Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wah ay wlh dana zuba musu kudi na gwara na zubasu a shadda, khalthum tace kyaleta hafsa kishi take ,joda tace tupp Allah sauwake inyi kishin wancan mai mugun halin , hafsa tace nidai yayana bayada mugun hali kema Dan kinki kwantar da hankalinki ne " joda tace nace dai bazaniba sekun dawo dole suka kyaleta sukaje suna yimusu liki, Wucewarsu keda wuya Sega wani yazo yaxauna baby tin dazu nake neman tayadda zan sameki mugaisa , joda tadago tace lfy? Yace lfyr ce dai wlh kawai kimun kuma ina sonki in bazaki damuba muje filin rawa, joda tace amma wlh kai bakada kunya nizaka cewa muje filin rawa namaka kama da mai rawa ne iye , Mahmud yaxo wucewa yagansu dasauri yadawo baya, yace kai malam lfy? Yaron yace lfy qlw bros dama naganta ina sone, Mahmud yace itakuma bata gayamaka cewa ansaka muna rana ba, joda tadago tana kallonshi yace to maxa kabar nan gurin wann matata ce, yaron yabashi hakuri sann yawuce Mahmud yaja hannun ta yace zo muje gurin rawa joda tace a'a ya Mahmud ni ban iya rawa ba , Mahmud yace sekuma kinje dole, haka sukaje yasakata dole tayiwa amarya da ango liki, Ahmed se bin ta da harara yake mansura na mamakin yanda yarinyar tahadu amma Sam bata gaban Ahmed duk yan matan gurin babu wacca tafita yayan masu kudin gurin da kowa , dayake khalthum ce ta gyara ta, khalthum akwai duniya ci dason wanka Mahmud yace kiyi rawa mana se in miki liki , joda tace kunya nakeji ya Mahmud bantaba rawa ba ni banma iya irin wann ba, Mahmud yace shikenan toki Dan taka, haka kuwa akayi yafara mata liki, abdallah na hango su nashi kishin ya motsa shima yaxo yana mata likin kudi, aykuwa se abun yazama kishi dollars, aykuwa mai kidi yakoma kansu yana xuba kirari joda kuwa duk ta tsargu Hankalin kowa yadawo kansu, Ahmed yarungume hannuwa yana kallonsu khalthum da hafsa sukayi jugum suna kallo, sukuwa sunki daina mata liki duk da barawa take ba, hafsa taje gurin mai kidi tace yasaka musu kidin FULANI, aykuwa Sega joda tafara motsawa duk Wanda yake FULANI agurin seda yaje filin rawar saboda yanda suke Jin kidan ajikin su........... ๐ŸŽ„ FULANIN DAJI ๐ŸŽ„ N@ B Aleeyu ๐Ÿ’• page 7โƒฃ7โƒฃ Joda tafara wani irin rawa yanda kidin ke tafiya haka rawar ta ke tafiya kowa yakoma kallonta hafsa takalli khalthum ashe ta iya rawa jita kamar macijiya, kowa yamatsa yabata guri Mahmud ya cigaba da liki hakama abdallah, gumi se karyemata yake amma taki bari shikuma mai kidi yakara da busar FULANI, nan joda tafara ajujuwa har takai gurin Ahmed anan tafada kanshi tareda rungumesa da hannu bibbiyu, hafsa tace yayi dae2 khalthum tace yo naga soyy, sun dade ahaka sann Ahmed yadago fuskar ta yaga idonta arufe Jan ta yayi yanda take rungume ajikinsa har mota, abdallah ya dinga ja dabaya yana dana sanin abunda yayi, mansura tabiyosa dear ina zaka ay seka bari hafsa ta maidata gida, Ahmed yace noo kikoma ina xua, gudun yamata wulankanci cikin kawayenta yasaka takoma, Mahmud yaxo yace man......baikarasa ba Ahmed yasaka hannu agabanshi batareda yajuyo ba yace enough enough Mahmud, yana kai nan yasa kai yawuce cikin motarshi ya ajiyeta yazagaya yatada motar se gida haka ya rungume ta tamkar jaririya, se dakinshi ya shimfideta kan gado sann yadauko mata ruwan sanyi yabata tasha tareda wani kyalle yagoge mata fuskarta, ar u ok? Naji yafada joda