Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba zan iya yawon bin ɗaki ɗaki gaisuwa ba tunda ko ba abunda kuka gada sai yawa kamar ƴaƴan geto area(lol).

Bai tanka ba ya riƙe hanun mami suka nufi hanyar da zai sada su da sashin hajiyar shi..
_tabbas babban gida ne da ya amsa sunan shi,aƙalla akwai sashi sashi kusan shida da boys quaters a cikin domin irin compound house ɗin nan ne,matan aure huɗu ke cikjn gidanko wacce da sashin ta,saura biyu na mai gida da sashin baƙi.  Gidan retire commisioner of police MU'AZU BARAU ke nan wanda ya bauta wa ƙasar shi cikin gaskiya da adalci   har ya aje aiki wanan dalili yasa har wana n lokaci ba'a manta dashi baa,yana samun ɗumbin alherai a wurin manyan mutane,yaran shi duksun kawo ƙarfi kowa nada abun hannu gwargwado yadda zai iya riƙe kan shi da iyalan shi sai yasran yan uwa birjik dake tare dashi a gidan da yan jikoki dake zuwa.


A hankali suke taka wa duk inda suka  gifta  harabar gidan sai ya tsaya an kwashi gaisuwa,itakam  ko a jikinta har suka nufi ƙofar da zai sada su da palon hajia lanti da sallama ya tura..,aka amsa masu daga ciki domin sashin kullum a cike yake da yan uwa,ɗiya da jikoki.

Hajia AMINA(wacce aka fi sani da lanti )na zaune saman kujera mai zaman mutum ɗaya sanye cikn lafaya kure shar abunka da baƙar mace doguwa sosai mai jiki sai ya amshi jikinta ainun,baka gane yanayin fuskar ta domin ba kasafai ta faya fara'a ba haka ba zaka kirata miskila ba ita dai haka yanayin fuskarta yake kuma bata cika shiga tsabgar dabe shafe taba musamman sha'anin yara,amma idan ka sake ta buɗe baki tayi magana akan ka!,taka ta ƙare ba zaku taɓa shan inuwa ɗaya ba wanan dalili yasa baa jinta da abokan zamanta har  yanzu da girma ya kama.

Itace matar aure ta biyu a gidan,Allah ya albarkace ta da haihuwar yara shida duka maza(shafi'u,jafar,hamza,umar,muhammad sai usman). Ko wane na zaune lafiya da iyalan shi cikin rufin asiri suna nan nan da ita kullum burin su faranta zuciyar taal,musamman a wanan lokaci da  mahaifin su ƙarfi ya ƙare sai yan uban ci ya tashi a gidan kowa nashi ya sani dalikin da yasa basa nisa da ita sosai kenan,idan aiki ya fitar dasu matan su da yara na tare da ita ko wace n ƙoƙarin faranta mata banda zainab wacce suka samu matsala tun lokacin da taga an kwashi shekaru da auren su bata haihu ba har matar usman da tazo daga baya haihuwar ta uku a yanzu.

Wanan yanayi na fuskar hajia lanti ke saka zainab shiga taitayinta duk lokacin da suka yi ido huɗu koda me tazo gidan sai tayi sanyi laƙwas.

Abunka da dangin miji doctor faiza ta faɗa wa hajia ai matsalar rashin haihuwar daga zainab ne shine dalilin da yasa ta tsane ta uwa uba tun bayan haihuwar mami da abubuwa ke faruwa da zainab ta tashi hanklin kowa lokacin hajia lanti ta tsaurara tsana a gare ta,a nata hasashe haihuwar ce zainab bata so da ɗan ta.

Lura da zainab tayi kowa gidan yi da itayake musamman matan yan uwn mijinta sun samu fuska wurin uwar mijin nasu ko wane lokaci suka haɗu ƙoƙarin gasa mata baƙar magana yake a gaban hajia har shi muhammad  din amma ba mai ƙwaɓar su.

Tun daga nan ta fara ja baya baya da lamarin su cikin ikon ALLAH ma a samu gurbin karatu a nan abuja tana masters  ɗinta wanda ana kamalla wa zata zama cikakkiyar barrister.

Wanan ya ƙara tunzura hajia gani take zainab tafi ƙarfin ɗan nata,tun aga haihuwa ɗaya ƙalau ƙalau yarinya na ƙoƙarin shga shekara sha ɗaya shiru babu wani labari!

Zube wa tayi ƙasa tana kwasar gaisuwa...,sai dai ko kallo bata ishi kowa a wurin ba.

Hasali ma hankalin su na kan muhammad  suka gaisawa duka...,mami ta tsallake su ta haye jikin hajia.

Wanan na ɗaya daga cikin dalilin da yasa sauran matan basa ƙaunar zainab duk da cin kashin da ake nata amma hajia bata da kamar mami cikin jikokin taa!

Yaran kuwa da sun gano mami kowa ke kama kanshi saboda cin zalin su taje bil haƙi kuma babu wanda ya isa ya kwabe taa.

Granny yunwa nake ji!,shafa kanta tayi.
Waya faɗa maki idan anyi kwalliya ana cin abinci?

Ehhh haka ne bana son ɓata kwalliya na,amma dai zan dha zoɓo irin mai daɗin nan da kike yi.
Ja'ira kawai buɗe firij ki ɗauko yadda zai ishe ki.

A guje ta sauka daga jikin ta tare da tattake ƙafafun sauran yarsn dake wasa a ƙasa ta haura wurin firij a...

Kausar matar babban ɗanta tayi magana"hajia tunda muka iso nake sha'awar zoɓon nan kin hana mun nida keda lalura ma(ta nuna ƙaramin cikin da take ɗauke da shi),sai ga mami ance ta sha yadda zai ishe ta".

Banza tayi da ita domin ba kasafai ta cika mai da martani baa!,siyama matar umar ta amshe,kin san itace yar gwal cikin jikokin hajia saboda haka bata san babu ba kawai ki haɗiye ƙwaɗayin ki auntyna kya dha shauran ta anjima da yamma idan hajia ta yi buɗe baki.

Haka dai duka cigaba a yaɗa habaici akan zainab wacce ba ita ta hana aba su zoɓo baa...

Muhammad  kam hankalin shi na awurin hajia ko banza ba ya maida hankali akan ƙana nan maganganun mata.

Jug mami ta dawo dashi shaƙe da zoɓo sai cup ta nemi wuri saman kujera ta zauna kamar wata babbar mace sauran yaran suka zuba mata idanu wanda kusan biyu biyu ne a cikj ta girma,uku sa anta ne duka maza sai mata biyu da suka girme ta d namiji ɗaya wanda shine  babba cikin jikokin(abdul gafar) yana can cikin gida.

Ƙare masu kallo tayi duke,yana kallon ko zaku sha ne?,yan warinta da ƙana nan duka amsa da eh!.

Dariyata kece dashi na mugunta!,abu mai sauƙi kowa yaja layi zan baku ai.

Zainab sai zullumi take cikin zuciyarta kada mami taja mata wani tashin hankalin!,ai kuwa suka ja layi duka ta shiga auna zoɓo tana basu a cup suna sha cikin jin daɗi yau baa masu mugunta ba sai ƙyalƙyalar dariya take...,hajia kau abun ya mata daɗi yan jikokinta sun haɗa kan su nan suka shige daƙin baccinta tare da muhammad  dayace yana son magana da ita  mai muhimmanci.

Suna shiga ya nemi wuri a ƙasa ya zauna tareda zayyane mata duk abunda ya faru a daren jiya daga bisani ya nemi alfarma a sanarwa mahaifin su domin a duba lamarin a idon basira ya fara tsorata matuƙa.

Tsaki taja,me akayi akayi zainab?,ita ɗin banza har zaka yadda da makircin ta akan gudan jinin ka?,ina ce nan muka zauna a kai a ɗakin nan kayi mata gargaɗi mai ƙarfi akan aibata mami?,yau kai da kanka kaxo mun da wanan maganar banza haka?,yaushe kazama shashashan namiji ne moha!?.

Wallahi a hir ɗinka ta miƙe zuwa habyar waje tana bambamin faɗa...,ke zainab ki kiyaye ni fa!, bana son makirci da munafuncin banza.

Daidai inda zainab ke zaune ta tsaya,ɗana da jikata sun fi ƙarfin ki,ki koma ki faɗa wa bokan ki asiri ba zai taɓa tasiri a jikin shi ba kwaraki sake sabon shiri daidai nake dake dominnaga ina ɗaga maki ƙafa a dalilin wanan(ta nuna mami) amma bakya gani!,kwana nan zaki nufi gidan ku domin baki isa ki tayar mun da hankali ba oya tattara ta ku tafi bana buƙatar ta a nan,wa yan nan sun ishe ni(ta nuna sauran surukan taa).

