Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 5
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN Littafi na biyu 2 Fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi rubutawa Shuraihu Usman Part 1. A littafi na farko idan mai karatu bai manta ba, mun tsaya a inda Aljana Akisa ta dawo da Malukussaifi birnin Kaimaru daf da rijiyar nan da Sarki Kamrunu ya sa aka jefa shi, ta yi masa sallama ta tafi bayan ta ba shi hular sa wadda ya samo. Malukussaifi ya tsaya yana tunanin yadda zai yi ya shiga birnin Kaimaru saboda yana tunanin ko ya sanya hularsa ta bata ko dakon garin nan wanda ake kira gammazi zai ganshi saboda na tsafi ne, haka dai ya tsaya yana ta tunani a bakin kofar shiga birnin Kaimaru. Can kuma a cikin birnin Kaimaru Damatu yar bokanya Akila tun ranar da Sarki ya sa aka jefa Malukussaifi a rijiya duk ta rude, hankalinta ya tashi domin ta san ba makawa sai va halaka,sai ta samu uwarta bokanya Akila ta ce da ita, "Ya ke wannan uwa tawa ma'abociyar yawan hikimomi, da kin buga kasa kin bani labarin Malukussaifi tun kafin zuwansa kuma har kika gaya mini ai shi ne ma mijin da zan aura to amma ga shi yau sarki zai halaka shi, saboda haka yanzu ya zama dole a kan ki ki yi amfani da irin hikimominki na tsafi ki kubutar da shi in kuwa ba haka to lallai ni ma zan kashe kaina na huta da radadin begensa da yake damuna." Ko da uwar ta ji haka ita ma sai hankalinta ya tashi jin yarta ta ce za ta kashe kanta sai ta ce, Ki yi hakuri, ki kwantar da hankalinki, zan yi iyaka bakin kokarina sai na ga na kubutar da shi da ga wannan halaka da ya abka." Haka tai ta yi mata dabara Tana rarrashinta har zuwa wannan rana da Aljana Akisa ta dawo da Malukussaifi bayan wannan garin Awannan ranar bokanya Akila tana gida tana buga kasa tana bokancinta, a cikin haka sai ta hango Malukussaifi a bayan gari yana tunanin yadda zai yi ya shigo ba tare da Gammazi ya yi masa komai ba. Ko da ta ga haka sai ta yi kiran yarta Damatu ta gaya mata, Ai ga Malukussaifi can a bayan gari yana tunanin yadda zai yi ya shigo. yanzu sai ki yi maza ki je ki same shi ki ce da shi ya shigo duk ta inda yake so domin kuwa gunkin nan gammazi tuni na lalata shi. Suna cikin haka sai suka ji ana bubbuga kofar gida, bokanya ta ce. To shi ke nan ma ya hutar da mu, ga shi can ya shigo yana buga kofa maza je ki. ki bude masa ya shigo," Damatu ta yi zumbur ta mike ta nufi kofar gida ta zare sakata ta bude kofa. Ko da su kai ido hudu da Malukussaifi sai suka rungume Juna suna shisshidar numfahi irin na ma'abota bege, sannan suka shiga cikin gida wurin uwarta, ita ma ta yi masa maraba a kai masa shimfida ya zauna sannan suma suka zauna tare da shi. Zaman su ke da wuya bokanya Akila ta mika hannunta baya ta jawo wani katon tire wanda yake cike da abinci da na sha iri- iri, suka ci suka sha, amma Damatu ta kasa cin abincin saboda bege tana zaune kurum ta kurawa Malukussaifi ido tana kallonsa tana mai cike da buri da bege Bayan da ya huta ya kwashe labarın duk abin da ya faru tun da ga lokacin da aka jefa shi a rijiya har zuwa wannan rana da Aljana Akisa ta dawo da shi ya gayawa bokanya da yarta kuma ya nuna musu hular da ya samo. Bayan haka ya kara da cewa, To ni fa ba zama ne ya kawo ni ba. yanzu ina dabarar yadda zan yi na dakko littafin nan na Halwanu Bokanya ta amsa masa da cewa. to