ai naje duba safna duk bamu haduba
Dr hanna tace ok Allah ya kaimu bye
Ahj Saddam tin bayan futar dansa yarikice yashiga wani hali kusan wuni yayi yanata saka da warwara dana sani da nadama kawai yake yana fadin dama dai dama dai da duk haka bata FARUBA
Allah yasa zai amfanar kuma ya gamsar daku LUV U ALL
07033524044
[1/31, 8:40 AM] SARATU: _*🍂BIYU BABU…!🍂*_
_SAMU DA RASHI…_
🍂🍂🍂
🍂🍂
🍂
_*AɭKAɭAMƖŊ✍:Saɾatų mųŋχaɭɩ*_
_*(AMSAR💕)*_
_watpadd @ Ssaratu75…_
*ɖҽɖɩcatҽɖ tɷ:AUNTY ZALY MMN AHMAD YOLA*
*🅿_____3*
_*Sadaukarwar page din farko nakune FADHILA NURADDIN and SIS HAFNAN,you are indeed a gift to evry1 dat meet you and I'm glad dat i met u,Allah yabar zaman tare💕*_
🌲🥀💦💦💦💦🥀🥀
💦💦💦🌲
____________📖AHJ SADDAM
Dan asalalin gwaram ne, mahaifinsa malam Abbas Wanda akafi sani da MlmAbashea,
Mahay fiyarsa safiya,
Wadda ita kadai ce matarsa
Suna da yaya 3hyhuwar ta tafari yan biyune duk Mata
Sai na3
Wato Saddam amma ana kiransa da gambo
Allah yayiwa iyayen sadam da yayyensa rasuwa, a wata rana tasanadin wutar lantarki wato Nefa
Wanda hakan yasa suka rasa rasuwar su, kasan cewar twins din dakin su yana kallon na iyayen, duk acikin palon
Saddam wanda nasa dakin yana farkon shigowa stakar gida
Hakan yasa Allah yaja kwanansa
Lokacin shekararsa 11
Yayan mahyfinsa wato baffa Akilu shiya taho dashi birnir kano ranar sadakar arbain
Baffa Akilu mutum ne mai mutukar kulada yara daga kan bare zuwa jininsa
Baffa Akilu yana daga cikin mutanen da Allah ya jarabta da rashin Aure
Baffa Akilu ya kasance akarkashin wani uban gidansa dake a kasuwar kwari mai arxiki daidai kwargwado ga karamci da tausayi wato Alhj Alkasim
Ahj alkasim yayi mutuqar murna ganin mlm Akilu tafe da dansa
Wanda shiya bashi shawarar ya daukoshi koba komai yaringa taima kamasa
Babu irin nasihar da Alhj Alkasim baya yiwa mlm Akilu akan yaje yasamu hutu yakai lokacin da xaihuta
Amma inaaa
Mlm Akilu yace yafiso ko mutuwa taxo tariskeshi yana kan Neman halak
Ahj Alqasim ya kara yiwa mlm Akilu ta a xiyya
Yakuma yiwa gambo wato Saddam
Take yaji yaron yashiga ransa hakan yasa yamasa nasiha mai sosa rai
Kasan cewar Ahj Alkasim bashida da namiji
Hakan yasa yaja Saddam ajiki yadauki duk wata dawai niyar karatunsa da komai narayuwa
Domin kullum burinsa ya kyau tatawa nakasa dashi, bare yanxu daya samu maraya, gani yake yayi babbar sa'a
Hakan yasa yabawa Ahj Akilu bq
Surunga kwana shida dansa Saddam
Daxarar Saddam yataso daga schll zaisa uniform yashiga Cikin gida ya karbi abinci
Matar Alhj Alkasim kullum saita masa gori
Kullum da kalar gorinda takemasa
Saddam tinyana jinzafi yana kuka harya saba
Saddam daya gama cin Abinci xai dauko bag dinsa yatafi islamiyya
