so bana yaudara ba
Kallon shi kawai takeyi yanda yake maganar
Amma idan anyi Miki miji kiyi hakuri
Abu na biyu shine number wayar ki pls nake so da sunan unguwar k
Abu na farko shine Ni bani da waya
Na biyu idan kana son sanin gidan mu kaje unguwar winti gidan Mallam Ibrahim
Wucewa tayi ba tare da ta sake wani magana ba
Komawa yayi cikin gidan
Kowa ya halara a cikin parlon
Ana so aji me sarki ke son fada
Assalamualaikum
Da farko abinda ya hada mu anan ba wani abu bane face fada muku cewa Insha Allah Auren Azeel da Mariya wani wata me zuwa
Aseel nan da sati Daya idan baka fito da mata ba zan hada ka da koma wacece
Idan da akwai me magana ya fada
Daddy ni akwai wace nake so yar gidan Mallam Ibrahim suna unguwar winti
Masha Allah
Azeel kana da abin fada
Daddy auren dole kuke so kumin ne ko yaya saboda wani aminin ka yace yana so amininta karku yayi karfi me yasa baka hada sa da Aseel
Na riga da na gama magana tunda tana son ka shikenan bana son wani magana kuma daga gare ka
Comment and share
🤴 GIDAN SÁRAUTA 🤴
(The house kingdom)
🌹Autar Ammi 🌹
(Sakeenah)
Daga alkalamin ✍️✍️Queen of essential writers
To Alhamdulilah Àllah ya kawo mu ina rokon Allah ya sa in fara lafiya yasa in
gama lafiya
Marubuciyar
**Holbereh**
**Aljanah Ce**
Yanzu kuma
**Gidan Sarauta**
Wannan iƙirarin labari ne
Free Page 9️⃣➡️1️⃣0️⃣
PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
💫P.E.W.A💫
Home of Perfect Writer's together we stand🤝
ESSENTIAL WRITER'S 📚🖊️*
Gidan sarki Rilwanu Suleiman
Kowa barin parlon yayi amma Banda Azeel da Mariya
Kallon shi tayi kafin ta bude baki tace
Kayi hakuri yaya Azeel na san ba dadi a matsayin ka na wanda ya mallaki hankali kansa ace za'ayi mishi auren dole amma ina me baka hakuri nasan baka so na amma zan yi kokarin ganin nayi Wa Abba na magana
Shiru yayi yana kallon ta shi yasan mariya tana da hankali da nustuwa amma shi baya son ta kuma idan yace ba zai aure taba rashin kunya yayi kenan duk a zuciya yake zancen
Ita duk ta aza ma bazeyi mata magana ba tashi tayi tare da barin parlon
Nima ina son ki mariya kar kiyi rashin biyayya ga iyayen ki
Juyowa tayi don tabbatar da cewa shi yayi maganar
Daga mata kai yayi alamun cewa shi yayi maganar
Da gudu ta zo ta rungume shi kuka ne ko farin ciki bata sani ba
Bangaren Aseel kuwa
Daki ya shiga tare da murnar yardar daddy wanka ya shiga tare shirya wa cikin manyan kaya
_*Unguwar winti*_
Safiya ta zayyana wa mama yanda suka yi da Aseel
Yanzu kinga abinda Allah keyi ba
Ba'a fadan magana a take saboda bake kika tsarawa kanki abubuwa ina so ki nustu safiya har tunda kin sami wanda yace yana son ki kuma da aure Allah zaba ma abinda ya fi alheri a gare mu
Ameen mama na gode kuma na miki alkawari cewa zan nustu indena rashin kunya Insha Allah
Allah Miki Albarka
Ameen tace
Yanzu kina son shi ne ko yaya
Tashi tayi ta bar gujin ba tare da tayi magana ba
Allah ina godiya kasake shiryar min da ita ya hayyu ya qauyum
Daki ta shiga Allah yasani tana son shi amma tunanin ta daya Allah yasa ba yaudarar ta zeyi ba
Aseel ne acikin mota kiran wani yaro yayi yace don Allah ina ne gidan Mallam Ibrahim
Wanne
Baban Safiya
Safiya mastifafiya
Murmushi yayi
Ehhh ita
Nuna mishi gidan yayi godiya yayi tare da ba shi 1k
Yaro kuwa se godiya yake
Kofar gidan yaje wani almajiri ya gani yace ana sallama da safiya
Yana zuwa ya sami safiya da mama na aiki
''Wai ance ana sallama da safiya''
Kallon yaron tayi kafin tace waye ?
