An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
🤴 GIDAN SÁRAUTA 🤴
(The house kingdom)
🌹Autar Ammi 🌹
(Sakeenah)
To Alhamdulilah Àllah ya kawo mu ina rokon Allah ya sa in fara lafiya yasa in
gama lafiya
**Piad Book ne**
*₦300*
Marubuciyar
**Holbereh**
**Aljanah Ce**
Yanzu kuma
**Gidan Sarauta**
Wannan iƙirarin labari ne
Free Page 1️⃣➡️2️⃣
Autar PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
💫P.E.W.A💫
Home of Perfect Writer's together we stand🤝
ESSENTIAL WRITER'S 📚🖊️*
-------------------------------------------------------
Bauchi State
Gari ne wanda ya haɗa masu kudi da talakawa wanda talaka sun fi yawa a garin Bauchi inda kuma suna da cima na kayan gona
Kofar fadar sarki Rilwanu Suleiman sarki ne idan kana bauchi zaka san shi me tausayi talakawa da taimakon al'umma
Sarki Rilwanu yana da mata daya tak da yara biyar maza biyu da mata uku
Azeel shine babban yayan su wanda ke karatu a kasar England yana karantar ''pharmacology'' inda yanzu saura mishi wata daya ya fito da kwalin kwararre likita me zaman kanshi
Se kuma Aseel na biyu kenan wanda ke military school dake Abuja inda shi kuma burin shi yazama soja kasa da kasa
Akwai Hadiza da mariya se autah Khadijah wace ake kira da hajaju
Mommy!! mommy kinga aunty hadiza ko bata son na dauki noor
Mommy dake zaune akan royal chair din ta Hadiza ki kiyaye Ni fa wani irin iskan ci ne zaki ce baza ta dau noor ba saboda ke ce mutum na farko da ta fara haihuwa ko ?
Mommy yanzu fisabidillah yaushe na zo amma har kin fara min fada saboda wanan abin ta fada tare da hararan hajo
Mommy kinga tana harara ta ko
Barta kishi take saboda ita ba Autar mommy da daddy bane shiyasa
__England__
Tafiya yake yi kamar me jin tausayin kasa kan shi a kasa farin rigar lab coat ne ajikin sa daga gani daga lab ya fito
Doctor Azeel!! Naji wata budurwa da bazata wuce 22 years a duniya ba ta kira shi yi yayi kamar beji me kiran sa ba sake kiran shi tayi
Dago kan sa yayi Ni kuwa nace Masha Allah dogo ne shi saurayi me jinin sarauta shi irin wankan tarwada ne ga shin kanshi a kwance luf eyelashes din sa kamar na mata daga gani ya hada jini da Fulani
Am sorry sir wata yarinya aka kawo kuma tana emargency room shine doctor mike yace se an kira ka tafada tare da wani kulle idon ta kamar me jin barcci
Ko kallon ta beyi ba yace me ma sunan ki
Mtwssssss wannan guy din ba abinda zaka mishi ka burge shi ta fada a zuciya
Mariya sir
Ki je ina zuwa
Sir amma ance emargency ne fa
Wani irin kallon ya watsa mata da yasa ta wucewa bata sake bi ta kanshi ba saboda ba karamin aikin sa bane ya ce ze mare ta
Waye mariya
Yar Alhaji Ahmed me gwala-gwalai baban ta shahararren me kudi ne kuma ita ce yarinya guda daya tilo wace Allah ya azurta su da shi
Hajiya falmahta mahaifiyar mariya kenan
Mariya Allah ya dora Mata son Azeel tunda suka fara piratical gashi kuma Allah ya hore masa kyau
Ita yarinya ce me kyau sosai da kyau hali
__Bauchi___
Unguwar winti
Gidaje ne da kaga unguwar zaka san cewa talakawa ne a gun sossai saboda yanayin ginin gujin
Safiya!! Safiya!! Don ubanki zo ki debo mana ruwa shegiya Kamar idan anyi abincin baza ki ci ba
Ni fa mama na dena cin abinci tunda se na ibo ruwa za'ayi girkin to bazan ci ba
Safiya ni kike wa magana haka dama kin saba ai idan baki ibo ruwan ai ubanki baze ci abinci ba
Se me ai ke ma ubanki baze ji dadi ba a kabarin shi tunda bakiyi biyayya ga mijin ki ba
Innalilahi waina ilaihi rajun yanzu safiya ni kike zagi Ni mahaifiyar ki kike zagi
A'a ban zage ki ba kince ubana Ni kuma na ce ubanki baze ji dadi ba
Don ubanki kinji Ni nace ubanki
Ba uba na bade
Tana fadan haka ta fice da gudu
Allah ka shirya min safiya ameen ya rabbi
Safiya kenan ya ga Mallam Ibrahim me gadin makarantar Hawza dake bakin titi Mallam Ibrahim mutum ne kamilale me tsoron Allah yana da rufin asiri duk wata yana karbar albashi da shi yake ciyar da iyalinsa safiya itace tilon yar su amma Allah ya hore mata rashin ji wanda ko maman ta bata bari ba baban ta kawai take tsoro saboda shi ke bude mata ido idan tayi lefi....
