musu nasihohi akan su hade kansu su kyautatawa mijinsu
Yanda aka watse aka bar zainabu ita d'aya tsuru sai abin yabata tsoro bataji motsin komiba saina karar AC data jiyo acan falo Shuuuuu
Banda Allah yasa tafara sabo da jin karar na,urar data kudunduna don tsoro to tanajin karar agidan momy
Gadanga sai karfe taran dare yasho bangaren nata mudine yakawoshi yanata masa tsiya ahanya
Dayake saida suka tsaya a yahuxa suya yasai kaji guda biyar kulli daya aka saka uku dayan kullin kuma aka saka biyu shine na khalisat
Kai tsaye part dinta yafara shiga
Bata falon saiya nufi bedroom yaganota kwance tsakiyar gado tafara bacci
Xumbur ta mike jin shigowarsa
Atsaye kerere yamiko mata kunshin ledarta
"Ga wannan kici Amma ki tabbatar kinyi sallah kafin ki kwanta dan in ana tare dani dole aringa ibada ba fashi
Ya dire mata yajuya abinsa yace "saida safe.
Tabishi da kallon takaici don tayi tsammanin adakinta xaifara kwana lallai wannan ai dixgine salon yarinya ta rainata xai nuna mara rashin matsayinta knn
Takaici yasa batabi takan namanba ma balle sallar ishsha,in dake kanta nan ta bingire tahau baccinta dan ita kam akwai saurin bacci
Ita kuwa zainabu idonta ko gexau ba alamun bacci ina zata iya bacci bataga gadanga yashigo ba
Saida tashi sallamarsa yashiga kana taja ajiyar zcy wanda saida yajita
Yazauna kusa da ita da murmushinsa yajata jikinsa yace "my zee kingaji da jiran angwanki ko yi hkr naji kina ajiyar zcy bakiyi fushiba ko?
Tagirgixa kai tana murmushi
Ya zame mata mayafin yakura mata idanu
"Kai my zee kinganki kuwa haka momy tagyaramin ke
Yahau shafa fatar jikinta
Yana murxa yatsunta dayasha qunshi ja
Tayi lakwas ajikinsa hhhmm su zee anji tab'i anyi likimoπ
Saida taji zai wuce gona da iri kana ta rike hannunsa dake ckn rigarta wanda yake gogar breziyyarya
Yace mata "kinyi sallah ?
Tace "a,a kai nake jira kazo sai inyi don bansan inda zanshiga insamo bandakibane
Yace "kaji matar gida daba saiki tabi bulayiba
Yajanyo hannunta yasauko da ita dg kan gadon yanufi toilet da ita yanunnuna mata komi yabarota tana alwala
Saida ta dauro alwalar tafito kana shima yashiga yadauro tashi
Kafin yazo tafara sallarta yajirata ta idar
kana suka bada farali na sallar nafila wacce ta wajaba akansu
Koda suka idar yadafa kanta yaringa kwararo musu addu,o,i
Gadanga ashe haka kake da saniπ€
Saida yaciyarta naman kazar nan ta koshi ya diddika mata yoghurt dakyar ta iya cin rabin kazarma
Da kansa yasungumeta yakaita gado
Yace "kirage kayan jikinki ko kyaji dadin bacci.
Hhhhh kokaji dadin ci daiππ·
Itakam yau gabanta keta faduwa don tasan anxo gurin fatanta dai Allah yasa Aliyunta yai mata da sauki a yau β¦β¦
*Auntyn Sayyada da shahida ce*ππΌ
*ALI GADANGA...*
πΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉ
*Short Story*
*Nabilancy Luv*π
(Auntyn S&S)
Page
2β£6β£
Ali gadanga jarmai sha yaki Ango gun zainabu da khalisat!
