Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 4
yi kyau, na jima ina son in sai miki kaya in ganki haka tamkar sauran yara, amma hakan ya faskara. Allah ya sakawa Ado da alkhairi, na fita cikin farin ciki, duk wanda ya sanni in ya kalle ni sai ya sake kallona, saboda mamakin kwalliyar da na yi, wasu kuma su ce iyen ba, an ci gayu cikin zuciyata kuwa ba wanda nake so daga ni irin Ado, yau dai ya ganni cikin gayu. Wasu Dattijai suna cikin siyan goro sai na ji muryar Sama'ila yana cewa, "Yammata muna son goro." Na kalle su cikin kunya, bayan an gama sayan goron na rusuna na gaishe su cikin ladabi. Ado ya ce a"a Sama'ila kaga mutuniyar taka ko? Yau kam duk kauyannan kin cinye 'yammata a kyawun kwalliya." Sama'ila ya ce,"Na yarda da kai.' Dadi ne ya rufe ni, na ce "ko dai kuna tsokana ta ne?" Ado ya ce, tunda ki ka fito tsakanin ki da Allah mu kadai ne muka yaba adon naki? Na yi dan murmushi sannan na ce, a'a Baba ma..........21......."S auran kalmar ta ki fitowa lokacin da na hango Baba Gaje ita da kawarta Dija suna dawowa daga biki, tuni su Ado suka gano ina cike da fargaba, sannan suka kalli inda nake kallo, ba su san Baba Gaje ba, amma duk sun yanke hukunci cewa ita ce, musamman Ado wanda ya ganta da dare, tana furta kalmar Kuluwa ina ki ka samo wadannan kayan? Cikin mamaki take magana, Ado ya shaidata a muryarta, don haka sai ya ce "Sannu Baba." Ya tsugunna shima Sama'ila sai ya tsugunna bata kalle su ba ni krum ta zuba wa idanu cike da masifa, tana karkada kai. Dija kuma tana fadin "Tabdijam, lallai yarinya ta rika." Ni kuwa tuni tsoro ya cika ni na soma kuka domin ban ta6a ganin fushinta irin na yau ba, don jikinta har 6ari yake, ta ce shin kai Ado ka ke ko wa? Ban ce ka fita hanyar ta ba?" Sama'ila ya ce, "Baba da aure muke sonta don Allah kiyi hakuri." Ta zaburo baki na kumfa "Ban hakura ba, na ce ban hakura ba iskanciin banza da wofi, na ce da ku aure zan mata? Tsinannu kun gama lalata 'yar uban wa zai aure ta?" Ado ya fusata ya kalle ta ya ce, Ni ne zan aureta." Ta kara kusanto shi"kai mara kunya ka fita daga inadunan in rufe ka kiyaye ni bar ganin ubanka ke da gari. Ado ya ce,"Baba insha Allahu sai na aure ta, ki rubuta ki ajiye sai na tsame ta daga wahalar da ki ke bata." Dija ma ta matso "kai dan sara sa'arka ce! ku ji mu da tsagera," Suka mike tsaye, Ado na cewa, "Yi hakuri Jidda, ki daina kuka kukanki yana soya raina." Baba Gaje wani tukuki ta ji cikin zuciyarta , ta cije yatsa sannan ta yi gaba fuu. Dija ma ta bita tana cewa, "Gaje gidan su zamu ke kai kashedi." Gaban Maigari suka zube, Baba Gaje ta saki kuka tana fadi "Maigari kun ne masu hukunci ya ya zaka yi da danka Ado wanda ke lalata min yarinya?" Dija ta yi zaraf ta ce, "Har batun cikin da ya yi mata kwanakin baya ki sanar da shi." Nan da na kuwa ta dad rushewa da kuka. Dija dama baki tuno min da wannan ba, Ranka ya dadw kwanaki har ciki ya yi mata cikin zuaran nan naku mai duhu, sai da kyar asibitin Garko suka cire shi, na ji tsoron kawo kara ne don naga ku ne masu garin amma sai naga an ci gaba ni dai ranka ya dade a shiga tsakanin su." Wakilin Maigari ya nuna ta "Ke ba mu son zancan wofi, Ado za ki ma sharri?" Maigari ya daga mishi hannu tare da cewa,"Dakata Wakili." Ya kalle ta "To baiwar Allah, kiyi hakuri zamu yi bincike kuma zan dau mataki. Ta ce, "Na gode, na gode." Ta mike suka