Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 2
gayamani shashasha...ta buga uban tsaki mtswww... Sannan ta kalli driver Wanda yake zaune shi betafiba kuma bece uffan ba, cikin d'aga murya tace dallah Malam mutafi kana 6atamin lokaci. Jiki na 'kyarma driver yaja mota suka d'au hanya, dan yasan akan ilham ze iya rasa d'an Albashin dayake samu, kuma gashi dashi ya dogara. Montocin da basu wuce sha biyuba suka sadasu da gida, sukayi horn megadi ya bud'emasu get suka shige. Bayan ya ajiye motar inda aka tanada domin ajiye motoci, ilham ce tafara bud'ewa tafita, d'akinta ta wuce kai tsaye tafad'a toilet tayi wanka sannan ta canja 'kaya, ta kwalama Ameeno kira, saida gaban Ameeno yayi mugun fad'uwa danjin ilham a gida yanzu, kuma tasan indai taje school ba yanzu bane lokacin dawowarta, jiki na 'kyarma ta isa ta dur'kusa tace gani, ilham tace jeki kawomin lemu da cake yauba saikin yimin girkiba, cike da farin ciki Ameeno tabar d'akin zuwa kitchen dan kowoma *_YARINYAR BABA_* abinda ta bu'kata. Saida ta kammala sannan tafita zuwa d'akin momynta, bata isketa d'akiba sai motsi dataji a kitchen saboda haka nan tanufa dan tasan yanzune lokacin da Momy ke shiga kitchen domin had'ama daddy abinci. Ranta yayi fari dan ganin Momy zaune kan kujera a kitchen tana yanka d'anyar ku6ewa, domin yau abinda zata had'ama megidan kenan tuwom semo da miyar d'anyar 'ku6ewa. Love u all Zee Elkaseem YARINYAR BABA [07:16 PM, 01-Oct-16] by ZAINAB ELKASEEM *YARINYAR* *BABA* _*Written & Edited*_ _*By Zee Mmn Khady*_ *```Just a short story```* *Page* 101-110 cikin ladabi ilham ta rissina "Momy sannu da aiki, cike da mamaki Momy ta d'ago ta kalleta ta girgiza kai tace "yauwa, tare da tambayarta "ya akayi kika dawo yanzu Alhalin kuma nasan lokacin tashinku beyiba,? Ilham tad'an 6ata fuska tadafe kanta cikin marairaicewar murya tace "Kaine ne yakemun ciwo shine na dawo amma nasha magani, Momy ta tausayamata tace "ayya Allah sauwa'ke ilham ta Amsa da "Ameen, daga nan suduka ba wanda ya'kara magana Momy ta maida hanakalinta kan yankan ku6ewar datakeyi. Wani shu'umin murmushi ilham tayi sannan takai dubanta ga hannun Momy dataketa ayki da sabuwar wu'ka sai wal'kiya take, tsawon minti biyar tana kallon wukar tare da hannun Momy ko 'kiftawa batayi, wani haske yafito daga idanunta yafada kan wu'kar hakan yayi dai-dai da fad'uwar 'ku6ewar da Momy ke yanakawa 'kasa tare da shigewar wukar cikin tafin hannunta, wani irin mugun 'yanka wu'kar tayimata, aiko kamar jira take jini yafara kwarara ba tsai-tsayawa. Momy ta ri'ke hannunta dake zubar jini tanata salati, cikin rud'ewa ilham takama momy tana tambayarta lafiya, Momy kasa yimata magana tayi saboda tsabar rad'ad'in da gurin keyimata, ga jini sai zuba yake ba tsai-tsaiyawa. Cikin rud'ewa ilham tad'auki waya takira dadynta tagayamshi halin da Momy keciki dan ganin datayi Momy ta galabaita, numfaahinta na niyyar d'aukewa. Da sauri daddy yabaro office d'insa dukda d'umbum jama'ar dake jiransa hankalinshi tashe yake tu'kin bako sallama yashigo gidan kwance ya iske momy tsakiyar falon ba Alamar numfashi tattare da ita, gefe kuma ga ilham da 'yan biyu sai faman kuka suke. Cikin kuka ilham tanufi dadynta tafad'a jikinsa tana kuka "daddy ka taimakemu kada Momy ta mutu, wayyo nashiga ukku