Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 3
tana hararar Abule." "Oh ni Abu? Lalle idan ta karewa kare barin haushi yake ya koma tunkuyi, na ga dai abin rabo ne auran Mace da ciki. Ki gwada naki salon mana mu gani, ai wani asirin baya ci da turaren hayaki sai an had'a da yan dabaru." "Uban wa ke asiri da turare?" Nene ta faɗi a fusace tana ture fai-fain tafasa gefe." "A'a ai kinji matsalarki baki cin ribar magana, yanzu mene na sakin na maguzawa a wannan hirar? Ni kinga wucewata yin abinda zai fisshe Ni. Ta faɗa tana mai sunkutar bokitinta ta fada Makewayi. Nene ta ciji yatsa tana mai tura baki gaba, sai kuma idanuwanta suka sauka kan kayan da Abule ke d'orawa saman yar katangar bandakin ta langa-langa. Abin mamaki harda wani tsohon dankwalin wata atamfarta me fanteka da mati ya sa mata tun a toshi. Har dai ta juya zata wuce, sai kuma dai ta sake juyowa tana kallon katangar zuciyarta na kiyastamata abinda Abule ke yi da kaya haka. Nan fa idanuwanta suka sake sauka kan wata tsummar rigar Mati da tun yana Saurayi ta sanshi da ita. Wani makirin murmushi ta saki da ta gama hasaso abinda take zato. Ai sai tayi gun 'yar katangar a hankali ta janye kayan bata bar mata komai ba sai zanin da zata yane jikinta. Da sauri tayi ɗaki gurin Inna dake gyangyadin shaiɗan na gabda Maghriba. Itama Innan sai da ta firgita na ganin yarda Nene ta fad'o Mata ba ko gafara dai. "Lafiya Nene kika katsemin barci haka dan rashin mutunta Uwar Miji?" "Bari dai Inna, ai abinda na gani yau idan ban sanar miki ba na cika ma-ci Amana, na rantse miki da izifi sittin Abule cikin zani gare ta. Idan baki yarda da batunnan ba biyoni kofar Makewayin ki gani." Inna ta watsa mata wani kallo she'ke'ke, sai kuma ta mi'ke tana tura d'aurin kallabinta gaba." "Muje na gani." Ta fad'a tana yin gaba. Abule da ta gama jika-jikan ta mi'ke za ta mai da zannuwanta ta d'aure yanda ta saba, ai sai ta tarar babu, ta d'auka ko baya suka faɗa dan haka ta fito a sad'ad'e tana Addu'ar Allah ya kau da idon Nene har ta kwashe. Sai dai fa turus! Ta yi ganin Inna da Nene tsaye tana sakar mata dariyar Mugunta. Jiki na tsuma ta sunkuyar da kanta 'kasa. "Shegiya guntuwa me bakin hali, abinda ban zaci gare ki ba sai gashi ya tabbata gunki. Uwar wa ta koyamiki wanann kinibibin ko dan ganin yar uwarki na da cikin? Inna ta faɗi tana mai kai mata rankwashi a jikakken kanta. "A'a Inna lafiya kike bugurmin Abule" Mati ya faɗa da shigowarsa kenan. "Zaka rama mata ne? Sha-sha-sha kawai, Matarka na cikin Zani dan sakarci ka kasa gane wa." Ya kwalalo ido yana dubanta, sai kuma ya hau sosa kai yana noƙewa. "A'a Inna ya za ai na sani, abinda rabon da ayi abu tun watan shekaran jiya. Ai sai Inna ta hau tafa hannu da Sallallami. "Haka Auren ya mayarmin kai Mati sai abinda Mace take so?Mene amfanin auren idan ba za ka taki mace tamkar gona ba? Ya kinan baƙar Munafuka sai kin faɗimin abinda kike bawa dana da har kike