tafi. Cikin dakin Baba Gajen suka yada zango sai sheka dariya suke yi, Gaje tana ta zugawa Dija godiya da dabarar da ta kawo mata. Shi ko Maigari Sai ya dubi Wakili da Liman ya ce, Dan yau zaya iya aikata abin da ya fi haka, shi yasa na ce ba zai je karatun nan birni ba, Liman ya ce ni kuma sam ban yarda Ado za ya aikata haka [18/09 6:50 pm] Inna👬👫: Idan rana tafito 22.......Su kam karkashin wata bishiya suka zauna suna hangen ruwan daga in da suke. M.B yana jefa 'yan kananan dutsuna cikin ruwa, ya kalli Ado ya ce Adamu yarinyar can da ta wuce kamar itama 'yar gidan ku ce. Ado ya ce da ba ka santa ba? M.B ya ce ba duka kannanka na sani ba, 'yanmata da Bintu da Asma'u na sani." Ado ya ce, to ai sune 'yammatan, ita wannan da ka gani da ita zan aura, sai wasu matsaloli suka shigo, kuma ni na yi niyyar auranta ne don na taimaka mata bawai don so ba. Cikin ikon Allah da na sama zuciyata auranta a 'yan kwanakin da muka yi sai na samu kaina da soma sonta nan ya kwashe komai har da tarihin Jidda ya ba wa M.B Nan ya ji ya kara tausayin yarinyar sosai, ya kuma bawa Ado labarin turetan da ya yi dazun na. Bayan sun dawo cikin gari suka sake hangen ta dauke da tiren goro. M.B ya ce wai shin Ado yarinyar can bata da aikin da ya wuce talla ne?" "Kwarai kuwa. "In ji Ado,"Tana talla ne sau 4 a kowacce rana, safe, rana, yamma da kuma dare." Tausayinta ya kuma cika zuciyar M.B kazalika sai gata da daren dauke da tire. Ado ya ce, "In na jin takaicin halin da yarinyar take ciki, lokacin da na yi nufin taimaka mata sai na kara mata damuwa." Ya dubi M.B Muhammad tana zaman zamanta na jawo ta, na kimsa mata sona cikin zuciya, a karshe a ka raba mu don Allah ban zalince ta ba?" M.B ya ce "Ba ka zalince ta ba, kayi nufin taimakonta ne. Zan yi nazari nima na gani wane irin taimako zan mata?" *************23..... Komai na bikin M.B suna tafiya dai- dai, yanda Hjy ke rawar kai da ji da Ango tare da fidda kudi daga cikin jakarta take kashe su yana ba wa M.B mamaki, ban da yasan komai game da makarkashiyar da suke kulla mishi, to da zai karyata duk wanda ya zo mishi da batun cewa da wata manufa suke son auran shi da Basma. Don haka ya bi ya lika security a guraran da bai saka ba, domin kara samun cikakken rahoyan sirrin duk wata makakarkashiya. Akwai fatitiikan da za a yi kafin daurin auren, da kuma bayan daurin auran tun saura kwana 2 biki dangin mahaifiyar M.B da Kakarsa Haja suka bayyana birni cikin su har da Binto da kuma Ado, haka nan dangin Mahaifinshi daga Garko, Binyo kam ta tsinke da lamarin bikin 'yan birni, fadi take ina ma da Kulawa muka zo bikin nan ta sha kallon duniya, , Allah Sarki Haja ta ce wa zai barta? Binto ta ce ai zan kai mata wadannan hotunna ta gani ki ko kai mata in ji Haja, Allah yasa ina son yarinyar na so kwarai Ado ya aure ta, domin yanda yarinyar ke sha wuya nasan Ado zaya rike ta da amana zai kula da rayuwarta, Binto ta ce Baba ya yi saurin yanke hukunci koda yake ya ce shekaru da dama da suka gabata suka kulla alkawarin auran Yaya Ado da Aina, haka ne in ji Haja, amma ban gushe ba ina mata addu'a Allah ya bata wanda ya fini, amin in ji Binto. Hjy ta jawo aminiyarta cikin dai wato Kilishi ta maida kofa ta rufe tare da cewa kin san sirri dukkansu suka zauna bakin gado. Hjy Shuwa ta kalli Kilshi ta ce, "Kawata kinga dai yanda komai ke tafiya min daidai ko?", Kilishi dafa ta