Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 3
biyu zuwa uku kamar yadda ya jero min tambayoyi.” Khalifa ya ce, “an ba ki iznin.” Ta dubi malamin ta ce, “ina so ka amsa min tambayoyina da hanzari idan ka kasance malami.” Ya ce, “yi tambayar ki, a shirye nake.” Ta ce da shi “menene kibiyoyin addini.” Ya amsa mata da cewa “kibiyoyin addini su goma ne; na farko kalmar shahada ita ce addini, na biyu sallah ita ce, abinci. Na uku zakka da sadaka domin samun tsarki. Na hud’u azumi shi ne garkuwa. Na biyar aikin hajji shi ne shari’a. Na shida jihadi a bisa tafarkin Allah, na bakwai da na takwas su ne umarni da kyakkyawa da hani da mummuna, wad’annan su ne darajar d’an Adam. Na tara jama’a su ne alheri. Na goma neman ilmi shi ne tafarkin abin godewa.” Ta ce, “ka fad’i daidai. Yanzu ina da wata tambayar, “menene al’amuran addini?” ZANCI GABA05 HIKAYAR ABUL HASSAN DA KUYANGAR SA TAWADDUD Ya ce “al’amuran addini guda hud’u ne; ingancin k’uduri da gaskiyar nufi da cika alk’awari da nisantar iyaka.” Ta ce haka batun ya ke, ga wata tambayar ta k’arshe, idan ba ka amsa ba zan tub’e rigar ka.” Ya ce, “fad’i ko menene.” Ta ce “menene rassan Musulunci?” Ya yi shiru bai amsa ba har lokaci ya yi nisa. Kuyanga ta ce, “tub’e min rigarka tunda ba ka amsa ba.” Khalifa ya ce, “amsa mu ji su ya kuyanga, ni zan karb’e tufafin daga gare shi na ba ki.” Sai ta ce da su “rassan Musulunci su ashirin da biyu ne, ga su: rik’o da littafin Allah mad’aukakin Sarki, koyi da manzanninsa, tsira da aminci ya tabbata a gare su. Kiyaye aikata alfasha, cin abu daga halali. Nisantar abin da yake haramun, da mayar da kayan da aka karb’a cikin zalunci. Tuba, da neman sanin ilmin addini da shari’a da k’aunar abokan arziki da bin mutanen kirki da ban gaskiya ga annabawa da jin tsoron jinkiri da zumunci da shirin guzurin barin wannan rayuwa da yafewa a lokacin da ake da ikon d’aukar fansa, da hak’uri yayin ciwo da hak’uri a lokacin jarrabawa da neman sanin Allah mad’aukakin Sarki da abin da Manzonsa ya sanar da mu da gujewa Iblis la’antacce da jayayya da rai bisa sab’awa mahalicci da kwad’aituwa bisa bautar Allah Makad’aici.” Yayin da Khalifa ya ji jawabinta sai ya umarci malamin da ya cire alkyabbarsa da rawaninsa da sandarsa ya fita yana mai jin kunya gare ta, ya zama abin dariya ga Khalifa. Daga nan wani mutum daga malaman ya mik’e tsaye ya ce, “ya ke kuyanga ga wasu tambayoyina gare ki.” Ta ce, “ina jin ka.” “Menene sharad’in cinikin bashi?” Ta ce “tamanin kayan ya zama sananne, kayan su zama sanannu kuma lokacin da za a biya ma ya zama sannanne.” “Menene sharud’d’an cin abinci?” “Sakankancewa Allah mai girma da d’aukaka shi ne ya azurta mu da ci da sha. Don haka wajibi ne mu gode masa bisa ga haka.” “Menene godiya?” “Komawar bawa zuwa ga Allah da abin da Allah ya yi a gare shi zuwa ga Allah da abin da ya halatta domin sa.” “Menene sunnonin cin abinci?” “Wanke dukkan hannaye yayin farawa da ambaton bismillah kafin a soma cin abincin. Da zama bisa sashen hagu da cin abincin