Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*_BAN SAKETA BA!!_*






*_NA Bilyn Abdul_*





_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*

https://mrsbilkisa.blogspot.com



*_wanan page nakune Basma er Lele & Zarah bukar, ALLAH yak'ara basira da hikima, bilyn Abdul namuku fatan alkairi arayuwa_*
*```(Zuma saidai wuta)*```
Acigaba da gashi zarah🤠.



*(page 39 & 40)*
Asubar fari zakara yabama su aunty sa'a.
Ba k'aramar tafiya sukayiba har dawaki, adawakinma wani k'auye suka shiga cikin ruk'uk'in daji.
Aunty tatsaya tana maida numfashi saboda gajiya, Dan yanzu dak'afa suke da6awa saboda hanyar batada k'yau, babu kuma d'an mashind'in dazai yarda yashiga dajin, itama zuby bazata yardaba.
Kai Zuby wai har yau bamuzoba ne?.
'Yar dariya zuby tayi, tareda dafa kafad'ar aunty, haba sadiya biyan buk'ata aii yafi dogon buri, ki daure aii munkusa, duk Wanda ya iya jure zama da mak'iyi, aii zaijure zuwan ranar d'aukar fansa kuwa.
Hakane aunty tafad'a tana murmushin mugunta.
Tafiya suka cigaba dayi, itadai Raihan binsu kawai takeyi cikeda fargaba da fad'uwar gaban.
Zuby ta ce, "banga laifinkuba dominku 'yan hutune, mazanku sun tsaya muku daga mota sai gida, muko ALLAH natuba yaku bayi wake ta tamu, idan tafiya zata tashi daga nan har birnin lantsandan zamu iya kai kammu da k'afa.
Kafin aunty ta ce, " wani abu sun iso wajen wani k'aton dutsi, zuby ta kallesu nanfa zamu hau.
Raihan ta gwalalo ido cike da mamaki tana kallon zuby, aunty zuby yanzu nan mutum ke zaune akan dutennan?.
Kwaraikuwa zuby tafad'a.
Aunty dai batace komaiba, saidai tana mamakin zuby sosai, tasan ta sanadinta zuby tasan kano, hartai aure aciki, amma yanzu tafita sanin birnin kano da kewaye, Inda tasani ita ko azance bata saniba.
Maganar Raihan ta katse tunanin aunty, aunty zuby to yanzu ta INA zamu hau?.
Wata matattakala zuby ta nuna musu, wadda babu shakka kayi kuskuren takawa tuni zakayo k'asa ka rugurguje visa k'ananun duwatsin wajen.
Ajiyar zuciya suka sauke suduka, cike da fargaba suka fara tattaki ga matakalar, saida suka kai k'arshe cike da jindad'i, abisa tsautsayi k'afar Raihan ta goce, takwala wata k'ara Dan tsorata, jitayi anyi sama da ita akan dutsen, sassanyar ajiyar zuciya ta sauke yayinda taga ta tsira, saidai tana bud'e ido tashiga wata sabuwar fargaban.
Zaratan samari tagani majiya k'arfi, wad'anda da mutuwa na tsoron mutum idan tagansu guduwa zatayi.
Aunty ma binsu take d'aya bayan d'aya, sunkai adadin goma k'artan, saikuma wani wargajejen mutum fari tas azaune, Wanda bana tsammamin yasan kalma d'aya tak daga yaren Hausa.
Aunty da Raihan suka kalli zuby wadda ita hankalinta akwance take babu alamar fargaba ko tsoron atareda ita..... Mamakinsu bai k'aruba saida sukaga zuby tak'arasa wajen wargajejen mutum nan mai kamada tankin ruwa ta gurfana tamkar zata MASA sujada.
Ya sarkina dodo yataya maka.
Daya daga cikin zaratan k'artan nan ya ce, "sarki ya amsa miki jinin dodo.
Aunty da Raihan suka zaro ido, tuni jikin su yafara rawa.
Zuby ta kuma gurfanawa agaban k'aton muminnan ta ce, " ya sarki ga alk'awari na cika kamar yanda nayi, nakawo k'awata ga dodo harma da k'arin k'anwarta idan dodo yana buk'ata.
d'aya daga cikin k'artin Yakuma amsawa, dodo da sarki sun jinjina miki tareda babban yabo, kin kuma tashi daga jinin dodo kin koma baiwar dodo, daga yau kema kinzama d'aya daga cikin 'Yar kungiya.
Hhhhhhhhhhhhhhhhhhh!!!!!!!. Wargajejen k'aton nan ya tuntsure da dariya, wadda duk kanin dajin ke amsawa, dutsen dasuke kai kuwa har girgiza yakeyi.
(Na ce, hummm, dabadan dariyar da k'aton nan yayiba saika d'auka gunkine aka dasa awajen wlhy.)
Aunty da Raihan tuni sun fara sakin fitsari awando, jikake tsulululu..., wani garjejen k'aton yazo yadamk'i gashinsu, tuni jikin su yak'ara tsananta rawa, summa rasa hawayen kuka.
Sunaji suna gani aka aske musu gashi, akayi musu zindir, wanka akayi musu da ruwan jini Dana magani, sanan akabama zuby su takai cikin wani k'aton tanki......

