Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saki tare da ajiye bowl d'in agwalimar ta a qasa taje da gudu ta fad'a jikin saliha suka rungume juna suna masu murnar ganin juna ,
Ryynt ta d'ago cike da mamaki tana kallon saliha don bata ji a bakin kowa cewa sun dawo ba.
Tace"yaushe kuka dawo ne saliha?
Saliha tace"yau muka dawo inna bata snr dake ba, dan har kiranta nayi nace ina nn shigowa"
Ryynt ta girgiza kanta tace"um um inaga ta manta,ya baki zo min da mami ba?
Wlh mami fita sukayi ita da Ameera.
Ryynt tace"ya umma to"
Saliha tace"umma tana qalau ta ma ce a gaida ke"
Ta fad'i hkne yayinda suka shiga d'akin inna wacce tana ganin saliha ta washe baki tana mata oyoyo,inda cikin sakin fuska sosai
saliha ta shiga gaidata.

Sun d'an jima a d'akin kafin suke fitowa suka je d'akin Ryynt sukayi zaune sae firar bayan rabuwa suke yayinda saliha keta kallon Ryynt da taga ta canza mata ftr ta tayi haske da laushi had'e da er qibar da ta qara mata kyau.
Haka ma sae kallon d'akin take ganin komai na Ryynt a cikin d'akin don bata san cewa Ryynt ta dawo gidan inna ba duk a tunanin ta yini taxo yi.
Bata dae ce komai ba suka ci gaba da firar su suna shan agwalima .
Suna cikin hkne suka jiyo sallamar mohd saliha ta amsa sallamar had'e da gaida shi snn ta fita ta basu guri.
Mohd ya qarasa daga cikin d'akin ya zauna kan bed yana mai kallon Rynt.

Billy Giro 😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮

_Inaga gaskiya kuyi haquri naci gaba da muku posting d'in daren nn sbd gsky da rana banida enuf time d'inda zan kammala typing har na samu na muku posting,dan haka daga yau inshaa Allah zamu koma er gidan jiya_