da hannu da yatsu uku. Da kuma cin abincin da yake daidai da mutum. Kada a ci abinci fiye da k’ima.” “Menene ladubban cin abinci?” “Yankar loma k’arama da cin gabanka da k’aranta kallon abokin zamanka.” “Wannan haka ya ke.” In ji malami mai tambaya. A nan asuba ta riski Shaharzad, ta katse zancenta mai dad'in saurare. DARE NA 444 A dare na d'ari hud’u da arba’in da hud’u, Shaharzad ta ce, na samu labari ya kai wannan hamshak’in Sarki, yayin da kuyanga ta amsa tambayar malamin game da ladaban cin abinci sai ya ce, “kin kyauta, haka yake.” Sannan ya ce da ita, “fad’a min game da k’udurce – k’udurcen zuci.” “K’udurorin su uku ne da kishiyoyinsu guda uku; Na farko k’udurin imani kishiyarsa ita ce jayayya. Na biyu k’udurin sunna, kishiya tasa ita ce bidi’a da dangoginta. Na uku k’udurin biyayya, kishiyarsa kusata da aikata sab’o.” “Haka yake. Fad’a min game da sharad’an alwalla.” “Sharad’an su ne, Musulunci, rarrabewa tsakanin abu mai kyau da mara kyau da tsarki da tsarkakken ruwa da gusar da abubuwan da ba na addini ba.” “Menene imani?” “Imani shi ne, yarda da Allah da mala’ikunsa da manzanninsa da littafansa da ranar lahira da kuma yarda da k’addara ta alheri da ta sharri.” “Menene abubuwa uku da ke kyautata abubuwa uku?” “Safiyanus Sauri ya fad’i cewa abubuwa uku masu gusar abubuwa uku su ne; takatsantsan ga waliyai yana kyautata rayuwar lahira, takatsantsan ga sarakuna yana kyautata rayuwar duniya, takatsantsan a wajen b’arnar kud’i na kyautata dukiya.” “Menene mabud’an sama, kuma k’ofofi nawa gare ta?” “Allah mad’aukakin Sarki ya fad’i cewa, ‘wa futhatus sama’u fa kanat abwaba.’ Ma’ana ‘Kuma, aka bud’e sama, sai ta kasance k’ofofi.’ Babu wanda ya san adadin k’ofofin sama sai Allah wanda ya halicce su, haka nan babu wani d’an Adam face yana da k’ofofi biyu a sama, d’aya wadda arzikinsa ke saukowa, d’aya inda ayyukansa ke hawa. K’ofa ta farko ba ta rufewa sai ranar da ya bar duniya, k’ofar aikinsa kuma ba ta rufewa sai ranar da aka tsayar da shi gaban Allah. Domin ko da mutum ya mutu akwai ayyukansa da ke samun sa walau na alheri ko na sharri.” “Haka ya ke,” in ji malami mai tambaya, ya ci gaba da cewa, “fad’a min game da wani abu da rabin wani abu da kuma abin da babu shi.” Ta ce da shi “wani abu shi ne Musulunci, rabin abu shi ne Munafunci, abin da babu kuma shi ne kafirci.” “Fad’a min yadda zuciyoyi suke.” Ta ce “akwai cikakkiyar zuciya da zuciya maras lafiya da zuciya mai zargi da zuciya mai alk’awari da kuma zuciya mai haske. Cikakkiyar zuciya ita ce ta Annabi Ibrahima mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Zuciya maras lafiya ita ce zuciyar kafirai, zuciya mai mai zargi ita ce irin zuciyar waliyan Allah, zuciya mai alk’awari kuwa ita ce misalin zuciyar shugabanmu Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da ta mabiyansa, sannan zuciya mai haske ita ce misalin zuciyar malamai. Haka nan zuciyar malamai ta rabu zuwa gida uku; akwai zuciyar da ke k’aunar wannan duniyar da abin da ke cikin ta. Da zuciyar da ta