juyashi haka ko kuma ki tafi gidan Ubanki wallahi." Ta faɗa tana jawo gashin Abule. Da sauri Mati ya shiga tsakani yana faɗin "Sakarta Inna." Da dai Abule ta fito daga hannun Inna ai sai tayi kan Nene dake ta sheka dariya a fusace tana faɗin " Bazan fita Ni kaɗai ba sai da ke bakar mujiya muga naki cikin mana in gaske ne." Ta kai mata wawura. Nene ta kankame jikinta tana ture Abule, ta ɗaga hannu zatai naushi, Abule tayi nasarar bankare hannun ta kuwa gatsa mata cizo a hammata da dazunnan ta barbadawa hammatar toka dan ta rage tsami, ai kuwa bata ɗaga bakinta gurin nan ba sai da ta cisge gashin hammatar Nene har jini yayi tsartuwa. Nene ta saki ihu tana dafe hammatarta. Abule kuwa ta yi wuf! Ta fisgo zanin Nene sai ga tullin tsummokara ɗaure a ciki. Wani abin mamakin har da wani koren Gajeran Wandon Mati da ya gaje shi tun gurin ƙaninsa yasha doyin jakai da warin fitsari, da Mati ya shafe shekara yana nemansa, yau sai gashi a cikin Nene ɗaure... *GIDAN MATI* © BINGYEL FULANI & RUFAIDA OMAR Inna ta hau tafa hannuwa tana salati iyakar k'arfinta, kan ka ce me magulmatan makwaftansu sun hau lek'e cike da al'ajabi. "Yau na ga abinda ya fi karfina ni Uwar biyu! Kai! Kai! Wallahi ba za ta sa6u ba, Mati!" Ta juya ga Mati wanda zufa ke ta karyomasa, gabadaya ya susuce, daman ita Abule ya san k'arya ce ta shukamasa musamman da ya ji tana maidawa Delu irin tuggun da ta shirya na iska, ita kuwa Nene bai ta6a kawowa k'arya ta ke ba, a zatonsa idan Abule ta ɓata rawarta da tsalle to yana da mafaka a wajen Nene. Sai dai ashe dukkansu taron na ayya ne. "Eh dole ka rasa bakin magana mana! To wallahi ba za ta sa6u ba! Ko ka k'ara aure ko kuma ka saki kowace shegiya ta koma akurkin ubanta. Za6i ya rage naka, yanzu na ke son amsata." Inna ta k'arashe tana gyara zaman siket dinta na buje. Nene da Abule suka shiga tashin hankali, kada fa su yi biyu babu. "Kai nake sauraro ka tsayamin k'erere kamar liman ya manta Fatiha." Mati ya saci kallon Matansa, to da ya rasa tafkekiyar gonar Inna da kuma gida ai ya gwammace ya k'ara auren ya samu haihuwa. Ya mai da idanunsa kan Innarsa. "Shikenan, ki nemo min mata." Ai sai Inna ta rangad'a gud'a. "Ayyiriririii! Haba ko kaifa, yanzu na tabbatar da cewa kai jini na ne. Sai ka shirya don kuwa yanzu za ka yi aure." "To amma..." "Amma me? Inna ta katseshi tana harararsa. "A'a wai dama gani na yi su biyun ma mangalar jakai na biyu bata iya rikesu da ita, shi ne nake tunanin kar ta ukun ta shigo kuma idan ina cin abinci sau biyar a rana na dawo sau uku." "To batunu ƙiyama sarkin ci, in ce dai gidan nan nawa ne?" "Naki ne har ni d'inma." Ya faɗa yana dukar da kai. "To tunda ni zan ma auren mene na tunani? Idan ta ciyarwa kake zan ƙarama akuya da rago ka kiwa ta. Ina ce dai shi ke nan?" Ta waigo ɓarin da su Abule ke tsaye. "Ku kuma sai ku shirya don kuwa falleliyar budurwa zan samar masa, ba irinku zawarcin titi ba." Bak'in ciki ya turnuk'e