Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 4
da dama masu ji da sadaukantaka. sun mutu acikin wannan dakin. don haka ku dauke shi ku kai shi can dakin kasa. cikin sauri dakarun suka kama hujurul mahas suka tashe shi tsaye. suka tasa keyar shi suna tafiya. awannan lokaci gimbiya salira sai kallon hujurul mahas take tana tausayin halin da ya tsinci kan sa har ta kai ga har ga za asa shi awannan dakin da ba a fita araye idan har an shige shi. nan salira taji lokaci guda hujurul mahas ya kwanta mata taji kamar taje ta dakatar da wadannan dakaru. amma babu hali haka ta cigaba da kallon hujurul mahas. shi ma hujurul mahas yana kallon ta da watsiyar ido. ko da dakarun suka lura da kallon da hujurul mahas ke yi wa gimbiya salira sai babban su ya daga wata sanda dake hannun sa ya bugawa hujurul mahas a dantsen hannun shi. sannan yace. kai 'ban ka!! mu da muke gidan bamu damu da mu ganta ba sai kai. wanda kake matsayin mai laifi.. hujurul mahas ya cije duk da yaji zafin dukan da wannan shugaban dakarun yayi masa" haka suka cigaba da tafiya suna wuce lunguna da sakuna ba cikin gidan. duk in da suka wuce sai jama'ar gari suna kallon su ana mamakin yadda wannan mutumin tsautsayi yazo masa muraran har shiga hannun sarki maharu. lallai muddin idan har ya shiga wannan dakin na azaba to tashi ta kare don saidai 'uwassa ta haifi wani amma ba shi ba. haka mutane gari suke ta fada. ahaka dakarun suka taso hujurul mahas wanda ke daure cikin sarka. har suka zo wani babban fili wanda ke share tas. babu alamar datti. ko ina ka duba fes fes. shi kan sa hujurul yana mamakin yadda akayi akazo dashi nan kuma aka tsaya bayan ance kuma dakin azaba za azo dashi. nan dai hujurul mahas ya tsaya kuma ya zuba ido yana kallon dakarun. su kuma dakarun sai suka fara kwance sarkar dake hannu da kafar sa sannan. har suka kwance duka. ko da hujurul mahas yaga sun kwance shi. sai ya fara zazzare idanu yana kallon gabas da yamma kudu da arewa. cikin shammata ya zage karfin dantsen shi. ya takarkare ya gabzawa wannan shugaban dakarun naushi akunne. a take shugaban dakarun ya sandare a tsaye tamkar gunki. sannan ya fadi kasa matacce ko shurawa bai yi ba. ko da sauran dakarun suka abinda ya faru ga dan uwan su sai suka kwarara 'uban ihu suka afakawa hujurul mahas su duka hudun sai gashi hujurul mahas ya kuntata su nan take ya shiga gabza musu wawan naushi suna zubewa kasa matattu kafin wani lokaci ya bazar dasu duka hudun. yana gama kashe su sai ya hango wasu gugun dakaru rike da makamai sun nufo shi. nan take hujurul mahas ya juya ya nufi wannan babban filin da gudu. kash rashin sani yafi dare duhu. abin da hujurul mahas bai sani ba shine. anan wannan dakin azaba yake. ko da hujurul mahas yaza dai dai tsakiyar filin sai kasar wurin ta rufza dashi aikuwa sai gashi ya fada ciki. nan kasar wurin ta dawo dai dai yanda take. su kuwa dakaru ko da suka dai dai wurin sai suka tsatstsaya suna waige waige. sai daya daga cikin dakarun yace. ai ya riga fada cikin wannan dakin na mutuwa. in da yana nan da mun ganshi. saboda tanan ya biyo babu yanda za ayi ya biyo tanan ba tare da ya fada wannan dakin ba. don haka mu koma muje mu fada wa sarki cewa ai wannan jarumi ya fada dakin mutuwa. cikin hadin baki dakaru