Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 3
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng 01 HIKAYAR ABUL HASSAN DA KUYANGAR SA TAWADDUD Ya zauna yana ta tumurmusar dukiya, yana ci, yana sha cikin bushasha yana ta rabar da zinariya da azurfa da jauhari. Kullum cikin cin nama yake da shaye – shaye da yawan dariya ga kuyangi suna masa wak’ok’i yana musu kyaututtuka. Bai gushe ba yana wannan d’abi’a har abin da ya mallaka gaba d’aya ya k’are ya zamana ba shi da komai duk abin da ya mallaka ya fice daga hannunsa, sai wata kuyangarsa guda d’aya da ya mallaka daga mahaifinsa. Ita wannan kuyangar ta kasance babu kamar ta wajen kyau da cikar halitta da k’oshi da hankali da ladabi biyayya. Ta fi ragowar kuyangin wajen ilmi da iya magana mai dadi. Ta nak’alci yadda za ta jawo hankalin mutum zuwa gare ta, ta san yadda za ta rarrashi masoyinta. Idan ka gan ta za ka yi tsammanin watan sha’aban ne ya tsaya saboda idanunta masu haske, tamkar an gina su da lu’ulu’u, suna walk’iya kamar kaifin takobi, jikinta kullum ba ya rabo da k’amshi da taushi da ni’ima. Kundukukinta kamar nunanniyar tuffa. Bakinta matsakaici kamar hatimi, hak’oranta jere reras kamar kibiyoyi. Jikinta mai kyan gani abin so ga kowa domin bai zama ramamme ko mai yawan k’iba ba. A taka’ice dai ita ta kasance kamar yadda mai wak’a ke cewa: Idan ta gabato ta fitinar da zuwanta, Idan ta tafi nan ne abu mafi azabtuwa Ta fi wata haske ta yi kama da rana Kyawunta shi ne abin so ga duk kowa Tana jan hankalin duk wanda ya gan ta da kyanta da iya maganar ta mai cike da tattausan lafazi da murmushinta ko dariyarta. Musamman idan ta haskawa mutum kyawawan fararen idanun nan nata. Da yake Abu Hasan ya karkatar da dukkan dukiyarsa ya zamana ba shi da komai sai ita, ga shi kwana uku kenan ba su jefa wani abu a cikinsu ba kuma ba su samu barci ba, sai kuyangar ta ce da shi, “ya shugabana, ka kai ni wajen Sarkin Musulmi Khalifa Haruna Rashid ya fanshe ni.” ka nemi biyana dinari dubu goma, hakan zai sa ka samu biyan bukata daga damuwar da ka shiga. Idan ya nuna cewar na yi tsada sai kace masa, “ya Sarkin Musulmi wannan kuyangar da kake gani k’imar kudinta ya fi haka ma, amma ka jarraba ta da kanka ka gani ta fuskar ilmi da hankali. Domin ita wannan kuyangar babu misalinta, kuma ba ta dace da wani ba face kai.” Ta sake gargadinsa cewa, “kada fa ka sallama ni k’asa da abin da na fad’a maka, domin wannan kud’in araha ce ga makamanciyata.” Ubangidanta ya kasance bai san darajar ta da k’imar ta ba, amma jin za ta kai wannan darajar sai ya d’auke ta ya tafi da ita wajen Khalifa ya shaida masa kamar yadda ta hore shi. Khalifa ya dube ta ya ce, “yaya sunanki?” Ta ce, “sunana Tawaddud.” Sannan ya ce, “ya ke Tawaddud a wanne fannin ilmi kika gwanance?” Ta ce, “ka sani ya Sarkin Musulmi ni inda da ilmin nahawu da furu’a da wak’ok’i da tafsiri da hisabi da k’ismi da labarun mutanen farko. Kuma na san Alk’ur’ani mai girma, na karanta ta fuskar ruwayoyi bakwai da goma da kuma goma sha hud’u. Na san yawan surorinsa da ayoyinsa da haruffansa da kalmominsa. Na san tsakiyarsa da rubu’insa da sumuninsa da wuraren sujjada da k’irgen adadin haruffan sujjadar. Na kuma san ayoyin da aka shafe da wadanda ba a shafe ba. Na kuma san surori