Tashi Zaune
Wallahi Kowa ya Tada Kansa Nimafa Tun Dazun Nake son Tashi Kareema ce ke Wannan Zancen cikin Muryar Rashin Lafiya Baki Suka Hada Gurin Kiran
Momy Kizo Ki Taimaka
Muna Mutashi Munkasa Tashi Cikin Wahalalliyar Murya Anty Amarya Tafara Magana Tana cewa Dallah Ku Rufe Mani Baki Dan Ubanku Bayan Kun Some Kun Barni Anata Gana Mani Azaba Harda Tsallen Kwado
Wani Irin Tashi Zaune Sukayi Suka Kwararo Ido Awaje Tsallen kwado Momy. Tace Zanyi Maku Karyane
Aikuwa Suka Bushe mata Da Dariya Hhhhhhh momy Wallahi Naso Idona biyu Hhhhhh
Ke Saudat Inga fa Momy Harda Zawo Tayi hhhhhh Haba kareema Gaske Nake Jin Warin Dunge Duk Yacika Dakin Hhhhhh
Ai Anty Amarya Jin Take Kamar Ta Tashi Ta Make Su Amman Babu Hali
Sukuwa Tashi Sukayi Kowace Tanufi Hayar Fita Anty Amarya Tace Yanzun Kuna Nufin Bazaku Taimaka Mani ba Ko Zawon Nan Kudan Wanke Mani
Ke Saudat Dake Akefa Inji waye Kareema Dake Take Nikam Badani Take Ba
Wai Momy Bakece Kikace Ke Jaruma Bace Gashi Ambarki Kwance
Ai gwara ma kija Ciki Kije Ki Wanke Yafi Maki Ai ke Kika Jamuna Kuma Kika Jawa Kanji Ai Duk Tsuntsun da Yaja Ruwa Shi Ruwa Kan doka Dan Haka Kowa Yayi Ta kansa
Kuka Anty Amarya Tafashe da Shi Haka Taja Jiki da Jan Ciki
(Wal,Iyazu Billah Allah Karamu da Irin Haihuwar Wannan Yaran Ya Allah Kabamu "yaya na kwarai Masu Tausayin mu)
Haka Su Anty Amarya Akasha Jinya Ta Kwana
Kwanaki Shidda Duk Wannan Abun da Faru Basu Yarda Sun Baro Sashen Suba Koda Yaushe Suna Sashen Su Idan Shakiyan cin Yayan Yatashi Zasu Zauna ne Su Tariyo Abunda Yafaru Sukafa Dariya Musamman Idan Suka Kalli Bakin Anty Amarya
Duk da Ayaune Zata Asibiti Asanyo Mata Hakorin Roba
Duk Shirin Su Akan Kai Rufaida A Gobe Yana Nan Kuma Sun Gama Shirya Komai
Ita kuwa Rufaida Tana Zaune A Gurin Mame ne Kuma Ridwan Baya Nan Tun Ranar da Ramlat Ta Koma Shima Yayi Tafiya Kuma Yana Nan Yana Tunanin Ina Yasan Mai Kamar Rufaida
Abba kuwa Har Yau Bai Hadu da Rufaida ba koda Yaushe Sai dai Suyi Hannun Riga
Ayau ne Su Anty Amarya Suka Shiya Zubawa Rufaida Magani A Abinci
Kuma Yaune Tafiyar Kuma Gobene Auren Saudat Wanda Suke Kidan Su da Rawar Su
Sun Anshi Kudi Gurin Alhaji Muntari kosu Kansu Basu San Adadin suba Gashi Alhaji Muntari Ya Hana Ayi Duk Wani Hidima Nabikin Auren Kawai Yake so A Daura Ko Yan biki Yace Kada Atara
Kuma Sunyar da saboda Su Lashe Money ne
Kareema ce Zaune Sashen Mame Ta Kasa Ta Tsare Husaina Kuwa Fira Tayiwa Rufaida Duk Wani Motsin Kareema A Idon Rufaida ne Rufaida ce Race Kareema Dan Allah Idan Kunada Sobo Irin Wanda Kuke Hadawa Inaso Kinji
Ai Kuwa Kareema Baki Na Rawa Tace Eh Akwai Ma Kuwa Bari Nakawo Maki Tashi Tayi Tana Sauri Kamar Zata Kife Murmushin Gefen Baki Rufaida Tayi Da Sauri
Husaina Tace Anty Rufaida Dan Allah Kada Kisha Na Rokeki Him Husaina ke Nan Kizuba Ido Kiyi Kallo Nasan Mi Nakeyi Har Zata Kara Magana Mame Tace
