Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jikin nasa amman kuma ya matse ta a jikin sa.

Ido ta lumshe muryar sa mai taushi taji yana fadin
"Kiyi hakuri banyi niyyar na saki kuka ba amman gaskiya na fada miki, damuwa ki tawa ce zan fiki shiga damuwa da gaske nake, ina jin ki tamkar su Najwa a tare dani dan haka dole na damu da damuwar ki, ki daure ki cika min buri na akan ki Maryam."
Ido ta runtse ya dago kanta daga jikinshi yasa hannunshi ya rike fuskata yana duban idota hawaye na zuba, idonshi cikin nata yake kallonta, da sauri ta runtse idonta dan ba zata iya jure kallonshi ba ya sakar mata fuska sannan ya dauko handkerchief ya fara goge mata hawayen fuskar ta sai da ya gama sannan ya amshi jakar ta yace
"Kwalliyar duk ta baci duk da daman ba so nake a gani ba amman dan shafa hoda kadan ba da yawa ba kar maza su kara rikice miki."

Kallon sa take dan a wani lokacin in yai abu mamaki yake bata ta kasa gane ina ya dosa, shima gane yasaki layi yace
"Saboda tsaro fa kar azo a saka miki damuwa."

Kai kawai ta dauke, ya bude jakar ya mika mata hoda ta amsa ta fara shafawa kura mata ido, har ta gama ta juya ta kalle shi, ya saki murmushin sa mai kyau ya juya ta kalli agogo har tara saura, tace
"Yaya lokaci na kurewa fa."

Bai Kalle ta ba duk da yaji dan in ta shine ba wata dinner ganin bai juyowa ba tace
"Yaya."
Ya dago yana kure ta da idon sa yace
"Menene?"

"Yaya dare nayi fa."
"Agogo ya kalla yace
"ko mu koma gida?"
Yadda ya hade rai yasa ta dauke kai kawai, ya gyara zaman sa ya tada motar suka bar wajen. Ko da suka je har ango da amarya sun shiga ana ta biki.



*Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu cika da kyau da imani. Amin*


*Antty*
[11/27, 14:18] Maryam S IndabawaπŸ₯°: ο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 60

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Suna parking ta fara kokarin bude kofar da sauri ya dannan lock ta juyo zatai magana, ganin ba fuska yasa ta koma ta jingina a jikin kujera, sai da ya gama danne dannen sa sannan ya dago yana kallon ta hannu ya saka a aljihu ya zaro yan 500 bandir biyu ya mika mata, amsa tayi tace
"Nagode."

Unlock yayi ya fita itama ta bude ta fita, gaba yai yana tafe tana bin sa a baya, a bakin hall din suka hadu da Tasleem wacce akai mata wata heavy makeup ga shi ta saka wani material mai kyalli an mata gown ta kamata sosai ba mayafi sai yar jaka da waya a hannun ta da hill shoe, tana ganin sa ta taho tana fadin
"Yaya ina ta jiran ka fa."

Kamar ba dashi take ba haka yazo zai shige ta kamo hannun sa ya dago a zafafe da sauri ta saki hannun nasa ya bita da wani bazan kallo, Maryam dai shigewa tayi ta barsu a wajen, tana shiga taga Muhammad zai fito, hanya ta bashi amman sai yaki yabi ya tsaya kallon ta, dagowa tai tana kallon sa tare da kallon bayan ta ko Yaa Aliyu ya shigo, a hankali tace
"Ina zaka?"

"Nemo ki mana. Ina ta kira bakya dauka."
Wayar ta kalla tace
"Tana silent ne."

"Wa ya kawo ki to?"
"Yaya ne."

"Oh ya dawo ne?"
Kai kawai ta gyada ta fara tafiya yabi ta yana fadin
"Amman kinyi kyau my love."

"Ka fini yin kyau in Jawahir ne?"
"Naganta tare da dayan Yayan nan naki."

"Oh Yaa Farouk, kace sun hadu."
Ta karasa wajen Najwa da ta dauke kai tace
"Haba Amatya ya da bata rai."