Aunty da Raihan suka fashe da kuka, bakin aunty na rawa ta ce, "Haba zuby yanzu nan muzakiyima haka........ Hannu zuby tad'aga mata kinga dakata kunama mai haihuwar d'an sharri yimin shiru.
Rama cuta ga macucu ibadane.
Zuby nikam azatona banta6a cutar dakeba.
Wani kallon banza zuby tabi aunty dashi, saikuma ta kwashe da dariya tana zagayasu, sukuma suna binta da kallo, sady baby! Idan maye yaci yamanta uwar d'a bazata mantaba.
Tare muka tashi dake tun muna k'anana, amma ayayin dakika samu damar auren mai kud'i saika manta dani atsarin rayuwarki.
Ban 6oye mikiba tunkan aurenki nace inason k'anin mijinki isma'il, kikayimin alk'awarin kota yaya zakisa ya aureni amma daga baya sainaji shiru wai malam yaci shirwa.
Wani abun mamakima saiga labarin yazo gareni zai auri k'anwarki, haka nashiga nafita NASA mamarku ta ce, bata yarda da auren isma'il da k'anwarki ba.
Bayanan ban gajiyaba nakuma tada miki zancen inason isma'il, amma saikikayi burus da batuna.
Babu yanda zanyi dole na hak'ura na auri murtala badan INA sonsaba, na aureshi visa tursasawar babana.
Kinsani sadiya kinsan halina kokad'an banida tsoron arayuwata, kuma bana Barin bashin gaba.
Wanan yasa nafara tunanin INA zan samu kud'i Dan nawuce da ajinki.
Ina cikin wanan tunanin ranar na hau WhatsApp saiga wani group anturo ana gargad'ar kada mutane sushiga na 'yan mafiyane.
Take kaina yakawo wuta Dan Dama kud'i nake burin yi toga hanyar mai sauk'i, tuni nake gaya miki na afka group d'in nan zuciya ta adake, Ashe mutane da gsk sukeyi group d'in na 'yan mafiyane, babu wani 6ata lokaci na afka cikinsu, saidai bazaka zama cikakken d'an cikinsuba saika sadaukar da d'aya daga cikin masoyanka.
Bazan iya bada Mamana ballantana baba, ko 'ya'yana, hakama murtala dukda banason da bazan iya bada jinin saba saboda mutumin kirmine, ko kad'an bankawo araina zan kawokiba kema, Dan burina saina zama mai k'azamin kud'i sanan na nuna miki wutsiyar rak'umi tayi nesa da k'asa.
Saidai kuma labarin ya canja alokacin da'akace idan bankawo wani nawaba za'abama dodo jinina, tuni kaina yakawomin haske akanki, saidai bansan a INA zan damk'ekiba.
Kwatsam saigaku jiya kumzo gareni cikin sauk'i, Dan haka nayi matuk'ar farinciki, ayanzudai taku tak'are Dan na cika umarnin dodo da sarki, kuma nazama cikakkiyar 'Yar kungiya, zanyi kud'i na Shana.
Ta kuma kewayasu tana dariya, sady baby yau wai INA babban gidan da ake mana raini akansa, INA motar hawan da ake hura mana hanci, INA mijin da ake mana salo, duk babu, saki uku gakuma mutuwa dake jiranku.
Hhhhhhhhhhh, kin fad'a tarkona sady baby, kin fad'a tarkon zuby, Zuma ga zak'i ga harbi.
Kuka sosai aunty da Raihan sukeyi, suna rok'on zuby tayi hak'uri k'artan badasu, wlhy komai take buk'ata zasuyi mata.
Bata sauraresuba ta iza k'eyarsu cikin kwantaina da mutane dayawa ke cikin, tsirara duk jikin su wani iri babu k'yawun gani, su tsoroma suke basu, Dan haka suka raku6e waje d'aya suna rabzar kuka.
(Nace duniya makaranta, Wanda baizobama jiransa takeyi).
Kowa yagina Ramin mugunta........