Nene da Abule. Musamman Nene da ta tabbatar bata kai na ta matancin ba, amman dai ai ita ce ta fari, kuma ma ta toshe yanda ba za a gane ba, don haka ta karkata baki. "Allah na tuba ko dubu zai auro ba kamar ni a zuciyarsa, ni ce dai Nenen Mati, kaf k'auyennan an shai da soyayyarmu." Inna ta bankamata harara kawai ta wuce d'aki. Shi ma Mati da saurinsa ya fita ya hau jakinsa ya fice. Abule ce ta saki shewa. "Aikin banza wai bille a d'uwawu, duk dai abinki bai sanya an fasa auroni ba, dad'in abin ma ba abinda bansani ba. Ina ce da sa hannun aljanu da 'yan bori a aurenki da shi ko?" Nene ta fusata, za ta kai mata bugu tuni Abule ta nufi d'aki, ta mai da dubanta ga masu lek'e. "An yi asara munafukai da tsakar rana babu ko kunya!" Babu wacce ta tankamata acikinsu, ta gama haukanta ta fad'a d'akinta. BAYAN WATA BIYU Ta faru ta k'are, duk wani shiri da gyare- gyaren da ya dace a yi na zuwan Amaryar Mati an kammala, amaryar ba wata bace illah Faɗime d'iya ga aminiyar Inna, Ladidi. Daidai da lefe Inna ce ta koma birni tare da Ladidi suka haɗo. Abu kamar wasa dai aka sanya biki sati biyu, duk irin borin Nene da Abule bai sa an fasa ba, ganin babu Sarki sai Allah ya sanya suka hak'ura. An kawo Amarya lafiya lau da gud'a da komai, cikin 'yan rakiyarta har da Shafa da Delu. Kwanan Amarya d'aya a gidan Inna ta tattara ta koma birni da zummar sai nan da sati biyu za ta k'ara lek'owa. Nene na zaune ta tsefe kitsonta wanda ya kusa shekara yayin da Abule ke kwance saman tabarmar kaba tana jifanta da wak'e- wak'en habaici tana ramawa suka tsinci muryar Mati da Amaryarsa suna shek'a uwar dariya, suka dubi juna da sauri kamar wadanda aka mintsila suka nufi k'ofar d'akin nata har suna bangaje juna, ƙarshe dai suka nutsu suna lek'esu. Amarya Faɗi ke kwance saman cinyar Mati, shi kuma yana yagar tsire yana sa mata a baki suna hirarsu cike da nishad'i. Nene ta dafe kirjinta gami da had'iyar yawu. Ba ta jira komai ba ta yi wuf ta shige ganin haka Abule ta ja baya tana mai rike ƙugu. "Kan uban can! Wato Mati dama amanarmu ku ke ci? To wallahi ba za ta sa6u ba! Sai dai ayi raba daidai!" Za ta d'auke ledar naman Faɗime ta cafke hannunta ta mik'e tsaye. Baki Nene ta saki ganin shigarta. "Riga da wando a gidan nan? Jakar Uba! Mati karuwar birni Innar ta auromaka ashe banda labari?" Harara Mati ya sakarmata bai ce komai ba don wani sa'in yana shakkarta. Faɗi ta kauda fuska gami da murgud'a bakinta da ya sha jan baki. "Ke Malama don Allah ki bar nan wallahi warinki na tayarmin da zuciya. Ga dukkan alamu dai ko wankan tsarki ba kya yi." Ta saki hannunta. "Kuma wallahi ki ka k'ara ta6a ledar nan sai na miki ihun mahaukaciya. Ce miki akai Ni haɗamammiya ce irinki? Ga naku kason can a gefe dan bazan yarda Miji na ya tashi da shanyayyen ɓarin jiki ba ranar gobe ƙiyama." Nene ta hau tafa hannu da shewa. "Hehehe! Yau nake ganin bariki a gidan nan, ashe kuwa yau wata za ta bi tsohon najadu