Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 3
duk sammak'al. Inna kuwa ba ta yanda za ta amince waninmu ya d'auramata lalle. Ina mafita?" *GIDAN MATI* BY BINGEL FULANI & RUFAIDA OMAR "Ke dadina dake jahilci kwarankwatsa dubu, haba ai ko karamin yaro ya san ruwa za a shekama Zubo a zuba Sugar shi ke nan ya zama lemo, batun lalle kuma kin manta Inna da shegen san fadanci kamar matar Bawan Sarki? Ai kawai kururuta mata kai zakiyi har ta sake ta baki kafar ki kunsa. " Nene ta yi shiru kamar mai nazari, sai kuma ta gintse fuska ganin Fad'ime ta fito zuwa makewayi. "Shegiya kai da wata fuskarta kamar taunanniyar gyada, Allah Abule yadda naki jinin Matar nan bank'i a cemin karta fito raye daga makewayin nan, ba ni zoban ki gani duka gidan zan had'a idan ya so a na tan sai na juye maganin" Ta fad'a tana wartar ledar zobon da Abule ta riga ta siyo. "A'A hankali dai Nene d'an kad'an ya ce a zuba saboda karfinsa." Ta balla mata harara "Wallahi duka zan juye idan za a sha giya asha ta dubu Abule!" Ta fad'a tana mai ficewa daga d'akin. Kai tsaye madafi tayi ta dauko kwanon sha ta juye zobon, ta tuttulo ruwa daga tulu ta sheka bisansa ta zuba Sukari wadatacce ta juya. Nan da nan ta kasafta na kowa, na Inna ta fara dauka dauka za ta kai mata, da shigarta kuwa ta tarar ta tana gyangyadi dan haka ta aje ta juya za ta fita. " Na shige su ni Uwar Biyu, Nene me nake gani haka?" ta juyo da sauri tana kallonta kafin kuma ta saki murmushi. "Zobo ne muka samu tsaraba daga Abule, shi ne na hadamana lemo da shi na san ai kin sanshi a birni." Inna ta balla mata harara tana turo kallabi goshi." To ke ina kika taba ganin anyi zobo ba a tace tikar ba? Wannan zobo za mu sha ko roman zobo? Idan ba ku iya abu ba ku dinga tambayata mana, ni nan da kuke gani na bayan zobo durinkis (DRINKS)har mangwar durinkis (MANGO DRINKS) Na iya, dan haka ban san jahilci d'auki ki ta ce shi sai ki kawon. Sum-sum Nene ta fice jin Inna ta koma yaren 'yan sama jannati. Sake gyarawa ta yi, tukun ta dauki na Fadime ta kai mata daki, komawarta daki ke da wuya Mati ya sawo kai Gidan. Kai tsaye dakin Fadi ya yi yana doka sallama, fasa kai dan karamin kwanon shan baki ta yi ta aje tana amsa masa da murmushi kafin kuma ta mike tana kokarin zare masa zungureriyar hular da ke kansa. Ya shaki kamshinta da yake so na Karkar dan haka ya washe baki "ALLAH Amarya son ki nake kamar na mutu" Ta yi murmushi tana rangwada kwalelen kanta "A'A Maigidana mai ya kawo mutuwa kuma, muna tare ai." "Hmm! Ba za ki gane ba ne, idan kina kusa da ni ji nake kamar numfashi... KYYYATTT...FYYTTATAT... Ya dakata yana mai kakalo kaki, kafin kuma ya dunkulo majinar yana mai furzo ta waje da ba ta dire ko'ina ba sai cikin kwananshan Fadime dake cike da zobo. Ita da shi suka zubawa kwanon ido kafin kuma ta kwabe fuska. "Haba Maigida na sha ce maka ka dainamin tofe-tofe a bangon daki ko kasa, wannan ko a kan titi ne ba abin so ba ne. Yanzu kalli yadda ka haramtamin abinda tunda na gani yawuna ke tsinkewa. " Ki hakuri na mantane, yanzu bari na karbo miki kasona sai ki sha." ya fada yana mai daukan kwanon ya fice. Bisa randa ya tadda wani kwanon rufe da Fai-Fai Dan haka ya aje wancan ya dau wannan ya tafi. Nene da ta shiga makewayi rage ciki tana fitowa tayo inda