Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma ya juyo,
Ryynt dake kallon sa tayi saurin sadda kanta qasa yazo gab da ita ya d'ago fuskarta yana kallon manyan idanuwanta da suka ciko da qwalla yace"mene ne ko kina zuwa muje?
Da sauri ta gyad'a masa kai, yaje ya d'auko mata hijab ya saka mata da kanshi yaja hannunta suka fita.

Kan hanya Ryynt sae kallon gurare take tayi da suka mugun bata sha'awa har suka isa wani makeken mall,
nn fa ta shiga ba ido haqqinsa don gurin ya had'u iya had'uwa kmr wata aljannar duniya yayinda man ke janye da ita yana musu siyayya ya tafi da ita gurin rigunan bacci ya ciro kusan kala biyar masu shegen kyau da baza su wuce iya cinya ba ita dae Ryynt sau d'aya ta kalli kayan ta kauda fuskarta dan jin tayi kmr ta nitse don kunya dan taga tsiraicin kayan sosai wacce duk a tunanin ta malika ya siyawa dan ita taga tana saka irin su.
Bayan sun dawo gida har anyi sllr magrib da isha'i Ryynt na kwance kan darduma lumshe da ido tana jin bacci mae dad'i na son fizgarta,
bata ji shigowar man ba sae qamshin turaren sa da taji gab da ita nn ta bud'e idanunta a hnkli ta ware su akanshi ya dafa goshinta tare da fad'in"jikin ne?
Tace"um um bacci nake ji"
Yace"to muje muci abinci sae ayi wanka koh?
Ba musu ta tashi suka je kan dining sae dae bata wani ci abincin sosai ba sbd baccin da ya mata yawa a ido ta ture plate d'in gabanta zata tashi man ya riqo ta yace"ba dae amae ba?
Kallon sa tayi snn tace"um um wanka zanyi nayi bacci"
Yace"indae wanka ne zan miki zauna ki qarasa cin abincin ki tukun"
Tace"um um ya ishe ni fa"
Yace"yi haquri dae ki qara ko kad'an ne kinji"
Ta girgiza kanta alamar a'a bae kula ta ba sae jawo plate d'inta da ta ture yayi zae ci gaba da ciyadda ita,cikin yanayin jin bacci d'auke da shagwa6a ta fashe mai da kuka,
da sauri ya ture plate d'in yace"yi haquri muje ayi wankan to"
Tace"um um nida kaina zanyi"
Yace"to tashi kije ki cire kayan jikin ki kafin na had'a maki ruwan wanka"
Nan ta tashi taje zuwa cire kaya shi kuma ya nufi bathroom ya had'a mata ruwan d'umi ya fito snn taje ta shiga.

Koda ta fito ta samu ya ajiye mata d'aya daga cikin rigunan baccin da taga ya siyo ai kuwa ta zaro ido tana kallon rigar snn tayi murmushin mamaki wae ita ya siyo ma kayan knn ashe kuwa zasu tabbata ba'a sa ba.
Nan ta wuce abinta ta bar rigar taje ta ciro turarukkan da umman saliha ta bata ta shafa.
Bayan ta gama shafa turarukkan ne ta bud'e wardrobe ta nemi kayan baccin ta sama da qasa bata gansu ba nn tasan cewa mohd ne ya d'auke su don kawae tasa waccan rigar da ya ajiye mata.
Rai 6ace cikin kukan shagwa6a taje tayi kwanciyar ta kan bed ta soma yin baccinta sanye da hijab da towel d'in da ta fito wanka dasu.

