kai ta wurin Sarkinsu, wanda ake kira da suna Akilu, suka nuna masa ita Ko da Sarki Akilu ya ga Shamatu, säi ya ce, Ya ya za ku kawo mini wannan, da ganinta laifi ta yi wa Ubangijinta ya mayar da ita karama haka, sannan kuma ku kawo min ita, ai kawai ku je ku mayar da ita inda kuka ganta ku yanka ta a can. Da Shamatu ta ji wannan magana ta Sarki sai ta ce, Wallabi dama ai haka Ubangijina ya yi ni, ba wani laifi na yi masa ba. Ana cikin haka sai 'yar Sarkin wadda ake kira Sadika, ta shigo wajen, ko da ta ga Shamatu sai ta kura mata ido. Ta ga kyakkyawa ce kwarai amma ga ta 'yar karama, sai ta tambayi ubanta ta ce, Wannan fa uban ya ba ta labarin yanda aka tsinci Shamatu kuma ya gaya mata ya umarci mutanen da suka kawo ta da cewa su mayar da ita inda suka dauko ta su yanka ta. A nan sai Sadika ta ce, Ai ba haka bane, dama na taba samun labari cewa akwai kananan mutane kamar ta, ba wani laifi ta yi ba dama haka take, yanzu kawai ai sai mu kai ta wajen abin bautarmu Idan ya karbe ta ya yarda da ita, to shike nan sai mu bar ta a wajensa ta rika yi masa hidima, idan kuma bai karbe la ba, to shike nan sai mu yanka ta." Uban Sadika ya yarda da wannan shawara ta 'yarsa, ya kuma yi mata izini da ta kai Shamatu wurin wanan Gunki nasu. Sadika ta kama hannun Shamatu suka nufi wajen da wannan abin bautawa na su yake, da zuwansu sai Sadika ta bude kofar wani daki Suka shiga. An bi bangon dakin an yi masa ado da dinare, ga shimfidu na kilisai, daga can gefe an yi wasu kwami-kwami na azurfa guda biyu, daya an cika shi da zuma daya kuma an cika shi da ruwan matsatsen lemo da abarba da nikakkiyar ayaba da ruwan inibi. Daga wani gefen kuma an ajiye wata tasa da kaji guda uku a ciki, daya soyayyiya daya gasasshiya, daya kuma dafaffiya. A tsakiyar dakin ga wani katon rago a kwance duk an yi wa kahonsa da kofatonsa ado da jan dinare da lu'u-lu'u. Da shigarsu dakin sai ragon nan ya yi ku ka. Sadika sai ta ce. Ai shike nan kin yi sa'a, abin bautarmu ya karbe ki, yanzu ma barka da zuwa yake yi miki" Shamatu ta tambaye ta, Ina Ubangijin naku yake ne? Sadika ta amsa mata la ce. ai wannan ragon da kike gani, shi Ubangijin namu, shi muke bautawa. To yanzu abin da nake so dake Shi ne, za ki zauna anan duk lokacin da ragon nan ya bukaci ya sha ruwa ki dauki tasar nan ta dinare ki debo zumar can ki hada da wancan ruwan ya'yan itatuwan nan ki ba shi ya sha. Haka kuma idanya bukaci Cin abinci, ki dauki waccan tasar mai gaman kajin can a ciki ki ba shi yaci, shi ne abincinsa, kullum za a rinka kawo miki gurasa guda biyu ita ce abincinki. Sannan kuma ki kiyaye, kullum idan kika ga ragon nan zai yi fitsari ko ya fara ki yi maza ki sa tasa ki tari fitsarin domin kullum da shi Sarki yake wanke ido. Haka kuma duk sanda ya yi kashi ki share ki kwashe ku zuba a wannan tasar domin muna hadawa da shi wajen yin maganin cututtuka." Bayan ta gama yi mata wannan bayani, sai ta fita ta mai da kofa ta rufe ta bar Shamtu da rago. Ko da Shamatu ta ga Sadika ta tafi, sai ta ce, Mahaukatan banza, wai ku rasa abin da za ku bautawa sai rago." Shamatau ta ci ta sha daga abincin nan na rago ta koshi, ta zauna har dare ya yita tashi