wayyo daddy.... Cikin tsananin rud'ewa daddy yacire ilham daga jikinsa yanufi inda momy take kwance ba Alamar numfashi tattare da ita, ga kuma hannunta har yanzu jini na zuba, cikin tsananin rud'ewa yacema ilham "taimakamin musata mota mukaita asibiti, Haka kuwa akayi da taimakon ilham akasa Momy mota suka nufi asibiti ilham sai kuka take duk ta wani firgice ta fita hayyacinta yanda kasan batada masaniya akan ciwon Momyn. Sun Isa asibiti emergency aka nufa da ita, nan likitoci suka taru kanta, sun gano tarasa jini sosai ajikinta saboda haka idan ba'ayi gaggawar 'karamata jiniba za'a iya rasa rayuwarta. Ilham kuwa yanzu nadamar gaske tayi datasan hakane da bata amince da zama cikin 'kungiyar _*JIN DADIN RAYUWA*_ ba dan gashi tana gani zata rasa momynta. Daddy kuwa cewa yayi a d'ebi jininsa a'karama Momy, cikin sa'a aka auna jinin akaga ze iyabata cikin 'kankanin lokaci aka eba aka 'karamata. Kwanan Momy biyar asibiti aka sallamota, duk ilham tabi ta rame saboda fargaba, tana gudun kada wataran awayi Gari Momy ta mutu. Cikin sati Momy ta warware kamar batasha jinyaba, sannan hankalin ilham yadawo jikinta, Sosai daddy ke kula da Momy tun ranar datayi rashin lafiya, ba'karamar Shiga damuwa yayiba, yanzukam Alhmdlh sunkoma normal Kowa yasaki jikinsa suncigaba da rayuwa kamar yanda suka saba. Love u all Zee Elkaseem YARINYAR BABA [07:21 PM, 01-Oct-16] by ZAINAB ELKASEEM *YARINYAR* *BABA* _*Written & Edited*_ _*By Zee Mmn Khady*_ *```Just a short story```* *Page* 111-120 A yau 'kungiyar *Aji dad'in rayuwa* tayi bikin karrama ilham akan namijin 'ko'karin datayi gurin kawo jinin momynta, hakan ba 'karamin cigaba yakawoma 'kungiyarsuba, dan tsafi ya nuna cewa shigowar Ilham wannan 'kungiya babban cigabane agresu. Saboda haka Abigael ta tabbatarma ilham daga 'yau batada sauran 6acin rai danagane da wani d'an Adam adoron 'kasar nan, kuma daga yau zata fara jin dad'in rayuwarta batare da momynta ta takurataba, dama batada matsala da daddy, Hakeem kuwa sai Kallon ilham yake yanamata murmushi, itama murmushin take tare dajin dad'i acikin ranta. *********************** Tun daga wannan lokacin ilham tari'ka yin abinda taga dama fita kuwa idan zatayi Momy bata isa tahanataba, kaya sai wanda taga dama take sanyawa, mini siket da body hug, da wando pencil sune kayan fitar ilham zuwa unguwa daddy kuwa yana gani beta6a hanataba, saima duk abinda take bu'kata ya sakarmata mukullin ma'ajiyar kud'insa kullum ta eba yanda takeso bedamuba domin kud'in akwaisu. Mota ilham ta gayama daddynta tanaso yasiyamata, gaban momy suka ajiye magana ta fad'amashi irin wacce takeso yayimata Al'kawarin zuwan motar cikin wannan satin, Momy kuwa data yun'kura zatayi magana tanaso tahana amma bakinta sai yakasa furta kome kamar ansa kwad'o da makulli an rufemata baki. Saida suka gama maganarsu daddy yacema ilham taje ta shirya ze kaita shopping, aiko cike da murna tanufi d'akinta shima nashi d'akin yawuce. Sunfito cikin shiri daddyn ilham sanye cikin jaket masu ruwan 'kasa ilham kuma wani matsiyacin wando tasanya wanda yafito da duk wani shape na jikinta, sai wata riga wacce batada maraba da bes, kanta bako d'an kwali tayi parking d'in gashinta, sannan suka wuce momy tana zaune tana kallonsu tanason magana amma takasa. Sai bayan fitarsu