ta girgiza masa kai, sekuma tasamasa kuka, Ahmed kam shiru yayi yana kallonta can yace kinsan Allah Zane ki zanyi Yanxun Dan bakida mutunci kikaje karti suka tasaki a tsakiya suna tabaki wann yatava boobs wann yataba hibs , kowa na kallonku, joda tace na shiga uku ni wlh bawanda yatabani acikinsu, Ahmed yace yimun shiru munafuka dama ay haka kikeso , ke baki San hukuncin aure ba koh " joda tace toni ay bana son auren ,Ahmed yadaka mata tsawa zanci ubanki wayake son auren daga an taimaka miki akayi, joda tace toni nagode da taimakon, Ahmed yace keee wlh zakici ubanki yanxu get out b4 nabata miki rai shegiya mai fuskar agwagwa ," nikuma asea nace ay fuskarku daya ehe ๐Ÿ˜ Fita tayi takoma dakinsu, gwaggo tace au har kun dawo inasu khalthum da hafsa, joda tace basu dawoba, seni kadai, gwaggo tace ke kuma ana zaune qlw sekika yanke jiki kika dawo gida, joda tace toni nadawo ne ay yayan hafsa ne ya maidani gida, gwaggo tace tsakaninku baruwana, joda tafashe da kuka ni wlh an cuceni kawai baza'a bawa mutun Wanda yakeso ba mezanyi da wann Dan bakin rai, gwaggo tace kyaji dashi in ni nacuceki toki gayawa Allah inyaso seya saka miki, joda ta zunbure baki tayi cikin dakin Tellphone tajanyo takira doctor bayan sun gaisa, yace toh ganinan xua nadai san abunda kike jira, joda tayi murmushi yauwa likita kagane, bara nayi sallah kafun kaxo , sallah tayi sann tasake wanka sabuwar atanpa tasaka ta cikin kayan bikin super ce tamata kyau sosae sann tasaka gyale kalar atanpar se takalmi flate, gwaggo sallah take saboda haka ta lallaba tawuce batareda taganta ba , tana kai gate yana fakawa da mota kawai tashige, suka tada hanya , wakar flavour yasaka mata mai taken vewrifull" joda najin dadin wakar sedan mamin take dikda bata iyaba , har suka kai wani gida mai kyau, yakalleta yanaga jikinki yafara bari zakiga queen of beauty " joda tace uhm..Muje dai , shi yabude gate din abunda yabawa joda mamaki kenan sann suka shiga Karamun gida ne amma yahadu komai naciki sabo ne " binsa kawai take itakam bataga alamun wani mutum agidan ba, joda tace nikam bakowa ne agidan, yace bana son azarbabi fah muje dae, wani daki suka shiga se kamshin sababbin kaya yake , yace tazauna yakira mata matar tasa joda tazauna cike da kaguwa, ba'a Fi minti uku ba se gashi yadawo da drink yana sha yace dubo nan joda ya nuna mata mirror wakika gani, yarinyar nan tafiki kyau luk at pinky lips dinta bakinta kamar cokalin tea gashin ta har gadon baya komai nata enough ina kewar ganinta nanda shekara daya , joda tajuya tarufe idonta, da hannuwanta, likita yace hakika joda so yawuce afadesa da fatar baki ina sonki joda tin randa nafara ganin ki, joda kam kasa tsayuwa tayi aranta tace shikuma wann nasa style din daban yake.......... Muje zuwa ๐ŸŽ„ ASEEYAH BASHEER ALEEYU ๐Ÿ’• ๐ŸŽ„ FULANIN DAJI ๐ŸŽ„ ๐ŸŽ„ ๐ŸŽ„ ๐ŸŽ„ ๐ŸŽ„ ๐ŸŽ„ ๐ŸŽ„ ๐ŸŽ„ ๐ŸŽ„ ๐ŸŽ„ ๐ŸŽ„ ๐ŸŽ„ ๐ŸŽ„ ๐ŸŽ„ ๐ŸŽ„ ๐ŸŽ„ N@ B Aleeyu ๐Ÿ’• page 7โƒฃ7โƒฃ Haka suka dawo gida Zancen namata yawo akai, kowannensu da abunda yake sakawa aranshi, joda na tunanin makomarta shikuma yana tunanin karta ki karban soyyr shi, joda tace nikam likita se yaushe zanga fuskar ka? Dasauri yataka burki seda ta tsorata, yace no joda bayanxu ba lokaci baiyi ba , joda tace towae mekake boyewa ne acikin wann fuskar, yace bakomai joda mamaki ne kawai aciki dakuma tsoro, Joda tace tsoro