Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 5
ina sai ta kai ga Agaysha tana huce kamar mai shirin dambe. "Zina kake min a kan gadonmu na sunna" Ta faɗi hawaye na kwarara daga idanunta. "Zina kuma Agaysha" Ya faɗi a ruɗe, ko dai abinda ya ke tunanin a mafarki ne a gaske abin ya faru, amsar da ta bada ya dawo da shi daga tunani. "Ya zaka kwanta kana numfarfashi a cikin barci, Allah ya isa tsakanina da Aljannar da ke shiga gona ta. Don taga bana ganin ta, kai kuma sai jin daɗi kake" Ta karasa tana gunjin kuka. Rungumo ta yayi yana tura mata sakonni masu wuyan fassarawa, "mafarki nayi kina shayar dani zumanki nefa ma femme (matata)" da haka ya rufe bakinta. Bata sake ɗaga zancen ba yayin da shi kuma ya gagara cire shi a ransa. * ** Zaune take tana kwalliya, murna ne fal a cikinta don grand frère ɗinta Abdoul zai kawo mata ziyara. Sanye take da riga da skirt na material mai kaloli, ɗinkin ya fito da surarta ya bayyana asirtaccen kyawun da Allah ya mata. Feshe jikinta tayi da turaruka fin kala biyar, duk da kasancewarsu masu saukin kuɗi sun fitar da kamshi mai daɗi da kwantar da hankali. Karfe biyu ya iso, kiranta yayi a waya cewan ya iso, yayin da ita kuma ta zura hijabinta purple kasancewar shine kala mafi karanci a kayan. Falon su tayi masa iso, wanda ke fitar da sassanyar kamshin freshener irin na Larabawa. Lumshe ido yayi sanda ya sa ka fara guda a cikin falon. Kamshin da ya daki hancinsa ya sa masa nishaɗi, se da ta kawo masa abin tarba sannan ta samu waje ta zauna. "yan mata" Ya faɗi fuskarsa yalwace da murmushi. "yayan yan mata" Ta faɗi tana maida masa da murmushi. Tsare ta yayi da ido yana neman abinda zai bambamta ta da halimar da ke zuwa masa a mafarki, mafarkinsa na jiya ya dawo masa inda yayi Wai Halima ta haihu an samu Abubakar suna ce masa saadik . Hure masa fuska tayi. Nan da nan yayi farka daga duniyar tunanin da ya shiga. "lafiya grand frère" Ta faɗi cikin yanayin damuwa. "Babu komi je pense à ton avenir (ina tunanin future ɗinki ne) " Ya faɗi yana murmushi wanda kallo ɗaya zaka masa kasan iyakarsa fatan baki ne. "wani abun ya faru ne?" Ta faɗa a ɗan firgice, kallonsa take cikin kwayar idonsa ko zata fahimci wani abun. Ganin bata fahimci komi ba yasa ta saukar da idonta. "abinda da Hammad ya miki mana, aka ce miki baya damuna ne. Addu'a ta kullum Allah baki miji na gari, shekaru ashirin da biyu ai ba a ce da ke yarinya ba" Ya faɗi ya na basar da damuwar da ta shiga kamar bai san tayi ba. "Au da ma Shine, ai mun shirya kasan na faɗa maka wancan yarinyar bacin biyan maza da take har da ɗaga wuya tana taɓa wa, wai karamar yarinyar da aka rabu da ni yar jami'a saboda ita kenan" Ta faɗi tana dariya kasa kasa. "don ta sha giya Shine me? Ba hakan ya ganta ya ce yana so ba, in ita giya tasha ke anya beyi gwajin takalmi da ke ba, wani irin zuciya gare ki, kina tunanin zai chanza ra'ayinsa ya aureki ne bayan tun farko ya nuna miki shi ba mijin aure bane, haba Halima da hankalinki da komi kina bari so na sarrafa miki rayuwa, oh ku ne masu bin na turawa da suke cewa 'everything is fair in love and war' Ko? Toh ki sa ma ranki cewa rien est juste dans l'amour et la guerre (nothing is fair in love and war)" Ya faɗi a fusace, tabbas ta san gaskiya ya faɗi amma ya zatayi da son Hammad. Kuka take mai hana sukuni ido ya sa mata duk da yana