Makiyya da Madaniyya da sababin saukar da aya ko sura. Na san hadisan Annabi da tarihi da hik’ayoyi da labarun da ake kokwanto a kan ingancinsu. Na san ilmin sanin rauhanai na san na mutanen Hindu da na Falasd’inawa da hikimomin jiya da na yau, na kiyaye da yawa ilmin ma’ana da na bayani. Kuma na nak’alci ilmin magani da kuma iya kad’a molo yadda zan kad’a shi na b’ata zuciya da yadda zan buga shi ya faranta rai. Haka nan na san yadda za a kad’a shi a yi rawa da inda za a kad’a a yi shiru kawai. Idan na yi ado na fitinar, idan na shafa turare a fitina da ni. Na zama babu wanda zai k’aru da ni sai wanda yake da ilmi mai zurfi mai hangen nesa.” Yayin da Khalifa ya ji wannan bayanin nata sai ya yi mamaki saboda k’arancin shekarunta da yadda ta iya bayani cikin hikima da lafazi mai dad’i. Ya waiwaya ga Abu Hasan ya ce, “bari na aika a kirawo ma’abota sani da za su yi mata tambayoyi kan abin da ta ce tana da shi na daga ilmi. Idan ta kasance ta amsa dukkan tambayoyin zan saye ta a wajenka, bisa kud’in da ka fad’a kuma na k’ara maka wasu a kai. Amma idan ba ta amsa ba, to babu wanda ya cancanta da ita sai kai.” Abu Hasan ya ce, “cikin farin ciki da so da yarda ya Sarkin Musulmi.” Khalifa ya rubuta takarda zuwa birnin Basra ya ce a kirawo masa Ibrahima d’an Siyyari. Ya kasance masani ne a fannin balaga da wak’e. Ya ce kuma ya taho da masana Kur’ani mai girma da malaman hikima da masana ilmin maganganu da masana ilmin taurari da mahukunta da masanan ilmin Hindu da Falsad’iya da hisabi. Shi Ibrahima ya kasance duk ya fi su sanin wad’annan ilman ya aika duka suka zo suka tafi da hanzari domin amsa kira. Yayin da suka isa fada suka zazzauna Khalifa ya bayyana musu dalilin kiran su sannan ya aika aka kirawo kuyanga Tawaddud ta shigo ta yaye lullub’i ta nuna kanta kamar walk’iyar tauraro. Khalifa ya sa ta zauna a kujerar zinariya ta gaishe da jama’a cikin murya mai taushi da fasahar harshe, sannan ta ce, “ya Sarkin Musulmi, ka umarci wad’anda suka hallara nan daga malamai da masana ilmin taurari da masana hindiya da falsad’iya su yi min tambaya duk irin wadda suka ga dama.” Khalifa ya ce da su, “ina so ku yi jayayya da wannan kuyanga bisa abin da take tak’ama da shi na daga ilmi cikin sha’anin addininta. Ku tambayi hujja game da irin abin da ta fad’a.” Suka amsa, “mun ji mun bi ya Sarkin Musulmi.” A nan Tawaddud ta sunkuyar da kanta alamar gaisuwa ga Sarkin ta ce, “a cikinku wanene masanin shari’a da fik’ihu wanda ya nak’alci Alk’ur’ani da hadisai?” Sai wani ya mik’e ya ce, “ni ne wanda kike tambaya.” Ta ce, “to yi tambayar ka gare ni.” Ya ce, “shin kin karanci littafin Allah mai girma kuma kin san aya shafaffiya da wadda aka shafe ta da ita? Kin san adadin ayoyinsa da haruffansa?” Ta amsa, “na’am na san wad’annan duka. “To tunda haka ne zan miki tambaya a kan farilla wajiba da sunna k’a’ima. Ya ce ya ke kuyanga wanene ubangijinki? Wanene Annabinki? Menene a gabanki? Ina ne alk’iblarki? Su wanene ‘yan uwanki? Menene tafarkinki?” Ta ce, “Allah shi ne ubangijina, Annabi Muhammadu mai tsira da aminci su tabbata a gare shi, shi ne Annabina. Alk’ur’ani shi ne a gabana, d’akin Ka’aba nan ne alk’iblata, musulmi su ne ‘yan uwana. Sunnar Annabi Muhammadu ita ce tafarkina.” Khalifa ya yi