Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Leemah? toh Kai yaya Nazir Nace Ni baxanzo ba kuma kake tambayar Wata Leemah. Am..ehhhh....dama kawai na tambaya ne Nazir ya fada Cikin inda inda, Feenah Cikin Ranta tace "wai su Soyayar tasu kuma da haka tazo, Arasa wanda Za'ayima boye boye Saini" kwafa tayi Afili tace, toh yaya Nazir Naga dai Xuwan baida wani Amfani Shiyasa. Yanada Amfani mana Sisto, kawai kudanxo muganku ma muji dadi Ai yanada Kyau, Murmushi feenah tayi tace "Aa" yaya kawai...katseta yayi yace idan kin Xauna mai Zakiyi Achan kudaizo yafi daga Haka ya kashe wayar....gira feenah ta daga Sama ta tabe baki tace Ikon Allah. Kausar tace Shi yaya Nazir kullum Saiyace ina Leemah Nikuma baya tambaya ina nike kodai....da Sauri Leemah ta katseta toh aikema yusuf Ke kadai yake waya dake.eh aini Soyayya Nake dashi kuma Yana tambayarku....feenah tace Ummm Soyayya Ruwan Xuma wasu na bayya tasu wasu Kuma na Sirrintata Lallai Soyayya Ansha wuya! Cikin Rashin kuxari Leemah tace besty Suwaye? A film ne Feenah ta bata Amsa. tashi Kausar tayi tace ni bari naje Na kwaso Sauran kayana domin gobe gaba daya nakeson na Mayar dasu, kai Kausar Kodai khady tanimi Sulhu kun Shirya Xa'aje Ayi Abinda Aka Saba..tsaki Kausar taja tace kincika maida Abu baya,,,Um um Kausar kidai fadi gsky dama daxun naga kina dan ciccije lips Feenah ta fada tana kallon Kausar:::Afusace kausar ta fita tace kanku Akeji. Tana fita Leemah ta mike tace bari naduba Abu....Wajen kayanta ta nufa tana kokarin Neman takardar dan dama duk lokaci xuwa lokaci Saita duba Letter din da Nazir yayi mata! Karo taci da takardar da Sauri taciro ta juya baya.....kallonta kawai Feenah keyi tana Murmushi. budewa tayi ta ware Ido ganin paper din tazama biyu, ta farkon tafara budewa tana ganin rubutun tagane Rubutun feenah ne! Gabantane ya fadi Cikin Ranta tace" Shikenan ta gani" karantawa tayi ta juya tana kallon Feenah wacce ta daure face Kamar batama San da Mutum a dakin ba. Tashi tayi takarasa kusa da ita, my Feenah am Sorry Namiki Laifi..katseta feenah tayi mekikaimun? Ehm...dama naga...toh Dan kinga Shine yaxama kinmun laifi, kece kikaima Kanki lefi tunda har kika iya barin Abu Na damunki Cikin Xuciya, koma menene dalilinki na boyemun I don't know! Kuka Leemah ta fashe dashi ta Rungume feenah, namiki Laifi besty wannan Shine Abu nafarko da nataba boye miki, kuma Shima inada dalilin yin Hakan. Haba Leemah Wani irin daliline Xai hana Ki fadamun Abu mai muhimanci irin wannan? feenah Idan Baki mance irin Rashin kunyar damuka Sha yiba,Zakiyi fargabar Ranar da Yaya Nazeer Zeji labari, kada Kiyi tunanin Abun ya tsaya Acikin gida ne kadai, Kinsan fa duk Abinda mutun ke aikatawa na boye dole wataran Sai Abin ya fita waje, kokin mance hausawa nacewa ba'a Cewa gaskiyar Mutum ta kare saidai Ace karyar Mutum ta kare.feenah bangare guda ga tsananin Kunya danakeji gaba daya Sirrin Jikin junanmu muriga da mun Sani Sannan Nazo na aure yaya Nazir da wani idon Xan kalleshi. (Hi Leemah help me Ask her😊 ni Kaina kun dade kuna bani kunyaπŸ™ˆπŸ™Š) Ajiyar Zuciya feenah tayi yayin da hawaye ke Sauka kan face dinta, Lallai yau nakara nadamar Abinda na Aikata Abaya! Leemat ai bake bace dajin kunyata nice ya kamata Naji taki, Amma Kuma Leemah yazamuyi da kaddara tunda tariga fata? Kawai inaganin kucigaba da Soyayarku har Allah ya nuna mana aurenku, Sabida ai Allah yariga yasani munyi laifi Abaya kuma Yanzu munyi nadama Mun tuba, Allahu gafururrahim ne kuma Shi ke rufama bawa Asiri Aduk Halin da yatsinci Kanshi, Leemah tun farko ba'a gane kedin kinayi ba, bekamata kixauna kina daga hankali ba tunda kedin kin tabbatar Yanzu kowani kikaga yana aikata irin laifunmu Zaki mishi Nasiha, duk kicire wannan Aranki maganar jin Kunya babu tunda wannan sirri ne tsakaninmu Kawai. Hakane Leemat ta fada Allah ya tabbatar mana da alkairi Ya kara Rufa mana Asiri duniya da lahira. Amn Feenah ta fada Suka Rungume Juna Cikin farin Ciki.

