Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 5
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels MAFARKIN ABDOUL Na safiyya ummu abdoul Ebook creator:- Shuraih Usman 99% Post at:- www.shuraih.waphall.com You can download more hausa novels ebook at www.shuraih.waphall.com MAFARKIN ABDOUL Alkalamin Safiyyah Ummu Abdoul WANNAN NA KU NE Labarin nan kirkirrarre ne don kaunarku gare ni, na sadaukar da labarinnan ga Ɗaukacin masoyana da ke 'Kasar Nijar. Ubangiji Allah ya Haskaka rayuwarku ya barmu tare 2010 Zaune take gaban fannin kimiyya (Faculté des Sciences) ta jami'ar Abdoul moumouni (Université Abdoul Moumouni Dioffo) da ke Niamey a jamhoriyar Nijar. Sun fito lectures kenan kasancewarsa ɗaliba yar aji uku a fannin tsirrai (plant biology), Yarinya ce 'yar kimanin shekaru ashirin a duniya, tana da matsakaici tsawo, Albarkan mazaunen da ke gareta da kumatunta yasa akan mata kallon mai jiki kasancewar ta ma' aboki yar sa hijab. Kalarta mai tsada ne, baka ce ba wuluk ba ma'abociyar fararen idanu kalar madara. Wasu na mata kallon mai girman kai yayin da dayawa kan so ta saboda hakurin ta da yalwataccen fara'an da ake samu a fuskanta. A zahirance kallon wayarta takeyi fuskarta ba yabo ba fallasa, amma tunaninta ya tafi chan wani duniyar. Ko a aji yau ba zata ce ga abinda akayi musu ba. Kiran da ya shigo wayarta yasa ta sakin ajiyar zuciyar da ya sa kawarta da ke zaune gefenta kallonta. "Sweetyna kana lafiya, duk hankalina ya gaza kwanciya, ina ka shige" Ta faɗi a marairaice kamar zatayi kuka. "barci na tashi ya kike ya makaranta?" "Alhamdulillah, ka ci abinci" Ta sake tambaya cikin yanayin kula "Bana jin cin abincin ne, ga de ni nan Haj na min favorite ɗina" Ya faɗi yana dariya. Itama dariyan tayi. Haka suka cigaba da hira cike shaukin juna. Har wajen mintuna ashirin sannan suka rabu cike da kewan juna. "Halima fisabillillahi bazakiyi ma kanki faɗa ba, wallahi Hammad ba aurenki zeyi ba. Ki natsu ki roki Allah ya baki nagari, kada so ya rufe miki ido" faɗin kawarta da ke zaune a gefenta. "Faɗima wallahi muna son juna da Hammad, kun kasa fahimtarmu ne, kuyi mana fatan alkhairi kawai" "ina guje miki halin mazan zamanin nan ne, basu da alkawari musamman in son da mace ke musu ya zarce misali, duk abin sa kar ki yarda ayi gwajin takalmi da ke" Faɗima ta ce cikin halin ko in kula. "in ma gwajin riga zai yi ba komai bane mu dai muna son junanmu kuma za muyi aure" Ta faɗi a kufule duk ranta ya ɓaci. Fuuuu ta tashi kamar mai shirin tashi sama. *** Da kyar ta iya isa gidan baffanta da take zama wanda ke bayan Homeland Hotel, da ke Off Ave du General de Gaulle, a wahalance ta yi sallama, ta iske matar baffanta haj Mas'uda a zaune tana kallon tashar Sunna TV. "Momma barka da gida" Ta faɗi tana mai samun wajen zama a kusa da kafanta. Kallo ɗaya tayi ma ta ta fahimci bata cikin natsuwa. "Halimatus sa'adiya taje makah da madina ta sha miya mai daɗi har da kadangare soyayye" Ta shiga rera mata tana tafi. Dariya Halima ta farayi yayinda ranta ya fara sanyi. "faɗa min waya taɓa ki" Ta tambayeta tana mai tsareta da idanu. "Faɗima ce na rasa mai na tsare mata, tsakani da Allah nake zaune da ita amma sai ta yi ta min bakin ciki da hassada" Ta faɗa ido cike da kwalla, zuciyar ta na