Dan gidan Sarki ne
Kirjin ta ne yaba da wani dummm
Kallon mama tayi
Ce mishi tana zuwa
Ki je ki sa hijabi ki same shi amma ki ce mishi idan ze zo yazo ta gujin baban ki
Insha Allah
Farin hijabi ta sa kuma yayi mata kyau ko kwaliya batayi ba
Samun shi tayi jingine da farar motar sa
Kallon ta yake yana murmushi safiya mastifafiya
Dago kanta tayi tana kallon sa
Ko ba sunan ki bane gimbiya ta
Ina wuni
Lafiya qalau ya kike ya mama da baba
Duk lafiyar su qalau
Hira sukayi amma rabin abin shi ke fada
Insha Allah zanyi wa Abba magana yazo a yi maganar auren mu ko
Murmushi tayi amma batayi magana ba
Wannan Kunyar taki zaki ma dena shi ne
Dariya tayi tare da ce mishi zo kasa in Dena ma na
Kina so na safiya
Kallon shi takeyi kafin ta daga mishi kai ta shiga gida da gudu
Shima murmushi yayi na samun nasara
Mama dake alwala taga ta shigo da gudu ke kuma lafiyar ki kuwa
_*Azeel*_
Azeel da Mariya ne a garden se soyayya suke sha
Ita kuma se zuba mishi shagwaba takeyi
Ni wallahi dear i na son zuwa akeleri shakatawa
Ki bari zuwa gobe se muje
To yau muje filin masoya
Hmm kina da rigima sweet love
Uhmm ni Banda wani rigima
Yanzu yaushe zaka fara aiki next week zan fara ke fa Nima next week a specialist hospital na bauchi
Ok that's good Nima chan zanyi aiki
Ihu ta kwala saboda murna
Dadi na dake kina abu kamar wata yarinya watarana
Wallahi dadi na ji
_*Aseel*_
Safiya da Aseel suma suna soyayya kullum se sunyi waya ta siya mata waya kirar Infinix pop 5
Me martaba yazo har gida anyi maganar auren su nan da wata uku me zuwa Insha Allah
Kwance yake yaji message ya shigo wayar sa
Sir Aseel Rilwanu Suleiman
Kana tunanin cewa zan Barka ne to zanyi ma abinda se mahaifin ka beze iya rayuwa ba
Naji cewa zakayi aure to ina sanar ma ka sede a lahira
Karanta message din yayi amma be gane waye bane
Kiran layin yayi amma a kashe be damu ba ya kira safiya suka sha soyayya
(Nace duk abinda kakeyi akwai me yi maka hasada a duniya Allah karaba mu da mikiyan mu lafiya)
Kuyi hakuri Banda lafiya
Ba update ranar sunday
Comment and share
🤴 GIDAN SÁRAUTA 🤴
(The house kingdom)
🌹Autar Ammi 🌹
(Sakeenah)
Daga alkalamin ✍️✍️Queen of essential writers
To Alhamdulilah Àllah ya kawo mu ina rokon Allah ya sa in fara lafiya yasa in
gama lafiya
Marubuciyar
**Holbereh**
**Aljanah Ce**
Yanzu kuma
**Gidan Sarauta**
Wannan iƙirarin labari ne
Free Page 1️⃣1️⃣ ➡️ 1️⃣2️⃣
PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
💫P.E.W.A💫
Home of Perfect Writer's together we stand🤝
ESSENTIAL WRITER'S 📚🖊️*
A yau ya rage sati biyu da auren Azeel da Mariya
Mommy da da aunty Hafsah siyan kayan akwati
Mariya ma ta koma gidansu Saboda be kamata ta zauna a chan ba
Assalamualaikum dear yakike
Waalaikalsallam MD
Ki shirya anjima zan zo na dauke ki
Ina zamuje kuma
Zanje siyar dake ne
Dariya tayi kafin tace ai ko ka siyar dani
nasan gujin arziki zaka bada Ni
Safiya ina son ki sosai kuma bana fatan rasa ki
Haka kawai taji zuciyarsu na bugawa a tare
Yaya Aseel don Allah kadena fadan haka ba abinda ze faru kana karya min zuciya Please ta fada hawaye na taruwa a cikin idon ta
Murmushi yayi tare da cewa na sani my dear wasa nake miki amma ki shirya ki fadawa mama kinji