"Wai sai yanzu zaki zo "
"To kema yaushe kika zo din."

"Au haka ma zaki ce ko?"
"To ya zanyi Yaya ne ya tsaya harkar gaban sa."

"Meyasa kika zauna ya kawo ki ai kinsan halin sa."
"Kinga mu bar maganar nan, amman fa kinyi kyau."

Ta kalli Abdul tace
"Ango kunsha kyau fa."
"Yace ai fushi muke. Ta hade hannaye tace
Tuba nake, sannan ta bar wajen tana murmushi, wajen su Jawahir taje suka gaisa sannan taje ta samu Momy da Ummi daga nan ta samu waje ta zauna tana mai daukar wayar ta, ta fara danne danne akai akai tana dagowa tana kallon yadda ake gudanar da abubuwa
"Amarya ta."

Ya fada cikin cool voice din sa ya zauna tai murmushi kawai yace
"Wallahi Baby kinyi kyau kamar na hadiye ki."
Murmushi ta saki, tana yin kasa da kan ta ya daga hannu ya kira MC ya karaso yace
"Ina son fili amare dani da tawa amaryar."

"An gama ranka ya dade."
Ya fada yana barin wajen, yan 1k ya dire mata a gaban ta har guda uku Maryam ta dago tana fadin
"Na menene?"
"Liki."

"Yaya ya bani fa."
"Wannan na mijin ki ne ba yaya ba."
Zatai magana ya daura hannunsa akan lips din sa yace
"Ba kyau mai da hannun kyauta baya."

"Amman ai sunyi...."
"Dauki kawai."
Dai dai lokacin da MC ya fara kiran suna Muhammad Auwal akan ya fito ango da amarya na jiran sa, kirari ya farai masa Muhammad ya mike ya juyo ya kalli Maryam da bata da alamar mikewa, yace
"Dear!"

Dagowa tai ya kafe ta da idanun sa yace
"Taso mana."
Ba yadda zatai ta mike yai gaba tabi bayan sa, ganin yai mata nisa yasa ya tsaya har ta karaso suka jera in kagansu sai sun baka sha'awa dan kuwa sun dace da juna, amarya a tsaye da ango suka hau stage din dai dai shigowar Aliyu ya hange ta a saman stage tana liki wani abu yaji ya tsaya masa a makoshi bai kara shiga damuwa ba sai da yaga Muhammad a gefen ta ji yai kamar ya bar hall din amman ya samu waje ya zauna tare da zaro wayar sa yana danne danne, hakika bai so zuwa dinner ba dan shi bai fiya zuwa biki ba in ba daurin aure ba amman dan ya kula da ita yasa yazo sai dai zuwan na neman ya sa masa hawan jini, in ya dago yaga yadda Muhammad yake mata magana kasa kasa yana mata liki ji yake kamar ya tashi yaje ya janye ta, sun jima Muhammad na barin kudi sai kirari MC yake masa sai da Maryam ta bar wajen sannan yabi bayan ta, zuciyar Aliyu kamar ta buga bayan sun zauna aka kai musu lemo ya bude mata ya mika mata ta dago ta kalle shi ta amsa tana murmushi ya kufala duk a kan idon Aliyu da ya kasa daina kallon su, kiran yaye da kannen amarya akai wannan yasa su Anty Asiya duk suka fita, Farouk ma ya fita ganin ba Aliyu da Maryam ya je ya kamo hannun Aliyu da kyar ya kai shi kan stage ai kuwa kannen sa duk suka hau zuba masa kudi, Maryam ya hango yaje ya kamo ta suka hau stage din, rafers din yan 1k Aliyu ya balle ya dinga zubawa kannen sa, suma suna masa liki, sauran suna rawa, Maryam dake gefe a tsaye ba abinda take ya juya yana zubawa kudi take camera man da mc suka hau kirari tare da fadin
"Yayan ango da tashi amaryar Allah ya kara dankon soyayya."