Baba ina wuni inji safiya
Ji ta kamar wata mutuniyar arziki
Turo bakin ta tayi gaba tana gunaguni
Abinci baba yake ci wai ke Hassana me matsalar ki ne yanzu me tayi Miki
Hmmm Mallam ...........zayano mishi komai tayi
Kallon safiya yayi hawaye ta fara yi
Marfin Samira ya dauka ya kwada ma ta a kai
Wayyo mama baba y kashe shikenan na mutu ya fasa min kai shikenan bázanyi yi aure ba
Idan bikiyi min shiru ba zan karkara ya ki ne
Zo ki dauki abincin ki
Bazan ci ba tashi tayi ta wuce daki tana kunbure kunbure
Gari yayi shiru kowa na barcci amma safiya idon ta biyu kallon mama tayi wace tayi nisa a barcci
Tashi tayi sadaf sadaf kamar wace tayi sata
Kitchen din ta wuce bude tukuyan tayi taliyar da mama tayi da wake ta fara ci a tukunyar taci sosai kokarin tashi take taji muryan baba na cewa waye ne
Zazaro ido ta fara yi ................
Idan kuna comment ni kuma zana muku yanda kuke so
Comment and share
Luv u oll 🥰🥰
🤴 GIDAN SÁRAUTA 🤴
(The house kingdom)
🌹Autar Ammi 🌹
(Sakeenah)
To Alhamdulilah Àllah ya kawo mu ina rokon Allah ya sa in fara lafiya yasa in
gama lafiya
Marubuciyar
**Holbereh**
**Aljanah Ce**
Yanzu kuma
**Gidan Sarauta**
Wannan iƙirarin labari ne
Comment dinku kawai nake so
Free Page 3️⃣➡️4️⃣
🌹 Autar 🌹PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
💫P.E.W.A💫
Home of Perfect Writer's together we stand🤝
ESSENTIAL WRITER'S 📚🖊️*
-------------------------------------------------------
Zazaro ido takeyi kamar wacce tayi wa sarki karya
Jin baba na ta tahowa ne yasa ta zame wandon ta tafara fitsari a gun
Haske baba ya hasko
Safiya me kike a cikin kitchen? Au dama a cikin kitchen nake tafada tana jan wandon ta
Wallahi baba na zata ina bayi ne Shiyasa kayi hakuri
Allah shirye ki
Ameen baba
Wucewa daki tayi wani irin ajiyar zuciya tayi kamar wacce tayi gudu
Wannan tsohon saboda ya haife ni yaringa gasa ana tsoron shi fa
_*Abuja*_
Wani matashin saurayi ne zaune akan kujera fuskan shi da murmushi akai ga dimple din sa na lostewa duk da cewa ba dariya yakeyi ba
Aseel kenan kamar sa da Azeel kamar an saga kara abinda ya bambanta su shi ne launin fata shi fari ne amma irin fari ne kyau
Waya ne makale a kunan sa daga gani waya yakeyi
Yanzu ke puppy love baza ki dena rigima ba baki san kin girma ba haba watarana se gidan miji ba
Ta dayan bangaren