🔮🔮🔮🔮
*```Page 67```*
Wacce ta kauda fuskarta gefe sbd qamshin turaren sa.
Mohd yakai hannu ya juyo fuskarta ,
ta watsa masa manyan idanuwan ta a cikin nashi cikin yanayi na alamar mene ne?
Yace"Ina son zamuyi magana ne"
Ta maida fuskar ta gefe tace"inajinka"
Yace"ba wata magana bace magana d'aya ce wacce kika sani wato zancen komawar ki gidana"
Ta girgiza kanta a natse ba tare da kalle sa ba tace"Aa ni bazan koma ba"
Yace"yi haquri dae kinji"
Tace"kawae kayi haquri kaima"
Yace"ni bazan iya bane"
Tace"amma kake tunanin ni zan iya"
Tayi mgnr ne yayinda ta kalle sa snn ta kauda kai.
Yace"meyasa baza ki iya haqura ba"
Tace"sbd rayuwar gidanka rayuwa ce da bazan iya taba"
Mohd yace"wnn rayuwar da kike tunani ae a dane amma ynz sabuwar rayuwa ce zamu gina nida ke"
Tace"Aa ni nafi son rayuwata a nn sbd nafi samun kwanciyar hankali"
Mohd yace"can ma d'in zaki sami kwanciyar hnkli fiye da tunanin ki"
Tace"fiye da tunani na zan sha duka na sani amma dai ba kwanciyar hnkli ba kam"
No Ryynt ki ajiye duka gefe dmn nayi miki alqawarin bazan ta6a sake kai hannu na a jikin da niyyar sake dukanki ba.
Tace" ta yaya bayan idan ranka ya 6aci baka da wani hukunci sae duka ,
rayuwar zo mu zauna kuwa bawai kullum cikin farin ciki ake zaune ba dole yau da gobe sae an sami sa6ani kuma ta yaya kake tunanin zan koma gidanka byn idan aka gaya ma magana yarda kake har ka d'auki hukunci ba tare da kayi bincike akai ba.
Numfashi ya fitar d'auke da alamar damuwa yace"Ryynt abinda ya faru ya riga da ya faru ina son dan Allah ki manta shi ki d'auka cewa yanzu wata sabuwar rayuwa ce zakiyi mai dad'in gaske da ba wani qunci ko tashin hnkli a cikinta"
Ryynt ta girgiza kanta a natse tace"ko d'aya bazan ta6a hangen abinda bashi bane"
Mohd yace"plz Ryynt ki fhmce ni.......
Ryynt da duk qamshin turaren sa ya soma fizgarta na son taji kanta a jikin sa tana mae shaqar qamshin ,
ta miqe tsaye da sauri tace"Dan Allah ka fita na gaya maka baxan koma ba wlh"
Cikin yanayi na alamar zai rarrasheta yaje zuwa riqo hannunta,taja baya da sauri had'e da fad'in "kar ka ta6ani bana so kuma dan Allah ka fita"
Mohd yace"yi haquri ki saurareni"
Tace"wlh indae akan komawa gidanka ne bazan ta6a saurararka ba don haka kawai ka fita"
Cikin mugun damuwa kmr zai yi kuka ya jawota da sauri zuwa jikin sa yace"haba Ryynt wae ta yaya kike tunanin zan iya rayuwa ne ba ke"
Ryynt dake yunqurin qwatar kanta tace"kan me wae ni to tunda dama can bada ni kake rayuwa ba"
Idanuwansa ya d'aura a cikin nata cikin muyar natsuwa yace"sbd ina sonki Ryynt"
Wani irin kallo ta mae snn ta girgiza kanta le6ace da baki tace"ni kuwa meye abin so a tare dani,nida sae wanda uwar sa ta mae baki ko zai soni"
Kallon ta yayi a sanyaye dan ya fhmci inda ta dosa yace"pls Ryynt ki daina zancen da ya riga ya wuce dan Allah"
Ta fizge kanta daga jikin sa rae 6ace tace"Dan Allah ka fita to"
Numfashi ya fitar cikin yanayin damuwa yana kallonta d'auke da idanuwansa da duk ya shiga damuwa sae sunyi jajur sun canza kala.
Bata tare da yace komai ba ya juya ya fita daga d'akin.
Ya wuce Saliha dake zaune a falo tana kallo,wacce ta bisa da kallo har ya fita sbd yanayin damuwar da ta gani a tare da shi.
Nan ta tashi ta nufi d'akin Ryynt wacce ta sama rae 6ace.
Taja hannunta suka zauna kan bed snn tace"Me yake faruwa ne Ryynt ko gida yake so ku koma baki tashi bane"
Ryynt ta kalle ta kawae dan ta fhmci bata san komai ba.
Saliha tace"kinga idan a kaina ne kawae ki koma gida gobe zanje can sae ma naje miki da mami ko"
Ryynt ta qirqiro d'an guntun murmushi tace"saliha knn nifa a nn nake zama yanzu rabona da wancan gidan har na manta"
Cikin mamaki saliha tace"kmr ya ban gane ba?
Ryynt tace"uhm kedai mu bar zancen muci gaba da firar mu kawai"
Saliha ta girgiza kanta tace"ina fa zancen fira kin d'auko min wata magana da najita banbarakwai me ya faru da kika dawo gidan inna da zama ko kin kusa haifuwa ne?
Da sauri Ryynt tace" haifuwa?
Saliha tace"eh mana ba kmr ciki na gani a jikin ki ba yanzun da na shigo.
Ryynt da ko kad'an bata ta6a kawo cikin yayi girman da za'a gane ba ta kalli saliha kmr zata yi kuka tace"wae ana ganin cikin?
Saliha tace"eh nima sae yanzu na fahimta da na shigo"
Kuka Ryynt ta fashe dashi saliha tace"kan me to tunda ba shege bane"
Ryynt bata ce komai ba sae kukanta take don ba abinda take tunani irin qila ma a school kowa ya gane tana d'auke da ciki byn ko da kuskure bata ta6a yarda ta nuna cewa mtr aure bace sbd bata so a sani.
Saliha dake kallonta za tayi magana knn wayar Ryynt ta shiga ruri saliha ce ta d'auko mata wayar kan bedside drawer ta bata wacce kafin ta kar6a sae da ta tsagaita kukanta ta kalli mae kiran wato umman saliha snn ta d'aga had'e da kara wayar a kunnen ta.
Tace"Na'am mama,eh ina ji"
Daga haka se tayi shiru lokaci mai tsawo tana sauraren umman saliha dake ta bata magana cikin rarrashi kan tayi haquri ta koma gidan mohd,wanda da fitar sa bai zarce koina ba sae gurinta dan yasan Ryynt zata ji maganar ta.
Ryynt sae sauraren umman saliha take cike da qwalla tap a idonta don ko kad'an bata son komawa gidan mohd amma ba yanda ta iya dole ta amince akan zata koma d'in sbd ta d'auki umman saliha tamkar uwa da bazata iya musa mata ba.
Tana gama wayar ne da en mintina sae ga kuma nasir ya sallamo da shima Man ne ya turo shi akan yaxo dan Allah ya qara bawa Ryynt haquri.
wanda duk da cewa yasan irin zamanda Ryynt tayi a gidan man yana son ta koma dmn ya fhmci irin nadamar da man yayi,kuma ko don qaruwar da suka samu a tsakanin su yana son ta koma.
Bayan sun amsa masa sallama ne ya shigo yasa Ryynt gaba yana rarrashi da ban haquri had'e da fhhmtr da ita ta kwantar da hnklinta inshaa Allah wnn karon zata ji dad'in zama ba kmr wancan karon ba.
Ita dae saliha sae sauraren su take har nasir ya gama rarrashin da yake ya fita ita kuma ta d'aura da nata dmn a iya abinda ta fhmta sa6ani Ryynt ta samu da man,wacce ta fhmci hkne tun daga kan wayar da taji tana yi da ummarta da kuma haqurin da nasir yazo yana qara bata.

