Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 5
nan ya ce Wannan ku kaiwa Sarki." Sannan kuma ya dauko wannan littafi na Halwanu ya sake mikawa mutanen nan ya ce Wannan kuma ku kula da shi sosai, idan kün je ku baiwa dan uwana boka Sakaradisa wannan littafi." Nan boka ya sallamesu cikin daren suka fice daga garin ba tare da kowa ya gansu ba. Wannan abu duk ya faru ba tare da sanin Sarki -Afarahu ba. A kwana a tashi har mutanen nan da boka Sakaradiyyuna ya aika suka isa garin Sarki Saifu'ar'adu. Da zuwansu suka wuce zuwa fada suka iske Sarki na zaune ana fadanci. Suka fadi suka yi gaisuwa gaban Sarki, suka mika wannan takarda ga Sarki, suka kuma mika wannan littafin Halwanu ga boka Sakaradisa. Nan da nan Sarki ya umarci magatakarda da ya karanta wannan wasika.Cikin kankanin lokaci ya karanta abin da wannan takarda ta kunsa, Sarki da wazirinsa Baharu da Boka Sakaradisa duk suka ji irin abin da Sakaradiyyuna ya rubuta. Ran Sarki ya baci hankalinsa ya tashi, ya yi duba ya zuwa Sakaradisa ya ce.Ina dabara?" Boka Sakaradisa ya ce Idan ba da gasake ka yi ba, to wannan tsinannen farin yaron sai ya karbe wanan mulkin naka kuma ya mayar da mu bayi, kai hatta tauraruwa Zahlu ma sai va hana mu bautarta." Bayan ya gama wannan magana sai ya mikawa Sarki littafin halwanu ya ce, Riki wannan, dan 'uwana ne ya aiko min da shi Wanpan shine littafin tarihin Nil Sarki ya karba ya ajiye. Can shi kuma Waziri Baharu da yake musulmi ne sai ya ce Wai sakaradisa me ya sa kuka damu da wannan farin yaro bayan a wannan lamari bashi da laifi ai in ma kamawa ne Sarki Afarahu da Sa'adunnizzanji su Sarki zai hukunta a bisa laifinsu kashe Manadihulbigali da suka yi. Amma shi wannan yaro Kuma da kuke cewa shi ne wanda zai karbe mulkin Sarki, ya aka yi kuka sani, kun san gaibu ne? ai babu wanda yasan gaibu in ban da tauraruwa Zahlu kamar yadda muka sani Sarki ya ce Haka ne Wazirk, wannan magana taka haka take, babu wanda ya san gaibu in bán da Zahalu, to yanzu Weziri ina dabara bamu shawara. Ana cikin haka sai wani daga cikin dogarawan Sarki ya shigo ya gayawá Sarki cewa ga wani tsoho ya zo yana so ya ga Sarki. Sarki ya yi umarni da a shigo da shi, nan- da nan aka shigo da da tsohon nan gaban Sarki. ya fadi ya yi gaisuwa. Sarki ya tambaye shi, "Me ya kawo ka." Tsoho cikin raurawar murya ya ce, Na zo ne na kawo karar shugabanmu gareka, domin ta raba mu da birninmu har ta kashe wasu da dama daga cikinmu, kuma ta kama ya'yayenmu da matayenmu suna yi mata bauta, Ko da Sarki ya ji wannan magana sai ya ce, Kai mutumin wane gari ne kuma waye wannan shugaba naku, wanda har ya yi muku wannan ta'adda?" Tsoho ya amsa ya ce, "Ni mutumin birnin Yemen ne, ni ada na kasance ni ne shamakin Sarki Ziyyazanun kafin ya rasu, kuma mu duk mutanen kasarmu, mun kasance masu biyayya ga Sarkinmu. to yana ciwon ajali kafin mutuwarsa ya yi mana Wasici da cewa, matarsa tana da ciki, idan ya mutu ta cigaba da sarauta bisa gadonsa na mulki har ta haihu. Idan ta haihu dan ya girma ta sauka ta ba shi mulkinsa. Haka muka bi wannan umarni nasa ba saba ba, bayan mutuwarsa muka dora wannan mata mai suna Kamriyya bisa gadon sarauta. to tun