Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 5
Allah zai sa yayi mata kwarjini amma ina don tsaki tayi tace "banga uban da ya isa ya sa nayi girki ba, dilla kalle ka wai kai har namiji ne anan. Mtsww! An dai rako maza wallahi, banda ba makwanci wahala ba abinda mutum zai buga kirji ya ce ya iya. Ka gayyato Halima daga inda take tayi maka" Ta faɗi tana barin shi zaune a inda yake. Kaninsa dama tun da ta fara masa masifa suka fice daga wajen. Dafe kansa yayi da hannu biyu yana tunanin wani irin hukunci zai mata. Ashe dai haka take. Wasu siraran hawaye ne suka fara zubo masa, yana tausayin kansa. A haka ya fara tunanin rayuwar sa, wanda ya sani da wanda aka bashi labari. ABDOULLAHI ABOUBAKAR Asalin kakanninsa yan jihar Borno ne a gabashin Nijeriya, sana'ar siyar da citta da tafarnuwa ya kawo su Nijar inda suka sauka a zindar. Mahaifinsa Aboubakar ya taso ɗan dangi kasancewarsa auta cikin yaran kakansu talatin da shida. Yayi karatu zuwa sakandire kafin ya faɗa harkan kasuwanci, tun yana karkashin ubangidansa mommadou har ya samu kantin kansa. Amanarsa da gaskiyarsa yasa ubangidansa masa tallar yarsa mafi soyuwa a gareshi Safiyyah . Nan take kuwa don shi ma ya daɗe yana sha'awar mallakarta a matsayin mata sai dai tsoro ya hana masa tunkararta. Anyi biki amarya ta tare a nan cikin gidansu tare da sauran yan uwansa maza. Shekarar su ta farko ta haifi yarsu Aisha, daga nan sai Abdoul wanda tsakanin sa da Aisha shekara uku ne, daga nan kuma Safiyyah tayi haihuwa bakwai wanda ya cika su tara gaba ɗaya. Duk abinda Alh Aboubakar ya tara akan karatun Yaransu yake karewa, makaranta mai kyau yake tura su, duk da kasancewar daga shi har safiyyah ba suyi wani karatun zamani ba hakan bai hana Yaransu samun sakamako mai kyau ba don kullum suna musu addu'ar samun nasara. Abdoul na da rauni ɗaya 'yan uwansa, baya son abinda zai ɓata musu, burinsa farin cikinsu sannan yana hakuri da duk wani mai son su. Wannan raunin da kuma kalaman Halima ya hana shi ɗaukan muguwar mataki akan Agaysha don duk abinta bata wulakanta su sai da in shi ta zage su a gabanshi ko tayi amfani da kissa ta hana masa yi musu wani abin arziki. Karar da wayarsa tayi yasa ya dawo daga duniyar tunanin da yake. Share hawayen da ya gangaro masa yayi sannan ya ɗaga wayar. "kun iso? Toh gani nan" Ya faɗi yana ɗaukan mukullin mota. Fita yayi dasu zuwa Assemblée, Auberge Mourna ya tsaya inda ya kasance gidan abinci mai lamba ɗaya. " wannan rowan abinci har ina, salon kada mu gaisa da Madam ne ko" faɗin Ɗahiru ɗan jihar Kano. Dariya Abdoul yayi yace "kun san tayi nauyi. Muna gama waya ɗazu sai ga kiranta. Wallahi oder nayi ɗazu na kai masu" Ya karasa yana istigfari a zuciyar sa. Ya kashe musu kuɗi sun ci sun yi kat sannan suka koma gidansa gaban sa na faɗi. Ba laifi ta karɓe su da kyau kuma ta chanza kaya zuwa shiga na kamala. Har cikin ransa ya ji daɗi don har lemun abarba da kankana ta basu mai sanyi.Tara 657 69 15 by Ummu-abdoul Hira sosai sukayi da abokansa, sai da akayi magariba sannan sukayi sallama. Ranar duk sai ta wanke laifukanta saboda lafiyayyar abinci tuwo da fakku (malohia murzazza) ta kawo musu karfe shida na maraice. "Ga fa fakku ku ci ku ba Yan Nijeriya labarin daɗinsa" Ta faɗi tana dariya. Kasancewar ta gwana a fannin girki yasa basu so ya kare ba, tas suka tashi da shi suna ci suna santi. Kudi suka aje mata dubu hamsin na kuɗin Nijeriya, zo