Shiru zainab take kanta na ƙasa ko a jikinta domin  idan da sabo ta saba da ire iren wanan cin mutunci daga hajia!,muhammad  sai hakuri yake bata domin da yasan haka zai aru da bai kawo maganar ba!.

yanzu duk sauran yan uwan shi sai ta faɗa madu ayi mahi zaman kanshi,abunda yafi tsana tsoguri tsoma.

Bai wani tsaya ba ganin hajia tayi shiru ya ce da ita zai shiga suleja wani aiki sai yamma zai dawo.

Allah tsare hanyata mashi ya wuce rai ɓace...,kamar jira suke ya fita ai kuwa aka mata chaaaa da ƙananan maganganu!

MAMI kam sai ɗura wa yan uwata zoɓo take tana dariya hankali kwance ko sha bata yi ba tun wanda tasha wurin firij.

Sai da zainab ta faki idanun shi ta miƙe zuwa sashin hajia mariya..
_Itace babba a gidan mai faɗa a ji kuma tana da sauƙin kai da faram faram amma fa akwai son girma domin tana iya baki kyautar dubu ɗari kai tsaye domin ta sayi girma wurin kibbutz!,yaranta takwas amma huɗu ke raya biyu mata sune manya a gidan sai sauran mazan jafar ɗin haji lanti ya girme su._

Sashin  ba laifi shaƙe da ɗan mutum musamman mata yan maula duk da mahaifin su muhammad  ba wani shahararren kuɗi ne dashi baa,amma ya tara zuri a abun alfahari masu arziki matuƙa kowa da irin buɗin shi suke riƙe da gidan.

Cike da girmama wa aka amshita sai hidima masu aikin sashen suke da ita aka cika mata gava da ksan ciye ciye.

Bayan gaishe gaishe wuri ya ɗan natsa hankalinta na kan chat da suke da sisterta safiyyah akan abubuwan da suka faru jiya!.

Sai da hajia ta sallami yan maula suka ƙara gaisawa ta tambayeta babu wat matsala ko?.

Tace babu sun zo yini ne taga sashin can mutane sun yi yawa a wuto nan du gaisa.

Allah sarki ai ya shigo kafun ya wuce mun gaisa,ina mai sunan hajia?,tana can suna wasa.

Shiru ya biyo baya daga bisani tace bari ta ɗan kwanta kafin a kira sallah tunda baƙi sun rage. A fito lafiya tayi mata tare da kishingiɗe wa ƙasa chat yayi daɗi.

Dama duk zuwanta gidan sashin hajia mariya take yini,tayi yadda takeso har su tashi wuce wa,nan bacci ya fara ɗaukan ta inda take kwace...,cikin baccin ta hango mami cikin jajjayen kaya saman wani babban tsauni ƙasa kuma yarane wanda ba zasu wue sa ana ba suna kewaye ta tsaunin wuta na tashi a tsakanin su cikin dare ne sosai a dokar jeji!

Ta furta;GREAT ZUMBA!
sauran suka harɗe hannayen su a ƙirji tare da furta;GREAT(cikin tsigar girmamawa).
Ta sake faɗa cikin ɗaga murya;GREAT  YOUNG  FEARLESS!

Suka amshi da;GREAT!.
Gaba ɗaya suka haɗa baki:BLOOD FOR BLOOD,forever we remain loyal,we are pround to be ,we learn to be fearless,rouget and heartless,we are bound to provide security  for ourselves so help us GREAT ZUMBA!.

ZUMBA!ZUMBA!!ZUMBAAA!!!

Sai ga sauran yan yan mami data ba zoƁO an saka su tsakiya tare da kece wa da dariya mai ban mamaki suna ta kuka!!!