Aliyu kuwa sam idon sa ya rufe sai da ya juye mata su tas sannan ya bar wajen, juyawa tai zata bar wajen Najwa ta kamo hannun ta tana dan jujjuga ta Maryam bata iya rawa ba hasalima kunya take ji, a haka ta koma wajen zaman ta duk bata da nutsuwa akai akai tana dagowa tana kallon Aliyu da ya hade rai kamar bai dariya.

Iyayen amarya da aka kira shi yasa Maryam fita ta hau yiwa su Ummi liki suma suna mata, a haka kai musu picture gaba dagan su. Har karfe sha dayan dare shagali ake sha, Maryam na zaune ita da Muhammad da sai hira yake bata tana dariya dan Muhammad ya iya daukewa mutum kewa da sasu nishadi, Aliyu dake hangen su yazo wuya, a fusace ya mike ya karaso inda suke tana ganin sa ta dauke kai yace
"Tashi muje."

"Yaya ba fa a tashi ba."
Wata tsawa ya daka mata wannan yasa ta mike da sauri tayi waje ya bi bayan ta har bakin hall din ya kalle ta yace
"Shige muje."

"Yaya ni zan taho da su Ummi wallahi ba zan iya zama ni kadai a gida ba."
Bai kula ta ba ya nufi wajen da yai parking tabi bayan sa kamar zatai kuka ya bude mota ya nuna mata, ta shiga ya rufe ya juya ya bar wajen da kallo ta bishi a tunanin ta lokacin zai fito amman me tin tana jiran fitowar sa har ta fara jin tsoro, wayar ta ta dauka ta fara kiran layin Basma tana dauka tace
"Ina Yaya?"

"Gashi can."
"Me yake?"

"Danne danne ke kina ina?"
"Shikenan."
Ta kashe wayar ta fara neman layin sa ko ya manta da ya barta a mota ne amman har ta gama ringing yana gani bai dauka ba sai da ta kira sau uku amman bai dauka ba kashe wayar tayi dan haushi shi yana can yazo ya kulle ta anan wai dan me yake mata haka ne yayiwa su Basma mana sai ita da ya raina. Kuka ta saki a haka wanda ta kudundune waje daya, bata san lokacin da bacci ya dauke ta ba. Sha biyu saura su Ummi suka tafi wanda sha biyu nayi Aliyu ya hau kada kan kannen sa duk sai da ya ga tafiyar su har amarya sannan yayo wajen motar sa, lokacin sha biyu da rabi tuni Maryam tai nisa a baccin ta, mota ya bude wanda yasa Maryam ta bude ido da sauri tana ganin ta a inda take ta saki ihu, da sauri ya rufe mata baki yana fadin
"Menene haka kiyi addu'a sai ihu ko?"

Ajiyar ta sauke ya kunna wutar motar duk da ta ganshi amman jikin ta sai rawa yake.

Ganin a tsorace take yasa ya kamo hannun ta yana murzawa a hankali yace
"Is ok am sorry kinji."
Idon ta lumshe ya saki hannun ta yace
"Me dazu nace miki?"

Yadda ya daure fuska sai da ya bata tsoro tai saurin yin kasa da kan ta yace
"Wato ke bakya jin magana ko?"
Shiru tayi ya girgiza kai zai magana wayar ta, ta soma ringing shi ya dauki wayar yana duban sunan ganin Ummi ce yasa ya kai kunnen sa yace
"Ummi."

Tace
"Kuna tare?"
"Eh Ummi yanzu zamu taho na tsaya naga kowa ya tafi ne shiyasa."

"To shikenan sai kun karaso."
Ta kashe wayar ya mika mata yace
"Ummi taga dare yayi."
Ya fara yana duba agogo daya saura kwata ya tada mota suka har wajen a hankali yake tafiya kamar wanda bai son tukin bai damu da ganin dare yayi ba ita dai Maryam tana jikin kujera tana ganin ikon Allah kamar ba zasu ba a haka suka karasa gida.