mai jin an ci amanar kauna. "tohhhh fa, me ta yi miki, kwata kwata ba tayi kalan mai wannan halin ba" Ta amsa mata fuska cike da alhini. "Momma a 'yan kwanakin nan sai tayi ta ce min in rabu da Hammad ba aure na zaiyi ba, ki duba fa ko haushin yafi mijinta kyau da kuɗi take yi ko mai yasa ni ban sani ba" Ta karasa tana kukan da yafi jini ciwo don a duniya bata da kawar da take kauna sama da Faɗima duk da kasancewarta kanwa a wajen kishiyar uwarta. "Na rasa me ke damun mutanen zamanin nan. Sam bama son gyara, da ga an nuna mana kuskurenmu maimakon mu gyara sai mu ce ana mana bakin ciki ko hassada. Mai sonka ke gyara maka, nasan son da Faɗima ke miki ba za ta bari ki cutu ba. Hammad dai iyayen ki ba sonsa suke ba, asali ma cewa su ka yi ki rabu da shi, ina mai shawartanki da ki roki zaɓi Allah in Hammad ne alkhairi Allah ya tabbatar in ko ba shi bane Allah ya kawo wanda ya fi shi a komai" "Momma ko ba Alkhairi bane Allah ya sa mu mallaki juna, ina sonsa da yawa Momma" Ta katse ta gudun yan aameen su amsa ma addu'ar ta,. "Halima ko dai Hammad ya sanki a ɗiya mace ne, in ba haka ba wannan irin nacin son da kike masa ya zarce hankali, dama mamanki ta faɗi na karyata gashi kina neman gaskata maganarsu". Ba ta jira amsarta ta ba barta zaune tana gunjin kuka. Kiran sallar la'asar da akayi ne ya tashe ta daga barcin wahalan da ya kwashe ta a wajen. Tashi tayi ta sallace la'asar da azahar ɗin da ake bin ta bashi. Tare da Momma da babbar yar momma Amina da suke kira Amna suka kammala girkin dare. Suka shirya, karfe shida duk suka haɗu gaba ɗaya suka ci abincin, don ka'ida ne a gidan cin abincin dare karfe shida don ya zazzage kafin ayi barci, sannan abincin safe baya wuce karfe takwas ɗin safe duk don samun ingantacciyar lafiya. Bayan kammala sallah isha'i ta koma ɗaki da nufin barci. Shafin Facebook ta shiga don duba abubuwan da ke kai, har zata sauka sai sakon gayyata ya shigo ta buɗe sai taga "ABDOULLAH ABOUBAKAR (ABDOUL ABOU)" Sai da ta duba shafinsa ganin bai bada wasu bayanansa masu mahimmanci ba iyaka dai taga shima ɗan Zindar ne. Har zata goge sai ta tuna da tobashinta Abdoul Abou sai tayi tunanin Shine. Tsaki ta ja kafin ta amince. Haka ta cigaba da shige shigenta tana hira da kawarta da suka haɗu a Facebook ɗin Tiddar Azzoubir. Da ta gama ta kalli agogo ganin goma saura na dare ta sa ma ranta tabbas Hammad ya gama kallon kwallo. Waya ta ɗauka ta kira shi sai da ya kusan tsinkewa sannan ya ɗaga. Yanayin yanda ya amsa mata yasa ta tambayeshi ko ya fara barci ne "ke dai bari hajiyata, wallahi na ɗanyi aron hannu ne kinsan gajiya yake sawa" Ya faɗi cikin halin ko in kula Bakin ciki ya cikata amma haka nan ta ɗaure ba tare da nuna ta damu ba tace "sweetyna yaushe zaka daina zuwa rage ruwan nan ne, lokaci yayi da ya kamata mu san mai muke ciki" "anya in munyi auren nan baza'a samu matsala ba, kishin ki na neman kaiki ga zargi na, gaskiya da sake toh" Ya katse ta a fusace. Nan take ta fara bashi hakuri da kalaman soyayya da tasan yafi so. Haka suka shirya suka cigaba da soyayya har sha ɗaya da rabi sannan sukayi sallama suna masu begen junansu . 