Kuga murna wajen Agaysha saboda sanin da tayi in ta juya su zuwa cepa zata samu kusan dubu ɗari don ma darajar cepa ya faɗi. Da naira dubu daya za'a baka cepa dubu uku, Yanzu kuwa dubu da dari shida zaka samu. Ko da ya dawo daga rakiyansu ya iske har ta gyara wajen ta baɗe gidan da kamshi. Har cikin ransa ya ji daɗi. Nan suka baje hira bayan ya ja musu limancin isha'i. *** "Yanzu Agaysha haka zamu dinga kallon su Ummu Abieha da sadiya, shekarun Sadiya and kusan talatin fa balle ayi maganar Ummu. Wai bakya jin wani iri ganin su a gida ba aure" faɗin Abdoul ransa ya kai kololuwa a ɓaci. Ace Yaransu mata babu wanda ya fito da niyyar aure. "wallahi kuwa babansu, duk masu zuwa kuma da matan su, da anyi maganar aure matayensu su tada rigima, nima fa abin na damu na." Ta faɗi tana gyara zama. "kin san har Halima ta mutu bata yafe min ba, kar ya zo alhakin ta ne ya ke kama mu. Allah ka yafe mana yaranmu su samu mazajen aure" Ya faɗi yana kwalla. "Aameen ni ko na hudu ne in dai za'a so su ba komi, " faɗin Agaysha "Amma ke bakya son kishiya, kike fatan ayi ma wasu don a auri yaranki. Lallai son kai ya miki yawa" Ya faɗi yana mikewa, don ya fara jin kiran sallah. Kiran sallan ya ki karewa, tun yana Jinsa daga nesa har yaji na bayan gidansu an kira. Leman da ya ji yasa ya taɓa gadon da yake kwance. Jike yake da zufa, da ma ana mafarki mai tsawo ne haka, shi dai har ga Allah bai taɓa ko jin labarin mafarki a bayyane kuma mai tsawo hakaba, tun da ya samu natsuwa da Agaysha, kalaci kawai yayi barci ya kwashe shi kafin ya kai ga wanka. Kallon agogo yayi karfe huɗu da minti biyar, tabbas la'asar aka kira, shi kuwa wani irin barci ne wannan tun karfe tara na safe. Abinda bai sani ba haka kawai Agaysha taji bata aminta da shi ba, ta sa masa maganin barcin da take ɗura ma yaranta in suka ishe shi. Don kar ma ya nemo Halima kafin ta dawo daga wajen bakanta. Abin tambaya anan shin dama ana mafarki a barcin da ba na Allah ba ko kuwa MAFARKIN ABDOUL daban ne. Amsar na wajenku masu karatu😜 Tashi yayi jiki babu kwari, yunwa yake ji amma bayi ya fara isa yayi wanka, gami da alwala. A zaune yayi sallah sannan ya shiga kitchen ya iske tayi tuwo kafin ta fita. A nan ya zauna ci hannu baka hannu akushi. Sannan ya samu karfin gwiwan fita. Gidan Yahai yaje don ya samu rakiyansa, nan ma ba wani zama yayi ba suka ɗauki jiki zuwa gidan iyayen Halima. Bayan an musu iso, sun gaisa da mahaifinta wanda murna ya hana shi ɓoyewa. Baffa ya faɗa masa komi dangane da alakar Halima da Abdoul banda rabuwansu. Nasiha sosai yayi musu musamman akan aje mace fiye da ɗaya a gida, mahimmancin hakuri da adalci. Sunyi murna kwarai da karamcin dattijan arziki. Tsoron Abdoul ɗaya yanda Halima zata amshi Zancensa, hakan ya sa Yahai ya bashi shawara da ya bi ta hannun iyaye kawai. Yasan dai yana da fada a wajen iyayenta maza shi yasa ya fara da mahaifinta. Bayan tafiyar su Abdoul ya ɗaga waya ya kira Baffa. Nan ya ke faɗa musu zuwan Abdoul da kuma yanda suka kwashe. "shi Abdoul ɗin ne yazo wajenka?" Ya tambaya cike da mamaki. Dariya yayi sannan ya bashi amsa da cewa "shi fa, ko minti uku basu yi da fita ba. Ga ma tsarabar da ya kawo ma yara nan. Yace zuwa Asabar kaga jibi kenan zai shigo wajenku". "Allah ya kaimu, yanzu muka dawo asibiti Halima har oxygen aka sa mata da muka isa, mun aza ma rai yayi halinsa sai mommansu ta nace akan Halima bata rasu ba. Amma