Mohd ya shigo yayi tsaye yana kallonta d'auke da murmushi snn ya kalli rigar baccin da ya ajiye mata da ta ture gefe.
Ya tafi kawae ya cire kayan jikin sa ya fad'a bathroom yayi wanka ya fito snn yaje yayi shirin bacci ya dawo gun Ryynt da har baccinta ya soma nisa ya jawota a hnkli zuwa jikinsa ya cire mata hijab nn yaji wani irin kamshin dad'i yana fita a jikin ta ya rungume ta had'e da lumshe ido yana shaqar qamshin ,
ba abinda ya fad'o masa a rai a lokacin sae daren rnr da suka zo yana mae tuna kaf abinda ya faru tsakanin sa da ita dan daren ya masa dad'i ba kad'an har baya jin zae iya manta shi a rayuwa.
A kasale ya d'ago ta zae cire mata towel ta farka firgigit had'e da riqe towel d'in gam ta kalle sa cike da shagwa6a tace"meye haka?
Yace"rigar bacci zan saka miki"
Ta ware manyan idanun ta tace"wace rigar?
Yace"wacce kika samu na ajiye miki kan bed"
Ta maqale kafad'ar ta cikin muryar shagwa6a tace"Allah ni bazan iya saka wnn abin kunyar ba,kawae ka bani kayan bacci na da ka d'auke min"
Mohd dake kallon yanayin shagwa6ar ta abin sha'awa yayi dariya yace"yi haquri ki saka kinji"
Tace"um um ban so"
Nan kawae yayi murmushi tare da kwantar da ita kan qirjinsa yana shafa bayanta yace"shike nn yi bacci tunda ba kya so".


Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮

🔮🔮🔮🔮
*```Page 71```*
Kasa d'agowa tayi daga kan qirjinsa ta lafe abinta tana shaqar kamshin turaren sa mae saka natsuwa daga nn fa bacci yayi awon gaba da ita.
Mohd sae kallonta yake har sae da ya tabbatar baccinta yayi nisa snn ya soma zare mata towel sannu a hnkli har ya zare sa gabad'aya ya d'auko rigar bacci zae saka mata yayi tsaye yana kallon albarkatattun qirjin ta dake matuqar bashi sha'awa kan cikar su da kuma yanda suke tsaye a jikin su.
A hnkli ya sauke idanun sa kan cikin ta da ya d'aura hannun sa akai yana shafawa yayinda yake fata a ransa Allah ya nuna masa abinda ke ciki ya fito lafiya.
Daga haka ne ya saka mata rigar bacci ya kwantar da ita d'auke da murmushi a fuskar yana mae kallon yanda rigar baccin tayi d'as a jikinta ta kuma yi mata kyau sosai.
yasa blanket ya rufa mata jikinta snn ya d'auke hijab da towel yaje ya kaisu inda ya dace ya dawo ya kwanta tare da kashe musu wutar d'akin.