A compound din Ummi yai parking zata bude taji a rufe take ta juyo ta kalle shi kamar bai san me take nufi ba ya dage mata gira, ta kalli kofar tace
"Yaya bacci nake ji."

"Shine bana so kiyi kamar yadda nima ba zan ba."
Ya fada yaba danne-dannen waya, dagowa tai ta kalle shi tace
"To saboda me?"
Leben sa ya cije tace
"Dan Allah ka buden wallahi bacci nake ji."

Kamar ba zai bude ba sai ya bude da sauri ta fice a motar tai ciki, kan ya fito ya rufe har ta haye sama, wanka tayi tana fitowa ta fada saman gado bacci take ji amman sai sam ta kasa da ta rufe sai taga fuskar Aliyu wanda a haka ta dinga juyi har wajen biyu da wani abu, can wajen biyu da rabi kirshirwa ta ishe ta, ta mike ta bude firij din dakin ta sam ba ruwa, sauka tayi kasa ta shiga kitchen dan dauko ruwa, fitilar falon a kashe sai hasken fitilin waje da ya leko, tana shiga ta dauka ta samu ta zauna tana sha, sai da ta sha sannan ta mike rike da guda daya, a bakin kofa taci karo da mutum tayi baya kamar zata fadi, da sauri ya taro ta, baki ta bude da nufin yin ihu da sauri ya daura hannun sa akan bakin ta, ido ta zaro jin ta rumgume jikin mutum, a hankali ya raba jikin su yana kallon ta, ganin Yaa Aliyu ne yasa ta saki kuka dan sosai ta tsorata bata taba tsammanin ganin mutum a lokacin ba, kirjin ta in ban da bugawa ba abinda yake.

Hannun ta ya kamo ya dan murza alamar rarrashi, yace
"Ya isa to menene na kukan meyasa da kika sauko baki kunna fitilar ba, me ma ya fito dake da daren nan, me ya hanaki bacci?"
Hannun ta, ta janye tayi hanyar bene da sauri ya kamo ta wanda hakan yasa ta fado jikin sa, matse ta yai a jikin sa yana kallon fuskar ta.

Hawaye ne ke bin kuncin nata, hannu yasa yana goge hawayen dake bin kumatun ta, a hankali cikin muryar sa mai dadi yace
"Ya isa to kinji am sorry daina kukan kinji."
Haka yai ta lallashin ta har tai shiru sannan ya sake ta ta hau sama tana shiga ta fada saman gado tare da lulluba addu'a tayi sannan ta hau tunanin abun da ya faru bata jima ba bacci ya dauke ta.


*
Washe gari da wuri ta tafi gidan Sitti dan kar Aliyu ya hanata fita, ranar lunching akai a wani event centre, tare Maryam da Najwa suka tafi makeup akai musu, karfe biyar aka gamai musu, ana gamawa Abdul da Muhammad suka daukesu, Maryam na gaba, ita da Muhammad, Abdul da Najwa ba baya, a haka suka tafi wajen lunching din ranar sakayau taji ta saboda babu Aliyu amman ita kuma taji kewar sa.

Yana zaune a falo yana danne danne a waya Ummi suka sauko da Yaya zasu tafi wajen Lunching din dagowa yai yana fadin
"Lafiya zakuyi?"

"Eh."
Kallon saman yayi yace
"Ina Maryam din?"

"Ai su sun jima da tafiya."
Da sauri ya mike yana fadin
"Bari na shirya sai na ajiye ku."
Da kallo suka bishi, ya shige daki bai jima ba ya fito sanye da dogon wando na jean da orange kalar riga, yace
"Muje."
Sukabi bayan sa, ya shiga suka bar wajen. Karfe shida saura sukaje wajen suka sauka ya shige, Maryam na ciki, cikin kawayen ta ana ta shagali wayar ta ta fara ringing tana dubawa taga sunan Aliyu, gabanta ne yai wata mummunan faduwa ta dauka tana sallama amsawa yayi yace
"ina jiranki a waje."
Yana fada ya kashe wayar sa, shiru tayi tana nazari Jawahir ta dafa ta tace
"Menene?"