WASHE GARI
yau ta kama Ranar Hutu gaba daya daluban Cikin Shiri Suke na tafiya gida....ba'abar Su Feenah Abaya ba dankuwa driver Suke jira ya karaso,Yayin da Kausar ita nata har yazo ta tafi, besty Saiki Sauka Agidanmu ko? No Feenah gida Zaku Ajeni...Oh Na mance yanxufa ni Sirika ce, duka Leemah takaima Feenah Suna dariya daidai Sanda driver yayi parking gabansu, karasawa sukai gaba dayansu baya Suka Shige Haruna yajasu Suka bar Wajen. Nazir ne yashiga Cikin gidan yana Kiran "mum" Amsawa tayi tace gani a kitchen fa, karasawa Nazir Yayi yasameta tagama girke girke kwashewa take tana kaiwa Kan dinning table...mum duk Wannan Abinci Haka da yawa bayan Feenah ita kadaice, waye ya fada Maka ita kadaice, dad dinku yau Zai dawo, Sosa kai yayi yace ai namance ne, Ai dole kamance! Sai Wani rawar kafa kake Kamar Yau Zaka fara ganin Feenah din. bahaka bane mum Kinsan nadade banganta ba, Uhum Kaji dashi mum ta fada,Oya tayani Shirya Abincin Nan. Zaune Suke Yusuf Na fadin wlh Yazeed jina Nake Kamar naje Zaria Ayau! dan Allah katashi katafi mana, duk Ka Wani ishe Mutane kan yarinya karama. bakasan menene Soyayya ba namaka Uxuri kaikam yazeed. Eh Naji angaya Maka Koda naci Xan Auri Karamar yarinya da Soyayya ne? Kawai dan ina tausaya ma kaina nane. Hakane fa yusuf yafada Yana dariya, ina tausaya Maka Ranar da Xaka Zama wawa awajen yarinya karama. Allah ya kayuta Yazeed ya fada da karfi......inno ce tafito tana tsaka Lfy Ko Halimatu ta karaso ne?? Kallonta Yayi ya wurga mata Harara, bansan kanayi ba Sainaga idonka Akasa, badai Yau Amadi na hanya ba wlh Zaka maimaita duk Abin da kake mun, tsaki yazeed yaja yace Saime toh inno?? Sai Ubanka ya maidani, tsaka yau ina Cikin farin Ciki ka batamun Rai Allah Saiya Sakamun. Yusuf dake ta faman dariya yace inno nima Wlh yau farin Ciki Nake Sosai...da Sauri Inno tace Ai shi yazeedu ko Ranar idi ce tazo A bakin Rai yake Aini Alhmdullah Zuwa gobe Narabu da kunnama mai Zafin harbi. Tashi yazeed yayi yace idan kagama biye Mata Kasameni. Wayyo Sunanka Suri yau tsaka, dariya Sosai Yusuf yayi yace Inno tamu. Uhum yusufa yushe Zakayi Aure? Inno Sai yarinyar tagama Karatu. dafatan dai ba katuwa bace irin kafurar yarinyar nan? Inno Wannan yarinyace kawar Halimatu ce kunama gaisawa da ita, Laaaa Kafso kake so dama? yarinya Mai hankali....dariya Yusuf yayi yace inno ba kafso ba kausar take....Oho Aini ban Iya Sunan yan boko din nan ba. toh inno bari na tafi, duk Abinda Yazeed ke Miki ki fada ma Abba dan yace mun wai Aure yakeso Shiyasa yake Miki haka! Bude baki inno tayi tana Salati yusufa Ashe Shiyasa Ranar da yakawo Kafura Naganta tafito daga wajenshi tana Sanda????? mamaki Yusuf yayi Cikin Ranshi yace Chafff Inno ta ganshi, Afili Cewa yayi Inno Ai aure yakeso Sosai, Kinsan feenah Kawar Halimatu kuwa? Kai dan Nan nikuwa nasanta itama tana Miskilanci irin na tsaka.yawwa Inno kawo kunnanki kiji! Mika kunne tayi Yusuf ya fada mata mgn. Tashi Naga tayi tana Rawa Tana haka Za'ayi yusufa... Karfe 5 daidai na yamma driver ya Sauke Su Feenah A mamakenken gidansu Wanda Leemah baccinta take batasan Anzoba, daka mata duka feenah tayi tace tashi Sarkin bacci! Adan tsorace ta tashi, haba Feenah bayan Nace Agida Xan Sauka kikasa y kawo ni nan. Ai naga Nan din ba daji bane. Nidai kirashi ya kaini, Sakko da kanki. Atare Suka sakko Leemah na Kiran Haruna....daidai Kuma Sanda mortar Nazeer tayi parking A harabar gidan, tare Suka fito da dad Suka nufo Wajen Su feenah. da Sauri feenat ta karasa ta Rungume dad, dady ur wlcm. Tnx Ummina. Karasowa Leemah tayi itama tana mishi Sannu, Amsawa yayi Cikin Sakin fuska,,,,Nazir Kuwa gaba daya idonshi nakan Leemah, dad ne yace mukarasa Ciki, Wai tafiya zatai dad feenah ta fada tana kallon Leemah, Aa halimatu muje kici Abinci kihuta sai Nazir ya kaiki Anjuma, toh Leemah tace tabi bayansu jiki A Sanyaye, Shiko Nazir murmushi kawaii yake najin dadi.

πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–
YAR LESBIAN CE
πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–
By
Nadeeya mohd Ahmad
(πŸ’–NadseerπŸ’‹)

dedicated to
Xaynab Ummu mahbub

*This would page is for All Online Hausa writers SistersπŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•Allah ya karo fasahaπŸ‘ love you All*

*Safiyya Abdullah Musa Huguma*

*Khaleesat Haydar*

*Jidda ja'o*

*Hafsat Rano*

*Zahra Muhd Mahmud* (Surbajo)

*Hudallah marubuciyar* (Zainab)

*Aysha Ali garkuwa*

*Miss-XoXo*

*Sadnaf*

*Mrs JH*

*Maman-Shakur*

And OthersπŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•

page....28

gaba dayansu Sun Hallara Kan dining table din Suna Shirin Cin Abinci. daddy ne yace Hafsat ina yaran Nan ne? Inaga ko basu gama huta gajiya bane mum ta fada tana kokarin Serving din Nazir dake wajen... ya kamata Akirasu ko? daddy ya fada yana kallon mum. Kallonshi tayi tace da Nabari ne Saci nasu daga baya. Nazeer ne yace Ai gara kawai Aci gaba daya mum! Banza tayi dashi, ganin Haka yasa dad yace ma Mubeena ta tashi ta kirasu, tashi tayi ta tafi da gudu Zuwa Sama. ba'afi Minti5 tsakaniba Suka Sakko Atare....daddy Yana ganinsu yace duk gajiya dince Haka yarana, Murmushi Leemah tayi ta Sunkuyar da kai qasa, yayinda Feenah tace dad Akwai gajiya Wlh. Ai kun kusa gaba daya daurewa Zakuyi dad yafada. tashi feenah tayi tafara Zuba Nasu Abincin, Sunaci Suna fira banda Leemah da duk take jinta A Takure musamma data dago taga Nazir take fuskanta, Haka dai kawai ta daure tana ci gashi duk Sanda Zata dago Saisun hada ido Atare Kuma Suke Sakar ma juna Murmushi... mum ce ta dago tace Nazir Anjuma Zan Aikeka gidan "Umma" ka kaimata Sako. Shirun data jine yasa ta kalleshi, gaba daya Hankalinshi baya jikinshi magana Suke da Leemah da ido ga wani kallo dasuka tsare junansu dashi! Mumy ce ta Saki Spoon din hanunta ta dan bigi Kafadar dad tana nuna mishi Su Leemah, daga gira dad Yayi Sama yana murmushi lokaci daya Kuma yayi gyran murya Ehmmm...gaba daya Suka juyo Suka kalleshi ganin Su Ake kallo yasa Leemah taji Kamar ta nitse Awajen, durkusar da kai tayi Kasa. Nazir kuwa Inda inda yafara yace Mum maga kikai? dad ne yai Saurin cewa ba magana tayiba nine nakusa kwarewa, Hafsat tashi muje kiban Ruwa, tashi mum tayi Sukabar wajen ita da dad. feenah kuwa da dama tunda Suka Zauna ta lura da yanda Suketa mgn da ido da HanciπŸ˜„itama tashi tayi tace Alhmdllh nakoshi....tashi Leemah tayi da Sauri besty jirani Nima na koshi, da Sauri Nazir yace baki koshi ba Common Xauna ki karasa,marairace Fuska tayi kamar Xatai kuka Allah yaya Nazir na...Kafin ta karasa yace Naji kin koshi Xauna muyi mgn, Xama tayi. Yace feenah dawo kema tare Zamuyi mgnr, dawowa tayi ta Xauna Nazir ya kalli Twins yace kuje Baba ladi ta Shiryaku Xankaiku gidan Su mai Kyau! Ai da Sauri Suka tashi Sukai Cikin gida. Juyowa yayi yana kallon feenah Sisto Nariga Nasan Kinsan ina matukar Son