Wallahi yaya ka dawo yanzu shekara dari kaki dawo saboda baka sona ko
Dariya yake yi shekara dari fa puppy love chab meyasa baza ki kira yaya Azeel ba
Zaro ido tayi kaman yana ganin ta so kake ka zo ace na mutu kenan ko wanan da yake daure fuska kaman wani kashi Ni fa i na tunanin cewa ba mommy ne ta haife shi ba mutum kamar hadari baya dariya
Shima zaro ido yayi chab ba ruwa na
Bye see you
Kashe wayar yayi batare da yaji me za ta sake cewa ba
Murmushi yayi tare da shafa sumar kansa
"Yaya Azeel kenan ko yaushe ze chanja oho "
Sir Aseel
Kamal lafiya
Wallahi kasan sati me zuwa za'a bamu matsayi ko
Ehh nasani
Wallahi ban yarda da Jamal ba saboda shi tsananin zafin hasada da kiya shi ya mishi mugun aikin ina so kayi taka sansan da shi
Murmushi yayi kafin yace kamal abu daya nake so ka dogara da shi wato "Allah" Jamal ba shida ikon cire min rai se Allah ya so ka dena sa irin abun nan a ranka
Shima kamal murmushi yayi saboda abinda ya sa yake son Aseel kenan yana da tsoron Allah ga addini tunda suka shigo Barack din mata ko shaye shaye be dame shi ba
Ok na gode
Yanzu de zuwa anjima za mu shiga suleja saboda zan siyo tsaraba wa hajaju na
Kai da autar kun nan se ahankali
Dariya yayi yana fada mishi abinda ta fada game da Azeel
Wallahi ko Ni tsoron shi nake ji me yasa be zo aikin soja ba yaje aikin hospital
Ra'ayin sa ne hakan
_*England*_
Azeel wai meyasa kake irin wannan tunanin ne wallahi ba abinda ze sami Dan uwan ka i na fada ma duk musulmi fa ya kamata yana tunani me kyau ba mara kyau ba
Wallahi sadiq baza ka gane ba idan har na kwanta barcci ba abinda ke zuwa min se ganin Aseel na kuka yana ne man taimako na
Yafada duk jikin sa yayi sanyi
Kana addu'a insha Allah ba abinda ze faru
Ameen na gode sosai sadiq
Babu komai
Rike kansa yayi saboda maganar da yayi sosai
Jinin sarauta basu son magana ko ya fada da tsigan tsokana
Harara ya galla masa
Nace ina mariya.......
Kwance take se faman kallon hoton Azeel takeyi hawayen da ya taru a idon ta ta share
Ya rabbi kasan meyasa ka dora min son bawan ka
Allah ka dora mishi sona kamar yanda ka dora min
Kuka ne yaci karfin ta
( Wallahi har ta bani tausayi soyayya
kenan)
_*Bauchi*_
Fadar sarki Rilwanu
Me martaba Allah jawo tsawon rai ya kara daukaka
Murmushi sarki Rilwanu yayi
Ameen
Kana da bako
Waye?