Daan tashi xai shirya ya dauko kekensa yabi baffa kasuwa
Yana taima kawa baffan nasa da shara hada kaya da mikasu ga ragowar shagunan Alhj Alkasim
Babu irin tijarar da matar Alhj Alkasim ba tayi masaba akan baxai kawo mata stintattun baki gida ba
Amma Alhj Alkasim yayi burus daita kuma yasa takum kumi akan duk wanda wayula kantasu saiya hukun tashi
Hakan yasa matarsa ta sanyawa kanta lis lama ta hakura amma taciki na ciki
Dan tasan halin Ahj astaye yake babu wanda ya isa yastallaka dokarsa
Tana mutukar kyamar Saddam
Ba tason taga yayan ta suna nuna kulawarsu akansa ko suce agidansu yake
Musamman yadda taga umma tana shish shige masa
Musamman idan takasa yin assignment tadinga binsa tana magiya
Hakan ba karamin dadi yakewa Alhj Alkasim ba
Saddam yataso cikin yanayin rayuwa ta abin tausayi
Duk wanda yaganshi kobai san tarihin saba xaiji kawai yau yaga kalar tausayi
Duk da yashaku da yayan Ahj Alkasim
Kasan cewar schll dinsu daya haka islamiyya
Tohh
A kwana atashi
Bayan wasu shekaru
Baffa yasa Saddam Agaba yana masa nasiha akan yayiwa Allah yanemo matar aure
Baffa yastufa sosai dan takai baya iya zuwa kasuwa Saboda yanayin girma da larura tayau da gobe
Saddam yatau sayawa baffa yasan kullum zancensa kenan
Saddam karna mutu banga auren kaba
Toh baffa insha Allah acikin shekarar nan xan nemo mata
Saddam kasuwanci yayi nisa shida Alhj Alkasim musam man yanda kowan nensu yake nuna stanstar kulawa tamkar uba da da
A wata jama'a Alhj Alkasim yayi sallama a gidansa
Ba tareda yajira amsaba yashiga kamar yadda yasaba
Alhj sannu daxuwa
Yawwa Alhj Alkasim yafada atakaice
Ungonan
Yamikawa matarsa invitation card
Tace tohh na auren waye?
Alhj Alkasim yace na auren yata umma
Masifa da bala i aranar ba sauki
Har Alhj Alkasim yagaji daji yadau key yana nufin futa
Lalle ma Ahj to wai yaron ubansa waye agarinnan
Alhj Alkasim yace badan kowa bane amma yayi karatu
Karatumme
Mutane dubu nawane su kayi karatu amma basuyi arxikiba tayita sukar balai San ranta
Candai data nisa
Sai tasas sauko damurya tace
Ahj kaifa kadau alqawari yayan ka sai sunyi kararu maizurfi sannan kayi musu aure sannan yaranka ba kalar talaka bane
Cikin stawa Alhj Alkasim yace ya isheki Jabriyya
Nasan nayi alqawari amma yanxu na janyeshi daga kan umma
Kuma wllh ashirye nake
Da duk wacca naga kanta yana rawa saina daste karatun nayi mata aure
Idan yaso intaje gidan mijin tacire kan
Alhj Alkasim afusace yadau key dinsa
Yana isa bakin kofa yaci Karo da yayan sa
Baba sannu
Barka da gida
Yawwa sannunku kundawo lfy
Ai ba sukai ga bashi amsaba sai jisukai tauuu sauti yagau raye falon
Jabriyya tadauke umma da mari tacilla mata invitation tace waye zubair?