ai yanzu wannan abu mai sauki'ne tun.da ga wannan hula taka, ai za ta taimaka maka kwarai Yanzu yau shauran kwana biyar ranar zuwa bautar wannan littafi ta zo sai ka bari a wannan ranar zan fita tare da kai ka saka hulanka yadda babu wanda zai ganka idan mun je mun yi sujjada Sai kawai ka dauko ka fito." Ya yi na'am da wanan shawara ta ta suka ci gaba da zama har kwana biyar wato anar fita bautar ta zo. A Wannan ranar bokanya ta yi shiri ta fita izuwa fada sauran bokaye. na biye da ita, cikinsu hadda Malukussaifi, amma babu wanda yake ganinsa saboda ya saka hularsa. Da zuwansu fada Suka tarar wuri ya cika macik da jama'a,bokanya akila da Jama'arta suka nemi wuri suka zauna shi kuwa Malukussaifi ya je gaban Sarki ya zauna babu wanda ya ganshi jim kadan Sarki yà yi umarni a tashi a tafi wajen bauta, Sarki da bokanya da duk sauran jama'ar gari aka tashi aka Qunguma zuwa wajen bautar littafi. Da zuwansu Sarki da kansa ya sa makulli ya bude kofa suka shiga da duk sauran jamaa, Sannan ya kuma dakko wasu 'ya'yan makullan ya bude adaka ta farko ya bude ta biyu ya bude ta uku ya ga littafi yana nan yadda yake, nan ya sunkuya yana mai wa littafi sujjada. Ko da Malukussaii ya ga haka duk sun sunkuya sai ya nufo wannan littafin kafin ya kai ga inda littafin yake sai littafin ya fado gabansa, ko da Sarki da sauran jama'ar dake kusa suka ji motsin fadowar wannan littafi, duk sai suka mike suka ga littafi na gewayawa amma ba su ga kowa a wurin ba. Sai suka tsaya Suna kallo , shi kuma Malukussaifi da ya ga haka sai ya sa hannu ya dau littafin yana dauka sai jama a suka daina ganin littain. koda ganin haka Sarki Kamrunu ya yi wa mutanensa tsawa ya umarce su da su fita duk inda wannan littafi ya shiga su nemo masa shi. Ran Sarki ya baci hankalinsa ya tashi idanuwansa suka kada sukai jazur kamar an hura wuta. Haka jama'a sukai ta jewa har dare' ba su ga iittafi ba, a karshe dai suka zo suka gaya wa Sarki cewa sun gaza samo wannan littafi. Sarki ya juya ya dubi bokanya Akila ya ce,Ya ke ma'abociyar yawan hikimomi da dabaru na mika wannan lamari a hannunki, ki san duk yadda za ki yi ki ga kin gano inda wannan littafi ya shige." Da akila ta ji wannan magana ta Sarki sai ta ce ai wannan abu ne mai sauki, da sannu zan binciko maka inda wannan littati yake, kai sai ma na kawo maka wanda ya dauke shi nan gabanka." Haka dai ta yi tai wa Sarki kalamai na na lami, da kartafa gwuiwa har iyarsa ta yi sanyi sannan ya sallami jama'a kowa ya tafi zuwa gidansa. bokanya Akila na komnawa gida Sai ta tarar da Malukussaifi yana zaune ga hula ga littafi a gabansa, ta nemi wuri ta zauna. Zamanta ke da wuya sai ya ce,To ni fa yau bukata ta ta biya tun da na samu littafin nan gobe zan kama hanyar komawa garin mu, kuma ina matukar godiya ga dukkan irin taimakon da ki kai min ba zan taba manta wa dake ba." Da ta ji haka sai ta ce, "I, ai kuwa lallai bukatarka ta biya, amma kuma ni ma ina so ka cika mini burina kamar yadda naka ya cika. Burina kuwa shi ne ka auri 'ya ta Damatu ma'abociyar kyawu kafin ka bar garin nan. Wannan kawai shi ne bukata ta." Ko da ya ji wannan magana sai ya ce shi sam wannan ba za ta yiwu ba, domin ya riga ya yi alkawarin ba zai auri wata ya mace ba har sai ya auri Shamatu 'yar Sarki Afarahu, haka sukai ta jayayya da shi da ita, amma sam ya ki yarda. Can ita kuma