rataya ga zuwa rayuwar gaba watau lahira. Da zuciyar da ta rataya wajen son Ubangiji mahaliccin Sarki. Haka nan an ce zuciya ita kanta ta kasu zuwa gida uku; wadda ta mutu irin ta kafirai da wadda babu ita irin ta munafukai da wadda take tsaye cif babu rawa, misalin ta muminai. Sannan an ce tsayayyiyar zuciya ta rabu kaso uku; zuciyar da take cike da haske da imani, da zuciyar da ke raunata da tsoron karkacewa. Sai zuciyar da take jin tsoron kub’ucewar rabo. ZANCI GABA06. HIKAYAR ABUL HASSAN DA KUYANGARSA TAWADDUD malami mai tambaya na biyu ya ce, “kin kyauta ya ke kuyanga.” Ya koma ya zauna. Kuyanga ta dubi Sarkin Musulmi ta ce, “ya Sarkin Musulmi, ya yi min tambayoyi da dama, yanzu zan yi masa nawa ‘yan tambayoyi idan ya amsa shi kenan, idan kuma bai amsa ba zan amshe alkyabbarsa.” Khalifa ya ce, “wannan daidai ne.” Ta juya ga malamin ta ce, “me za ka fad’a game da imani?” Ya mik’e tsaye bisa dugadugansa sannan ya ce, “imani shi ne mik’a wuya a bayyane bisa ga abin da Annabi mai tsira da amincin Allah su tabbata gare shi ya zo da shi. Imanin mutum ba ya cika sai ya tabbata a bisa halaye biyar, su ne; dogaro ga Allah, mik’a al’amari ga Allah, rashin mamaki game da sha’anin Allah da yarda da hukuncin Allah, sannan al’amarunsa duka su zama domin Allah.” Ta ce, “haka zancen ya ke. To ina so ka fad’a min menene farillar farillai da farillar cikin farkon kowace farilla da farillar da kowace farilla ta dogara gare ta da farillar da ke dulmiya kowace farilla da kuma sunna mai shiga cikin farilla da kuma sunnar da farilla ba ta cika sai da ita.” Nan take ya d’auki lokaci bai ce komi ba, ya yi shiru na wani lokaci. Ganin bai tanka ba sai Khalifa ya umarce ta da ta fassara su, sannan in ya kasa zai sa ya tub’e alkyabbarsa, ya ba ta. Ta ce, “ya malami, ka sani farillar dukkan farillaiita ce tabbatar sanin Allah mad’aukakin Sarki, amma farillan farkon dukkan farillai ita ce shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Muhammadu manzon Allah ne. Farillar da kowace farilla ke buk’ata ita ce alwalla. Farillar da ke dulmiya kowace farilla, ita ce wankan janaba. Ita kuwa sunna mai shiga cikin farilla ita ce tsettsefe yatsu da gemu mai kauri. Ita kuwa sunna wadda farilla ke cika da ita, ita ce aske gashin gaba da fisge gashin hammata da kaciya.” A nan gajiyawar malamin ta bayyana, ya tsaya gaban Sarkin Musulmi ya ce, “Allah ya sani ya Sarkin Musulmi cewa wannan kuyanga ta kasance mafi sanin ilmin furu’a da waninta fiye da ni.” Ya juya ga barin ta yana mai k’ask’antacce. Ta juya ga ragowar malaman da ke zaune ta ce, “ya ku manyan malamai, a cikin ku akwai gwani a kan rubutu da karatun Alk’ur’ani mai girma, wanda ya nak’alci ruwaya bakwai da nahawunta da lugga da furuci?” Wani malami ya mik’e tsaye ya dube ta ya ce, “yalla ke kin karanta littafin Allah mai girma, kin haddace surorinsa, kin san yawan ayoyinsa da juzu’o’insa da shafaffun ayoyi da wad’anda aka shafe su da su da k’ira’o’i da surorin Makka da na Madina? Kin san tafsirinsa da musabbaban