Alhaji Ahmed me gwala-gwalai
Barshi ya shigo
Bayan Alhaji Ahmed ya shigo sun ci sun sha
Me martaba ka manta ni kenan
Ina zan manta da aminina
Hira sukayi sosai
Ya maganan Mariya da Azeel
Yana nan inji me martaba se da sukayi hira sosai kafin alhaji ya wuce
Ni kuwa na ce wani magana kenan
_*Unguwar Winti*_
Wanka ta fito tayi kwaliya amma hoda da jan baki se kwali
Kaya ta sa kamar ba ita ba
Mariya kenan tana da kyau sosai duk da cewa ba karamar yarinya bace saboda a shekara yanzu haka tana 13 years amma kuruciya be bar taba
Mama na tafi islamiyya se na dawo
A dawo lafiya
Bayan taje islamiyya ana karatu bayan anyi musu hadda kawar ta A'isha
Nifa wallahi ina son na aure dan gidan sarauta
Mtwssssss ke dama tunanin ki ai bana mutane bane
Me kike nufi
Nifa wallahi yan sarauta baya burge ni a to Ni da in aura Dan sarauta gwara na aura idi ( saurayin ta)
Dariya A'ishah ta kwashe da shi
Allah ya sa ki aura Dan sarauta
Ke daga yau karki sake min magana shegiya me fuskar bangon mutanen duniya
Yi hak...... Marin da safiya ta mata ne yasa ta yin shuru wucewa tayi kamar zata tashi sama
Ai wanan iskanci taya zata ce min zan aura Dan "gidan sarauta" shegiya bazan sake mata magana ba don uban ta
Masifa take tayi
Kuyi comment and share
Ni kuma inyi muka novel ✍️✍️✍️
Daga Alkalami
🌹**Autar Ammi** 🌹
🤴 GIDAN SÁRAUTA 🤴
(The house kingdom)
🌹Autar Ammi 🌹
(Sakeenah)
Daga alkalamin ✍️✍️Queen of essential writers
To Alhamdulilah Àllah ya kawo mu ina rokon Allah ya sa in fara lafiya yasa in
gama lafiya
Marubuciyar
**Holbereh**
**Aljanah Ce**
Yanzu kuma
**Gidan Sarauta**
Wannan iƙirarin labari ne
Comment dinku kawai nake so
Free Page 5️⃣➡️6️⃣
PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
💫P.E.W.A💫
Home of Perfect Writer's together we stand🤝
ESSENTIAL WRITER'S 📚🖊️*
-----------------------------------------------------
Masifa take yi kamar zata ara baki
Ko sallama batayi ba ta shige cikin gida
Ke da waye kuma safiya inji mama
Mama wallahi zanyi rashin mutunci taya A'ishah za tace wai dan sarauta zan aura
Ke kuma ai fata me kyau ta Miki
Ni na dena mata magana ma
_*Fadar sarki Rilwanu*_
Duk ma aika tan gidan aiki suke yi
''Ni ko nace me ake yi bari de mu shiga daga ciki''
Hajaju na gani ansha wanka tayi kyau masha Allah saboda ta fito kamar princess dinta
Daddy please i want to follow u
Me zakiyi a airport ne wai Khadijah haba
Kashe mutane zanyi ta fada tana turo karamin bakin ta
Kallon ta kawai me martaba yakeyi
Me sunan mama Allah shirya min ki
Ameen ni fa Yakamata ana bani girma tunda sunan hajjo gareni amma duk kun renani kai da mommy ga wannan yaya Azeel haushi ma yake bani wallahi matar sa taji jiki balle yaran sa
Kinga ba ruwana kinji
Jakadiya me kulla da Khadijah ce ta fito
Tana murmushi
Me martaba kana fama da surutu hajaju ai se ku bar min miji a aepot kuke cewa ko me
Dariya ne ya kubucewa wa Khadijah wai ke tsohuwa yaushe zaki waye ne kuma a haka yaya na ze aure ki chab ae gwara me fuskar samudawa ki aure sa
Daddy mu tafi k..........
Maganar ne ya yanke tsanadiyar rashin ganin me martaba baya gun
Idon tane ya kawo ruwa
Mama hansai ina daddy yake
Ba surutu kike yi ba taya za ki San ko ya tafi ko be tafi ba
Kuka takeyi kamar wacce aka ce wa maman Sweety zata kwace mata mommy (😂😂)
Tsaye yake da trolly din shi eye glass fari a idon sa fuskar de kamar na samudawa inji hajaju da fada
( Nace ba Aseel ne ze dawo ba ?)
Hmmmm Finally kasar haihuwa yafi kasan aro
Motoci ne kusan guda biyar suka zo daukar mutum daya
Murmushi yayi har dimple din sa ya loste
U are welcome my son
Daddy Ina wuni
Ya hanya ?
