Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 4
har sun bushe sosai. yana takawa sai dai kaji karar farfashewar su ya cika dodon kunne.. haka ya cigaba da tafiya yana waige waige. ya rike takobin sa da hannu biyu gam gam yana jira wani abu ya kawo masa harin ba zato. kwatsam ba zato ba tsammani. sai yaga wasu irin jibga jibgan dodanni suna dirowa daga saman kogon kamar baza su kare ba. turusss ya ja birki ya tsaya a razane. tara da yin baya baya. dodannin suka cigaba da durowa daga saman kogon har sai da suka cika wurin dubu daya da wani abu sannan komai ya tsaya. kawai sai wadannan dodanni suka fara gurnani mai matukar razanarwa. hakanne yasa hujurul mahas ya tushe kunnuwan sa. har sai da dodanni suka tsitt. sannan ya sake kunnuwan nasa. sai gashi dodanni sun fara marmatsowa. shi kuwa hujurul mahas ya tsaya a in da yake. ya rike takobin sa sosai da hannu biyu. yana jiran su karaso? .. Comment and likes BY ABBAS WITH:- Shuraih 99% ρðšтєđ by Shuraih 99% νįά● Shuraih 99% Fðя мðяє ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1 By ABBAS With Shuraih 99% Part 19 ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ lokaci daya gabadaya dodannin suka farmasa. shi kuwa hujurul mahas shigar su yayi ya hausu da sara da suka cikin nuna bajinta irin nasu na kwararrun mayaka. amma duk wanda ya sara makamin baya tasiri ajikin su. nan fa ya zage dantse yana bubbugesu ta hanyar kai musu sara da karfin takobin sa. sai dai kaga sun fadi can gefe amma takobin baya illata su. sai kaga sun mike an cigaba da artabu. al'amarin daya dugunzuma hankalin hujurul mahas. ya fara tsorata da lamarin wadannan dodanni. nan fa dodannin suka tasar masa suna kokarin rikirkita shi. da yaga in dai bai yi da gaske ba dodannin za su kaishi kasss. sai ya kara zage dantse yana bazar dasu suna Dada tashi. cikin shammata wani dodo mai jarabar tsiya. ya makawa hujurul mahas dundu agadon bayan sa. take hujurul mahas ya kife akasa yana aman jini. su kuwa dodanni sai suka kara yin caaaa akan hujurul mahas don su karasa shi. zumbur ya tashi. cikin zafin nama yayi tsalle ya gabazawa wannan dodo naushi akunne. take dodon ya fadi kasa ma matacce ko motsi bai yi ba. ko da hujurul mahas yaga haka sai ya lura da cewa lagon dodannin akunnen su yake. kawai sai ya zage dantse ya cigaba da naushin dodanni akunne suna zubewa kasa matattu. cikin kankanin lokaci sai gashi hujurul mahas ya bazar da dodanni sama da dari shida. al'amarin daya bawa dodannin mamaki kenan. to shi wannan wanne irin shu'umin bil'adama ne mai nacin tsiya da karfin dantse da dabara. nan fa suma dodanni suka kara kaimi wurin kai wa hujurul mahas mugayen hare hare. amma ina basa samun damar taba shi. don ya riga ya zame mu su annoba sai karkshesu yake. nan da nan cikin kankanin lokaci sai gashi hujurul mahas ya bazar da gabakidaya dodannin. sai gashi gawarwakin su bircik zube awuri. a galabaice hujurul mahas ya fadi kasa yana haki kamar ransa zai fita. saboda tsananin jigata da yayi. ***** aljani bagzas yana kai kawo acikin wannan dakin halwar sa tsafi. ya kasa zaune. ya kasa tsaye . sakamakon wannan labari daya riske na cewar an sace mashin sihiri. wanda ya tayar masa da hankali. to yanzu shi boka saljan da ya sace wannan mashin sihiri ina ya nufa. kuma ina yake da zama ayanzu. bayan ya kaura daga in da yake da zama. to idan hakane dole ne agareshi ya bazama neman