wani kululun ba'kin ciki yatokaremata a wuya, da sauri tashige d'aki tafad'a gado tafashe da kukan ba'kin ciki. Kuka tayi sosai sannan tatashi jikinta duk ba kwari tafad'a toilet tayo Alwala ta kabbara sallar nafila, bayan tagama ta dad'e zaune tana addu'oi sannan taji sau'kin ba'kin cikin dake damunta. Cikin satin motar ilham ta 'karaso had'ad'iyar mota 'kirar camry dunkulalliyar kalar ja me duhu, ilham tayi farin ciki sosai, tun daga lokacin ta'karo wulakanci tacigaba da baza tsiyarta. Momy kuwa ta du'kufa da addu'a kullum ba dare ba rana, saboda tayi imanin addu'a itace takobin mumuni. Love u all Zee Elkaseem YARINYAR BABA [07:23 PM, 01-Oct-16] by ZAINAB ELKASEEM *YARINYAR* *BABA* _*Written & Edited*_ _*By Zee Mmn Khady*_ *```Just a short story```* *Page* 121-130 Haka rayuwa tacigaba da tafiya da ilham, dan yanzu ilham ta wuce duk 'yanda me karatu ke tunani yau kimanin shekarunta hudu cikin 'Kungiya likafa taci gaba, dan yanzu 'kungiya tafara sakar masu kud'i suna fantamawa a gari, sa6anin da, da ba'a basu kud'i saidai suna abinda sukaga dama batare da wani ko wata ya takura rayuwarsuba. Yayinda kullum 'kungiyarsu ta _*AJI DADIN RAYUWA*_ take 'kara ha66aka dan yanzu Abigael ta'kara samo masu salon tsafi, Inda arana sai susha jinin mutum a 'kalla biyu ko ukku. Ilham tasaki jikinta cikin 'kungiya, fantamawa take cikin Gari tana yanda taga dama batare da wani ya takurataba, dan yanda ilham ke hawa manyan motoci masu tsada da yanda take fita gari ko d'an gwamna Albarka, ko kad'an dadynta bekawoma ransa kome akan hakan ba, dan atunaninsa kud'i sane ilham ke amfani dasu, besan ilham ta dad'e da barin amfani da 'kud'insaba sai wanda 'kungiyar aji dad'i ke basu. Momy kuwa har yau har gobe tana son tsawatama ilham amma takasa, addu'a kullum take Allah yayimata maganin abin, kuma ya ku6utar da ilham daga sharrin shaid'an. ********************** _BAYAN AHEKARA UKKU_ Yau 'kungiya tayi taro na musamman wanda ba'a ta6ayin irinsaba, su ilham ne duddur'kushe gaban Abigael wacce ke zaune kan wata katafariyar kujerar tsafi, sanye take da ba'ka'ken kaya sai wani jan kyalle data d'aure 'kugunta dashi. Yayinda duk matan dake gurin suke d'aure da wani yadi me sil6i me zanen jikin maciji, iyakar d'aurin be wuce gwiwarsuba, sunyi d'aurin gaba dashi an d'aure daga baya. Mazan kuma sanye suke da gajerun wanduna kalar ja. Sun nutsu suna sauraren bayanin da Abigael kemasu na yanda 'kungiya zatasamu cigaba. Bayan ta gama ne taro na shirin tashi tace "sannan bayani na 'karshe 'kungiya na bu'katar jinin mahaifin ilham,....... Wani mummunan fad'uwar gaba ilham taji cikin tsananin firgici ta d'ago da dara-daran idanunta takai dubanta ga Abigael tana fad'in "no impossible bazan ta6a bayar da jinin dadyna ga 'wannan 'kungiyarba, kunsan kuwa yanda yake nunamin so.....ta fashe da wani mahaukacin kuka, dan gabanta yan 'kungiyar ke sadaukar da iyayensu ko 'yan'uwansu dan suji dad'i kuma da ita ake cin moriyar abun, yau kuma abun yafad'o kanta anya tanada hujjar hana jinin dadynta, "Nooooo...... Tafad'a da 'karfi, hakan yayi dai-dai da dawowar ruhinta jikinta, Momy tagani tsaye kanta tana tofa mata addu'o'i duk illahirin jikinta yajike da gumi kamar wacce aka watsama ruwa. Love u all Zee Elkaseem YARINYAR BABA [07:38 PM, 