****************************
Iman da Dr kam ansha soyayya, daren nan zir a angwaci suka cinyeshi, iman ta murzu, Dan Daren jiya Sabon Daren farko Yakoma musu.
Wanan karan dai babu kuka amma yasha shagwa6a da ta6arar iman, da k'yar suka tashi sukayi sallar asubar, suka sake bud'e sabon babin barci.
Sai shabiyu dawani Abu suka tashi, alokacin tuni musayeef ya tashi yay tafiyarsa 6angaren su yaya.
Imam ta tashi da k'yar, fuskar Dr ta tsurama idanu, barcinsa yake amma tamkar yana murmushi, fuskarnan fayau sai hasken angwaci yakeyi, talumshe idanu tasake bud'ewa akansa, tana k'aunar Dr harma batasan iya adadin k'aunar datake masaba, tana fata ALLAH ya sa babu wata k'addara dazata sake raba rayuwarsu anan gaba.
Ahankali tamik'e tanufi bayi danyin wanka, Dan jikinta sai ciwo yakeyi wlhy.
Ruwa mai zafi ta had'a ta gasa ko INA najikinta hartaji d'an k'arfi.
Tafito d'aure da tawul tana goge jikinta da k'arami, Dr dake kwance yatsura mata idanu jiyake tamkar ya had'iyeta saboda so, tunda yake baita6a tunanin yaso wani Abu bayan iyayensa da mama da ya'yaba bayan IMAN, yanajinta sosai azuciyarsa, fatansa ALLAH ya tsawaita rayuwarsu suci amfanin juna.
Iman dabatasan yanayiba ta k'arasa jikin madubi tayi kwalliya mai sauk'i, durowa tanufa, tad'akko wata dakakkiyar shadda zani dariga, ta d'aura zanin, tana k'ok'arin saika riga suka had'a ido da Dr da idonsa yake tsaye kam a k'irjinta ko k'yaftawa bayayi, da sauri tasaka rigar tana fad'in daddy katashi?.
Bai amsataba baikuma daina kallontaba, d'ankwalin kayan tad'auka tak'araso Inda yake tareda rankwafowa ta hura MASA iska a idonsa.
Ya lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya.
Ta ce, ''kallonfa?, aii saika karemin muni Dr.
Murmushi yayi tareda ziro k'afafunsa k'asa, yakafeta da idanunsa yana fad'in, aii kozan shekara dubu INA kallonki bazanga muninkiba.
A'a daddyn musayeef banda zigadai.
Tasowa yayi yarungumeta tabaya, yad'ora Kansa saman kafad'arta suna kallon juna tamadubi, ahankali ya CE da gsk nakeyi Ni'imatullah.
Cike da mamaki take kallonsa ta ce, "wanan sunanfa daga ina?.
Saitin kunnenta yamatsar da bakinsa ahankali yarad'a mata maganar danima banjiba masu karatu.
Ta zaro ido waje saikuma tasa hannu tarufe fuska tana fad'in nidai babu ruwana kaje kayi wankanka.
Dariya yayi yana k'ara matseta ajikinsa, nikam da ruwana harda d'an tsaki tsaki.
Dariya tayi, nidai kaje wanka Kasan musayeef zai iya shigowa d'akinnan akowane lokaci.
Da sauri yakalli gadon, o, wai yana INA?.
Hummm sai yanzu kalura baya nan?.
ALLAH nazata yana barcine.
Tab wanan yaronne zaikai sha biyu dawani Abu yana barci?, Nima tunda natashi ban ganshiba.
Musayeef sarkin wayo kenan, shiyyasa dole NASA agyara MASA d'akinsa azuba komaiba Yakoma da kwana can.
Aiigara dakayi wanan tunanin da anka, Dama INA niyar yin magana.
Dariya yayi yanufi bayi yana fad'in to an hutash sheki.