wannan lokaci sai ta fara korar mutanenmu tana jawo wadansu mutane daban tana ba su mukamai a majalisar kasarmu Ana haka rannan sai ta haihu da namiji, bayan yaro ya kwana bakwai ta fito mana da shi fada muka ganshi. Amma tun daga wannan rana har yau shi shekara ashirih kénan ba mu kuma ganin yaron ba. Shi ne na zo na nemi taimako a gareka domin kuwa na ga kai Sarki ne mai girman lamari." Ko da boka Sakaradisa ya ji wannan labari sai ya dubi Sarki ya ce, Ai wannen Sarauniya da ake magana ba wata ba ce illa baiwar nan taka Kamriyya, wadda ka ba ta guba ka aike wa da Sarki Ziyyazanun domin ta ba shi ya sha, shi ne ba ta aikata hakan ba ya rike ta a zaman mata, kuma ga shi har ta shekara ashirin tana mulki amma ba ta aiko maka da haraji wai ita ma shugaba ce tana gasa da kai ai lallai ne ka yaketa." Da jin wannan magana Sarki ya fusata ya ce, Wato wannan tsinanniyyar dai na tura ta ta kashe Sarki Ziyyazanun shi ne ba ta aikata hakan ba, kuma har ta kira kanta shugaba tana jayayya da ni, to na rantse da Zahlu sai na yake ta na rusa birninta." Waziri Bahru ya ce da Sarki, Ai ba yakar ta za ka yi ba, domin kuwa ita ma yanzu ta tara sadaukai masu yawa karkashinta. Ka ga yanzu idan ka tura a yake ta kuma aka je ba ai nasara ba mutuncinka zai zube a idon sauran sarakunan duniya, a kuma rika cewa ka yaki mace kuyangarka ta gagareka. Abin da za a yi shi ne, tun da ita Kamriyya ta ki aiko maka da haraji har tsawon wasu shekaru, to ta saba maka, kuma ga Sarki Afarahu ya kashe maka dan aike, shi ma ya aikata laifi a gareka. To yanzu ka hada su yaki da junansu, duk wanda ya karya wani mu kuma sai mu rufar masa mu karasa shi. Ka ga shike nan mun huta." Boka Sakaradisa ya yi dariya ya ce, Madalla da wannan shawara taka, ai kawai ran Sarki ya dade haka za a yi, shi ke nan Wannan shawara ta yi sarki iya yi na'am da shawarar Waziri, nan da nan ya sa aka rubuta takarda zuwa ga Sarki Afarahu ya shaida masa da cewa, Mun samu labari ka kashe dan aikena Manadihu saboda haka ka aikata laifi a gareni. Amma girmanka wajenmu na gafarceka bisa ga abin da ka aikata. Amma ina so yanzu kaje ka yaki kamriyya sárauniyar yemen, shi ne diyyar da za ka biyani a maimakon Manadihu." Bayan da aka gama rubuta wanan takardar aka tashi wani sadauki wanda ake kira da suna Sijiinfili aka hada shi da sadaukai dari uku da dukiya dukiya aka umarce su da su kai wa Sarki Afarhu wanan takarda da kuma wannan dukiya. Nan da nan suka daura surada suka hau suka tafi. Can kuma Sarki Afarahu hankalinsa ya tashi saboda ya san idan Sarki Saifu'ar'adu ya samu labarin an kashe Manadihulbigali a kasarsa kuma babu zancen auren Shamatu da Sarkin ya nena ko ya san ba makawa sai ya aiko an yaki kasarsa, saboda haka ya dimauce ya rasa yanda Zai yi. Bayan wasu yan kwanaki Sijijimfili da sauran jama'arsa suka iso garin Sarki Afarahu. Ko da Sarki Afarahu ya samu labarin ai ga baraden babban Sarki sun iso kasarsa an aiko su, sai hankalinsa ya tashi, ya tara yan majalisarsa, cikin su har da Malulkussaifi da Sa'adunizZanji. Sarki ya ce, To kun ga babban Sarki can ya aiko Sijijinfiili ya yake mu sakamakon kashe Manadihul bigali." Malukussaifi ya dubi