suka ce. haka ne!! " al'amarin hujurul mahas kuwa lokacin da ya fada wannan dakin sai ya tsinci kan sa a wani irin duhu matsananci. al'amarin da ya firgitashi kenan zuciyar shi tana dukan uku uku. can sai yaga cikin dakin ya haskake da wani irin haske. wanda yasa hankalin ya kwanta. amma da ya ga abun dake ciki sai hankalin sa ya tashi. wani kogon dutse ne ya gani ku sa dashi. acan gaba ma ga wani shuri babba mai cike da manyan kofofi. bayan sauran dakunan dake gaba. hujurul mahas ya tashi daga zaman da yayi ya cigaba da kallon wannan kogon dutse. yana cikin wannan kallon kogon dutsen ne ya jiyo wani irin gurnani mai matukar tayar da hankali...... Comment and likes BY ABBAS WITH:- Shuraih 99% ρðšтєđ by Shuraih 99% νįά● Shuraih 99% Fðя мðяє ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1 By ABBAS With Shuraih 99% Part 13 ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ afirgice ya zare takobin sa ya fara ja da baya yana jiran yaga abinda zai futo. amma sai gurnanin ya cigaba da karu wa. nan fa hankalin sa ya dugunzuma. kamewa yayi awuri daya bisa abinda ya gani ya futo daga cikin wannan kogo. wata jibgegiyar macijiya ya gani tana futowa mai kawuna goma. ga hakoranta bircik acikin bakinta bare kuma dogayun fikokin dake bakinta atsatsaye masu tsinin tsiya. haka ya cigaba da kallon macijiyar tana futowa har ta gama futowa. ko da hujurul mahas yaga girman macijiyar da tsayin ta. sai ya tabbatar da cewa rayuwar sa na tsakanin mutuwa da rayuwa. awannan lokaci tuni macijiyar ta fara kewaye shi. tana gurnani. ko da hujurul mahas yaga haka sai ya fara amfani da karfin sihirin sa don ya tsallake macijiyar da take kewaye shi. ko da yayi sama sai macijiyar tayi amfani da jelarta ta bugoshi. sai gashi ya bugu da jikin dutsen kogon take kansa ya fashe. da sauri hujurul mahas ya shafa kansa koda yaga jini sai ya tashi afirgice ya cigaba da kallon macijiyar. sai yanzu ya tabbatar ya shiga tsaka mai wuya kashe wannan macijiyar sai yayi da gaske. dole ne yasan dabarar dazai yi ya kashe ta. nan take yakara rike takobin sa gam gam ya fuskanci macijiyar. kawai sai ya ruga da gudu ya tunkari macijiyar. ko da ya iso daf da ita sai ta kawo masa wawan sara akai. cikin zafin nama ya goce. sannan yayi tsalle ya gabzawa macijiyar sara da takobin sa a tsakiyar kai. take tartsatsin wuta ya tashi har da hayaki. al'amarin da ya razana hujurul mahas kenan. ya tabbatar tasa ta kare. haka macijiyar ta cigaba da kai masa mugayen hare hare yana tsallakewa. akarshe ta kara buga masa wannan jelarta ta. wannan karon sai da yayi sama sannan ya fado ya bugu da jikin kogon dutsen. agalabaice ya fara numfarfashi. kamar ransa zai fita duk da haka sai da macijyar ta kara kawo mishi sara. cikin zafin nama ya mirgina ya bar wurin. macijiyar ta karci kasa. ta haifar da dogon rami. hujurul mahas yayi zumbur ya tashi ya rike takobin sa ya cigaba da kallon macijiyar yana tunanin dabarar da zai bullo mata ya kashe ta. yana cikin wannan tunanin ne bai yi aune ba sai ji yayi macijiyar ta shammace shi ta kafta masa sara akai. take ya fadi kasa yana kakarin mutuwa. wata farar kumfa tana fita abakin sa. ita kuma macijiyar sai ta tsaya akan sa tana gurnani tana shirin karasa shi.... Ahankali ya fara bude idanun