Ita dae Ryynt gabad'aya jikin ta yayi sanyi dan ganin take shike nn rayuwar ta zata koma cikin qunci da rashin walwala.

Da dare guraren qarfe tara mohd ne ya shigo gidan ya sami inna a falo tana kallo ,ya gaida ta ta amsa ba yabo ba fallasa ya zauna jim kad'an snn yace"Ryynt fa?
Inna tace"tana ciki na rasa meke damunta kmr wata marar lfy nake ganin ta yau"
Man yayi shiru kawai don yasan ba wani abu bane ke damunta sae rashin son komawarta gidan shi.
Yace da inna "bari naje na ganta to"
Tace"to"
snn ya tashi ya tafi d'akin Ryynt ya sameta kwance tana bacci yaje gab da ita ya duqa a hnkli yana kallon fuskarta da ke mai mugun kyau idan tana bacci.
Ya jima a haka kafin yake maida dubàn sa kan jikinta da komai ya cicciko 6ul 6ul ya qara kyau da haske a nn idonsa yakai kan qirjinta da ya taso saman rgrta sbd yanda rgr ta d'an kama ta,
kai tsaye ya kauda idon sa a gun ya maida duban sa kan cikinta had'e da d'aura hannunsa akai ya shafa d'an cikinta da ya taso snn ya kai hannu zuwa yaye rgr jikinta dmn yaga cikin.
Se Ryynt ta shiga juyi a hnkli had'e da gyara kwanciyarta ta juya mishi baya.
Nan ya miqe tsaye ya kalle ta kawae snn ya juya ya bar d'akin yayinda Ryynt ta bisa da ido dan dama ba bacci take ba jin zai shigo yasa ta qirqiro baccin qarya.

Shi kuwa mohd a nn falo ya sami inna naci gaba da kallonta ya zauna yayinda inna ta kalle sa tace"ya akayi jikin ne ko kuwa?
Yace"Aa inna inaga bacci ne kawai don naji jikin nata ba zafi sae vacci da na samu tana yi"
Inna tace"inaga fa hkne sbd yau duk bata samu tayi baccin da ta saba yi ba sae fira da suka zauna ma yi ita da saliha wacce sae da yamma sosai ta bar gidan nn,
Mohd bai ce komai ba sae cewa yayi"to inna yaushe za'a bani Ryynt mu koma tunda dae ta amince zata koma.
Inna tayi shiru don tun d'azu da yamma yazo da kanshi ya snr da ita cewa Ryynt ta amince zata koma gidan sa har taji dad'i a ranta don ynx sae taji tana son Ryynt ta koma sbd ko kad'an bata son idan sunje qauyen su Ryynt mai gari yaji cewa har auren Ryynt ya mutu shiyasa ta qara jawa mohd kunne sosai kan ya riqe Ryynt amana kmr yanda Abba ya masa da yaje ya snr dashi.
Inna tace"muhammadu ai kasan ko zata koma sae munje qauyen su tukun don tun ba yau ba kabiru ke jiran idan Ryynt sunyi hutu se muje"
Mohd yace"inna idan qauyen nasu ba wani nisa me zae hana gobe muje don Allàh dmn so nake jibi mu fara shiryen shiryen tafiyar mu nida Ryynt.
Inna da dama tasan da zancen tafiyar sbd d'azun da yazo ya snr da ita ,
tace"to ai sae kaje ka snr da kabiru duk abinda yace kaga sae kazo ka snr dani.
Mohd yace"to"snn ya tashi ya fita.