"Yaya ne wai yana waje."
"To kije kiji mana."

Mikewa tayi ta nufi barin wajen fita tayi tana dube duben ta ina zata hango shi, tana tsaye taji ana mata horn, juyawa tayi ta karasa wajen motar, kofar motar ya bude ta shiga ta zauna yace
"Rufe kofar."

Tana rufewa yaja motar ya bar wajen, wayar ta ce ta fara kuka tana dubawa taga Muhammad ne dauka tayi takai kunnen ta yace
"Ina kika je naga fitar ki na biyo ki bakya nan."

Wayarta ya amsa, ya kashe, juyowa tayi tana kallon sa ya hade rai ya ajiye wayar, wata unguwa suka shiga wacce ta gama haduwa duk zagayen ta a garin bata taba zuwan ta ba ta hadu sosai, bakin wani katon gida mai kyau suka karasa yai horn mai gadi ya bude suka shiga, parking yai ya fito ya rufe kofar ya zagaya ya bude mata, ta sauko tabi bayan sa ya nufi kofar wacce take da tumbprint din sa, hannu ya saka a kofar ta bude suka shiga wani hadadden falo ne wanda yake dauke da kujeru orange da lemon kala, haka labulaye da center carpet sai kamshi dakin yake ga wani sanyi mai dadi, kujera ya samu ya zauna ya kalle ta yace
"Wa yasa ai miki wannan kwalliyar?"

Shiru tayi yace
"Ba magana nake ba?"
"Sitti ce tace sai nayi."

Mikewa yayi ya dauko lemo a firij, ya zauna yana kallo TV yana shan coke kallo ta yayi yace
"Zauna man."

Kamar ba zata zauna ba ta dan zauna a gefen kujerar ta zauna ya dauki waya yana dan danne danne a haka ya gama shan lemon ya dan shafa cikin sa sannan ya dago yace
"Yunwa nake ji, ki shiga ki samar min wani abunda zan ci."

Mikewa tai tace
"A ina zan dafa maka?"
Ki shiga waccan kofar akwai wani corridor ki bi nan ne kitchen."
Ta juya ta shiga, wani falo ta kara shiga wanda yafi wanda suka zauna kyau, tana mamakin gidan wanene nan, corridor tayi ta shiga kitchen din, yai kyau, babu ce kawai babu, dan yai kyau a gyare wajen yake ta bude firij taga akwai wasu kayan amfani, kaza ta dauka ta wanke ta daura akan wuta ta dauki dankali ta yanka ta daura masa farar taliya da miyar kaji da dankalin turawa tana gamawa ana kiran magariba ta fito ta tada baya nan a kitchen tai alwala ta fito a tada sallah a falo tana zaune ya shigo ta dauko masa abincin ya dauka ya fara ci, ya dago ya kalle ta yace
"Ke bazaki ci ba?"

Kai ta girgiza yace
"To."
Ya cigaba da cin abincin sa sai da ya gama sannan ya zauna yana kallon ta, ta dago tace
"Yaya don Allah ka kai ni gida."

Banza yai mata har sai wajen bakwa da rabi sannan ya tashi yace
"Muje."
Ta mike yabi bayansa suka shiga mota, yana zuwa gida ta bude mota ta fita, zata wuce yace
"Ungo wayar ki."

Ta juyo ta amsa ta bar wajen da sauri ranta a matukar bace, tana shiga ta fara neman layin Farouk yana dauka tace
"Yaya kana ina?"
"Ina gidan Sitti."

"Please kazo ka dauke ni Yaya anan zan kwana."
"Meyasa kika koma gida?"

"To ba Yaya bane."
Tai magana kamar zatai kuka yace
"To gani nan zuwa."
Ya kashe waya sallah kawai tayi Farouk ya kira ta, tai wa Ummi sallma ta tafi.