Bayan Dr yafito daga masallaci yanufi 6angaren mama Dan iman tanacan suna shan hirarsu itadai deexerh.
Deexerh nabata labarin Umar farukh, iman ta ce, " amma dee.... Miyasa bazaki bashi Dama yazo gidaba Dan asan dashi.
Wlhy aunty inajin tsoro, shima kullum nacinsa kenan, sau biyu yana kaimin ziyara amakaranta, yanzu haka yana fushi dani akan nak'i had'ashi da uncle.
Kai amma dee.... Bakida kai, ke Matan na Neman mijin aure ido rufe ke kina zillewa bayan kin samu, kobak'ya sonsane?.
Wlhy aunty INA sonsa kawai inajin tsoron kamar yanda nafad'a miki.
Tsoron kuma?, tomiye abin tsoron anan?.
Kinsandai uncle yanada sauk'in kai amma bazan iya tunkararsa da wanga batuba, shiyyasa na CE, "farukh yatsahirta harna kammala makaranta.
Cabd'i Jan, tsaya kallon ruwa kwad'o yaymiki k'afa 'yammata, yanzu idan ansamu tattali ake.
Ni kibar komaiba ahannuna zan Sanar da daddyn musayeef, shima Umar d'in kisanar dashi yashirya zuwa bayan na Sanar da Dr saiya saka MASA ranar zuwa.
Waye kuma? Dr dake shigowa yafad'a.
Atare suka kalleshi, yazauna kusada iman, dee.... Tai saurin tsungunin iman wai kada tafad'a yanzu.
Dariya iman tayi ta ce, " zan Sanar maka amma ba yanzuba.
Okey ko yaushene INA saurarenki.
Daga nan suka d'ora hira, har marwan yadawo daga makaranta mom ma tashigo akacigaba da hira mai dad'i irin ta 'yan family d'in dasuka shak'u da juna sosai...............





*_kuyi hak'uri, wlhy nayi typing sosai, Nazo zanyi posting na danna delete, bakuji iron haushin danakejiba yanzu wlhy😭._*








*luv u oll my fan's*
*(((S)))........2017*
[8/6, 6:03 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_*