Damatu tana daga dakinta, tana jin duk irin jayayyar da suke yi, ko da ta ji ya ce ba zai aure ba ta, sai ranta ya baci hankalinta ya tashi, haka ta raba dare tana tunani, can sai ta tashi ta shiga dakin da Malukussaifi yake kwance, sai ta tarar da shi ya yi nisa a cikin barcinsa, sai ta dauke hular nan tasa ta yi kokarin ta dauke littafin ammna sai tai gudun kar ya farka saboda da shi ya tada kai sai ta hakura ta koma dakinta da hular. Gari na wayewa Malukussaifi ya farka daga baricinsa ya duba ya ga bai ga hularsa ba, nan da nan ya tambayi bokanya ko ita ta dauka, ta ce ba ta dauka ba. Suna cikin haka sai Damatu ta shigo ta ce masa, "Ni ce na dauke hular kuma ba zan baka ita ba, har sai ka aure ni." Da jin wannan sai ya yi shiru, can sai ya tuna da hudubar da Shaihu Jayyada ya yi masa ta cewar ya dogara ga Allah, a dukkan lamarinsa. Nan da nan sai ya fusata ya ce, Ba zan aure ki ba, hula kuma ki rike, ni na dogara da Allah shi zai kubutar da ni." Ya tashi ya yi musu sallama ya kama hanyar sa ta komawa gabar kogin nan da dabbar nan Hashisha ta kawo shi. Ita kuma bokanya Akila bayan da rana ta dan daga, sai ta yi Shiri ta tafi fada. Da zuwanta ta fadi gaban sarki ta yi gaisuwa ta nemi wuri ta zauna, zamanta ke da wuya,sai Sarki ya dube ta ya Ce Ya ke mai yawan hikimomi ya labarin littafi me kika gani game da shi kuma?" Akila ta ce, Ai wato wanda ya dauki wannan littafi ai yanzu ma ga shi can ina kallonsa ya kama hanyar zuwa bakin kogi, yanzu maza ka sa a bi shi a kamo shi." Nan da nan Sarki ya yi tsawa, sadaukai mayaka duk suka mike ya umarce su da cewa maza su bi wannan mutumin su kamoshi. Nan da nan suka daurawa dawaki sirada suka hau, kimanin mutum dari biyar suka bazama neman Malukussaifi. Shi kuma can Malukussaifi ya samu kwana biyu yana tafiya cikin dajin yana Cin ya'yan itatuwa, yana shan ruwan kwazazzabai. A rana ta uku, yana cikin tafiya sai ya ji karar kofaton dawaki suna biye da- shi. Ko da ya waiga ya hango mutanen nan da Sarki ya turo a sukwane kan dawaki, sai ya ranta a na kare, ya yi ta gudu suna biye da shi har dare ya yi. Sai ya Zo wani waje mai duwatsu cikin duhun dare, ya kwana karkashin wani dutse duhu ya boye shi Su kuma mutanen nan su kai ta neman sa amma ba su gan shi ba, sai suka tsaya suka tattare hanyoyi suna jira gari ya waye Su kama shi Da Malukussaifi ya ga haka sai ya yi tunanin a kan cewa yanzu dabbar nan Hashisha tana kwance a gabar kogi, tana jira rana ta bullo. A nan sai ya yi ta rokon Allah yana fatan ya boye shi, ya wuce ba tare da mutanen nan sun ganshi ba. Allah ma ji rokon bawañsa, ya amsa addu arsa. Haka ya fito ya ratsa ta cikin mutanen nan ya wuce amma ba su gan shi ba. Da zuwan Malukussaifi gabar kogi ya tarar da dabbar nan Hashisha tana kwance. ya yi tsalle ya dafe gashin ta ya yi lif Can su kuma mutanen dake neman sa, da gari ya waye 'suka duba ba su ganshi ba, sai suka rika bin sawunsa cikin yashi har kusa da gabar kogi. A wannan lokacin ita kuma wannan dabbar ta fara ruri ta mike, mutanen nan duk Suka juya a firgice saboda jin kukan Hashisha, suna cewa, Aiya, wannan ai ya hadu da Hashisha ta lashe, ai sai mu koma mu ga ya wa Sarki. MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN Littafi na biyu 2 Fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi rubutawa Shuraihu Usman Part 2. Haka