Suna zuwa ta shiga dakin Najwa yan matan amarya ne a wajen Najwa na zaune kan sallaya ta karasa ta zauna, Najwa ta kalle ta tace
"Ina kika je ne?"
"Ba Yaya bane ya dauke ni kawai."

"Wane Yayan?"
"Wanne kuwa? Yaya dai."

"Wai shi Yaya mai yake damun sa ne."
"Uhmm."

"Ace ba zai barki ki sake ba, haba kina da saurayi amman yabi ya kankane?"
Wata kawar Najwa Hauwa tace
"Amman ba thesame father suke ba ko?"

"Yes cousin ne Yaya na fa."
"Ah son ta yake amman ko?"

Wani kallo Maryam ta bi Hauwa dashi da mamaki tace
"Yaya ne fa... Yayana ne shi"
Hauwa tayi dariya sosai tace
"Baya takura miki akan samari?"

"Uhmm ko waya baya so tayi dasu ba, ya hanata kula su sam."
Najwa ta fada, Hauwa ta kuma dariya tace
"Wai amman kinji Yaya ne, to haka kawai bazai dinga hana ki waya da samari yana kwace maki waya, idan babu wani abu a kasa"



*Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa muyi kyakhawan karshe. Amin*



*Antty*
[11/28, 13:42] Maryam S IndabawaπŸ₯°: πŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 61

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



Maryam ta hade rai, Hauwa tai dariya, Maryam tace
"Kai ke wallahi baki san Yaya bane ko ke bai miki haka ba?"
Ta fada tana mai da tambayar kan Najwa.

"Ya min amman ba kamar naki ba."
"To ai ni dan muna tare ne."

"Uhmm cewa fa yayi kar ta tsaya kula samari ta riki karatu dan Allah kalli wannan budurwa mai kyau wai ita za a cewa kar ta kula samari."
Dariya suka sheke da ita Basma tace
"Uhmm kalli fa yadda Affan ya rikice daga ganin ta."

Dariya Hauwa tayi tace
"Tabb, lallai Yaya Aliyu"
Maryam dai sai kallonsu take don bata san me ya basu dariya ba, Hauwa tace
"Toh wallahi son ki yake...."

Maryam ta zaro ido ta koma baya da sauri tace
"Don Allah ki daina cewa haka plsease, wallahi Yaya na ne fa, ke ai Najwa kinsan Yaya fa"

Najwa tayi wani murmushi tace
"Tinda ba ciki daya kuka fito ba ai an gama Maryam, ki daina tinda manyan yan soyayya suka gane to da wata a kasa fa. Ni daman na fara zargin sa dan yadda da kika zo hutun nan ya adabe mu da zarya har sai da kika koma sai muyi sati nawa bamu gansa ba amman kina nan kullum yana nan kuma bai son ya barki ki je ko ina ke kulawar Yayan tai yawa. Yadda Yaya yake miki ma ai bai mana ba, ke dai ce ban san lokacin da zaki yi wayo har ki fahimci inda ya dosa, wai Yaya ne. A'a ba Yaya ba..."

lokaci daya hankalin Maryam ya tashi wai Yaya son ta yake, ji tayi ta kasa nutsuwa sai kara tabbatar wa suke Hauwa na kara zuga Najwa, Maryam tace
"Wallahi ku daina cewa haka ba kyau, ni ai Yaya yafi karfi na wallahi ba ruwan sa."

Dariya kawai Hauwa take don Maryam tayi mugun bata dariya, haushi suka bata ta mike ta bar dakin, dakin Sitti taje ta zauna kan gado maganganunsu na mata yawo a kai, Sitti ce ta shigo ta zauna a gefen ta tace
"A'ah Yaushe kika dawo."

"Yanzu."
Ta fada tana kwanciyya akan gado, Sitti tace
"Meyake damun ki?"

"Ba komai Sitti bacci nake ji."
"To kinci abinci ne?"
Kai ta girgiza tace
"Na koshi."