Follow
comment
vota
and
share.
[6/4, 11:15] LEEMA: *🅱RILLIAT WRITER'S ASSO....*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*☠ƘUNGIYAR ASIRI☠*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_{ƙirƙirarren labari}_
       *NA*

          *L££MA*
wattapad
*@leemaMuhammad826*

  _Sadaukarwa gare ku_👇🏻
*_MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)_*

*_REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)_*

*MACE MAI NEMAN ALJANNA WATTSAPP GROUP ina miƙa saƙon gaisuwa ta musamman a gare ku ALLAH SAKA MAKU DA ALHERI A KAN HIDIMA DA KUKE D AL'UMMA❤*


*🅿7-8*

      Yaran da suka sha zoɓo su biyar ne reras jere tsakiyar  yan
*ƘUNGIYAR ASIRIN* sai kuka suke yi saboda tsabar ruɗewa!.
Tsawa mami ta daka masu mai firgitar wa wanda ya saka su duƙe wa aƙasa kamar zasu faɗa cikin wutar dake ƙara kuruwa kamar ana zuba mai fetur.

Kuyi ma mutane shiru ai ƙwaɗayin ku ya ja maku!,dama ina haƙe da ku irin cin zarafin da iyayen ku ke yiwa mummyna saboda rashin aihuwa,sai na kashe ku kuwa ma ya huta!.

Abunka da yara ne duka basu haura shekaru goma baa,ukun ma basu kai baa,ko wanne ya shiga rera marayar kuka mai ban tausayi sun ji an ambaci mutuwa ko wanne ya fara kiran"mumy,daddy!".

Suna ji suna gani mami ta bada umurni a ɗaure ko wanne cikin su jikin bishiyar dake jejin wanda ko wane bishiya akan babban rami a ƙasa mai zurfi wuta na tashi,saman bishiyar kuwa ƙarfuna ne masu tsini kamar allurai da ka ɗaga kai suna kallon ka jira suke kayi motsi su fara nasu aikin.

Dama saman tsaunin nan mami ta tashi sama kamar balbela hanunta riƙe da takomi,hannu ɗaya kuma babban ƙwarya ne ta nufi wurin da suke da zubar chaka ma kausar nan take zainab ta zabura daga baccin da ya fara ɗaukar ta a guje ta nufi sashin hajia lanti tana faɗin"kausar!"..

Koda ta shiga palon cike da ɗan mutum kowa yayi cirko cirko ana jimamin abunda ke faruwa,kutsawa tayi cikin mutane har ta isa tsakiyar palo inda  yaran nan biyar ne kwance a ƙasa ciki ya haye kamar mai shirin haihuwa yau ko gobe!,mami na zaune saman kujerar data fara zama tun farko babu alamar tsoro ko damuwa a tattare da ita.

Ɗaya bayan ɗaya ta shiga jijjiga su babu mai motsi har ta iso wurin kausar ta  ɗaga rigar ta,fasa ihu tayi tare da fido idanu a waje ganin alamar wuƙa an suke ta har jini ya bushe a jikinta!.

Cike da zafin nama ta nufi mami gadan gadan....,kawai ta kauce mata ta bugu da bango juwa ya kwashe ta ƙasa ta zube!

Mami ta isa wurin da take kwance tana shafa jikinta...,idan baki daina shiga hurumi na ba wata rana zaki yiwa rayuwar ki mummunar ila ne mummy!

Tana ƙoƙarin ɗagowa ta danne ta sosai!,a haba wanan ne kuma baki isa ba kawai kisha bacci lafiya sai da safe.

Babu wanda yabi ta kan zainab domin ba sonta ake baa,chirko chirkon da akayi jiran isowar jami'an tsaro ake yi an buga masu waya.

Abunda ya faru bayan fitar zinab a sashin hajia lanti shine;bayan mami ta gama ɗura masu zoɓon da yan mintuna suka fara amai!,idan wanan ya gama wanan ya fara tun ana ɗauka da zauƙi har suka galabaita kafin a nufi asibiti sun fita hayyacin su ba mai motsi.

Nan wuri ya kachame da koke koke sai kiraye kirayen waya...,aka tasa inna mardiyya mai aikin hajia lanti a gaba sai ta faɗa abunda ta zuba a ciki??

Rantse rantse ta shiga yi bata zuba komi ba domin ba aƙalla sun share shekaru tana aiki a gidan wani abu makamancin haka bai taɓa faruwa baa!.

Iyayen yara suka tirje akan lallai mami zaa bincika domin dai tare suka sha me yasa babu abunda ya faru da ita?.