Yau yasha Amarci wanda yamantarshi abubuwa da dama ciki harda mancewa da wata matar dayake da ita wai khalisat
Tabbas Aure akwai dadi kusan kwana yayi yana gurxar Amaryarsa yana jiyar da kansa dadi yayinda ita takeshan wuya amatsayinta na cikakkiyar mace
Tasha kuka da ihu haka yasha cixo da yakushi duk don azabar datakeji amma gadanga bai bartaba sai gefin asubahi
Ajigace baccin yadauketa tanata ajiyar xiciya tabπ€ ai dole Zee taga banu sau hudu fa yayi yana hutawa
Ahhhh!banga laifin angoba don lafiyayyene
Kuma jarumi
Koda aka kira assalatu shiya fara tashi yashige toilet yayi wankan tsarki tareda dauro alwala yazo yayi nafilfilinsa
Yatashi zainabu don tayi wanka tayo alwala
Amma takasa tashi daya fahimta saiya dauketa calak yakaita har ckn kwami yace tayo wanka tayi alwala yana jiranta afalo
Dayake yahada mata ruwan dumin saita fara, ganin yafuta domin baxata iya agabansaba don kunya
Cikin mintina takammala ta fito ta tararsa akan sallaya yana tasbihi
Tajira doguwar riga tasaka hijabi tazo tabi sahu
Da suka idar ta gaidashi akunyace
Ya amsa yana me shi mata albarka " zainabu Allah yayi mk albarka Allah yabaki aljanna yakuma baki yara masu kyakykyawar tarbiyya irin taki da ace haka kowacce mace budurwa take rike budurcinta bata yadashi a kwararo tabbas da mata sunburge agun maxajensu kuma da sun xama abin koyi naji dadi sosai dana sami abar sona acikakkiyar mace fatana dai Allah yabamu yaya masu albarka
Ahankali tace "Amin, itakanta tayi farin ckn hakan taringa murmushi kasa kasa
Da kansa yahada musu abin kari
Sai wajen karfe sha daya na safe kana yashiga bangaren khalisat ba dan ransa yasoba don dai yashiga yafutarda hakkine kawai don ko babu komi inyashiga yaga yata kwana zai fita agun ubangiji
Daya shiga yaita mata sallama yaji shiru yakutsa kansa dakinta yaganta abararraje akan gado sai shararr bacci takeyi
Yabubbuga gadon tayi firgigit ta tashi
Haushine fal aranta nayanda yatafi jiya da dare yabarta babu wani tarayraya ko wani making love amatsayinta na yar,uwarsa
Ta kauda kanta gefe ko gaisuwa bai samuba
Yace "ke baxuwa nayi kiyimin shan qamshiba naxone inga ko kina bukatar wani abun da bakidashi akicin insiya miki sbd infita hakki.
Ta yatsina fuska tace "ni ai babu abinda nakeso ayanzu bayaga mijina kuma tunda yaimin nisa shikenan . Karasa maganar da xumbura bakinta
Yace "tabbas nayi mk nisa inma zaki cireni arai gara ki cire.
Tace "haka kace ?
Ranta abace
Yace da gadara "eh haka nace din ko har kin manta irin karan tsanar da kk doramin ada can
Tayi kasa da kanta
Yaci gaba "ai banxaci akwai ranar da har zaki budi baki kinuna muradinki muraran akainaba
Aidama duk mutimin da akace yasaba harka to tabbas inya dade baiyiba to akwai matsala dole maita ta fito muraran toki sani gara ma tun wuri yawunki yakoma don kwalelenki ni din mallakin xainabu ne
Inkinga zakiyi xaman gadi tokiyi baxan matsa mk ba zankuma fita hakkinki ta gun abinci da tufafi amma kisani bakiyimin ba sbd kin gama xubda mutumci da darajar da Allah yayi mk awaje gun maxan banxa dan haka ki kama bakinki tam ! Yaja tsaki yafice
Tabishi da kallo xa dacin rai
Harda hawayenta to me Aliyu kenufi wato knn saidai yakalleta baxai lasa mata xumaba knn tab aiko walh bai isaba dan ko da halin danbe saiya bata hakkinsa ko ayi uwar watsi bari kwananta yaxo
Takira kairat awaya take sanar mata
Khairat tace " to me xance mk khalisat ai kuma banda tacewa akanki tunda baxaki nemi taimakon malamaiba nikam saidai inbaki hkr ko insa ido...kiyi hkr kawata shawararki nakeso ko yaya take natuba
Khairat tace "hhhmmm to niyanzu me xance? Yaushene xai dawo dakinki ?