Washe gari ya fito daga bathroom Ryynt dake zaune kan bed ta had'e kai da guiwa ta d'ago fuskarta tana kallon sa cikin fushi.
Murmushi yayi dan yasan laifinsa ya qarasa gurinta tare da janyo ta zuwa jikin sa yana fad'in "yi haquri ba kya son riga na saka miki ko"
A shagwa6e ta ture sa daga jikinta tana kallon sa idonta tap da qwallah le6ace da baki kmr er qaramar yarinya zata yi kuka.
Hakan ba qaramin birge sa yayi ba don sosai yake son shagwa6a a rayuwar sa.
Shiyasa duk ya sukui sukui ce ya soma lallashinta har ta fasa kukunda tayi niyya.
Yakai hannu zai yaye blanket d'inda ta rufe jikinta dashi har wuya,tayi saurin kama blanket d'in ta rirriqe had'e da dalla masa harara dan rigar komai nata ana gani,
da murmushi ya saki blanket d'in yace"to ni zanje masallaci kema ki tashi kije kiyi arwala kiyi sallah kinji"
Daga nn bai jira me zata ce ba ya fita dn sauri yake ko zae sami jam'i ,
koda ya dawo tana zaune kan darduma ta idar da sallah tana addu'a yaje ya zauna kusa da ita suka tofa addu'ar a tare ,
ta tashi zata bar gurin ya jawota ya zaunar tare da fad'in"zauna muyi magana"
Cikin fushi ta fizge hannunta ta miqe ya sake janyota ya zaunar yana mae kallon fuskar ta yace" hln dae kin manta mgnr da na gaya miki a rnr, ta kalle sa tana son tuna wace magana ce yace"ina wnn mgnr da na gaya miki a kunne gidan innaa,
kin tuna"
maqale kafad'a tayi tana kallon sa tace"ai nasan ma baza ka min ba ka fad'a ne kawae"
Yace"waya gaya miki kawae dae ki daina musa min kiga ni kuwa zan maki abinda nace"
Tace"ba wani nn wayo kake min nasani amma shi yaya nasir nasan da gaske zae yi min"
Kallon ta yayi dan tabbas wayo yake mata d'in don ko giyar wake yasha ba zae zubar mata da ciki ba, ya fad'a ne kawae don ya sami natsuwar ta a rnr,don a rnr bayan kalaman rarrashi da ya gaya mata ce mata yayi duk ta daina musa mae akan komai shi kuwa yayi alqawarin da kanshi zae zubar mata da ciki tunda bata so kuma ba zae sake takura ta akan komai ba.
Kuma ko nasir yasan wayo kawae yake yi mata,amma kuma wata qil da gske yake mata tun da duk haushin sa suke ji a lokacin sae yanzu ne da komai ya dawo normal.
Ya kalle ta yace"meyasa kike tunanin da gaske Nasir yakeyi?
Tace"shifa har asibiti muka je akace cikin bai isa zubàrwa ba sae ya qara watanni amma kai tun daga rnr ko mgnr ma baka sake yi min ba"
Ta qarashe mgnr had'e da turo baki tana kallon sa shaye da toka shi kuwa ya fashe da dariya don ya fhmci duk dae wayon ne ake yi mata,
yace"inafa zan miki zancen Ryynt hnkli a tashe amma kinga yanzu Alhmdlh sae ki daina musa min akan komai ni kuma sae na miki abinda kike so sae ma ki samu kiyi karatun ki cikin natsuwa dan nasan shine abinda yafi damunki ko"
Ta gyad'a masa kai kawae tana kallon shi don har yanzu bata yarda da gske yake ba.
Shima dae ya fhmci haka yace"in tambayeki Ryynt wae meyasa kike son 6arar min da cikin nn ne dan Allah,shin baki san irin sonda nake masa bane"
Tace"shi cikin da aka samu ta dalilin abinda ka kira a qaddara"
Kallon ta yayi jiki sanyaye cikin rashin jin dad'in mgnr duk da dae yasan cewa laifin sa ne yace"wace irin magana ce wnn Ryynt,shin idan kin 6arar da cikin nn ba kya gudun had'uwa da fushin ubangiji ko kin manta cewa rayuwa ce zaki hallaka ko rayuwa kuwa ta d'an adam wanda bai ji ba bai gani ba,i beg u idan akan wnn maganar da na gaya miki ne kike son 6arar da cikin nn dan girman Allah kiyi haquri kar ki zubar min dashi wlh ina son sa,
Ya qarasa mgnr ne kmr zae yi kuka dan har idon sa sun canza launi.
Itama kmr zatayi kuka ta kalle sa tace"to ai cikin ne ba zae bar ni nayi karatu ba gashi har ya fara min girma idan ban 6arar ba ya kake so na koma school to"
A hnlkli ya riqo kumatun ta yace"um um Ryynt in dae karatu ne zan san dabarar da zan miki idan kin haifu sae kici gaba ba ma sae kin koma secondary school ba high school kawae zaki d'aura"
Tace"kamar ya?
yace"jarrabawa zakiyi waec n neco ba sae kinyi ss2 n 3 ba"
Girgiza kanta tayi tace"wane irin abu ne hk ko Ss one d'in ma ban kammala ba fa kasani"
Sae da ya share mata en silallan qwallar da suka xubo mata snn yace"na sani Ryynt amma kinada basira sosai ta yanda inshaa Allah zaki iya yin hk d'in bata tare da an sami wata matsala a karatun naki ba,kawae kice kin yarda dan Allah i beg u"
Shiru kawae tayi tana kallon sa kmr yanda shima yake kallon ta dmn jin me zata ce.
Murya can ciki mae d'auke da jin kuka sosai tace"to naji amma kuma ai kasan nayi qanqanta da haifuwa wata qil ma mutuwa kawai zanyi"
Tana kaiwa nn ta fashe mishi da kuka yayi saurin rungumota yanaji kmr ya taya ta kukan dan haka kawae yaji ta bashi tausayi dan tayi qanqanta d'in kmr yanda ta fad'a"
Rarrashin ta ya shiga yi sosai yana fad'in ta kwantar da hankalin ta inshaa Allah lafiya lau zata haifu ba abinda zae sameta nn ya samu har ta daina kukan yayinda still yake rungume da ita quite 4 a while some time kmr ba kowa a cikin d'akin sae can mohd ya d'ago fuskar ta yana kallon manyan idanuwan ta dake d'auke da jin bacci yace"bacci" ta gyad'a masa kai ya tashi rungume da ita a jikin sa suka je kan bed ta kwanta nn wayar sa dake kan bedside drawer ta shiga ring,
malika ce mae kiran bae d'aga wayar ba sae da ya fita dan baya son yayi disturb in Ryynt.