boka saljan domin ya dakatar dashi game da mallakar mashin sihiri da yake wurin sa? aljani bagzas ya kara tunawa da sarki maharu. ana wata ga wata. yanzu fa shima sarki maharu ya tafi neman boka saljan. idan haka ne ya zama dole yanzu yanzu. na tafi neman boka saljan ba tare da bata lokaci ba. tun da an ce da zafi zafi ake dukan karfe" tukuna ma yanzu ina batun su aljani mardis dana tura su raba sarki maharu da mashin sihiri. in kyautata zaton an labarta musu cewa wannan mashi ya bata don haka nasan nan da nan zasu bazama neman boka saljan duk in da yake. ya zama dole yanzu nima na shirya na bi bayan su. Comment and likes BY ABBAS Post:- Shuraih 99% ρðšтєđ by Shuraih 99% νįά● Shuraih 99% Fðя мðяє ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1 By ABBAS With Shuraih 99% Part 19 ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ lokaci daya gabadaya dodannin suka farmasa. shi kuwa hujurul mahas shigar su yayi ya hausu da sara da suka cikin nuna bajinta irin nasu na kwararrun mayaka. amma duk wanda ya sara makamin baya tasiri ajikin su. nan fa ya zage dantse yana bubbugesu ta hanyar kai musu sara da karfin takobin sa. sai dai kaga sun fadi can gefe amma takobin baya illata su. sai kaga sun mike an cigaba da artabu. al'amarin daya dugunzuma hankalin hujurul mahas. ya fara tsorata da lamarin wadannan dodanni. nan fa dodannin suka tasar masa suna kokarin rikirkita shi. da yaga in dai bai yi da gaske ba dodannin za su kaishi kasss. sai ya kara zage dantse yana bazar dasu suna Dada tashi. cikin shammata wani dodo mai jarabar tsiya. ya makawa hujurul mahas dundu agadon bayan sa. take hujurul mahas ya kife akasa yana aman jini. su kuwa dodanni sai suka kara yin caaaa akan hujurul mahas don su karasa shi. zumbur ya tashi. cikin zafin nama yayi tsalle ya gabazawa wannan dodo naushi akunne. take dodon ya fadi kasa ma matacce ko motsi bai yi ba. ko da hujurul mahas yaga haka sai ya lura da cewa lagon dodannin akunnen su yake. kawai sai ya zage dantse ya cigaba da naushin dodanni akunne suna zubewa kasa matattu. cikin kankanin lokaci sai gashi hujurul mahas ya bazar da dodanni sama da dari shida. al'amarin daya bawa dodannin mamaki kenan. to shi wannan wanne irin shu'umin bil'adama ne mai nacin tsiya da karfin dantse da dabara. nan fa suma dodanni suka kara kaimi wurin kai wa hujurul mahas mugayen hare hare. amma ina basa samun damar taba shi. don ya riga ya zame mu su annoba sai karkshesu yake. nan da nan cikin kankanin lokaci sai gashi hujurul mahas ya bazar da gabakidaya dodannin. sai gashi gawarwakin su bircik zube awuri. a galabaice hujurul mahas ya fadi kasa yana haki kamar ransa zai fita. saboda tsananin jigata da yayi. ***** aljani bagzas yana kai kawo acikin wannan dakin halwar sa tsafi. ya kasa zaune. ya kasa tsaye . sakamakon wannan labari daya riske na cewar an sace mashin sihiri. wanda ya tayar masa da hankali. to yanzu shi boka saljan da ya sace wannan mashin sihiri ina ya nufa. kuma ina yake da zama ayanzu. bayan ya kaura daga in da yake da zama. to idan hakane dole ne agareshi ya bazama neman boka saljan domin ya dakatar dashi game da mallakar mashin sihiri da yake wurin sa? aljani bagzas ya kara tunawa da sarki maharu. ana wata ga wata. yanzu fa shima sarki maharu ya tafi neman boka saljan. idan haka ne ya zama dole yanzu yanzu. na tafi neman boka saljan ba tare da bata lokaci