Mami kau tace ai nan suke tare babu wanda yaga tasha zoɓo,hasali ma a gaban kowa ta basu har ya ƙare bata sha baa!,baa sake bita kanta ba hajia tace lallai ne a kira jami'an tsaro su tafi da inna mardiyya.

Mutame da dama dai basu goyi bayan a tafi da ita ba domin dattijuwa ce mai gaskiya da amana.

Ana haka ne zainab ta shigo!,amma abun mamaki cikin su babu wanda ya  ga alamar yanka a jikin kausar sai zainab shi yasa ake ganin shirme kawai take yi bata cikin hayyacin ta.  Ubannin yaran sun iso gidan har da muhammad dama an jima da kiran su a waya....,da kyar aka rarashi hajia tayi hakuri kada a tafi da inna mardiyya,a fara zuwa dasu asibiti idan an tabbatar guba suka ci sai a shiga bincike.

kwasan su akayi zuwa asibiti,iyaye mata na gida saboda ruɗewa muhammad  bai nemi zainab ba har suka fita tana kwance wurin data faɗi!

Duk wanda ka gani a wurin hankalin shi a tashe sun sha kuka banda hajia lanti duk da abun ya taɓa zuciyar ta amma ta daure kada ta karya masu zuciya. Mami kau daɗi fal ranta ko ba komi sun ɗanɗana kwatan kwacin ciwon da mummynta keji idan suna mata gorin haihuwa.

Katse shirun tayi"kukan me ku ke yi wai?",ku kwantar da hankalin ku babu wanda ya mutu a cikin suboats,kawai Allah ya jarabce ku ne domin ya gwada ƙarfin imanin kurt(za ku kasance masu tawakkali ko zaku zama butulu marasa godiyar ALLAH?).

Hajia lanti tace kwarai kuwa mami,yarinya ƙarama da kaifin basira kuma naga dai haihuwar nan lokaci near, ALLAH ke bayar wa ga wanda yaso kuma ya amsa idan lokacin ka yayi!,sai muyi tawakkala Allah da ya bamu su idan ya amshe su zai bamu wasu.

Granny inace ko mutum ke ba kanshi haihuwa ai?, wane mutum!,haihuwa,aure,arziki da mutuwa duka lokaci ne babu wanda ya isa ya baka shi.

Amma kun san da haka kuke cima mummyna mutunci akan rashin haihuwa granny?, cikin palon babu wanda bai sha jinin jikin shi ba domjn basu yi tunanin mami tana gane abubuwa haka baa,yawanci idan sun zo gidan hankalinta na kan yara ne ashe tana hankalce dasu.

Hajia lanti ta yafutu ta da hannu,zo nan ki zauna kusa dani mai suna na,wanan ba maganar yara bane kar ki sake cewa komi kinji?,tana lafe gefen hajia tace saboda bakwa son gaskiya baa!

Kallon matan dake tsaye suna zirya tayi,idan zaku gyara halin su ko wacce ta kwantar da hankalin ta babu abunda zai faru da yaran kurt,amma idan ku ka sake zagin mummy na sai dai ku haifi wasu yaran!.

aƙalla sun jima zugum har aka kira sallah kowa ya nufi wurin sallah,mami ta tayar da mummyta tayi sallah.
Tsam ta miƙe kanta na ciwo amma ta rasa me ya fau da ita near,ta kasa tuna komi haka ta nufi hanyar ɗakin da take sallah idan tazo...

Tun suna sallah wayar hajia keta ruri har aka idar ta miƙa hannu,lamban uncle jafar ta gani.

sallama hajia tayi,sai suka ji ta furta alhamdulillah ina suke?,masha Alah sai kun iso lafiya ALLAH kawo ku cikin aminci.

Tunda ta fara wayar hankalin su na kanta har ta kamalla sanan ta dube su;sai ku gode wa ALLAH yaran ku suna cikin ƙoshin lafiya gasu nan dawo wa gida.

Ko wacce ta shiga washe baki suna gode wa ALLAH...

Zainab na ɗakin baƙi bayan ta idar da sallah ciwon kai ya matsa mata bata ko iya ɗaga kan,kishingiɗe wa tayi saman sallaya sai bacci.

Isowar su gida yasa aka sake dawo wa palo ana jirar shigowar suasion,mami da sauran yaran suna kusa da hajia har iyayen su maza suka shigo da sauran yan uwn sumul kamar ma ba abunda ya faru.