mamaki da irin kalamanta da cikar fasahar ta duk da k’arancin shekarunta. Mai tambaya ya cigaba, “ya ke kuyanga, da me ake sanin Allah?” Ta ce “ana sanin Allah ta hanyar fahimta.” Ya ce “menene fahimta?” Ta ce “fahimta iri biyu ce; da wadda take a b’oye da wadda take a bayyane.” Zanci gaba insha allah gobe02 HIKAYAR ABUL HASSAN DA KUYANGAR SA TAWADDUD kuyanga tayi bayaninta sosai, tana cewa, “fahimta iri biyu ce; da wadda take a b’oye da wadda take a bayyane. Fahimta b’oyayyiya ita ce wadda Allah mai girma da d’aukaka ke halittar mutum da ita, yana bayar da ita ga wanda ya so. Amma bayyananiyar fahimta kuwa ita ce wadda mutum ke samu ta hanyar neman ilmi.” “Kin amsa daidai.” In ji malamai. “To amma ina ne mazaunar hankali?” Ta amsa da cewa “Allah ta’ala kan jefa shi a cikin zuciyar mutum, daga nan sai haskensa yakan tafi zuwa k’wak’walwa daga nan ya tabbata kenan.” “Wannan haka yake.” In ji malami mai tambaya. Sannan ya ce, “ta yaya kika san Annabin Allah?” Ta ce “ta hanyar karatun littafin Allah da wasu alamu da kuma tabbatattun hujjoji da karamomi.” Ya ce, “haka ne.” Daga nan ya ce, “fad’a min game da shika-shikan Musulunci da sunna k’a’ima.” Ta ce, “shika-shikanMmusulunci guda biyar ne, na farko shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah mad’aukakin Sarki, kuma Annabi Muhammadu bawansa ne, manzonsa ne. Na biyu tsaida sallah, na uku bayar da zakka, na hud’u azumin watan Ramalana, sai cikon na biyar shi ne aikin hajji zuwa ga d’akin Allah mai alfarma ga wanda ya samu iko ga haka. Sunna k’a’ima kuwa su hud’u ne; dare da rana, rana da wata, sune suke kusatar da rai da buri su k’arar da d’an Adam, bai sani ba cewa a kullum suna kusatar da shi ne zuwa ga ajali.” Ya ce, “haka ne. To ki fad’a min game da tabbatar imani.” Ta ce ‘wad’annan su biyar ne, sallah da azumi da hajji da kuma jihadi a tafarkin Allah da nesantar haram.” “Haka ne, to ki fad’a min abin da ke k’arfafawa zuwa ga sallah.” Ta ce da malamin “aniyar bauta zuwa ga Allah, ka san kai bawa ne ka bi shi.” Ya sake tambayar ta “wad’anne wajibabbun sharud’d’a ne suka zama tilas a cika su kafin a kai ga yin sallah?” Ta ce “na farko tsarki da suturce al’aura da nisantar kayan k’yale – k’yale da tsayawa a wuri mai tsarki da fuskantar alk’ibla da daidaita tsayuwa da niyya da kabbarar harama.” “Haka ne, to fad’a min abin da ake fita daga gida domin sallah.” Ta ce “ana fita da niyyar bauta zuwa ga Allah.” Ya sake tambayar ta “ da wacce niyya ake shiga masallaci?” Ta amsa “da niyyar bauta wa Allah.” “Don me muke fuskantar alk’ibla a sallolinmu?” “Domin cika umarni uku daga K’ur’ani mai girma da umarni d’aya daga hadisi.” “Fad’a min game da sallah? Menene farkonta? Menene k’arshenta? Me ya haramta ta?” “Ana yin sallah cikin tsarki. Rashinsa na haramta ta. Farkonta shi ne kabbarar harama, k’arshenta shi ne sallama.” “Menene hukuncin wanda ya bar sallah da gangan?” Ta ce “an rawaito daga ingantattun hadisai cewa duk wanda ya bar sallah da gangan ba tare da wani dalili ba, to ya bar addinin Musulunci.” kuyanga ta rik’a bai wa malamin nan amsa daidai yadda ya tambaye ta, shi kuma yana cewa, ‘haka ne.’ Sai ya ce, “ina so ki fad’a min menene ma’anar sallah?” Ita kuwa ta ce da “Sallah ita ce wata hanyar ganawa tsakanin bawa da ubangijinsa, kuma tana da darajoji guda goma su ne, na d’aya tana haskaka zuciya, na biyu tana haskaka fuska, na uku tana sa yardar Arrahamanu, na hudu tana fusatar da shaid’an, na biyar tana maganin masiba da bala’i. Na shida tana juyar da muguntar abokan gaba, na bakwai tana rub’anya lada. Na takwas tana hana yin azaba a ranar lahira, na tara tana kusantar da bawa zuwa ga ubangijinsa, tana kuma hana shi aikata miyagun ayyuka, na goma ita ce ginshik’in addini.” “Wannan batun gaskiya ne, menene mabud’in sallah?” “Alwalla ko taimama.” “Menene mabud’in taimama?” “Niyya da kuma ambaton sunan Allah mad’aukakin Sarki.” “Menene mabud’in ambaton sunan Allah mad’aukakin Sarki?” “Cikakken imani.” “Menene mabud’in cikakken imani?” “Ban gaskiya ga Allah.” “Menene mabud’in ban gaskiya ga Allah?” “Sakankancewa.” “Menene mabud’in sakankancewa?” “Biyayya.” “Menene mabud’in biyayya?” “Kad’aita Allah da dagewa wajen bauta masa.” “Fad’a min game da farillan alwalla.” “Farillan alwalla guda shida ne bisa mazhabar Imamu Shafi’i, Muhammadu d’an Idrisa, Allah ya yi musu rahma. Niyya yayin wanke fuska, wanke fuska, wanke hannaye i zuwa gwiwar hannu, shafar kai, sai wanke k’afafu i zuwa idon sawu. Da kuma jerantawa. Sunnonin alwalla kuma guda goma ne, yin bismilla da wanke hannaye kafin tsoma su a cikin k’warya, kurkure baki, shak’a ruwa da fyacewa. Shafar gaba d’ayan kai da shafar kunnuwa da sabunta ruwa a gare su. Da kuma tsettsefe gemu mai kauri da tsettsefa yatsun hannu da na k’afafu da soma gabatar da dama kafin hagu da yin wanki uku – uku tare da jerantawa. Idan ka gama alwalla sai ka ce, “na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Muhammadu bawansa ne, kuma manzonsa ne. Ya Allah ka sanya ni cikin bayinka masu tuba, kuma ka sanya ni cikin tsarkaka. Tsarki ya tabbata gare ka, yabo naka ne kai d’aya. Na nemi gafara a gare ka, ina tuba gare ka. Domin a ruwaito hadisi daga Annabi mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cewa, ‘duk wanda ya karanta wannan addu’ar bayan ya yi alwalla, za a bud’e masa k’ofofin aljanna ya shiga ta wadda ya ga dama.” Malami ya ce, “kin yi gaskiya, idan mutum ya yi nufin yin alwalla a ina mala’iku da shaid’anu ke tsaya masa?” “Idan mutum ya yi nufin yin alwalla, mala’iku kan sauko su tsaya a damansa, sannan shaid’anu za su tsaya a hagunsa. Idan ya ambaci Allah a farkon alwallarsa sai shaid’anu su gudu. Daga nan sai mala’iku su yi masa laima ta haske da fukafukansu, kowannensu yana da fuffuke hud’u, suna tsarkake sunayen Allah mai girma, suna nemar wa mutumin gafara gwargwadon lokacin da ya kasance yana alwallar bai yi magana ba. Amma idan a farkon alwallar bai yi bismilla ba sai shaid’anu su kewaye shi, mala’iku su juya ga barin sa. Sai shaid’anun su sanya masa waswasi cikin alwallar har ya yi nak’asu a cikin ta. Manzon Allah mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce, “kyakkyawar alwalla na korar shaid’an, ta fusata shi.” Sannan an rawaito yana cewa, “idan wata masifar ta fad’awa musulmi a lokacin da ba shi da alwalla, kada ya zargi kowa sai kansa.’ ZANCI GABA03 HIKAYAR ABUL HASSAN DA KUYANGAR SA TAWADDUD “Me mutum ya kamata ya soma yi da zarar ya farka daga barci?” “Ya kamata ya wanke hannunsa sau uku, kafin ya tsoma su a cikin k’warya.” “Menene farillai da sunnonin wankan janaba?” “Farillan su ne, niyya, game jiki da ruwa da sadar da ruwa ga dukkan gab’ob’i, ana nufin ruwa ya tab’a dukkan sannan jiki duka na daga gashi da fata. Sunnonin kuwa su ne a fara da alwalla sannan cuccud’a jiki da tsettsefe gashi da jinkirta wanke k’afafu sai a k’arshen wanka.” Yayin da yarinya ta bayyana wa malamin farillan wanka da sunnoninsa da na alwalla sai ya ce, “kin yi daidai, yanzu fad’a min dalilan da ya sa ake yin taimama da farillanta da sunnoninta.” Ta ce, “dalilan bakwai ne, rashin wadatar ruwa ko jin tsoron kada ruwan ya k’are, zama a wurin da babu ruwan da ya kamaci alwalla, rashin lafiya, ko karaya a gab’b’an alwalla da samun rauni a gurbin alwalla. Farillanta guda hud’u ne, su ne; na d’aya niyya, na biyu turb’aya, na uku bugun k’asa na farko, na hud’u shafar fuska da hannaye. Sunnoninta su ne bugun k’asa na biyu da juyowar shafar hannu da kuma gabatar da dama a bisa hagu.” “Menene sharud’d’ai da farillai da kuma sunnonin sallah?” “Sharad’an sallah guda biyar ne, in ji ta “na d’aya tsarkin gabb’ai, na biyu suturta al’aura, na uku cikar lokaci da sakankancewa da ganin wani. Na hud’u fuskantar alk’ibla, na biyar tsayawa a wuri mai tsarki. Amma farillan sallah guda goma sha biyu ne; niyya da kabbarar farko da tsayawa bisa karatun fatiha da ambaton bismillah har k’arshenta a bisa mazhabar Imamu Shafi’i. Da ruku’u da daidaito cikin ruku’un da daidaita zama da nutsuwa a cikin zaman, da sujjada da nutsuwa cikin sujjadar da zama tsakanin sujjadai biyu da nutsuwa a cikin zaman da tahiyar k’arshe da zama a gare ta da salati ga Annabi mai tsira da aminci su tabbata a gare shi. Da kuma sallamar farko bisa niyyar fita daga sallah da ambatonta. Sunnoninta kuwa su ne, kiran sallah da ik’ama da d’aga hannaye yayin kabbarar harama da addu’ar shiga sallah da neman tsari daga shaid’an da cewa ‘amin’ a k’arshen karatun fatiha da karatun sura bayan fatiha da kabbarori yayin tashi tsaye da fad’in, ‘Sami’Allahu li man hamidahu’ da kuma ‘Allahumma Rabbana wa lakal hamdu.’ Haka kuma da bayyanawa a wurin da ake bayyanawa da sirintawa a wurin da ake sirrantawa da zaman tahiyar farko da karatun tahiyar farko da salati ga Annabi a tahiyar farko da salati a farkon tahiya da kuma sallama ta biyu.” “Kin fad’i daidai, in ji malam, “ fad’a min a kan me zakka ta wajaba?” Kuyanga sai ta amsa masa, “zakka ta wajaba a kan dinari da azurfa da rak’umi da saniya da akuya da alkama da shinkafa da sha’ir da gero da dawa da gyad’a da wake da auduga da zabibi da dabino.” Ya amsa, “wannan haka yake, a cikin nawa ne zakka ke fita daga dinari?” Ta ce da shi, “babu zakka a kan abin da yake k’asa da misk’ali ashirin na dinari. Idan ya kai misk’ali ashirin za a fitar da rabin misk’ali zuwa ga abin da ya samu na abin da ya zarta haka. Ma’ana idan dinari ya kai misk’ali ashirin ko fiye za a bayar da kaso d’aya bisa arba’in na yawansa a matsayin zakka.” Sai ya ce da ita, “zakkar azurfa fa?” Ta amsa,“ita ma kamar dinari take.” “Zakkar farin kud’i fa?” Ya tambaye ta. Ta ce da shi, “abin da ya kama k’asa da zambar d’ari babu zakka a kan sa, amma daga zambar d’ari zuwa sama ana fitar wa a kowace dubu kud’i hamsin.” Ma’ana ana kasawa arba’in a