01-Oct-16] by ZAINAB ELKASEEM *YARINYAR* *BABA* _*Written & Edited*_ _*By Zee Mmn Khady*_ *```Just a short story```* *Page* 141-150 washe gari da misalin 'karfe tara na safe, Zaune suke kan dining suna breakfast Kowa naci hankalinsa kwance Amma banda ilham wacce taketa juya spoon d'in cikin cup d'in tea ba abunda ke zuciyarta sai tunanin yanda zata ku6utar da daddy daga hannun shugabar 'kungiyarsu Abigael. Duk abinda ilham keyi daddy na kula da halin datake ciki Saboda haka shima duk sai yaji yashiga damuwa lokaci guda Ya maida dubansa ga ilham yace _*"YARINYAR BABA*_ meke damunki? Da sauri takai dubanta ga daddy sannan tasaki fuskarta ta 'ka'karo wani busashshen murmushi Wanda zamu iya kira da ya'ke Wanda yafi kuka ciwo tace "Ba kome, cikin damuwa daddy Yakama hannunta ya had'e danashi cikin sigar rarrashi yake magana "Haba ilham ashe akwai wata damuwa dazata sameki ki 6oyemin. Ilham ta wasance tace wallahi daddy ba kome, kawai hakanan naji jikina ba dad'i amma yanzu ma naji kome ya wuce. Duk abinnan Momy na zaune tana kallonsu, bata sanyamasu bakiba, illah wani irin 6acin rai dake addabar zuciyarta Ganin yanda daddy kullum yake 'kara shagwa6a ilham Gashi itakuma yanzu bata iya hana kome. Cikin jin dad'i dady yace "yauwa ilham d'ita kinsan banison 6acin ranki ko kad'an, wani murmushi ilham tasaki wanda bekai cikiba. Dady yace "yanzu dai ki shirya mufita shan ice cream, ko kin washe dan banison kina shiga damuwa, 'Kila idan muka fita muka d'an zaga gari kin warware. Su Hassan da hussaina dake zaune sunajin duk yanda daddy ke rarrashin ilham kamar wata 'karamar yarinya, Wanda kosu beyima haka, suda suke 'kannenta wacce tabasu kusan 9 Year's, sukace "daddy muma muna zuwa.... Kafin su ida fad'a ya tari numfashinsu tare da d'aga masu hannu yace "kubari anjima driver ya kaiku banison 6ata lokaci.... Sunajin haka suka nufi d'akinsu suna turo baki dan sun dad'e da sanin yanda daddy ke nuna banbanci tsakaninsu da 'yar'uwarsu. Bayan sun wuce ne daddy ya kalli ilham yace bari inshiga toilet inyi wanka, Kema kije ki shirya, bejira jin amsar dazatabashiba yanufi toilet d'in Ilham tayi saurin binshi takamo hannunshi idanunta na zubar da hawaye tace dan Allah daddy kada kayi wankannan...... Dady yace dan me? Ilham tarasa amsar dazata bashi sai hawaye dake zuba daga idonta. Ganin batada niyyar yimashi magana yasa ya zare hannunshi daga nata tare da saka 'kafarshi toilet d'in. Love u all Zee Elkaseem YARINYAR BABA [07:45 PM, 01-Oct-16] by ZAINAB ELKASEEM *YARINYAR* *BABA* _*Written & Edited*_ _*By Zee Mmn Khady*_ *```Just a short story```* *Page* 131-140 lham lafiya mike damunki, tundaga d'akina nake jiyo ihunki kina fad'in impossible, meye baze yiyuba? Cikin tsananin rud'ewa jikinta na 'kyarma tace "ba kome kawai nayi wani mafarkine wanda ya tsoratani, Cike da damuwa momy tace ilham dole kiri'ka muyagun mafarkai ilham baki damu da addininkiba, baki damu da sallah ba barantana addu'a Nidai sai dai ince Allah kyauta. Haka momy tabar d'akin ilham zuciyarta cike da tunani barkatai, al'amarin ilham yana matu'kar tsoratata, gashi ko kad'an bata iya tsawatar mata. A ranar haka ilham ta wuni sukuku ba 'karfi jikinta ko kad'an tana tunanin yanda zata tseratar da daddynta daga sharrin Abigael, Bakin iya tunani tayi amma