Ok se kazo
Ka she wayar tayi amma duk jikin ta yayi sanyi bata san meyasa ba tanaji kamar zata rasa wani abu a tare da ita amma tana rokon Allah ya kawo mata me kyau
Safiya an nustu kamar ba ita ba kallon ta nayi yanda tayi kyau atamfa tasa da gyle green color fitowa ta yi
Mama nayi kyau kuwa
Ehhh mana safiya kamar wata mahaukaciya
Turo baki tayi mama na tafi
A'a ina jakar ki
Wani jaka kuma
Na kaya mana ai maman Aseel din takira ta roke baban ku cewa kije bayan bikin Azeel se kidawo
Yaushe a kayi haka
Je ki dauki kayan ki ki tafi
Tana kokarin yin magana ne kiran Aseel ya shigo
Daki ta shiga ko wani kaya hanun ta ya kai dauka takeyi
Sallama tayi wa mama
Samun shi tayi a cikin mota shiga tayi suka wuce inda take fada mishi abinda mama ta fada mata
Ehhh mommy ne tace tana so ki je
Amma meyasa baka fada min ba
Ehhh haka kawai
Hira sukayi har suka isa fadda
Suna zuwa parlon sarki Rilwanu Suleiman suka je inda aka tarbe ta da kyau kuma suka dan taba hira kadan duk da cewa tana jin kunyarsa matsayin sa na surkin ta
Nuna mata dakin ta yayi
Oyoyo aunty amarya yaya Aseel
Da murmushi tace oyoyo amaryar waye
Dariya tayi kafin tace mata amaryar Sadiq
Baki da kunya ko
Kunyar wa zanji yaya ai aure zakuyi Nima aure zanyi kaga kowa ze zamo baba nima zan zamo mama
Kokarin buga ta yake tayi sauri ta shiga dakin safiya
Dear se anjima ko idan mun hadu a dining table ko
Ok bye
Dakin ta shiga samun hajaju tayi a kan gadon
Wallahi aunty safiya a nan zan na kwana dake kar kimo gudan ku fa
Idan yaya Azeel ya dawo daga aiki zamu je dining table muci abinci ko
Haka kawai taji zuciyar ta ya buga saboda kiran sunan Azeel din da tayi
Azeel ya dawo daga aiki wanka yayi tare da saka jallabiya su je masallaci bayan sun dawo kowa ya hallara a dining table din Khadijah se zuba takeyi
Idan bakiyi shiru ba zan cire Miki bakin ki
Azeel ka bar min auta ta sake fa to
Kallon safiya yayi kafin ya dauki cokalin cin abinci sa kowa cin abinci yakeyi a niste amma safiya duk a takure take
Kallon Azeel yayi tare da cewa baza ki ci abinci bane
Dago kanta tayi suka hada ido saukar da kanta tayi tare da girgiza mishi kai
Dear ki ci mana ko kunya kike ji muce wa daddy ya tashi
Daddy kallon ta yayi kafin ya ce kunyar wa zata ji
In nine Ina da mata kyakkyawar gaske ta ma fiki kyau Azeel ma yana da Mariya
Dariya tasa har qishirwa ta da dimple dinta suna lostewa Azeel kallon ta yake
Wallahi yau duk banda Lafiya ina barar addu'a ku pls
Comment and share
🤴 GIDAN SÁRAUTA 🤴
(The house kingdom)
🌹Autar Ammi 🌹
(Sakeenah)
Daga alkalamin ✍️✍️Queen of essential writers
To Alhamdulilah Àllah ya kawo mu ina rokon Allah ya sa in fara lafiya yasa in
gama lafiya
Marubuciyar
**Holbereh**
**Aljanah Ce**
Yanzu kuma
**Gidan Sarauta**
Wannan iƙirarin labari ne
Free Page 1️⃣3️⃣🔹1️⃣4️⃣
PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
💫P.E.W.A💫
Home of Perfect Writer's together we stand🤝
ESSENTIAL WRITER'S 📚🖊️*
Kwance yake a kan gadon sa saki kawai yake tayi wannan wani irin abu ne in rasa marfalki wa zan yi se na budurwa Kanina
Tashi yayi tare da shafa sumar kansa se kuma yayi murmushi yarinyar tana da kyau ba lefi