kuma kamar ya? Yace eh tsoro nasan idan kika gan fuskar nan komai ma zai iya faruwa idan ki kaga hallitar da Allah yamun wann dalilin ne yasaka nake saka face mark nafi son kiso zuciya ta sama da fuskar nan tawa ganinta bayada wani amfani Watakila ma idan kika ganta bazaki sake yarda ko hanya ta hada mu ba, joda , kam dole ta hakura , yana ajiyeta Sega su hafsa dasauri joda tashige gida batareda sun ganta ba, tayi shiru kamar mai bacci, koda su kazo tana bacci khalthum tasha dariya sann suka fita, wanka tayi sann tasake wasu kaya , tana cikin shiri segasu sundawo , hafsa tace muje gurin kae amarya, joda tace wah zaije kai amarya din. hafsa tace tome ne aciki Dan kinje, joda tace Allah sauwake mun naje kaima wani mugun amarya toni waema miye ruwana dasu nifa danke nake xua bikin nan hafsa Hafsa tace ollrt yanxun ma kije danni okey, joda tace wlh ba inda zanje kubace mun dagani, khalthum tace muje hafsa kar mu rasa motar hawa mudae baza'a bamu lbr ba, joda tace safe journey. khalthum tace oho dai kedai kishi ne kurum bazaki iya ganin mijinki dawa ta ba amatsayin matarshi, joda taadauko filo ta jefa mata sann tafashe da kuka dasauri suka bar dakin Gwaggo tace to lfy sarkin kuka, joda tace ni wlh ki musu mgn sudena tsokanata wae daga nace bana xua shine wae ina kishin yayan hafsa ne " gwaggo tace yo dama meke cinki inba kishi ba, joda takara fashewa da kuka tana bubbuga kafa , ko Dan kwali bata saka ba tafito waje tayi hanyar garden tana kuka, bayan wani window ta tsaya tana kuka tana zance ita kadai, kamshin tirare taji dasauri tadago taga waye fararen kafafun sa ta zubawa ido sann tayi sama light din wurin yaki kae ga fuskarsa amma dae tasan abdallah ne sbd shiyake saka irin wann kayan Dagudu taje tayi hugging dinshi tana kuka, ya abdallah shikenan kahakura dani, Dan Allah mugu du daga gidann, bana son yayan hafsa natsanesa kamar yanda yatsaneni, sekuma tasaka kuka, tareda kara kankame shi, shiru taji yayi a hankali ta sakesa, tana son ganin wani yanayi yake ciki , amma fuskar shi bama ita yake kallo ba kujera tajawo tahau yanda tsawonsu zaizo daya , na shiga uku tafada ๐Ÿ™†๐Ÿป tareda zare ido " Ahmed yakura mata idonsa masu ban tsoro fuskar nan ba annuri acikinta , yasaceki kugudu yafada acikin lion voice dinshi? Wato ke yar iska tantiriya koh har kinsan saurayi ya daukeki kugudu domin kuji dadin aykata masha'a Joda tace wlh a'a bahaka.....bata karasa ba yabuge mata baki sann yakwabe kujerar tafadi akasa, joda kam tini tasaka mishi kuka, Ahmed yace wlh yanxun zakici ubanki idan bakimun shiru ba shegiya munafuka , musa afuska fir'auna azuci, joda tashiga girgiza masa kai hawaye na fita a idonta, dagota yayi sama sann yace idan bakiyi hankali ba wlh boarding skull zan mai daki tinda ke ta tacciya ce. .......... ๐ŸŽ„ FULANIN DAJI ๐ŸŽ„ N@ B Aleeyu ๐Ÿ’• page 7โƒฃ8โƒฃ Joda tace ni wlh bazanje boarding ba haka kawai arabani da gwaggo na, Ahmed yakwabe mata baki ina mgn kina mgn koh? Joda tasadda kae kasa tana hawaye kafarshi yasaka yayi ball da ita sann ya juya yabarta agurin kuka take kamar me, aranta kuwa cewa take Allah yasa yafusata din yasakeni , nidae nace ameen kufa ๐Ÿค Tin lokacin joda bata kara zancen abdallah ba koma ganinsa bata sake yiba sema lbr dataji cewa yatafi Malaysia gun hafsa daga ranar tafidda shi aranta amma can kasan zuciyar ta na