barzahu. Idan kin fasa kirana mahaukaciya ba ki cika d'iyar Ladidi mai siyar da kayan maye ba!" Fad'in haka keda wuya, ta kai hannu za ta d'auki ledar, Faɗime ta damk'i gashinta ta mai da ta baya, tayi taga-taga za ta fadi k'afar Mati dake ƙasa ya miƙe ta kwashe ta sai gata Tim! A ƙasa tayi zaman 'yan bori. Faɗi ta juya da Mini-minin idanuwanta ta dubi Mati "Sannu Maigida bata dai jima ciwo ba ko?" Mati ya washe baki ya ce "Faɗi Amarya ina gabanki ai bana jin ciwo." Ta yi masa far! Da ido ta ce, "Mai gidana na sha ce maka Timah zaka dinga kirana yarda kawuna na birni ke faɗi. Taɓɗijam! "Yau na ga sabon salo wai tafiya bariki da Uwa" Cewar Abule daga bakin ƙofa. Amarya ta waigo ga Nene dake baje ƙasa tana cije baki, "Ke kuma ki ci gaba da shiga shirgi na, wallahi da ruwan sanyi zan dafaki dan ban iya dambe tsakar gida ba, balle na haifawar maigidana talauci, ku da kuka saba kuje can ku ƙarata, ga tsiyarku nan." Ta faɗa tana tura musu kasonsu na tsire. Muna zuwa. MUN GA YABONKI YAKE GARKUWAR MUNANA, MUNA GODIYA. *GIDAN MATI* ©ƁINGYEL FULANI & RUFAIDA OMAR "Maigidana Randar Zuciyata, Idan ka fita kaje shagon Bakari Mai Ashana ka ce a baka Makilin da Burushi." Mati ya washe baki yana kallon kwalelen kanta da yasha zanen shuku yana ta ƙamshin Karkar. "Wani sabon Abinci ne muka samu Amarya Timah?" Ta yi far! Da ido "a'a kai dai jeka kawo za ka ga abinda zan maka da shi." "To shi ke nan, bari na yi wanka sai na fita na siyomiki, kinsan tunda na sameki bana iya fita banyi wanka ba. Ta yi murmushi "Yauwa kama tunamin abinda na ce zan nuna maka rannan, muje Makewayin na maka kaga sai na cuɗamaka baya ma." Ta faɗa tana jawo hannunsa su fita. Fisgewa ya yi yana nuna mata waje da baki, sai kuma a hankali ya ce "Ki rufan asiri safiya ce fa? Kinsan su Nene sun tashi kar ya zama abinda zan kasa cin abinci yau." "Haba Maigida Ni wallahi kanamin irin wannan sai in dinga ganinka ragon maza, ranar kwana nane fa, kuma baka shiga haƙƙin kowa ba dan ka shiga Makewayi da ni, Matarka ce ni, ba ta aro ba, ko ta titi, kuma ko su ka shiga Makewayi da su ba abinda zai dameni tunda na san aikin lada ne. Ya zare ido yana dubanta "Da gaske aikin lada ne?" "Kwarai kuwa, ai zaman Aure indai ba cuta lada gare shi." "Au to muje, amman dan Allah saɗaf-saɗaf bana so Nene ko Abule su tsinkayi motsi na. "To shi ke nan muje" Ta faɗa tana me yin gaba. Ruwa ta tuttula daga tulu a ɗan kwatashin wankan na su, ta sunkutu ta yi Banɗakin da shi, shi kuma Mati ya hau kewaye tsakar gidan, da dai yaji kamar babu motsi ko daga ɗakunansu, ai sai ya yi wuf! Ya faɗa Makewayin. Abule ta yi miƙa ba salati ba rufe baki, ta miƙe tana mai riƙe mararta sakamakon fitsarin da ya rike mata ita. A hankali ta fito waje, ganin ba kowa ya sa ta tsugunna nan gefen kwatamin tsakar gidan ta tsiyaya abinta, ta wawwatsa ruwa ba ko cuɗawa ta miƙe, za ta koma ɗaki ta jiyo kamar kacaniya a Banɗaki, a zatonta Kajin maƙotane