Ya,isa Haka Nan Kada kidame ta Ai Kinji Abunda Tace ko shuru Tayi Tazama Wata Kalar Tausayi Rufaida Tace Kiyi Hakuri Babu Abunda Zai Faru Sai Alkhairi kinji Saki Ranki Yau Ranar suce Amman gobe Kuma Dariya Tayi Kawai Sai Aka Canza fira
Kareema Kuwa Da ihu Ta Isa Gurin Anty Amarya Ta Labarta ma Hhhhhh Manya Zaki Sha Sobo Maza Dauko Azu Maganin Jiki Na Rawa Suka Zuba Magani Harda Wanke Bayan Robar Dan Kar Agane
Yi maza Ki Kai Mata Ai Da Gudu Ta Kaiwa Rufaida Amsa Rufaida Tayi Ta Bude Agaban Kareema Tashanye Ta Ajiye Robar Kareema Saboda Murna Da Gudu Ta Fita Sai Gurin Anty Amarya Aikuwa Suka Kama Rawa Harda guda
Rufaida kuwa Dariya Tayi Mami ce Tace Rufaida kin Tabbar Babu Wata Matsala Cewa Tayi Eh Mame kwantar Da Hankalin Ki
Kar Nake Ganin Su Iska Na wahaladda Mai Mayan kara.......
Comments And Share
Daga Alkhalamin โ๐ป
Yar mutan Gusau
4/19/20, 7:52 PM - +234 706 361 7906: ยฎ๐
*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..๐๐*
_{ฦungiya Domin, wayar da ฦan mata Farin jini writer's domin ci gaban Mata.}_
โ
{ F J W A}โ
๐
https://www.facebook.com/Farin-jini-writers-association-108359057471117/
๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ
๐๐ปโโ BANI CE BA ๐๐ปโโ
๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ
(Aljana ce)
By
Hassy soja
Kai Amman na jidadi sosai wlh ina godiya sosai masoyana Allah Ya Bar Zumunci Amin.
Gaskiya naji dadin comments din Ku sosai Allah Ya bar mu tare Amin.
Bismillahi Rahamanin Rahim DA sunan Allah mai Rahama mai Jin'kai
Sadaukarwa Ga Mahaifina Allah Ya Jikan sa yayi masa Rahama Amin.
Page 66----70
----------------------------------------
Anty Amarya CE Ita da yayan ta Suketa Kulle Kullen Tafiya Gurin Boka Dan Tukunya domain Yaune Tafiyar
Saboda Harda Alhaji Muntari Akeso A Hada Shikuwa Ambassador Korar Kare Akeson Ayi Masa Idan Rufaida Ta Kwashe Masu Duk Wata Kadara Tashi Takardune Makullan Motoci Makullan Gidage Dai Dai da Account Nashi Za,a Dauke ATM Din Shi Duk Wata Takar dar Mallakar Gida Ko wani Company Kai Harma da Takardun Banki Baki Daya da Takardun Karatun Sa
Hhhhhhhh Sai Naga Bayan Wannan Iyalan Wannan Alkawari ne
Ni Kaltume Said Naga Bayan Ku Hhhh
Rufaida CE Zaune Cikin Daki Ita Daya Sai Faman Dariya take Ita Daya
Mame CE Tayi Sallama Ta Shigo Rufaida Lafiyar ki Kuwa Anya Kina Ganin Babu Damuwa Nifa Naganki Yau Kamar Ranar Da Aka Kawo ki
Murmushi Rufaida Tayi Tazo Tariko Hannun Mame Ta Zaunar da Ita Tace Mame na Kiyar da Dani Wallahi Babu Abunda Zai Faru Sai Alkhairi Inaji Ajiki na Komai Yakusa Zuwa Karshe
Sai Dai Kash Abba Zaiyi Wata Yar Rashin Lafiya Kuma Sannan Yau Akwai Baki Agidan Nan Kuma Bakin Alkhairi
Tsorata Mame Tayi Takwararo Ido Waje Tace Rufaida A,i na Kika San Wannan Labarin Nifa Yau Mamaki Kike Bani
Murmushi Rufaida Tayi Tace Mame Zanfada Maki Wani Abu Amman Sai In Kinyi Alkawarin Taimaka Mani Duk da Nasan Ko Bance Alkwari ba Zakiyi