2 NAMIJI KO TSIYA Juyi ta ke yi hannunta rungume da filo Mafarki take amma na ido biyu (day dreaming) ga ta da Hammad ɗin ta sunyi aure. Auno su take irin soyayyar da zasu kwasa, kamar an mintsile ta tashi tayi ta lalubo kananan kayan da ta siya don kaiwa gidan aurenta. Murmushi ta saki gani take an ɗaura aurensu da Hammad an gama. "Toh in ya cigaba da Aron hannu fa?" wannan sashi na zuciyar mutum da ba'a taɓa yaudara ya tunatar da ita, bata ɓata lokaci ba tayi fatali dashi kana ta faɗin "ai na san zai daina da munyi aure". Kwanciya tayi don tayi barci amma ko gezau barcin ya gagare ta, sai ma tunani da ke neman kar da ita, bata bari ya hargitsa ta ba ta dauki wayarta ta hau Facebook "Assalamu Alaikum yan mata" Ta iske na Abdoullah Aboubakar, ita sam ta manta wani Abdoul. Amsa sallamar tayi , ashe yana kusa nan yayi ta janta da hira, tun tana sharewa har ta fara bashi amsa. *** TUSHEN SU Alhaji mousa uomarou ɗan asalin garin Zindar ne, duk da tarihi ya nuna fatauci ya kawo kakanninsa Kasar Nijar daga Kano, har auratayya da chakuɗeɗeniya ya sa sun zama yan kasa. Yara biyu Allah ya mallaka masa wato Idrisa da Abbas. Gidansa sannan nan gida ne da a unguwar yadakwandage kasancewar yafi sauran rufin asiri. Yayi kokari wajen ganin yaransa sun samu yalwataccen ilimin zamani, haka ma na addini. A rana ɗaya sukayi aure inda Idrissa ya auri Mas'ouda balarabiyar Kasar Aljeriya amma mazauna Kasar Nijar shi kuma Abbass ya auri yar gwoggonsu khadija. Wata goma sha ɗaya bayan aurensu khadija ta haifi yar ta mace wacce aka sa ma suna Halima. Mas'ouda kuma sai bayan shekaru haɗu Allah ya buɗe mata kofar haihuwa. Lokacin Idrissa ya sami aiki a fannin kuɗi da tattalin arzikin yammaci Afirka wato Union Économique et Monétaire Ouest Africaine (UEMOA). Don har sun koma garin Niamey da zama. Halima ta taso cikin gata da kula, sannan ta sami ingantaccen ilimi tun daga na addini har zuwa na zamani. Rashin haihuwar mahaifiyarta tun bayan haihuwanta yasa Abbass kara aure, inda ya auro Sauda. Tun da ya auri Sauda kuma haihuwa ta sake buɗe wa a gidan. Sai ya zama kamar ana gasar haihuwa ne a gidan tsakanin khadija da Sauda. Bayan Halima ta kammala sakandarenta a LYCÉE AMADU KURAN DAGA (LAKD) ta samu gurbi karatu a université Abdoul Moumouni Dioffo, dalilin haka ta koma gidan baffanta Iddrissa. A shekaran Halima ta haɗu da Hammad wata rana ta dawo daga registration dai dai kwanar da ya raba su da homeland hotel shi kuma ya fito daga otel ɗin. Hammad Touareg(Buzu) ne ɗan asalin Agadez ne. Fari ne kyakkyawa kamar shi ya kera kansa. Ba shi da hayaniya don magana wahala take bashi Yana da son kyale kyalen duniya amma mace da kuɗi sune kan gaba. Bai sha wuya wajen zulmiyar da Halima zuwa ga sonshi ba amma bai taɓa yunkurin taɓa ta ba yanda bai yi yunkurin zuwa neman aurenta wajen iyayenta ba. A dalilin haka iyayenta suka raba ta da shi amma fir ta ki don a tunaninta bata fara sonsa don ta daina ba haka kuma a shirye take da ta jira shi duk lokacin da ya shirya suyi auren. Babu abinda ya fi faranta ran Halima kamar ta zauna tana MAFARKIN ido biyu. Zaune take da Hammad suna ciyar da junansu abinci a baki, suna yi suna jifan juna da kallo mai cike da kauna. Yaransu suka shigo suna kwala mata kira cike da murnan dawowasu.... Ire-iren mafarkan nan Halima keyi sai ta ji duk duniya babu macen da ta kai ta dacewa da samun masoyi. A haka