Khalisat tace " wama yasani bai min bayaniba sbd banda matsayi
Khairat tahau fada "walh kada kibari namiji yarainaki kawata tun wuri ki kwato "yancinki kafin kixama bora tunda baxakiyi asiriba
Khalisat tace ckn kwantar da murya "to yaxanyi _plz give me gud advise_
khairat tace "to nikam dai solution daya yakamata kifara kafin musan mezamuyi dg baya kiringa kissa kala kala tarinjayarsa sannan kizama mekwantar da murya agunsa da biyayya kiringa shige masa da nuna masa dirinki me kyau tahanyar bayyanawa inya shigo kuma kice lallai lallai kinaso yadawo dakinki agobe kokuma ki gayawa su dady sbd inkika barshi zai iya sati kuma tunda tare aka kawoku kinga matsayinku daya ba uwargida acknku duk amarene kada kibari ace itace gaba dakema ato. π
Khalisat tace to kawata duk yadda ake ck zangaya mk nagode
Nan sukai sallama taxabga uban tagumi tana tunanin Anya wannan hanyar zata b'ille mata kuwaβ¦β¦??
*Auntyn Sayyada da Shahida ce*ππΌ
*ALI GADANGA...*
πΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉ
*Short Story*
*Nabilancy Luv*π
(Auntyn S&S)
Page
2β£7β£
Kwance suke Ackn bargo suna manne da juna zainabu ta shige jikinsa sosai tana magana da shagwaba "Dan Allah Aliyunah kada karabu dani ina sonka karikeni amana kaga ni marayniyace inka rabu dani mutuwa xanyi dan baxan juri zama aduniya babu kai atare dani ba kada kajuyan baya nan gaba don..β¦β¦ yatoshe mata baki da hannunsa
Dayan hannun kuma yahau shafa mata baya dama ba kaya ajikinsu
"Kiyi shiru Abunah kidaina zancen rabuwa atsakaninmu ina mk son da babu wacce zan iya yiwashi arayuwa nima ba iya rayuwa zanyi babu ke ba kinjiyar dani dadin da bantaba jiba kuma baxan taba jiba inba ina taredakeba kuma nima fa marayan ne hargara ke to aname zan iya rabuwa dame bani gata ta marairaita ni haba zee ai babu wannan maganar
Ta kara kankameshi danjin dadin maganarsa
Yaji wani magana disu yana shigarsa yaji sha,a warsa data tafi na mintuna biyar baya tana shirin dawowa gashi zainab din tana masa wani abu akunne me kamar busar algaita
Ya birkitota samansa tayi rufto akan kirjinsa saida tace "wash!! Cikin kissa
Yafara tsotsar nashanun
Duk da takusa tafiya itanma amma saita hau kukan karya tana fadin "darling kabari sai anjima mana ina bukatar hutu haryanxufa bandaina jin zafin ba
Yasan tabbas tana juriya sbd ayanxun ma sau biyu yayi sha,aninsa kuma dagasken tanajin zafi to ai sai ahankali komi zai dawo normal
YYi dif ya kyaleta yana maida ajiyar zuciya amma ya ruk'umk'umeta ajikinsa kamar wanda za.a kwace masa ita
Yace mata "Zee ina jinki araina gashi gobe inaso inkwana bangaren khalisat...!!