ke kacaniya, sanin da ta yi sunsha faɗawa wawakeken masansu azo a yi ta hayaniya ya sa ta zari sanda da sauri ta yi makewayin. Sai dai fa turus! Ta yi tana sakin wani razanannen Ihu ganin Mati zaune a dutse daga shi sai gajeran wando, Amarya Timah kuma duƙe saitin hammatar Mati da wani ɗan ƙarfe a hannunta tana ta kwasar gashin hammatar tana hura masa iska, shi kuma yana dariya gami da fadin "Wai, ci gaba, daɗi wallah." A firgice Faɗi ta yada ɗan ƙarfen saboda yadda ihun Abule ya kiɗimata, Abule kuwa da ƙyar ta jawo sauran numfashinta tana son daidai ta kanta, sai kuma ta ɗaga sanda ba tai wata-wata ba ta saukewa Faɗi ita a kafaɗarta. "Sai na nakasaki baƙar mujiya me salon karuwai kawai, dan Ubanki ce miki akai nan bariki ne da zaki shiga wanka da Mijina, ko kuwa ce miki akai ni ɗin zan yarda." Ta sake ɗagawa za ta rafka mata Mati ya riƙe sandan jiki na ɓari, "Karki kuma dukanta, zan fa rama mata, ke Abule ki fa fita idona da wanann jahilcin na ki, baki san aikin lada ba ne take yi? Ba na son sakarci fa." Ai sai ta yi baya tana kallon Mati sama da ƙasa, kafin kuma ta rangwaɗa guɗa. "Ahl lalle Mati yanzu na san ka ɗauru tamau! a Minjaye, yanzu saboda wannan me zubin botoramin kake cewa zaka dake ni, Ni Abu? Da ka ce aikin Lada na ga dai kwanana ya shiga daga sanda aka kira assalatu." "To na ji, yanzu dai wuce ki tafi haka ba zai ƙarawa faruwa ba." "Bazan tafi ba, Ni fa idan ba jini na fidda mata ba bazan ji daidai ba." "Haba Abu tawa, na ce kije dai, da daddare zaki ji saƙo." Ta ɓallawa Faɗime harara dake dafe da kafaɗarta, ki sake gwadamana karuwanci gidan nan ki gani, wallahi na lahira sai ya fiki jin daɗi, shegiya da wani idonki kamar tsaka ta saka kwai." Af! Abu mai sauki, wai kura ta zo gidan Maharbi, idan karuwancin ne ki gwada naki mana mu gani, ai wallahi babu wata me siffar Fanteka da ta isa ta hanani kula da Mijina. Aikin lada ne yanzu na fara, wanann sandar kuma bashi kika ci." Faɗi ta faɗa tana murguda baki. Sanin Mati ba zai barta ta sake taɓa Faɗi ba, ya sa ta juya ɗakinta takaici fal ranta. ** ** ** Tun bayan da akayi cacar baki tsakanin Abule da Fad'ime gidan ya k'ara kacamewa. Tsakanin Abule da Nene sai ka rantse tun da can kansu a had'e yake tsabar amincin da suka k'ulla na munafunci. Koda suna cikin habaice-habaicen su ne Fad'ime ta fito tsakar gidan nan za su ɓige da shewa suna watsamata bak'ak'en magana a fak'aice. Ko kallon inda suke Fad'ime ba ta yi balle su saka ran za ta tankamusu. Ranar wata laraba wanda ya yi daidai da cikar Inna kwanaki goma sha shida a birni, Abule da Nene suna zaune a gaban d'akin Abulen suna k'us-k'us tare da Shafa makwafciyarsu. Shafa ke yi musu tallar magungunan gyara na mata kala-kala. Ta d'aga wani k'ullin gari tana fad'in. "Kun ga wannan? Na rantse da daren farkona da jikan Lamid'o yana da masifar kyau. Ke wannan da ku ke gani sunansa 'Saki Matar Uba'." Nene da ke soshe-soshenta ta dubi Abule