har ta kai aji uku ana saura mata shekara ɗaya ta kammala karatunta hakan ya tada hankalin iyayenta don sun so ta kasance a ɗakinta a wannan shekaran kasancewar ta cika shekaru ashirin a duniya. Nan dai Halima ta kekashe ta ce ita bata da masoyi sai Hammad.... WANNAN KENAN *** Washegari kamar kullum ta Shirya ta isa makaranta, faɗi ma bata ga wani fara'anta ba, ba yabo ba fallasa suka kasance tare har aka tashi. A hanyar ta na komawa gida ta shiga Faba-faba (wata yar bus da ake motar haya dashi a Nijar) nan ta iske wasu yan mata biyu a ciki. "Kin san Allah Faɗima, ko da tonton oumar ya ce an tsaida ranar auren mu da Hammad ban yarda ba, tsoro na kar in ya ce ya fasa" faɗin ɗaya daga cikinsu. Wacce da gani ta fi rawan kai. "ke ma kinsan yana sonki kawai don ya fiye ka'idoji ne amma kawai ki kiyaye shike nan. Allahu ya nuna mana" faɗin wacce aka kira da faɗima. Hankalin Halima ya kasu kashi kashi sai take ji kamar Hammad ɗin ta ne, wani zuciyar na faɗi mata ai Hammad ba ɗaya bane a duniya. Bata san sanda bakinta ya fara furta "kar dai a ce ke ce amaryan grand frère (yaya namiji)". Nan duk suka juyo suna kallonta. Murmushi ta sakar musu sai ta ɗauko littafin da ahlin ɗinsu Hammad sukayi wai barka da sallah ta ce "ko ba wannan bane angon naki grande soeur (yaya mace)" Nan ma fuskarta cike yake da murmushi yayin da ranta ke rokon Allah kar ya kasance Hammad ɗin ta. "kinga irinta ko Sadiya, da rashin mutunci mukayi da kin kwan ciki, yi hakuri kanwarmu . Ya gida ya su mama" "Lafiya lau, gashi har na zo in da zan sauka, zan faɗa masa mun haɗu da pretty damsel ɗinsa" Ta faɗi tana dariyan da yafi kuka ciwo. Tana sauka ta hau kabu-kabu wanda shi ya karasa da ita gida. Jinta take kamar mahaukaciya, haukan ma sabon shiga. Ko da ta isa ɗaki ta shiga Direct, sai da ta tuɓe ya rage daga ita sai breziya da siket sannan ta kira shi a waya. "Akan me zaki je kina min bincike Halima, ko an ce miki sadiya bata san duk yan gidanmu bane" Ya tare ta da shi kafin ya amsa gaisuwanta. "Ai ban san cewa gidanku ɗaya ba sai yanzu. Yanzu Hammad sakayar da zaka min ke nan" Ta faɗi a raunane, idanunta na fitar da kwalla. Zuciyarta kamar ta fitar dashi saboda azaba kunan da yake mata. "ki fahimce ni Halima, ban taɓa miki Alkawarin zan aure ki ba, ina sonki mais (but) kin san hali na, hakan yasa kike zargi na kuma kike bincike na, bafa muyi aure ba kenan. Kuma kinga sadiya shekarunta goma sha shida ne kawai, zan iya zama in tsara ta yanda nake so" Ya karasa yana dariya. Halima da jikinta ke karkarwa burinta ta tashi daga muguwar MAFARKIN da take tayi kokarin faɗin "Amma Hammad.... " bata kai aya ba ya katse ta da ban hakuri. " Don Allah Halima kiyi min rai s'il vous plaît (please) kada wannan ya taɓa soyayyar mu kinji Don Allah " bata karasa jinsa ba tayi hurgi da wayar ta kara rushewa da kuka wanda ya fi jini ciwo. Hey sweetiesssss da fatan kunyi sallah lfy. Keep voting and commenting plssss Mafarin Mafarki 1.1K 67 5 by Ummu-abdoul Tsabagen kukan da tayi ya haifar mata da matsanancin ciwon kai. Tun da ta shige ɗaki ba ta fito ba sai faɗi ma mommansu zazzaɓi take yi. Washe gari ma haka ta yini sukuku, mamaki ya cika ta rashin ganin kiran Hammad, zuciyar ta guda na ingiza ta kan cewa ta kira taji ko