ta ajje zobanta, ganinsa bude ya sata doka ashar "Ko wane shegen ya budemin oho, to idanma diba akai an sha wuta bal- bal tunda nawa ne. Ta fada tana hararar dakin Inna, kafin kuma ta daga kwanon ta kwankwade tas! Har kakin Mati. Minti biyar da sha cikinta ya yi wani irin juyi, jin kamar ruwa da wani wari na binta ya sata lekawa abin da ta gani na binta ratata ya sata doka ihu tana dafe mazaunanta "Wayyo ni Mati! Yoyon Kashi ya kamani. Muna zuwa. *GIDAN MATI* ©BINGYEL FULANI & RUFAIDA OMAR Ihun Nene ya janyo hankalin mutan gidan, gaba daya suka fito har da Abule wacce ta gwaggwa6e a d'aka tana kwa6a lallen. Kan kace me tuni Delu ta gyara zamanta jikin garu tana lek'e, itama Shafa ba'a barta a baya ba wajen ganewa idonta. Mati a rude ya nufeta. "Nene, lafi..." Kii! Ya ja burki sakamakon wari da k'arar sakin tusa da ya bugi kunnuwa da hancinsa. Inna ta sanya salati. "Me zan gani haka Nene? Wane irin shashanci ne haka ki wuce Makewayi mana" Nene dake ta kokarin danne mazaunanta da hannu ta daddage ta ja numfashi sama tana mai hade jikinta dan ta tsayar da gudawar, ganin kamar an kara kunnu ta ya sa ta sakin wani wawan ihun "Wallahi ba ta tsayawa, na shiga uku ruwan jikina zai k'are. Kai Mati! Kai mati zan mutu, za ta zuƙen jini" Ai sai ta zabura ta danna a guje zuwa karshen gidan abu na yoyo. Mati ya yi sauri ya bita ganin ta zube gun, "Nene, nene, jin shiru ya sa shi toshe hanci yana jijjagata, sai kuma ya dago a tsorace yana duban Inna. "Kamar fa ba ta numfashi Inna" "kai kauce nan, wane irin ba ta numfashi matsa ni ka ga na ba ta fastu aidi (First Aid)shashasha ko dabarun lafiya baka iya ba dake kanka ya cika da gashin jakai." "Um Inna yanzu dai bata ba'a ake ba ki duba ta kiga ni Aradun Allah Inna ba ta motsi" Inna ta dan na masa harara, sai kuma ta hau karewa Nene dake yashe kallo, ganin har yanzu Abun na tuttulowa daga jikinta ya sa ta kallo Mati "Tunda dai kai ne Mijinta matso kusa daidai bakinta ka lalubo harshenta ka gantsara mata cizo, shi ne zai sa ta farfadowa yanzu" Mati ya kalli Inna da ta kauda kai gefe tana jijjiga kafa kamar ba ita ta fadi wannan zance ba, ya waiga ga Abule dake matsar kwalla, ya dora idonsa kan su Delu dake bisa katanga, ai sai ya hau girgiza kai yana mai sharce gumi "Bazan iya ba! Kwarankwatsa dubu Inna wannan zalunci ne, ya zan ciji marar lafiya. Kuma sannan wannan ai Yahudanci ne." ai sai inna ta zabga salati tana mai fashewa da kuka Mati ya ce mata Azzaluma, kafin kuma ta share hawayen tana mai watsa ma masa dakuwa "To ka tsaya jahilci Nenen ta mutu, numfashin mutum na daukewa da minti goma idan bai samu taimakon gaggawa ba yake mutuwa" Jin haka ya sa Mati yin wurin Nene da sauri yana lalumar bakinta. Da dai ya zakulo harshen ai sai ya gatsashi da karfi. Baya ya yi yana ganin Nene ta yi wani irin cilla kafa. Tana fadi a hankali " Na mutu Mati" cikin magagi. Abule ta ƙara sautin kukanta "Inna dan Allah mu kai ta gun kula da lafiyan da kika kai Faɗime kwanaki" Mati ya kalle ta, sai kuma ya yi waje da sauri. Ba daɗewa sai ga shi da mai Baro. Abule ta taya shi kama Nene aka dora ta bisansa. Suka ɗunguma Asibitin ƙauye. Bayan dube-duben da likitan ya yi sakamako ya fita. Nene dai banda Maleria ba abinda ke damunta. Likita duk tambayoyin da ya yi sun