Alhamdulillah har drip ɗin da akasa an cire kafin in dawo. Ban kira ku ba don bana son hankalin ku ya tashi ne" hawayen da suka zubo masa ya goge don ya san da Ace Halima ta rasu ko iyayenta baza su kai shi rashin ta ba, in bai yi karya ba ai cewa zaiyi ya fisu sanin wacece Halima da darajan da Allah ya bata. Samun irinta sai an tona. "Allah ya bata lafiya, gobe bayan Jummu@ zamu zo mu duba ta, in kuma an sallame ku shike nan" Ya faɗi bayan ya gama tunanin anya a duniya akwai sauran masu riko da zumunci irin yayansa. "Toh shike nan, Allah ya baku iko, ya sanya Alkhairi tsakanin ta Abdoul in babu ya musanya mana" "kai baffa ba bu ko yar kunyar nan. Yar farin ku ce fa kar ka bari a ji kana kwararo addu'a fa" mahaifin Halima ya tare shi da tsokana, nan sukayi dariya. *** Ko da su Abdoul suka isa gida Agaysha ta dawo tayi yan birne birnenta wanda aka tabbatar mata da in har Abdoul ya shigo gidan toh sai yanda tayi dashi. Suna gab da shiga gidan Yahai ya ja shi gefe yace "karanta addu'ar shiga gida haɗe da suratul ahad, ba wani jinsi na shaiɗan da zai kasance tare da kai. Kayi sallama kuma tun daga bakin kofa kar ma Ace sun rako ka zuwa bakin falo. Ire iren sakacin nan ke sa tsafi yai tasiri a gidan mutum. Rashin yin addu'ar fita gida da shigowa " Ba musu ya karanta, suka shiga da sallama. A ciki ta amsa tana yatsine fuskanta kamar taga kashi. Cikin tsawa ta ce " Daga ina kake na dawo baka nan" Ta tambaya kamar wani ɗan ta da take shirin mazga. "Gida na ya zo fa gashi na kawo miki shi har gida, dafatan banyi laifi ba" Yahai yai saurin amsa mata don ya san kaidinta, Allah kaɗai yasan tsafin da tayi. "Auho! Kasan akwai wata karuwa da take neman rusa mana zaman lafiya a gidanmu, wallahi na aza wurinta ya je don yau da asuba sunanta ya tashi da shi a baki, tsoron zuwansa wajenta na bashi maganin barci a tea, kasan abinda ya ban mamaki" Ta karasa tana jefa ma Yahai tambaya, dama ita haka take da son nuna isa, in tayi abu gani take wayonta ne ya kaita ga hakan. "Sai kin faɗa madam" "ko da na fita kuka yake yana kiran Halima ta rasu, tsakanin ka da Allah ko a littafi ka taɓa karanta mutum na barci yana mafarki Alhali barcin magani ne, nayi Alkawari sai na hukunta yarinyar nan, duk tsafinta sai na hukunta ta" Ta karasa tana kara yamutsa fuska kamar Halima ne a wajen. "gaskiya shi yasa na gagara yarda da ita, a sani na ke kaɗai ce aboki na ke so, kwatsam ya zo min da zancen wata Halima. Allah raba nagari da mugu, mtsw! Mata basa kyautawa wai takan namiji su siya wuta da hannunsu, sai ki ji suna malam malam yoh ko da ayar Kur'ani akai lakani dashi ai bazai tashi da ga shirka ba. Annabi ya faɗi su zasu fi yawa a wuta. Kuma ba komi bane zai kai matan zamanin nan wuta sai son mallake ɗa namiji. Allah ya shirye ta da sauran masu yi " Fuuuuu! Ta shige ɗaki ba tare da ta amsa aameen din ba. Nan ya ja Abdoul kofar gida suka tsara yanda komi zai kasance. Ya kara nanata masa kar ya yarda tasan aikinta bai ci ba, tunda hutun sa ma ya kare, ya lallaɓa ta kafin ya wuce. What will you say about this chapter? Hop u are happy dt Halima is still alive.... Thnx for bn there happy reading as I will b happy seeing u voting and commenting... Luff yhuuhhhhGoma Magogin Karfe 686 79 12 by Ummu-abdoul Ranar Asabar tun da safe Abdoul ya shirya ma tafiya. Karfe tara Yahai ya iso suka ɗauki hanyar Niamey. Duk kayan marmarin da suka gitta mawa sai sun