sa. Sannan ga macijiyar tsaye a kanshi tana jiran yayi wani motsi. Comment and likes BY ABBAS WITH:- Shuraih 99% ρðšтєđ by Shuraih 99% νįά● Shuraih 99% Fðя мðяє ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1 By ABBAS With Shuraih 99% Part 14 ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ tashi yayi zaune daga kwancen da yake. ya amayar da dafin wannan macijiyar da ta saka mishi. cikin zafin nama ya mike zumbur kafin macijiyar tayi wani yunkurin farmasa tuni ya daka tsalle sama. a saman ya zare wasu takubba guda biyu. sannan. kawai sai ya caka mata takubban guda biyu acikin idanun ta biyu. faruwan hakan kenan sai kan macijiyar guda biyu ya daina aiki. ko da hurul mahas ya ga haka sai ya gane lagon macijiyar a idanun ta yake. kawai sai ya zage dantse ya cigaba da caka takubban sa acikin idanun macijiyar... ita kuwa macijiyar ta fara karaji ta na kawo masa muggan hare hare amma yana kauce wa... wani gagarumar bajinta hujurul mahas ke nuna wa. domin cikin kankanin lokaci ya faffasa idanun macijiyar tare da taimakon takubban hannun sa. kawai sai gani yayi macijiyar ta fadi kasa rikica ko kwakkwaran motsi. ta riga ta zama gawa. shi kuwa hujurul mahas sai ya fadi akasa a sume. *** al'amarin aljani mardis kuwa tare da wadannan dakaru . sai da suka yi kwana uku acikin sararin sama suna zabga uban gudu tamkar tauraruwa mai wutsiya sannan suka fara hango kofar birnin zamar. awannan lokaci suna iya hango dandazon muggan dakarun da suke kaikawo awurin. duk da cewa dare ya fara yi. kawai sai suka fara rage karfin gudun nasu. sai da kusa da birnin yanda dakarun baza su gan suba. sannan suka fara sauko wa kasa. sai ga shi sun dira bisa kasa ahankali. su ka nemi wani wuri abayan wata bishiya suka buya tare da taimakon ganye bishiyar. yanda baza agansu ba. bayan sun nutsu sai aljani mardis ya dubi wani badakaren aljani wanda shi ne dan babba acikin su. sannan yace. yakai karsas ina so nasa ka Comment and likes BY ABBAS WITH:- Shuraih 99% ρðšтєđ by Shuraih 99% νįά● Shuraih 99% Fðя мðяє ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1 By ABBAS With Shuraih 99% Part 15 ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ wani aiki. da zarar dare yayi ina so ka rikida izuwa siffar bil.adama. ka yi shiga ta wadannan dakaru mu kuma sai mu rikida izuwa siffar fursunoni. sannan sai na saka mana sarka hannu da kafa yadda ba za su gane mu 'yan harin ba zato idan har mun shiga cikin birnin ni na san abin da zan yi. abin da yasa kaji nace kayi shiga irin ta wadannan dakaru kuwa. shi ne. dakarun suna dayawa. baza su gane wani ne daban ya shigo cikin su duk da suna ba da tsaro. na musamman. da zarar mun ga dakarun sun fara hango mu. sai ka fara ihu kana ikirarin azo ataimaka maka ga wasu fursunoni. na tabbata za su zo gare mu domin su ganewa idanun su. abu ne mai wuya su gane cewa kai ba acikin su kake ba. idan kuwa har suka gane hakan cewa kai ba daga yankin su ka futo ba. to komai zai iya faruwa. yanzu dai bari mu jarraba wannan shawarar da nazo mana da ita. na tabbata zamu cimma nufin mu. ko da aljani mardis yazo nan a jawabin sa. sai aljani karsas ya gyada kai alamar ya yarda akwada wannan shawara da aljani mardis yazo da ita ko za ayi nasara. suma sauran dakarun aljanun