sonshi, hafsa ma takoma skull, su joda ansha kuka kamar me, dakyar ta hakura itama hafsa din tasha kuka ciki harda kukan rashin samun soyyr Mahmud da tayi, atunaninta kafun tadawo yayi sabuwar budurwa, idan yafahimci joda nada aure, wata zuciyar kuma tace koday kigayamasa, can kuma tace noo bana kishi da yar uwata, to amma kuma miye amfanin boyewa din dawann tunanin tabar gidan Gwaggo tagama fura tamikawa joda tace takai a fridge din babban palor na gidan, a hankali take tafiya har ta isa gurin tabude fridge ta jiye furar sann tajuyo, dae2 nan suka ci karo da amina nanko joda ta tsaya cike da tsoron abunda zata mata, amina tadinga zunburo baki kamar mai shirin daukar selfie, joda tarava gefen ta zata wuce amina ta tare hanya, sann tace sannu anty joda matar big bruhh, sekuma ta kyalkyale da dariya , joda kam tini tafara ruwan hawaye, amina tace au kuka ma zakiyi, dubeki Dan Allah wae ke kin waye koh? tobara kiji maganar da bata tashi wlh wlh wlh sau nawa? Joda cikin muryar kuka tace uku, amina tace gud to wlh kar na sake ganin kinyi kwalliya kokuma kinsa ka kayan masu kama da na yayan manya danke bayar manyan bace tsiya gaba tsiya baya Kuma daga yau kexaki riga gyara mana dakinmu nida hjy sann kirika wanke mun under wears dina okey tareda jamata kunne, joda tace ollrt anty amina ta mata soko alright, ni zaki yiwa speak yaushe ma kika shiga skull din. kar nakara jin kinyi speak wlh sedai kiyi hausa ko kuma kiyi fulatanci ay muma munaji , joda tace insha Allah zan kiyaye, tajuya zata wuce amina ta janyota zo muje na nuna miki toilet dina akwae pants dina uku dasuka baci da mensis dina zaki wanke kitabbatar kinsaka Gishiri kadan da dettol akwae warm water dasu zakiyi amfani idan kin gama ki dauraye da hypo dauraya na biyu zaki gan tirare Wanda ake sakawa saboda karnin sabulu ko karnin blood din understand? Joda tace yes, amina kuwa tabuge mata baki wato har kin manta **** abunda yakamata kowacce mace tayi kenan domin Kare kanta daga cutar infection sann zaki iya insert na miski fari ko zaitun da habba domin kara tsabtace HQ dinki musamman matar aure ko budare suna yi infection base mai aure ba so kowa seta kiyaye marta barta , gyaruwar HQ dinki shine martabarki ( Allah yasa mudace ameen )**** ๐ŸŽ„ FULANIN DAJI ๐ŸŽ„ N@ B Aleeyu ๐Ÿ’• page 7โƒฃ9โƒฃ Haka joda taje ta wanke pants din xuciyarta se tashi yake sann tagyara mata dakin Tass ko ina seda tagyare tsab ta kunna tirare , tafito kenan tahadu da hjy a downstairs, hjy tabita da muguwar harara dasauri joda ta nemi sauka, hjy tayi saurin jawota inazaki munafuka, mekikayo adakin yata, amina tace kyaleta hjy ni nasaka ta ayki, bara naduba wlh idan baimun ba sekin kara wani, dakin tashiga tana Kare masa kallo yanda yadawo Tass harda can zamata jerin daki kuma bakaramin kyau yayi ba, tafito tana kinci sa'a yarinya yanxun sora dakin hjy, joda tace lokacin sallah yayi fah, hjy takai mata ran kwashi lokacin sallah dayake mu kafurai ne koh? Joda tace a'a bahaka nake nufi ba hjy takwabe mata baki yimun shiru makirar "ya , maxa jeki gyara mun nawa, tana shiga amina tace wlh hjy ta iya gyaran daki dubi fah yanda dakina yadawo harda canza style aikam da baimun kyau ba senaci ubanta tinnda bansakata janzamun kaya ba, hjy tace ohhh....kice munsamu yar gyaran daki, amina tace sosae ma hjy kinga munsamu hanyar cin ubanta , da aeki kadae semu maidata tsofuwa wahala tamaida ita baya daga baya dole mijin yasaketa inyaga ko kallonta baya iyawa Bari kiji hjy nahana ta saka kayan kirki sann nahanata make up da wann shegen speak datake yanxu kuma bara taxo sena hanata daka bra yadda boobs dinta zasu zube awar silifa , sann wanka a sati sau biyu banda saka tirare, hjy ta kyalkyale da dariya kae amma dae se yau nakara tabbatar ni na haifeki wann bala'in haka yo ay kice yarinya tazama hoto duk wata hanyar gyara kin tosheta, amina tace baki wasan wann ba sena gusturemata gashin nan nata yanda natsani nagan ta zuvo shi, hjy tace nagode yata nabaki dama kiyi duk abunda yadace Tana fitowa amina tasata agaba da scissors, tagutsire mata gashin ta yakoma kamar nawata baby, sann tabata wata sabulu tace dole da ita zaki rinka wanka kuma nagaya miki sau biyu ko uku zakiyi wanka asati daya , sann tabata baseline dinda zata shafa dakuma man kitso joda kam ba tagane kona miye ba, bacin ranta daya ashe wae bata wanka kullum amma in bancin haka babu abunda yamata zafi gashin ta kuwa dama ya isheta da Gwaggo tasama zaune tana karanta iziya, gwaggo tace ke kuma daga kae fura sekika maida gari naku joda tace wlh a'a gwaggo anan takwashe komai tazayyane mata amma taboye zancen wanka da gutsure gashi duk taboye kawai dae tagaya mata cewa itace zata rika yimusu gyaran daki, gwaggo tace to miye aciki ay duk acikin aykinmu ne " kodan kinga sunbarmu muna cin bulus, koba komai ma kinga zaki kara kwarewa da ayki a yanda kike da shegen son jikin nan, joda kam tabe bakinta tayi tashige daki tayi alwala ta tada sallah Su mansura kuwa se zagwadi ake an shigo gidan Ahmed, randa aka kawota bai shigo gidan ba se kusan 12 shima itace tamatsa mashi da kira danko yamanta cewa shiwae angone duk wata waya tashi daya san za'a nemeshi kashe ta yayi, yana kuwa xua ta taresa da hugging, hannunsa take kallo bataga ledar kaji ba, aykuwa tasa tanbaya Ahmed yace nasiyi miki kaji sekace wata mayyar nama kaxarma wace iri ce bakiciba , mansura tace hakane honey muje daki na, Ahmed yace to mezanyi a dakinki nifa bacci nakeji seda safe, mansura tace bazamuyi sallar godiya ga ubangiji ba, Ahmed yace kyayi ke kadae danni na rigada nayi shaf'i da wut'ri......... Muje zuwa ๐ŸŽ„ ASEEYAH BASHEER ALEEYU ๐Ÿ’• FULANIN DAJI N@ B Aleeyu ๐Ÿ’• page 8โƒฃ0โƒฃ Daga ranar joda tazama kazamar karfi da yaji tin gwaggo bata damuwa har abun yafara cinta , a skull ma haka khalthum kefama da ita idan tamatsa mata seta saka mata kuka, gashi lokacin zafi ne " haka zakiji tana ta wani tsamin ba dadi duk yanda khalthum taso daure wa amma ina dole ta canza site , Ba abunda yafi damun kh irin bakin da joda keyi skin dinta duk ya takuje yayi wani iri dashi harma kara gwaggo da ita, abu dayane bata bari ba shine karatu dukda suna gab da fara paper, agida kuwa tazama boya tana dawowa skull sometime ko sallah batayi zakiji anzo nemanta hasana mai ayki kuwa tayi ta masifa acewarta wahala ce tamaida joda hakan, yau Mahmud yakawo musu ziyara tareda chocolates dinda yasiyowa joda, bakaramun mamaki yayi ba ganin yanda joda tadawo kamar yar 60 , dakyar yake iya zama a tareda ita, Mahmud yace joda ke kuwa wani irin ciyo ne haka kinbi kin rame kinyi baki komai naki yacanka, meyasa kike zama da datti ne haka,Joda kam tagumi tayi tana kallon sa duk yanda yaso