Kirasa wanda xaki kula sai mastiyaci dan masiyata
Umma wadda ayashe take akasa stabar karfin marin
Dakyar tayi yinkurin dagowa tace meya yimiki
Jabriyya tace ubanki ne xai daura miki aure dashi rana ita yau
Amugun tashin hankali umma tamike tace waaahh da zubayr
Atake taxube agaban Alhj Alkasim
Babana wai xubayr xaka auramin
Insha Allah fadar Ahj Alkasim
Wayyo Allah babana wllh sau biyu muka taba haduwa
Dan Allah Abba kataima kamin wllh Abba bana sansa
Alhj Alkasim ya rusuna yadago ta yace umma
Kaf cikin samarin dakike tarawa babu Wanda yake da niyyar aurenki duk nabi daya bayan daya naji tabakinsu mayau darane
Zubair kadaine yace min yanada niyya kuma yayi shirin aure
Umma muddin nabarki akan kicigaba da karatu to tabbas xaki kaucewa tarbiyyata
Da duk wani burina
Na shiga Aljannah adalilin Ku yaya mata da Allah yabani
Umma tadago kai araunane
Tace to Abba indai wannan ne burinka to dan Allah Abba karka aura min zubayr
Wllh dana auri zubayr gara ka auran Saddam Abbb takarashe maganar cikin shashshekar kuka takuma kamkame hannun uban dan Allah Abbbbaaaa
Umma bata ankara ba takarajin wani wawan Marin daya gigi tata batasan lokacin da tayi loww tafada jikin Abba ba
Abinka da yan hutu bata taba sanin xabin mariba
Alhj Alkasim ya lura yar tasa tasuma
yan uwanta kuwa tasneem da yaya duk sun raxana astaye
Hawayene kawai ke sintiri afuskarsu
Alhj Alkasim Wanda tun marin datai mata na farko xuciyarsa takai kolo luwa amma ganin yayansa agurin yahanashi aikata komai
Danshi mutumne da bayason yayan sa suga sa insa tsakaninsu ganin yaya mata ne gidan wani xasu Kuma koda maxnane aixasuyi aure Kuma duk abin da sukaga iyayen su sunayi shi zasuyi
Alhj Alkasim yamika hannunsa kan center table yadau ko water bottle
Ahankali Umma tafara sauke ajiyar xuciya
Alhj Alkasim yace ummata kiyi hakuri kinji nariga nagama magana da iyayen zubair bai kamata naxama karamin mutum ba
Tabdijan Nana tace tanata faman huci tanata sintirin kai kawo a falon
Wllh umma ko xaki mutu baxaki auri Saddam ba yaronda bamu san dangin saba aiduk kansu bagwara
barayi ne kawai na uwar stintau
Alhj Alkasim yace nana idan kika sake furta kalma daya
Toh kinfada abakin auren ki
Yajiyo yace umma ina kaunar Saddam kuma nikaina nayi tunani ba adadi akan nabashi daya daga cikin yayana
Toh amma danayi naxari saina ga wllh duk kanku ba wadda ta dace da auren Saddam
Saboda inhar xan aura masa daya daga cikin ku
Toh hakika xai kaiku ga halaka
Nina hango abinda baxaki taba hango waba
Kuma nasan abinda baki saniba ninake tare dashi nasan halinsa ciki da bai
Auren ki dashi baxai taba kaiki ga samun Aljanna ba
Dan haka dan Allah kiyi hakuri kiyarda da babanki baxai miki xaben tumun dare ba
Umma ina kaunar ku ina fata da burin Allah ys kuza memin sadaka tujjariya
Da sauri yatashi yanufi dakin jabriyya
Yana shiga yatarar tanata hada jaka
Alhj Alkasim yace Kinyi akan gaba
Kibar gidannan har saina nemeki
Ya futa ahasale
Alhj Alhj ana magana
ya akai
Ahj baffa Akilu ne yake magana
Ahj Alkasim to muje
Suka gaisa da baffa cikin mutum tajuna kamar yadda suka Saba
Alhj Alkasim yace baffa inasanar dakai daurin auren yata umma ranar jama'a maixuwa insha Allah
Baffa yace habba Alhj amma ai
Alhj Alkasim yakatse maganar baffa
Yace tabbas nasan xakayi tambaya dan nasan kaima kasan kudurina akan yayana
Toh amma kai kanka nasha gaya maka matsalolin umma