suka yi wata iriyar shewa gami da cafkewa. "Inda ranka ka sha kallo! Yo Allah na tuba idan kura na magani ta yiwa kanta mana!" Fad'in Abule. "Atoh, taya ni gani! Wai Matar kwarto da tallar maganin mata." Nene ta cafke. Jin haka ya sanya Shafa kallonsu a fusace kafin ta d'an kalli d'akin Fad'ime, ga dukkan alamu batasan ma me suke yi ba. Ta maido dubanta gare su cike da borin kunya ta ce. "Oho dai, gwara ni akan ku, haka za ku k'arata a borori." Ta hau tattara komatsanta a sadda suka yo mata ca! kowannensu da bak'ar maganar da yake yarfamata. A daidai nan kuma Faɗi ta fito daga ɗaki da gudu zuwa bakin makwararar tsakar gida ta hau sheƙa amai kamar ba gobe. Nene ta miƙe ido waje tana tafa hannu, yayin da Abule ta dafe kirji tana duban Faɗi dake duƙe. "Duka-Duka yau kwana nawane da Auren ni Nene? Taya ni lissafi Abule. Abule ta hau kasafta yatsun hannunta, sai kuma ta zare ido waje. "Duka-duka kwana goma sha bakwai kenan, kar dai da ruɓaɓɓan kwai aka shigo?" "Oh ni Nene, wannan wace irin haɗama ce haka, ranar farko da rabon ciki kamar marainiyar Karya? Ke kuma maƙaryaciya kika cemin ba ai komai ba ranar jikin tagarsu kika kwana?" Abule ta ɓalla mata harara, "tuna dai, ke kika cemin ranar da aka kawo ta jini take, koma dai menene ni ban yarda da wannan Salon ba, ban taɓajin cikin dake bayyana kansa daidai da lissafin zuwan Amarya ba. Sai dai idan da shi aka shi..." Nene ta yi Wuf! Ta rufemata baki jin sallama kamar ta Inna. "Barta ta ƙarasa mana manyan Akuyoyi, ai na dade tsaye ina sauraronku, wanda ya gani dai shi ya ji kunya wai kallon fitsarin makaho. Idan ba ku da kuke cikin ƙauye, haihuwar ƙauye, renon ƙauye, auren ƙauye, ina na taɓa ganin ana laɓewa sabuwar Amarya? Kunyi asara wallahi Nene, matsa ni na duba 'yar mutane, shashashai masu wankin kai da ruwan daddawa, idan ma da cikin ta shigo sai me? Na ce sai ƙaƙa? Irin kune a jahannamar ma can ƙasan wailun kuke. Sannu 'yarnan, sannu." Inna ta k'arashe tana mai k'arasawa ga Fad'ime wacce aman ya d'an lafawa. Gefe guda ta ajiye akwatin kayanta, ta yaye gyalenta ta dora saman akwatin kafin ta tattare zaninta dinkin rafa siket. Ruwa ta zubo a buta gami da mik'omata. "Tayani duba Abule, toh wallahi ba za ta saɓu ba bari Matin ya zo, ni ban yarda wannan cikin nasa bane, ga dukkan alamu dai mutum da abinsa ya zo, ai daman ni nasan za'a rina, angama yawon ta zubar an k'untso.." "Ki ka k'ara magana a wajennan sai na nunamaki ni ce nan na isa da Mijinki don kuwa yana zuwa zan sanya ya sallamaki ga tsohonki." Nene ta yi d'if ta ja hannun Abule wacce ranta ke ƙuna suka fad'a d'aka. Shafa kuma da ke gefe kunne waje, tayi saɗaɗa ta fice daga gidan. "Mun shiga uku Abule, yanzu idan ta tabbata matarnan juna biyu gareta ya za mu yi?" Fad'in Nene kenan yayinda gumi ke tsirfomata. Abule wacce ta rasa bakin magana tsabar bakin ciki da tashin hankali, sai a lokacin ta iya bud'e bakinta ta ce. "Hum, ni na rasa ma abin cewa