Lafiya qalau sarki Rilwanu Suleiman
Hararan sa daddy yayi ka rena Ni ko
Azeel
Mota suka shiga
Ita duk a zaton ta yaya Aseel ne ashe boss ne
Birki ta ja
Yaya kai ne
A'a bani bane
Ya fada tare da hararan ta
Ya dawo ai kuma dariya tayi tace daddy yaya Aseel fa
Gobe ze dawo Insha Allah
""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""
Wanka tasha tayi kwaliya tayi kyau sosai ta fito a yan mata
Mama mun wuce
To Safiya A'isha kuyi a hankali don Allah kun san de gidan sarki za ku wannan wawiyar wai da bazata je ba
Se anjima tafada tare da jan hanun A'isha
Motoci ne birjik a cikin gidan Aseel ne ya fito daga mota se wata budurwa kallon budurwa nayi da kyau ikon Allah
Me kuma mariya keyi a gidan me martaba
Ku biyo NI don jin ya zata kaya
Comment and share
🤴 GIDAN SÁRAUTA 🤴
(The house kingdom)
🌹Autar Ammi 🌹
(Sakeenah)
Daga alkalamin ✍️✍️Queen of essential writers
To Alhamdulilah Àllah ya kawo mu ina rokon Allah ya sa in fara lafiya yasa in
gama lafiya
Marubuciyar
**Holbereh**
**Aljanah Ce**
Yanzu kuma
**Gidan Sarauta**
Wannan iƙirarin labari ne
Comment dinku kawai nake so
Free Page 7️⃣➡️8️⃣
PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
💫P.E.W.A💫
Home of Perfect Writer's together we stand🤝
ESSENTIAL WRITER'S 📚🖊️*
Azeel dake kokarin rungume Aseel tsayawa yayi kallon ta yake ita kuma se faman washe hakwaran ta takeyi
Brother Ina ka samo wannan kuma ya fada kamar be santa ba
Big bro se kabari mu shiga ciki ai ko
Hada fuska yayi kamar ba shine yayi maganar ba hararan sa yayi kafin ya rike hannunsa su ka wuce ciki
Daddy da mommy se murmushi suke yi saboda yanzu gidan ze dawo gida
My puppy love
Na'am my Yaya soja mazan fama
Hada giran sama yayi
Waye mazan fama kenan
Rike haba tayi kafin tace wa ai yaya na mazan iska ne ba na fama ba
Barin je inyi wanka lil sis
Yanzu fa kadawo suna daban daban zan na ji
Wucewa yayi ko jin ta beyi ba
_Azeel_
Daki ya shiga na ce Masha Allah dakin ya hadu iya haduwa daga gado se closet din shi se bayyan gida komai Black and white ne ba buri amma komai ya hadu
Wanka yayi ya kusan 5 mins a toilet din kafin ya shirya cikin gezina fari yayi kyau sosai se kanshi Tulare yakeyi na Royal Black
Tunani yakeyi to me mariya keyi a gidan su kuma ba wanda yayi magana ko dai Aseel na sonta ne ? A'a da yana son ta ai baza tana sona ba duk da cewa bata fada ba amma yanayin ta ya nuna
Share zancen yayi tare da fitowa zuwa parlon
Kowa ya halara har ta mutanen unguwar sun zo murnar dawowar yaran sarki Rilwanu Suleiman
A'ishah kiyi sauri don Allah kinga kar mutane su riga mu cika gujin haba kina tafiya kamar sabuwar amarya
Wallahi duk na bi na gaji ne ai mun iso ma
Shiga cikin gidan sukayi
Dogarin suka nuna musu inda ake bikin
Ki ga saboda dawowar yaran sarki Shiyasa aka shirya biki
Shiyasa fa suke bani haushi wallahi Basu san za fin kudi ba
Kinga safiya yi shiru kar ajimu
Aseel da Mariya se hajaju ne zaune
Suna hira yayin da me martaba da mommy ke magana da manyan bakin su har da mahaifin mariya
Nifa wallahi aunty mariya i dan kina maganar wanan mugun haushi kike bani ga handsome bro dina ki aure Sa mana
Kallon ta mariya tayi kafin tace ai handsome bro dinki Yana da budurwa
Kallon sa hajaju tayi da gaske
Ehhh mana za ta zo ma