Bandaki ta shiga tai wanka ta fito ta saka kayan bacci a jikin ta ta kwanta akan gadon Sitti.

*
Washe gari yini da safe duk yan mata na dakin Najwa, Maryam kuwa na dakin Sitti kwance Najwa tayi tayi ta fito taki dan tin jiya bata kara komawa wajen su ba Basma ce zaune suna hira jefi jefi, wayar Maryam ce tai kara ta dauka ta kai kunnen ta tace
"Asslamau alaikum."
"Wa'alaikum salam."

"Ya kk ya gida?"
"Alhamdulillah."

"Jiya kuma sai kika gudu."
"Kai nane yake ciwo."

"Ayyah ya kike ji yanzu?"
"Ya daina."
"To sannu ya anjima fa? Nazo na kai ki?"

Kai ta gyada tace
"To in mun shirya zan maka magana."
"Shikenan sai anjima."

Sukai sallama, ta kashe wayar, Basma tace
"Wai da Muhammad za ayi ne? Affan na damu na fa."

"Ke kyale wani Affan dan Allah."
"Uhmm shikenan."
Ta koma ta kwanta.


Biyar har an fara kwashe yan tafiya wajen yinin bikin sauran yan matan suna waje suna jiran motoci, yau Maryam bata bi Najwa ba dan tin jiya ma bataje wajen ta ba da zasu tafi makeup tazo su tafi amman taki tace ba inda zata.

Biyar da rabi ta fito zuwa compound din gidan Sitti sanye take da less cream kala wanda akaiwa ado da coffee, ita tai kwalliyar ta kuma sosai tai kyau batai wani shafe shafe mai yawa ba amman ita kanta sai da ta kalli kanta ta kuma kalla dan tayi kyau, coffe kalar mayafi ta yafa, da wani half cover takalmi da jaka, sai dankunne da sarka da ta saka golding sosai tai kyau kamar ita ce amaryar.

Suna tsaye ita da wasu yan mata motar Muhammad ta karaso, wayar ta ce ta hau kara ta zata shine tana dubawa taga Najwa ce dauka tayi tace
"Kina gida ne?"

"Eh ke kina ina?"
"Mun fito yanzu zamu karaso akwai wata friend dina da zasu karaso yanzu please ki samu wani ya kawo mana su."

"Ok."
Ta kashe waya, Muhammad ne ya fito ya karaso, yana murmushi, ya karaso yace
"Amaryar Muhammad."

Tai kasa da kai yace
"Gaskiya ina kishi kar wani ya kalle min kyakyawar matata kinga yadda kikai kyau kuwa?"
"Kai Muhammad kai dai maganar ka kenan."

"Ai gaskiya ce shiyasa nake nanatawa kullum."
Murmushi tayi yace
"Zamu iya tafiya?"

Kai ta girgiza tace
"Akwai wasu da zan baka ka kai mana su, in Yaa Farouk bai zo ba sai ka dawo ka dauken amman yanzu please dear ka kaisu."

"An gama ranki ya dade suna ina?"
Nan ta shiga ta kira su, suka zo suka tafi a bakin mota yace
"Zan dawo fa."

Tace
"Toh."
wata hadaddiyar mota ta kunno kai harabar gidan duk mutanen dake gurin sun raja'a ga ganin motar, baka ce wuluk haka gilashin ta, kai ta dauke zata juya, jakarta ce ta fadi ta durkusa ta dauko tana juyowa taga Yaya Aliyu ya fito cikin wata shadda yar gaske sai maiko take, yayi wani irin kyau wanda duk wanda ya ganshi sai ya kyasa.

Idon 'yan mata kuwa kamar ya fado dan kallon da suke masa, ta ganban ta yazo ya wuce ya shiga dakin Sitti bai jima ba ya fito, tana tsaye suna magana da wasu yan mata ta kai su wajen wata mota aka zuba su kenan ta juyo suka hada ido kai ta dauke ta nufi cikin gida wayar ta ce ta hau kara tana duba taga Aliyu ne

Please Login or Register in order to submit comment