Mame Son Nake Yanzun Zanje Falo Zan dinga Shamaku Kamshi Zan Dinga Wani Abu Narashin Kyautawa Amman Ina son kidin ga Tambayata Miyasame ni Kiyi Abun Wanda Kowa Zai Yarda Na Chanza Da Gasken
Mame nasan Zaki So Jin Ba,asi Amman Kada Kidamu Da Sannu Zan Warware Maki Koma
Mame kinyar da Haba Rufaida Dan Wannan Ai Bakomai Bane Amman Ga Dukkan Alamu Sun Nuns Cewa Wannan Ba Ai Nahin Rufaida Ta Bace
Bazan So Afada Mani Sirrin Dake Boye ba Bisa Ga Tilas tawa taba Amman Zan Jira Lokaci Kamar Yanda Ake Bukata
Murmushi Rufaida Tayi Tace Mame ke Nan Wannan Halayar Taki Suke Kara Mani Ganin Girma da Darajar ki
Allah yakara Kareki Da Kariyar Sa Keda Ahlinki Yanzun Dai Lokaci Na Wucewa Kiyi Saurin Tarbar Yaronki Kuma Yau Insha Allah Za,ayi Komai
Am Mame Wannan Auren Da Aka So Yiwa Ramlat Tofa Icce Ya Juye da Mujiya
Bangane ba
Nasani Baki Gane ba Amman Yanzun Haka An Daurawa Saudat Aure Wanda Aka Dawo Dashi Yanzun Bada Dadewa ba Amman Kuwa Sun Rifta Domin Kuwa Kwadayi Mabudin Wahala
Naso Hadawa da Ita Saudat Din Amman Nabarta Yanzun Duniya ce Zata Koya Mata Hankali Komai Yafaru da Ita To Kwadayin tane Yaja Mata
Ramlat Shigo Mana Kin Tsaya Abakin Kofa Nasan Kinji Komai Kuma Nasan Zaki Yarda Tunda Kinga Yan Daurin Aure ko
Mame data Maida Idonta Akan Kofa Taga Inda Ramlat Zata Shigo Aikuwa Taji Anbude Kofa An Azo Kafa Kara Bude Ido Tayi Ganin Wanda Yabude Kofar Yashigo
Mikewa Tsaye Mame Tayi Tace Ramlat Miyaka woki Gida A wannan Lokacin Duka Duka Yaushe ne Kika Koma Wato Mugunyar Dabi,a Zaki Koyawa Kanki ko Tazare Ido Tana Makawa Ramlat Harara
Hade Hannuwa Ramlat Tayi Tace Mame Kiyi Hakuri Wallahi Ba Haka Bane Tarema Da Kayana Nake Yadawo Danine Gida Haihuwa
Saboda Tafiya ce A Gabansu Momy Ma Tawuce Ita da Dady Kin San Har kokin yan siyasa Dan ma Naga Abba Kamar son Yake Ya Ajiye Ya Huta
To Naji Suda Sarkin Labari Ki karasa Shigowa
Koda Ramlat Tashigo Cewa Kawai Tayi Allah Yabamu Nasara Anty na Koma Ince Mamana Dan Nariga da Nasan Komai
OK Ku Fita Ramlat Gani Nan Fitowa Da Sannu Zaku San Komai Da Yardar Allah
Fita Sukayi Ita Kuwa Rufaida Tafara Shirinta
.
Amman momy Naji Dadin Wannan Auren Da Akayisa Ayau Gashi Zakuyi Tafiya Badani ba Koda Yake Shine fa Zai Zo Daukata kin San Yace Bai Son Gayyar Nan Shiyasa Aka Dawo Da Auren Yau
Yanzun Shike Nan Duk Wata Wahala Takare Mani Yanzun Kune Aciki Amman Idan Aka Kwaso Dukiya Kusan dani Dan Bazan Yarda Ayi Mani Rowaba Idan Kuwa Kukayi Kuskure Duk Sai Natona Maku Asiri Ay he Dan nasan ki Momy Gurin Son Kudi Ko Danki Zaki Iya Kashewa Balle muda muke Mata Ba Sonmu Kike ba Namiji Kikaso Sai Gashi Kin Haifi Mata Biyu
Ke dalla yiwa Mutane Shuru Wawuyi Kai Ai Tun Yanzun Kike Batun Tona Muna Asiri Tashi Kitafi Mijinki Najira Dan Nagama Yimaki Mai Wahalar Daura Auren Kinga Yanda Muka Sanya Akayi Auren Kinga Mun Wuce A Ganmu Ace Za,a Kushe Auren Saboda Bakin Ciki Kuma Ina Fada Maki Bazama Zakiyi Araina kiba Kiduba Yanda Nake Mulki Dan Haka Yanzun Aiki Nakine