suka amsa sun yarda da wannan shawara. " hakan kuwa suka yi ba yan dare ya yi sai aljani karsas ya rikida izuwa irin wadannan dakaru masu gadi. su kuwa su aljani mardis suka rikida izuwa fursunoni. aljani karsas ya sa musu sarka hannu da kafa. aljani yasan dalilin da yasa shi bai zama shugaba da zai jagoranci dakarun da suke tare dashi. shiyasa yasa aljani karsas. bayan aljani karsas ya daddaure su da sarka sai kama sauran sarkar da ta rage ya fara jan su. haka suka ta tafiya har suka fara isowa in da wadannan dakaru suke. da yake cikin dare ne. sai ya fara jan su aljani mardis da karfi suna cijewa. ya shiga kwalawa dakarun kira azo taimaka masa. aikuwa sai dakarun suka ankara dashi... saura suka tsaya abakin kofar shiga garin saura suka nufo in da su aljani mardis suke. cikin kankanin lokaci sai ga dakaru sun kewaye su aljani mardis. nan take wani badakare mai kirar samudawa. ya ratso ta cikin dakarun. ya bayyana atsakiyar filin. nan take ya cafke sarkar dake hannun aljani karsas " da wata irin babbar murya yake magana. zan tafi dasu wurin shugaban mu sarkin kofa. domin shi zai yanke hukunci. don haka ka biyoni abaya. yana gama fadar haka. ya dakawa fursononin tsawa yace. kai kananan kwari. ku na tunanin mugun nufin ku zai sauka akan mu ne? ko kadan ba ku isa kuyi mana komai ba. domin ka ta wacce siiiiga ku ka zo sai an tona muku asiri. yanzu gashi kun shiga hannu. daya daga cikin dakarun mu ne shi ya tona asirin ku. dama kuna so ku kawo mana mamayar ba zato? ko haka ba ne? ya wankawa daya daga cikin fursunonin mari. yace. "ba tambayar ku nake ba. dukan su fursunonin suka ce. eh. shugaban dakarun ya finciki sarkar dake daure ajikin fursunonin. ya fara jansu. aka buda masa hanya ya wuce. saurana dakarun suka bi shi abaya duuuu? kamar dokuna. suka tunkari wurin sarkin kofa. sauran dakarun dake bakin kofa suka ba da hanya. kai tsaye aka tura su aljani mardis gaban wannan sarkin kofa mai kirar manyan samudawa. jikin sa gabadaya acike jijiyoyi. ga damatsan hannayen sa burdin burdin". sarkin kofan ya tashi tsaye. ya kyalkyale da dariya kamar bazai daina ba. daga ya murtuke fuska. yace. wadannan su ne fursunonin. aka ce eh" ina wanda ya kawo su." aljani karsas ya ratso ta cikin dakarun cikin siffa irinta dakarun. aka ba shi hanya. ya tsaya a gaban sarkin kofa. ko da sarkin kofa yaga wanda ya kawo su. sai yayi murmushi. ya fara zagaye aljani karsas. shi kansa ya fara tsorata da al'amarin sarkin kofa" kada fa asirin su ya tonu fa" sarkin kofa ya kyalkyale da dariya sannan yayi tsit. ya dakawa su aljani mardis tsawo yace. karya kuke ku ba mutane ba ne. nasan me kuke nufi. kun shirya wani makircin ku ne daban. sai gashi hakan ku bai cimma ruwa ba? sarkin maharu. wato sarkin birnin ya fada mana akwai wasu bakin aljanu za su zo nan birnin a cikin siffa ta bil'adama. abinda ya fada mana. mu kama ku mu sakaku acikin sarka mu gurfanar daku gareshi. ko ku bimu acikin ruwan Sanyi. mu tafi daku amutunce. idan kuma ko kace da tsiya zaku bimu. zamu kai kune a wahalce." ko da su aljani mardis suka wannan batu. sai suka fara zazzare idanu. suka tabbatar da cewa asirin su ya tonu......... Comment and likes BY ABBAS WITH:- Shuraih 99% ρðšтєđ by Shuraih 99% νįά● Shuraih 99% Fðя мðяє ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1 By ABBAS With Shuraih 99% Part 16 ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ sarkin kofa ya dakawa wasu dakaru tsawa. wanda su kasance karatan samudawa. yace. Ku kama su ku kara daure cikin sarka. a tafi dasu gurin sarki"" ! dakata !!! aljani mardis ya dakawa wadannan dakaru tsawa. kada dayan ku ya matsa kusa damu" lokaci guda aljani mardis ya rikida izuwa ainihin halittar sa. suma sauran aljanun suka dawo ainihin halittar su" ko da sarkin kofa yaga haka sai dakawa dakarun tsawa. yace. me kuke jira dasu ku kamasu ku daure su cikin sarka" awannan lokaci sarkar da ta daure su aljani mardis ta tsinke. ko dakarun suka zo wurin su aljani mardis domin su daure su. cikin zafin nama aljani mardis. yayi amfani da hannun sa. ya daki badakaren mai rike da sarkar akai. take badakaren ya fadi kasa matacce. sauran dakarun kuwa suma ya gaggasa musu naushi daddaya suka bace awurin. ko da ganin wannan abun sai gabakidaya dakarun suka afakawa su aljani mardis. aka ruguntsume da azababben yaki. shi kuwa sarkin kofa gefe daya ya koma ya cigaba da kallon wannan gumurzu. wohoho!! nan fa su aljani mardis suka zamewa wadannan dakarun masifa. sun kuntata su. ban da Sara da sukar dakarun babu abinda su aljani mardis suke. cikin kankanin lokaci sai jikin ya rine da jini. domin sai gididdibar dakarun suke ba ji ba gani. sai dai kaga lokaci guda aljani mardis ya fillewa dakaru ashirin kai alokaci guda. shima aljani karsas sai gagarumar bajinta yake nunawa. domin shima ragargazar dakarun yake. haka suma sauran aljanun. sai karkashe dakarun suke" ko da sarkin kofa yaga za'a karar da wadannan dakarun nasa. sai kwarara uban ihu. Wanda yayi amsakuuwa afilin gabadaya" babu shiri dakarun suka janye yakin dukan su. aka budawa sarkin kofa hanya ya shigo. tsakiyar filin ya tsaya. sannan ya zare takobin sa ya daga sama ya kwarara wani ihu daban. Wanda yasa dakarun wajen suka toshe kunnuwan su. har sai da ya tsaya da dariyar sannan aka samu sauki. sannan ya fuskanci aljani mardis ya daka masa tsawa. kai shu'uman aljanu karyar ku tasha Karya. kun kashe mun dakaruna gabada ya. Wanda suka rage ba su fi guda arba'in ba . duba kasa duka gawarwakin dakaruna ne. Wanda suke tayani gadi" ba dan dalili kwaya daya ba da sai nayi muku mugun kisan gillah. sarkin mu yana bukatar ku a raye. yanzu zan kama Ku na daure ku acikin sarka... aljani mardis ya dakawa sarkin kofa tsawa yace.. karya kake kace zaka kama mu ka samu cikin sarka. ba ka isa ba wanene kai. idan har kaga an kama mu anan to tabbas bama numfashi. sarkin kofa. yayi murmushi yace. kada ka wahalar da kanka abanza. da kai da wadannan abokan tafiyar taka. domin daure Ku acikin sarkar nan ya zama dole. aljani mardis. yace. to bari na fada maka ko sarkin ku ne yazo nan yace zai saka mu a sarka to ba zai Iya bare kai karamin alhaki. mafita daya ce ka bamu hanya kawai mu wuce har can cikin wannan birni domin mu sarki maharu da mashin sihiri... kafin aljani mardis ya rufe bakin tuni sarkin kofa ya tunkaro shi kai tsaye. aljani mardis ya tsaya awurin da yake. yana jiran karasowar sarkin kofa. sarkin kofa yana zuwa ya kawowa aljani mardis cafka.. cikin zafin nama aljani mardis ya sunkuya ya goce ya bi ta