Astagafurullah abinda ya ce kenan tare da waigawa ko akwai wanda ya ji sa
Wanka yayi ya shirya cikin kananun kaya wanda ya fito da asalin kyau sa
Kira ne ya shigo wayar sa heart beat ke yawo akan screen din
Dagawa yayi da murmushi
Mariya:Assalamualaikum sweet heart
Azeel:Waalaikalsallam my HB ya kike
Mariya:Lafiya qalau SH wai safiya ta zo ne
Azeel: ehh man ta zo se bayan bikin mu zata tafi
Mariya: a wani gari aka taba yin haka ko a naku al'adar shuwa Arab haka su ke yi? Ai wanan ba hali bane gaskiya
Ranshi duk ya gama ɓaci baki da hankali ne wato mommy da tace ta zo ita bata san me takeyi ba ko har da wani Maganar al'adar mu to ki ji kar saboda soyayyar da ya shiga tsakanin mu ki ce zaki fada min magana kin ji Ni ko biyayya nayi amma idan naga dama zan iya fasawa kashe wayar yayi batare da yaji me za tace ba
Rike wayar tayi tana me da ta sani saboda Maryam tace ai tunda yana son ta komai tace ze ji ta,
Aseel
Zaune yake waya a kunnen sa
Ok yanzu kana nufin gobe mu hadu a meduguri
Ta dayan bangaren
Ehh gashi saura kadan ka zamo ango ko ya fada ta sigar tsokana
Murmushi yayi tare da cewa Wallahi kuwa ban so haka ba
Hira sukayi bayan sun gama
''Ya tashi ya fara hada kayayyakin sa cikin traveling bag, bayan ya gama gyara komai dakin safiya'' ya wuce don sanar da ita
Part din su ya wuce nan ya same ta da hajaju se hira sukayi
Kwanciya yayi a kan gadon
Ke kam baza ki dena surutu bane wai kuma ki rasa wa zakiyi wa se matata
Turo bakin ta tayi
Wallahi Nima matar wani ne ai itama tana da surutu Ni kadai kawai ka sawa ido
Dariya duka suka sa yi hakuri mana Sweety na .
Murguda baki tayi kafin tace shikenan
Kallon safiya yayi tare da fada mata cewa zeyi tafiya Insha Allah gobe
Kuka hajaju ta fashe da shi wallahi baza ka je ko ina ba haba ni wallahi zuciya ta buga wa tayi da kace zakayi tafiya poppu luv kayi hakuri kace baza ka je ba kuka takeyi tsakanin ta da Allah
Safiya ma hawaye kawai takeyi
Tashi yayi ya bar musu dakin
Parlon sarki ya wuce
Bayan ya gaishe shi ne yake fada mishi cewa zeyi tafiya gobe
Shima de sarki be so tafiyar ba amma kuma ba kyau tunani idan mutum zeyi tafiya
Addu'a yayi mishi na fatan alheri
Daki ya wuce fadawa yayi a kan gadon tunani yakeyi game da tafiyar duk kansa ya kulle
Daukar waya yayi tare da kiran Azeel shima fatan alheri yayi masa suka yi hira
Washegari
Kowa ya fito ya shirya cikin kayan sojoji yayi kyau
Kallon sarki Rilwanu yayi tare da cewa daddy ina me ne man yafiyar ka idan na maka lefi
Kallon sa sarki yayi tare da cewa kai me biyayya ne kuma baka min lefin komai Allah ya baka abinda kake ne ma my son
Mayar da kallon sa yayi kan Azeel
Rungume Azeel yayi tare cewa idan nayi ma wani abu ka yafe min
Daure fuska Azeel yayi tare da cewa zan gaura maka mari idan ka sake fadan abu maka mance haka
Ɗariya yayi yace sorry bro
Kallon safiya yayi da duk fuskar ta ya gama jikewa da hawaye
I will miss
Kuka ta fashe da shi sosai
Mota ya shiga ak a ja su shi da daddy da Azeel
Alhamdulilah na gama free páge
Ina jiran ku yan amana
Sekinat Yahaya
GT Bank
**0879566752**
Domin turo da shaidar biya
**09048622108**
*Allah baku ikon biya*
Comment and share
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels