ne yasata kafeta da ido gani takeyi kamar tasan fuskar amma zaiyi wuya ma dan tana ganin a talavijin ne dan haka dai ta dan saki rai tace sannu baiwar Allah
itako dije tunda ta ganta tausayinta ya kamata ji takeyi kamar tayi kuka duk nawa suke ita da hafsy yanzu fa suke shekara sha bakwai amma in suka jera kana iya rantsewa ta haifi dije ganinta a haka ya raunana zuciyar dije sosai ganin cewar bata ganeta ba yasata yin murmushi tare da fadin
*dijan gala tame gari ba auren talaka ba talaka noma da sassabe*
hafsy najin dije ta fadi haka ta saki wata dariya tare da farin ciki tayo cikin dije da niyyar ta rungumeta sai kuma ta fasa ta shiga kallonta tana fadin dagaske kece dije?kece kika zama haka ? anya kuwa?
rungumeta dije tayi kafin ta fashe da kuka nice hafsy meyasa kika fasa rungumata ko baki son rabata ne ?
ah ah dije indai kece dijeta dana sani kuma uwar mazga me bani kashi bazan ki rabar jikinki ba illa dai kada in shafa miki datti kin ganki kuwa dije tabbas Allah na sonki ji yadda rayuwa ta sauya miki ni kuwa dubeni duk na tsofe banda bauta da wahala a hannun uwar miji da kuma kishiya da shi mijin kanshi ba abinda nake tsinta dubi yadda kika koma kamar ba'a duniya kike rayuwa ba wlh dije nayi miki murnar tafiyarki binni dama nice nasamu koda kwatan abinda kika samu ne ta karasa maganar tana kuka
dena fadar haka hafsy Allah na sonki bai kuma manta dake ba ba kuma dan na fiki bane nima yasa nazama haka ki yadda da kaddarar ki kizama mai juriya da haquri har ki samu kici jarabawar ki yanzu dai muje dakin ki tukun
dakin ta suka shiga sai kace dakin tsohuwa qaramin gadon qarfe ne shima duk ya tsufa dakin ko kyan gani babu sallaya ta shimfidawa dije a gurin ta zauna inda suka shiga hira sunata nishadi tare da tuna baya
dije na lura da yadda hafsy keta mutsu mutsu dan haka ta tambayeta lfy?
dan marairaicewa tayi tare da fadin wlh dije narasa yadda zanyi ne abincin dazan sama miki naketa tunani yanzu gashi yadda kike din nan da wuya ki iya shan ruwan gidan dan na rijiya ne
kada ki damu hafsy maza samo yaro yasama mana abinda zamu ci
jiki ba kwari ta mike ta fita neman yaro inda bata sha wahalar samu ba kuwa dan sun cika qofar gidan suna jiran baturiya ta fito su qara kallonta
dubu daya dije t bawa yaran tace su siyo taliya sai kayan miya da maggi aikuwa da gudu suka karba sai kace a mota suka tafi sai gashi da wuri sun dawo dari tabasu tace su raba aIkuwa murna ba' a magana
tashi hafsy tayi ta hura wuta sunada ice fitowa tayi sukayi girkin tare har suka gama kuwa cikin mutanen gidan ba wanda ya dawo ranar hafsy ta barge haushin yunwar kwana da kwanaki kuwa dan ta debi girki daman ga mutumin kauye da son taliya kallonta dije ke yi cike da tausayawa kafin ta tambayeta matsalarta duk yanayin zaman da takeyi a gidan da kowa saida ta fada mata aikuwa take dije ta danna wata uwar ashar tsumi ya motsa nan ta shiga zazzaga bala'i kallonta hafsy tayi taga yadda ta rikede lokaci daya ta koma dijengala dinta ta da 'yar takife jahannama ga fasinja uwar suburbuda da mazga sai da tayi me isarta kafin ta nisa tace ina 'yan gidan suka tafi?
shi yana bakin kasuwa ita kuma kihiyar tawa da innarsa sun tafi suna can gidan su abokiyar zaman nawa dan kinsan duk gidan nan tsoron ta sukeyi har hi me gidan hi yasa ma inna ke binta kamar ita ta haifi dan
girgiza kai dije tayi tare da fadin hukuncin ta kanta zai fara kenan?
dafe kirji hafsy tayi tare da fadin na higa uku dije wane hukunci kum?kaddai kicemin har yanzu muguntarki na nan nidai rufamin asiri wlh karsu rama akaina
dayalla rufawa mutane baki kin san ni idan na tashi rama abu to da basira nake amfani an fada miki gaba duka zan afka musu ni nasan me zanyi musu uwar ita kishiyar taki zanci wlh ni ba ruwanaa
ke dije rufawa kanki asiri wlh wannan inta tauheki ko qafarki baza'a gani ba ruhehiya ce hi yasa ma fa ita kanta inna da hi hamidan din ke tsoronta dan mullikekiyar katuwa ce ance aljanu ne suka hura mata iska wai data hararesu
kallonta dije tayi tare da fadin ke hafsy a ina taga aljanin da har zata hararesu ?
ance tun tana qarama
kafin dije tace wani abu suka tsinkayo muryar hamidan na fadin iskancin banza da wofi wace shegiyar ce ta shigomin gida tasan kuma inna da hansai basa nan har aka taramin yara a qofar gidan yana fada ya qaraso dakin
tunda hafsy tajishi jikinta ya kama rawa ta dinga kallon dije tana yarfa hannu ita kuwa dijen ko'a jikinta illah zuge jakarta da tayi ta lalubo siririn farin glass dinta ta manna a fuskarta tare da qara gyara zamanta
yaye dan yalolon labulen dakin yayi tare da fadin nace wace hegiyar ce ta higar min gida bada izini na ba
cikin rawar murya hafsy tace am dama.....da...ma um...daga...kinga barshi in gabatar masa da kaina daga abuja nake ma'ana birnin tarayya nasan kasan sunan garin ina daya daga cikin hukumar farin kaya ta 'yan sanda masu bincike inda muke bi kauyuka muna bincika yadda suke gudanar da zamantakewar aurensu hakika mun kuma samu yadda mukayi tsammani dan gashi nan mun gani a gidanka sbd haka yanzu basai nayi wani bincike ba zan kira waya jami'anmu na 'yan sanda masu sa kaki suzo su tafi dakai mun same ka dai lafuffuka da dama duba da yadda na riski matarka duk da bata cemin komai ba ta rufa maka asiri amma banga alamar kana kula da ita ba ji yadda dakinta yake ji suturar jikinta gashi tun zuwana na aunata naga bata ci tana qoshi koma taci ta koshin bata samun me kyau dan haka zamu tafi dakai can ofishin 'yan sanda mafi kusa kafin gobe a wuce dakai abuja daga nan sai musan abinyi dakai hukuncin daurin rai da rai ko kuma daurin shekara hamsin
tunda tafara maganar hantar cikinsa ta kada jikinsa yafara mazari
*kun san ance shege na kauye sai tsoron 'yan sanda* ๐
gurfanawa yayi a gurin tare da fadin wlh wlh ranki ya dade alqu'arn idan da laifina a ciki in mutu a tsaye
yaseen laifin hansai ne da innah
qara hade rai tayi tace au wato ma kanada wasu matan kenan?
ah ah guda daya ce kuma itama kaddara tasa na aureta ko hafsy?
nidai ban sani ba cewar hafsy da tayi zuru tana kallon dije ikon Allah tare da yabawa da basirar ta
ah ah hafsy duk wanda yaga yanayin zamana da hansai yasan kaddara ta hada auranmu amma wlh bada son rai ba ranki ya dade in kina yiwa Allah kiyi haquri wlh ban san an fara wannan binciken ba
oh wato sbd shi zaka daina kenan
kafin yabata amsa sallamar su inna ta karade gidan tare da sababi ganinsa da hansai tayi a bakin kofar hafsy yasata tahowa gadan gadan kofar dakin tare da fadin munafiki uwar me kuma kakeyi a anan
alama yakeyi mata da hannu yi shuru yana mata nuni da cikin dakin
uwar miye a cikin dakin da kake nunamin mutuwa tayi ko me
inaga dai cewar inna da itama ta nufo dakin gadan gadan suka qaraso ya kauce ya basu guri
koda dije taga hansai duk rashin tsoronta saida ta ji gabanta ya fadi wata narkekiya ce duk da batasa yawan shekaru amma kam akwai kiba
ganin dije da sukayi a hakimce gata 'yar gayu yasasu dan rage sauti tare da kallon hamidan wacece ita kuma wannan din?
hukuma ya fada kamar me rada daga garin su baba buhari take nan ya kwashe duk bayanan da dije tayi masa ya fada musu
cike da rawar jiki harda rusunawasuka gaida dije suma nasu sharhin ta rattabo musu aikuwa nan duk jiki ya hau tsima suka shiga bata haquri ganin duk sun rude yasa tace su fita zatayi waya duk suka miqe suka fita suna makyarkyata hansai ce karshen fita dan da kyar ta mike bayanta dije tabi da kallo a ranta tace jar ubancan wannan duwawun ai sai inyi matakala dasu in zan hau katanga
suna fita ta kalli hafsy tace y kikaga ni
jinjina kai tayi dan ta kasa magana tasan dije ta ballo musu ruwa
magana tafara yi kamar me waya cikin daga murya ok sir,yes sir su ta dinga fadi kafin daga baya ta ce su shigo ta gama
duk sunyi tsiru tsuru a gabanta se raba ido sukeyi
naso naqarasa muku banida carji afuwan
*vote*,
*comments*
*with 08066364077*
*Alqalamin khady* โ
[16/12, 11:41] โช+234 806 493 3819โฌ: ๐๐๐๐๐๐
TA ME GARI
NA
khadija usman
1โฃ4โฃ
tun sassafe ta shirya ta tafi makaranta a can suka hadu da su rufaida aka shiga hirar yaushe gamo tare da tambayarta yadda tabaro mutanen gida
bayan ta dawo a parlo ta iske mamy zaune ita da wata hajiya saudat qawarta tana duba wasu kaya da sallama ta shigo parlon ta tsugunna ta gaishesu cikin fara'a hajiya saudat ta amsa amma ita ko mamy ciki ciki ta amsa dan har yanzu tana kule da yarinyar tarasa wane mataki yakamata ya dauka akanta amma kawai bari ta turata gidan su naseer tasan acan su zasuci ubanta ba ruwanta koda abu ya biyo baya sunfi kusa
am kinaji na cewar mamy
dije da har ta mike ta fuskanci da ita take dan haka tace eh mamy
maza idan kin shiga ki shirya ki fito kizo habu ya kaiki gidan yayyenki ku gaisa da su kije kiga amare tunda kin gudu bakije kinga gida ba koh ?
ta karasa maganar tana murmushin mugunta
tunda dije taga mamy na murmushi tasan akwai abinda ta shirya mata dan haka cikin ranta tace dena gaigaye mamy nima da shirina zan tafi gudun bacin rana amma a fili saita ce to bari inje in shirya
yauwa to yi sauri kinji
dije dariya ma abin yaso bata a iya shekarin datayi a gidan nan tana iya cewa bata taba samun dariya ko magana irin haka ba a gurin mamy amma yau sai gashi wai ita take yashewa baki dan kawai tasan inma taje ubanta zataci
da sauri ta shirya ta fadawa basira inda zata sannan ta debi guzurinta a 'yar qaramar hand bag dinta ta fito saye da doguwar riga arebian gown cofee colour inda ta sanar da mamy ta fito wasu kaya ta bata tace ta kaiwa yusra zata kirata a waya tarasa dalilin daya sa mamy harda wani farin ciki takeyi dan ta turata gidan a ranta tace wlh kome zai faru sai dai raba biyu kowa yaji jiki
suna tafiya ita da baba habu driver sun zo dai dai wani store tace dan Allah ya tsaya tana zuwa ba musu ya tsaya ta shiga gutin ba jimawa ta fito tace su tafi yaja mota kuwa suna tafe suna hira har suka qaraso gidan
tabbas gida yayi kyau matuka babu makusa inda cikin sanyin jiki ta fito ta nufi bangaren dama dan bata san ya tsarin gidan yake ba
tana zuwa bakin parlourn ta shiga kwankwasawa an dan jima kafin taji ance yes come in
murda handle din kofar tayi ta shiga parlourn tabbas ya hadu iya haduwa ba qarya inda ta shiga da sallama dauke a bakinta ga mamakinta sai gani tayi yusra na washe baki tare da fadin oyoyo sister ta taso da niyyar rungumeta
qamewa tayi a gurin tana kallon ikon Allah murmushi yusrah tayi tare da qarasawa ta rungume dije itama dijen ganin yadda tayin yasata itama yin hakan ta dan jima a haka kafin ta saketa ta kamo hannunta tare da fadin qaraso ki zauna ya gajiyar tafiya ance shekaran jiya kika dawo kinyi gudun hijirar gashi kin dawo kin same mu ya mutan gidan duk lfy suke dai ko?
ita dai dije yake kawai takeyi dan tasan wlh wannan faran faran din da dalili hmmm koma meye ai zan gani bari na biki yadda kk so sakin jiki tayi suka shiga hira tamkar ba yusran data sani ba amma dije ta tabbatar da dalilin yin hakan aikuwa suna tsaka da hira taga wayar yusra tayi qara dauka tayi tare da barin falon ta shige bedroom dinta takai wajen minti 30 kafin ta fito ta sake neman guri ta zauna tare da fadin me za'a kawo miki sister ban dai yi girki ba nasan ze biyo da take away so something with drinks duk akwai su ba matsala
um um ba abinda zan sha ga sakonki inji mamy ta miqa mata ledar hannunta karba tayi tare da fadin tnx
yusrah ce ta kara kallon dije kafin tace naga kinki sakin jikinki ki manta da komai kawai kinji
no ba haka bane tashi ma zanyi in tafi naga yamma tayi
kije ina? cewar yusrah a dan hade rai
gida mana kinga bamuyi da baba habu ya zo ya daukeni ba gara in tashi da wuri dan taxi zan shiga
ah ah wlh bazai ma yiyu ba kizo gidan nan baki hadu da yayanki ba ai bazai ma sabu ba nasan ya kusa dawowa kawai ki jirashi ta karasa maganar tana murmushin da ita kadai tasan dalilin yinshi
tsaf dije ta karanceta a ranta tace hmm kin girmeni amma baki fini wayo ba tabbas in kuka min abinda ban gamsu dashi ba toh naku salon muguntar da zanyi muku saiya ci uwar wannan a fili kuwa cewa tayi ok to bari in leka bangaren ya habeeb ko
ok ba matsala muje in rakaki miqewa tayi ta suka fita
part din sajida zaune suka sameta sanye cikin riga da wando three quater sai wata 'yar mitsitsiyar riga wadda da kadan ta rufe cibiyarta kanta yasha qananan kitso jikin nan sai kamshi ke tashi sajida bata da kyau kwarai amma akwai wanka domin irin matan nan ne masu son komai suga sune a farko shiyasa komai nata yake kan gaba ko cikin friends dinta
da fara'arta ta tarbesu amma ta rasa dalili tun ranar da ta tambayi habeeb meye alaqar su da dije ya fada mata da ganinta da tayi gurin dinner taji sam bata ra'ayinta ko da ta ganta yanzu gabanta saida ya fadi amma sbd halinta na 'yan duniya kuma goggiyar 'yan boko yasata sakin fuska nan ta karbi dije hannu bibbiyu abinci me rai da motsi takawowa dije inda ta bude ciki taci t koshi dan dama yunwa takeji tunda dawowarta kenan daga skull mami ta tunkudota nan ba laifi amaryar habeeb ta iya girki amma dai gaskiya basu dace ba cewar dije dan wannan ai kusan sa'arsa ce
sun dan taba hira kafin suka tashi suka koma part din yusrah inda suna shiga yusra ta shige ciki tace ma dije tana zuwa miqewa tayi itama ta shiga toilet din dake parlour ta dauro alwala tazo tayi sallar la'asar
bayan ta idar ne ta koma kan kujera ta kama kallon wani film da ake haskawa a bollywood film din yatafi da hankalinta hakan yasa sam bataji tsayuwar mota a gidan ba illa jin sallamarshi kawai da taji yayi
amsawa tayi ga mamakinta shima din cikin sakin fuska ya shiga fadin ah ah mutanen kauye yaushe aka dawo?
kallon mamaki tayi masa tare da fadin shekaran jiya
to an dawo lfy?
lfy qalau suna gaisheku
hmmm muna amsawa
ok bari na shiga ciki in dan watsa ruwa
shiru tayu bata bashi amsa ba a ranta tace kinga dije anya kuwa bazaki tashi ki gudu ba ba mamaki mutanen nan shirya yankaki suka yi dan kin san dai ko giyar wake kika sha bamai yimiki dariya irin wannan amma da ganin yadda suka miki kin san da mugunta a zuciyarsu dan haka tunda qafafunki ki tashi ki fece kafin a karya miki su miqewa tayi ta nufi qofa harta daga labulen ta tsinkayi muryar yusra na fadin ina kuma zaki?
am dama zan tafi ne tunda ya dawo
cikin hade rai tace mamy bata fada miki cewar sai kinyi kwana biyu zaki koma ba
zaro ido tayi tare da fadin kwana biyu fa a nan gidan?
eh ko bazaki zauna ba?
to amma ai ban taho da kaya ba kuma ma skull dina fa?
iyeeeh lallai yarinya wato skull dinki da yaushe kika fara bokon yau she ma ministry tasan da zamanki shine zaki fadamun makaranta to bari ma kiji da ke kin dauka abinda kikamin kisha a banza wlh duk duniya bawanda ya isa ya hana inci ubanki ba duka ba zagi amma zaman prison zakiyi a gidan nan na tsawon kwana biyu cikin awa biyu kika barar min da burin danaci a bikina toh ke cikin kwana biyu sai duk wanda ya ganki ya tausaya miki dan haka kada ki kuskura ki fita a gidan nan dan dama an sanar da me gadi kada yabari ki fita
kirjin dije fa ya shiga lugude inda takeji kamar ta arta bata san tanadin da sukai mata ba tasan ma makaman yakin su sunfi nata dan haka ta yunkura da niyyar artawa taji ya riketa haba classic lady ina zaki kuma ai kinzo gida kuma sai jibi ya fada tare da hade rai mutsu mutsun kwacewa takeyi inda ya riqe hannun da karfi riqo bana wasa ba hakan yasata sakin qara don jinda tayi yana barazanar ballata wurgi yayi da ita gefen kujera inda saida kanta ya dan bugu kafin ya dauketa da wani wawan marin dayasa ta ganin star wata qarar ta saki yayi saurin aza hannunshi a saman bakin shi alamar tayi mishi shuru
kasa shirun tayi inda nan ya shiga fyadarta yusra na gefe tana dariyar mugunta saida ya gama canzawa dije hallitar fata abinka da fari duk jikin sai yayi ja yayi rudu rudu kafin ya kyaleta ya zauna yana maida numfashi
cikin daurewar fuska yace dan uwarki ubanwa yasa kiyi min abinda kikaimin
shiru tayi in banda shasshekekar kuka ba abinda takeyi da alama dije akwai zuciya
yusar ce ta taso cikin daga murya dan uwarki ba magana akeyi miki ba ta karasa maganar cikin daka tsawa
uwarki ce๐
sukaji ta ce ๐
cikin zaro ido kusan a tare suka fadi
me kikace
cikin jan kuka da majina tace cewa nayu uwarki ce kuma wlh tunda kuka taba mana godiyarmu duk sai kunci ubanku
kallon kallo aka shiga yi shi naseer yana nazari da tunanin rainin hankalin yarinya itako yusra ta tuna da yadda suka kwashe kwanakin baya amma kuma kai ai da gani wannan ba irin wadan can bace dan haka a hasale tayo kan dije da niyyar dukanta wata irin zabura dije tayi kayo cikin yusra ganin da yusra tayi dije tayo kanta yasata sakin ihu tayi bayan naseer
ke ni zaki yiwa iskanci cewar naseer wlh zan babbala ki
itako dije ko'a jikknta ta nufosu tana qara barw baki miqa hannu yayi da niyyar riqota aikuwa tayi caraf da hannun a bakinta ta dankara masa cizo kuma gam ta rike hannun qara ya saki wadda tasa yusra saurin barin gurin ta ruga da gudu tayi bayan kujera duk yadda yaso ta saki hannun ki tayi saida taga jini yana bin yatsansa besan sadda yakai mata mangari ba aikuwa zafin da taji ne yasata tashi ta dane bayansa ta shiga yakushinsa tako ina baji ba gani cizo duk ta dabaibayeshi ga azabar da hannunsa keyi ga jini nabin yatsan dan ta dauke mai fatar koma cinyewa tayi oho waya sani
duk yadda yaso yaraba dije da jikknsa abu ya faskara gashj tana kuka tana yakushinsa duk ta damalmale masa jiki ta hada masa jini da majina cikkn daga murya ya kira sunan yusra sakamakon wani dankareren cizon da dije ta mallara masa a kunne hakan yasa shi finci kota da iya qarfinsa ta fada kan kujerar da yusra ta labe a bayanta riqe da waya jikinta na makyarkyata tana son yin kira takasa nemo number ma ido biyu sukayi da dije aikuwa ta kwalla wata qara wadda duk gidan ya amsa kanta dije tayi ta cakumeta aikuwa yusra memakon ta tabuka wani abun sai kawai ta bude baki ta shiga kurma ihu nan ko dije ta fara caskala ta itama harda rabon nata cizon a kumatu
ganin tana shirin kashe masa mata yayo kanta ai kafin ya qaraso ta saki dije ta qara nufarsa ba shiri shima ya juya dan ko kadan bazai so ta qara dane shi ba yarinya kamar mayya sai shan jini takeyi
habeeb na zaune a parlour shida sajida suka tsinkayi ihun yusrah da sauri suka taso suka nufo part din suna zuwa suka shiga kokarin budewa dan lokacin da naseer ya kamo dije da niyyar duka yusrah ce harda rufe kofa dan haka suka shiga bugawa yana fadin nasir nasir lfy bude mana
yusra ce ta nufi kofar danta bude dije tasha gabanta tanata kada kai tana bude baki naseer ko nacan yasa tissue yanata qoqarin goge jinin dake bin hannunsa da bayan kunnansa fuskarsa kuwa tuni duk ta hade tayi burdin burdin dan tasha yakushi
da dabara yasamu ya qaraso ya bude kofar
ya salam meya faru haka naganku a wannan yanayin ?
kafin yabada amsa yaji kukan dije daga cikin parlourn
leqawa yayi aikuwa ya ganta ta fara jifa da duk abinda ke falon tanayi tana kuka
tambayar nasir yayi meke faruwa nan ya sanar masa dalili
gurin dije ya nufa inda take kokarin jefo da wani fishers dishuis ya riqeta gam tare da hadata da jikinsa ya rungume ta tsam ya shiga yi mata addu'o'i a kunne
dije na jinsa tayi luf tare da qara gyara kwanciyar kanta a kirjinsa dukansu sai suka tsinci kansu cikin yanayi me wuyar fassarawa dije kam sai sauke ajiyar zuciya takeyi tare da qara shakar daddadan kamshi turaren dake jikinshi har take taji wani bacci na shirin kwasheta
jin shirun da sukayi ne yasa naseer leqowa dan duk su yusra da sajida gayyar tsorone hakan yasa suka kame a waje
yanayin daya gansu ciki duba da yadda yaga habeeb ya wani rufe ido bakinsa saitin kunnen dije gashi kuma ita ta wani lafe a jikinshi
duk radadin da ilahirin jikinshi keyi mishi sai yaji ya dena ji yayin da yaji zuciyarsa tayi masa wani irin zafi dan me zai rungumeta haka to me hakan ke nufi
jin shirun da matan sukayi ne yasa su dan shirin leqowa dan da alama abun ya lafa tunda sunji shiru aikuwa suna leqowa idon su yasauka akan abinda naseer ya kurewa gani
daram dammmmmm gaban sajida yayi dubs da yadda taga mijinta rungume da wata mace bata san lokacin datayi kansu ba tana zuwa tajanye dije daga jikinsa dije najin an jata tayi saurin qara langabewa ta zube a gurin
shi kuwa bude idonsa yayi a hankali ai kuwa ya saukesu cikin na sajida data kafeshi da ido ckin tuhuma waigawa yayi ya kalli inda dije ta sheme kafin ya maida dubansa ga naseer yace sai ku maidata gida tunda kun rama
yana gama fadar haka ya juya ya fice a dole sajida ta bishi itama............
*vote*
*comment*
*with 08066364077*
*Alqalamin khady*โ
[16/12, 11:41] โช+234 806 493 3819โฌ: ๐๐๐๐๐๐
TA ME GARI
1โฃ5โฃ
team dijeee kuna qarawa wutar nan fetur sai dai fa kuma hmmm a dai yi shuru yanzu muci gaba da gashi
ga masu tambayar littafin daga farko masu kirana da masu yimin mgn ta pc pls ku taimaka ku dinga tambaya a group dina in baki ciki kiyi min magana zan tura link kiyi join nasan mutan gidana akwai karrama bako da kin tambaya zasu hau tururuwar tura miki dan akwai su da karamci ๐
ina mugu mugun ji daku member's na khadeeja fans novels๐
******
ita kam yusra ko ta kan dije dake kwance bata qara biba ta lallaba ta shige daki shima naseer din binta yayi inda ba shiri dole ya dauki emergency care box suka nufi part din habeeb yayi musu dressing kafin suka dawo ind take kwance har yanzu tana nan yadda suka barta itako dije bacci ne ma yadauketa a gurin sai sauke ajiyar zuciya takeyi cikin baccin
koda suka shigo suka risketa a hakan naseer ya kalli yusra yace ke jeki tasheta ta tafi gida
wani
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 25