Bai wani jima sosai d'in nn ba ya dawo ya samu har Ryynt tayi baccinta.

Yayi zaune gefen gado ya jawo stool ya d'aura laptop akai yana wani aiki wanda har yayi nisa da aikin ne wayar sa ta shiga ring still dae malika ce,
sae da yayi tsaki kafin yake d'aga wayar cikin fad'a yace"wae malika sau nawa zance miki Aa nace ba sae kin zo ba kawai kibi ummanki ku koma ai nima ina nn dawowa,oho koma yaushe ne dae"
Yana gama fad'ar haka ya katse kiran yaci gaba da aikin sa.
Har guraren qarfe goma snn ya rufe laptop d'insa ya tashi ya nufi bathroom yayi wanka ya fito.
Bayan ya gama shiri ne yayi tsaye akan Ryynt dake ta faman juyi ya hau kan gadon a hnkli ya janyo ta zuwa jikin sa yace"Ryynt mene ne?
Da qyar tana yarfi da hannu tace"cikina"
Kai tsaye yakai hannu ya cire mata hijab ya kuma kwance zanin da ta d'aura kan rigar baccinta ya yaye rigar yana duba cikin yace"nuna min daga ina yake maki ciwo"
Murya can ciki mae d'auke da son yi kuka tace"mird'a min yake yi gabad'aya"
A hnkli ya maida ta ya kwantar yaje ya tsiyayo fresh milk a cup yazo da magani ya tashe ta ya bata sae yi yake yana shafa cikin yayinda take rungume a jikin sa idanun ta a rufe kmr mai yin bacci man sae kallon goshin ta yake da yayi zufa zufa duk irin sanyin Ac da ke cikin d'akin kuwa nn ya ciro handkerchief ya share mata zufar ta bud'e idanun ta a hnkli tana kallon sa shima kallonta yake yayinda yakai hannu kan santala santalan cinyoyinta yana shafawa da sauri ta kai idonta akai snn tayi saurin janyo hijab ta rufe cinyoyin ta tafi dashi har izuwa qirjinta duk ta rufe don sae lokacin ta tuna cewa ya cire mata hijab da zani kuma sam ta manta yanayin rigar da ke jikinta.
Kallon ta kawae mohd yayi bae ce komai ba sae hannun sa yakai ya d'ago fuskarta yana kallonta yace"cikin ya daina maki ciwo?
Kai ta gyad'a masa ta saka hijab zata miqe tsaye yace"ina zuwa?
Tace"wanka zanyi"
Yace"to muje na tayaki wankan ko"
Ta maqale kafad'a had'e da fad'in"ni kunya nake ji kawae kayi zamanka"
Yace"Aa sae dae ki za6i d'aya da na tayaki wanka da na shirya miki idan kin fito wanne kike so"
Tace"bari idan na fito ka shirya min"
Ta fad'i hkne kawae don ta samu ta tafi kafin aman da takeji ya kufce mata.
Shi kuwa har ransa yaji dad'in ganin ta d'an fara sakewa dashi yace"shike nn jeki"
Nan ta nufi bathroom wacce koda ta fito bata same shi a d'akin ba sae gado da ta samu an gyare tsaf.
Dad'i taji har ranta ganin baya d'akin don ita ko shiri bata iya yi a gabansa bare zancen yace shi zae shirya mata nn ta nufi wardrobe da hanzarin ta dmn ta samu ta shirya kafin ya dawo sae dae koda ta bud'e wardrobe duk ya cire kayan da tazo dasu ya saka mata wasu qananin kaya kala kala,kafin ta iya komai sae jin mutum tayi a bayanta ya rungume ta a hnkli tare da fad'in "ya kika ga kayan suna da kyau?