Ko wane cikin yaran ya koma wurin iyayen shi mata suka rungume yaran cike da so da ƙauna,sai lokacin muham ya lura zainab bata wurin ya yiwa mami alama da hannu taje wurin shi,"ina mummyn ki?",tana bacci kanta na ciwo ne.

Babban yayan su ya yi bayani an duba kowa a asibiti babu wani matsala sai yan magunguna da aka basu kawai.

Godiya suka yiwa Allah dukan su hajia tace ya kamata a fito da abinci kowa yaci tunda hankali ya kwanta....,masu aikin suka shiga shirya masu abincin saman babban kafet na cin abinci.

muhammad  ya riƙe hanun mami suka nufi ɗakin da zainab take bacci...,tashinta ya shiga yi su tafi wurin cin abinci!,cikin bacci tace ba zata iya fita ba kanta na bala'in sarawa ne.

Hankalin shi bai kwanta yace kawai ta tashi su tafi gida,da kyar ta miƙe hanunta dafe da goshi hannun shi zagaye a ƙugunta suka fito....,kallo ya dawo kan su ,haushi kamar ya kashe sauran matan domin mazajen su ba masu yawan zama bane basa samun kulawa sosai irin haka.

Hajia tace menene kuma?,bana son tashin hankali fa!,hajia kanta ke ciwo zamu wuce gida.

Allah kai ku lafiya kawai tace!,sauran yan uwan shi maza suka mata fatan samun lafiya,matan kuwa babu bakin magana.

Sai da suka isa wurin mota yace ina jakarta  da takalmi?,ta nuna hanyar sashin hajia mariya.
Sai da ya zaunar ta ita,mami ma ta shiga sanan ya nufin sashin ya kwaso kayan hajia mariya tayi masu Allah tsare gaba suka nufi gida.

Har suka isa tana cije leɓe ya kwantar da ita a daƙi tare da samo mata magana da kyar tasha,ya nufi kitchen tare da mami suka girka taliya a sauƙaƙe.
Bata wani ciba  ta koma bacci...,yinin ranar bacci kawai take har dare sanan ta warware tayi wanka da taimakon mijinta suka baje a palo yana tambayar ta abunda ya faru a babban gida bayan tafiyar shi?.

Ni ban san komi ba kawai ta bashi amsa,ya maganar tafiya kazaure?.

Mami tace wai har yanzu baki haƙura da tafiyar bane mmumy?,harara ta watsa mata kawai domin babu abunda zai hanata zuwa kazaure tare dasu a gobetween,sai dai idan ta tuna da maganar mami na sai dai gawarta sai tsoro ya ziyarci zuciyar ta!.


follow
vote
comment
share
[6/5, 14:48] LEEMA: *🅱RILLIAT WRITER'S ASSO....*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*☠ƘUNGIYAR ASIRI☠*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_{ƙirƙirarren labari}_
       *NA*

          *L££MA*

wattapad
*@leemaMuhammad826*

  _Sadaukarwa gare ku_👇🏻

*_MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)_*

*_REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)_*



*🅿11-12*

      Kallon zainab yayi cikin kulawa"kiyi hakuri mana Darling har wani lokaci",kamar zata yi kuka ta zame ƙasa daga saman kujera,yanzu ka mun adalci kenan?,wattani nawa rabona da iyaye na?,idan kai aka yiwa haka ya zaka ji?.

Wattani kika ce,akwai wacce zata share shekara bata ga iyayenta ba kuma suna a gari ɗaya bare ke da akwai taraza sosai a tsakani.

Cikin ɗaga murya ta fara magana, daɗin auren bai kai mun nan ba da zan man ta da iyaye na har tsawon wani lokaci ban waiwaye su ba,kamar yadda na faɗa maka idan kaga ban tafi tare da kuba zamu haɗu a can!

Ɗaki ta wuce abunta Mani nata kwasar dariya...,uhm mami taurin kai yayiwa mammyb ki yawa na rasa yadda zan shawo kanta. Kada ka damu daddy zan maka maganin ta yadda ko kara ka aje ba zata sake tsallake wa ba!.

A'a ban saki ba domin Ni al'amuran kima sun fara bani tsoro,wai meke damun kine?,dariya tayi kuma"kada ka tashi hankalin ka babu abinda zai faru da kai,sanin abinda ke damuna idan lokaci yayi zaka ji kuma ka gani sai da safe daddy!".