suka Koma gaban sarki a sukwane suKa shaida masa ai wanda ya dau littafin Hahisha ta lashe shi. Bayan faduwar rana Hahisha ta kwanta a waccan gabar Malukussaifi ya sauka ya kama hanyar komawa hasumiyar Shaihu Jayyada. Da zuwansa ya yi masa sallama, Shaihun ya amsa ya yi marhabin da zuwan Malukussaifi kuma ya kwashe labarin duk abin da ya faru gareshi a tafiyarsa ya gaya masa, kamar yana nan akai ya gaya wa Malukussaifi. Sannan kuma ya tuna masa da cewa shi gobe zai mutu, idan ya mutu, ya yi masa wanka ya sa likkafani ya rufe shi, sannan kuma zai ga wasu mutane sun zo jana' izar sa ka da ya yi wa kowa magana daga cikinsu. Haka kuma bayan an gama zai ga sun koma, kada ya waiwaya har sai ya daina jin motsinsu, sannan ya binne Shi ya yi tafiyarsa. Asuba na yi Shaihu Jayyada ya cika, Malukussaifi ya aikata komai kamar yadda ya umarce shi. Bayan ya gama tsaf. ya kamo dokinsa ya yi masa sirdi ya hau ya kamo hanyar komowa kasar Duwar. kasar Sarki Afrahu inda aka raine shi. Can kuma a kasar Duwar din Sa'adunizzanji ya kosa da rashin dawowar Malukussaifi ubangijinsa. Wata rana Sarki Afarahu yana fadarsa tare da sauran jama'a, ga boka Sakaradiyyuna na zaune a gefen sa sai Sa'adunizzanji ya shigo fadar cikin fushi nan da nan Sarki da sauran jama'a duk suka mike tsaye cikin rawar jiki. Sa'adunizzanji ya numfasa ya ce da Sarki, Wato kun tura uban dakina neman wani littati kun tura shi ga halaka ko, to nan da yan kwanaki kadan idan bai dawo ba na rantse da tauraruwa zahallu duk garin nan sai na halaka ku." Ya juya ya fice a fusace. Ko da ya fita sai Sarki Afarahu cikin dimuwa ya dubi Sakaradiyyuna ya ce, Ka gani duk kai ka jawo mana wannan bala'in. Boka Sakaradiyuna ya ce da Sarki Afarahu, Kwantar da hankalinka, wannan ni zan sabbaba abin da zai halaka shi." Nan sai boka Sakaradiyyuna ya rubuta takarda zuwa ga dan uwansa boka Sakaradisa dake can fadar babban Sarki Saifu'aradu. Ya kwashe labarin duk irin abubuwan da suka faru game da lamarin Malukussaifi har zuwa inda ya nemi auren Shamatu da yanda ya tura shi ya zo da kan Sa'aduninzanji, ya kuma gaya masa yanzu ma ya tura shi ya nemo littafin Halwanu. Sannan kuma ya ce da shi ya gayawa babban Sarki Saifu'radu wannan labari, ya kuma gaya masa idan har wannan yaro ya auri Shamatu to zai zamto sanadiyyar rushewar mulkinsa sannan kuma zai mai da su bayi, addu'ar nan da Annnabi Nuhu (AS) ya yi ta tabbata a zamaninsu. Ya kuma ce ya gaya wa Sarki ya aiko wa da Sarki Afarahu da kyauta ya kuma nemi auren Shamatu domin ya kare mulkinsa daga kubucewa daga hannunsa. Ya kuma ce ka ga ko da wannan yaron ya dawo mana a kan bukatarsa, sai mu ce ya taho wajen babban Sarki ya karbeta, ballantana ma na san yanzu wannan yaron ya halaka tuni. da ya gama rubuta takarda sai ya bai wa wasu bayi su bakwai ya ce su tafi can kasar babban Sarki Saifu'aradu su kai wa dan uwansa boka Sakaradisä wannan takarda nan da nan bayin nan suka kama hanya kwanci tashi, har suka isa wanan kasa. Da zuwansu suka kai wa boka Sakaradisa wannan takarda, ya karba ya bude.ya karanta ta sai ya mayar ya ajiye yana jiran gari ya waye da safe ya tafi da ita fada ya karantawa Sarki Saifuar'adu ita. Waye war gari ke da wuya, boka Sakaradisa ya shirya ya tafi fada, ya kwashe laberin dake cikin takardar nan kaf ya gaya wa Sarki, kuma ya kwadaitar da shi auren