Kuma Ba Ragi Babu Ragisa Shin Waima Matansa Nawa Yayan sa Nawa
Oho Nikam Babu Ruwana Naira Kawai Nasani
Hahhhh Saudat Amarya Aikam Muna Zuwa Gurin Boka Dan Tukunya Zan Sa Amallake Maki Alhaji Muntari kuwa Za,ayi Aiki Da Cikawa Muda Talauci Sai,dai Muji Ana Fada In Munzo Yiwa Abba Jaje hhhhh
Su Abba Za,a Dan Dana Rayuwar Talauci
Him Ai Bazaiji Daci Kwarai ba Kin San Baban sa Shima Almajiri
Saboda Warin su Nakeji Na Talauci Shiyasa Na Hana Kuna taccen Tsohon Rabar sa Ni Yanzun ma Ko Amace Ko Araye Oho Masa
Kai Amman momy Kinyi Taimako Da Mun Tashi Cikin Dattin Talauci Hhhhh Suka Tabe Harda Anty Amarya
Kirrrrr Kiran Wayar Saudat Yashigo Hello Alajina Ka Iso ne OK Gani Nan Zuwa
Bye mom bye sis Sai munyi Waya Naji Duk Abunda Yake Tafiya juyawa Tayi Taja Trolley dinta Ta Tafi Abunta Babu Rakiya
To Amarya Munce Aje Gidan Alaji Lafiya
Rufaida Tafito Ansha Kwalliya Har Angaji Fuskar nan Kamar Me Sai Walkiya Take
Tafe Take Tana Ran gwada Kamar Zata Karye Shigowar Anty Amarya Ke Nan Itada Kareema
Suma Su Mame Ana Zaune Su Ramlat Hasan Husaina Ridwan Wanda Dawo warsa ce Ake Wannan Shagalin Domin Husaina da Kanta Tashiga Kichin Ta Hada Masa Abinci Da Kanta
Anty Amarya ce keyiwa Su Mame Habaici Ita Ai Maisa,Ace Tunda Gashi Yarta Ta Auri Miji Wanda Yadace Da Su
Amman Mame Haka Zata Dauwa ma Kullum Cikin Kukan Talauci Yarta Kullum Tana Gida gurin Cin Arziki
Amman Zanyi Maganin kune Fitowar Rufaida ne Ido Yako Kanta
Wata Mahau kaciyar Dariya Ce Su Anty Amarya keyi Itada Kareema Harda Rike Ciki
Kallon Rufaida Suka Karayi Suna Tafa Hannu
Ridwan Juyawa yayi Yaga Abunda Akeyiwa Dariya Kasa Hadiye Dariyar sa Yayi Shima Ya Tayasu Dan yarinyar Bata Bashi Haushi Saima Burgewa
Husaina Wani Haushi ne Yakamata Tafara Gunguni Wai Danmi Za,ayi Mata Dariya Ai Gyara Mata Za,ayi
Ramlat ce Tace Sannu Rufaida Amarya Wannan Kwalliya Haka
Ina Zuwa Baki Rufaida Ta Murguda Tace Miye Ruwanki Kikeyi Mani Shisshigi Ramlat Tace ni Tana Mai nuna Kanta Rufaida Tace Wanda Ya Tsargu Shuru Ramlat Tayi
Ita kuwa Husaina Tace Amarya Miye Haka kinga Kanki Kuwa
Fuskar ki Tayi Furum Furum da powder Ja Ai Powder Tayi Yawa Wannan Jam bakin Sai Kace Duka Kika Shafe shi Kwalli Kuwa Ba,a Magana Riga Daban Zani Daban Dan Kwali Daban Ga Wata Uwar Damara Da Kikaci Kamar Mai Zuwa Dambe
Harara Rufaida Ta Watsawa Husaina Tace Aikin Ke Nan Sanya Ido To Nafi Karfin Ku eehe
Mame Tace Rufaida Kina Hankalin ki Kuwa Kike Sa,insa da Yan Uwanki
Haba dai Suwaye Yan Uwana Nikam Banda Yan uwa Anan Ta Nuna Su Ramlat Harda Mame
Ridwan dai Baice Komai ba Amman Yanzun Kam Mamaki Yake Anya Yarinyar Nan Ita Daya Take
Kai Gama Mamaki ba Yaga Anty Amarya Tacewa Rufaida Ke Yar kauye Zo Nan Sum sum Rufaida Taje Gurinta Harda Dukawa Akasa
Wata Irin Gudace Anty Amarya Ta Ran gwada Ayurrriiiiiii Ayuriiiiiiriiiiyuuriii