ba. tun da an ce da zafi zafi ake dukan karfe" tukuna ma yanzu ina batun su aljani mardis dana tura su raba sarki maharu da mashin sihiri. in kyautata zaton an labarta musu cewa wannan mashi ya bata don haka nasan nan da nan zasu bazama neman boka saljan duk in da yake. ya zama dole yanzu nima na shirya na bi bayan su. Comment and likes BY ABBAS Post:- Shuraih 99% ρðšтєđ by Shuraih 99% νįά● Shuraih 99% Fðя мðяє ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1 By ABBAS With Shuraih 99% Part 20 ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ labu daya dana ke tunani shi ne . kada hujul mahas su hada baki da boka saljan don suga sun mallaki wannan mashin. domin wannan itace hanya mafi sauki da suke ganin zasu kawar dani da ba tare wata matsala ba. tukuna ma ta yaya boka saljan zai hada kai da hujhrl mahas ai kawai na tabbata boka saljan shi kadai zai yi amfani da wannan mashin. saboda shima shahararren matsafi ne. don haka abinda zai fishsheni shine nayi gaggawar barin wannan gida na tafi neman mashin sihiri kafin wadannan hamshakan bil'adaman su rigani. samun mashin sihiri. Aljani bagazas na gama fadar haka acikin zuciyarsa. kawai sai ya nufi wata akwatin sa ya dauko takobin sa . sannan yayi gagarumar shigar yaki mai matukar razanarwa ga duk wanda yayi arba da shi. bayan ya gama shirin sa tsaf. sai ya bude fukafukan sa. ya tashi sama. ya luluka acikin gajimare. yana zabga uban gudu... ** hujurul mahas na kwance cikin halin suma . yayi wanwar a kasa tamkar matacce. duk wanda ya gansa a wannan hali zai yi zaton matacce ne. sai bayan sa'a daya da wani abu ya farfado. tashi yayi zaune a matukar galabaice. a lokacin da yaji wata irin yunwa ta addabe shi. nan da nan ya futo da abincin sa. dake cikin jakar sa. ya kama ci. sai da ya koshi sosai. lokacin abinci ya kare. sannan ya dauko ruwa a battar sa yasha. sannan ya shiga sabon tunani. hujurul mahas. ya tuna lokacin da aljani mardis. yazo masa a cikin kogon dutsen da yake rayuwa aciki. in da aljani mardis ya bayyana acikin kogon dutsen. a razane hujurul mahas ya juyo. yana fadin mutum ko aljan? aljani mardis. yace. yakai wannan bil'adam. kada ka tsorata dani. domin ni ba cutarwa ba ne agareka? samar da nutsuwa a gareni yasa kaga nazo wannan kogo naka? cikin mamaki hujurul mahas yace. kamar yaya. zaka samar wa kan nutsuwa idan har ka zauna anan kogon. rashin nutsuwa yana nufin. babu zaman lafiya? me kake nufi" aljani mardis yayi murmushi yace. kada kayi tunanin da wata mummunar manufa nazo nan kogon. na yi la'akari ne da shahararka a bangaren tsafi. na lura da kai cewa kai ne kadai zan iya zama da kai na tsira da mummunan tarkon da akayi min saboda zalunci? ka sani cewa an kashe iyaye na dangi na. da dai wasu da na shaku dasu ta hanyar abokantaka. ba wani ba ne wannan wanda ya kashe iyayena face wani aljani wai shi aljani bagazas. aljani bagazas ba shida mutunci ko kadan. azzalumi ne shi. da yake mahaifina da sauran karfin sa. haka suka yi ta gumurzu da aljani bagazas har tsawon kwana biyu. babu hutawa sun ruguza komai na gidan. a karshe aljani bagazas yayi galaba akan mahaifina ya kashe shi. mahaifina yayi wa aljani bagazas munanan raunika ajikin sa ko ta Ina kamar bazai rayu ba. duk haka sai da aljani bagazas ya shiga har cikin gidan mu bayan ya kashe mahaifina. ya kashe mahaifiyata ita sai da suka yi gumurzu da ita. lokacin bana