jin kukan har kahon zuciyar sa. Sai da tayi mai isarta sannan ya fara lallashinta. "Kinsan rayuwarki na da mahimmanci a tattare dani, kiyi hakuri kiyi tunani kinfi karfin Hammad in aka dubi halayya da kamala, ki hakura tun yanzu kafin ya kara miki wani takaicin gaba. Ki kuma cigaba da addu'a Shine maganin komi" haka yayi ta bata kalaman karfin gwiwa har ta sake. "Ana fa fama da zazzaɓin cizon sauro, da typhoid ga tattalin arzikin duniya na cikin ha'ula'" Ta faɗi tana mai sauya hiran. "Eh wallahi, ko ina har fa Nijeriya kuma rashin tsaftar muhalli duk ke kawo hakan fa" Ya faɗi cikin halin ko in kula. "Ta ya kenan?" Ta tambayeshi don bata fahimce shi ba. "sakacin mu yayi yawa, ba ma gyara gwata a anguwanni, bola ko ina, ciyayi sun fito jikin gidaje, amma son kai irin na mutanen mu yanzu ba'a gyarawa. Sauraye sun samu mafaka, in ka gyara cikin gidan ka ai zaka fira waje, kinga dole zazzɓin cizon sauro yayi yawa. Typhoid kuwa yanzu kinga damina ne, muna tara ruwan sama muna sha ba tare da an tafasa shi ba. Tsakanin sama da inda ka tara ruwa ai akwai germs da zasu shiga. Ko rijiyoyi da suka cicciko kinga ai ko alam mutum yasa dattin zai kwanta kafin a sha." "wai yaushe ka fara aiki da asibiti ban sani ba. Tunaninka sak abinda ya ke faruwa. Allah dai ya kare mu da lafiya". "Aameen ya rabbi" Haka suka cigaba da hira yaje yai sallan la'asar ya dawo, sai wajajen biyar na yamma yai musu sallama suka rabu. Yanda Abdoul ya tafi haka shawaran da ya bata ya bi ta gefen kunnen ta don kuwa sabon soyayya suka fara da Hammad, duk tayi masa zancen aure yakan ba ta amsa da cewa "ai kawancenmu yafi soyayya mahimmanci kar ki bari zugin kewaye ya zama katangar biyan bukatar zukatanmu" a haka yake binta da daɗin baki har ta saduda. Ana cikin haka sai ya sauya salon soyayyar su ya zama hiran da suke na batsa ne, tun bata sakin jiki har ta kware a sarrafa kamai da kan motsa sha'awar su wanda hakan yasa yakan bata kula na musamman. Sukan kashe awanni suna waya har sai sun kai ga samun natsuwa, wata rana suna cikin irin wayar se ya ce mata "Baby ina so in na zo Niamey zaki ɗan min wasu abubuwan da kike kwaɗaita min a waya" Ya faɗi cikin sigar rarrashi. "Anya sweetyna kana so na kuwa, kasan dai bazan taɓa yin zina in saɓa ma Mahalicci na ba don faranta ranka" Ta ce a fusace "wa ya ce miki zina za muyi ai kin wuce ayi aron hannu da ke, wallahi iyakarmu romance, ba zan taɓa keta haddinki ba." haka yai ta faɗa mata kalamai masu nuna aminci da yarda har ta amince. Washegari kuwa sai gashi, ta shirya da sunan zata shiga makaranta kamar yanda ya raɗa mata ta faɗi sai ga Abdoul ya iso gidan babu sanarwa ya zo mata sallama za shi karatu Kasar Faransa. "haka ba ko ɗan notice" Ta faɗi a zolayance "Na duba ne naga tabbas in ba wani kwakkwaran abu zai kaiki skul ba toh kina gida, shi yasa kawai na ga gara in zo yau tunda tafiyanmu ta nuna zuwa France" "aiko da ka taka zero, yanzu take shirin shiga makarantar wai an kira ta" faɗin haj Mas'ouda da ke shigowa falon. Kallonta Abdoul yayi alamun rashin yarda, murmushin yake ta sakar masa wanda ya tabbatar masa da zarginsa. "shin ina zata je tayi karya da makaranta" Ya samu kansa da tambayar kansa hakan. "Sai muje mu dawo kawai momma" Ya faɗi ma Haj Mas'ouda yana murmushi "Toh a dawo lfy, kaga sai kayi mata faɗan rashin tsaida miji, ta