Sarki Afarahu ya ce,Kwantar da hankalinka, mu Za mu fita mu tare shi idan da nufi yake ya zo mana, za mu yake shi mu kashe shi sannan shi ma babban Sarkin da ya aiko shi mu je mu yake shi." Nan da nan sadaukai sukai ta daura surada suka hau dawaki, Malukussaifi ya shige gaba shi da Sa'adunizzanji sauran jarumai suka bi su suka fita taryar Sijijiimfili Ko da Sijjimfili ya hango irim shirin da su Malukussaifi Suka yi sai ya san lallai sun zata yaki ne ya kawo shi. Sai ya turo daya daga cikin mutenensa ya zo ya shaida musu cewa ai ba da yaki suka zo ba kawai an aiko su ne. Da suka ji wannan bayani sai suka ba Sijjinfili da jama'arsa damar su karaso inda suke da suka zo sai suka hadu suka dunguma cikin birni, aka sauki Sijijinfili da jama'arsa akai tayi musu hidima har dare ya yi duk aka kwanta barci. Bayan da gari ya waye Sarki Afarahu ya fito fada jama'a duk sun taru ana Jira a ji sakon da Sijijimfili ya ke tafe da shi. can an nutsu sai Sarki ya ce da shi, Shin menene sakon dake tafe da kai?" Sijijimfii ya dauko takardar da Sarki Saifu'ar'adu ya ba shi ya mikawa" Sarki Afarahu, shi kuma ya karba ya mikawa magatakardansa domin ya karanta. Magatakarda ya karanta kowa ya ji abin da babban Sarki ya rubuto Ko da Malukussaifi ya ji haka sai ya ce, To ai wannan ma zancen baza ne ya ya wata can ta yi masa laifi shi bai yake ta ba sannan kuma ya aiko mana wai mu je mu yake ta. a nan yana nufi kai Sarki a Karkashinsa kake kenan, to ba za mu yi abin da ya neba ba shi ya zo ya yake ta in kuma ya ji haushi mu ya zo ya yake mu Sarki Afarahu ya yi shiru yana tunanin cewa lallai Malukussaifi da Sa'adunizzanji lallai jarunmai ne na gaske, amma kuma duk da haka sai ya tuna ai babban sarki Saifa ar'adu yana da yawan sadaukai jarumai fiye da kima, kuma ya san lallai idan ya yi fiushi da su duk zai halaka su. Sai ya dubi Malukussaifi ya ce, Ya dana, ai ya zama dole mu bi umarnin babban sarki, mu Je mu yaki Kamriyya, idan ku ba za ku ba to ni zan shirya in tafi da mutanena na yake ta. Da Malukussaifi ya ji wanan nmagana ta Sarki Afarahu, sai ya yarda da hakan saboda kasancewarsa mai biyayya a wurin Sarki domin daukarsa da ya yi Uba a wajensa. Ya ce,To shike nan mun yarda da wannan magana , za mi bi ka mu je mu yaki wannan sarauniya ta kasar yemen. MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN Littafi na biyu 2 Fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi rubutawa Shuraihu Usman Part 4. . Bayan wasu yan kwanaki kadan sukai shirin yaki, Sarki Afarahu da Malukussaifi da Sa'adunizzanji da Sijijimfili da sauran Sadaukai suka fita suka kama hanyar zuwa garin babban Sarki Saifu'ar'adu, domin su yi gaisuwa da nuna amsa umarni, sannan su wuce zuwa kasar Yemen su yaki Sarauniya Kamriyya. Da zuwansu garin babban sarki, sai ya turo aka tarye su aka kai su fada kowa ya yi gaisuwa gabansa suka zauna ban da Sa'adunizzanji, shi sai ya yi tsaye yana muzurai ko gaida Sarki bai yi ba. Ganin haka sai babban sarki ya dubi Sarki Afarahu ya ce, Shi kuma wannan waye wanda yake tsaye?" Sarki Afarahu ya ce, Wannan shi ne Sa'adunizzanji." Babban Sarki ya ce, To shin shi ya fiku ne duk kun yi gaisuwa amma shi