gidan. bayan na dawo na samu an kona gidan mu kurumus. arazane na shiga duba ko ina acikin gidan. kawai sai nayi kicibis da gawar mahaifiyata. sakin takobina nayi ta fadi kasa. na daura hannu bisa kai. saboda tsananin firgita kasa kuka nayi. ina kukan a zuciya? na jima ina kukan zuci kafin na tuna da mahaifina nan da nan na kara gaba. ina neman shi. gawar na gani shima a kasa a yashe" wannan karan kuwa kuka na sake iya karfi na. ina kuka hawaye na zuba. sai da na yi kuka mai isa ta. sannan na janye gawar mahaifina daga jikina na zuba mata idanu? sai daga can na kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa. wanda dajin gabadaya ya amsa kuwwa! daga can na tsaya da ihu. ina fadin cewa. tabbas sai na nunawa aljani bagazas ni ya tabo" sai na nuna masa bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane" sai na nuna masa shi ba komai bane? sai gwada masa irin tawa annobar? a wannan lokaci idanuna sun rufe. komai zan iya aikatawa ga wanda ya hanani zuwa in da aljani bagazas yake. domin sai na dau fansa? mun yaki mai tsanani ni da aljani bagazas. kamar za muyi ragas? a karshe na sumar da aljani bagazas? nan da nan kuwa na bar gidan aljani bagazas don na sake shiri. wannan shi ne. dalilin da yasa nazo nan kogon. ina so ka taimakamin. ina so kace zaka taimakamin. domin rayuwata tana cikin hatsari muddin na kasance ina yawo a waje ba a cikin kogon nan? abinda nake so naji daga bakin ka kace zaka taimakamin? bani da niyyar ha'intar ka har cikin zuciyata. duk wani abu da ya danganci sharri banzo dashi cikin kogon nan ba? da alkairi nake tafe? sa'adda aljani mardis yazo nan azancen sa sai hujurul mahas yayi shiru na tsawon lokaci. daga can sai yayi ajiyar zuciya ya dago da kai yace. shi kenan na yarda da kai. na yarda da duk wannan batu naka. zan zauna tare da kai? aljani mardis yayi farin ciki sosai? haka mukayi ta rayuwa ni da aljani mardis. cikin kwanaki kadan muka shaku dashi sosai matuka! akullum sai ya nishadantar dani da labarai masu dadi. daidai da sakan daya bana so ya rabu dani?? sai gashi rana daya an dauke aljani mardis? "lokacin da hujurul mahas yazo nan a tunanin sa. sai yayi ajiyar zuciya" ya fada acikin zuciyar sa" ko ta yaya sai dawo da aljani mardis gareni koda zan rasa rayuwata" muddin ban shawo kan aljani mardis ya dawo gareni ba. to tabbas ni ma banga amfanin rayuwata" hujurul mahas yana cikin wannan tunani sai yaga wata kyakkyawar budurwa ta diro daga saman rufin kogon??? Comment and likes BY ABBAS Post:- Shuraih 99% ρðšтєđ by Shuraih 99% νįά● Shuraih 99% Fðя мðяє ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1 By ABBAS With Shuraih 99% Part 21 ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~budurwar ta rufe fuskar ta da wani bakin kyalle ba'a ganin fuskar ta. tana sanye da wasu korayen kaya masu tsananin kyalkyali da sheki suna daukar idanu. daga ganin budurwar hujurul mahas ya tabbatar da cewa wannan kyakkyawa ce. duk da bata bude fuskarta ba" bayyanar budurwar ne ta samar da haske a cikin kogon. hujurul ya zuba mata ido yana kallon ta. don ya tabbatar da cewa awannan hali da yake bazai iya yin komai ba? idan ma kashe shi tazo tayi sai dai ta aikata nufinta? da kyar ya budi baki yace. wace ce ke? daga ina ki ke! sannan saboda me kika zo wurina" budurwar tasa hannu ta yaye mayafin da ta rufe fuskarta. kyan fuskarta ya bayyana a fili. kawai sai ta saki