lake ma Hammad wanda sam ba aurenta a rayuwarsa." Ta ce fuskanta na nuna alamun takaici. "Momma lokaci ne..." gwaɓe mata baki da akayi ne yasa ta yin shiru. Se dai a ranta tai ta surutun an sa mata idanu. Fita sukayi tana tunanin yanda zasuyi da Abdoul don ya sauke ta a inda Hammad ke jiran ta. Sake-sake kawai takeyi don har sun kai ga gate ɗin makarantar su sai wayarta ta ɗau kara. Kafin ta ɗauka yai saurin ɗauka ya amsa wayar kana ya sa wayar a handsfree "baby ina jiran ki tun ɗazu, na matsu naji ɗumin jikinki" aka faɗi a ɗayan ɓangaren. Da ace zata iya nutsewa a kasa da tayi don kunyar da ta shige. "se dai kaji azaban wuta don ubanka, kai rayuwar da ka zaɓa ma kanka kenan lalata yaran mutane toh Halima tafi karfin ka kuma ka fita hanyar ta ko in wulakanta maka rayuwa" bai jira amsar Hammad ba ya figi motar zuwa gida. Haj Mas'ouda ya zayyana ma komi nan ta fara kuka tana salalami "Halima me yasa zaki ɓata rayuwar ki haba nayi mamakin abin da yasa kika kasa rabuwa dashi ashe, ancen mahaifiyarki gsky ne da tace an gama kwakule ki. Tir wallahi da halinki" Ta faɗi tana shirin tsallaketa ta wuce. Kafafunta ta riko tana rokon ta, rantsuwa take mata akan ba abinda ya shiga tsakanin su asali ma wannan ne na farko nan dai ta kwashe yanda sukayi ta fada musu. "Toh da kika tashi zuwa ki isko shi aka ce miki haka ne zai sa ya aureki? Sai ma ya kara tsanar aurenki. Kinga dai ni namiji ne, duk macen da na lagudata ta yarda ta aure ni wahala zata sha, kuma haka duk wani namiji yake, uwa uba ya sa ki a ɗiya mace to babu sauran mutunci tsakani. Zama ayi ta wayar batsa shi ke kai matasa ga aikata, zina, kuma da yake ce miki turmi da taɓarya ne kawai zina ina ya bar ayar Allah da yace kada mu kusanci zina, kinga kenan hatta karatun batsa, zantuttukan batsa, kallon batsa ana iya danganta su da kananun zina, kuma abin nisantarwa. Halima ki ji tsoron Allah ki tsoraci kwanciyar kabari, wuta gsky ne kuma azaban Allah gaskiya ne. Momma na wuce sai in na dawo" Ya karasa zancen yana mai da akalar zancen zuwa ga haj Mas'ouda. Godiya ta bishi dashi da albarka da tayi ta sanya masa. Nan ta bar Halima da bakin ciki da kunya.Sauyin Rayuwa 771 74 9 by Ummu-abdoul Da kyar ta iya tashi ta sallaci magriba da isha'i sannan ta sa tuwon shinkafa da fakku (malohia murzazza) don taci. Jinsa take kamar maɗaci haka tai ta tutturawa har ta cinye kaɗan ɗin da ta ci. Har zata kwanta ta yi tunanin ta ba Abdoul hakuri don ta san da wuya ya sake amincewa da ita. Nan ta iske missed calls ɗin Hammad fiye da talatin. Bayan ta tura sakon ban hakuri ga Abdoul ta kwanta tana wasikar jaki nan sai ga kiran Hammad ya sake shigowa, kamar bazata ɗaga ba don yana gab da tsinkewa ta ɗaga da sallamanta "Ni zaki wulakanta Halima? Nasan hana ki zuwa akayi amma ya akayi baki tsara su yanda mukayi planing ba, kin ban mamaki kuma ki rusa mana budget don wallahi zancen aurenmu yasa naso haɗuwar mu ba komi ba wallahi" Yayi shiru yana huci a tunaninsa zata ce wani abu sai tayi shiru wanda hakan ya kara harzuka shi. "kin ma maida ni mahaukaci ne ko, haka Allah ke abunsa, ya bani daman mallakar ki a matsayin mata nai wasa da wannan daman yanzu gashi kuma soyayyar ta dawo min kina min wulakanci" Ya faɗi kamar zeyi kuka. "tsaya! tsaya! Hotel ne zakayi zancen aure dani, ina in har haka ne gidanmu yafi dacewa da muyi, ban