tabbata ba abinda ta ci na ɓata ciki tunda dai abincinsu guda ne. Dan haka ya daura ma karin ruwa ya rubutawa Mati O.R.S da Napkin na manya aje a siyo mata. Ta kuma dinga daura napkin din duk bayan sa'a biyu. Karshe ya sallemusu da cewar su je Binni a duba ta da kyau shi kam iya na sa ke nan. Da komawarsu gida Abule ta yi wuf! Ta fada ɗakin Nene tana sakayo kaba. Kallonta take cike da tausayi ganin harta tsotse rana guda. "Ni Nene anya ba maganin fadi kika sha ba? Na ganta sumul fa" Nene dake ji da yoyon kashinta ta mike a hankali jiki na rawa" Shi ne wlh a randa na tadda shi a bude na sha, na shiga musanyamin ta yi bakar muguwa wayyo ni. Mene makarin ki taimake ni Abule" Abule ta dafe kirji ido warwaje "Lalle dara ta ci gida Nene! Makarin da wuya Nene, ba za mu iya ba, sai kuma rushe da kuka." Nene ta yi ruf da ciki tana numfarfashi. "Ki fad'amin Abule, ko menene shi zan iya." Jin haka Abule ta fyace majina ta soma magana. *GIDAN MATI* ©BINGYEL FULANI & RUFAIDA OMAR Abule ta yi k'asa-k'asa da murya. "Makarin shine a jik'a wandon kwarto a shanye." Nene ta zabura tayi zaman 'yan bori wanda ya yi daidai da sullu6owar tusa ta mai k'ara. Abule ta toshe hancinta, a hankali Nene ta numfasa har da lumshe idanu don ba k'aramin sassauci ta samu a cikinta ba. "Na shiga uku, yanzu ina zan ga kwar... Af! Fad'uwa ta zo daidai da zama ai Abule, yo bana manta ashe muna da su a kurkusa ba? Ga Basharin Shafa?" Abule wacce itama shaf ta mance da batun Jik'an Lamid'on ta sauke ajiyar zuciya tana mai jin zuciyarta wasai, babban abinda ya sanyamata damuwa da lamarin ba komai bane sai na tsoron kada ya kasance Nene bata warke ba ta tonamata asiri mutan gari su zageta. Ta daki cinyarta tana mai washe rinannun hak'oranta. "Kai Allah mungode maka, ai ni dinma kaf tunanina bai je nan ba. Ko jiya da daddare ya haurawa Kulu Gurguwa." Suka saki shewa don Nene har ta hango warakarta a sauk'ak'e. "Kai Allah Ya k'arowa Bashari ilimin kwartanci, wannan ai gaba ta kaini. Ashe kwarto da ranarsa. (Kun ji jahilci!)" Dariya suka k'ara kwashewa da ita. A yammacin ranar Shafa na durkushe a gaban murhu tana kokarin iza wuta ta tsinkayi sallamar Nene da Abule. Da mamaki ta dubesu kafin ta mike. Abule ta ci burki anan tana k'arewa gidan Shafar kallo domin rabonsu da shiga gidan har sun mance. Daga can gefen garu ta hangi jerin manyan duwatsu wanda ta taimakonsa ne Shafa ke k'arewa cikin gidansu kallo. Ta6e baki ta yi gami da bin sahun Nene da har ta shige rumfar Shafar ba tare da ko neman izni ba. Shafa za ta yi magana Abule ta hanata ta hanyar rik'o hannunta tanamata alamar ta yi shiru gami da yi mata nuni da gidansu, nan take ta fahimci ba su kaunar Fad'ime da Inna su san da zuwansu. Ta gyara zaman d'aure kirjinta suka shige ciki. Nene ta washe baki. "Shafa Shafa, Shafar Bashari, uwargida ran gida! Kin tare gaba kin tare baya, turmin tsakar gida sha lugude!" "Wannan haka yake." Fad'in Abule tana gyada kai kamar k'adangaruwa. Shafa ta yamutsa fuska tana kallonsu d'ai- d'ai. "Halan dai Nene acan asibitin har allurar mahaukata suka manta suka yi maki?" Nene ta hau daure fuska za ta kwa6omata mai zafi ganin haka yasa Abule saurin tarewa. "Kai Shafa, dad'ina da ke zolaya. Nene ai taki ce, banda abinki ai makwafci ance ya fi dan