tsaya sun siya. Sannu a hankali suka isa, hiran da ya ɗau hankalinsu yasa basu ga wani nisan tafiyar ba. Sun isa sun taradda an sallame Halima har ta dan warware. A falon Baffa aka sauke su inda shi ya fara tarbonsu kafin kowa. Bayan sun gaisa ne ya kalle su yace "ko zan san me ke tafe da ku?" Duk da sunyi mamakin tarbon arziki da suka samu, amma basu yi tunanin zai jefe su da wannan tambayar ba. Sunkuyar da ka Abdoul yayi sai Yahai ne ma da yayi karfin halin tattaro natsuwarsa ya ce "Baffa mun zo neman izinin ka ne, don neman auren Halima" Shiru ya sake ratsa wajen. Zukatansu nai musu ki ɗan lugude don basu san ko zai amince ba. "Ba zan ce komi ba sai Halima ta faɗi ra'ayin ta, in ka samu ta amince ka gaggauta turo min waliyanka, in kuwa bata amince ba ina rokon ka arziki kar ka sake zuwa min gida, na barku lafiya" yana kai aya ya tashi ya shige gida. Sun zauna ma kamar minti goma sai ga Halima ta shigo da kawarta Shamsiyya Ummu A, fuskarta a sake, amma ko kallon ɓarayin Abdoul bata yi ba. Hankalinta gaba ɗaya ta ba Yahai. Sun gaishe shi, sai shamsiyya ta kalli Abdoul ta ce "ɗa na! Fatan dai kana lafiya" da murmushi mai nuna tsantsan farin cikin an san da zamansa ya ce "Mommy ina fa lafiya, nayi zunubi mai girma, don Allah ki sa baki a yafe min kinji" Ya faɗi yana marairaice fuska. Jin duk sunyi shiru ya sa ya fara basu labarin duk abinda ya faru da ya koma gida har zuwa mafarkansa da yayi masu ban al'ajabi. Shamsiyya dai da ka kalle ta kasan ta na cike da tausayin sa yayin da Halima tayi ko oho, ganin sun tsare ta da kallo ne alamun suna son ji daga gareta ne ta muskuta ta ce "Abdoul mafarki ba gaskiya bane, Allah ne yake aikowa bawa wasu lamarika daga cikin buwayarsa, domin ya haskaka masa wata baiwa tashi wadda zai gane rayuwa da abinda yake cikinta.... Idan bawa yayi mafarki mai dadi kona ra'ayinsa sai yayi Sadaka kamar yadda yazo a hadisi Majma'ul Bahraini cewar "Annabi yace kunemi yayewar bakin ciki, da bacin rai wajan yin Sadaka " hardai zuwa karshen hadisin, shiyasa akeso bawa ya kasance mai yawan addu'a aduk lokacin dazai kwanta barci, sbd yanayin mafarkin dazai iyayi, idan mai dadine sai yafadama mafi kusanci dashi kuma abokin sirri agareshi amin domin yatayashi rokon Allah nake alheri akan mafarkin. Idan kuma mafarkin abin tsorone kokuma tashin hankali wanda zai haifar da bacin rai, ana so kana farkawa ka nemi tsari ka tofa ɓarayin hagu sannan ka chanza kwanciya, shima dai mutum sai yayi Sadaka yanemi tsari akan abinda yagani acikinsa, yanemi kuma zabin Allah na alheri akan mafarkin, yazama mai sirri akansa wajan barwa cikinsa sirrin mafarkin, tosai Allah yaji tausayinsa kuma yayi imani tare da tawassali da Annabi wajan zabin alherinsa. Wannan bayani kadan kenan daga cikin abubuwan da Mafarki yakunsa, Allah yasa mudace da rabo mai amfani adukkan rayuwarmu Amin. " tana kaiwa nan ta tashi tsam sai zuwa cikin gida. Dukkansu ba wanda kansa bai ɗaure ba don a zahiri sun ga tsantsan rashin bawa lamarin mahimmanci. Sunyi zugum na wasu yan mintoci chan shamsiyya tayi karfin halin magana inda ta ce "Kun san ba lafiya ta cika ba, jiya aka sallamo ta daga asibiti, mu ɗan ɗaga mata kafa. Ɗa na kasan dai kai me laifi ne sai ka san yanda zakayi ka wanke kanka" Duk sukai dariya sannan suka tambaye ta jikin Halima inda ta amsa musu da taji sauki sosai. Sun ɗan taɓa hira kafin daga bisani sukai sallama suka tafi. Wasa