yana tsaye Ko da Sa'adunizzanji ya ji wannan magana sai ya fusata ya ce da babban Sarki, To don me zan gaishe ka, kana zaton ni talakanka ne, to baka isa na gaishe ka ba." Nan da nan sai jayayya ta balle tsakanin babban Sarki da Sa'adunizzanji, su kai ta yi Can sai boka Sakaradisa ya matsa kusa da Sarki Saifu'aradu ya rada masa ya ce, Ran Sarki ya dade, mai ya kai ka jayayya da wannan bakin bawan. Ai in ka biye masa yanzu yaki ya tashi a nan, ka rabu da shi kawai ya fi" Sarki ya yarda da wannan shawarar ta boka ya daina jayayya da Sa'aduniZZanji, ganin haka shi kuma Malukussaifi ya umarci Sa'aduni da ya zauna, sannan ya zauna. Akai ta fitowa da abinci iri-iri ana baiwa jama'a, suka ci suka sha, kai haka dai akai ta yin hidima har kwana biyu Bayan wadannan kwanaki sai babban Sarki ya sallame su suka fito domin su tafi su yaki sarauniya Kamriyya. A wannan lokacin bayan sun fito sai Malukussaifi ya umarci Sarki Afarahu da ya koma gida shi da Sa'adunizanji da sauran sadaukai za su tafi wurin wannan yakin. Sarki Afarahu da rabin mutanen da suka fito suka koma gida, Malukussaifi da Sa'adunizzanji da sauran sadaukai suka kama hanyar su ta zuwa Yemen domkn su yaki Sarauniya Kamriyya. A lokacin da suka je kasar babban Sarki Saifu'ar'adu kafin su fito, bash san ba sai babban Sarkin ya rubuta takarda zuwa ga Sarauniya Kamriyya ya ce,"Zuwa ga sarauniya Kamriyya, na rubuto miki wanan takarda domin ina so ki biya ni haraji har na iya tsawon shekarun da kika yi kina mulki. ldan kuma ba haka Ba rundunar mayakana suna nan tafe Zuwa gareki Da ya gama rubuta wannan takardar sai ya aika wa wani dogari ya umarce shi da ya yi maza ya tafi kasar Yemen ya kai wa Sarauniya Kamriyya. Bayan yan kwanaki dogarin nan ya isa birnin Yemen da zuwansa ya wuce zuwa fada a kai masa iso ya shiga ya yi gaisuwa ya fadi sakon Sarki. Da Kamriya ta karanta wannan takarda sai ta ce da dogarin nan, in ce ko dai shi Sarki Saifi'ar'adu ba shi da hankali ne? Yanzu kamar ni ya ce in biya shi haraji, to ka koma ka gaya masa ba zan biya shi ba, kuma idan yaki ne zamansa nake. Kwana biyu da yin wanannan sai Kamriyya ta samu labarin ai ga wata rundunar mayaka nan ta nufo biminta kuma ga yadda labarin ya zo mata ta firgita da jin yadda aka gaya mata yawan su da kuma irin shirinsu. Wato wannan runduna ba wasu bane illa Malukussaifi da Sa'adunizanji da Sijijimfilk da sauran jama'ar da suke tafe da su kafin magaruba Malukussaifi da jama'arsa suka karato birnin yemen suka hangi katangar birnin an gina ta da farin dutse da manya manyan kofofi na jan karfe. A nan sai ya umarcesu da su sauka a nan su kwana, gari na wayewa su auka cikin garin da yaki, nan duk aka sauka aka kafa rumfuna na tanti, duk suka saki dawakinsu domin Su yi kiwo su kunma kowa ya shiga rumfarsa ya kwanta aka bar wasu suna gadi Can bayan an natsu cikin dare sai Kamriyya ta hau doki ta sulalo ta fita daga cikin birni ta nufo inda su Malukussaifi suke. Da Zuwa da sai ma su gadun nan suka tare ta suka tambaye ta ina za ta, ta ce da su ai ite lallai shugabans take so ta gani nan da nan aka je aka gaya wa Malukussaih cewar ga wani mutum ya fito daga cikin birnin nan ya