besty dinki ko? Umm ni bansaniba feenah ta fada tana yatsina face...Kara juyowa yayi yana kallonta Haba my Sis Nasan kinsan komai kuma bakya karya kigaya mun gsky. Eh Nasani Yaya Nazeer kawai Haushin boyemun dakayi Nake ta karashe mgnr harda Dan Hawayenta....haba Sis Menene Abun kuka kuma, Nifa daman Nabari ne kidawo Nagaya miki kamar Surprise Haka, kinsan bana boye miki Abu itama Leemah ban so tasaniba Nakasa daure ma Zuciya tane yasa Nagaya mata. Turo baki tayi tace Naji Amma dafatan Son tsakani da Allah kake mata? dariya tabashi yace irin Son danake miki Shi nake mata, Aa yaya Nazir nafison Nata yafi Nawa...Shiru yayi yace toh kitayani addu'a tasoni fiye da komai, toh yaya Nazir Zanyi. Leemah ce tace karfa mum tafito! bayan Sun gane komai feenah ta fada tana dariya..Atare Suka Zaro ido fada musu kikai Leemah ta tambayeta? No kune kuka tona kanku kallon juna Kamar wani Xai dauke dayanku din nan. Nazir yace Ai Hakan ma yayi kinga Sai Amana Aure da wuri! Leemah ce ta marairaice fuska Aa nifa Sai feenah tasamu miji Zamuyi Aure Rana daya...dariya Nazir yayi yace wato Ku Haryanzu yara ne, banda Abunku Ai gara daya taga auren daya Sabida idan Rana dayane daya bazatakai daya gidan Aurenta ba. Waye ya fada maka yaya Nazir? Aikoda Rana daya mukai Aure Sai Nakai Leemah gidanta kafin na wuce Nawa. Nazir ne yace kinmanta Kabeer Xaki Aura kuma yola Za'a kaiki,ba Lallai Na yarda baby taje yola Aranar Aurenmu ba...da Sauri feenah ta tashi tana cewa Ai bazaka Rabamu ba dan yanxu kasamu mun Amsheka, daga Haka tabarsu Zaune A wajen. Juyawa yayi yana kallon Leemah baby kawarki Akwai Rigima, Uhum bata Rigima Kaidinne Kake Sakata Rigima, Umm Na lura bakwason Laifin junanku Toh ya Soyayya ta yanzu Aranki??? Shiru tadanyi daga bisani tace tasamu waje babba Acikin Zuciyata, kallonta Nazir yayi kamar ba ita tayi mgnr ba ta wani fuske, Cikin Xuciyarshi yace Lallai Leemah irin macen danake muradin Aure ce, Afili cewa yayi Alhmdllh my baby Yanzu kinga kamin Ki koma Skul Sai Asaka mana Rana...Xaro ido tayi tace da wuri Haka? Eh mana bakiji Hausawa nacewa Abari ya wuce Shi ke kawo Rabon wani ba? Hakane but yaya Naz..but what? Nazir ya katseta da Sauri. Kabari lokacin daxa'a Saka Ranan feenah da kabeer Sai Asaka tare da namu. Kin kawo Shawara mai kyau baby Shiyasa nake kara Sonki,duk da kin barni Cikin tunaniki, kullum dake nake Kwana kuma dake nake tashi. Nima Haka yaya Nazir. Kin tabbata? Kallonshi tayi Suka hada ido ta kashe mai Ido daya tace Ummm, Ajiyar Zuciya Nazeer yayi Dan wani irin farin ciki yakeji wanda baya misaltuwa. "I love you So much my baby" Nazir ya fada yana Mata Murmushi. "love you more my baby" Leemah ta bashi Amsa kasa kasa. Xancire miki kunyar Nan Soon duk da Naga Alamar nama fara kokari Wajen cireta....dariya Leemah tayi ta tashi tace kada Su mum Su Sakko, tashi Shima yayi ya rakata Har kofar Room din Feenah yace kishirya Anjuma Nakaiki gida. Ok tace tashige Ciki.