lafiya yayin da ɓangaren zuciyarta mafi gaskiya na faɗi mata ta kyale shi. Waya ta ɗauka ta kira Abdoul saboda amincin da ke tsakanin su yasa basa kyashin faɗi ma junansu sirrin rayuwarsu. Saurarenta yayi cikin natsuwa da fahimta. Sannan ya ce "ki ɗaure ki fitar da shi a ranki tun a yau, kar ki saurare shi, zafin da zaki ji kaɗan ne akan sai gaba ki sami ɓacin ran da yafi wannan. Ina office yanzu za muyi magana in na koma gida" Ta gode masa kana ta ɗan yunkura don cire damuwa a ranta. Haj. Mas'ouda na ankare da duk wani take takenta amma ta basar. Cikin lokaci kankani ta zabge ta rame, fara'anta ya zama ragagge ga yawan tunani. A lallaɓe ta kammala jarabawan zangonnan ta tafi Zindar. Abdoul kaɗai yasan matsalarta hakan ya sa shakuwa fiye da farkon haɗuwansu. Bakin cikinsa ɗaya sanda suka haɗu tana tare da Hammad da babu abinda zai hana masa aurenta. Ga shi saura wata bakwai a ɗaura aurensu da Agaysha. Kaifin basiranta da hankalinta yasa yake saka ta kan gaba a dukkan lamuransa don duk shawarar da zata bashi matukar zai yi amfani da ita toh akwai nasara. *** Tana Zindar aka ɗaura auren Abdoul da Agaysha. Duk wani shiri na biki akan shawaran Halima akayi. Halartan bikin ne kawai batayi ba amma ko a ranar sunyi waya yafi sau goma, yana lallaɓata da ban hakuri akan matsalarta da Hammad. Amarya Agaysha ta tare a gidanta da ke Jeune cadre wanda ya sha gyara kasancewarta yar gidan masu kuɗi.. Agaysha Iggalher fara ce mai jiki, tana da tsawo bata da wani diri amma baza'a kira ta a chushe ba, yar asalin agadez ce buzuwa ce, amma ta taso a Dosso, iyayenta masu kuɗi ne kuma yan boko. Sun haɗu da Abdoul ta hannun yayanta sidi inda da farko ta ki amincewa da shi kasancewarsa talaka, amma tunda ya samu aiki ta makale masa. Aurensa bai sa shakuwarsu ta ragu ba sai ma a ce ta karu don duk wanda yake tare da ita ya san alakarta da Abdoul, wanda bai san danginsu ba takan ce masa yayanta ne, walau uwa ɗaya ko tubashinta. Tayi samari kala kala amma ba wanda ta yi soyayyar wata uku da shi ba gani take duk mayaudara ne. "Na rasa me ke damun matan adarawa (hausawa) da buzaye sam basu san wani abu kula da miji ba, duk soyayyar da za'a maka kafin ayi aure ne sama they are not caring😡" Abdoul Ya turo ma Halima ta bbm ɗin da suka maida hanyar hiran su, hakan yasa suka rage 2go. Ɗan Aljani dariya haɗe da ɗaga hannun ba ruwa na ta tura masa "Allah ba wasa ba, kin san aboki na bayarben nan da wannan inyamurin wallahi har ban son zuwa gidansu, kinga dai ba Kasar su suke ba amma matan basu yi kyashin kula da su ba" Ya sake tura mata, bata so ta shiga harkan iyalinsa, don bata so ayi mata. Amma ta dake ta amsa da "Allah GF (grand frere) matanmu na kokari wajen kula sai dai abinda ba'a rasa ba, aure ɗan hakuri ne" Ta tura haɗe da aljani mai murmushi "Ni wallahi har danasanin aure yanzu nake, kai aure dama haka yake, mace bazata natsu ta kula da kai ba wai kar ka raina ta, na yaushe kuma. Shi yasa mazan Hausawa da buzaye suka gwanance a Aron hannu " Sai da tayi dariya ma'ishi kasancewa ta san ya tsani kalmar nan ta aron hannu da gayu ke amfani dashi mai makon zina. "dariya ta kike wai, kin san dai a nahiyar mu anan ba Kasashen fa suke da Al'ada iri ɗaya kamar Nijar da arewacin Nijeriya. Toh kina isa