saukar ayoyi?” Ta amsa, “na’am.” Ya ce, “nawa ne adadin surorinsa da yawan kurinsa da yawan ayoyinsa da yawan kalmominsa da yawa haruffansa? Nawa ne adadin ayoyin sujjada da yawan annabawan da aka ambaci sunan su a ciki? Nawa ne adadin surorin da aka saukar a Makka da yawan wad’anda aka saukar a Madina? Tsuntsaye nawa aka ambata a cikin sa? “ Ta ce, “ya shugabana ka sani adadin surorin Alk’urani mai girma guda d’ari da goma sha hud’u ne. Saba’in daga cikinsu an saukar da su a Makka, arba’in da hud’u kuma an saukar da su a Madina. A cikin sa akwai kuri guda d’ari shida ashirin da d’aya. Akwai ayoyi dubu shida da d’ari uku da talatin da shida, sannan ya k’unshi kalmomi dubu saba’in da tara da d’ari hud’u da talatin da tara. Haka nan ya k’unshi haruffa dubu d’ari uku da ashirin da uku da d’ari shida da saba’in. Game da wanda ya karanta kuwa, duk harafi za a ba shi lada goma. Ayoyin sujjada su goma sha hud’u ne.” A nan asuba ta riski Shaharzad, ta katse zancenta mai dad'in saurare. DARE NA 446 A dare na d'ari hud’u da arba’in da shida, Shaharzad ta ce, na samu labari ya kai wannan hamshak’in Sarki, yayin da malami gwanin Alk’ur’ani ya tambayi kuyanga sai ta cigaba da ba shi amsa ta ce, “amma game da annabawan da Allah ya ambata a cikin Alk’urani mai girma su ashirin da biyar ne. Su ne; Adamu, Nuhu, Ibrahima, Isma’ila, Ishak’a, Yakubu, Yusufu, Lud’u, Yunusa, Salihu, Hudu, Shu’aibu, Dawuda, Sulaimanu, Zulk’ifil, Idrisu, Iliya, Alyasa’u, Yahaya, Zakariyya’u, Ayuba, Musa, Haruna, Isah da Muhammadu tsira da amincin Allah ya tabbata a gare su duka! Amma tsuntsaye da aka ambaci sunansu a littafin Allah su tara ne; sauro da k’udan zuma da k’uda da tururuwa da hudahuda da hankaka da fara da alallaka da tsuntsun Annabi Isah Amincin Allah ya tabbata gare shi, watau jemage.” Malami ya ce, “kin kyauta, fad’a min wacece mafificiyar sura a K’ur’ani?” Ta ce “suratul Bak’ara.” “Wacce aya ce ma fi girma a cikin ta?” Ta ce da shi “Ayatul kursiyu, ta kuma k’unshi kalmomi hamsin, kowace kalma tana d’auke da albarka hamsin.” “Wace aya ce take d’auke da ayoyi tara a cikin ta?” Ta ce “wurin fad’in Allah mad’aukakin Sarki ke cewa, ‘Inna fil khalk’is samawati wal ardhi…’ har zuwa k’arshen ayar.” “Wace aya ce ma fi adalci?” Ta ce “wajen fad’insa Mad’aukakin Sarki, ‘Innallaha ya’amuru bil ma’arufi. Wa yanha anil fahasha’i wal munkari wal bagyi…” “Wace aya ce ma fi kwad’aitarwa?” Ta ce “tana cikin suratul Ma’arij, inda Allah ke cewa, “A yad’ ma’u kullun ri’in minhum an yad khala Jannata na’im.” “Wace aya ce mafi sa wa mutum ya yi tsammani?” Ta ce “ita ce wadda ke cewa, ‘K’ul ya ibadiyallazina asrafu ala anfusihim, la tak’nad’u min rahmatillah. Innallah yagfuruz zunuba jami’a. Innahu huwal gafurur rahim. “Ke da wace k’ira’a kike karatu?” Ta amsa “ina karatuna da irin yadda ‘yan aljanna suke yi bisa ruwayar Nafi’u.” “A wace aya ce aka ambaci k’arya bisa ga annabawa?” Ta ce “a cikin Suratul Yusuf, inda Allah ke cewa, “wa ja’u ala k’amisihi ba damin kazib.” “A wace aya aka gaskata kafirai a cikin ta?” Ta ce “fad’insa mad’aukakin Sarki, “wa qalatil yahudu laisatil Nasara ala shai’in waqalatil Nasara laisatil Yahudu ala shai’in wa hum yatlunal kitab.’ Dukkansu sun fad’i gaskiya.” “Wace aya ce Allah ya fad’e ta ga kansa?” Ta amsa “inda yake cewa, “wa ma k’alak’tul jinna wal insa illa li ya’abudini.” “A wace aya ce Mala’iku ke magana?” Ta ce da shi “ayar da ke cewa, ‘wa nahnu nusabbihu bi hamdika wa nu k’addisu laka.” Cikin suratul Bak’ara.” ZANCI GABA INSHA ALLAH07 HIKAYAR ABUL HASSAN DA KUYANGAR SA TAWADDUD Me za ki fad’a game da neman tsari a kan shaid’an yasasshe da abin da ya zo a cikin ta.” Ta ce, “neman tsari daga shaid’an wajibi ne, Allah ya yi umarni da haka a lokacin da za a soma karatun K’ur’ani. Akwai dalili game da haka wajen fad’arsa mad’aukakin sarki, “fa iza k’ara’atal k’ur’ana fas ta iz billahi minasshaid’anir rajim.” “Fad’a min yadda lafazin neman tsarin yake. Kashi nawa ne? Akwai sab’ani a ciki?” Ta ce “wasu na cewa ‘A’uzu billahis sami’ul alim, minasshaid’anir rajim. Wasu kuma na cewa ‘A’uzu billahis zulquwwa minasshaid’anir rajim. Amma duka abin da ya fi shi ne abin da Alk’ur’anin ya yi furuci da shi watau, ‘A’uzu billahi minasshaid’anir rajim. Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya k’ara tabbata a gare shi ya kasance idan zai fara karatu yana ambaton haka. Kuma an rawaito daga Nafi’u, ya karb’o daga mahaifinsa cewa mai tsira da amincin Allah ya k’ara tabbata a gare shi ya kasance idan ya tashi sallah cikin dare yana cewa, ‘Allahu Akbar Kabiran Subhanallahi bukratan wa asila. Daga nan sai ya ce, ‘A’uzu billahi minasshaid’anir rajim min hamazihi wa nafa. An rawaito daga d’an Abbas Allah ya yarda da shi ya ce, “farkon abin da Mala’ika Jibrilu ya sauko da shi bisa ga Annabi shi ne neman tsari, sannan ya ce fad’a masa bismillah, sannan ya fad’a masa ya yi karatu da sunan Allah wanda ya halicce shi ya bai wa d’an Adam sani.” Yayin da gwani ya ji zancenta ya yi mamakin lafazinta da fasaharta da ilminta da fifikonta. Ya ce da ita, “ya ke kuyanga, me za ki ce akan fad’ar Allah mad’aukakin sarki, Bismillahir rahmanir rahim?” Ta ce, “wannan aya ce a cikin K’ur’ani mai girma cikin suratul Namli. Kuma ana sanya ta a farkon kowace sura, amma akwai sab’ani tsakanin malamai cewa ita aya ce a kowace sura ko a’a.” Ya ce, “kin kyauta.” kuyanga ta cigaba da ba wa gangaran game da sab’anin malamai a kan Basmala. Ya ce da ita, “kin kyauta, fad’a min me ya sa ba a rubuta basmala a farkon suratut Tauba?” Ta ce “yayin da surar ta sauko bisa sakankancewar alk’awarin da ke tsakanin Annabi Muhammadu mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da kafirai, sai ya gabatar da ita ga Sayyadina Ali d’an Abi D’alib, Allah ya girmama fuskarsa. Ya tafi zuwa Makka ya karanta ta gare su a ranar salla, amma bai karanta masa da bismillah ba.” “Fad’a min falalar Basmala.” Ta ce “an fad’i cewa Manzon Allah ya ce, babu wani abu da za a ambaci basmala a kansa face ya yi albarka. Haka nan an rawaito hadisi daga gare shi cewa, ‘na rantse da ubangijin d’aukaka ba a ambaton basmalah a kan mara lafiya sai ya samu lafiya.’ Haka nan an ce yayin da Allah mad’aukakin Sarki ya halicci gadon al’arshi sai ya raurawa, raurawa mai girma, sai ubangiji ya rubuta Basmala a jikinsa, sai ya daina raurawar. Yayin da aka saukar da ita sai ya ce, “na samu aminci daga abubuwa uku; girgizar k’asa da shafe k’asa da kuma ambaliyar ruwa.’ Darajarta mai girma ce, albarkarta na da yawa, zance a kanta zai yi tsawo idan aka fad’ad’a. Ta ce an fad’a daga Ma’aiki cewa za a zo da wani mutum a ranar lahira idan aka yi masa hisabi sai a yi umarnin a kai shi wuta. Sai mutumin ya yi k’ara wajen Allah ya ce, “yaya za a yi min haka?” sai Allah ya ce, “don me ka ce haka?” sai mutumin ya ce, “Ya ubangijina ka ambaci kanka Arrahmanu kuma ka ambaci kanka Arrahimu amma ga shi za ka sa a kai ni wuta.” Sai Allah mad’aukakin sarki ya ce, “ni na ambaci zatina da Arrahamanu, kuma Arrahimu, ku kai wannan bawan nawa zuwa aljanna, domin rahamata domin ni ne mai yawan rahma, mai yawan jink’ai.” “Haka yake, fad’a min menene asalin Basmala?” Ta ce “yayin da Allah ya saukar da Alk’ur’ani an rubuta shi da sunan Allah mad’aukakin Sarki. Yayin da Allah ya saukar da cewa “kiraye ni Allahu ko Arrahmanu duk yadda kuka kira suna da martaba, kyawawan sun tabbata gare shi.” Sannan ya ce, “ku rubuta su da cewa mun fara neman albarka da sunan Allah, magamin kyauta a duniya.” Yayin da aka saukar da cewa, ‘Ubangijinku makad’aici ne, babu wani Sarki sai shi, magamin kyauta a duniya mai keb’ab’b’en jin k’ai a lahira.” Sai suka rubuta, ‘da sunan Allah Mai Rahma Mai Jin k’ai.’” Yayin da gwani ya ji kalamanta sai ya sunkuyar da kansa yana cewa a ransa, ‘wannan shi ne babban abin mamaki! Ta yaya wannan kuyanga ta san asalin Basmala? Wallahi sai na hilace ta, na d’aukaka bisa kan ta, na rinjaye ta.’ Sannan ya d’ago kai ya dube ta ya ce, “shin Allah ya saukar da Alk’ur’ani gaba d’aya ne ko daban-daban?” Ta ce, “Mala’ika Jibrila amintaccen Allah, Allah ya k’ara yarda a gare shi, shi ya sauko da shi daga wajen Ubangijin talikkai bisa ga Manzonsa, shugaban ma’aika, cikamakin annabawa, Annabi Muhammadu, tsira da aminci su tabbata a gare shi. Allah ya ba shi umarni da hani da wa’adi da tsawatarwa da labarai da buga misali cikin shekara ashirin da uku da ayoyi mabambanta bisa gwargwadon aukuwarsu.” Ya ce, “kin kyauta, fad’a min farkon surar da ta sauko bisa ga manzon Allah.” Ta ce “Abdullahi d’an Abbas ya fad’i cewa surar farko da ta soma sauka ita ce suratul Alak’, Jabiru bin Abdullahi kuwa ya ce, suratul Mudassir ce ta soma sauka, sannan aka rik’a saukar da ayoyinsu a mabambantan lokuta.” “Fad’a min ayar k’arshe da ta sauko.” Ta ce da shi “k’arshen ayar da ta sauko ita ce ayar riba. Sannan an ce, “iza ja’a nasrullahi wal fatah.” ZANCI GABA INSHA ALLAH08 HIKAYAR ABUL HASSAN DA KUYANGAR SA TAWADDUD yayin da kuyanga ta shaida wa gwani bayani game da ayar k’arshe da ta sauka sai ya ce, “haka yake, ki fad’a min sunayen