Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 5
daman tunda ya shigo take hangenshi ta sama,?ara gyra fuskarta tayi sannan tasa hijab dinta tace ma Anani Kamal yazo ita ta tafi, kitchen ta fara shiga ta hado mashi drinks da ruwa, sannan taje,zaunawa tayi tace."sannu da zuwa sahiba." Kallonta yake yana murmushi dan kallonta kawai yana sashi farin ciki, balle tayi magana, cewa yayi. "Yauwa masoyiyata fatan na samu ki cikin koshin lafiya."!? "Lafiya lau Alhmdulh, ya gida ya Momy dasu Husna."!? "Duk suna lafiya lau, suna ma gaidaki." Murmushi kawai tayi, sannan ta sauko ta zuba mashi drinks din yasha bayan ta gama sha tace mashi."Dady yace ka turo iyayen ka, suyi magana asa baikon bikin mu." Wani irin farin ciki ne ya lublubeshi, dan bai san sanda ya furta."Alhmdulillh, Allah na gode maka." Cigaba da kallonta yayi sannan yace."masoyiyata da gaske ne ko kuma mafarki nike." Kulle fuskarta tayi da tafe hannunta sannan tace. "Da gaske ne ba mafarki kake ba, nice nan gabanka nike gaya maka Dadyna yace ka turo iyayen ka gobe." tashi yayi yace mata."zafi zafi kan buga karfe masoyiyata, ni zan tafi yanzun naje na gaya ma magabata na, dan yau ji nike kamar ance an daura auren ma." Ita dai Smile kawai take bugawa dan Zainaba ba daga baya wajen iya murmushi, raka shi tayi bakin mota sai da taga tafiyarshi sannan ta koma cikin gida ta gaya ma Anani yanda sukayi dashi. Daga gidan su Zainaba gidan Sadiq kawai ya wuce, bayan sun gama gaisawa yace mashi."Abokina Zainaba tace man Dadynta yace na tura iyaye suyi magana asa baikon bikinmu, wata shawara kake da ita kuma."!? "Alhmdulillh ai Kamal komai yazo cikin sauki, yanzun ka tashi kaje gida karda Momy taga baka dawo da wuri ba ku samu matsala, gobe da safe sai kaje ka gaya ma Baba Bala, sai yaje ya nema maka auren ta." "Hakane, amman Sadiq nayi ma Momy adalci kuwa idan taji kawai ansa man biki ba tare da ta sani ba."!?... Shiru Sadiq yayi yana kallonta tabbas yasan irin son da kamal yake ma Momy bai san bacin rainta ko kadan, amman idan ba ta haka aka bi ba taua zai samu Zainaba din da yake so, idan har aka cigaba da biye ma Momy to tabbas Kamal zai mutune baiyi aure ba, murmushi ya danyi yana cewa... "Wannan shine adalcin Kamal, da kaje ka ja mata abun magana, ai gwara kayi auren kasan ma rabonka ne yazo kusa shiyasa, idan kuma Momy ta matsa tace zata hanaka wallahi rabo yana iya kasheta kaga gwanma taji kawai ansa bikin nasan ko zatayi maka fada, amman kuma dole tayi hakuri." "Maganarka gaskiya ce Sadiq, ni na tafi, komai kenan sai kajini." "To angon Zainaba bada kanka asare kaje gida kace ya faWi." Dariya kawai yayi ya tafi gida dan yaga lokacin dawowarshi yana son kure mashi, baida lokacin tsayawa ba Sadiq ansa. Bayan ya koma gida wanka ya fara yi sannan yaje apartment din Momy, abinci suka ci sannan suka wuce massalaci, bayan sun dawo wajen Momy suka koma sukayi firar dare, dan duk daren duniya tare suke fira da Momy sai 11 suke zuwa su kwanta. Bayan sun koma apartment dinsu waya ya kira Zainaba suka sha wayar su sannan suka kwanta. Bayan sun gama breakfast ya ce ma Momy ya tafi wajen aiki, daga nan ko bai wuce ko ina ba sai gidan Alhaji Bala. Yako yi sa'a ya tadda shi a gida bai kai da fita ba, bayan sun gaisa da matarshi ya shiga dakin Baban nashi, zaune ya tadda shi yana karanta newspapper, bayan ya gaidashi ya fara yi mashi bayanin abun da ya kawo shi."Baba daman zuwa nayi na gaya maka inda nike neman aure ance na tura iyaye na, amman maganar gaskiya Momy bata san ina neman auren ba." Kallonshi Alhaji Bala yayi yana cewa...."Subuhanillahi, Kamalu, ya akayi zaka fara maganar aure amman baka gaya ma Momynka ba."