Baffa yace hakane Alhj to amma da fatan ba wanda bataso xaka bata ba dan tinda ga nan nake jiyo kukanta
Ahj Alkasim yace E tabbas
Baffa yanisa yace nikaina kullum saina yiwa Saddam fadan ya nemo matar aure
Indai yara sunkai lokaci aiyin auren yafi alkyri
Saidai kuma idan Allah bai kawo ba
Amma Alhj maixai hana kayi hakuri kabata xabin nata
Atake Alhj Alkasim yamike yace baffa ai wani baya auren matar wani
Matar mutum kabarinsa fatan dai Allah yahada kowa da rabon alkyri
Baffa yace Amin
Toh Alhj Allah adawo lafiya Allah yakiyaye
Umma haryanxu tana yashe agun sautin kukanta kwai ne ketashi
Yan uwanta sunyi rarrashin har sungaji
Jabriyya wanda tini tadau hanyar gidan boka qurzumus
Bayanta ajiye kayanta agidan dan yayarta dasuke uba daya
Saddam yashigo da sallama
Baffa ya amsa ya kasuwa
Alhamdllh inji Saddam
Imm baffa kasan abin mamaki
Yanxu inakan hanya umma takirani
Baffa yace inajin ka
Saddam yace yana ta kuka wai Alhj ya kori Mamansu kuma next Friday xai daura mata aure da wani ita kuma tace garani
Baffa kaga shikkenan nahuta Neman wata
Daman nadade nima inason ta kadan kadan amma dana tuna mamansu sai naji nastaneta
Baffa yace nasan xa arina
dan yanxu nan Alhj yafuta daga dakin nan
Bayan danaji hayaniya da koke koke daga cikin gidan sai naga yafuto Afusace
baffa yaga yawa Saddam duk yadda sukayi da Alhj
Ya kara da cewa Saddam nikaina badan halin matar saba Dani zance masa ina Neman Auren yarsa
To tabbas ninasan da abinda Alhj ya hango akanka tabbas akwai
Saddam shawarata kacire umma aranka da rayuwarka
Domin nayiwa Alhj shagube ne akan yabarta taxabi Wanda take so bance masa kaiba kaistaye
Saboda nima baxanso ka hada jini da yayan Alhj Alkasim
Saddam, umma ba xata taba xamowa mace ta alkyri a rayu warkaba sai dai tazamo maka matar kaddara
Saboda umma idonta ya bude sosai tuntana karama
Sannan uwa uba tarbiyyar mahayfi yarta yayi mutukar tasiri arayuwarsu
Dan haka kayi hakuri da ita
Koda kuwa bayan raina
Dama dai ace ""......
..
Tohh fahh......
AMSAR 07033524044
[1/31, 8:42 AM] SARATU: _*🍂BIYU BABU…!🍂*_
_SAMU DA RASHI…_
🍂🍂🍂
🍂🍂
🍂
_*AɭKAɭAMƖŊ✍:Saɾatų mųŋχaɭɩ*_
_*(AMSAR💕)*_
_watpadd @ Ssaratu75…_
*ɖҽɖɩcatҽɖ tɷ:Aunty zaly yola mmn Ahmad*
*🅿_____4*
_*Sadaukarwar page din nan nakine FARIDA AUWAL
Cike da fata da addu'a Allah ya tabbatar mk da Alkyri Allah yasa kicimma burukanki💕*_
🌿🌾🌿🌿🌿🌿🌿🌾🌿🌾🌾
____________📖Baffa yaci gaba da cewa
Dama dai ace acikinsu akwai wacca ta gado halin Alhjne to da sauki
amma duk da haka tasirin uwa yana iya canxa da a kowane lokaci
Sani shi kadai ne ya iya xaman hakuri da jabriyya aduk sanda tayo yaji
Itama jabriyya ananne kadai take sakewa dan tashiga tafuta yadda take so
Tayi nisa matuqa wajan nemarwa yatta mafuta
Ta kowane irin hali
Taje gun wannan matsafi taje gun wancan boka
Gaba dayansu sun Tabbatar mata da cewar Aure bazai tabbataba
Hakan yasa tasakar musu makudan kudade dan cimma burinta
Alhj Alkasim yariga yagama sanin halin matarsa
Muddin suka samu sabani har takai tahada kayanta da niyyar yaji
to tabbas akwai shirin kulla sharri aranta
Hakan yasa tun aranar data tafi ya kudiri niyyar sai yaga bayan asirinta awannan karan
Ta hanyar azkar da sallolin dare addu'oin kariya daga sharrin sihiri da shaidanu
RANA BATA QARYA
Saidai uwar ya taji kunya
Ayaune babban masallacin juma'a dake zoo road wato masallacin murtala ramat