Shanmatu. Ya umarce shi da ya nemi aurenta kamar yadda aka rubuta a cikin takardar nan Ko da Sarki ya ji haka nan da nan, sai ya sa aka kawo wasu manyan adaku çike da dinari guda hudu, ya kuma sa aka kawo wesu adakun guda biyar cike da kayan ado irin na mata da abubuwa iri-iri na daga nau'in dukiya, sannan ya sa aka kirawo wanj babban Sadauki daga cikin mayakansa, wanda ake kira manadihu, tsawonsa Kamu saba'in ne ga shi da manyan idanuwa jajaye, ga shi baki mai katon kai da gajeren wuya mai ladi da lafta-laftan kafafuwa. Kai saboda gimansa ma ba ya hawa doki sai giwa. Da zuwan Manadihu ya fadi gaban Sarki yai gaisuwa. Sarki ya umarce shi da ya dauki wannan dukiya ya tafi garin Sarki Afarahu ya kai masa ya kuma gaya masa yana neman auren yarsa ne Shamatu. ldan ya yarda ya shaida masa ya dauke masa haraji na shekara bakwai kuma duk sauran kasashen dake kusa da kasarsa, harajinsu na wadannan shekarun ya karfa ya bashi. idan kuma ya ce ya ki to ka yake shi da shi da Sa'adunizzanji, ka zo min nan da su a daure cikin sarka, Manadihu ya ce, An gama" Nan da nan Manadihu ya koma gida ya yi shiri ya kuma zabi sadaukai dubu wadanda zai tafi da su. suka kama hanyar zawa garin Sarki Afarahu. Sukai ta tafiya dare da rana ba ji ba gani, har suka iso kasar sarki Afarahu da zuwansu sarki ya tarye su aka kai su masauki akai tai musu hidima har dare ya yi, sai Sarki ya ce su huta sai gobe da safe ya ji abin da yake tafe da su. Bayan da gari ya waye rana ta dan daga fada ta cika makil, Manadkhu da sauran abokan tafiyarsa suka shigo fada domin su isar da sakon bebban Sarki Saifura'adu a wajen Sarki Afarahu bayan duk sun yi gaisuwa sun zauna, sai Sa'adunizzanji ya shigo fadar. Da shigowar sa sai aka mike tsaye har da Sarki Afarahu, sai Manadihu ne kawai bai mike ba yana zaune sai Sa'adunizzanji ya dubi Sarki ya ce, Wannan shi kuma waye shi daga. ina ya zo wannan gari' Sarki ya amsa masa ya ce, "Ai Wannan dan aike ne daga babban Sarki Saifuar'adu." Sa'adunizzanji ya ce, To shi ya fika daraja ne da har kai za ka mike yana zaune? Ya dubi Manadihu cikin fushi ya daka masa tsawa mai firgitarwa ya ce kai munafiki bakin kare me ya kawo ka nan? Manadihu ya fusata ya ce, yau ga la'anan ne, kai waye kai za kai min wannan tambayar? Ko kai ne Sa'adunizzanji, wanda Sarki ya ce in kai masa kai a daure cikin sarka. To yau kashinka ya bushe, abin da ya kawo ni wannan gari kuma shi ne babban Sarki ya turo ni na nema masa auren Shamatu ne idan kuma kun ki na yake ku. Ko da Sa'adunizzanji ya ji wannan magana sai ya ce, Au matar ma uban dakin nawa ka zo nema to karya kuke." Ya yi wuf ya zare takobi kafin Manadihu ya ankara ya tsinke masa ka ya kashe shi." Da boka Sakaradiyyuna ya ga haka sai ya dubi Sarki ya ce, La,la,la, to maza ka umarci duk jama'ar nan su yaki Sa'adunizzanji. In kuma ba haka ba, to wallahi Zan aikawa da babban Sarki in ce kai ne ka sa aka kashe dan aikensa Manadihu." Nan da nan Sarki ya umarci jama'arsa da sauran sadaukan nan dubu su yaki Sa'adunizzanji da yaransa su tamanin din nan. Nan da nan guri ya kaure da yaki aka yamutse ba ka iya jn komai sai kuwwar mazaje da karar karafkiyar takubba da karar duka da kulki, haka a kai ta gwabza yaki har tsawon kwana uku. A rana ta ukun ana cikin gwabza yaki Sa'adunizzanji ya gaji sun rufar masa gabadaya suna neman kama shi. Can