Yaje ya sami Abba ya snr dashi buqatar sa Abba bae musa mae ba ya amince ya dawo ya snr da inna, inna tace"to Allah kaimu goben"
Yace"Amin snn ya fita"kafin yake yi mata sallama.

Koda ya fito gate ya had'u da Amir ya faka motar sa knn ,
nn ya jira Amir d'in har ya fito suka gaisa .
Bayan sun gama gaisawa ne Amir ke cewa"yaushe ne zakuyi tafiyar kaida Ryynt dan nima kwanakin nn so nake nayi tafiya zuwa wajen nn"
Mohd yace"eh to idan na samu gsky ending of dis week nake son muje sbd nafi soñ nasha amarci na da Ryynt a waje"
Amir yayi er dariya yace"ai fa ,hln wacce qasa zakuje ne to?
Wlh abinda ya kawo ni knn jin ra'ayin qasar da take so muje so sae nazo na samu tana bacci wacce ko ba bacci take ba nsn baza ma ta gaya min ba.
Amir yace"kawai to kuzo muje India a Mumbai city"
Mohd yace"uhm kaji ka sbd kaima can kayi d'in ba"
Amir yayi murmushi yace"eh kam shiyasa nake neman abokan tafiya sbd tafiyar zata fi dad'i"
Mohd yace"haka ne gsky amma da germany naso muje sbd wasu kayan yara da na gani ina son siyowa a can but zamu fara zuwa India d'in dae daga baya sae muje Germany.
Amir yace"olryt what about gyaran gidanka da naji kace kana so zaka yi"
Eh yana nn har ma na yiwa nasir magana bcs so nake koda zamu dawo ya kasance an kammala canza komai na gidan sbd Ryynt nake son yiwa surprise.
Amir yace"that's gud to ai indai Nasir ne ai kasan zai sa a maka komai kan time"
Mohd yace"hakane ne gaskiya that's y na bashi kula da aikin ai "
Yana gama fad'ar haka ya d'aura da cewa"ni zan tafi akwai wani aiki da nake son yi ne yanzu"
Daga haka sukayi sallama ya fice shi kuma Amir ya shiga daga ciki.

Washe gari guraren 11am suka kama hanyar zuwa qauyen su Ryynt ,Abba inna,Nasir ,Amir,mohd,Ryynt saliha ,mami har umman saliha duk suna cikin masu tafiyar shiyasa suka cika kusan mota biyu ,yayinda motar mohd ke d'auke da mohd dake jan motar se Amir ,inna da kuma Ryynt, motar Nasir kuwa shida Abba ne a gaba ,umman saliha, Saliha da kuma mami sune a baya.

Da suka isa qauyen cikin mutunci da karamci mai gari ya tarbe su cikin nuna matuqar farin ciki da zuwan su inda mai gari da kanshi ya shiga dasu gidan shi nn cikin wani babban falo na saukar baqi da aka qawata sosai da kuma hadaddiyar liyafar da aka shirya musu wa su kad'ai dan dama yasan da zuwan su, wanda kafin su fara sa albarka a liyafar sae da matan mai gari har 'ya'yan shi suka zo suka gaida su had'e da yi musu ya hanya yayinda kowanen su ya saki fuska yana mai fad'in "Alhmdlh"
ya muka same ku?
suka ce "lfy lau"

Bayan sun sa albarka a liyafar da aka kawo musu ne en tsaran Ryynt dake nn qauyen sae zowa suke suna ganin Ryynt wacce ta saki fuska sosai suna maraba da ganin juna a nn ne wata er maqotan su Ryynt wato a lokacinda sukayi zama cikin gari taja Ryynt sae yawata wa suke a qauyen tare da saliha da kuma mami da suke janye da ita yayinda man ke can duk ya matsu yaga dawowar su haka kawai dashi kansa bai san dalilin matsuwar tasa ba.