*_NA Bilyn Abdul_*





_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*

https://mrsbilkisa.blogspot.com






*(page 41 & 42)*
Dr kishingid'e gefen gado, kan musayeef na kan k'irjinsa yayi filo dashi, barcincisa yakeyi ajikin babansa, ahakali Dr ke shafa sumar yaron data kwanta luf luf, yakai dubansa ga iman dake tsaye tana shirin barci.
My life wai wace maganace zaki fad'amin d'azu ne?.
d'ago idonta tayi tad'an kalleshi tana murmushi, saida ta d'aure igiyar rigar barcinta sanan taja kujerar madubi tazauna suna kallon juna.
Uhmm damafa akan d'iyarkane deexerh, deexerh kuma?, mike faruwa da ita?. Babu komai sai alkairi.
Yaushene kuke ganin zakubar dee.... Tafara kula samari harta sami mijin aure?.
Kallonta yake cike da mamaki, yad'an k'an k'ance idanunsa, miya kawo wanan maganar?.
Iman ta juya kwayar idonta tana gyara zama, bafa wani Abu bane, ni kawai ina ganin lokaci yayi dazaka bata dama tafito da miji.
Ajiyar zuciya Dr ya sauke, yad'an tashi zaune tareda gyarama musayeef Kwanciya, hakene my life, saidai ina ganin abarta ta kammala karatun shiyyafi a'ala, kinsanfa yarannan dasun fara soyayya saisu zubar da komai mai muhimmanci arayuwarsu.
Murmushi iman tayi, hummm Dr kenan, zan iya yarda dabatunka tawani 6angaren, amma tawani gefen zand'an musaka, musamman Idan na kalli rayuwata.
Karka manta ina ss 2 secondary aka cireni aka baka, miyasa iyayena basuyi wanan tunaninba.
Kai ya girgiza yana murmushi, kema asanan akwai abinda yakawo dalili, amma dukda haka na fahimceki, yanzu ita khadijan tanada Wanda takesone?.
Ajiyar zuciya iman ta sauke, tareda fad'in abinda nakeso ka tambaya kenan.
Yasake murmusawa amma baice komaiba.
Dee..... Tanada Wanda takeso, sun had'une alokacin dakayi wata jiyya a asibiti, 'yarka tanason guy d'in sosai domin na fahimci haka a zancenta, shima kuma yana Sonta bil'hak'i da gsky, Dan har yana buk'atar ganinka daga nan yaturo iyayensa, kaga bayan kammala makaranta saimusha biki.
Dariya Dr yayi, Dan ganin yanda ta k'arasa maganar cike da d'oki, yashafa kansa yana kallonta, my life nima nakusa zama kaka ko?, yak'are maganar da d'aga gira.
Jinjina masa kai tayi tana d'an zaro ido, fuskarta d'auke da murmushi, ta sara masa alamar girmamawa.
Dariya yayi sosai, my life kodai kema zaki zama soja ne?.
Kagako damun kafa tarihi miji soja mata soja, d'ansuma zaizama soja, lamarin so nice.
Dr yalek'a fuskar musayeef yana fad'in gsky zamu bada ma'ana, da maganatu idonsa biyu datuni labarinnan yakai kunnen mama da yaya da aunty.
Iman tamik'e tana dariya, ta hawo gadon tazauna kusada Dr tareda d'ora kanta akafad'arsa, aii wanan d'an naka har nakan rasa inda ya koyo magana, gashi kai ba gwanin surutuba, nimadai hakan nake, amma shi magana kamar akku, tad'anja hancin musayeef daketa barcinsa.
Dr yashafo fuskarta yana fad'in kin manta da deexerh, aii dukkanain surutunta musayeef yad'obo.
Uhhmmm kumafa hakane habibi na.
Kallonta yayi sosai, ya maimaita sunan ahankali habibi!..
Kai takad'a masa tana murmushi, rungumeta yayai yana sumbatar wuyanta daketashin k'amshin wani fitinannan turare.
Yad'ago suna kallon juna, ngd sosai.
Ka cancanta tafad'a cike da salo.
Nima nayi dace yafad'a ahankali.
Nice nadace habibi na, nima nadace my life yafad'a yana rungumeta.