murmushi" al'amarin da ya rikirkita hujurul mahas kenan? baisan lokacin daya tashi tsaye ba? baki a bude? ya ambaci sunan ta? ""salira" abin da iya fada kenan tare da nunata yatsa"" salira ta kara yin murmushi wanda ya kara rikirkita hujurul mahas. cikin murya mai dadi tace. ni ce salira 'yar sarkin wannan garin wato sarki sarki maharu? hujurul mahas yace. me ke tafe dake" salira tayi murmshi tace. alheri ne ke tafe dani. ka yar da dani. ka da zuciyarka ta yaudareka don kaki yarda dani" ba komai bane yazo dani face na taimake ka. taimakon kuwa shi ne. in fitar da kai daga wannan kogo? hujurul mahas yace. ni fa ban gane me kike nufi ba" ki fitar dani daga wannan kogon. nufin ki mahaifin ki ne ya turo ki! salira ta matso kusa daf da in da hujurul mahas yake? ta zauna ta dube shi tace. ko kadan ba mahafina ba ne ya turo ni. ra'ayin kai na ne. barin ka acikin wannan kogon halaka zaka yi. muddin ban kubutar da kai ba. babu wanda zai ceci rayuwar ka. yanzu haka babu wanda yasan na shigo wannan kogon. hatta mahaifina" tun ranar da nayi arba da kai a cikin fadar mahaifina. dakaru sun taso ka a gaba naji tausayin ka ya kamani bazan iya barin ka halaka ba. shi ne nazo domin ceci rayuwar ko da kuwa zan halaka' hujurul mahas yayi a jiyar zuciya sannan ya dubi salira yace. ta yaya ki kazo har nan wurin alhalin mahaifinki nan bayan kuma ya saka dakaru ko ta ina a wannan gida. don tabbatar da tsaro. salira tayi murmushi tace. ai karfin tsaro awannan gidan to mahaifina ne. amma fa a wurina? shi yasa kaga nazo har cikin wannan kogon ba tare da wata matsala ba.' hujurul mahas yace. Kenan mahaifinki baya nan. salira tayi shiru tana so ta fada masa al'amarin amma tana fargabar abin da zai biyo baya. sai kuma ta tuna ai idan ta fada masa ba komai ba ne tun da wannan shi zai sa hujurul ya ce ya janye da mallakar mashin sihiri. shi Kenan ta samu damar za ta sace zuciyar hujurul mahas. don ya manta da wata lushmat" salira ta dago da kai tace. ai an sace mashin sihiri....... da sauri hujurul mahas ya dago dakai cikin mamaki. yace. an sace mashin sihiri . salira tace. kwarai kuwa an sace mashin sihiri" to wanene ya sace. tukuna ma wanne irin sakaci mahaifinki yayi har aka sace wannan mashin yadda yake bada tsaro akansa" tabbas wanda ya sace wannan mashin ya cika mashahurin hatsabibi. ! yanzu ina mahaifin naki yake' salira tace. ai yanzu mahaifina ya bi bayan wanda ya sace mashin sihiri wanda ni kaina ban san wanene ba. na tabbata yanzu aljani bagazas ya samu labarin cewa an sace mashin sihiri kuma shima ya tafi farautar wanda ya sace mashin. ko da jin haka sai hujurul mahas ya mike tsaye da sauri. ya dubi salira yace. ki taimaka ki fitar dani daga wannan kogon domin zama bai kama ni ba. salira tace. kamar yaya nufin ka har yanzu baka janye bukatar ka ta mallakar mashin sihiri ba. . yace. ta yaya zan janye bukata ta ta mallakar mashin sihiri. bayan ta sanadin mashin ne na fado tarkon mahaifinki har na tsinci kaina anan" son na mallaki mashin ne yasa naki yin hakuri har na tunkari wannan birnin naku domin na raba mahaifin ki da mashin sihiri. bayan na samu labarin cewa mahaifin ki ya bada tsaro akan mashin sihiri. amma hakan baisa na ki tunkarar mahaifin ki ba" karshe ga abinda ya faru dani' yanzu kuma ga dama ta samu kuma kina Neman kice nayi hakuri na janye batun mashin sihiri. salira tace. ni bazan ki in hana ka ka tafi