sahabban da ke karb’ar ayoyin K’ur’ani a zamanin Annabi.” Ta ce da shi “su hud’u ne; Ubayyu d’an Ka’ab da Zaidu d’an Sabitu da Abu Ubaida Amir bin Jarrah da Usmanu d’an Affan yardar Allah ta tabbata a gare su.” “Su waye makarantan da ake karb’ar karatu daga wajen su?” Ta k’ara da cewa “ su ma su hud’u ne; akwai Abdullahi d’an Mas’ud da Ubayyu d’an Ka’ab da Mu’azu d’an Jabal da Salim d’an Abdullahi.” “Menene ma’anar fad’in Allah da yake cewa, kada ku yanka ga kafaffu?” Ta amsa masa da cewa“kafaffun nan su ne gumaka, wad’anda aka kafa ana bauta musu daga barin Allah makad’aici, muna neman tsarin Allah bisa ga haka.” “Menene ma’anar fad’in Allah cewa, ‘ka san abin da ke cikin raina, ni ban san abin da ke cikin ranka ba?” Ta ce “fad’ar Annabi Isah ce lokacin da mutanensa suka ce shi da mahaifiyarsa su ne Allah, dalilin haka ya ce da Allah kai ka san abin da ke raina, ni ban san abin da ke cikin naka ba, kai ne masanin abubuwan da ke b’oye.” “Me za ki ce game da fad’in Allah cewa, ‘Ya ku wad’anda kuka ba da gaskiya, kada ku haramta halal, abin da Allah ya halatta a gare ku.” Sai ta ce da shi “Malamina Allah ya ji k’ansa ya fad’a min cewa, wani sahabi Zahhaku ne ya ce, “akwai wasu mutane musulmi da suka ce, ba za mu ci abu kaza ba don ba shi da tsarki, sannan za mu tufata da gashi.” Sai wannan ayar ta sauka. Amma K’atadata ya ce an saukar da ayar ne a kan wasu sahabban ma’aiki mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, wato Aliyu d’an Ubayyu da Usmanu d’an Mus’ab da wasun su da suka taru suka ce mu keb’e kanmu, mu yi tufafin gashi, mu bar cin abinci mai dad’i sai wannan aya ta sauko.” “Me za ki ce game da ayar da Allah ke cewa ya rik’i Ibrahima Badad’i?” Ta ce da shi “an ce shi Badad’i ne kasancewar sa masoyin talakawa, a wata fad’ar kuma aka ce kasancewar sa mai ciyarwa ne domin Allah. A wata fad’ar kuma aka ce saboda kasancewar sa mai mik’a wuya ga Allah, zuciyarsa ba ta yankewa daga ambaton Allah da tuna ayyukansa.” Yayin da Gwani gangaran ya ji wannan jawabin nata tamkar zubar ruwa daga girgije babu tsayawa, kuma gamsasshe, sai ya tsaya bisa dugadugansa ya ce, “ya Sarkin Musulmi wannan kuyanga ta fi ni ilmin k’ira’a da wanin sa.” Sannan kuyangar ta ce, “ina neman iznin in yi maka tambaya d’aya, idan ka kawo jawabinta ni ce fansarka idan ba ka kawo ba zan cire alkyabbarka.” Sarkin Musulmi ya ce, “tambaye shi mu ji.” Ta dubi gangaran ta ce da shi “wace aya ce ke d’auke da Kaulasan ashirin da uku da ayar da ke k’unshe da Minjaye goma sha shida da ayar da ‘ayn’ d’ari da arba’in a cikin ta?” Gwani ya yi shiru bai amsa ba, tambayar ta zo masa a bazata. Ta ce, “cire alkyabbar ka.” Ya cire. Sannan ta juya ga Sarkin Musulmi ta ce, “ayar da ke k’unshe da Minjaye goma sha shida tana cikin suratul Hudu inda Allah ke cewa, “K’ila ya Nuhu ihbid’ bisalamin minna wabakatin. Ayar da ke k’unshe da Kaulasan ashirin da uku kuwa ita ce ayar bashi da ke cikin suratul Bak’ara, inda Allah ke cewa, ‘Ya ayyuhal lazina amanu iza tadayantum bi dainin