ta share dakin tas ta tara kashi da fitsarin rago kamar yadda Sadika ta gaya mata. Da gari ya waye Sadika ta zo ta ga dakin ragon nan ya yi fes an share, ta ga ga fitsari da kashin ragon nan Shamatu ta tara, sai ta ji dadi ta ce, "Madalla dake wannan bakuwa, haka nake so ki kyautata ga wannan abin bauta namu, me yiwuwa ma shi kansa ya ji dadi ya taimakeki ki ya mayar da ke wurin yan uwanki. ta karbi wannan najasa ta kawo kaji guda uku da zuma da ruwan matsattsun 'ya'yan itatuwa ta ce. Ga abincinsa." Sannan ta miko gurasa guda biyo ta ce, ga naki abincin." haka kullum ake yi, kullum idan an kawo abincin nan sai Shamatu ta baiwa ragon nan gurasar nan ya ci ita kuma ta cinye wadannan Kaji ta sha zuma ta sha wadannan 'ya'yan itatuwa. Idan kuma ragon ya yi fitsari ko kashi a kan shimfidar kilisan nan sai ta dauki tsumangiya ta zane shi har sai da ya zamto ragon nan ba ya fitsari ko kashi sai in ita ta tara sannan ya yi, ta tarbiyantar da ragon nan da haka ta kasance cikin wannan hali. Shi kuma can Malukussaifi lokacin da Iluru ya ajiye shi a bimin Gailanu sai ya rinka tafiya ya ga dogayen bishiyu ga wata korama ruwa na gudana, gefen ta ga ya'yan itatuwan nan iri daban-daban ya ci ya koshi ya kuma sha ruwan koramar nan sannan ya cigaba da tafiya har yamma ta yi sai ya zo gindin wata doguwar bishiya sai ya kamata ya hau can samanta ya zauna yana hangen kasa Zamansa ke da wuya sai ya hango wani fatalwa tsoho yana tahowa inda yake. Ko da ya zo kusa sai ya ga fatalwar kansa kato kuma lailayayye kamar bal, ga manyan idanuwa da nanannen hanci ga jikinsa duk gashi kamar dabba. Yana zuwa daf da wanan bishiya sai ya jiyo kanshin Malukussaifi ya daga kansa sama ya hango shi ya tsaya ya kura masa ido kur yana kallon sa har tsawon kimanin sa'a guda, sannan sai ya juya ya komà ta hanyar da ya biyo. Da Malukussaifi ya ga fatalwar nan ya juya ya tafi sai ya yi ajiyar zuciya ya godewa Allah. Jum kadan sai ya hango wannan tsohon ya komo tare da wadansu falalwoyin 'yan uwansa ya kirawo su Suka karaso suka taru suna tallonsa can sai suka juya gabaki daya suka koma ta hanyar da suka biyo. Ganin haka sai abin ya ba wa Malukussaifi mamaki ya zauna yana ta tunanin wanan lamarin, yana cikin haka can sai ya kuma hango su sun dawo tare da wata tsohuwa mai farin gashi kamar na rago da suka karaso wajen sa suka dube shi sukai magana da wani yare wanda shi baiji abin da suka ce ba, sukai ta magana da wanan yare can sai ya ga duk sun tafi sun bar tsohuwar nan a wurin ita kadai. Bayan tafiyar su sai tsohuwar ta yi masa nuni da hannu da ya sako sai ya ce, Aa ba zan sakko wajenki ba domin kuwa in na sakko cinye ni za ki yi." haka tai tai da shi ya sakko ya ki, sai ta vi masa magana da yarensa ta ce, Ka gasgata ni ka sakko zan taimake ka na kubutar da kai daga wadanan fatalwi yan'uwana ba za su yi maka komai ba don inda ina so su cinye Ka da tuni na sa sun jefo ka sun cinye ka, kuma ka ga idan na barka a nan har dare ya yi to za su zo su cinye ka a nan, saboda haka ka gasgata ni ka sakko." Da ya ji haka sai ya mika lamannsa wurin Ubangiji sai ya sakko An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 5 of 5