uwa, a baya ma rashin fahimta ne." Dariya Shafa tayi gami da tafa hannuwa. Nene da Abule suka dubi juna, dakyar dai suka shawo kanta ta yarda zata sauraresu. Nene ce ta soma magana bayan ta gyara zaman nafkin dinta. "Ki taimakeni Shafa ki bani aron wandon Bashari." Shafa ta fiddo idanu gami da dafe k'irji. "Yau naga ta kaina! Nene me zakiyi da wandon Basharina? Anya Nene ba ki samu matsalar kwakwalwa ba? Au to na fahimta, wato dai duk matattarar kwararar gudawar da aka sanyamaki bai isheki ba sai kin had'a da wandon Basharina? To mine amfanin na Mati?" Nene ta share zufa tana girgiza kai. Abule ta cafke zancan. "Kinga Shafa duk ba haka bane, wannan maganar da za mu yi sirri ce, don Allah ki rufamana asiri." Shafa ta dan zubamasu idanu na 'yan dak'ik'u kafin ta gyada kai don ba za ta bari gulmarnan ta wuce ta ba. "Ina jin ku." Abule ta zayyanemata duk abinda ya faru da kuma makarin asirin. Shafa ta saki shewa har da tafa hannuwa. "Yau abin namu ne! Oh ni matar na Lamid'o!" Saida ta basu wuya Nene harda matsar kwalla sannan ta amince da sharad'in Nenen za ta kyautarmata da tunkiyarta da take kiwo. Ba musu Nene ta aminta daganan ta mik'e ta fita zuwa d'akin kwanansu ta hau lalube. Jimawa kad'an sai ga ta rik'e da wani tsohon wandon Bashari da ya gada gun Lamid'o ta mik'amata. "Gashinan, kuma kada ya kai gobe a wajenki, ko ta katanga ki jehomin." Nene ta hau godiya kafin kuma cikin lallami ta ce. "Ki taimakamin Shafa, ki bani sabon d'inki mana." "Cab! Ai idan kinga Bashari ya yi sabon dinki to mutuwa akayi a danginsa don haka ban bayarwa, idan ba kwa so ku k'ara gaba." Ta k'ara he tana girgiza k'afa gami da jefamusu tafin hannunta. "A'a me ya yi zafi? Mu je Abule hakan ma ya wadatar" " To karki manta dai ki jefon ta katanga." Da komawarsu kuwa Abule ta tarkata lallen ta watsar Masai, shi zaman duniya dama rabo ne, idan ba ka da shi kuwa za ka zo ne a banza ka koma a wofi. Tuna hakan ya sa ta nutsuwa ta ma fita daga batun Fadi. To haka ma ga Nene sai wayar gari akai aka ganta sumul tamkar mai bugun Iska. Itama ta mai da rayuwarta shiru ta hanyar aro nutsuwar dole. Daga bisa ni ta kulla Amintaka da Shafa ba ma ta zaman gidan balle ta zubda hali. Bayan watanni, ranar wata laraba wanda ya yi daidai da kwanan Inna guda a birni ta je hado kayan haihuwar fadi. Faɗimen ta tashi da nakuda. Gidan daga Abule sai Nene dake shirin fita. Ta gyara zaman yafenta tana mai sauke kabar shiga d'akinta. Ta juyo gami da duban Abule, za ta yi magana kenan suka ji nishi da salatin Fad'ime. Cikin hanzari suka dubi juna. "kinji abinda na ji?" Abule ta ya tsina fuska" na ji mana kila abinne ya zo." "To ya za ai ko mu dubu yar magaji... " Abule ta ƴi saurin rufe mata baki. "Ke gafara, kinmanta yanda ta musanya miki magani? To yaune ranar ramuwa dan haka maza kwaɓe gyalen nan ki dauka surfe mu yi yanzu dan karma makota su jiyo bayan awa guda ma lekata." Da sauri Nene ta aje gyalen ta juye hatsinta a turmi suka hau dukansa ba ka jin karan komi sai tunkwal-tunkwal. Fadime cikin azaba haka ta rarrafo bakin kofarta tana kiransu amman suka yi biriss da ita. Har sai da suka bar jin muryarta tukun suka zubda taɓaren suna ma su nufarta. Ganin ruwa gefenta ya sa Nene zare ido "Ke abu ai fayar ta fashe." Abule ta karasa itama