tsakanin kafofin sarkin kofa. nan ya zare takobin sa ya sari bayan sarkin kofa. nan take yaji kamar ya sarin karfe. al'amarin da bashi mamaki kenan . lalle sai yayi da gaske. afusace sarkin ya juyo. ya kara kawo masa cafka. nan ma ya kara kaucewa. haka rinka kawowa aljani mardis cafka yana gocewa. daga karshe ya samu nasarar bige aljani mardis. sai da yayi sannan ya bugu kasa agalabaice. kamar ransa zai fita. nan fa sarkin kofa ya tunkaro aljani mardis kai tsaye. shi kuwa aljani mardis ya fara mika hannu don ya dauko. takobin sa. amma hannun sa yaki ya tarar. gashi sarkin kofa saura kadan ya zo in yake . cikin sauri aljani karsas ya harbo masa wata karamar wuka mai tsananin kaifi. ya cafe wukar. nan take ya kamu da tsananin farin ciki domin wannan dole tayi tasiri ajikin sarkin kofa. adai dai lokacin sarkin kofa ya iso ya tsaya akan aljani mardis. nan take ya futo da wata murtukekiyar sarka. sannan ya juya da kansa domin ya kira wasu dakaru. kafin ya juyo tuni aljani ya tashi zumbur yayi tsalle. yayi amfani da wukar hannun sa. kawai sai ya farke masa ciki . nan take wukar ta kamashi. sai ga tumbin sa ya zazzago waje. nan take sarkin kofa ya fadi kasa yana shure shuren mutuwa. su kuwa sauran dakarun sai suka tarwatse. suka kama gudu acikin daji ba tare da sanin in da za suje ba" shi kuwa aljani mardis sai yayi murmushi. yana duban wukar. sannan ya juya ya dubi sauran aljanun yace. muyi sauri mu shiga cikin birnin nan ba mu da lokacin tsayawa. cikin sauri dukan suka dunguma suka shiga cikin birinin kai tsaye.." **** cikin dare ne sosai sarkin maharu yana kwance acikin daki. a wannan lokaci idanun sa biyu bai yi bacci ba. Kawai sai yaji takun sawu. acikin dakin da yake. zumbur ya tashi zaune ya fara waige waige. amma bai ga komai ba. da sauri ya tashi yaje ya bude kofa. ya lelleka waje bai kalli komai ba. nan take ya tuna da mashin sihiri. cikin sauri ya koma cikin dakin. ya nufi in da ya aje wannan mashin. yana zuwa ya tarar babu komai an dauke mashi. kawai sai ya sa hannu ya fara bincika wurin. amma babu mashi. nan take hankalin yayi mugun dugunzuma. yace . shi kenan ta faru ta kare......... Comment and likes BY ABBAS WITH:- Shuraih 99% ρðšтєđ by Shuraih 99% νįά● Shuraih 99% Fðя мðяє ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1 By ABBAS With Shuraih 99% Part 17 ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ da sauri ya dauki takobin sa. yana fadin aikuwa yau garin nan babu zaman lafiya. cikin daren nan kowa hankalin sa ya tashi" "an dauke wannan mashin" ya kara fada tare da cije leben bakin sa" da sauri ya fita waje yana fadin ina masu gadin gidan nan. yana fada yana kara fada. cikin kankanin lokaci sai ga kowa ya furfuto. sun sussunkuyar da kai. ya daka musu tsawa yace. karya kuke munafukai ku futo min da wannan mashin. idan kuma ba haka zan yanke mummunan hukunci akanku. kun sanni ba ni da sassauci" dukan su dakarun suka dago da kan su afirgice. suka ce. bamu dauki wannan mashin ba. sannan kuma bamu kalli wanda ya dauka ba. babu wanda ya shigo domin ko ta ina acikin gidan nan mun tabbatar da tsaro." sarki maharu ya kwara uban ihu. kawai sai ya dakarun da sara da suka. yana fadin karya kuke yi ku futo min da wannan mashin. ba ku isa ba. kafin a