Sun jima sosai a qauyen don sae yamma suka kamo hanyar dawowa wanda kafin su baro qauyen sae da sukayi wa mai gari d'inbin alhairi dashi har mutanen qauyen sa wanda hakan ba qaramin dad'i ya masa ba don sae godiya yayi ta musu ya kuma tara duk mutanen qauyen akan suyi musu godiya kan alhairin da suka musu.

Haka ma a gurin Ryynt sosai taji dad'in alhairin da aka yiwa mai gari da mutanen qauyen su amma kuma cikin mota sae kuka take ta son tayi sbd baffanta da ta tuna wacce gurin yawon su da suka je har inda aka kad'e Baffanta sae da taje da kuma dajin da sukayi zama ita da baffanta ,
ga mamakinta bukkar su na nn daram ba a rushe ba shiyasa komai ya dawo mata sabo wacce a lokacin har sae da tayi er qwalla kan ganin bukkar dan ta d'auka koda zasu ga bukkar duk gara ta cinye sae ta samu abokin mahaifinta ne a ciki da shine ke kula da gonar sarki yanxu.

Mohd tuqi yake amma gabad'aya ya rasa natsuwar sa dan ta jikin mirror yana kule da irin yanayin da Ryynt take ciki amma haka ya dake har suka dawo garin kano Nasir dake tare dasu Abba shi ya sauka a family house mohd kuwa kai tsaye gidan inna ya nufa.

Wanda yana faka motar suka fito suka d'unguma gabad'ayan su cikin gidan inna yayinda mohd yabi Ryynt kai tsaye zuwa d'akinta wacce sam bata san cewa yana biye da ita ba don da shigarta d'aki kukan da ta matsu tayi shi ta fashe dashi zata fad'a kan bed mohd ya jawota ya rungume qam a qirjinsa had'e da kai bakin sa saitin kunnen ta yana rarrashin ta ba tare da yasan dalilin kukan nata ba.

Billy giro😊

🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮

_Wnn page in naku ne maryam sifawa n ummi bunxa Allah ya bar min ku akan qaunar da kuke min Luv u❤_

🔮🔮🔮🔮
*```Page 68```*
A hnkli tayi saurin janye jikinta daga nashi ta zauna kan bed.
Shima ya bita kan bed d'in ya zauna yana mae kallon ta sae fmn share hawayen fuskarta take yace"me aka miki ne?
Komai bata ce mai ba sae girgiza kanta tayi alamar ba komai yace"to mene ne?
Murya can ciki tace"ba komai"
Tana gama fad'ar haka taji inna na qwala mata kira ta miqe had'e da fad'in "na'am inna"
Mohd ya bita da ido har ta fita ya sauke numfashi snn ya tashi ya fito d'akin ,
Amir dake zaune a falo yace"yauwa dama kai nake jira ka fito ka maida ni gida"
Makulli kawae man ya miqa masa yace"je maida kanka ni ta matata nake tukun"
Amir yayi dariya yace"hm abubuwan da angwaye keyi ne kaima ka soma"
Mohd yace"Amir knn nidae ungo kar6i makullin ni ko a kabubu ne zan koma"
Amir yace"ikon Allah lallai ka tsunduma da yawa a mota naga sae kallon yrnyr nn kake tayi hk a qauye da suka fita duk ka rasa natsuwarka yanzu mun dawo sae fmn bibiyar ta kake idan wata gare ka naga ai kana da mata sae kaje ka rage qishirwar ka a can ko kafin ka sami wnn"
Mohd dake kallon sa d'auke da murmushi ya girgiza kansa yace"kasan cewa idan kana jin qishin ruwa babu wani abu da zaka sha ya kore ma wnn qishin gabad'aya har sae idan ka sami ruwan tukun,kuma ai malika da kake wani zancenta kasan still basu dawo ba,kuma bibiyar Ryynt da nakeyi kai baka fhmci damuwar da take ciki bane dan Allah tun a mota"
Amir yace"kewa ce fa ka sani ba wani abu ba sbd dole ne ta tuna da rayuwar ta da tayi a baya musamman mutuwar mahaifinta"
Jiki sanyaye Mohd yace"hkne shiyasa take ban tausayi wlh har bana son ganinta cikin damuwa komai qanqantar ta kuwa"
Amir bai ce komai ba sae kalar tausayi da ya nuna a fuskar sa yayin da man yace"muje to muyiwa inna sallama sae mu tafi ko"
Nan Amir ya tashi suka tafi d'akin inna wacce suka samu ta tsiyaya wa Ryynt fura a cup tace"ungo kar6i kisha idan kin gama sae kije ki d'an watsa ruwa ko jikin naki zai d'an sake miki.
Ryynt ta kar6i fura ta fara sha sbd har da yunwa na damunta don bata wani ci abinci sosai a qauyen ba.
Man dake kallonta ya maida dubansa gun inna yace "inna mu zamu tafi sae anjima idan na dawo"
Inna tace"to en albarka Allah hutar da gajiya"
Suka ce"Amin"snn suka fita.