batasamu wata mafitaba. Washe gari kuka ilham tayini tanayi ta kulle kanta cikin d'aki, dan jiya 'kungiya ta tabbatar mata da kada ta kuskura tawuce kwana biyu bata bada jinin daddyntaba. Haka tayi kuka tagode Allah batare da wani yasaniba, har kanta yafara ciwo. _*BAYAN KWANA BIYU*_ Yaune kungiya ta ibarma ilham kada ta wuce bata kawo jinin mahaifintaba, _*Misalin 'karfe 3:00am na dare*_ Taron 'kungiyane kamar yanda suka saba, saidai yau tsai-tsaye suke yayinda Abigael ke zaune kan katafariyar kujerarta, ilham kuma tana dur'kushe gabanta tana sharar hawaye, Cikin tsananin 6acin rai Abigael ta kalli ilham tafara magana tare da mi'kewa tsaye tana nunata da sandar dake hannunta "Kisani ilham baki isa kisha jinin iyayen wasu ba kuma kiyi arzi'ki da kud'in kiji dad'in rayuwa kekuma kice baza'aji dad'i da jinin iyayenkiba. Tunda kika shigo cikin 'kungiyarnan yau tsawon shekara bakwai bamu nemi wani kwa'kkwaran Abu daga garekiba sai yau, saboda haka dole kibi umarni ko kinso, ko kin 'ki. Sannan kisani guri na'kara kure mana kinaso ki kawo mana cikas, tokisani gobe da daddynki yashiga toilet da niyyar yin wanka baze fito da raiba, dole ne musha jininsa yanda akasha jinin iyayen Kowa cikin wannan 'kungiya. Abigael nagama fad'in haka taro yatashi, ilham na dur'kushe inda take takasa ko motsin 'kirki sai wasu hawaye masu yaji ke zuba daga idanunta. 'Dago kan dazatayine taga wayam ba Kowa gurin ba Alamr mutane sun zauna, hakan ya tabbatar mata duk sun tafi, Wata uwar 'kara tayi sannan tafd'i gurin tana birgima, Jitayi andafata Hakeem tagani, cike da tausayawa yake rarrashinta, har a zuciyarshi yakejin ilham besan 6acin ranta amma yazasuyi dokar 'kungiyace dole tabi, haka Kowa yayi. Sai gab da dallar asuba sannan ilham da Hakeem sukabar gurin. Love u all Zee Elkaseem Yarinyar Baba [05:48 AM, 02-Oct-16] by ZAINAB ELKASEEM *YARINYAR* *BABA* _*Written & Edited*_ _*By Zee Mmn Khady*_ *```Just a short story```* *Page* 151-160 saka 'kafar daddy keda wuya cikin toilet d'in ya dorata akan wani jan abu me kama da bawon ayaba, wanda keda tsananin tsantsi sai kuma ya had'u da santsin tiles d'in dake toilet d'in 'kafarsa tayi gaba yayinda yakasa d'aga ta bayan, kawai sai jinsa yayi 'kasa tare da sakin wata razananniyar 'kara Da gudu Momy tayo kansa tana salati, amma kafin ta 'karaso inda yake har rai yayi halinsa. Wata irin razananniyar 'kara ilham tasaki lokacin da aka tabbatar mata da mutuwar daddynta, tashiga rera wani irin kuka na fitar hayyaci, Koke koke akayi sosai 'yan'uwan daddy Dana momy duk sunzo akayima daddy sutura aka kaishi makwancinsa. *su daddy an kwanta dama, oh,oh duniya kenan* ********************** Yau kwanan daddy bakwai da rasuwa ilham bataje meeting d'in 'kungiyaba, saboda haka 'kungiya tayi matsanancin fushi da ita, Yau da misalin 'karfe biyu da rabi na dare duk 'yan 'kungiyar sun halarta hada ilham, gurin yayi tsit Kowa yana jiran jin irin hukuncin da Abigael zatayima ilham dan ba wanda besan yanda Abigael take jiran zuwan ilham ba, Saboda tsarin 'kungiyarsu ba'a fashin zuwa meeting saboda hakan ba 'karamin cibaya yake kawomasuba rashin zuwan d'aya daga cikinsu. Cikin bala'i da matsanancin 6acin rai Abigael ke magana "ilham kina nema kikawo mamu na'kasu cikin wannan 'kungiyar tamu, a tarihin