Inno ce tsaye Kan yazeed Tana fadin Haba tsaka ka kiramun ita Naji ko tana inane. Inno nace miki wayata Bazata iya Zama A kunanki ba dan Allah kitafi ki bani waje yazeed ya fada yana nuna mata Hanyar Sama.... tsaka! tsaka! tsaka! Sau nawa nakira ka? Oho yazeed yace ke kikasan tsaka. Kwafa Inno tayi tace yaro yarone ina tausaya maka Ranar da Zaka Shigo hannuna, Xakayi nadamar yimun wannan Abun Dan Ubanka,yanzu namaka Uzuri dan nagane dalilin dayasa kakemun wannan Abun...Amma muje Zuwa ni inno jikar Saluhu da balaraba Nakusa Na dana maka tarkon da bazaka iya tsallakeshiba. Kallonta yazeed yayi yace iyaka kice idan Abba ya dawo Xaki fada mishi, Toh Sai me? Haka kace ko? Eh Haka nace mtsww kizo kitafi koma ma huta. Fatima kayimawa tsaki bani ba...muxuba ni dakai. Tashi yayi yana toshe kunanshi...daidai nan Abba yayi Sallama Cikin parlon. Suman tsaye Yazeed yayi dan yasan yau Inno Sharri Xataimishi ba kadan ba. da karfi Inno tace Ayirirerere yau Ga dana Ya dawo huta Roro. ...da fara'a Abba ya karaso kusa da ita ya gaidata amsawa tayi Cikin walwala da Sakin fuska, Abba ya kalli yazeed my Son lfy kuwa? Sannu da dawowa Abba! Yawwa Son duk kuna lfy ko? Alhmdllh Abba. Ya katsaya Haka kamar wani police? da Sauri Inno tace Nakirashi ne ya kiramun Halimatu A waya Shine yake kokarin kiranta Saikuma ka Shigo. da mamaki yazeed yake kallonta Suka hada Ido ta watsa mishi Harara, Shi kuwa cikin Ranshi yace Tabbas wannan tsohuwar Akwai Abinda ta Shirya Mun. Abba ne ya katseshi toh kakirata mana, toh Abba. Kiran Leemah yayi ta dauka ya mika ma Inno! Allo Halimatu. daga bangaren Leemah tace Na'am Inno ta. Kina inane munata jiranki Shiru Har Abbanku ya dawo. Inno Naje gidan Uncle Umar ne, yanxu gani Ahanya tare da feenah da Twins. Har Naji dadi Halimatu chanake kokin fasa Xuwa ne. Aa Inno Gani nan,me kika dafa mana? Saidai kinxo Yar nan.Toh Inno gani nan. Anshi tsaka kashe ban iyaba....Amsa yayi da Sauri yabar parlon danshi tsoro yake kada tamai Sharri wajen Abba. Mamy ce ta Sakko daga Sama Cikin Adonta, barka da dawowa Abban Leemah,yawwa barka Maman Leemah.tashi inno tayi tace bari nabarku Ku gaisa, Kuma Amadi gobe Xaka maidani inda ka daukoni, bata jira amsarshiba ta bar wajen. Yazeed na fita yaci karo da Yusuf dake Shigowa Yanzu...Aa Dr Ashe kana ciki? Ina ciki Yusuf Zomu karasa Akwai matsala fa. Karasawa bangaren yazeed Sukayi, Yusuf yace Matsalar Menene Aboki? Yusuf mamaki nake Abba ya dawo inno batace mishi komai ba, kasan Halin Inno da Rashin hakuri gani Nake Anya ba Wani Abun ta Shirya ba? Gyara Zama Yusuf Yayi yace banajin Akwai Abunda ta Shirya, Inaga kawai dan tasan Za'a Maka fada Shine tadan kauda Zancen. Shiru yazeed yayi daga bisani ya girgixa kai, Anya Kuwa yusuf? nasan Halin Inno Sarai wlh Amma mubar mgnr ni bawani tsoroma nakeji ba taje tayita fada. dariya Yusuf yayi wanda shi kadai yasan Ma'anarta yace Aikuwa Abar mgnr kawai. yawwa yazeed haryau baka samo Wacce kakesoba? bansamo ba Yusuf ni banga wacce tamunba! Kallonshi Yusuf yayi yace duk Matan dake fadin garin kaduna babu wacce tamaka? Eh Yazeed yace Atakaice danshi gabanshi ma dan faduwa yake.. Ok Yusuf ya fada Amma Kana nan kan idan kasamu yarinyar data kalle Cikin idonka tayi magana Xaka Aureta ko? daga Kafada yazeed yayi yace yes.