Neman mashin sihiri Amma ina kara guje maka irin hadarurrukan da zaka shiga" wai tsaya ma kasan wanda ya sace mashin sihirin ne' hujurul mahas yace. tabbas na san wanda ya sace mashin sihiri. ke dai kawai ki fitar dani daga wannan kogon ?Comment and likes BY ABBAS Post:- Shuraih 99% ρðšтєđ by Shuraih 99% νįά● Shuraih 99% Fðя мðяє ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1 By ABBAS With Shuraih 99% Part 22 ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~salira tace. zan fitar da kai daga wannan kogon. amma fa baza ka tafi kai kadai. hujul mahas yace. kamar yaya. tace. sai dai na bika mu tafi tare. saboda bazan taba samun sunkuni da kwaciyar hankali ba face ina tare da kai. ko da na zauna anan wurin mahaifina. duk wata ingattacciya kulawa da zai bani bazai iya bani maganin jure rashin ganin ka akusa dani. bin ka shi ne kadai samun farin cikina. idan yaso komai zai faru a tafiya neman mashin sihiri ya faru tare dani. domin a halin matsayin ka aguna yafi min komai"" da sauri yace. har da iyayen ki? tayi murmushi tace. bazai zabe ka sama da iyaye na ba. amma son ka da ya shiga cikin zuciya ta ya haddasa min bana ganin kowa nayi farin ciki sai kai. kai ne kadai wanda tun farko ganin ka naji zuciya ta ta cika da tsananin sonka. tun da wannan lokacin bani da buri yafi naga ka waiwaye ni amatsayin wacce kake so. don haka kada ka juya min baya? shiru yayi yana kallon ta har ta gama magana sannan yace. babu ki barni nayi shawara da kaina idan na gamsu da bayanin ki. za ki ji amsa ta. yanzu kina tunanin idan mahaifinki ya dawo yaga babu ke babu matsala" tace. babu matsala matukar mahaifina ya dawo yaga babu ni. saboda 'batan wannan mashin sihiri zai hana shi kwanciyar. don bazai damu dani ba. ko da kuwa ba na nan. domin yadda ya dauki komai nasa mai muhimmanci ya aje agefe ya dawo yana hidima akan wannan mashi. idanun sa sun rufe akan wannan mashin. sannan rana an sace mashin. kaga kuwa babu zaman lafiya ga wanda ya sace mashin. domin shima ya na nan yana boye boyen mashin. saboda gani yake ako da yaushe mahaifina zai iya bayyana agare shi. na tabbata muddin mahaifina bai samu wannan mashin ba to bazai waiwayeni ba. don haka ka yarda mu tafi tare. hujurul mahas yayi murmushi yace. shi kenan babu matsala. cikin murna ta tashi tsaye tana dariya. shi kuma yana murmushi. kawai sai ta dafa hannun sa. take suka bace bat atare. sai gashi sun bayyana acan bayan gari. babu kowa awurin domin yana daf cikin daji. hujurul mahas ya kyalkyale da dariya ita ma salira ta ta ya shi"...... shin sarki maharu yana haduwa da boka saljan. idan sun hadu me zai faru. waye zai samu damar mallakar mashin sihiri? ina labarin su aljani mardis. shin aljani bagazas zai cika burin sa na mallakar mashin sihiri. shin sarki majarul daufus zai samu damar yaudarar hujurul mahas. idan salira da lushmat suka hadu da juna me zai faru. acikin su wacece zata auri hujurul mahas? mu hadu alittafin mashin sihiri 2 na biyu. domin jin cigaban labarin. ni abbas wanda ya rubuta ina muku fatan alheri???? Toh masoya sai kunjini apart 2 nashi wanda zai dan dau lokaci sabida ba a gama aiki akai ba Shuraih 99% Amma kafinnan zamu shiga sabon littafi mai suna JARUMI JAZUR Na barku lafiya Comment and likes BY ABBAS Post:- Shuraih 99% ρðšтєđ by Shuraih 99% νįά● Shuraih 99% Fðя мðяє ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 4 of 4