d’auki kaso d’aya.” Sai kuma ya tambaye ta da cewa “to yaya zakkar hatsi take da sauran kayan amfanin gona?” Ta ce “daga dami talatin zuwa abin da ya yi sama ana fitar da kowane goma dami d’aya.” “Yaya zakkar rak’uma take?” Ya tambaye ta. Sai ta ce da shi, “a dukkan biyar ana bayar da tunkiya ko kuma a had’a ashirin da biyar a bayar da rak’uma mai ciki.” Sai ya k’ara da cewa “yaya zakkar tumaki da awaki take?” Ta ce “tunkiya ko akuya ake fitar wa a duk guda arba’in.” “To mene ne azumi?” Ya sake tambayar ta. Sai ta amsa da cewa “azumi shi ne kamewa daga cin abinci ko shan abinsha da jima’i da kiyayewar amai da gangan, duk wannan ana yin su da nufin ibada. Wajibi ne a kan kowanne musulmi baligi, maza da mata, ‘yantattu da bayi sai dai ga matar da ke cikin haila ko bik’i. Kuma azumi yana wajabta ne da ganin jinjirin watan Ramalana, wanda shaidu biyu adilai suka hak’ik’ance da ganin sa. Da kuma labarin ganinsa da aka bayar daga wanda za a yarda da gaskiyar maganarsa. Akwai daga wajibansa shi ne tashi bisa niyyar azumin a kowace safiya da kamewa daga ci da sha da jima’i. Sunnoninsa kuwa sun had’a da jinkirta sahur da gaggauta bud’e baki da barin zance face na alheri da zikiri da karatun Alk’ur’ani mai girma.” “Wannan bayani haka yake,” ya ce da ita “fad’a min abubuwan da ba sa b’ata azumi.” Sai ta yi wuf ta ce, “shafa mai da shafa kwalli da k’urar hanya da had’iyar wani abu da fitar maniyyi a cikin mafarki. Da ganin mace ajanabiyya da tsaga jiki da k’aho duka wad’annan ba sa b’ata azumi.” Ya ce da ita, “haka yake, to labarta mana game da sallar idi.” Ita kuwa sai ta ce, “raka’o’i biyu ne a kowace sallah. Kuma suna cikin salloli na sunna. Ba a kiran sallah, ba a tayar da ik’ama. Amma ana cewa, ‘a daidaita sahu’ sannan sai a yi kabbara sau bakwai a raka’a ta farko, bayan kabbarar harama. A raka’a ta biyu kuma kabbara biyar ake yi, bisa koyarwar mazhabar Imamu Shafi’i kenan, Allah yayi masa raham ZANCI GABAO4. HIKAYAR ABUL HASSAN DA KUYANGAR SA TAWADDUD bayan yarinya ta gama yi wa malamin nan bayani a kan sallar idi a gaban Sarki Musulmi sai ya ce, “kin fad’i daidai, to fad’a min yadda ake sallar kisfewar rana ko wata.” Yarinya ta ce, “ba a kiran sallah ko ik’ama, raka’a biyu ne kowace, ana yin ruku’u biyu da tsayuwa biyu da sujjada biyu, sannnan a yi zaman tahiya, a yi sallama.” Ya ce ‘ to fad’a min yadda ake sallar rok’on ruwa.” Nan ma sai ta ce da shi “raka’a biyu ce, babu kiran salla, babu ik’ama. Bayan an yi sallama limami zai gabatar da hud’uba sannan a rok’i Allah gafara kamar yadda ake yin hud’uba a sallar idi. Bayan nan sai a yi addu’a cikin k’ask’antar da kai. Sai ya tambaye ta “yaya ake sallar wuturi?” Ta ce masa “ita salla ce mafi k’aranci raka’a d’aya, mafi yawa raka’a goma sha d’aya.” Sai ya ce “yaya ake sallar walaha?” Ta ce da shi ‘sallar walaha ana yin ta bayan hudowar rana, mafi k’aranci raka’a biyu, ma fi yawa raka’a goma sha biyu.” Sai ya juya ya ce da ita “me kika sani game da i’ittikafi?” Ta ce da su “i’ittikafi sunna ne ana zama a masallaci ana ibada.” “Menene sharud’d’ansa?” Sharud’d’ansa, na d’aya niyya, na biyu kada a fita daga masallaci sai domin biyan buk’ata, na uku babu cud’anya da mata na hud’u ya zamana ana azumi, na biyar ban da zancen duniya sai