Atare Suka Sakko daga motar gaba daya Suka Shiga gidan. Da gudu Twins Suka karasa Ciki Suna kiran mai Kyau! Suma Shiga Su leemah Sukai ba kowa a parlon dan Haka Sukai Xamansu Anan. Nazir yace bari Naje Wajen Yazeed da Sauri Twins Sukace Suma Zasuje, fita Sukai Atare Sukai part din yazeed. Feenah tace ina mamy da Inno Suke ne? Leemah tace kya tambayeni nida mukazo tare, Kinsan Abba yadawo maybe mamy Taje mishi wlcm Sunyi missing juna kinsan, itakuma inno Inaga Wani Abun takeyi duka feenah takaima Leemah ke bakida Kunya ko? Toh Menene Ai gsky na fada, yawwa Feenah dazun baby kecemun Wai Asakamana Rana kamin nakoma Nace Nooo Saikin tashi Naki Auren. Toh waye kuma baby!? dan Rufe ido leemah tayi tace yaya Nazir mana. Tabe baki Feenat tayi tace Umm. Saiki bashi phone number dinki Kada mukoma Skul kina tunani. dariya Leemah tayi tace baki lura ba Amota ya amsa? Ina Xanlura fa kunshige gaban mota kuna Xancen love, Amma harda kukan munafurci ni feenah ina tsoro waye waye mtsww magulmata daga Ke har Shi. Inno ce ta Sakko daga Sama tana A'uzubillah wake tsaki irin na tsaka? Tashi Leemah tayi takarasa gunta tana dariya. Inno ta ya gida? Lfy Halimatu ta Shine kika fara Xuwa gidan Su Naziru baki Xomunba. Sorry Inno ba gashi yanzu Munzo tare da feenah ba. Kallon feenah Inno tayi tace Nafisatu yan makaranta... ina yini Inno? Lfy Nafisatu ya karatu? Yasu Hafsat?ya garin kuma? Ya Ummaru? Kallonta feenah tayi ta kauda kai don idan Akwai Abinda tafi tsana Shine yawan tambayoyi irin ya kaza ya kaza. daga gira Inno tayi Sama Ahhh Wlh kwarai Halinku daya da tsaka....kallonta feenah tayi tace waike kowa Saikin bata mishi Suna ne? bude baki inno tayi tace Laaa aisaiki fadamun bakyason Ina tsokanar yazeedu bawai ki rinka mun Kwana kwana ba. tsaki feenah tadanja Kadan. Inno tabe baki tayi tace Ummm gaskiyar Yusufa. Kallonta leemah tayi tace inno mai yusuf din yace miki? Zomuje daga Chan na fada miki Inno taja Hannun Leemah Suka bar Wajen. Kinsan me Yusuf ya fada mun kuwa? Aa inno fadamun! Kasa kasa tayi da murya, yace mun yazeedu da Nafeesatu Sun dade Suna Son junansu, Amma Sabida gaba dayansu Sarakan miskilanci ne yasa Suka Ki tsayawa Su Sanar da junansu, Amma yazeedu ya fada ma Yusuf yana Son Nafeesatu, kuma yazeedu Aure yakeso Sosai Sabida RANAR dana kori Kafurar yarinyar nan naje amsar kudi gunshi ya rufe kofa da Sauri ya Hanani Shiga, daga baya da idona Naga yarinyar