Ya cika da iyayen yaya da waliyyansu
Naa ibi yanabi daki daki
har akaxo kan iyayen zubair dana Amar yarsa UMMA KALTUM
Sautin da umma tajiyo na maroka shiya tabbatar mata da tafaru takare
Aikuwa tasaki wani irin ihu Mecike daban tausayi
Da gudu yan uwanta suka shigo
Sister lfy
Umma kiyi hakuri kidauka kaddarane auren ki da zubayr
Afusace umma tace
kaddara ta galla musu harara kume yasa bata fada kankuba
Kawai danni baba yast
Kafin takarasa wayarta tadau ruri
Tana dubawa taga umman suce takira
Araunane umma ta daga tace
Hajja daman Abba baya sona
Hmmm uwa uwace
Harta manta marin da tasha😀
Jabriyya tace ai kisa ranki a inuwa aure dai Ahj bai isa yahadaki da mastiya ciba
Mai stunstun sama yaci bare yabawa na kasa
Umma tarushe da kuka
tace wayyo Allah na amfa riga anfa daura auren
gasu Baba nan sun dawo takuma rushewa da ihu tana tirje tirje
Jabriyya batasan lokacin da danno wasu makudan ashar ba
Niii
HAJJA niii Alhj zai tozarta
Tayi cilli da wayar ta
Tamike tanata hucin tiririn takaici
Habba hajja yaka mata kidauki duniya da sauki
Ina amfanin rashin mika lamura ga Allah da yadda da qaddara mai kyau ko Mara kyau
Dakata sani... "
Wannan bai shafi shafin rayuwar kaba
Ka wanixo da guntat takin wa azinka
ko dan labcimma baka stomawa
sani yace
tab jahilci yafi hauka wuyar magani
Sani yasan halin hajja tayi nisa
Yana dai kara tinasar daitane kawai saboda hakkin musulunci
Sani ya kasance
shi kadai ne adanginsu hajja Wanda yake iya danne xuciyarsa yazauna da ita
Duk da cewar dangar takarsa da ita tayi nisa amma sanin duk wadanda suka fishi kusanci daita bazasu iya koda kwana daya da ita lafiya ba
hakan yasa yake hakuri daita aduk lokacin da tayo yaji
Fuwww
Hajja tafice tabar sani sororo astaye
Bata nufi ko inaba sai gurin boka qurzumus
Takwa zazzage masa buhun zagi dacin mutunci
Kuma tace dole saiya nemo kudin ta yabata yanxu yanxu
Boka yasan halinta staf zata iya toona masa asiri
Takuma gayawa duk wadanda tayi masu hanyarsa sudaina xuwa
Hakan yasa ya lalo kuda denta yabata
Hajja ta fincike tayi gaba
Boka qurzumus yaga samu yaga rashi
Fadi yake almura bakar bahara😂
Hajja a kan titi taciro wa yarta tahar hada talatsa number yaya
Hello
Hannatu kina jina
Lalle lalle kafin akai umma kitabbata kinsiyo allurar nan tastarin iyali kidirka mata
Koda ukuce
Hankalin hannatu yatashi
Atsorace tace habba hajja wane irin allura planning har guda3takarasa maganar acikin shagwaba
Hajja tace aixatafi aiki
Dan kostau stayi baxan bari yagifta akan umma ta hyhu agidan stiyaba
Kina jina ko
Hanna tace
Hajja inama laifin ayi mata ta2months
Tinda batafa taba hyhu waba wllh akwai mastala
Hajja ta daka mata stawa tace
saidai kiga mastala akanki mai mugun fata
Xakibi umarnina ko kuwa
taka rasa maganar acikin bal bali
Hanna saida tarazana tace to hajja
batajira hajja takara magana ba takaste kiran jikinta duk yayi sanyi
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🌾🌾🌾🌾🌾
Kwana3
Ahj yaware na bikin umma
Yan uwan hajja duk dasu akai komai tamkar basu san bata gidanba
Sunyiwa umma nasiha sosai akan tabi mijinta kuma katta kuskura tayo irin halin mahyfiyarsu
Ahj Alkasim shiyace xai kai umma gidan mijinta da kansa bayan kowa yaje yaga gida anata Addu'a r Alkyri
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
Ahj Alkasim tindaga kofar futowar umma daga gida yake fado mata addu'a tana fada har suka isa mota