tana lek'e-lek'e, a karshe suka kinkimi Fad'ime suka maidata ciki. Haka suka kar6i haihuwar santalelan d'anta suka yanke cibi. Nene dake rike da jaririn wanda bai bar komai na Mati ba, katon kan Fad'ime ya yo. Ta yiwa Abule ido kafin ta fice zuwa d'akinta rike da jaririn wanda ta cusawa yatsanta a bakinsa gudun kada sautin kukansa ya ankarar da gulmammun makwaftansu. Abule ta dubi Fad'ime wacce ba k'aramin k'aruwa ta samu ba wajen haihuwa sai murk'ususu ta ke da alamar dai akwai abinda ke damunta. A hankali ta sulale ta bi bayan Nene. Idanu ta ware a tsorace ganin Nene na kokarin sanya jaririn cikin kwali. "Nene! Bakya tsoron asirinmu ya tonu?" Nene ta harareta. "Kinsan iyakar tsawon lokacin da na dauka ina ajiyar kwalinnan? Ai bazan bari damarnan ta kufcemin ba, yau dan kwal ubannan sai kwanan daji." Kafin Abule ta ce wani abu suka tsinkayi sallamar Mati. A razane suka dubi juna har Nene batasan sadda ta cire yatsanta daga bakin jinjirin ba ai kuwa ya canyara kuka. "Lafiya Fad'i? Kin haihu ne?" Mati dake jefowa Fad'insa tambayoyi ya tsaya gami da saurin bin inda ya jiyo kukan jaririn. Duk kokarinsu na kada ya fahimci shirunsu saida ya gane. Nan ya hau salallami, wani wawan tsalle da ya doka sai gashinan gaban Nene, ya kwasheta da mari kafin ya fiddo jaririn daga kwali. "Ka gantanan, yasin ba hannuna ciki! Yanzu na shigo daga makwafta ina.." Fad'in Abule yayinda Mati ya katseta da sauri. "Dalla can rufemin baki kema bakar munafuka! Wato kun yi shirin kashemin mata da d'a ko?" Sautin karar Fad'ime ya kid'imashi, a guje ya fice zuwa d'akinta. Kan kace me Shafa da Delu sun shigo domin tun kukan jaririn na farko sun tsinkaya saidai ba su k'ara ji ba sai yanzun da Mati ke balbalin fad'a. Lek'owarsu suka san abinda ke faruwa suka bazamo cikin gidan. Su ya bari a wajen Fad'ime yayinda ya fice nemo abin hawa don mik'a Fad'ime asibiti. Delu na gyara jaririn tana zubamusu habaici Shafa na tayata. Su kam kowacce na d'akinta sun k'unshe gaba daya a tsorace suke da abinda zai biyo baya. "Shegen, ashe d'agamin k'afa kawai ya ke." Fad'in Nene a k'asa-k'asa tana shafa kuncinta. Mati na dawowa aka wuce kai Fad'ime ga likita bayan ya kora Nene da Abule gidajensu da shika (saki) d'ai-d'ai. *GIDAN MATI* ©FULANI BINGYEL & RUFAIDA OMAR BAYAN WATA GOMA Rayuwa mika a gidansu Mati, abubuwa da yawa sun faru ciki harda dawowarsu Nene bayan sunyi Bikon Mati sau kusan goma. Wanda Nene sai da ta koma yini a gona gun Mati tsaban son ta koma dakinta. A rana sai tai wanka sau hudu ko biyar. Goge hakora kuwa masu sai da gawayin ƙauyen sai da suka shaidata, haka ma masu Gishiri. Saboda tsabar tsafta sai da ta koma yawo da tsumma tana goge kafarta idan tai kura. Wannan fa duk shawarar ƙawarta Shafa ce. To haka ma ga Abule itama sosai ta nutsu dan har dan abin kwalama take kaima Mati gona. Musamman ma Kundun Kaza da ta san yana so. Karshe dai ya mai dasu. A daren Inna ta tarasu da ta ta nasihar ta nunamusu laifinta ne tare da neman gafararsu. "Haba Inna, ta ina kika zama mai laifi? Mu keda laifi mu yakamata mu nemi gafara." Fad'in Nene kenan tana mai k'arashewa da sheshshek'a. Fuskar Inna cike da damuwa ta girgiza kai bayan ta k'aremusu kallo gaba daya har Matin tana mai shafa kan jikanta Atiku dake saman cinyarta, ya