Wani giiirrrr! Zainabu taji akirjinta banda ya ambaci sunan khalisat din ita tama mance da cewar ma tanada wata aba kishiya
Tayi diff tadaina masa wasan da take yi masa na shafa kansa da take
Yafahimci kishine ya motsa kokuma haushi taji sai yahaucewa
"Kingane ne bawai da wani abu nafada ba kodon ina so inje inji wani abu agunta a,a kawai dai nufina anan shine kinga itama budurwace dole innayi mk sati to itanma satin zan mata dole kuma bazan iya kwana bakwai banji dumin kiba kinga gara muyi dabara inyi mk biyu inje itanma inmata biyun inkuma kinaso inyi maki satin ne itanma inje inyi satin agunta to?
Tace ckn sanyin murya "a,a ka koma goben yafi gara muringa kwana bibbiyun amma wacece uwar gida ackn mu?
Yace "kece mana zainab ai itama tasani kowama yasani tsiranku da tazara kinfi wata da zama matata kana aka bani ita amatsayin mata duk da kunshigo gidannan tare kuma ubantane yabani gidannan yamaidani cikakken mutum hakan baxai saka inmaisheta uwar gidaba dole kece amatsayin babba zee sai abinda kk ce zamuyi dagani har ita
Ahhh!π€π
su gadanga ne haka? Ahhh lallai anji dadin wani guri dole akwantar da kai yamance zainabun daya lakada akan wani yamance zafin ransa toko dai ya canxane???
zainab datayi lakwas tace "to aikamata yayi kataramu agu daya kafada kowa yaji kuma kayi mana nasihohi akan zaman tare kakuma kakuma kafa mana dokokinka amatsayinka na mijinmu kokuwa ?
Yahau gyada kansa "tabbas hakane, kinmin tini kuma ayau za,ai hakan tashi muyi wanka sai inkirata taxo bangarenki ayi maganar.
******
Haka kuwa akai Domin daya shirya kai tsaye yashiga part din khalisat yasameta akwance akan doguwar kujera daganinta kuka tayi dan idonta yayi jajir alamar ansha kuka
Yace mata "ke lfyrki kuwa?
Ckn kissa tace "kaina ke ciwo tun daxu
Yace "oh sannu may be tunani yasa mk ciwon kan kinsan tunani dasa abu arai ba yanda bayayi kinsha magani?
Zuciyarta cike da takaicin maganarsa tace "eh nasha.
Hhhmmm gadanga kenan da gayya yafada dan yasan halin mata ko karya takeyima
Yace "to taso muje dakin zainabu zanyi magana daku duka?
Ko motsi batayi ba balle alamar zata tashin
Ransa yabaci yace "ko bakiji me nace mk bane?
Taji sarai rantane yabaci dajin hakan dan wannan ai wulakancine da xaice mata wani wai taje dakin zainabu aname dan akaskantar da ita.
Tace masa "naji mana gani nayi baka tausayina bayan nace banda lfy kuma sai asani tafiya wani waje in andamu ayi maganar dani ace ita tashigo part dina mana.
Yace "baxance taxo dinba ke nace kije nata kuma dole nace bajin ra,ayi ba.
Yajuya yace "maxa kibiyo bayana kitaho inba hakaba baxaki kara ganin kafata adakinkiba.
Dataga dagaske yake maganarsa ai tuni ta tashi tabishi xugui xugui da kananan kaya ajikinta mini skert da body hug me karamin hannu ta dameta kamar yadda siket din yamatseta kanta tasa hula ta yayi
Yaso yace takoma tasako hijab to amma gudun kada ta bata masa lokaci kuma gidan su kadaine yasa yakyaleta kawai
Zainabu tana zaune akan two siter kallo takeyi hankali akwance taji shigowarsu
Kwalliya ta tsala da wani swiss less takashe dauri mekama da ture kaga tsiya hhhhh dije ta iya koyar da dauri dakun gani dakunsha dariya to amma fa kayan yafito da ita dan tayi azababben kyau wanda ko randa aka kawota datasa galila bata kai yau kyauba
Khalisat kanta saida ta furgita da ganin kyan da zainabun tayi taita kallonta sai ayau tagano ashe haka zainab keda zallar kyau
Taringaji inama ita keda kyan zainabu da baxata zauna tayi rayuwar nigeria ba sai turai
Tayita kokwanto shinma gashin xainab dinne ta xuboshi har gadon baya ko itanma irin natane na kari ??