Suna xuwa kofar gidan zubayr
Ahj Alkasim yake tayiwa umma nasiha tamkar yaciri xuciyarsa yabata aro
Saboda stabar son tayi aiki da nasiharda yake gaya mata
Daga karshe yace
umma a yau
kuma a yanxu zan gaya miki babban dalilina dayasa nace baxan aura miki Saddam ba
Ahj Alkasim yaja numfashi yanisa yace
Saboda inhar na aura miki Saddam to tabbas bancika uba mai adalciba
Domin kuwa ihar daya daga cikinku ta xama matar sa
Tohh lalle xai kaita jahannama
Da sauri umma ta dago taqurawa babanta ido
Cikeda alamar tambaya tana jiran taji dalili
Ahj Alkasim yace kwarai kuwa dan tabbas ba wacca acikin ku da xata iya yimasa biyayya ta kuma bishi
Musam man Ke
Wllh
Saidai shii ya biki
Saboda yanada sanyi hali Wanda akasari yafi kyau ga halin mace shi dabi arsa da halayarsa daban suke dasauran matasa kamarsa
Nikaina inajin zafin rashin samun ya mai irin halin daxan bashi
Ahj Alkasim mur yarsa tayi rauni yaci gaba da cewa
Shiyasa duk mutuminda yayi sakaci wajan bin sunnar Annabi s a w to xaita tafka asara da dana sani arayuwarsa idan kuma
yagane daga baya tofah
Lokacin bakin alqalami yabushe
Tabbas samarwa yaya uwa tagari musam man mai addini
ba qaramar taka sa'a bane arayuwa
domin tana mutuqar taka rawar gani wajan tarbiyyar yaya
Umma kuyi hakuri nasan narusa rayuwarku bakuyi sa'ar uwaba
Allah yagani nayi duk kokarin da xanyi akan nasami mace tagari amma Allah bai banba
DESTINY
Kenan
ba wanda ya isa yacan xashi dan rubutaccen Al amarine daga Allah
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🌾🌾🌾🌾🌾
Ahj Alkasim yace shiyasa
Nayi dagaske na jajirce wajan neman sanin waye zubayr
domin inada tabbacin insha Allahu zai saita ki
hanya madai dai ciya
har kikai ga samun Aljannah takar kashin qafarsa
Dan haka kikwantar da hankalinki kinji ummata
Ya danyi murmushi yace
au kema kiyi mana habba Amarya
Koda yake saikin shiga gidanki kinga irin qoqarin da mahay finki yayi miki sannan nasan zakiyi dariya
Umma ta dago kai araunane
don magan ganun Abbanta sun stuma sassan jikinta
Tace ngd Abba
Ahj Alkasim yayi irin muryarta da take cikin kuka
yace
nima ngd umma
Umma ba tasan sanda takifa kanta acinyar Abba ba tasa dariya
Cikin farin ciki Ahj Alkasim ya dagota
yace ko kefa daman dariyar nakeson gani
Kinga umma
barina fada miki halayen mijinki zubayr
Kinaji umma
Yanada ilimin arabi da boko mutane da yawa sun masa shaidar yana riqo da addini
Sallah ajam i bata wuceshi
ga mutunta al umma
sannan uwa uba yanada jajir cewa
E dan tsayayyene
Umma ina mai tabbatar miki tinda zubayr ya kasan ce mai kula da ibar Allah to tabbas xaki same shi mai sauke duk kan hakko qinki akan sa
dan yasan Allah ne ya dora masa
Dan wllh duk Wanda kika samu yana sauke hakkin Allah
Toh sauke haqqin mutane baxai taba yimasa wahala ba
Saboda yana tare d Allah yazama naAllah
Toh anan dai Ahj Alkasim ya shiga da umma yakuma damqa amanar yarsa ahannun sirkinsa
Yayi musu Addu'a sosai sannan yayi sallama yamike
Umma ta kama hannun Abbanta tace
Dan Allah baba ina Neman alfarma
Yace fadi ummata inajinki
Umma tace baba dan girman Allah baba ka wuce gidan Uncle sani kadawo da hajja dann
Kafin taka rasa fada Ahj Alkasim yace karki damu nayi miki Alqawari insha Allah
A KWANA A TASHI
Maisa ba fade zama sarki
Bayan wasu shekaru
Ahj SADDAM yaxama hamshaqin mai Arxiki
Bayan Allah yayi wa baffansa rasuwa
Wanda Ashe karar ne shima Ahj Alkasim Yarasu