tare da cewa "Kawata na ta6a ki da alheri na kula sai dai menene shirinki na gaba?" Shuwa ta ce, "Shirina na gaba kuma na karshe shi ne kashe Bello, ta hanyar sa mishi gabu cikin abinci." Kilishi ta zuba mata idanu. "ZUWA yaushe za ki aikata haka?" Kilishi ta tambaye ta. "Da zaran anyi biki." In ji Shuwa. "Ba ki tsoron a zarge ta in abin ya yi wuri? Sannan Likitoci za su gano cewa ya ci guba wacce amsa a ki bada lokacin da kanwarki ta ji tuhuma ta yi yawa? Ta ce ke ce ki ka bata?" In ji Kilishi. Shuwa ta yi dan jim sannan ta ce,"Haka ne. Na so in yi wauta, zan bari sai sun dan kwana 2. Kilishi ta girgiza kai tare da yin murmushi. "Ya ya za ki yi da cikin da kanwar taki zata samu, musamman in an samu irin natattun cikin nan an yi an yi ya fita ya ki fita? Ina nufin dadewarsu za su kusanci juna kuma ciki zai iya shiga, kinga dan in ya zo duniya in bai gaji Kakanshi ba dole ne ya gaji dinbin dukiyar da ubansa ke da ita wadda ki ke burin kanwarki ta gada daga b.aya ki mallake." Shuwa baya"Haka ne kuma fa, lallai Kilshi kina da baiwa. To yazamuyi [19/09 9:15 am] Inna👬👫: Idan rana tafito 24..... Nan da nan Jami'an tsaro suka nufi gurin da mutumin ya fado, shi kuwa Ango tuni dangi suka zagaye shi don jin me ke faruwa? Lokacin da su Hjy Shuwa suka fahimci M.B ne ya yi harbin ba shi aka harba ba, sai suka cika da mamaki gami da tsoron me zai biyo baya? Lokacin da suka isa guri inda mutane suka yi cincirndo don ganin kowane ne Hjy Shuwa ta riko hannu M.B tana cewa me yake faru ne Bello? Ya ce," An turo shi ne don ya kashe ni?" Ta ce,"Su waye za su mana wannan dayan hukunci?", Ya ce "Sai Allah, shi ne kawai ya sani. Sai dai kada ki damu ko su wanene burinsu bai cika ba, kuma na sani zamu hadu dasu karo na 2. Jikinta na rawa "To bari in kira Dady in sanar dashi. "M.B ya ce "Hjy ki bar shi kawai, wannan Jami'an tsaro za su yi gaba dashi in yana da sauran rai ne ya musu bayanin dalilin sa na son kashe ni, in kuma ya mutu shi kenan sai in mun tsaya a gabn Ubangiji." Hjy Kilishi ta matso,"To ai dama karsa shi kayi domin barin irin wadannan a bayan kasa fitina ne." M.B ya yi murmushi ya kalli mutumin lkcn da Jami'an suke saka shi a mota, sannan ya dubi Hjy Kilishi"Da ina da wata dabara da zan iya yi lkcn da na hango shi wacce zan kama shi kon kare kaina bayan harbin to da ban harbe shi ba. Tilas ke sa mu harbi don mun fi son mu ji bayani daga bakin me laifi, kila ba shi kadai ba ne ta yiwu wasu suka sa shi da makamancin haka kin ga duk zamu ji'." Ya zuba hannuwanshi cikin aljihu "Hjy ku koma ciki lkcn tashi ya kusa, kada wannan ya dame ku, domin IDAN RANA TA FITO TAFIN HANNU BA YA KARE TA. HAKAN NAN ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA KO ANA RUWA MUZURAI SAI FA YA YI." Mar 7, 2015 Aisha Ummu Shureim Sa'eed 45.. Cikin sanyi jiki tare da tunaninko ya gano sune? Suka ce "Haka ne." 25.....Amarya dai tana can gurin kawaye suna lallashi ta don ita kuka ta kama riris, sannan ta kasa zuwa gurin suna dawowa gurin ta rugo ta rungume mijinta shi ko ya shiga lallashinta. Hjy Suwa ta kira mai abun magana ta ce ya sanar da kowa an gode za a tashi haka saboda wannan farmaki da aka kawo. Maimakon gidansu za su wuce kamar yanda a ka tsara daga gurin party ango da Amarya za a yi musu rakiya zuwa gidansu sai kawai a ka koma gida gaba daya in da suka iske mutanan gidan cirko-criko. Haja