takar bamasa amma taki, yana fita kuwa yawuce supermarket yasiyo mata sabulun himalaya tareda mansa dakuma tiraren smart collection, yakawo mata joda tayi godiya aranta kuwa tace ina ni ina wann sabulun mai kamshi ina wanka dashi zasu tsigeni idan sukaji kamshin sa ajikina haka takaisu daki acikin akwati ta ajiye bata sake waiwayarsu ba , mansura kam abu yafara damunta yau kwana uku Ahmed yaki kulata sedai su sha fira itadinma ita kadai ke zuba bada shiba, idan ta tabasa komai baya cewa , gashi amatse take koba komai tasha abubuwa barekuma yanda take da bukata Yau kam tasha al'washin nemamsa da kanta domin kuwa bazata jure hakanba, Ahmed kuwa yana lure da take2 ta shi isa yamata banza arayuwar shi yana son mace mai al kunya da Jan aji , bayan sun gama dinner sunyi kallo kusan har 12 mansura tacanza tasha zuwa wata ta shar da ake sako BF, aikuwa tayi sa'a ansaka wani, tuni tafara murmushi aranta kuwa tace yanxun zakaji feelings. Ahmed kuwa yi yayi tamkar bai gane komai ba , seda tamatso a kusa dashi tafara romancing dinshi, sann yadaka mata tsawa miye haka? Dallah kicire mun wann iskancin kawai zaki sa mutum kallon haram, mansura tace hava dear duk kauce war danake kaki kagane iye, yau kwana biyar ace babu wani abu da muka gudanar amatsayin mu na ma'a u rata , Ahmed yace ohhh....ay seki fito fili kigayamun cewa namiji kike bukata ba kizo kina kunna mun bf ba kokuma a zatonki shi zaisa nakulaki , mansura tace sorry dear yanxun muje daki, Ahmed ya ballah mata harara muje daki inmiki ubanme acan, mansura ta kimtse fuska tace kabani hakkina, Ahmed yace hakki koh? tobanga dama ba, sena tashi yana kai nan yafita , haka mansura ta kwana daddafe da mara tsananin sha'awar datake ji, Ahmed kuwa tin safe yafita domin baya son wata maganar Mansura nafitowa taga baya nan, tsaki tabuga ni wlh bazaka kasheni ba da lfy na wanka tayi ta sauya kaya......... Like ยท Reply ยท Report ยท 10 hours ago Pharidah Ahmad FULANIN DAJI N@ B Aleeyu ๐Ÿ’• page 8โƒฃ1โƒฃ tazare key din motar ta se zaky hotel, tana kae tasa Kiran sabon saurayinta kamal, shikuma dama yana expecting kiranta tinda sunyi dashi 2ydx idan angon yafara , haka yaxo yasameta suka aikata masha'arsu, kamal yace sury kin jiki kuwa billahillazi kinfi korama kinji yanda naji sama na yawo dani, mansura tace dole nefa kasan nasha gyara kamar mutuwa shikuma angon Dan apixy ne " baitashiba gara kawai na nema Dan bazan iya koda sati dayaba batareda naji ehem ba, kamal ya kyalkyale da dariya bakida dama Karfe 1 dae2 tadawo gida tasake shiri sann tafito parlor domin tasan yanxun Ahmed zaizo, amma shiru ba labarin sa, bai dawo gida ba se guraren 11 yana xua ya hau dinner bayan yagama yaxauna parlor , ganin fuskarsa adaure yasaka mansura low tasan tin abun jiya ne " wato kar nasake tambayarshi koh " ay nasan maganin ka Daki taje ta dauko wani caset, da kakanta yabata wa'azin gombe ne " tasaka ananan suna saura re Ahmed dae baice kala ba , se gashi ana fadan hukuncin Wanda yaki bawa iyalanshi hakkinsu alhali yana qlw, da matar da ta guje mijinta, Ahmed yakalleta yaga shi take kallo, tsaki yabuga yabar gurin se dakinshi wanka yayi yasaka jallabiya sann yadawo parlor koda yazo har tafara bacci, bubbugata yayi firgigit tafarka , kisameni adakina yafada kawai seya koma , mansura tayi jugum tomeni Allah yasa dae kudine zai bani da