Hakan yayi sanadiyyar korar karen da hajja ta yiwa Saddam
Itama Tasneem ranar sadakar bakwai din Ahj
hajja ta dan qawa mahy fiyarta ita
Mahyfin tasneem kanine agun Ahj Alkasim su biyu ne kacal agun mahyfi yarsu sai tarin wadanda suke uba daya
Mahyfin tasneem yarasu tintana shekara 3
Hakan yasa Alhj Alkasim yayi yunqurin Auren mmn tasneem amma inaa
Hajja ta shiga tafuta tace sam
Babu macen data isa tai shearing mijinta
Hajja bata barta hakaba har saida takuma yin asirin data korata jiharta wato kasar Ghana Wanda acan iyayenta suke
Taxo bautar kasa anan kanin Ahj Alkasim yaganta iyeyensu sukaje har Ghana suka nemi aurenta
Babu yadda basuyi ba akan Ahj Alkasim ya basu tasneem bayan sadakar arbain
amma fafur yaqi
ganin ita kadai zai dinga kallo yana tuna dan uwan sa
Tole suka hakura duba da cewar dangin uba sunfi su qarfi
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🌾🌾🌾🌾🌾
Ahj Saddam yayi aure harda dansa wanda alokacin yashiga primary schll
xaman su fly shida matar sa duk Kansu basu da haya niya so silently
Hmmm daman ai sai hali yazo daya ake abota
Hajja wacca ahalin yanxu ta fanstama neman inda Saddam yake tamkar wacca tasamu hau
Hajja tun bata yarda da jita jitan da takeji na Saddam ya zama mai arxiqi
Hardai taxo ta yadda
Bayan ta tabbatar daga majiya mai tusheee
Kasan cewar yanzu abin duniyar yaja baya sannan
gaa donta dana yayan sam basuyi mata albarka ba
Kasan cewar da zarar mastala ta kunno kai xata kwasa takaiwa boka yawar Ware mata
Sai ana mata nasiha saita tubure
Wai ita sam bata xuwa gun bokaye saidai malamai
fafur taqi yadda
wai ita Allah ma ya stare ta da zuwa gun boka
Hmmm lalle jahilci yafi hauka😁
Baya ga irin stist stinewa yan uwan Ahj data dingayi a lokacin rabon gadon
Saboda tana jin haushin sun shigo cikin rabo
Ahaka dai akai baran baran
Daman can saboda Ahj suke daga Mata kafa
Dan shine komai nasu arayuwa
Hajja
ta kashewa umma aure
Bayan nan
takuma yin nasarar hallaka mijin Hanna
Wanda laru rarsa tayi musu kaka gida
Hajja ta gano muddin yana darai to tabbas xasu wayi gari a tutar holoqo
Saboda kullum ana hanyar asibiti gobe wannan kasa jibi wancan gari
Hakan yasa hajja ta hada kai da umma saida su kaga bayansa
Wanda sai daga baya suke gayawa Hanna
Aikuwa taja dogon tastaki tace kuntai makeni dan wllh sai yanzu nasan bashi da amfani
Ni kenan kullum acikin dawai niya
Hajja tai shewa tace yawwa yar gari
Daman tin farko da kika ga na kafe saikin aure shi aina hango abinda baki saniba
Bello bashi da kowa dan cirani ne yazo birni yatara uba uban Arziqi
Sai larurar sace take lashe kudin
Yanxu kuwa kinga sai muci karenmu babu babbaka suka fada atare suka sheqe da dariya
Har uwar fa😏
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🌾🌾🌾🌾
Hajja tai nasarar rufe bakin duk wani makusancin mijin Hanna
Dakarsu samu damar sanar da iyayen sa cewar ya rasu
Balle axo raba gado abasu abinda ya sawwaqa
BELLO yakasance tun yana yaro yake fama da laru rar sikla
Wanda iyensa basu da karfi
Hardai da suka gaji sai suka turo shi Alma jiranta jihar kano
Bello yasha wuya ahaka harya girma har ya samu Sana'a yazama mai arziqi
bello koda yayi kudi sam bai damu da iyayen Saba
Dan yana tuna irin wulaqancin daya sha arayuwarsa
A dalilin Alma jiranta da suka turo shi
Bayan sunsan yanada larura
Hakan yasa yayi busus dasu
Bello ya hadu da Hanna
A xaryar asibiti da yake yawan yi dan Neman magani