na alheri.” “Fad’a min abin da ya wajabta aikin hajji.” “Na farko cikar hankali da Musulunci da samun ikon zuwa. Shi kuma wajibi ne ga musulmi sau d’aya a rayuwa.” “Menene wajibabbu a aikin hajji?” Wajibabbu su ne, harama da tsayuwar arfa da d’awafi da safa da marwa da kuma aske gashin kai.” “Menene farillan aikin Umra?” “Harama domin ta da d’awafi da tafiya cikin ta.” “Menene sharud’d’an harama?” “Cire d’inkakkun tufafi, da nisantar turare da nisantar aski ko cire gashi da nisantar yanke farce da nisantar farauta ko kisan namun daji da kuma nisantar jima’i. “Menene sunnonin hajji?” “Fadin Labbaikal lahumma labbaika da gewaye d’akin Ka’aba da ban kwana da wurin kwana daga Muzd’alifa da jifa da duwatsu.” “Menene jihadi? Menene sharud’d’ansa?” “Jihadi shi ne yak’i domin d’aukaka kalmar Allah. Sharud’d’ansa su ne fita a kan kafirai idan suka auko muku, samun jagora da bin umarninsa. Da tsayawa yayin gwabzawa da abokan gaba. Sunnoninsa su ne kwad’aitar da jama’a bisa yak’i a kan tafarkin Allah domin fad’ar Allah mad’aukakin Sarki cewa, “ya kai annabi, ka kwad’aitar da musulmi akan fad’a da kafirai.” “Haka yake, menene sharud’d’an ciniki da sunna tasa?” “Sharud’d’ansa su ne jawabin mai kaya da amincewar mai saye, kada mai sayarwa ya zamana bawa ko yaro k’arami ko matar wani wad’anda ba su da ikon sallamawa. Sannan a gujewa riba da dangoginta. Sunnoninsa kuwa su ne, daddalewa kafin a rabu, domin hadisi ya zo cewa, mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa, “masu ciniki su daddale kan komai tun kafin su rabu.” “Fad’a min abin da aka hana sayensa da wani abu.” “A bisa wannan na tuno da wani hadisi ingantacce cewa an ruwaito daga Nafi’u cewa Manzon Allah mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana musayar busasshen dabino da d’anye, ko busasshen b’aure da d’anye ko dafaffen nama da d’anye. Haka nan musayar d’anyen mai da soyayye da dukkan abin da ya kasance iri d’aya ne na daga abinci wanda aka sauya masa kamanni. Watau duk wani na’uin abinci da ya zama iri d’aya ba a musayen su.” Yayin da malamin nan ya ji dukkan bayanan kuyanga, ya hak’ik’ance abin da ta fad’a daidai ne, ya gamsu da ilminta da zurfin tunaninta da sanin fik’ihunta. Ya hak’ik’ance ba zai iya kayar da ita a wajen tsantsar ilmi ba. Ya ce a ransa, “Babu makawa sai na k’ure ta a gaban Sarkin Musulmi ta hanya mai sauk’i cikin dabara.” Ya dube ta ya ce, “ke yarinya, menene ma’anar alwalla a cikin lugga?” Ta ce, “ma’anarta shi ne tsarkake gabb’ai daga datti.” “Menene ma’anar sallah a cikin lugga?” “Ma’anarta fata nagari.” “Menene ma’anar wanka a cikin lugga?” “Ma’anarsa tsarkakewa.” “Ma’anar azumi fa a lugga?” “Azumi a lugga yana nufin kamewa.” “Ina ma’anar Zakka a lugga?” “Zakka tana nufin k’ari a kan dukiya.” “Fad’a min ma’anar aikin hajji a lugga.” “Hajji a lugga na nufin ziyara.” “Ina ma’anar jihadi a lugga?” “Jihad na nufin kiyayewa ko k’ok’artawa.” Daga nan malamin ya yi shiru. saboda ta gama yanke masa duk wani hanzarinsa da kuzarinsa. Ya tsaya kan dugadugansa ya dubi Sarkin Musulmi ya ce, “ya Sarkin Musulmi, hak’ik’a wannan kuyanga ta kasance mafi sani daga gare mu a fannin furu’a.” Kuyanga Tawaddud ta ce, “ina neman iznin Sarkin Musulmi na yi wa malamin nan tambaya

Chapter 1 of 3