*++++*• *++++++*• *++++*
Washe gari iman tabama dee..... Labarin yanda sukayi da Dr, cike da farinciki Dee.... Tarungume iman, kai aunty nayi farinciki sosai wlhy, yaushe ya ce, "yazo su had'u?.
Nanda kwana biyu, Dan zaikoma wajen aiki ranar lahadi, woow! Bari na gumtsama bobo na.
Tofa Dee.... Kinfa afka da yawa.
Um'um aunty kefa kikace karna tsaya kallon ruwa kwad'o yamin k'afa.
Haka batun yake d'iyar uncle isma'il, maza kira surikina ki gumtsa masa bayani kawai.
Dariya sukayi harda tafawa......
Shigowar Xoxo yasa suka mik'e suna ihun murna, cike da farinciki suka rungume juna.
Bayan sun zauna iman ta ce, " haba my sisi abin ko waya babu.
Uhummm kedai bari, gidanne zasuyi bak'i shiyyasa nahad'o inawa inawa nayo nan.
Bak'i kuma kamarya?.
Xoxo ta harari iman, kina nufin daddyn musayeef bai fad'amiki komaiba.
A'a wlhy basanar dani komaiba, k'ila ya manta.
Lallai daddyn musayeef zan ramane, wai ina kishiyarki naji gidan tsit, gashi kuma kuncika gida da ihu keda dee.....
Deexerh dake ajiye tire ta ce, "lah wai aunty bata baki labarin mun iza k'eyarta gidan tsohoba.
Xoxo tad'an zaro ido, kamarya dee....?, Kaini 'yan ganau mana.
Gilas kof dee.... Tamik'ama Xoxo cikeda lemo, hhhhh aii randa nadawo ranar suka kama hanyar sokoto da sakamako mai k'yau har uku uku.
Xoxo takwashe da dariya, dee..... Wai kina nufin anshare tarihinsu saidai alabarin kundin k'addara.
Wlhy kuwa, sunyanki tikitin barin kano tuni.
Shegiya dee..... Shiyasa nake k'ara sonki, ammafa yau zanyi barci mai dad'i.
Iman dake zaune tanajinsu ta girgiza kai kawai batareda tayi maganaba.
Xoxo ta kalli iman, lallai sisi shine koki Sanar minma.
Kai saikace wani abin farinciki?.
Okey keda abin bak'inciki kika d'aukeshi, tab ni fishinma danake da daddyn musayeef ya wuce na huce.
Iman ta ce, " kudai kula sani", ni Dan ALLAH miya faru agidan har bak'i suka koroki?.
Ki tambayi mijinki shiyyafi cancanta yasanardake.
Kai sisi.... Bafa ya nan suna kasuwa tareda yaya, saifa anjima zai dawo, nikam wlhy nak'agara naji.
Hhhhh saiki maida kwad'ayinki Dan bazakiji mutuwar sarki abakinaba, shine abokin ango mafi kusanci.
Iman tazaro ido waikina nufin komai Normal?.
Xoxo ta ce, "bafa zakijiba.
Da sauri iman ta tashi saigata da waya, Dr takira, bayan sund'anyi musayar kalaman soyayyarsu ta ce, " hafsat fa tazo mana yini.
Woow! Kice kawai amaryarmu insha ALLAHU.
ban ganeba?.
Oh my life sorry Dan ALLAH, wlhy namanta nabaki labari, randa nadawo dazumud'in fad'a miki abinnan yafaru, karki damu ganinan zuwa gidan yanzu.
Tom saikazo iman tafad'a tana Yanke wayar.

Babu dad'ewa Dr ya iso gidan, lallai amarya saikika gudo kenan?.
Dariya Xoxo tayi, bayan sun gaisa ta ce, "badole na gudoba kun cike gidan da mutane.
To aii haka akeso, babban taroma yana nanzuwa a hanya.
Iman ta ce, " wai nikam sai k'ara 6addani kuke.
Ruwan data bashi yad'auka yasha yana dariya, karki damu yanzu zakiji komai, amma ina dee.....?.
Taje kaisu musayeef islamiyya.
Okey.
Kiyi hak'uri wlhy narikicene, idan kintuna randa abinnan yafaru nasu Raihan dasafe kafin faruwar haka ai na Fita nace zamuje tad'i.
Iman ta ce, "eh.
Yauwa to Dama gidansu hafsat mukaje muka gaida Abba, muka kuma nemi izinin turo manya.
A take yabamu dama, shinefa yau manya sukaje tambayar auren, ranar nataho dazumud'in fad'a miki, aka dakushe farincikina.
Dasauri iman taje ta rungume Xoxo ta na murna.
Shidai Dr sai dariya yake musu.
Dr yamik'e kunga bari nad'an watsa ruwa, mitumin ma yacemin yana zuwa yanzu.
Dr Nabeel kake nufi?, iman ta tambaya.
Eh, nagaya masa gimbiyarsa tana nan, shine yace gashi nan zuwa.
Xoxo tace nayi gudun gara.......
Kinfad'a gidan zagoba Dr yak'arasa mata yana dariya.

Cikin 'yan mintina Nabeel ya iso.
Xoxo sai 6oye fuska take wai ita kunya.
Zama yay d'an nesa da ita yana dariya, gimbiyata yaukuma nine nazama abin jin kunya?.
Iman tayi dariya itama, to aii dole aji kunyar Ango, barima nabaku guri.
Hhhhh tomun gode, amma ina my boy?.
Suna islamiyya shida 'yan biyu.
Okey, ALLAH yasa sudawo kafin nawuce nayi missing nashi.
Zasu dawo insha ALLAH Iman tafad'a tana shigewa d'aki.