Bata samo amsar ba gadanga yakatseta da cewa
"Ke khalisat kinsan da cewa zainabu itace matata tafarko kuma bawai na karbi aurenki bane don bana sonta na karbi auren kine dan wasu manufofi ciki harda rufin asirinki...takatseshi
"Dakata dan Allah wannan fa kamar cinfuska kakeso kaimin knn dama kiran kenan?
Ya girgixa kai yace "banyi wannan maganar da nufin ci mk fuskaba na tarakune danna nunawa kowacce matsayinta aguna da kuma matsayinta ackn gidannan da kuma fadakar daku yanda zaku xauna dani lfy domin kunganni banason tashin hankali saidai inyazo adole nake karbarsa
Inaso ki sani ke zainabu kece amatsayin uwar gida kowa yasani babu me canxa hakan dan haka inaso kixama me kama girmanki kada kizamo kinxama me tada rigima atsakaninku duk da bansanki da tarxomaba haka kuma akiyaye bacin raina banida dadi duk wacce tayi badaidaiba zan mata hukunci me tsanani sannan ku hade kanku ku hade kanku inhar kunason zama dani.
Zainab tace "to naji insha Allah zan kiyaye.
Yajuyo kan khalisat da taketa hade haden rai yace mata
"Kema nadawo kanki inaso amatsayinki na karama kece karama yazamo kinbata girma kuma banason yaxama kinxamo me tada min fitina don baxanyi tolerating nonsens daga garekiba nasanki nasan halinki nan gidan Aurene bawai gidan haya ko gidan zaman kai ko gaban iyaye da za.ayi iya shege ba dolene ayi biyayya in anason zaman lfy dan haka kisani uwar gida zainabu ta yanke shawarar indawo dakinki agobe kawai tanaso inringa muku kwana bibbiyu kawai dan haka saiki gode mata data zamo uwar gida agunki me adalci β¦β¦
Kai gadanga an aiya wulakanci da cin fuskafa ππ
Su khalisat anshaka ankasa hkr ta karkace baki tareda jan tsaki tace "Allah ya kiyaye inyi godiya gun wannan kucakar yarin...
Ya mike afusace zaikai mari tuni zee tayi saurin rikoshi tana fad"haba habibi saurin fushi ba naka bane bakyau dukan macen Aure kayi hkr shi yaro hakuri ake dashi akoyaushe. Kambu π
π€π€ zee ta jangwalo rigima
Khalisat ta nunata "ke bakauyiya ki iya bakinki niba yarinya bace mara aji irinki yarinya tana can kauye adakin kasa me rufin kara
Zainabu taso ta mayar mata dacewa "ita me ajice tunda ba sadaka aka badataba to amma ba dama dan gadanga ya hankada khalisat din waje yana mata fada kamar yadoketa
Zainabu harda kwallarta najin xafin maganar khalisat tabbas dole tazama me baki bazata bari taringa taba mata iyayeba don iyaye sunfi komi taci darajar gadanga amma ajuri xuwa rafi β¦β¦
_Muje zuwa fans_
*ALI GADANGA...*
πΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉ
*Short Story*
*Nabilancy Luv*π
(Auntyn S&S)
Page
2β£8β£
Aliyu Gadanga yadawo kusada Zainabu yana rarrashinta ganin tana hawaye
Duk yabi yarikice baya son yaganta adamuwa
Yaji duk tsanar khalisat takaru aransa
Saida yaga ta hkr ta daina xubda hawayen kana hankalinsa yakwanta yajata xuwa dakinsa don yakara mata rarrashin na musamman
Itako khalisat zarya taringayi afalo tana cizar yatsa domin wannan abu yatsaya mata arai wai yau ita gadanga zai mara sbd wata? Yau ita akaiwa cin fuska
Saida ta zubda hawayen bakin ciki kana taji ranta yai sanyi wannan Auran kuwa zata iyashi? Ta tambayi zcyrta
Zaki iya mana amma inkin kwantar da murya!!!,inkin ringa tausasa kalaminki!,inkin zamo mebin mijinki,!!!inkin zamo meyiwa mijinki ladabi da biyayya!!!uwa uba inkin xamo me rokon Allah akan yarinjayo mk zuciyarsa kanki!!!!...