Komai bata iya ce masa ba sae hannu yakai ya zaro kala d'aya daga cikin kayan yaja hannun ta yakai kayan kan bed ya ajiye ita kuma ya tafi da ita gun dressing mirror ya zaunar wacce tana ji tana gani ya cire mata hijab ya fara shafa mata mae bata iya hanashi ba don ko magana ma da taje zuwa yi hanata yayi kawae dae ya rage hasken d'akin zuwa dim light.
Tsaf ya shafa mata mae kmr wata er baby don ko towel d'in jikinta bae bar ta dashi ba ya kuma shafa mata duk wasu turarukkan sa da yake amfani dasu yayinda kanta ke qasa cike da jin kunya ta kasa hana shi komai har ya d'auke ta ya tafi da ita kan bed ya saka mata tufafin da ya d'auko wato riga da wandon da sukayi matuqar kyau a jikinta ita kanta ta yaba da kayan sbd kayan basu da tsirai ci ko kad'an dmn kayan irin na Indiyawa ne er duguwar riga mai guntun hannu da aka d'an matse body d'in rigar se tunda daga kan qugu aka baje ta har zuwa guiwa yayinda wandon ya kasance skin tight.
Mohd sae kallon Ryynt yake tayi wacce har yanzu ta kasa d'ago ido ta kalle sa duk da ba wani haske ne a d'akin ba.
Ya kira sunan ta a natse had'e da d'ago fuskarta suka kalli juna ta cikin ido nn man ya qara jin wata irin kasala ta saukar mae wacce tun lokacinda yake shafa mata mae ya soma jinta ,
a hnkli ya matso fuskar sa gab da tata ya d'aura tsinin hancin sa akan nata Ryynt da ta fahimci abinda yake son yi ta kauda fuskarta gefe ,
bae ce komai ba sae hannunta yaja suka je kan dining,sae dae Ryynt ta kasa cin komai sbd zuciyar ta dake fmn tashi hkn yasa shima mohd ya kasa cin komai sae kwantar da ita yayi kan qirjin sa ya shiga shafa bayanta yana tambayar mene ne,
Shiru kawae Ryynt tayi don ba abinda take jin so irin agwalima wacce tasan da kmr wuya samunta a nn,
Mohd dake shafa bayanta a natse yace"gaya min me kike so kinji"
Ta d'ago fuskarta kmr zata yi kuka tace"agwalima nake so kuma nasan a nn babu ko?
Cikin damuwa yace"No Ryynt da kmr wuya amma kina son fruits?
Da sauri ta gyad'a masa kai yace"to muci abinci sae muje a siyo ko"
Tace"um um kawae kai kaci sae muje"
Ya girgiza kansa yace"um um kema kici ko kad'an ne kinji i beg u"
Ya fad'i hkne yana mae kallonta cikin nuna damuwar son taci abincin.
Hakan yasa ta kasa musa mae duk da tana ji kmr idan taci zatayi amai amma hkn ta dake ya fara bata abincin tana ci sae Allah Allah take kar amai yazo mata yayinda take ta kallon shi bae ci abincin ba sae bata da yake,
Mohd ya kalleta ganin ya d'ebo abinci a spoon yakai bakinta taqi bud'e baki taci sae kar6ar spoon d'in tayi ta kai bakin shi ,
da kmr mamaki ya bud'e bakinsa a hnkli ta sakà mishi yana mai kallonta cike da jin dad'i a ransa.
Inda cikin ikon Allah Ryynt kuwa taci gaba da ciyadda dashi yana ciyadda ita har suka kammala cin abincin.
Man dake ta kallon Ryynt cikin so da jin dad'i ya zaro tissue ya goge mata d'an qaramin bakinta snn yaja hannunta d'auke da murmushi a fuskar sà ya tafi da ita gun wardrobe d'in ta ya ciro black after dress da ya siyo mata tsadadda mai kyau ya saka mata snn ya ja hannunta suka fita.