!? Sosa kai ya fara yi sannan ya dukar dakanshi kasa ya fara ce mashi."Baba na lura Momy bata san taga munyi mata maganar aure, da zaran munyi mata maganar aure zatace bamu isa aure ba, sama da shekara goma kenan, ina nuna ma Momy aure nike so, amman sai tace ita ban isa aure ba, idan nayi aure Yanzun to matar da na aure wayau zatayi man ta kwashe man kudi ta gudu, ko kuma tayi man wayau ta dunga anshe man kudi, haka sukayi da Yaya Usman, da ya matsa mata sai ta barshi yayi auren amman a gabana take sa yana sakin duk matar da ya aure tace mashi ai tayi mata rashin kunya, ni kuma wallahi aure nike so shiyasa na yanke shawarar ban gaya mata dan ko na gaya ma ta ba saurara zatayi ba balle ta anshi uzirina shiyasa nace sai dai taji ansa man baikon biki, amman mudun taji zanyi aure wallahi sai ta hana, kaji dalili na Baba." Zuface ta wanke Alhaji Bala da kuma tarin mamakin Momy, tabbas bari yayi kama da mutun, shiyasa duk sakin da Usman yake ma matanshi bai taba jin tayi complain ba, aikuwa idan har maganar Kamal gaskiya ce to tayi na karshe dan zai nuna mata karfin ikon uba kan yaranshi, kallon Kamal yayi yace...."Ita Saudatun take wannan aika aikar Kamalu."!? Duk da har kasan zuciyarshi baiji dadin tonama mahaifiyarshi asiri ba a wajen yayan babanshi, amman ba yanda ya iya dan baida choice da ya wuce wannan dan ya tabbata Baba bala ne kawai zaiyi masu maganin matsalar Momy shida Usman a hankali yace..."Eh itace Baba." Girgiza kai kawai Alhaji Bala yayi ya cigaba da cewa..."Allah ya yi maka albarka, yanzun gaya man gidan da ita yarinyar take, daman yau zani abuja maganar auren yayanka, kai kuma wani gari take ita yarinyar."!? "Nan kaduna, a unguwarmu, sai dai ba layinmu daya ba, Alhaji Masa'ud speaker din governor to diyarshi ce." "Masha Allah, ai tare mukayi secondary school dashi Baban nata, Abu yazo da sauki ma, sannan dan Allah Kamalu idan akayi auren nan karka biye ma Momynka kayi na dan'uwanka kaji."? "Eh Baba insha Allah." "Yauwa Allah yayi maka albarka, kace masu gobe insha Allah zani zo, yau dai Abuja zani zuwa anjima insha Allah." "To Baba, Allah ya kaimu na barka lafiya." Bayan tafiyar Kamal ya kira Zainaba yake shada mata gobe iyayen nashi zasu zo, ta gaya ma Dady, dan yau bai samun damar shigowa da marece, bayan sun gama waya ya tafiyarshi wajen aiki, ranshi tas..... *>?? SDEENDTM DATA SERVICES>??* *MTN* . *Airtel* 1GB = ? 300. 1GB = ? 300 2GB = ? 600. 2GB = ? 600 3GB = ? 900. 3GB = ? 900 4GB = ? 1200. 4GB = ? 1200 5GB = ? 1500. 5GB = ? 1500 *GLO* . *9MOBILE* 1GB = ? 350. 500Mb ? 500 2GB = ? 700. 1.5GB ? 1100 3GB = ? 1050. 2GB ? 1600 4GB = ? 1400. 3GB ? 2000 5GB = ? 1750. 4GB ? 2500 *VALIDITY: 30DAYS/1MONTH* For cable subscription or sell recharge card Call this number or whatsapp =?G?؀?08066268951* *Muje Zuwa.... =ؤ?* *Yar'mutan kankia cec'?* Share domin Allah *?&?NIDA UWAR MIJINA?&?* _By_ *'Yar mutan kankia c'?* *MANAZARTA WRITERS ASSOC* https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ _It's 500 via account number 0777512438 jamila Abubakar Bello access bank, shidar biya via 08160508316_ <ؓ??? SDEENDTM DATA SERVICES>??* *MTN* . *Airtel* 1GB = ? 300. 1GB = ? 300 2GB = ? 600. 2GB = ? 600 3GB = ? 900. 3GB = ? 900 4GB = ? 1200. 4GB = ? 1200 5GB = ? 1500. 5GB = ? 1500 *GLO* . *9MOBILE* 1GB = ? 350. 500Mb ? 500 2GB = ? 700. 1.5GB ? 1100 3GB = ? 1050. 2GB ? 1600 4GB = ? 1400. 3GB ? 2000 5GB = ? 1750. 4GB ? 2500 *VALIDITY: 30DAYS/1MONTH* For cable subscription or sell recharge card Call this number or whatsapp =?G?؀?08066268951* *Muje zuwa..=ؤ?* *Yar'Mutan kankia cec'?* *?&?NIDA UWAR MIJINA?&?* _By_ *'Yar mutan kankia c'?* *MANAZARTA WRITERS ASSOC* https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ _It's 500 via account number 0777512438 jamila Abubakar Bello access bank, shidar biya via 08160508316_ <ؓ?

Chapter 3 of 5