Ta zauna tayi tagumi wadannan zantukan nayawo aranta wato dai wadannan sune mafitar?
Tabbas ma kuwa!!! Zcyrta ta bata amsa da compedence
Tahau gyada kanta ta gamsu knn
Tace Afili " Aliyu ina sonka zanzamo meyin biyayya agunka dabin maganarka Amma ta yaya za.ai kasoni kamar yadda nake sonka?? Meyasa baka sona ne Aliyu?why??
Nasan ninaja komi tun farko,to amma ai komi yawuce.
Da komin ya wuce kintaba kwantar da kai agabansa kin nemi yafiyarsa??
Dummm!!gabanta yabuga bantaba fa!! Tabaiwa kanta amsa
Lallai yakamata tayi hakan shima yana ckn kissar da kawarta tace taringayi wani namijin yanada zcyr tausayi da raguwar zuciya akan mace to shin Aliyun nada tausan kuwa???
Batada wannan amsar ita dai kawai taci damarar samo soyayyarta kawai shine
Tayi murmushi data tuna cewar ma gobe nata ne
Saikuma ta hade ranta data tuna cewar wai waccan yar kauyen ce tabada umarnin yadawo mata, tana nufin knn ita ishashshiya ce agun miji watoma baida ra,ayin kansa sai nata lallai saitayi da gaske kan yarinyar can inba hakaba xata mallake gidan itako baxata juri iskancin kishiyaba duk da bata mata kallon kishiya sai kallon yar Aiki yar kauye.
Da dare masoyan suna manne da juna tayi lakwas ajikinsa tana masa shagwabarta
"Yanzu Mijina gobe baxanji dumin jikin kaba nawata xakaji bani ba...
Ya toshe mata baki yana cewa "hakanace mk zanji dumin wata ? Kinga alamar ina muradin jikinta ne ? Itanma tasan ban damu da komi nataba ki kwantar da hankalinki ke kadai nakewa kallon mace kuma ke kadai ce zanwa so baxan hada sonki dana wata ba fatana ma kece uwar "yayana
Ta lumshe idanunta taji dadi har ranta
Hhhmmm mata da kishi ake haba zee yakamatafa kiji tausan yar uwarki mace kada kishin mijinki yarufe mk ido,domin ma khalisat tafiki bukatar abar, tunda tarigaki d'and'anar bananar gadangan!!Au kada zainabu taji nahada fadaπ·ππΌπ
π
*******Aranar da Angonta zai dawo dakinta tayita rawar jikin yin komi
Akayi masa girki kala uku duk bawani dahuwa yayi yanda akeso ba tunda ba.a iya ba ba girki take agidaba ansaba cin na "yan aiki a littafi ta karanta tayi ko kamshi bai fito ackba garama kuskus yai kamshi tunda yaji kifi da curry da albasa
taringa hada xufa tana
Sharcewa wai ita nan tayi aiki
Ta xauna akan kujera sharaf ta ringa nishi hhhmmm mata anyi aiki angaji
Saida tahuta na mintina 20 sannan na mike da sauri ganin magrib ta kusa tasan lokacin dawowar gadanga yayi don bataji shigowar mota gidanba
Toilet tashige tasallo wanka
Amaimakon tayo alwala tafito amma ina
Kwalliyace kawai agabanta to agida anraina iyaye ba.a bin maganar uwa balle ayi koyi da ita momy tayi iya bakin kokarinta na ganin khalisat t taso da ibada amma ina Allah bai bata ikon daukaba don intayi fada saidai tayo mata gunguni tana kuka tana dire dire wai ita antakura mata daddy yayo kan momy da fada adole komi ta xuba mata ido baiwar Allah tanajin ciwon abun haka ta hkr to garanar taxo anyi aure ba.a kware akomi ba