ce lallai kai yake so ya gani ya ce ku je ku ce da shi ya koma gebe ya dawo. suka komo suka gayawa kamriyya amma sai ta ki ta dage, ta ce ta lallai sai ta gan shi, suka koma suká sake gaya wa Malukussaifi, sai ya ce a shigo da shi, aka shigo da Kamriyya duk suka fita suka barsu su biyu a cikin tanti. Malukussaifi ya ce, Me ke tafe da kai?" Kamriyya ta bude fuskarta ta ce, "ba namiji ba ne, ni mace ce kuma ni ce Kamriyya Sarauniyar wannan birnin da kuka kawo wa yaki. Abin da ya kawo ni shi ne, na ga rundunarka tana da karfi kuma ni ma tawa rundunar tana da karfi, sai na ga in mu kai yaki za a zubar da jini sosai, shi ne na zo yanzu mu yi kokawa ni da kai duk wanda ya yi nasara a kan dayan to shike nan ya ci shi da yaki, ba sai an gwabza a filin daga ba. Da ya ji wannan magana tata sai ya ki ya ce sam shi ba zai yi kokawa da ita ba, tana mace shi yana namiji. Haka dai sukai ta jayayya har ta shawo kansa ya yarda za su yi kokawar. Kamriyya ta cire duk kayan dake jikinta ta tsaya daga ita sai wata riga doguwa mai shara-shara, wadda duk ana ganin halittar jikinta. Ita ta yi haka ne domin ta yaudari Malukussaifi ya kamu da sha'awarta ta samu ta yi galaba da shi. Shi kuma da ya ga haka sai ya ce bai yarda ba, ba zai yi kokawar a haka ba, sai ta sa kayanta. Ta rika kawo masa wabta yana gocewa har ta yaga masa riga ganin haka shi kuma sai ya fusata ya cire rigarsa, yana Cirewa sai Kamriyya ta ga sarkar nan da ubansa ya ba ta kafin ya mutu ya ce in ta haihu ta rataya wa dan a wuyansa. Tana ganin haka, sai jikinta ya yi sanyi ta tambaye shi inda ya samu wannan sarkar ya gaya mata, ya ce shi dai tashi ya yi ya ganta a wuyansa tun yana karanmi. Nan da nan ta ce, Wallahi kai dana ne, duk inda a kai kai dana ne, domin kuwa wannan sarkar asalinta ta ubanka ce Sarki ziyazzanun. Kafin mutuwarsa ya bani ita ya ce idan na haihu na rataya wa dan da na haifa a wuyansa, shi ne da na haife ka na rataya maka i ta, kuma tana wuyanka na je far da kai a daji. Ni ce uwarka." Malukussaif ya ce ai shi bai yarda ba, ya za ai in dai uwar tasa ce ita ta yada shi, Sukai ta jayayya can sai ya ce, To na ji. yanzu meye kuma shaidar ki bayan wannan Ta ce.akwai shaida, zan koma cikin birni zan zo da irin yaran ubanka domin su yi maka shaida." Nan da nan Kamriyya ta koma cikin birni ta kirawo wasu tsofaffi su hudu wadanda suka rage daga cikin yaran Sarki Ziyyazanun, ta taho da su gurin Malukussaif ta ce da su, Ku raba mana wannan gardarmar, ni na ce dana ne, shi kuma ya ce ba shi bane."Tsofaffin nan suka dube shi suka ga yar alamar nan dake kundukukinsa (kumatunsa kenan), sai suka ce, lallai babu shakkar cewa danta ne,"Shugabanmu ne kai, mun rasa ka yau tsawon shekara ashirin da daya." Nan dai har sai da Malukussaifi ya gasgata su ya san lalai Kamriyya uwarsa ce ba aljana ba ce uwarsa. Sai ya ce da ita, Ke kuwa me ya sa kika yadda ni kina mahaifiyata?" Kamiyya ta fashe da kuka, ta zare takobinta ta mika masa ta ce, dana, karbi takobin nan ka yanka ni, domin ka rama abin da na yi maka, domin ni yanzu burina na duniya ya cika tun da na sake saka ka a idona. Yimaza ka yanka ni ka shiga birninka, kaci gaba da mulki. "Malukussaifi