wasa se da akayi wata biyu Abdoul na zaryan neman sulhu amma Halima ta kafe akan ba'a haifi namijin da zai wulakanta ta ba, nan ta maida hankali a aikinta ba ta saurari zancen ba. Yanzu ma zaune take ya zo, momma ta kora ta dole taje gare shi, tsayuwa tayi a kan shi, bata ce masa komi ba. Kiran da taga ya shigo wayarta ne ya hana mata cewa komi don niyyar ta kwance masa rashin mutunci . Ɗaga wayar tayi da sallama. Maimakon a amsa sallama sai saukar ashar taji, neman tsari take da ga sheɗan. Faɗin da tayi "Abdoul yafi karfin ki jaka" nan ta fahimci wacece kuma. Shiru tayi ma wasu dakiku sannan ta ce "kin kira a sa'a ma, tun ɗazu ya ke jira na fitowar kenan se ga kiranki, gashi ku gaisa" Ta karasa tana mai mika masa wayar fuskarta cike da murmushi. "macuci, azzalumi, annamimi, wallahi in baka tuba ba wutan Allah sai ya ci ka" Ta faɗi tana haki bayan muryarsa ya sauka a dodon kunninta. Murmushi kawai ya saki ya katse kiran tare da kashe wayar gaba ɗaya. "bani wayata, meye nufin ka na kashe min wayar gaba ɗaya" Ta faɗi a tsiwace, kallonta yake yana so idanuwar su su haɗu amma fir ta ki. "Ki zauna, magana nake so mu yi" Ya ce yana nuna mata kujera. Zama tayi babu gardama. "Halima, L'erreur est humaine, (ko wani mutum na tare da kuskure) ki yi hakuri s'il vous plaît Il faut me pardonner. (don Allah ki yafe min)" Ya faɗi yana rusunawa. Ganin tayi shiru ya sa ya cigaba "Nasan ba a son rai mafi yawa daga cikin mata ke auren mijin aure ba, burin kowacce mace ta kasance uwar gida, amma ina zamu kai kaddarar rayukanmu. Allah ya faɗi a cikin littafi mai tsarki LIKULLI AJALIN KITAAB, wato ko wani kaddara a rubuce ta ke. Ba wai zan aure ki don in cikata giɓin da nake da shi a gida na ba, kin san dai ina son matata, toh ba wai zan aure ki don son nata ya ragu bane, sonki da kaunarki yasa nai sha'awar aurenki, don in yi bautan Allah in nemi yardansa. Bayan wannan banda wani dalili. Bana so in miki karya shiyasa kika ga nayi shiru akan zancen laifin da nayi Il faut me pardonner." tsare ta yayi da idanu, burinsa su haɗa ido amma fir ta ki yarda. Shiru sukayi na kusan minti biyar, zuciyar ta na rawa kamar pendulum, chan dai ta tuna isa da mulki da Agaysha ke Gwadawa akan Abdoul na ta ne ita kaɗai yasa ta tsaida zuciyarta ta ce kamar bazata magantu ba "ka turo ayi magana" Ta na faɗi ta shige cikin gida. Murna a tare da shi ba'a magana, sai da ya kira baffanunsa suka tsaida masa da ranar da zasu je sannan ya bar falon da aka sauke sa. Itama da ta shiga ciki ta faɗa ma momma abinda ta yanke ta ji daɗi sosai. Nan suka yi addu'ar Alkhairi amma kowannensu zuciyar sa kal da murna. *** Kamar yanda suka yi alkawari haka suka zo da zancen neman aurenta. Iyayensa sun yaba da karamci da halin girma iri na iyayen Halima. An tsaida auren bayan wata uku kamar yanda Halima ta roka sanda momma ta tambaye ta. Tun da lokacin wani sabon shaukin kaunar juna ya shiga tsakaninsu. In baya gari ko Kasar suna manne da juna a waya. Agaysha tayi asirin, tayi tsafin amma kullum lokacin bikin matsuwa yake duk da bokanta ya tabbatar mata baza'a taɓa auren ba. Yau ma ta shirya zuwa maraɗi don ganin wani boka, sarkarta da ammbasadan Nijar a Saudiyya ya ba Abdoul ne ta siyar, tayi karyan zuwa ta'aziyya ta ɗau hanyar maraɗi. Sanda layi ya kai kanta ta shiga don ganin sa. Kallo ɗaya yayi mata ya kwaɗaitu da ita. Nan ya ce mata "Halima ba ko mi bace face abin