Him Duk Tusa Kanku Kunga Yanda Abu Ya Kasance hehehe
Tashi Muje Munyi Unguwa Sai Mundawo Maki Da Tsaraba Muje Gaba Sukayi Rufaida Na Biye Dasu Sai Faking Space Suna Zuwa Rufaida Tace Masu Fitsari Take Ji Bari Nako Nakara Jan Kunnen su Dan Nabar Kayana
Tafawa Anty Amarya Tayi Ita da Kareema Kamar Wasu Sa,anni Cewa Anty Amarya Tayi Minti Biyu
Da Dan gudu Rufaida Takoma Falo Ta Isko Mame Tayi Tagumi Dagudu Ta Karasa Gurin Mame Ta Duko Gurin Kunnenta Tayi Mata Rada
Mame Jinjina Kai Tayi Kamar Wata Kadan Garwa
Komawa Tayi Gurin Ramlat Itama Tayi Mata
Da Dan gudu Ta juya Har Takai Bakin Kofa Tajuyo Tace Sauran Kuma Kuje Kutaba Mani Kaya Dan Bani Nan Mutum Yaga Aikin Dan Kauye da cikawa
Anty Amarya dake Labe Wata Dariya Tayi Tace Yarinya kin Shigo Hannu
Rufaida Kuwa Cewa Tayi Him Zan Gane Waye Ahannu Ku Koni
Bayan Fitar Rufaida me Ridwan Yayi Murmushi Yace Him Mame Da Yayanta Abun Nan Naku Shirine
Amman Zamu Sanine Intayi Wari
Dariya Sukayi Su Duka
Matsawa Tayi Suka Bude Mata Mota Da Kansu Suka Rufe Anty Amarya Tabawa Mota Wuta
To Zuwa Anjima Insha Allah Za mu Hadu Daku Gurin Boka Dan Tukunya Dan Jin Yazata kaya
Comments And Share
Hassy Soja
Yar Mutan Gusau ce
4/19/20, 7:52 PM - +234 706 361 7906: ๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ
๐๐ปโโ BANI CE BA ๐๐ปโโ
๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ
(Aljana ce)
BY
Hassy soja
ยฎ๐
*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..๐๐*
_{ฦungiya Domin, wayar da ฦan mata Farin jini writer's domin ci gaban Mata.}_
โ
{ F J W A}โ
๐
https://www.facebook.com/Farin-jini-writers-association-108359057471117/
Ina godiya sosai Allah Ya bar mu tare Amin
A gaskiya na jidadi sosai Allah Ya bar zumunci
Wow masha Allah Ina yinku over ๐๐๐๐๐
Gaskiya na jidadi sosai Comments din Ku sosai Allah Ya bar zumunci Amin.
Bismillahi Rahamanin Rahim DA sunan Allah mai Rahama mai Jin'kai
Sadaukarwa Ga Mahaifin Allah Ya Jikan sa yayi masa Rahama Amin.
Page 71---75
*************************
Tafiya Su Rufaida Keyi Saboda Dadin Mota Harda Gyen gyadi Tafara
Su Anty Amarya Kuwa Cikin Nishadi Suke Jin Suke Sunfi Kowa Sa,a A duniya Suna Cikin Tafiya Motar Tayi Tsaye Tsaf Akan Titi Ita Batayi Gaba ba Kuma Batayi Baya ba
Mamaki ne Yakama Anty Amarya da Kareema Sufa Sun San Lafiya Motar Take
Bude Gaban Motar Kareema Tayi Tace Momy Motar Nan Banga Wata Matsala Gareta ba Na dauka Ruwane Babu Ashe Ba Haka Bane Bari Dai Akara Kin San Wannan Motar Zata Bata Muna Time mssssss
Anty Amarya ce Taja Wani Dogon Tsaki Jin Take Kamar Tafashe Da Kuka Dan Bakaramin Haushi Abun Yabata ba
Sun Kusan Awa Biyu Babu Motar data Gifta Kuma Sunyi Sunyi Motar Ta Tashi Amman Takiya
Komawa Cikin Motar Sukayi Sai da Suka Zauna Sannan Rufaida Ta Falka Tace Anty Amarya Yakamata Ku Kara Tada Motar Agani Ko Allah Zai sa Motar Tatashi