sai kuka take lkcn da su Ado suka zo mata da labarin dukkan su suna falo ne suna jiran zuwan su M.B bayan an gama jajantawa yana rungume da kafadun Haja yana lallashinta ya dubi Hjyr "Ina su Basma su zo mu tafi dare na kara yi." Nan take Hjy Tasa kuka," Gaskiya ba za kuje ba, ka sani ko ba shi kadai ba ne me nemn ran naka? Haka kawai kuma sai ku je can ku kadai su kashe mana kai a banza." Husna da Safina suka gurin Mahaifin su da ke tsaye yana saurarn kowa, Dady kada ka bar Bros ya tafi fa." Ya dubi Hjy." Kada wannan farmakin ya dame ku, don ba zai zama barazana ko tsoratarwa a gurin dan Sanda kamar ni ba, zamana ni kadai ko zamana cikin mutane ba shi ne zai kare ni daga mutuwa ba, ku fahimci wanna ni ba zan canza da komai ba kuma ba zan kasa walwa ba don wannan. Haja ta ce "A'a ka dai zauna tukunna Muhammadu kada su kashe min kai Marayan Allah, me ka tare musu?" Ta sake sushewa da kuka tare da cewa "Ni shi yasa birni bata ban sha'awa, yanzu ka ji an kashe mutum."Su Ado suka ce "Da ka dan saura tukunna." 26... Husna da Safina suka kyale mahaifinsu suka je suka rungume Yayan nasu suna jijjiga shi"Don Allah Bros kada ka tafi ka ji Dady ka ce wani abu mana." Dadyn ya yi gyaran murya sannan ya ce "Hakika Bello ya fiku gaskiya, domin kuwa duk wata kariya da wani dan Adam zai baka tana bayan ta Ubangiji, ku lura mana duk cikar gurin da ku ke da yawunku bai sa kun ga mai harin nashi ba sai shi kansa, Allah ya kare shi kuma ya kare kansa." Dady ya kalli M.B "Bello kai kuma sai ka hakura na kwana 2 saboda an ce masu rinjaye sune sama, kai da ni ne muke tare amma duk falon nan basu amince ka je gidanka yau ba." M.B yana dariya ya daga hannuwa sama na bi, suka kwashe da dariya shima yana murmushi don da wuya kaga M.B yana kyalkyata dariya. Ya kal [19/09 6:51 pm] Inna👬👫: Idan rana tafito 27...Tana shiga gurin Hajiya Shuwa nan take ta hau ta da zagi"Yar iska me ki ka je yi gurinsa? Ban gargade ki ba ne?" Basma ta ce, "Na je fa gaishe shi ne." Ta ce "To ban ce ki dinga zuwa gurinsa ba, don na gaya miki kada ma ki yarda da shi ko gidan ki ka ji." "To" kawai Basma ta ce amma cikin zuciyarta cewa take yi ai mijina ne kuma ba zaki haramta min abnda Allah ya halasta min ba. Basma zata juya Hjy ta ce "Ina za ki?" Zan je dakin su Husna ne, a'a cewar Hjyn shigo nan ki zauna. Duk da wannan gadin da Hjy ke yi wa Basma ta saka ta a dakinta sun zauna tamkar kurame, bai hana Basma ciro wayarta ba shi ta turawa text tana me shaida mishi irin tsantar son da take mishi tare kuma da shaida mishi cewa ta yi mafarkin tana kwance bisa kirjinsa, le6unnanshi yasa kan nata yana mata sunba ta bn mamaki, ina son ganina haka a gaske zan samu? Lokacin da sakon ya same shi murmushi ya yi duk da ya ji dadi bai hana shi ji a cikin zuciyarshi banbarakwai ba, a son zuciyarshi shi ne zaya fara kai kokon bararshi gare ta matsayinshi na miji duk da addini ba ya hana ba ne matsayinshi na mijinta. Sai ya rubuta cewa, Ni na ki ne Basma yanda na tabbatar da cewa ke tawa ce, daina mafarkina zamu yi zama na har abada insha Allah. Zamu kasance cikin yanayin da yafi mafarkinki. Ya tura mata tana gama karantawa ta yi murmushi tare da cewa, my D kenan, haka nan suka ci gaba da yiwa juna musayar kalaman so da kauna har zuwa lkcn yin Sallah, inda M.B ya fita. 28.... Inda M.B ya fiya. Ranar da suka cika sati daya, ranar Dady ya rike