taɓa haɗa makwanci da namiji ba kuma bazan fara akanka don kana min barazanar aure na zaka yi ba. Na kara gode ma Allah da ban saɓa masa saboda kai ba, wallahi kunyar da naji yau yafi min sau dubu akan wanda zanji ranar kiyama inda na cikata umurninka." Ta karasa tana mai shessheka. "haba Mon amour (masoyiyata) kin san Allah ɗaya ko to Je t'aime de tout mon Coeur (ina sonki da dukkan zuciyata. Kiyi min rai ki sake bani lokaci mu tattauna wallahi duk abinda zamu tattauna mai mahimmanci ne, akan zancen aurenmu ne. Ki taimaka min ba son ni ba" Ya faɗi cikin sigar lallashi da ban hakuri. "Na ji gobe ina gida kazo kawai" Ta faɗa a takaice. "wani irin kina gida, haba sweetyna kar kiyi min haka, in zaki samu fitowa ki same ni a hotel din. Don Allah ba don ni ba" abinda ya samu kansa da faɗi kenan bayan ya tattara natsuwarsa zuwa yanda bazai bayyana fushinsa. "bafa zan saɓa ma Mahalicci na don faranta ma abinda ya halitta ba. Kayi hakuri kawai kazo gida" itama ta faɗi kai tsaye ba tare da shakka ko tsoro ba. "lallai duniya juyi juyi yanzu duk son da ake min an dena ne, sai ni kuma da Allah ya jarabta da sonki. Wai ba kiyi mamaki ba Halima, anya zan iya rayuwa babu ke, ki taimaka. Mana don Allah" Ya karasa da sumbatar iska, wanda yasan Halima na so kwarai da gaske koda ranta a ɓace yake da ya mata takan manta inda kanta yake. A mamakinsa sai yaji tace "Ni in bazaka zo ba muyi maganar anan shike nan, banyi mamakin chanzawarka ba don kana son gani na komi zaka iya" "shike nan kin zaɓi rabuwarmu akan ki zo, kin san dai babu abinda zan miki, just tattaunawa zamuyi akan mafitanmu" Ya nace akan son yardar da ita akan ra'ayin shi. "se da safe don na ga baka da niyyar gane annabi ya faku. Bazan saɓa ma Mahalicci na bafa" bata jira cewarsa ba ta kashe wayar. Buɗe kofar da akayi yasa tayi saurin share hawayen da ya gangaro mata. Har ga Allah tana son Hammad amma ya ta iya. Rungumarta Haj Mas'ouda tayi tana share mata hawayen. "kin cika yar hallak Halima, ubangiji ya dubi hakurin ki ya baki mijin marainiya, kar ki sa damuwa a ranki, wani baya auren matar wani haka wata ba ta auren mijin wata. Don haka mata masu cewa zasu bada kansu don a auresu babban kuskure ne da suke tafkawa, in Allah beyi shine mijin ba sai dai bakin ciki ya kashe su don bayan asaran mutuncin su har da asaran masoyi. Kuma duk saurayin da kika ba shi kanki walau karami ko babban zina wallahi ranar da aka ɗaura aure duk son kan koma kiyayya, hantara da wulakanci zaki kwasa maimakon soyayya da tattali. Halima bakya mamakin meyasa auren yanzu babu karko wallahi maimakon mata su gina soyayya a zukatan masoyan su sukan gina sha'awa ne, tura ma samari kalamai da hotonan batsa wai da sunan su rike su har su aure su. Daga ranar da akayi auren kuma ya kashe kishin shaawarsa se ya fara gasa ta. Ki cigaba da addu'ar zaɓin Allah ki aje son rai. Gara ki so mijin da kika aura da ki auri mijin da kika so. Kar kiyi gaggawa a aure, Allah ne mafi sani a dukkan Al'amura, Allah ya miki Albarka " Ta karasa tana lallashi ta, sannu a hankali ranta ya in fara haske ta nemi bakin cikin ta rasa. Hamdala tayi ta nanatawa a zuciyarta akan gatan da Allah ya mata na samun mai ɗaura ta a hanya. *** Sannu a hankali ta fara farfaɗowa daga cutar da ke addabarta, tun tana tuna Hammad sau ba adadi har ya zama takan kidaya