jima ya karkashe wadannan dakaru" adai dai lokacin gimbiya salira ta futo tana fadin. lafiya abbana me ya faru... agigice ya ce. an sace wannan mashin sihiri. an sace" zama bai kamani ba . dole ne na tunkari gidan aljani bagazas. domin ina tunanin shi zai dauke wannan mashin" yana gama fadar haka sai suka ga an jeho wata farar takarda. basu ga Wanda ya jeho ba. cikin tsananin mamaki suka dubi junan su. salira tace bari na je na dauko.. sarki maharu yace. dakata" kawai sai ya nufi in da wannan farar takarda take. yana zuwa yasa hannun ya dauka. sai yaga ashe wasika ce ajiki. ko da ganin haka sai ya warware takardar ya fara karanta wasikar kamar haka.............. ni ne boka saljan wanda nake zaune acan dajin jahur. to kasani yanzu na kaura a dajin jahur. na canja wurin zama baza ka taba sanin in da nake ba"" ni ne na sace maka wannan mashin sihiri saboda baka isa ka mallake shi ba. yanzu kam babu kai babu samun mashin sihiri. ka rabu dashi kenan baza ka same shi. ko kadan babu sa hannun aljani bagazas awannan tabargazar da akayi . shi ma nasan za a labarta masa cewa ni na dauke wannan mashin. nasan dole shi ma zai ce zai shiga farautata. to inaso ka sani dakai da aljani bagazas ba ku isa kuje in da baza ma kusan in da nake ba. har sai na gama mallakar wannan mashin sihiri. ina fatan zaka yi hakuri ka rungumi wannan kaddarar da tazo maka ba kayi zato ba. bari na barka haka kada ka hadiyi zuciya ka mutu? ko da sarki maharu yazo nan akaranta wannan wasikar sai ya yayyaga ya watsar. sannan yace. idan na ya isa na bar shi shege nake. duk in da yake sai na nemo shi. idan yana ji da shu'umanci to nasa wasa ne? mu zuba mu gani? salira tace. me kuma ya faru daka karanta wasikar? sarkin maharu yace. kinga barni kawai yau din nan? yana gama fadar haka ya fara tattara gurayen tsafin sa yana sawa ajikin sa. ita kuma gimbiya salira sai ta tsaya tana kallon sa. sai da ya gama shirin tsaf sannan ya dubi salira yace zan sa dakaru wasu daban za suyi gadin ki. yana gama fadar haka ya fice acikin gidan gabada ya. ya hau kan dokin sa ya zabure shi da gudu" ****ita Kuma salira sai ta tsaya ta bishi da kallo tana sake sake. akan lamarin da hujurul mahas ya shiga. ya zama dole tasan yadda za tayi ta ceci rayuwar sa kafin mahaifin ta ya dawo. babbar matsalar yanzu cikin dare ne. ga kuma hanyar da za'abi a shi ga gidan azabar nan guda biyu ne. daya tana can waje. in da hujurul ya shiga. dayar kuma tana cikin gidan sarautar ta su. ta yaya za ta wuce wadannan dakaru ba tare da an tambaye ta ina zata ba. domin an basu gadin ta kada subar ta ta fita acikin wannan gida. dole za suce zasu dakatar da ita yanzu me ne abinyi. ta tsaya tana nazari. tun lokacin da tayi arba da hujurul mahas ta ji kamu da kaunar sa. taimakon sa agareta ya zama dole. za ta taimake sa ko da yace baya son ta. idan ko yace baya son ta. baza ta daina bibiyar sa. har sai ta koya masa sonta acikin zuciyar sa. ta hanyar nuna masa dabara irin tasu ta mata. haka salira ta tsaya tana sake sake daga karshe ta yanke shawarar bari gari ya waye ta kaddamar da wannan kudirin nata da tasa Comment and likes BY ABBAS WITH:- Shuraih 99% ρðšтєđ by Shuraih 99% νįά● Shuraih 99% Fðя мðяє ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1 By