wuta sai sun tare kuma ranar ne suka tare. Kafin a kaita sai da Hjy da kawarta Kilishi suka saka Basma a gaba kan cewa kada ta kuskura ta ba da kanta ga angon nata, wai ta bijire mishi ta wannan fanni. Basma ta dubi Yarta ta ce "Anty har yanzun kin kasa sanar dani dalilinki na hada wannan lamarin?" Kilishi ta ce, "Kin kusan gama aikinki, kuma nan za ki ji komai." Basma ta ce "Shi kenan." Ko kayan gyaran Amarya da ake hadawa ita dai da kudinta ta siya kuma a 6oye. Amarya ta gama sakin jiki yau za su 6arji Soyayya ita da mijinta, amma ga mamakinta 12:30 bata ji shigowar Maigidan nata ba, gashi tuni take neman layinshi amma ya ki shiga, fitowa cikin falon tayi don duba dakinshi kofar na kulle don haka ta daga labulan window shi ta hango kwance rigingine filo manne a kirjinshi yana bacci. Sai kawai ta juya ta koma dakinta cikin sanyin jiki. Washegari bayan ya dawo daga Masallaci dakinta ya nufo ta yi dai- dai bisa gadonta me shegen kyau, ya maida wani abu da ya yi yunkurin taso masa sannan ya yi karfin halin karasawa ya saka hannunshi ya girgiza kafadarta a hankali. Mika ta yi wadda dole tasa shi kau da kan shi gefe, domin ganin yanda surarta ta matantaka ta firgita shi, ta bude idanunta a hankali ta zuba su kan fuskar M.B tare da furta "My D." ya dube ta "Amarya tashi kiyi sallah ko?" Ta tashi zaune cikin yanayi na shagwa6a ta ce, shi ne jiya ka bar ni ni kadai ina ta jin tsoro. Ya dan ware idanu cikin murmushi, sorry my dear, jiyan nan na gaji sosai ban san lkcn da bacci ya kwashe ni ba, yanzun dai tashi ki je ki yi sallah kafin gari ya yi haske, kin ji ko? Ta yunkura ta nufi bayinta da kallo ya bita yana son fantama amarci da abar son tasa amma zuciyarsa ta kasa amincewa da hakikanin son da take masa, ma'ana ya sani tana sonshi amma me yasa ta kasa sanar dashi game da shirin da Yayarta ke yi kansa? Koda yake ya sani bata san rayuwarshi ake nema ba, sannan bai san me zayo biyo baya ba cikin zaman nasu, sam bai ji dawowarta ba sai dai ya ji muryata tana cewa "My D, baka zauna ba." Ya ce dama zan je kicin ne don shirya mana breakfast, ya nufi fita ta ce my D ba mu da masu aiki ne? ya girgiza kai tare da cewa bana son masu aiki masu yi mana gadi kawai sun isa, amma duk aikin cikin gida zamu yi kayanmu ta marairaice fuska ban fa iya aiki ba musamman girki ka kuma sani ya ce ni zan yi mana kada ki damu maimakon mu dauki masu aiki tunda ba dadewa za a yi ba yana fadin haka ya fita [19/09 7:52 pm] Inna👬👫: Idan rana tafito 29... Sai dai su ba kamar mutan birni ba wai har da kungiyar da suke kwatarwa yara 'yancin kai kamar yanda Ado ya sha bani lbr. Ina cikin wannan halin ne sai na ji muryarshi tana fadin subahanallah, 'yammaya me ya yi zafi..... Na dube shi da jayayan idanuna babu komai ya shiga waige-waige can ya dube ni zo muje karkashin bishiyar can in ji damuwar ki. Wala Allah ko zan iya taimaka miki. Na girgiza kai zai yi wuya ka iya taimaka min sai dai ka taya ni da addu'a ya ce kada ki zama mai gardama a gare ni kila ni ne sanadin fitarji cikin matsalar. Jin haka sai bn kuma magana ba, ya yi gaba na bishi. Komai na karanto mishi har zuwa yau dinnan shiru ya yi cikin tausayawa tare da tunanin ita ina zai fara?" Can ya yi wani tunani kuma ya gamsu da cewa za ya gwada hakan. Sai ya ce Kuluwa zan taimake ki hanya ta farko shi ne zan nemi Baba Gaje in bata kudi masu yawa ta