su, tafiya tafiya har bai wuce ya faɗo mata sau biyu ko uku a rana ba. Kwatsam wata ɗaya da faruwa wannan Al'amarin suna kallon tashar Dounia TV (Radio Télévision Dounia) su duka har da baffa, bayan Ummitr Bingel sa Gimbiya Zuby sun gama shirin da sukanyi na mu shakata sai aka sako tallan auren Hammad da wata Amina. Shiru ya ratsa su a falon har aka sa wani shirin. Se chan ne baffa ya nisa ya musu nasiha mai ratsa zuciya, ya nuna musu illar yaudara da kuma mata su zubar da mutuncinsu. Tun daga ranar ta tattara lamuran Hammad ta sa a bola sannan ta kona. Ta samu aiki a makarantar da ta gama wato Université Abdou Moumouni bayan ta kammala masters ɗin ta. Ba laifi tayi kiba tayi kyau abinta yayinda maza suka sa ta gaba, ita kuma bata basu uzuri daga sun nemi raina hankalinta zata kora su, tsoranta zuciyarta ta kamu da son wani ta kara wahala. *** 2014 ... Gari na wayewa dare na yi kwanaki na tafiya har su isko watanni. An wayi gari Halima kan manta Hammad in ba taji an kira sunan shi ba ko taganshi kasancewar yakan kawo matarsa makarantar da take aiki. Bata da wani abokin ɗebe kewa da ya wuce Abdoul sun shaku sosai, komi ta samu in na yara ne takan siya ma yaransa ne safiyyah da ta ci sunan mahaifiyarsa hakan yasa suke ce mata Ummu abiha ,sai biyun Halima kuma a hakan suke kiranta. Agaysha ta san da zaman Halima kuma tana kishi da ita amma bata ɗauka da gaske bane don a cewarsa Halima kawarshi ce kawai da ya ɗauka kanwarsa uwa ɗaya. Hakan ya kwantar mata da hankali don duniya in dai kawance kawai Abdoul ɗin ta zeyi da koma wacece ba soyayya ba toh babu abinda ya shafe ta. Kalmar budurwa ne dai ta tsana don ko da wasa kace mata "ga budurwan Abdoul" toh zaka shiga cikin jerin makiyanta da bata da kamar su. *** Wata rana cikin ranaku, Halima na zaune a ofishinta da ke cikin Faculté des Sciences, kira ya shigo wayarta wanda daga amon kiɗan ta san yayanta ne. Da sallama ta amsa wani farin ciki na ratsa ta, lumshe ido duk sukayi a yayin da suka ji muryoyin junansu, shiru sukayi na yan dakikai, su kaɗai suka san mai zukatansu ke raya musu. "yan mata jiya nayi mafarki da ke wanda naga ya chanchanci in isar miki shi ta hanyar labarta miki". Ya katse masu shirun. "wow! Allah sa alkhairi ne MAFARKIN ABDOUL ɗin" Ta faɗi tana dariya. Shima cikin dariyar ya caɓe "Au wai har kin sa mai suna ne, tun kafin kiji" tun kan ya dire tace "kasan da ace ina da fikrar rubutu babu abinda zai hana in mai da shi littafi har in sa mai sunan MAFARKIN ABDOUL" Ta faɗi cike da alamun iyakan gaskiyarta kenan. "wai tsaya, in kuma mafarki nayi ana nakaɗa miki duka, shima alfahari zakiyi dashi" Ya faɗi yana mai cigaba da dariya, wanda ta kasa bambantashi da na keta. Cikin Alamun gundura da dariyarta tace "Ni ba abinda ke cikin mafarkin ya sani murna ba balle ka samu abin tsokanata da shi, wanda yayi mafarkin ne ke da mahimmanci Alaranma" dariyan ya cigaba da yi ba tare da ya damu da fushin da ta fara ba. " Toh hajiya halimatu ai ba yau ne farau ba, ina ga ba'a cike sati. Banyi sau biyu ba, wannan dai kawai ya tafi da hankali na sannan ya magance min matsalar da nayi shekaru biyu ina fama. Shiyasa zan faɗa miki in ba haka ba ai se kin biya. Ya sake kara sawa yana dariya. "yanzu kana da matsala shi ne baka taɓa faɗa min ba, kuɗi ne ko ciwo ko har yanzu mamansu Ummu abiha ba ta dena tozarta