wannan 'kungiya yau tsawon shekaru goma sha biyu kenan da kafuwarta amma babu wanda yata6ayin fashin kwana biyu be halarci taroba, amma ke yau tsawon kwana bakwai bakizoba, sabida haka yanzu zamuyimaki hukunci dai-dai da laifinki. Sannan ta kalli sauran 'yan 'kungiyar tace kunsan duk wanda yayi fashin kwana d'aya bulala goma ce, saboda haka zamu had'a goma sau bakwai zamuyima ilham hukunci kamar yanda akema kowane d'an 'kungiya. Hakeem najin haka hankalinsa yayi matu'kar tashi dan yasan da'kyar idan akayima ilham bulala saba'in ta rayu saboda yasan azabar bulalar ana bugunka kamar ana zubama wuta ajiki. Saboda haka cikin tsananin tausayin ilham yafito ya dur'kusa gaban Abigael sannan ya had'e hannuwansa alamar Neman alfarma yace "ina neman alfarma daga gareki shugaba da a rangwantama ilham sakamakon jikinta baze iya d'aukar bulalar 'kungiya d'ai-d'ai har saba'in ba. Hakeem yanada 'kima a idon Abigael baze iya naman wani Abu tahanshiba, saboda haka aka sassautama ilham zuwa bulala hamsin. Ilham na dur'kushe gaban Abigael, Abigael ta nunata da hannu take wata igiya ta d'ad'd'aureta ta yanda ko motsin kirki bata iyawa, sannan tanunata da sandar tsafinta bulalace taji tanata sauka ajikinta me tsananin azaba batare dataga Wanda ke dukantaba. Haka akayimata bulala hamsin tanata ihu, bayan an gama ne, Abigael tace "sannan kuma hukuncin na 'karshe agareki muna bu'katar jinin momynki daga yau zuwa gobe, bamu buk'katar 6ata lokaci..... Love u all Zee Elkaseem YARUNYAR BABA [05:50 AM, 02-Oct-16] by ZAINAB ELKASEEM *YARINYAR* *BABA* _*Written & Edited*_ _*By Zee Mmn Khady*_ *```Just a short story```* *Page* 161-170 washe gari haka ilham ta tashi cikin tsananin tashin hankali, dan yanzu tariga tasan Momy kad'ai taragemata idan taba 'kyngiya jininta wane hali zasu shiga itada 'kannenta, Wani irin kuka tafashe dashi, kukan yinsa take kamar na fitar rai har batasan shigowar momy d'akin ba. Momy takai kimanin minti goma tsaye tanama ilham magana amma ilham batasan da zuwantaba, saboda haka zama tayi gefen gadon tare da dafa ilham d'in tace "ilham meke damunki,? Meyasa kike kuka haka,? Wani irin rud'u ilham tashiga dan batasan da zuwan momy d'akinba. Saboda haka batada amsar dazataba momy kawai sai tafad'a jikin Momy tacigaba da wani irin kuka me tsuma zuciya, Momy kuwa ganin ilham na kuka batasan lokacin da itama wasu zafafan hawaye suka zubo daga idanuntaba, tashiga rarrashin ilham dan a tunaninta ilham tana kukan rashin mahaifinta ne..... Haka sukayita kuka bame rarrashinsu, ilham dai tana kukan yanda Abigael takeson takawo jinin momy, itakuma momy tana kukan tausayin 'yarta dan tasan irin sha'kuwar dasukayi da mahaifinta. Ranar haka ilham tawuni baci ba sha, duk tabi tafita hayyacinta, momy tayi rarrashin harta gaji, tasamata ido. _*3:00am*_ na dare, duk yan 'kungiya sun halarta, yayinda ilham take dur'kushe gaban Abigael tanata kuka tana ro'konta akan tabarmata momynta kada takasheta, wata irin mahaukciyar dariya Abigael ta 6a66ake da ita, sannan ta d'ad'd'aure kamar bata ta6a koda fara'aba tace ilham kina wasa da 'karfin tsafin wannan 'kumgiyar amma yanzu zakiga abin mamaki. Momy na kwance kan katafaren gadonta tana bacci marar dad'i, duk tahad'a uban gumi sakamakon mafarkin datakeyi meban tsoro daban