Shuru Sukayi Kamar Dai Suyi Gardama da Ita ko Kuma Suci Mata Mutumci Amman Tunowa Da Maganar Boka Dan Tukumya Dayace Masu Kada Suyarda Sukawo Masa Rufaida Ba,ahayyacin taba Ko Kuma Bada Son Rantaba Yasanya Anty Amarya Kame Bakinta Tayi Shuru
Kareema Har zata Fara Yiwa Rufaida Masifa Anty Amarya Tace Kada Kifara Kyaleta Gwada Ki Gani Kila Motar Tatashi Amman Ai Munfita Bukatar Hakan Ko
Shuru Kareema Tayi Sai Cika Take Tana Batsewa I wa Balam Balam Key din Ta sanya Ta Tayarda Motar Cikin Ikon Allah Tayarwa Biyu Cikin Ta ukkun Motar Ta Tashi
Murna Gurin Anty Amarya da Kareema Kamar mi
Rufaida Kuwa Murmushi Tayi Ta kara Gyara Zamanta Haka Suka Cigaba Da Tafiya
Koda Suka Isa Inda Anty Amarya keyin parking Mamakine Yakama Kareema Har Sai da Takasa Hakuri Tace Momy Kuma Mutum ne Ke Rayuwa A Wannan Gurin
Tsawa Anty Amarya Tayi Mata Tace Kiyi Mani Shuru Mana Kina Son Musamu Matsala ne Iye
Shuru Kareema Tayi Rufaida Kuwa Yi Tayi Kamar bata San Akan Miye Suke Zance ba
Ganin Itace ne yasa Rufaida Fara Juya Tana Murna Harda Tsalle Sai Dariya take Tana Nuna Itace Tana Fadin Sunan su
Anty Amarya Kuwa da Kareema Sai Kallonta Suke Dafari Sun Danji Tsoro Amman Daga Baya Suka Gane Kauyan Cinne Tatashi Sai A Lokacin Ne Suka Kara Yarda da Dan kauye Duk Inda Yake Baya Boyuwa
Anty Amarya Ce Tace Ke Natsu Ban Son Hauka Gurin Nan Akwai Katon Kare Karama Kinatsu
Ai Sai Rufaida Ta Daina Wannan Abun Suka Dauki Hanya Sunyi Tafiya Sosai Cikin Duhun Itace Inda Kareema Saboda Tsabar Tsorata Rungume Anty Amarya Tayi Kafarta Kafar Anty Amarya
Anty Amarya Kuwa Abun da Yaso Bata Mamaki Bai Wuce Rashin Jin koke koken Abubuwan Da Tasaba Jiba
To Amman Ai Kuma Ba,Abun Mamaki bane Ganin Yau Sunada Yawa Harsu Ukku Sannan Kuma Dan Tukunya Yasan da Zuwan su
Isar Su Kusada Bukkar Boka Dan Tukunya kenan Anty Amarya Tabude Murya Iya Karfinta Ta farayiwa Boka Dan Tukunya kirari
Wanda Sai da Ta firgita Yar ta Kareema domin Kuwa Kareema Tunda Take Bata Tabajin Anty Amarya da Maka mancin Wannan muryar ba
Itafa Batama Dauka Mutum ne Me Irin Wannan Maganar ba Amman Juyawarta Sai Taga Anty Amarya Tajuya Da Baya baya Tana Tafiya Tana Wannan Ihun
Wani Aikin Sai Kai Boka Dan Tukunya Wani Abun Mamaki Sai Gwani Na Gwanaye Wanda Babu Wanda Ya Isa Ya Gansa Ko Yazo Gurinsa Sai Ya Gawurta
Sai kai Bokan da Babu Irin sa Aduniya Sai kai Boka Dan Tukunya Wanda Bai Maida Kisan Kai bakin Komai ba Wanda Ya Gawurta Anbuga An Barka Ganin ka Ma Sai Batacce Wanda Baya Kallon Kowa Sai Batacce Sai Kai Boka Dan Tukunya Wanda Yamaida Sarki Ba Ko Bawan Kaskan tace Wanda Yake Maida Mai kudi Talaka Acikin Kwananki Kalilan
Gani Nazo Nazo da Duk Abunda Ka Bukata Wasa da Bukatar Ka Tamkar Wasa da Rayuwane
Hakika Yau Aiki Zaiyi Kyau Kuma Ga Yarinya Kamar Yanda Kake so Idan Zatayi Kwanaki Duk Babu Wanda Ya Isa Ya Hana
Hhhhhhhh Wata Irin Mahauka ciyar Dariya Boka Dan Tukunya yakeyi Duk Ilahirin Wurin Amsa Dariyar Yake