arewacin Nijeriya zaki ga korafin iri ɗaya ne, matan banda rashin kula har da da rashin biyayya suna tunanin gyaran gado ne kawai aure, mstwww " Nan ma dai dariyar ta sake bin shi da shi, tana mamakin sa. Toh ai ba duka aka taru aka zama ɗaya ba. Don kuwa yanda ta tsara rayuwar Aurenta bata tsammanin za'a samu matsala da ita a wannan fannin. Burinta kullum rayuwar aurenta ya zama sanadin shigar ta Aljanna mai babban daraja. Ganin ba ta niyyar bashi haɗin kai balle har ya c faɗa mata matsalarta yasa ya juye hiran zuwa tambayar ta ya zancen karatunta da take shirin kammalawa. Karfe goma na dare yai mata sallama ta sa masa tsiya faɗi take "wajen buzuwa fa zaka kake sallama, ashe suna da rana haka" dariya sukai gaba ɗaya sannan sukai sallama.2012 Zaune take tana kintsa kayanta saboda zata kai ma Haj Mas'ouda ziyara kasancewar ta kammala karatunta na licence na shekaru 3, (kwatankwacin kwalin degree inji yan 9ja) sakamako fito yayi kyau. Wannan zuwan ma baffanta ya sa ta nemi gurbin karatun masters a cewarsa tunda taki aure. Wayarta ce ta fara kuka, kallon number ta yi don ko mutuwa take bazata manta numb nan ba. Kamar bazata ɗaga ba chan dai yana gab da tsinkewa ta ɗaga haɗe da sallama. "meye duniyar ne Halima, ace zaki iya share ni haka. Shekara biyu kenan fa, haba Halima alkawari bai ce haka ba" Ya faɗi yana mai kwantar da murya. " qui est sur la ligne (wanene akan layi) ta faɗi a ɗan fusace duk da ta fahimci muryan. Dariya yayi mai isarsa sannan yace " mon nom est Hammad de agadez (sunana Hammad daga agadez)" Ya faɗi yana dariya. "Au wai kai ne, ni ban gane muryan ba." Nan suka gaisa. "ina takwarata" Ta tambaya "hmmmn hajiyata kinsan mun rabu kuwa" Ya faɗi cikin halin ko in kula. "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Me yayi zafi haka Master" Ta faɗi tana mai dafe kirji kamar yana ganinta "Wallahi bazan iya ba, idanunta sun buɗe da yawa, duk wani hanyar rage ruwa ta san shi, wai yarinyar nan ce ke faɗa min don bana laguda ta toh tana shakkar son da nake ikrarin ina mata" "haba Hammad, yarinya ce fa karama, hakuri zakayi, amma dai da aka tsaida rana sannan zaka ce ka fasa, ka yi hakuri" "yarinya ce karama amma ko ke da kika gama jami'a ba za ki yi abubuwan da take ba, har ɗaga wuya fa ance tana yi." " Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, ni ko ta ɓata wayonta kuma ta kunyata ku, Allah raba mu da zaɓen tumun dare." Ta faɗi tana mai kashe wayar. Cigaba da shirya kayanta tayi sannan ta ɗauki hanyar Niamey Sai chan cikin dare sannan ta labarta ma Abdoul duk inda hankalinsa ya kai a yawa duk sun tashi. Ya rasa meyasa lamuran Halima ke tsayar masa a rai, ko dan tana mutunta shi ne ko menene shi kan shi ya rasa ganewa. Tun daga ranar Halima da Hammad suka fi tif da taya mannewa kafin a ankara shakuwarsu tafi na da. *** Ziyara suka kai birnin Paris na Kasar Faransa. Sun sauka a ɗaya daga cikin otel da suka fi tsada watau RITZ Paris da ke lamba ta 15 Place Vendôme, 75001 Paris. Sunyi wanka, sun rama sallolinsu sannan suka zauna cin abinci. Daga nan kuma suka Lula duniyar da su kaɗai suka san da shi don kawar da gajiya. Basu kai ga isarwa ba yaji saukan ruwa a fuskarsa. A firgice ya farka yana lalube ko idanunsa zai kai ga Halima amma

Chapter 1 of 5