Tsalle ta yi kafin tace wow my Dan uwa yanzu yaushe ne auren kuma zata haifama na baby's ko
Eh
Tashi yayi tare da nufan inda Azeel yake kawai suka bangaje juna
Da masifa ta fara magana baka da ido ne zaka buge Ni
Kallon ta yake yi yanda take mosta bakin ta gata kaykyawa da ita
Ai dama haka kuke yaran masu kudi baka da ikon da zaka ce min yi hakuri
Don Allah kiyi hakuri ban sani ba shiyasa amma ina neman tafiyar ki
Kallon shi takeyi gashi da kyau abin sa
Ba komai tace tana kokarin jan A'isha da ta tsaya kallon mutum kamar wani dan India take kallo
Uhmm yi hakuri zan iya sanin sunan mallamar kuwa
*SAFIYA* kawai tace mishi tare da wucewa amma tana kallon kyau sa da haduwar sa amma bayi da girman kai
Kinga wannan shine yaro na biyu ga me martaba
Safiya kallon A'ishah takeyi don jin karin bayani
Wallahi kuwa soja ne shi ba ruwansa yana da fara'a ga shi be damu ko kai talaka ko me ba kowa yana wasa da shi
Akwai babban yayan su shima amma ban san sunan sa ba saboda sunan su iri daya ne kuma dukan su ance suna da saukin kai
Amma Aisha ke munafuka ce taya kika san abubuwan nan
Wallahi nima summaya ce take fada min wai tana son wannan da ya tambaye sunan ki
Wucewa sukayi
Aseel har suka bace mishi kallon hanyan yakeyi haka kawai yaji yana son ta ga shi sunan ta me dadi
Wucewa yayi zuwa gujin Azeel da ya zauna yana dadana wayar sa
Big bro
Dago kansa yayi tare da zubama masa sexy eyes din sa
Nayi mata wallahi
Murmushi ne ya bayyana a fuskar sa
Wallahi she is very cute ga gashin kanta ya bayyana a goshin ta amma fa tana da masifa daga gani
Wacece kuma wace tayi Sa'a
Sunan ta safiya wai amma i luv her ya fada kamar zeyi kuka
Ka fada mata mana taki tsaya wa ma
Don't worry she is ur wife to be inshallahu
Ameen bro
Tambayan da yayi ina suka san juna da Mariya
Yar Alhaji Ahmed me gwala-gwalai ne fa aminin daddy Kuma a airport na ganta na abuja tace min wai nan ta nufa muka taho tare kuma kasan akwai mota na a airport shine muka hada hanya da ita
Wallahi yaya mariya bata da matsala she is nice
Kallon da yayi masa ne yasa shi yin shuru
Anyi biki an waste A'isha anyi saurayi wani dan Alhaji Abubakar kuma har ya karbe number ta se soyayya suke sha duk da cewa kunya ya hana ta magana da shi sosai
Suna hanyar su na koma wa gida ne Khadijah ta rike safiya tana cewa yar uwa don Allah ki boye ni wallahi wannan tsohuwa nan bazata barni ba
Kallon ta kawai safiya keyi saboda kaman da suke yi da Aseel sosai
Jakadiya na zuwa ta finciko ta
Ke ranar bikin ma baki girma ba wallahi anji jiki da ke
Nifa ba inda zani meeting din ai ba dole se naje ba
Aunty na ki ce mata Ni na girma
Dariya safiya tayi kafin tace mama ki barta ai ita babbar yarinya ce
Ya ta ki bar wannan yar duk taga wahalar Dani gobe za ta cekul
Kingan ki ko school ake cewa ba cekul ba tsohuwa kawai
Aunty na bye
Daga mata hannu tayi amma yarinyar ta shiga ranta sosai
Safiya kinyi farin jini fa a gidan nan
Ita ce Autar su
Juyawa sukayi har sun kai bakin gate din fita taji an rike mata hannu ta
Kallon hannun tayi ta kalle sa
Sorry pls sake hanun ta yayi kallon Aisha yayi yace don Allah dan bamu minti ɗaya
Murmushi tayi kafin ta masta kadan
Ni sunana Aseel Rilwanu Suleiman
Kiyi hakuri na tsayar da ke a hanya ko kuma a ina zan ce ma oho ya fada yana murmushi
A gaskiya ina son ki kuma