wallahi." Sallamar Mati ce a gidan ta katse su, suka yi shiru suna sauraron yanda Inna ke gayamasa rashin lafiyar Fad'ime da kuma cewar Fad'imen na tunda ta zo ba ta ga Al'adarta ba. Muna zuwa *GIDAN MATI* BY BINGEL FULANI & RUFAIDA OMAR Kamar wasa cikin Fad'ime ya tabbata, Inna har Asibitin K'auyen ta mik'a ta tare da Abule da Nene wadanda suka tik'e akan sai sun bisu sun ji da kunnuwansu. Itama Innar ba ta yi gigin hanasu ba don ta fi so su ji abinda zai hana su bacci. Ranar kam sun riga su yin gaba, zagi da tsinuwa ba irin wanda Fad'ime da Inna basu sha ba. Tun daga wannan lokacin kuma sai sabon tashin hankali da makirci ya k'ara ɓallewa a gidan. Akwai ranar da Nene ta shigo da Kuliya cikin gidan, sanin cewa Faɗime ba ta so. Hakanan ta lallaɓa ta d'ora mata ita bisa gadonta tana cikin barci. Allah ne ya tsare da kwallayenta na jere basu zubo bisanta ba, saboda yadda ta dinga razana tana bige- bige a ɗakin. Ƙarshe dai Inna ta cece ta da fitsari ya fiddo ta, ta juyo motsi ɓarin Faɗimen. Shi kuwa Mati yana can ya saki gañɗa ɗakin Abule. Sai washegari ne Inna ta sanar masa, karshe dai ta yi maganin abin da cewa duk wacce ta k'ara kawo wani Abu gidan ko da Ɓera ne, ko ta jefi Faɗime ko Mati da bak'ar magana to a bakin aurenta. Da wannan aka samu bakinsu ya rufu suka koma rara gefe, ƙarshe dai Nene ta tattara ta tafi wani ƙauye bikin kanwar kishiyar matar babanta. Inna zaune gefen Fad'ime tana lalla6ata ta samu ta ci kwad'on Zogalen da ta had'amata, ita kuwa Abule tana tankad'e Garin Tuwo tana wak'e-wak'en habaici. Fitowar Nene daga bayan gida ya sanya suka bita da kallo. Tayi daurin k'irji da tsohon zanin da ta ci 'yanmatancinta da shi duk a huje, k'asan duk ya rarake har idan ka zura hannu a 6uli guda zai ta6o mazaunanta. Fatarnan kallo daya za ka yi mishi kasan akwai nakiyayyar d'aud'a da bai kammala fita ba, jikinta kuwa babu alamar ya wanku. Sai kyalli takeyi da nason datti da hamami dake tashi. "Ke jik'ar Maduga, wai wankan da ruwan Taɓo ki ka yi shi ne?" Cewar Inna. Juyowa ta yi ta mata murmushi, sai kuma ta yi gaba tana murzo wata naɗaɗɗiyar dauɗa a wuyanta. "Ah'ah Nene magana fa nake miki." Fasa ɗaga labulen kabar ta ta yi ta juyo tana kallon Innar, sai kuma ta haɗe mata hannuwa biyu tana roko alamun ta kyale ta. "Uhm! Sabon salo, wai gemu a kafaɗa, halan da kika je bikin rashin magana kika koyo? To ai gaba ta kai mu, tuntub'en me carbi" Inna ta faɗa tana riƙe hab'a. Ganin haka ya sa Abule ture tankaɗen gefe, ta mike zuwa dakin Nene. Da shigarta ta same ta tsaye tana jan Jagira a girarta me kama da ta Tunku. Ai sai ta yi turus! Da mamaki tana ƙare mata kallo daga ƙasa zuwa sama. Ta sha Atamfa koriya fatau, da dinkin rigarta irin na Lema, wani abin mamakin har kallabin irin na atamfar ne, ba wai wari da wari ba. Kwalliya dai irin wacce ko da tana Amarya ba ta taɓa yinta ba. Sai ƙamshin man kadanya ke tashi da ta mulkawa jikinta. "Wannan kallon