Billy giro😊

🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮
🔮🔮🔮🔮
*```Page 72```*
Sun d'an jima kafin suke dawowa dan sae da suka d'an zaga gari kmr yanda Ryynt ta buqata.
Koda suka shigo mohd ne riqe da wata babbar leda da aka ciko tap da 'ya'yan fruits kala kala har wad'an da ma bata saba gani ba.
Haka ma Ryynt na riqe da wata leda mae d'auke da ice cream taje ta saka a fridge shi kuwa mohd kitchen ya tafi da ledar fruits d'inda ke hannun sa,bai jima sosai ba ya dawo d'auke da fruits d'inda ya gyara a cikin fruit bowl yazo yaja hannun Ryynt da ta cire after dress ta mayar a wardrobe yaje da ita kan sofa ya zaunar ya kunna musu TV suna kallo yana bata fruits a baki tana ci kmr wata er baby kan yanda ya rungume abar sa a gefen qirjinsa sa ita dae Ryynt ta zamo speechless sae kallon sa kawae take don abubuwan nasa har mamaki suke bata don komai sae yace baza tayi da kanta ba sae shi ze yi mata wacce ko ledar ice cream da ta shigo riqe da ita sae da tayi da gaske snn ya barta ta riqo ledar.
Haka yaci gaba da bata fruits in sae da tace ya isheta snn ya cinye sauran.

2 dayz later
Ryynt ce zaune kan kan bed sae waya take da mutan gida wato su inna da su umman saliha,saliha, mami har ma da qawar ta Sarah. Wacce tana gama wayar ne sae ga mohd ya shigo d'akin nn take ce masa tana son zata je 6angaren su mtr Amir bai musa mata ba ya jata suka tafi 6angaren suka sami Amir zaune a falo shida d'an shi saddiq da mtr sa suna kallo abinsu.
Cikin sakin fuska suka gaisa da juna mtr Amir taja Ryynt suka je daga ciki ,
a nn man ya kalli Amir yace"shin wae kai ka dawo ke nn ko kuwa?
Sae da Amir ya nisa snn yace"Aa nifa ajiye aikin ma nake ganin zanyi na koma Nigeria na gaji da zama qasar wasu ina masu aiki bayan qasata na buqata"
Mohd yace"au ka fara kishin qasar taku knn"
Amir yace"ka jika idan banyi kishin qasar mu ba tawa zanyi kawae dae wlh kmr kar mu jima gida karon nn naji ina sha'wan ci gaba da zama cikin en uwa haka my wife da taji zamu dawo har kuka sae da tamin ita gida bae isheta ba ,
sae da na mata bayani snn hankalinta ya kwanta.
Mohd yace"knn itama tana son komarwa ka aiki Nigeria?
Eh to tana so amma ba don komai ba sae don ganin Khadija na gida ynx sae duk taji nn d'in ya fita ranta,mohd yace"ni kuwa Amir har kaima d'in baka da labarin inda Aamil yaje wae?
Amir yace"inafa zan sani man kuma abin tausayi ya tafi ya bar Khadija da sabon ciki mae matuqar bata wahala da komai bata iya yi sae an mata bayan baqin cikin da ya tafi ya bar ta dashi"
Mohd ya nisa kawae ba tare da ya iya cewa komai ba sae wayar sa da ke ring a cikin aljihu ya ciro ya d'aga.

Ryynt kuwa da mtr Amir ta jata zuwa ciki sosai ta sake da Ryynt don sae jan ta take da fira hkn yasa Ryynt ta sake itama sae fira suke abinsu bayan kayan motsa baki da ta jerawa Ryynt a gabanta.

9:00pm
Tuni suka dawo 6angaren su har sunci abinci suna zaune a falo suna shan ice cream yayinda Ryynt ice cream d'inta har ya soma narkewa kan yanda take faman danne danne a wayarta d'auke da er damuwa a fuskarta ta d'ago ta kalli man dake kallon labarai a TV amma duk wani motsi nata yana kule dashi shiyasa da ta kalle sa ya sauko kan doguwar kujerar da yake zaune dan ita zaune take a qasa ta jingina bayanta a jikin doguwar kujerar.
Bayan ya zauna kusa da ita ne yace"ya akayi ne Ryynt?
Ryynt dake kallon sa tace"so nake dan Allah ka bud'e min whatsApp Saliha ke son mu riqa chat "
Ba musu ya kar6i wayar ta ya tura mata watsApp a wayar shi ya kuma saita mata har yana nuna mata yanda ake chat d'in dan ya fhmci she is innocent.
Cikin jin dad'i ta masa godiya sae dae koda ta duba Saliha bata online bata hau ba sae wata numba taga ta turo mata text ta kalli

Please Login or Register in order to submit comment