sai suka hango wani sadauki a sukwane bisa doki. Da zuwansa sai suka gane ai Wahashilfala ne ya dawo. Ya kutso cikinsu yana kakkare sara da bugu, can sai ya ga ai Sa adunizzanjl ne ake yaka. Koda shi Sa'adunizzanji ya hango shi sai ya ce da shi,Taimake ni, saboda kai suke yakata. Nan da nan Malukussaifi ya hau su da sara da bugu da kulki da suka da mashi, cikin wasu yan sa'o'i ya yi musu muguwar barna ya rarake su, suka juya zuwa gurin da Sarki yake zaune suka shaida maasa ai Wahashil fala ne fa ya dawo yake yakar su saboda haka Sarki ya tsayar da yaki in ba haka ba to zai karar da su a wannan rana. ko da Sarki ya ji wannan labari sai ya mike ya hau dokinsa ya nufo filin daha ya yi tsawa da a daina yaki, duk aka tsaya cirko-cirka. malukussaifi ya yi wa kansa kirari ya yi kira ya kare da cewa ni ne Malukussaifi dan Sarki ziyyazanun Sarki A farahu bu ya bugi dokinsa ya kusanci Malussaifi, da Zuwansa sai ya sau ka daga dokinsa ya je gabansa ya durkusa yana mai ladabi da kalamai na nuna nadama da neman gafara. Ko da Malukussaifi ya ga haka, nan da nan shi ma sai ya sauko daga dokinsa ya kama hannun Sarki ya ce, "ai kai ubana ne ba kome na yafe maka. Haka dai aka sasanta su ka dunguma cikin birni baki daya. da gari ya waye Sarki ya fito fada ya zauna, boka Sakaradiyyuna na kusa da shi a zaune. Can sai ga Malukussaifi da sa'adunizanji sun shigo, da zuwansu sai Sarki da sauran jama'a duk suka mike kamar yadda suke yiwa Sa'aduninzanji bayan da su kai gaisuwa gaban Sarki sai duk aka zauna, zaman su ke da wuya Malukussaifi ya dauko littafin Halwanu ya mikawa Sarki ya ce, "Ga littafin da ake bukata daga gare ni na kawwo.' Sarki ya karba ya mikawa boka ya karôa ya ajiye. Aka cigaba da harkokin mulki har lokacin tashi daga fada ya yi duk jama'a suka watse boka Sakaradiyyuna ya dauki littafi ya koma masaukinsa yana tunanin to yanzu kuma wane makircin zai sake kullawa Maluussaifi Bayan da dare ya yi sai boka ya sa aka kirawo masa wasu mutane daga cikin irin ragowar mutanen da Sarki Saifu'ar'adu ya aiko su tare da Manadihulbigali, su ashirin da biyar ne cikinsu dubu suka rage Sa'adunizzanji bai halaka su ba, da zuwan mutanen gaban boka Sakaradiyyuna suka fadi suka gai da shi, sannan suka zauna. Boka ya ce da su ya kirawo su ne domin ya ba su takarda su kai wa babban Sarki Saifu'ar'adu. Nan da nan ya dauko takarda da alkalami ya fara rubuta takarda ya ce, Bisimil.zahlu, zuwa ga babban Sarki Saifa'ar'adu, na rubuto wannan takarda domin na sanar dakai cewa sadaukin nan daka aiko ya nema maka auren yar sarki Afarahu fa, to sarki afarahu dai ya kulla makirici sun hadu shi da sa'aduninzanji da wannan farin yaro daya ajjiye sun kashe manadihul bigali, dan aiken nan naka. zamu cigaba MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN Littafi na biyu 2 Fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi rubutawa Shuraihu Usman Part 3. kuma idan ma ka sake to wannan farin yaron zai auri Shamatu, wanda ko idan har hakan ta faru-to ba makawa sai ya ture mulkinka, domin kuwa ya samo wannan littafi ma da na tura shi ya nemo. Abin da nake so yanzu ka turo sadaukai masu yawan gaske su zo su yaki Sarki Afarahu da Sa'adunizzanji, da Wannan dan yaro sannan ka mai da Shamatu kuyangarka. Da ya gama rubuta wannan takarda, sai ya ninke ya mikawa mutanen

Chapter 1 of 5