mamaki..... Abigael dake zaune kan katafariyar kujerar tsafinta tayi nuna wani iccen bedi dake nesa kad'an da gurin dasuke, saiga momy ta bayyana d'ad'd'aure jikin iccen anyimata mugun d'auri yanda ko motsin kirki bata iyawa. Abigael tayi nuni da momy tare da cewa ilham kalli can, Cikin sanyin jiki ilham takai dabanta ga inda Abigael ta nunamata Wani irin matsancin tashin hanakali tashiga sakamakon ganin momynta daure jikin iccen bedi gakuma wani 'katon mutum ya tunkareta da wata shar6e6eyar wu'ka da niyyar soka mata ita aciki. Ilham naganin haka batasaan lokacin datafasa wata uwar 'karaba tanufi gurin da gudun tsiya wanda ita kanta batasan tanadashiba, yayinda shima wanda ze kashe Momyn ya zura a guje yanufi momy da wu'ka tsirara a hannunsa. Amma kafin yakai ga momy ilham ta isa ta shige gaban momyn takareta, shikuma idanunshi sun rufe besan lokacin daya caka wukar da niyyar cakata a cikin momy, amma sai ya cakata a cikin ilham Lokacin tasaki wata mahaukaciyar 'kara wacce duk illahirin dajin saida ya amsa, tafad'i nan ba alamar numfashi tattare da ita. Lokacin momy tafarka daga mawuyacin baccin datake duk tahad'a uban gumi kamar an she'kamata ruwa, Lokacin kuma mugun mafarkin datayi da ilham yashiga dawomata a kwalwa. Cikin tsananin firgici tatashi ba abunda bakinta keyi sai addu'oi tanufi d'akin ilham dan ganin halin datake ciki. Love u all Zee Elkaseem YARINYAR BABA [05:52 AM, 02-Oct-16] by ZAINAB ELKASEEM *YARINYAR* *BABA* _*Written & Edited*_ _*By Zee Mmn Khady*_ *```Just a short story```* *Page* 171-180 Da hanzari momy ta Isa d'akin cikin tashin hankali dan ganin ilham kwance 'kasa tayi wata irin kwanciya wacce daganin wanda yayita kasan be cikin lafiyarsa koma ace babu rai tattare dashi, Ilham......ilham....ilham...momy tashiga jijjigata tana kiran sunanta, amma ba Alamar numfashi tattare da ita, cikin tsananin tashin hankali momy takira Ameeno me aikin ilham takama mata ilham suka kaita mota driver yaja suka nufi asibiti. Suna zuwa aka nufi emergency da ita wani likitane ya tabbatar masu da mutuwar ilham. Nan momy ta aza hannu aka tafashe da wani irin matsanancin kuka me ban tausayi, haka aka d'auko gawar ilham aka koma da ita gida, Bayan sunkoma ne momy tashiga kiran 'yan'uwanta dana daddyn ilham tana sanar dasu, cikin 'kan'kanin lokaci gidan yacika da jama'a haka akayima ilham sutura aka kaita kushewa. _*Oh ilham anshafe babinta tazama labari,*_ _*Ya Allah ka tsare mana 'ya'yanmu a duk inda suke, Allah karesu daga duk wani sharri na duniya Allah kabamu ikon tarbiyantar dasu tarbiya tagari*_. A gurin 'kungiya kuwa tun lokacin da 'yan 'kungiya sukaga yanda akyima ilham kisan wula'kanci duk sai hankalinsu yatashi dan basu ta6a manta ranar da aka kafa 'kungiya saida Abigael ta tabbatar masu babu cuta ba cutarwa ga 'yan 'kungiya, amma gashi yau an kashe 'yar'kungiyar kenan suma watarana za'a iya kashesu. Aiko nan suka shiga magan-ganu 'kasa-'kasa take suka yanke shawara tsakaninsu, aiko kamar had'a baki sukayo kan abigel suna fad'in bazamu ta6a yarda da kisan 'yar'uwarmuba, suka rufar mata da duka, kafin ta farga sunyimata laga-laga, saida suka tabbatar dabata numfashi sannan suka barta, amma meze faru suduka suka kasa matsawa daga inda suke, yayinda wani ba'kin haya'ki ya turni'ke gurin