Anan suka wuni akasha soyayya Xoxo da Nabeel, harma tsare tsaren yanda auren zai gudana sukayi.
Dan Nabeel ya ce, "kusa ya ce, " asaka bikin shima yasha angwanci kafin akoma yajin aiki.
Itadai Xoxo tashitai tashige d'akin iman saboda kunya, sukuma suna mata dariya.
Sunsha yini bayan magriba su iman sukaje suka maidata hargida, Umma tanata godiya dak'ara sakama wanan k'awance na iman da hafsat albarka.
Bayan sun ajiyema Umma alkairi suka dawo gida.

Bayan gama cin abincin dare, akadasa hirar family, anan yaya yake Sanar dasu, kawu yakirashi wai su Raihan basuje sokoto ba.
Dr ya ta6e baki, to yaya mu miye namu, mudai aii mun Fita hak'insu, tunda tun randa muka sakesu muka kirasu muka shaida musu, Dan haka sunemi yaransu can ba ananba.
Mama ta ce, "a'a dukda hakadai kuyi hak'uri Ku nemesu ko dan zumincin dake tsakani.
Mama wane nemansu zamuyi su aii ba k'anana yara bane, kinsandai halin wad'an nan 'yan iskan yaran yanzu haka suna gidan zubaida Mara mutuncin k'awarnan tata.
Wlhy kuwa yaya suna canma, garama tun wuri su kirasu nidai wlhy babu abinda zanyi, yamik'e afusace yabar falon.
Kowa da kallo yabisa, Dan sunsan halin fushin isma'il, idan yasoka yasoka, idan yak'ika kashiga uku...........




*_" hummm masoya ina alfahari daku akowace dak'ik'a ta rayuwata, ngd sosai da k'aunarku gareni, kuna k'aramin kwarin guywa gsky, ngd sosai, Nima ina k'yaunarku aduk Inda kuke, duk Inda masoyina yake ina alfahari dashi, kona sanshi ko bansanshiba ALLAH yabarmu tare, inamuku fatan alkairi arayuwa."_*









*luv u oll my fan's*
*(((S))).....2017
[8/6, 6:03 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_*






*_NA Bilyn Abdul_*





_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*


https://mrsbilkisa.blogspot.com




*_(page 43 & 44)_*
Deexerh ta kalli iman atsorace, aunty miyasa uncle yake kirana Dan ALLAH?.
ke babu komaifa wlhy, naga duk kin wani rikita kanki.
Ba haka bane aunty wlhy tsoron uncle nake tun randa yazane su Raihan, iman takama hannunta suka fice tana fad'in saikuma akace kema dukanki zaiyi.

Afalo suka iskeshi kwance kan doguwar kujera, suna shigowa yatashi zaune, deexerh tak'arasa kusada k'afafunsa ta zauna a k'asa, iman kuma tafice dasu had'a break itada mom.
Kalon minti d'aya yayma dee.... Ita kuma kanta yana k'asa tana wasa da zoben hannunta Wanda Umar yabata, gabanta sai dukan tara tara yakeyi.
Dr yay gyaran murya tareda jingina bayansa da kujera, khadija yakira ainahin sunan deexerh.
Muryarta nad'an rawa ta ce, "na'am uncle.
Yad'anja numfashi sanan ya ce, " waye Umar farukh??.
Gabantane yafad'i, tad'an d'ago atsorace tana kallonsa saitaga shima ita yake kallo, da sauri ta maida kanta ak'asa, muryarta na rawa ta ce, "wanine.
Wanine kamar ya?, inason nasan matsayinsa agurinkine.
Ido tad'an zaro kanta na kallon k'asa, tayi shiru Dan bazata iya cewa saurayinta bane.
Ya ce, "ke nake saurarefa.
Iman tashigo falon da sallama zata d'auki Abu akicin d'intane, harta gotasu zata shiga kicin saitaji Dr yana fad'in bakida bakine???.
Iman tadawo baya tana kallon Dr, daddy musayeef miya farune?.


Please Login or Register in order to submit comment