ka bane." Ta faɗi kamar zatai kuka. Wannan na ɗaya daga cikin dalilin da yasa take da mahimmanci a gareshi. Takan nuna damuwa ko farin ciki yayinda ɗaya ya same shi. "ba ko ɗaya, wato ke hajiya ko. Kina kwasan. Albashi, toh cepa miliyan ɗari nake so, karkaɗa kunni ki sha labari" Ya faɗi. Yana dariya, itama ta tayashi Gaisuwa da fatan Alkhairi gare ku duka. Ubangiji Allah ya Haskaka rayuwarku ya baku dukkan abinda yake Alkhairi a gare ku. Keep voting nd commenting pleaseeeeee. MAFARKIN ABDOUL 729 62 2 by Ummu-abdoul MAFARKI... "Na ganni ne a wani lambu mai ban sha'awa, bayan kayan marmari da ya yalwatu a cikin lambun har da wasu furanni masu fitar da daddaɗar kamshi wanda ya sa na kara kishingiɗa a resting chair ɗin da nake zaune a kai. Lumshe idanu nake farin ciki na yalwatuwa a zuciyata. Sallaman da kikayi ne yasa na buɗe idanu ina mai sakin murmushi. Farantin hannunki kika aje a gefe sannan kika fara shayar dani salad ɗin kayan marmarin da kika zo da shi. Wanda daɗin sa bai sa na ankara da ya kusan karewa ba har se da kika daga Yankar karshe na abarba sai na na riko hannunki haɗe da spoon ɗin da ke baki na. Hakan yasa kikai saurin ɗago idanu kika kalle ni, idanunmu na haduwa kika kasa ɗauke idanu na wasu dakiku. Muna cikin haka sai ga yara biyu sun zo a guje suna kiran "Abbu! Ummu!" kallo ɗaya nayi musu na san yan biyu ne kuma daga tsatsonki suka fito saboda tsabagen kaman da sukayi da ke. Sun faɗo jiki na kenan suna haki kiran sallah ya tada ni daga barci, faɗa min me kika karanto a ido na da kika tsare ni da kallo" Ya karasa yana mai tsokanarta, "ka bari sai mun sake haduwa a dreamland sai ka min tambayar, kasan me?" Ta dakata ko zai amsa "A'a se kin faɗi" Ya bata amsa Se da tayi dariya son ranta sannan tace "za ka yi kyau da rubuta labarin soyayya fa. Wannan iya tsara lbr haka" ba ta dena dariyar ba shi kuma kansa duk ya ɗaure, "yanzu ba za ta ba MAFARKIN mahimmanci ba bare ta kai ga fahimtar abinda ya ke damuna game da ita b" Ya faɗi a ranshi yayin da a bayyane shiru yayi mata kawai. Jin ya kyale ta yasa T faɗin "hello!" dariya kawai ya bi ta dashi kana sukai sallama. Shiru tayi tana tariyo labarin da ta sanya ma MAFARKIN ABDOUL, bata san me ke shiganta ba ta dai tsinci kanta cikin wani yanayi daga tafin kafarta har Kirjinta wanda salon bugun zuciyarta ya chanza nan take. Amon muryar Abdoul take ji a kunninta sa'ilin da yake bata labarin. Nan take wani farin ciki ya mamaye ranta yayinda tsoro kuma ya shige ta sanda ɓari guda na zuciyarta yace da ita "in baya sonki fa". Nan take sai ta shiga damuwa. Sai sa su ka yi sati biyu babu wani kwakkwaran magana da ta shiga tsakanin su, iyaka sukan gaisa da ɗan hira sama sama. "Amarya a gidan Abdoul barka da yini" Ya shigo WhatsApp ɗinta daga lambar aminin Abdoul Yahai. Aljani mai dariya kawai ta tura masa sannan suka gaisa a mutunce. "kina gara ɗan uwa na fa Halima shi tsoransa ki yankuna shi wanda hakan zai taba zumuntarku amma wallahi nasan duk kuna sonjunanku, meye amfanin cutar da kai, in shi ya kasa buɗe hanya ke baza kiyi ba? Ya tura mata haɗe da aljani mai jan kai. Bata ce komi ba sai aljani mai dariya da hawaye ta tura masa, ganin bata da niyyar bashi haɗin kai yasa ya kyale ta. Daren ranar ta tsawaita hirarsu da Abdoul har yake faɗi mata mafarkan da ya keyi kusan kullum

Chapter 2 of 5