suduka suka shiga wani irin mawuyacin hali wanda ko nufashi basu iya maidawa....... Hakeem kuwa yana gefe ba abinda yake sai zubar da hawayen ba'kin cikin kisan da'akayima ilham d'insa. Yana kallon yanda 'yan kungiyar keta wahala cikin wannan ba'kin haya'kin me tsananin yaji. Love u all Zee Elkaseem YARINYAR BABA [05:52 AM, 02-Oct-16] by ZAINAB ELKASEEM *YARINYAR* *BABA* _*Written & Edited*_ _*By Zee Mmn Khady*_ *```Just a short story```* *Page* 181-200 haka sukacigaba da sha'kar azababben hayaki me d'aci da yaji cikin 'kan'kanin lokaci numfashinsu yafara d'aukewa, kafin kace me wasu dayawa daga ciki sun rasa rayuwarsu, Haka Abigael tacigaba da sarrafa tsafinta saida ta tabbatar da duk 'yan 'kungiyar sun mutu bame sauran numfashi sannan ta 6a66ake da wata mahaukaciyar dariya. A hankali Hakeem ya bud'e idanunshi wad'anda ko gani baya iyayi sosai, yacigaba da jan ciki yana matsawa daga inda yake, har ya isa inda wukar da aka kashe ilham take yade yasa hannu ya d'auko. Abigael kuwa tajuya bayanta, tanata zuba wata uwar mahaukaciyar dariya, dan ganin tayi nasarar kashe mutanen dasukayi niyyar kasheta, har Hakeem yazo gaf da ita batasan yazoba saboda tsananin sautin dariyar datake gagga6awa, dan yanzu burinta idan kome ya lafa zata sake sabbin yan kungi. Hakeem kuwa iya 'karfinsa ya da6ama Abigael wannan wu'kar gefen cikinta, wata matsananciyar 'kara tasaki tare da d'aga sandar tsafinta ta bugama hakeem a ka, shima wata uwar 'kara yasaki lokaci guda sukayi mutuwar kasko. _*Wannan shine 'karshen 'kungiyar aji dad'in rayuwa tare da 'yan 'kungiyar baki d'aya*_. Bayan kwana bakwai da rasuwar ilham, momy ta aiki Ameeno me aikin ilham kasuwa tasiyo mata cefane, kan hanyarta ta dawowa gida taga an dadda6e wani me siyar da jarida anata siye matsawa tayi itama dan ganema idonta, ganin hotunan su ilham 6aro-6aro cikin shigar yan mafiya yasa hankalinta yayi masifar tashi, kud'i tami'ka itama ta siyo sannan ta wuto gida. Bayan taba Hajiya cefanen tawuce d'akinsu can ta iske jummai me aiki dame aikin 'yan biyu, bata tsaya wata-wataba ta tattara yanata-yanata tace tom sai anjimanku ni aikina daga yau yakare gidannan, su jummai suka tambayeta dalili bata tsaya wani dogon bayaniba tami'ka masu jarida tafice ko bankwana batayima momyba tabar gidan. Su inna jummai ma koda suka fahimci abinda jaridar ta kunsa tattara yanasu-yanasu sukayi sukabar gidan tare da bawa momy jaridar. Koda momy ta karanta tayi kukan ba'kin ciki, 'karshe kuma tagodema Allah dayasa ilham ta mutu kafin ta kashesu, amma dukda haka tanamata addu'ar neman gafara gurin ubangiji itada mahaifinta. _*Alhmdulillahi Anan nakawo 'karshen wannan takaitaccen littafin nawa, ina fatan masu karatu sun ilmantu kuma sun nishand'antu sun kuma d'auki darussan dake ciki*_ Litatafan marubuciyar. 1)Siyasa ko soyayya 2)Duniya juyi 3)Halin girma 4)Gidan Asali 5)Autar Hajiya 6)Alhini 7Yarinyar baba. *ZANEN ZUCIYA* *Coming* *Soon* ```Kyakkyawar gaisuwa ga group members *Ciwon ya mace* *Zee Mmn khady fans nd novel*``` *Sai kunjini a sabon littafina bye* Love u all Zee Elkaseem By HAYATU BABA ZUBAIRU (admin Hayat hausa novels Hausa novels and fashion And Cool novel, makeup and cooking) WHATSAPP NO: 07039625239 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 2 of 2