Ɗakin ta kawai ta nufa yana wurin zaune cikin mamakin ta ..,daga bisani ya kashe kayan wutan tare da rufe ko ina ya wuce ɗaki.

Tana kwance hankalinta ba kan waya
kamar bata da wata matsala a rayuwa,zee tashi ki haɗa mun ruwan wanka, ɗan guntun tsaki taja,nifa bana son damuwa kawai baka da halin ganin mutum yana hutawa sai ka dame shi!.

Nike damun ki zee?,bayan kai akwai wani ne cikin ɗakin nan?,uhm Allah baki hakuri in shaa Allah zai haɗa ki da daidai ke  ya wuce Ban ɗaki....,gyara kwanciya tayi tare da cigaba da surutai ƙasa kasa.

Yana tsakiyar wanka ta kwala ihuuu!,babu shiri ya dauro towel sauran jikin shi da komfa...,saman gadon ya haye tare da riƙo ta"meke damun ki?",zan mutu mara na ciwo kamar zai fashe!",hanunta duka biyu riƙe kam a marar ta.

Innalillah wanan masifa dame yayi kama,da an fita wanan a shiga wanan?,ya Allah idan wani laifi na aika ka yafe ni!,yadda take ihu haɗe da nishi sama sama yasa ya ƙara fita hayyacin shi domin yana matuƙar son matar shi abubuwa ne suka zo masu wani iri.

Bai tsaya sauya mata kaya ba kawai ya ɗaura babban hijab saman kayan bacci dake jikinta,ya saka jallabiya tare da ɗaukar wallet da key mota tana rungume a jikin shi ya nufi hanyar fita....,kiciɓis suka yi da mami a palo"ina kaza kai ta daddy?",ɗauko hijab ɗin ki asibiti zamu bata da lafia,ba zan barki ke ɗaya a gidan ba dare ne.

Ban zuwa ko iya,itama ai babu abunda ya same ta , ka rasa yadda zaka yi da ita ne sai nayi maka maganin taa!,kawai ka kuma ciki zuwa da safe zata warke sumul.

dakata!"ya daka mata tsawa",na rantse da Allah idan wani abu ya faru da ita,zan manta da soyayyar da nake maki sai na dauka mummunar mataki a kanki tunda na lura ke hatsabibiyar yarinya ce!.

Ni ɗin daddy?
tsaki jaya tare da nufan hanyar fita domin cikin halin da zainab ke ciki baya tunanin ko hajiyar shi tazo zai iya ƙyale zee haka nan.
Sai daya saka zee a mota sanan ya rufe mami ta waje sanan yayiwa motar gear...,ydda ya rinƙa horn yasa mai gadi buɗe masa gate da wuri.

Ɗan leƙowa yayi,ka kula da mami ita ɗaya ce kada ka bari ta fita zamu asibiti da zainab ba lafiya.  In shaa ALLAH za a kula ALLAH bata lafiya.

Wani asibitin kuɗi dake kusa dasu ya nufa...,amsanta akayi kafin aka buɗe mata file a wurin.

Ma aikaciyar jinyar ta tambaye shi abunda ke damun taa?,faɗa mata yayi ta nufi ɗakin da aka aje taa,babban
likita ya bada dama ayi mata alurar ciwon mara da ƙarin ruwa,idan ta farfaɗo a duba ta da kyau.

Sai sintiri yake domin ya rasa natsuwar shi gashi bai fito da waya ba saboda sauri,ɗakin ya nufa tare da zama gefen gado yana ƙare mata kallo..,da alama bacci take yi a wahalce ƙarin ruwan na shigarta.

Cikin baccin take mafarki wai tana riƙe da jariri a hannu tsamo tsamo cikin jini,zaki na biye da ita cikin dokar jeji sai gudu take yi kamar ranta zai fita...,idan ta waiga saitaga yayi daf ta ita,ta ƙara kai mi har suka isa bakin tafkeken rami mai girma da faɗi babu wata hanya sai nan,idan ta kowa maya kuma zakin nan zai haɗiyeta!,gashi nan tsaye ƙikam ya buɗe baki sai miyau ke dalala!.

Ƙara

Please Login or Register in order to submit comment