Guraren qarfe tara na dare sae ga mohd ya koma dawowa gidan, d'akin inna ya fara zuwa ya samu tana bathroom yayinda Ryynt ke kwance kan bed kmr wata mara lafiya sanye da kayan baccin ta riga da wando,
sae da ya ajiye ledar da ke hannun shi snn yaje gab da ita ya zauna had'e da riqo hannun ta yana mae kallon fuskarta,ta kalle sa sau d'aya ta kauda idonta snn ta zare hannunta a hnkli tare da juya mai baya ya kalle ta kawae snn ya kalli inna wacce ta fito daga bathroom knn ya gaida ta ta amsa ba yabo ba fallasa snn yace"ya gajiyar hanya tace "Alhmdlh ai ba wata gajiya yanzu sae bacci ita Ryynt kaga har ta samu tayi baccin ma"
Nan Mohd ya kalli Ryynt da kulawa snn yace"idonta biyu fa inna maybe dai baccin take ji "
Inna tace"au to shine kazo kayi zaune ka sata a gaba kana kallo awa wanda ke shirin had'iye ta"
Mohd yayi murmushi kawae had'e da d'aga wayar sa da ta shiga ruri bayan ya gama wayar ne yace"inna ni zan tafi nayi baqo a gida ne"
Tace"to sae da safe d'an albarka Allah kiyaye hanya"
Yace"Amin"
snn ya fita ba tare da ya d'auki ledar da ya ajiye ba don dama fruits ne ya siyo musu.

Washe gari tun da safe Ryynt ce ke harhard'a en kayanta da zata je dasu gidan su Saliha sbd umman saliha ce ta nemi inna da tana son Ryynt taje mata kafin su tashi tafiya.
Bayan ta kammala komai da qarfe goma nasir yazo ya d'auke ta ya kaita.
Da 11 sae ga mohd yazo gidan inna don shi bae san da zancen zata je gun umman saliha d'in ba sae a bakin inna yaji.

Tunda Ryynt taje gidan su saliha aikin komai bata yi sae gyaran jiki da umman saliha keyi mata taci wnn tasha wnn ta shafa wnn sae duk nn take jikinta ya fara nuna sauyi don wani irin haske ta qara tana sheqi kmr wata amarya duk fatar ta ta canza gabad'aya cikin en kwanakin da basu wuce uku ba wanda a cikin kwanakin sosai mohd yaso ganin Ryynt kmr me amma umman saliha bata barshi ba don tasan duk ta yarda yaga Ryynt ba lalle bane ya iya haqurin barinta kan irin gyaran da tasha ita kuwa tafi so sae sunyi tafiyar ko komai zai wankana.
A cikin en kwanakin sae duk mohd ya soma ramewa sbd kawai rashin ganin Ryynt da yaji kmr ya kwashe wasu shekaru ne bai ganta ba.
Next day ne tafiyar su India shiyasa da dare umman saliha ta tasa Ryynt gaba tana mata en nasifofi snn ta bata turarukkan mata masu qamshi kusan kala biyar da zata riqa amfani dasu idan tayi wanka zata shiga bacci.
Sosai Rynt ta mata godiya dmn taji dad'i har ranta duk da cewa har yanzu jikinta mace yake na rashin son komawarta gidan man.
Nasir ne yazo ya maida ta gidan inna ita da saliha sbd saliha so take ta kwana gidan inna dmn gobe da safe tana son taga tafiyar su Ryynt.

Washe gari tun da safe suka tafi.
Cikin jirgi Ryynt sae kuka take tayi man kuwa duk ya sukuikui ce yana faman rarrashin ta da qyar

Please Login or Register in order to submit comment