wann tunanin tabisa baya , suna shiga Ahmed yarufo kofa yanuna mata gado, ba musu mansura tazauna, Ahmed ya kashe light din. aykuwa gabanta yashiga dukan uku Mansura tace lfy Ahmed menene, Ahmed yace hakkinki zanbaki tinda kinkai karata agurin Allah. mansura tace no wlh bahaka bane Dan Allah Kayi hakuri kabari se gobe ni yanxun ban shirya ba kuma bana Jin dadi, Ahmed yace ni dinma bashiri ne daniba amma naga alamar ke zaki iya kauce hanya idan baki samu biyan bukata ba , mansura tafashe da kuka na shiga uku, Ahmed kam ko sauraran ta baiyi ba yashiga aykinshi ayadda yake sarrafa ta kadae yasaka ta manta dawani abun, Ahmed kuwa yakudurta aranshi Yau seta rana kanta har kusan 3 bai wani abu ba, mansura kuwa tasha gurza tin tana nishi har tafara kuka yanda yake mata ne basauki , lokacin da yafara ibadar aure kuwa ihu take kamar zata shide Ahmed kuwa bai mata a sauki ba kuma yaki saurara mata, har kusan safe abu guda ake seda yamata lissss ko yatsanta bata iya dagawa sann yabarta yaje yayi wanka yawuce masallaci yabarta agurin , yana dawowa yaganta a yanda yabarta wata irin tsawa yadaka mata seda tamike zaune bata shirya ba, Ahmed yace maxa kificemun adaki kafun nayi miki Dan baxan Duka fasika jahilar yarinya Sanin dalilinsa na kiranta fasika baisa tayi kokarin cemasa kala ba illah kawai tafita adakin dakyar take takawa tsabar azabar dataji, kusan kwana uku tana jinyar jiki Ahmed kuwa bai sake bi takanta ba, dukda baya ganinta, mansura takira hjy tayi mata bayani, hjy tace ay kinga irinta ke wlh shegen kwadayin tsiya gashi duk kudin da muka batar sunje abanxa, mansura tace Allah anty bakiji yanda naji bane bana iya jure bukatata Hjy tace to ay ga abunda kika jamana nan, nan talabar tamata yanda suka maida joda, tuni ciyon ta yabace, mansura tace kae amina shegiya ce, tamun dae2 karku bari yagane kuma karku sakata ayki agabanshi, hjy tace ay bama zai gani ba wlh haka nake son ji, kinga ma naji yana waya da Mahmud cewa wae zamu je Egypt honeymoon kafun mu dawo tazama kiyashi gabadai suka sa dariya........... Like ยท Reply ยท Report ยท 10 hours ago Pharidah Ahmad FULANIN DAJI N@ B Aleeyu ๐Ÿ’• page 8โƒฃ2โƒฃ Joda tagama gyaran dakin amina dana hjy sann takoma yimusu wankin underwears, danko har na hjy itake wankewa, joda tana wankin pants din hjy kawai seta saka dariya, tace yoni wai duk wann wake ken wandon duwawu ke cikashi....nima dae asea abun yabani dariya Ashe afili take zancen kawai taji ana fadan duwawun uwarki shegiya , joda ta tsorata dajin muryar hjy, danko tasan makomarta abi kadan tayi setaci Duka bare kuma irin wann subul da baka , tsawo ne mai kauri tasaka tadinga dukanta seda ta mata liss sann tabarta tsabar tasaba da Duka ko kuka batayi, tagama aykin ta tsab dasauri ta tsere batareda tasanar tagama ba, tana xua tasame gwaggo zaune tayi tagumi, joda tace hey gwaggo lfy? gwaggo tace ina lfy joda narasa meke damunki duk kinbi kin canza Joda tayi ajiyar zuciya tace gwaggo lfy na qlw ki sakani a addua, gwaggo kam seta fashe da kuka joda ma haka ba mai lallashin wani acikinsu , Mahmud ne ya katse musu kuka, dasauri gwaggo tajuya ta share hawayenta, Mahmud yagaida gwaggo sann ya dubi joda yace yadae yar kanwa, joda takirkiro murmushi tace qlw yayana, Mahmud yace gurinki naxo gwaggo , gwaggo tace nikuma Ince dae ko lfy? Mahmud yace

Chapter 5 of 11