Hhhhhhh Gaskiya ne Kin Cika Umarni na Baki Daya Dan Haka Matso Gani Nan Bayan Iccen Tsamiya Ina Ganawa da Sarkin Aljannu na duniya
Sanan Kisa Abokan Tafiyar ki Tafiya da Baya baya Jikin Anty Amarya Na Kyarma Tace Angama
Juyawa Tayi Tace Ku Maza Kuyi Yanda Akace Kareema ce Tace momy Rufe Mata Baki Anty Amarya Tayi Tajuya Kareema Taja Hannun ta Suka Fara Tafiya
Ganin Rufaida A Tsaye Bata ko Motsaba Yasa Anty Amarya Katsa Mata Tsawa Tace Mikike Jirane Yar Kauye
Har Yanzun Dai Rufaida Bata Motsaba A Hasale Anty Amarya Taci Gaba Da Jan Hannun Kareema Har Suka Isa Inda Boka Dan Tukunya Yake
Ai Dan Tukunya Wata Mahauka ciyar Dariya Yakece Da Ita Boka Dan Tukunya yace Saura Amaryar
Anty Amarya Tace Angama Har Zata Juya Taji Boka Dan Tukunya yace Kibarta Takawo Kanta Dan Tun Yanzun Nafara Aiki Akanta
Kamar daga Sama Kuwa Sai ga Rufaida A gaban su
Bushewa Da Dariya Boka yayi Yace Kinga Nasa Aljannu Sun Kawota
Anty Amarya Dariya Tayi Tace Boka Dan Tukunya Indai Kaine Kawuce Nan
Zauna Anan Gurin cewar Boka Zama Kuwa Rufaida Tayi
Zamta Keda Wuya Wata Iron Uwar Guguwa Ta Tashi Bukkar Boka Dan Tukunya Wata Irin Kaara Sukaji Anyi Mai Figitar wa
Take Boka Dan Tukunya Ya Mike Tsaye Cikin Rawar Jiki Da Mummunan Tashin Hankali
Dole Su Anty Amarya da Kareema Suma Suka Mike Tsaye
Amman Banda Rufaida A Yanda Ta Zauna Haka Take Kanta Akasa Bata ko Motsaba
Wa Irin Girgiza Bukkar Dan Tukunya keyi Taruge Baki Daya Zuwa Can Kuma Wuta Takama Bukkar Baki Daya Wutar Ci Takeyi Sai da Komai Ya Kone Tukuna Boka Yadora Hannu Akai Yana Ihu
Anty Amarya Ganin Boka Dan Tukunya Na Ihu Sai Ta Rude Ta Rike Kareema Ta Kama Hannun ta Da Suka Bar Rufaida Zaune Da Niyar Subarta Agurin
Amman Kuma me Anty Amarya Ta Kada Daga Kafarta Dan jin Take Kamar babu Kafa Ajikin ta
Kareema Jin Anty Amarya Ta Kasa Gudu Yasata Cewa Momy Mikika Tsaya Yine Kizo Mu Gudu ko kafin Kareema Ta Rufe Baki Kawai
Sauran Mayan Aikin Boka Dan Tukunya Harda Tukunyar Taxa Dake Gefen Su Suka Kama da Wuta bal bal bal
Boka Dan Tukunya Ne Ya Rude Yafara Sabbatu
Shike Nan Tukunyar Ta Kone Ta Mutu Wayyo Karyata Ta Kare Dama Da Tukunyar Nake Takama
Bakin Anty Amarya Na Rawa Tace Boka Sakar Mani Kafa Nayi Gida Nafa Aikin
Boka Yace Ke Rufe mani bakin ki Wayasa Nima koma Kinda Sa Hannu Gurin Karyani
Rufaida CE Ta Wani Irin Bushewa Da Dariya Dariya take Ba Kakkauta wa
Hhhhhhhhhhhhhhh
Hhhhhhhhhhhhhhh
Hhhhhhhhhhhhhhh
Kurufe Mani Baki Banzaye Azzalumai Matsafa Mushrikai
Hhhhhhhhhhhh hhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh
Kun Dauka Duniyar Takuce Kun Dauka Ku Me Bawa Kanku Nasara To Kusani Babu Abunda Yake Samuwar Bawa Sai da Iznin Allah Sannan Kuma Kusani
Tunda Nashigo Rayuwar Ku Kunzama Tarihi Kuma Kusani Baku Kadai Bane Agurin Akwai
Tanuna Wani Gefe Daya Wata Irin Zabura Sukayi Su Duka Suna Nuni Da Hannun su
Kune Waye Yakawo Ku Gurin Nan Waye Ya Nuna Maku Inda Muke