A lokacin yakai kusan shekara 43ba aure
Tinda Hanna ta bawa hajja labarin yana sonta
Shi kenan hajja tace kurun kus mai abin yazo
Hanna taso bijire wa hajja
Dan ganin bello ba mijin moro bane amma inaaa
Hajja ta gano gun morar
Hajja tayo kulla kullenta
Akasha biki
Hanna tahyfi safna ba dadewa Allah yayi wa bello rasuwa
Lokacin safna tana basic 1a schll
Hanna Hannaatu umma kaltum umma
Sautin kwala kiran hajja kenan da takewa yayanta
Cikin razani da Al ajabi
Tohh
tabdi cewar umma bayan ta cabe baki
Hanna tace
ko lfy
hajja take kwala mana irin wannan kiran haka
Umma tace hmmm ai in kika bibiya gidan masu kudi ta gano
Hanna tace
Tashi dai muje kinsan zuzutun hajja
Katta shigo taji muna gulmatta
Hmmm uwa kenan mai siyan mutunci agun yayanta
kuma mai barar dashi har su taka
Atare suka yunkura suka futo falo
Hajja fly suka fada atare
Hajja acikin kambama murya tace yau yau nayi gamo
Can kuma sai
tasas sauta murya tace wllh wllh baxai yiwuba
Can basai ta fashe da kukaba
Da farko dariya su hanna suka fara yimata aboye
Amma yanxu seriously sun kasa gane kan hajjantasu
Toko madai hajja kantane ya kwance
Ko kuma dai gidan masu kudin ta gano
To dai
Kubiyoni
AMSAR💕💕
[1/31, 8:50 AM] SARATU: _*🍂BIYU BABU…!🍂*_
_SAMU DA RASHI…_
🍂🍂🍂
🍂🍂
🍂
_*AɭKAɭAMƖŊ✍:Saratu munzali*_
_*(AMSAR💕)*_
_watpadd @ Ssaratu75…_
*ɖҽɖɩcatҽɖ tɷ:AUNTY ZALY MMN AHMAD YOLA*
_*Na sadau karmiki da page din nan nakine sukutum AUNTY HAUWA S ZARIYA Mmn Uswan naji dadin tarba da kulawarki gareni jzkllu bi khayr💕*_
________________________________
*AREWA WRITES ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{arewa gin shiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts/104535871033350/?substory_index=0&app=fbl
*BISMILLH RAHMANI RAHIM*
P_____5
____📖 Cikin muryar kuka hajja taci gada da cewa"gaskiya duniya akwai butulci"yanzu kamar Saddam ace ya manta ko wa yayi silar arzikinsa
ai baici ace ya manta da zuri'ar Ahj Alkasim ba".
Haba hajja daman akan maganar wannan solobiyon kiketa kwala mana wanan kiran?,ta karasa maganar tana shirin barin gun.
Umma tayi sauri ta riko rigarta
tace" haba yaya
da dina dake saurin ƙufula
ki tsaya muji karashen zancen mana.
Hajja tace" umma
sakonan zai zo kigane inda nadosa
gaba dayan ta tarikice tace" yau na tabbatar damu yan Rakiya ne"
Umma tace" Rakiya fa ki kace?,
RAKIYA R wa kuma".
Kwarai umma mu yan Rakiya ne
Gashi nan kiri kiri
Saddam ya nunawa duniya cewar
Munzama
Ƴan Rakiyar masu Arziqi
kenan munra kosu duniya
ta kuma baye labba da kuka"
Umma wanda itama takai bango
ta dai daure tace"
hajja ai wllh ko yanxu mun godewa Allah,dan munci arziqi
babu wani abu damai kudi zainuna mana".
Bata karasa faɗi ba taji wuff hajja ta buge bakinta to" ke dallah can
har kinsan meye duniya?
ai muddin kana darai toka nemeta kamar bazaka mutu ba".
Yarinya bakisan kuɗi ba
baki san kuma amfanin suba,
su kansu masu kuɗin sunfi talaka masifar sansa da zafin Neman sa
Shiyasa yawan su basa zakkah basa tausaya na assault.
Hanna tamike tsaye
tanata layi tace"
hajja kemafa daba kuɗin ki ba
idan baba yafitar da zakkarsa indai ya baki ki rarrabawa maqota
ba kya basu
Sai kice gida bai qoshiba.
Afusace hajja tace"
toh dan ubanki gidan ya qoshine
ko kintaba ganin ya bani zakkah
koku bai taba bawa ba.
Umma wacca tinda aka bigewa baki
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 15