Tatsalo kwalliya da english waers "yar b'igil din riga iya cibiya yellow da jan wando pencil yazauna akan diri ga kirji yaciko yasha breaziyya me k'ok'o gashin kanta sai kyalli yake yaji gyara
Ta dawo falo ta hakince ta kunna kallo MBC 2 ne wani american suka sako amma ita hankalinta ba.a gun yakeba don bata fahimta kwata kwata tadai xuba idanune amma hankalinta nacan gun Aliyu tana ayyano irin soyayyar da zasuyi ayau
Aliyu bai shigo gidan da wuriba dan sai bayan magriba yaje gidan dady ne akan muhimmiyar maganar da dadyn akawowa gadangan
Dady so yake Gadanga yakwaso abokansa da yaransa kaf yadawo dasu kano zai basu Aiki kowanne dan cigabansu yake so
Dady mutum ne me kishin Al,umarsa da son taimakon marasashi
Dayake yabude wani kamfani ne na shinkafa me suna *S&S RICE*
Akwai vacancy sosai saidai yafi so yakawo nasa kafin yaxuba yan gari don yanajin yan kauyensu tamkar yan,uwansa suma suna sonsa sbd yanda yake yi musu tabbs da ace zai futo dan takararsu zai samu quri,unsu
Sosai gadanga yaji dadin hakan yaita yiwa dadyn godiya
Dady yace masa "to Aliyu meye na godiyar dan kaina nayi kuma dan Allah duk da komi xasu samu ta dalilinkane kaima inaso inga ina faranta makane sbd rikon amanarka da kaunar dake tsakanin mu gashi kuma kana yiwa "yata rikon amana
Zancen nan na dady yatsayewa gadanga
Tabbas dady mutum ne kuma ubane agunsa yakamata yanda yake masa shima yasaka masa da khairan
Yaji aransa baikamata yaringa yiwa khalisat abinda yake mataba zuciyarsa ta karye akan abubuwan da yake mata duk da ita tajanyo to amma ai akullum baiga tayi nadamar halayen taba
Koda kuma xai mata sassauci baxai iya hada sonta dana Zee din saba
Momy tabashi wasu kaya aledoji biyu tace yakaiwa "yayanta
Yanajin dadin yanda sukewa zainabunsa sun dauketa tamkar "yar cikinsu basa nuna bambanci to aishima yaji yakamata yaringa kwatanta adalci kada yabambanta su
Part din zainabu yafara shiga duk da yau kwanan na khalisat ne to amma ai dolene yashiga yaga abar sonsa suyi sallama
Tana kwance akan gado
Yashigo yatararta akurya
Ita bata zaci bama zaixo mata ayau din datajishi shiru
Yaxauna kusa da ita yana fadin "My zee qalau kuwa?
Ckn narkewa tace "banida lfy
Da sauri yataba jikinta yaji sanyi qLau
Yayi murmushi yace "anya kuwa dear kodai rashin lfyr tafiyata wani dakinne yakamaki?.
Hawayen daya makale yakarasa zubo mata
Nan yafahimta yahau goge mata yana rarrashi
"Kiyii hkr zainab kada kitashi hankalinki kullum fa muna tare babu kuma abinda zamu fasa can fa kwana kawai xanyi babu abinda zanyi acan.... "a,a ni ban hanaka bata hakkin taba kada Allah yakama mu baruwana
Yace "kinyarda nayi komi knn?
Tayi masa shiru kawai
"To naji abar maganar nan kinsha magani?
Ta gyada kai alamar E.
Yace "ok, kinga yau na dade ko? To walh ddy ne yazomin da wani zance me dadi kinsan me yace ?