ila ajalin musamman faktubuhu... har zuwa k’arshen aya. Aya kuwa mai d’auke da ‘ayn’ d’ari da arba’in tana cikin suratul A’arafi inda Allah ke cewa ‘Wakhtara Musa k’awmahu saba’eena rajulan limee k’atina…” wuraren da babu kalmar girmama kowa a ciki sun had’a da surorin ‘iqtarabas sa’atu wan shak’k’al k’amar’ da surar Arrahmanu da surar Izawak’a.” Yayin da Gwani gangaran ya ji haka, sai ya cika da mamaki ya ajiye alkyabbarsa gare ta ya juya yana mai tsananin damuwa. sai wani malami, likita masanin cututtuka ya tashi tsaye ya ce da ita, “tunda kun gama da zancen sanin addini ga ni na zo da zancen sanin jikin dan Adam. Fad’a min game da mutum, yaya aka halicce shi? Jijiyoyi nawa ne gare shi? K’ashi nawa gare shi? Nawa ne fak’onsa? Wacece jijiyar farko, kuma me ya sa ambaci dan Adam da wannan suna na watau Adam?” Kuyanga ta gyara tsayuwa ta ce, “an ambaci Adam da wannan suna na Adama saboda rasuwar da mabambantan kamanninsa. An ce an halicce shi daga marashiyar k’asa, watau kenan mabayyaniya. K’irjinsa an yi shi daga k’asar Ka’aba, kansa kuma daga k’asar gabas, k’afafunsa daga k’asar yamma. Allah ya halicci k’ofofi bakwai a kansa wad’anda suka had’a da k’ofar idanu da hanci da kunne da baki. Sannan da wasu k’ofofin zarcewa biyu daga k’asansa; wato dubura da zakari ko farji. Idanu an yi su domin gani, kunnuwa domin jin sauti, hanci domin sunsuna, baki domin d’and’ano. Allah ya sa harshe domin ya yi furuci daga abin da ke zuciyar mutum. Ya halicci Adam bisa abin hayarwa guda hud’u, su ne; ruwa da k’asa da wuta da iska. Ya kasance wad’anda suke launin rawaya daga mutane suna da d’abi’ar wuta, kasancewar ta mai zafi, busasshiya. Bak’ak’e kuwa suna da d’abia’ar k’asa, kasancewar ta busasshiya, mai sanyi. Majina kuwa ta fito ne daga ruwa kasancewar ta mai sanyi, mai danshi. Jini kuwa daga iska kasancewar sa mai zafi, kuma mai danshi. A jikin dan Adam an halicci jijiyoyi guda d’ari uku. Sannan akwai k’asusuwa guda d’ari biyu da arba’in da rayuka uku; na numfashi da na tafiya da na d’abi’a. Allah ya sanya wa kowannensu hukunci da irin aikinsa. Haka kuma Allah ya halicci zuciya ga mutum da saifa da huhu da hanji guda shida da tumbi guda uku da hanta da k’oda guda biyu da mazawari da matsina da k’wak’walwa da k’ashi da tsoka da fata da kuma sanya masa hak’ori domin magana da tauna. Haka nan Allah ya halicci d’an Adam da kafafen ji guda biyar; ji da gani da sunsuna da d’and’ano da tab’awa da ji a jiki. Ya sanya zuciya ta zama a sashin hagu na k’irji, ya saka tumbi gaba ga zuciya, ya sanya matsarmama kusa da hanta, wani lokaci tana matsowa kusa da zuciya, kodayake hanta tana daga gefen dama, idan ta cika ta zubo bisa ga hanta sai mutum ya ji tashin zuciya. Allah ya halicci wasu abubuwan da ba su kai wannan aiki ba suna k’asa da inda tumbi yake. Sannan a tsakanin k’irji akwai hak’ark’ari da sauran abubuwa wanda ya had’a da huhu domin tace iskar numfashi.” ZANCI GABA INSHA ALLAH This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it

Chapter 2 of 3