Alhaji Daman Kunsan Gurin Nan ne Kai Inah Bazai Yuyuba Kuna Nufin Gaba Dayan ku Kunsan Inda Nake Zuwa
Wani Banzan Kallo Abba Yayi Mata Mame Kuwa Murmushi Tayi Tace Ai Duk Abunda Kukeyi Aboye Kusani Allah Baya Bacci Kuma Baya gengadi Kuma Duk Abunda kukeyi Wata Rana Zai Bayyana Kamar Wannan Ranar
Ridwan ne Yace Kaico Da Halinku Tunda Kun kasa Yarda Da kaddarar Allah Har Sai Kunyi Shirka
Murmushi Ramlat Tayi Tace Ku Atunanin Ku Rufaida Saboda Bukatar Ku Ta Yarda Tabi Ku To Bari Nasanar Daku Abunda Baku Saniba Yanzun
Duk Wannan Abun Aikin Rufaida ne Duk Abunda Kuke Kullawa Tasani Kuma Ko Maganin da Zaku Bata A Abun Sha Tasani Shiyasa Ta Aika Kareema Ta Amso Mata Kuma Ta Shanye Agabanta Ku A Bahagon Tunanin Ku Asirinku Zai Kamata Shi Yasa Tayi Maki Basaja Tazo Agaban Ku Tayi Muna Rashin Kunya Wanda Daman Mun San Hakan Sannan Kuma Bayan Kun Fita Sai Ta Dawo Ta Sanar Damu Zata Tsayar da Motar
Mubiyo ta Abaya Dan Ganewa Idon mu Abunda Zai Faru Kina Fita muka Sanar da Yaya Ridwan Zamu Biku Da Baya Dan Ganin Inda Zaku Dosa To Mun biyo Bayanku Kuma Munga Inda Motar Ta Tsaya Shi Yasa muka Koma
Muka Nemi Abba Koda Abba Yazo Ce Masa Mukayi Tafiyar Gaggawa Ta Taso Kuma Harda Shi Aciki
Abba Yaso Musawa Amman Yakasa Kuma Bai Tambayi Ina Zamu ba Haka Muka zo Muka Sameku Muna Zuwa Dan Mesa Daku Motar Ku Ta Tashi Wanda Nasan Aikin Rufaida ne to kuma Munji Komai Kuma Munga Komai Dama Ance Gani Ya Kori ji
Abba Yanzun Kaga Kalar Matar ka da Yayanka Cewar Husaina wadda Me Jin Kamar Takasu Da Duka
Hasan yace Cube Ku Har Dai Kai Katon Banza Anty Amarya Kunji Kunya Wallahi
Abba darker Ya Bude Baki Yace In Alhaji Kabiru Ambassador Nasake ki Kursum Saki Ukku Allah Ya,isa Tsaka nina Dake
Wata Irin Ihu Tayi Aguje Tazo Gurin Rufaida Daniyar Shakure ta Amman Kafin Ta Kawo Anyi Sama Da Ita Ansakota NASA Jikake Tim Ta Rafki kasa
Kareema Kuwa Cewa Take Na Tsaneki Rufaida da Kafin Ta Ci Gaba Bakinta Ya rufe Ruf
Rufaida cewa Tayi Kuja Abba Kutafi Yanzun Zan fito Hannu Ta daga Ta Nuna Gurin su Anty Amarya da Boka da Kareema Take Gurin Yayi Wani Iron Duhu
Suyawa Rufaida Tayi Tace Sai Mun Hadu Daku
Ta wuce Tasamu Ridwan Rike da Abba suka Saka shi mota Sukayi Gida Har Rufaida
Takuce
Hassy Soja
Yar mutant Gusau
4/19/20, 7:52 PM - +234 706 361 7906: ๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ
๐๐ปโโ BANI CE BA ๐๐ปโโ
๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ๐ฒ
(Aljana ce)
By
Hassy Soja
ยฎ๐
*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..๐๐*
_{ฦungiya Domin, wayar da ฦan mata Farin jini writer's domin ci gaban Mata.}_
โ
{ F J W A}โ
๐
https://www.facebook.com/Farin-jini-writers-association-108359057471117/
Ina Alfahari da Ku Mosoya Na A yanda Kuke Nuna Mani Kauna
A gaskiya Naji dadi Sosai Allah Ya bar Zumunci Amin
SADAU KARWA ZUWA GA MAHAIFINA ALLAH YA JIKANSA DA RAHMA ALLAH YASA ALJANNAH CE MAKO MARSA SHIDA AL,UMMAR