ya rungume ta yana hawaye yana cewa, Ki yi shiru ba komai." Bayan haka sai Kamriyya ta ce, Ai sai ka kwana a nan, gobe da safe za mu fito ni da jama'ar gari baki daya. Mu zo mu tarye ka mu shigar da kai garinka, in baka mulkinka." Sukai sallama Kamriyya da tsofaffin nan suka koma cikin birni. Da komawarsu ta bai wa tsofaffin nan abinci da guba suka ci duk suka mutu, babu wanda ya san abin da ya faru, ta zauna tana bakin ciki tana cewa a zuciyarta, "Ka ga shegen yaron nan da na jefar da shi don ya mutu saboda kada ya karbe mulki na, ashe bai mutu ba ya dawo. Haka dai ta zauna tana ta tunanin makircin da za ta sake kullawa danta Malukussaifi. Can sai dabara ta zo mata, ta tashi ta hau doki cikin wannan daren ta kuma komawa bayan gari wurin Malukussaifi. Da Zuwanta a kai mata iso ta shiga ta ce, Ya dana na dawo. Abin da ya dawo da ni shi ne, na z0 ne domin na faiyace maka dukkan yanda lamarin ya faru a baya. Ni na kasance na kan sami tabin hankali wani lokacin, Wani lokacin ka ganni da hankali. Lokacin da na yadda kai ba nida hankali, a wannan lokacin ban san abin da nake ciki ba. Na ki gaya maka ne dazu saboda ganin wadannan mutane da na zo da su. Abu na biyu kuma shi ne, ubanka ya bar maka dukiya mai yawan gaske, saboda gudun kada wasu daga cikin Sarakunan duniya su kwace maka ita sai na debi mutane muka dauki dukiyar muka tafi can dan daji muka binine ta. Bayan mun binne wannan dukiya, mulanen da na je da su sai na kashe su, yanzu duk duniyar nan babu wanda ya san inda wannan dukiya take sai ni. Saboda haka yanzu tashi mu tafi in nuna maka dukiyarka." Bai yi musu ba ya tashi ya bita suka hau dawaki suka kama hanya sukai ta tafiya cikin daren nan, har gari ya waye rana ta fito suna ta tafiya subiyu cikin daji har rana ta tafi. Kai haka dai sukai ta kutsa kai cikin daji su biyu har kwana uku. A cikin wannan hali duk lokacin da dare ya yi sai ta kwanta ta yi barci shi kuma ya tsaya yana gadinta har sai ta farka, sannan su ci gaba da tafiya. To a wannan rana ta uku sai barci ya kama Malukussaifi, mahaifiyarsa ta ce, To yau kai ma ka yi barci ni kuma na yi gadinka." Malukussaifi ya kwanta ya tada kai da cinyar mahaifiyarsa ya fara barci. Cikin kankanin lokaci sai ya fara minshari, barcinsa ya yi nisa. Ko da Kamriyya ta fahimci ya yi nisa cikin barci, sai ta zame jikinta a hankali ta tashi ta dauko wata Gariyo (wuka) mai guba ta dubi kan Malukussaifi ta kafta masa sara jini ya yi tsattuwa sama, ta kuma saransa a wuyansa, ta sake saransa a kirji, sannan ta yanke shi a ciki. Ta juya ta hau dokinta ta tafi ta barshi cikin jini kwance, tana zaton ta kashe shi. Haka ya kasance cikin wannan hali har asuba ta yi, sanyin asuba ya buge shi ya farka daga suman da ya yi. Malukussaifi ya ga duk jikinsa jini ya yunkura zai tashi amma sai ya kasa saboda gubar dake jikin gariyon nan ya shige Shi nan sai ya yi addu'a ya roki Ubangiji da ya kawo sababin da zai kubuta daga wannan hali da yake ciki. Yana rufe bakinsa sai ya ga wasu tsuntsaye guda biyu sun zo sun sauka akan wata bishiya da take kusa da shi. MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN Littafi na biyu 2 Fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi rubutawa Shuraihu Usman Part 5. . Daya da ga tsuntsayen sai ya dubi dayan ya ce, "Shaihu Jayyada, ka ga fa wannan uwarsa ce fa mahaifiya ta aikata masa wannan aiki, Saboda kwadayin mulki kawai " Sai daya tsuntsun ya amsa ya ce, Haka ne Shaihu Abdussalam, amma ka ga da zai ci ganyen wannan bishiyar ya shafa a jikinsa da sai ya warke sarai, kamar ma bai yi Wani ciwo ba." Bayan sun gama zantukansu sai tsuntsayen suka tashi Suka tafi Shi kuma Malukussaifi yana daga kwance ya ji duk maganganun tsuntsayen nan sai ya kuma yin addu'a ya roki Ubangiji ya Kawo sababin yadda zai iya samun ganyen wannan bishiyar. Nan da nan sai iska ta taso ta girgiza bishiyar ganyenta ya zubo masa a jiki, ya Samu ya kama guda daya da lebensa ya auna ya hadiye, da yin haka sai ya fara jin karfin jikinsa. ya mika hannu ya sake dauko ganyen ya rinka gogawa a jikinsa. Nan da nan duk jikinsa ya warke, ya mike ras, kai ba ka ce ma wani abu ya taba Samunsa ba. Ya tashi ya yi godiya ga Madaukakin Sarki, ya hangi dokinsa yana kiwo. ya bi shi ya kama ya hau ya kama hanya ya fara tafiya, ba tare da ya san inda ya nufa ba. idan ya ji yunwa sai ya ci daga ya yan itatuwa. yana shan ruwa daga kwazazzabai Bayan Malukussaifi ya samu kwana arba in yana tafiya cikin daji. Sai ya hango wasu manyan duwatsu guda biyu masu tsayi, tsakanin duwatsun akwai kogi mai gudu ya raba su. Daya dutsen wanda daga bangaren hagu wato bangaren da Malukussaifi yake ja ne, dayan kuma na dama da shi fari ne. Da ya karaso gindin wannan jan dutsen Sai ya ga wani kogo a jikinsa, ya ji ana magana daga cikin kogon ana cewa, Barka da zuwa Malukussaifi dan Sarki Ziyyazanun, dan Tabi'ul Yamani, dan Usudul baida'a, dan Samu dan Nuhu Alaihissalatu wassalam. Sai ya ga wani farin mutum dogo ya fito daga wannan kogon yana yi masa barka da zuwa cike da farin ciki Sai ya tambayi mutumin ya ce, Kai kuwa ya ya a kai har ka san Sunana, bayan kuma kai ba ka taba gani na ba sai yau?" Sai mutumin ya ce, Ai yau shekara ta ashirin ina zaune a nan ina jiran zuwanka, domin na nusassheka aijiyar da kakanka SAMU ya yi maka, kuma ni ma dai na gaji wannan gadin a wajen babana, shi ma wajen kakana ya gada, Shi kuma a wajen nasa uban, shi kuma a wurin kakansa. mutumin nan ya kama hannun Malukussaifi suka shiga cikin kogon nan. da Shigar su sai wannan mutum ya yi tafi sai ga kujeru guda oiyu an kawo tare da abinci. Suka zauna sai mutumin ya ce da Malukussaifi ya ci wannan abinci. Shi kuwa sai ya ce, Ya ya za'ai in ci abincin alhalin ban ga wanda ya kawo shi ba, ai ba zai yiwu ba. Shin wai kai yaya Sunanka ne kuma mene ne addininka? Mutumin nan ya amsa masa da cewa, ni sunana Ihimimiddalibi, kuma ni Malami ne. ina bin Addinin Annabi Ibrahim (AS). Saboda haka ka gasgata ni ba zan cuce ka Da. Da ya ji wannan bayani na Malam Ihimimuddalib, sai ya saki jikinsa Suka kama cin abinci Bayan Sun ganma cin abincin nan. sai Ihimimuddalib ya ce da Malukussaifi. To gobe da asuba za mu fita mu hau sanman dutsen nan zan jarraba ka domin na tabbatar da cewa kai ne mai wannan ajiya ko kuwa ba kai bane." Nan suka kama zikirillahi har dare

Chapter 2 of 5