da zai kawata MAFARKIN ABDOUL, yanzu dai ɗan tsatsuba ya na son ya ji kalan ruwanki, da shi zai halaka Halima" " Ruwa kuma.! ya mai biyan bukatu" Ta tambaya cikin rashin fahimta. "eh! Kwaye min wannan zanin in ɗiba" ba musu ta Kwaye, ta tsorata da ya cire zanin da ya ɗaura a kugu amma zuciyar ta da ta tuna mata shike nan kafin ta koma an hallaka Halima da auren saura mako ɗaya ya sa ta sakin jiki. A wahale ta fito runbun boka ta sa mu abin hawa, Gidan kawarta Taghayshuwane ta je, nan ta huta washe gari ta koma zindar. Shiru! Shiru tana jiran a ce mata an fasa aure amma sai shirye shirye ake, ta kira boka yace shi dai yasan baza'a yi auren nan ba, ta kwantar da hankalinta ko an taru za'a fasa. Hakan yasa ta ji sakayau fatanta a fasa ranar ɗaurin aure don zai fi musu zafi. BIKI BIDIRI .... Karfe goma na safen 13 ga watan febweru 2016 a Nijar, Nijeriya, Kamaru da Chadi aka ɗaura Auren Abdoullah da Halima bisa ga sadaki mafi karanci. Anyi shagulgula sosai inda mawakiya Sa'a Vocal ta wake ango da amarya. Hanifa creations and couture suka fito da amarya da ango da zafafan ɗinkuna inda mutane sukai ta santi. Ranar Lahadi da safe aka yi walima a gidan ta da ya kama mata a nan Niamey. Agaysha bata yarda da an ɗaura auren ba sai da aka kai amarya gidan iyayen mijinsu da maraice sannan taga sun dau hanyar Niamey. Nan ta ɗau waya ta aika ma Abdoul sako kamar haka "Ango mijin Amarya, ina maka murna, na ba ka wata uku kyauta kasha amarci lafiya" ko da ya karanta sai da yai dariya a ransa cewa yake "wannan bata san abinda ke damunta ba" nuna ma Yahai wayar yayi ya karanta. "mtswww ! Wasu matan fa na kwafsawa, akan wani dalili zaki bar ma wata mijinki wata kawai don ya auro ta da yaudaran kai zata ginshe shi. In kaga an ginshi juna amaryar bata iya takunta bane. Ai ta baku daman fahimtar juna a ne amarya kuma ta kafa gwamnatin ta da kyau. Aminina kasha amarci lafiya" Ya karasa suna masu tafawa. How una dey? Op una dey enjoy am well well May Allah albarkatize una eyes make una read well nd ur hands make una vote nd comment. Luv u wolla😍😙😘😚😗 Cikan Mafarki 800 58 20 by Ummu-abdoul An watse taro Lafiya yan Uwa sun koma gidajensu lafiya lau sai addu'an zaman lafiya da aka bi maauratan dashi. Ɓangaren Agaysha kuwa kawayenta na nuna mata gara da tayi hakan kafin wata ukun ya wuce za'a tura mata warin jaɓa da ɓallewan jini. Haka dai sukayi ta shawara har dare ya tsaga. Washe gari ma haka sukai ta bata shawaran da suke ganin zai fishe su, kafin suka watse aka barta da kunan zuciya. Mafarkin ido biyu ta yini tana yi, idonta na hasko mata Abdoul ɗinta da Halima. Tayi kuka kashi kashi, ta yini tana tsine ma bokayen da sukayi mata aiki, barinma wanda ta ba jikinta. Kamar an muntsile ta, wayarta ta ɗauko ta kira shi don ta ci masa mutunci. Ringing biyu ya ɗaga. "mace mai garɗi Uwargidan Abdoul kina lafiya" Ya faɗa yana kasa da murya, hakan bai hana ta jin kaurin muryar kamar saukar aradu. "kasan kuwa an ɗaura auren" abinda bakinta ya iya furtawa kenan. "Kinsa kokwanto, baki bada gaskiya akan zan iya hana auren ba. Aiki da kokonto ai ba zai taɓa karɓa ba." Ya faɗi daga chan ɓarayin. "Kokwanto kuma?" Ta tambaya tana zare idanu kamar yana ganin ta. "Eh! Ai da kin mika gaskiya, kin amince zan iya yin komi duk da ba haka ba. Amma bai yi latti ba, ki samu ki zo sai a tura mata cuta wanda zai kar da ita har lahira." jin hakan ya

Chapter 4 of 5