Tayi ms shiru tana shan qamshi abinta
Yaci gaba "dady yace inje kauye inhado kan abokaina da Duk yarana zai basu aiki a sabon kamfanin daya bude nashinkafa...
Da sauri ta mike daga kwancen da take da murnarta tace "kai naji dadi amma, yaushe zaka tafi kauyen?
Yayi dariya yace "hhhmmm Sai karshen sati
Ckn marairaita tace "to amma dai dani zaka tafi ko?
Ya kyalkyale da dariya yace "inafa so kk gwaggwonki tayi mana fada itada iyata suce daga aure munzo tare kibari sai kindau ciki sai muje tare nan da wata uku ko
Yafada da zolaya yana kallon fuskarta
Itako kunya taji tayi saurin rufe fuskarta tana fadin "nidai a,a gaskiya ba yanxu zanyi cikinba.
Yariko hannunta tareda dago fuskar yace mata "to sai yaushe?
Tace "nima bansanibafa..
Yaringa mata dry hoo!zainabu an iya sokanci
Saida yasadata da farin ciki sannan yabarta yatafi part din khalisat β¦β¦
*Auntyn Sayyada da Shahida*
*ALI GADANGA...*
πΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉ
*Short Story*
*Nabilancy Luv*π
(Auntyn S&S)
part 2β£9β£
Khalisat na nan afalo ranta na quna tasan Aliyu nacan tareda zainabu wato yama mance da ita knn tunda taji shigowarsa kusan awa guda knn
Da sallama yashiga falon yaganta azaune akan doguwar kujera
Da saurinta ta taso tazo tayi masa sannu da zuwa tareda kawo hannu zata karbi breaf case dinsa (jakar Aiki)
Yaso yahanata to amma kuma yaga hakan baidace ba itama fa matarsace kuma duk abunda zai mata na cusgunawa iyayenta baxasuji dadiba insunji
Yabata yai wucewarsa abinsa ko amsa mata bai ba
Saida sukaje ckn daki ta ajiye tana fadin "sannu da xuwa mijina.
Tafada tana kallonsa tana murmushi
Ya amsa can kasan makoshinsa
Yazauna agefen gado yana rage kayan jikinsa
Ganin zai sille kaya yasa tafita tashiga kicin ta dauko abinci takai masa falo akan center table ta ajiye
Tashiga da sallama dakin ta tararsa yasa ka jallabiya tace masa "ga abinci can nakai maka falo
Yakalleta da hade rai har zaice mata ya qoshi kuma saiya fasa ganin ta marairaice fuska kuma sai yanxu yaga kayan jikinta yakare mata kallo tayi kyau Amma yaji inama xcyrta ma me kyance
Taji wani dadi ganin yana kallonta ckn kissa tajuya tana rangwada duwai dinta na motsawa gwanin sha,awa don khalisat akwai hips
Ga fatarta akwance tana sheki yabita da kallo banda sha,awarsa anesa take da tabbas zata iya tashi ayanzun
Yaja tsaki yashige toilet don watsa ruwa
Saida yadauro alwala yasallaci ishsha,i kana yafito yayi sallarsa adakin sannan yafita zw falon
Yana zama akan 3 seater yadau remote yacanxa tasha zuwa Arewa don kallon maimaicin shirin dadin kowa
Tana kusa dashi akan 2 seater saitayi sauri ta sauko kaza tahau zuba masa kuskus din a plate
Harda juice ta hada yayi sanyi kuwa dan shirme harda indomie fa ga kuma joloup na shinkafa
Ta miko masa plate din kuskus din da ladabi yakarba yafara ci da bismillah
Lomarsa uku dakyar ya iyaci magi baijiba bai dahuba babu wani gud testing sai kamshin kawai
Ya tsiyayi ruwa yakora don lemo ba best drink dinza bane dama dai xobo ne
Tana kula dashi bata kawo aranta ko rashin dadin girkin nata bane yasa ya ajiye saita hau bude masa sauran kwanukan "azuba maka wannan ??? Ta