ABBAS With Shuraih 99% Part 18 ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ a zuciyarta" ta koma Daki kuyanginta na biye da ita" ** al'amarin su aljani mardis kuwa tun lokacin da suka shigo cikin birnin tun kafin su karasa cikin garin wani shu'umin badakare ya tsayar dasu yana labarta musu cewa ai an sace wannan mashin sihiri. a cewar su aljani mardis basu yarda ba. sai sun je sun tabbatar da gaskiyar lamarin. kawai suka ji jama'ar gari suna ta fadan an sace mashin sihiri na sarki. nan da nan zance ya cika gari. acikin daren. jin wannan maganar daga bakin jama'ar gari ya tabbatar musu da cewa gaskiya ne an sace mashin sihiri don haka basu yi kasa aguiwa ba. nan da nan suka juya da baya suka bude fukan fukan su suka tashi sama suka luluka acikin gajimare suka bace bat. don ko ta yaya sai sun nemo wanda ya sace mashin sihiri? *** kwance yake cikin halin galabaita don bai dade da farfadowa ba daga suman da yayi ba. cikin karfin hali ya tashi duk da cewa jiri yana daukar sa bai karayah ba. ahakan yaje ya dauko wata jakar sa wanda zuba maganunkan sa aciki. don faduwar da yayi ne yasa jakar ta fadi can gefe. zama ya shiga manna maganin ajikin raunin da wannan macijiya tayi masa. ya na manna maganin kamar zai rusa ihu amma dage yana cije laben bakin sa" don kada sauran muggan abubuwan dage cikin kogon su jiyo shi. yanzu yanzu sai su farmasa bai shirya ba. bayan ya gama sa maganin acikin raunikan dake jikin sa. sai yaji wata irin matsananciyar yunwa tazo masa bai yi zato ba. nan fa hankalin sa ya tashi. don saboda babu in da zai samu abinci acikin wannan kogon. shiru yayi yana nazari. can sai ya tuna akwai sauran guzurin abincin sa acikin wannan jakar. nan take ya duba jakar da ya futo da maganin. sai gashi yaga sauran guzurin nasa. nama ne gasasshe wanda yaci ya rage tun kafin ya fado hannu sarki maharu. haka yaci naman sosai har rage da yake nama yana da yawa. sai aje sauran don bai san me zai faru ba nan gaba ba. haka ya zauna awurin tsawo lokaci. sai gashi ya ji saukin jikin sa ba kamar dazu ba. awannan lokaci tamkar babu abinda ya same shi a gumurzun da yayi abaya. kawai sai ya mike tsaye. ya dauki takobin ya mayar da ita cikin kufenta. sannan ya dauki jakarsa ya rataya. kawai sai yaga an yi rubutu ajikin bangon kogon. kamar haka..... sai kayi bakin artabu da muggan halittun dake cikin wannan kogon guda goma kafin ka samu hanyar fita daga wannan taskar wahalar. hujurul mahas ya tsaya yana tunani.. to shi sarki maharu shi wanne irin azzalumi ne. ta yaya ma ya samar da wannan gida mai cike da munanan hadarurruka" amma babu komai. duk abinda yayi farko zai yi karshe. tunda har yana rike da wannan mashin sihiri dole sai an samu Wanda zai halaka shi. ya raba shi da mashin sihiri shi kenan tashi ta kare. hujurul ya jima atsaye yana tunani. daga karshe sai ya tunkari wannan kogo dake gaban sa. kawai sai ya shige kai tsaye. ba tare da fargabar komai ba. yana shiga yaji an rufe kogon ruf. babu ta in da zai bi ya fita. waigowa yayi ya duba kofar kogon sai yaga ai arufe take. to waye ya rufe bayan babu kofa. kuma shi ne kadai acikin kogon. tow. ya fada acikin zuciyar sa. kawai sai juya ya cigaba da tafiya. yana taka kwarangwal din mutane. wanda sun dade

Chapter 3 of 4