bani ke in tafi dake can birni ki dinga taya matata aiki, zan saki Makaranta Islamiyya da boko kiyi ilimi shi kenan kin zama yar birni sam bn san sanda na shiga sheka dariya ba, na dube shi Allah da gaske ka ke yi kuma?" Shima cikin murmushu ya ce sosai ma na ce wai wa ka ganni a birn?" Ya ce balle kin shiga Makaranta, na yi ajiyar zuciya na yi shiru ina tunanin yanda zan zama 'yar birnu, can kuma na tuna Baba Gaje fa zata iya hana ni zuwa, nan take sai raina ya yi duhu cikin sanyin jiki ya ce menene kuma?" Na dube shi in ta ki yarda fa?" Ya ce sai mu canza dabara. Na ce to Allah ya dora ni a kanta, domin duk kudin da za a bata in ta tuna cewa zan iya jin dadin rayuwa ta zata ki amincewa ya ce kada ki damu Allah yana tare da mu na ce to Allah ya shige mana gaba. Ya tashi tare da cewa ki koma gida kada ki yarda ki daga hankalinki kan wannan insha Allah tare zamu bar garin nan. Ina tsaye ina kallon dan birni ya tafi har ya 6ace wa ganina kai ko wannan ya ishe 30. Ya ce kada ki damu Allah yana tare da mu na ce to Allah ya shige mana gaba. Ya tashi tare da cewa ki koma gida kada ki yarda ki daga hankalinki kan wanna insha Allah tare zamu bar garin nan., Ina tsaye ina kallon dan birni ya tafi har ya 6ace wa ganina kai ko wannan ya ishe ni alfahari duk cikin kauyannan akwai wadda dan birninan ya ta6a kallo ma balle magana kazalika babu wadda Ado ya ta6a cewa yana so sai dai ni, don ko Aina'u bashi aka yi. Daga nan bn nufi gida ba na koma gurin su Binto ina tare da su har muka kai Amarya muka fito waje muna ta gada, duk sanda na tuno gida sai na ji tamkar kada na koma, sannan na samu kaina da taurarewa cikin zuciyata ina fadin ai dama yau kawaye gidan amarya suke kwana sai gobe in anyi rufi da budar kai bayan an gama jere sannan kowa zai watse don haka a sai na yi kwanciyata. Da safe muna cikin karyawa Laure ta shigo tana cewa "Kuluwa ga Babanki nan a waje ya zo neman ki na fito da sauri na rusuna ina kwana Baba?" Ya ce lafiya Jidda nan ki ka kwana?" Na ce I ya ce to shi ne ba ki zo kin shaida min ba? Sanin kanki ne zan damu na rike hannunsa to i hakuri Baba jiyan na neme ka bn ganka ba nan na koro masa labarin duk yanda muka yi dasu Baba Gaje har zuwa batun dan birni Baba ya ce anya zan bari kiyi nesa da ni Jdda? Ke ce kurum ki ke kwantar min da hankali, na ce in ba dama ko Baba Gaje ta bari ni sai na fasa, muka nufi hanyar gida yana cewa aure ne ya zama dole Jidda shi ne kurum zai raba mu. Sallamar dan birni ce ta dira a kunnunwanmu, Baba ya amsa masa dan birni ya tsugunna ya gaida shi sannan ya dube Jidda Baba ne wannan ko na ce i shi ne Baba kaga wannan shi ne dan birni da nake fada maka. Baba ya ce af towo yanzu nan take yi min zancanka, dan birni ya shiga sanar da Abbana, nufinshi na son taimaka mini. Baba dai ya yi shiru na sani yana jinjina rabuwa da ni ne can ya ce to bari dai muji ta bakin Babar tata dan birni ya ce to gobe ya zo zaya wuce ya ce shi ba bako ba ne a garin dan gari ne dan Maigari wan mahaifiyarsa ne. Baba ya ce haba yaro ai ni nasan ka kai ne dai baka saniba. ..... Don Allah yan uwa kuyi hakuri wlh book 1 din anyi sallakel dayawa wlh dasani da sallakel da yawa haka da ban faraba Banida karshen bk 1 amma 2&3 akai infara 2 din ko inbari? Ko akai wanda yake karshe ya cigaba pss An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download

Chapter 3 of 4