fa? Ban fa san irin kakannin ki ba?" Ta faɗa tana kaɗawa Abule hannu ganin yarda ta ƙame. "A'a mamaki kawai nake, tunanina ko dai ƙanwar Nene aka musaya mana. "Uhm! Kibar mamaki, kawai nasihar da Innata tamin kan zaman duniya da ƙiyama nake ta tunanowa yau." "Anya kuwa Nene? Ke din ce kike tuna wanda ya mutu? Abokin kuka ai ba a ɓoyemasa mutuwa. Ki faɗamin abinda ya faru dake kika saki makaman haka? Ko duk tsoron kar Innar Mati ta kora ki gida ne?" Ai sai ta gundumo ashar tana me ture ɗaurin kallabin da ta dade tana murd'ashi dan ya yi kyau gefe. "Ni wallahi har kin ɓatamin rai, tsohuwar banzar can zan ji tsoro? To Talle Bodara ce ta ba ni maganin Ɓari, sharuɗɗan cikar maganin shi ne ko daka Ni Uwar Miji za ta yi kar na sake na tanka ta. Kin ganshi a bakin Masai ake barbaɗashi." Ta karashe gami da bankad'a k'asan katifarta, wani k'ulli ta fiddo a bak'ar leda ta nunamata. Abule ta washe baki don tsabar farinciki. Ganin babu damar ihu ya sanya ta kaiwa Nene runguma sai dai tun kan ta k'ara sa had'a jikinta da na ta ta yi baya da sauri tsabar tashin da Nene ke yi kamar mai warin k'ashi. "Dagaske ki ke yi?" Nene ta ta6e bakinta. "Ni idan na fad'i abu na fi son ki yarda, zan miki k'arya ne? Nan da ki ke ganina ba ta wasa bace ba. Bari ki gani, wuyarta dai Fad'ime ta tsugunna saman Masai, ko kwad'o ne a cikinta sai ya fad'o. Jin haka suka saki shewa gami da cafkewa, sai kuma da sauri suka rufe baki. "Um kinga bari na je kafin wannan Tsohowar karuwar birnin ta ankara." Dariya Nene ta yi. "Ai mukam Allah Ya had'amu da suruka." Suka dara sannan Abule ta fice. *** Shiru-shiru ciki zai zube anjima, gobe, bai zube ba. Ko ciwon kai Fad'ime ba ta yi ba ballantana a kai ga ciki. Ganin haka Abule ta yanke gwada ta ta sa'ar ko za'a dace. Nene ta ba ta goyon baya d'ari bisa d'ari, da wannan ta shirya tafiyar kwana daya da sunan ziyartar jikar abokiyar kakarta. Dawowarta akayi sa'a babu kowa sai Nene a gidan da ke faman zazzaga bala'i ta katanga tare da Delu wai Akuyar Delun ta shigo ta cinyemata shanyar da ta yi ta k'anzo. Ganin Abule ba k'aramin dadi ta ji ba, itace har da rungumarta tana tsalle, da ace akwai mutane a gidan da sun sha mamaki. Bayan sun k'ule a d'akin Abule ne ta hau bata labarin abinda ta samo. "Ba k'aramar wuya na sha ba in fad'amaki. Ban ta6a rawar 'yan bori ba amma shege la'antaccen bokannan sai da ya sanyani yi. Amma tunda kwalliya za ta biya kud'in sabulu da sauk'i. Bari ki gani." Ta ɓalle ɓarin zaninta ta fiddo k'ullin magani har biyu ta nunawa Nene. "Ya ce na kwa6a lalle da garin na d'aurawa Inna a k'afa don rufe bakinta. Shi kuma wannan." Ta nuna d'ayan, "A had'a Lemon Zobarodo a sanyawa Fad'ime a ciki ta shanye." Shiru ya biyo baya kafin Nene ta jinjina kai. "Tabd'ijam! Aiki ja! Yanzu banda abinki ina mu ina iya haka? Ni kinga banda kwaɗa zobo da kuli ba abinda na sani kansa, sai yau da na ji ana lemonsa, kema kuma na san

Chapter 2 of 3