ta fito daga bangarenshi tana Sanda, Toh ke Halimatu Kawar taki bata taba gaya miki tanason yazeedu ba? Leemah datunda Inno tafara maganar ta daskare Awajen tace, inno bata gayamun ba, Kuma inaga yusuf Wasa yake miki Feenah bazata boyemun komaiba,inno ke bakiga basa Shiriba ma da bro? Ke da alla Sakarya Yusuf yace irin tasu Soyayyar Kenan kedai Kada kifada Mata kibari muga gudun Ruwansu. Ajiyar Zuciya Leemah tayi tace Toh Inno.Amma kasan Xuciyarta Sam bata gasgata maganar ba. fitowa Sukai parlon Leemah jikinta duk yayi Sanyi So take Abunda Inno tafada yazama Gaskiya da tafi Kowa farin Cikin hakan kuwa. Su mubeen ne Suka Shigo tare da Nazir Wajen inno Suka nufa Suna dariya. Yusuf Naga ya Aje Wata mage kofar yazeed ya nufo Cikin gidan Shima. Kiran feenah Akai Awaya tace laaaa Leemah Kausar ce, bari Naje Waje na'amsa karfa kibiyoni. Toh Leemah tace Hakan ba Karamin dadi yama yusuf ba. Tana fita yace inno inaga wajen yazeed Zataje bakiji tana kada Leemah ta betaba. Ai ita Sakaryar Halimatu din nan bata yardaba inno tafada. Kallon leemah yusuf yayi yace barta inno yanxu zata yarda ai. Fitan Feenah yayi daidai da lokacin da Yazeed ya fito daga daki da Sanda A Hannu,dama ganin magen da yayi yasa yakoma ya dauko Sada dan yakoreta dan idan tana wajen bazai iya wucewaba tsoronta yake. Sandar yasaka yana dan ture magen itakuwa taki tashi. Feenah ce ta hango Abunda yake tace Kausar dan kashe kadan, bro din Feenah Kema mage mugunta Bari naje namishi ta tassss.

*Gud nyt loversπŸ’•πŸ’• Ina typing Ina gyangyadi duk because inasonku kamar yanda kuke Sona yasa na daure nai muku wannan*


πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–
YAR LESBIAN CE
πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–

By
Nadeeya mohd Ahmad
(πŸ’–NadseerπŸ’‹)

dedicated to
Xaynab Ummu mahbub

Page....29/30

Karasawa tayi Cikin tafiyarta wacce kamar bata Son taka kasa. daidai gaban yazeed taja ta tsaya Kai Malan! dagowa yazeed yayi daga durkusan da yake ya Zuba ma kaykyawar fuskar feenah ido take gabanshi ya fadi Rasss. Itama feenah Ido ta Saka Cikin Nashi yayin da itama gabanta ke faduwa wani irin kwarjini taga yamata,jitake kamar

3 Comments On YAR LESBIAN CE Book 2
avatar
umar-6-7

1 year ago

Reply

Nice book

avatar
abubakar-ibrahim-7

9 months ago

Reply

Yes

avatar
mahmud-shareef

30 days ago

Reply

Yeah

Please Login or Register in order to submit comment