sha billensa a goshi an rambad'amasa kwalli yayinda fuskar ke ta kyallin mai. Ta cigaba da magana. "Um um Nene, bari fad'in haka, maganar nan haka take. Abule da bakinta ta sanarmin musabbin wannan rashin jituwar a sadda take zuwa yawon biko, nayi kuskuren ware wani kaso na dukiyata da zummar bawa jikan Matina na farko, kai kuma Mati bai kyautu ace kai da kake Maigida ba kana nuna halin k'aranta, Abule ta sanarmin da irin yanda ka sanyata k'aryar ciki wanda tun daga ranar zaman lafiya ya k'ara k'aranci a gidanka. To yanzu wannan sai ya zama izna gareka, matuk'ar kana son had'in kan iyalanka kada ka k'ara wannan gangancin. Nima a karshe ina neman gafarar..." Da sauri duk suka tari numfashinta kowa na kara neman gafararta, Nene da ke tashin k'amshin turaren matan arewa ta rungumo kafadar Abule dayan kuma ta rungumo Fad'ime wacce farinciki ya cika don har zuciyarta bata son fad'ace-fad'ace, washe bakinta ta yi wanda ya sha durji da gawayi ta ce. "Yanzu mun zama tsintsiya mad'aurinmu d'aya. Daga gareni Nenen Mati babu abinda zai k'ara fitowa daga wurina." Farinciki ya cikasu babu ma ya Mati wanda har aiken kiss ya yi musu ta iska bayan ya fakaici idon Inna, suka tuntsire da dariya kuwa. Cikin iko na Ubangiji kuwa tun daga ranar babu hayaniyar da ta k'ara tada hankula a GIDAN MATI, Nene a matsayinta na babba ta ja girmanta da sauran mutuncinta da ya rage, hakanan Fad'ime tana binsu sau da k'afa, saida ya zamana rainon Tanimu ya koma ga Nene, kai kace itace ta haifeshi. Fad'ime me kawaici kuwa ta d'auke kanta daga Atiku, muddin ba nono zai sha ba to fa babu abinda k had'asu sai kwanciyar bacci. Bangaren Mati shima kuma daidai gwargwado yana kokarin yin adalci tsakankaninsu. Wannan ya kwantarwa Inna hankali. SAUYIN RAYUWA Gida ne wanda ya sha filasta madaidaici, tsakar gidan an shafeshi da sumunti. Dakuna ne jeras har hud'u sai falo babba guda daya wanda daidai talakan k'auye ya tsaru. Nene ce ta fito daga d'akin dake jikin na maigidannasu tare da Atiku da kanwarsa Sa'a, ta cakare cikin atamfa mai kalar ruwan masara, tana kokarin rufe k'ofar d'akinnata bayan ta saki hannun Atiku ta ce. "Wai mutanennan kuna so dai dare ya yi mana ba mu tafi gidan bikinnan ba ko? Abule! Kanwata!!" Kusan a tare suka amsa gami da fitowa daga d'akunansu sanye cikin atamfa irinnata. Abule rik'e da d'iyarta da Allah Ya bata wacce ko wata shida bata cika ba a duniya yayinda Fad'ime ke goyon yaronta na uku Sallau don Nene kam Allah bai bata ba. Nene ta washe baki. "Inye, cakarewa. To ai ni har kun fini kyau." Suka dara. "Wane mu?" Fad'in Abule da ke saita zaninta. Suka rufe ko'ina suka jera gidan Delu wacce ke aurar da yanmatanta uku. Kowa a gidan bikin ya yaba da shigarsu, Shafa ita kanta ta yi kyau tamkar ba ita ba, cikin hukuncin Allah mijinta Bashari ya shiryu ya daina kwartanci, hakanan Delu itama mijinta ya daina dukanta tun watarana da diyarsu Bushira (wacce duk cikin yaran ya fi kaunarta saboda nutsuwarta) ta gwada d'aga hannu da zummar ramawa uwarsu, wannan abu ya dagamasa hankali ainun karshe dai ya saduda bayan limamin garin ya shiga lamarin ya mishi nasiha. Karshe. Mu hadu a wani sabon Labarin na mu mai suna BUDURWAR KURMA... MUNA GODIYA An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 3 of 3