Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a hannu, tana sauke ruwan ta rufeta da duka tace" tun safe ko aiki guda bakiyi cikin ayyukanki ba sai yanzu kk kawo sawun ruwa daya" shiru tayi batare data kawo wani uziri ba,ummul shukri bata amsar uxiri ko qaqa,fito mata tayi da wasu manyan barguna tace ta kwasa taje ta wankesu gashi dare ya soma shiga sosai don ma garin da hasken farin wata hk ta kwashi barguna ta nufi babbar qorama dasu ta soma tiqar wanki, tana cikin shanyawa ta gano inuwar mutum a bayanta, juyawa tayi da sauri idanunta ya gane mata prince nasaar, murmushi yyi mata da fararen haqoransa yace" wankin dare kuma baki tsoron mura" wani irin murmushi tayi tamkar kuka iyakarsa le6enta tare da rissinar da guiwowinta tana gaishe shi, tsugunawa yyi kusa da ita yace" ina buqatar kwarkwara kuma ke nkso" kalmar taji tayi mugun bugarta ta zaro manyan idanunta waje tare da dafe kirjinta tace" na shiga uku, wlh ni ban iya komai ba" dariya ta bashi yyi har jerarrun haqoransa suka bayyana yace" zaki koya ai, zaki zama baiwar dake kula dani kwanan nan" gabanta ke faduwa sosai tana kallonshi, babban abunda bimbii ke karewa a wannan yanayin data tsinci kanta aciki na bauta shine budurcinta bata qaunar abunda ze iya rabata da budurcinta, zama kwarkwara a gdn sarauta ai dole sai ka rabu da budurci kuma ga hadari na daukar ciki, itakam tafi qaunar ta cigaba da kasancewa a baiwa mara gata idan har budurcin bazai ta6u ba, sanya hannunsa yyi da niyyar riqo hannunta ta daka wani uban tsalle tayi gefe, abunda tayi yyi masifar daure masa kai,tunda yake ba baiwar data ta6a masa hk sai bimbii shi gani yake kamar taimakonta zeyi amma har ta gwada masa wannan cin fuskar a matsayinsa na jinin sarauta yace"bimbii wannan abunda kkyi kuskure ne babba kar ki kuma gwada hkn ga duk wani jinin sarauta" yyi mgnr fuskarsa a sake tamkar beji haushin abunda ta masa, shiru tayi ta sunkuyar dakanta qasa, wani dutse ya nuna mata yace" ta zauna ta tayashi hira" ji tayi kamar ta kurma ihu amma ba yadda ta iya hk ta zauna daga can gefe ta dosana duwawunta akan dutsen, Allah ya sota ta gama wankinta, murmushi yyi don yana lura da rashin sakewarta yace" bani labarin qasashenku na baqar fata tare da al'adunku" shiru tayi ba tace komai ba, shan kunu sannan ta sauka daga kan dutsen ta sauke guiwowinta a qasa tana roqonsa tace" don girman Allah ka rufamin asiri kabarni na koma bakin aiki na"murmushi yyi yace" wannan ce kawai buqatarki?" ta daga masa kai alamar ehh, yace" shikenan jeki saida safe" miqewa tayi da sauri tabar wurin tana qara dubawa don tabbatar da cewa babu wanda ya ganta tare da prince nasaar, shi kuwa yana daga zaune yana kallonta harta 6acewa hangensa, tana shiga 6angarensu taga su israt da khulood sai zaman jiranta suke suci abinci, suna ganinta kuwa suka tarota da murna suka tmbyta abunda ya sanya ta jima bata fada musu komai ba game da abunda ya faru da ita, suna gama cin abinci israt ta kalli bimbii da murmushi a fuskarta tace"albishirinki!" bimbii ta kalleta tace"goro" israt tace" babban prince ya fitar da ranar za6en sabuwar baiwa dake kula da 6angarensa, nida khulood muna son shiga gasar saidai bamu da chanchata sbd rukunin bayin da muke ciki basu shiga za6en" murmushi bimbii tayi tace" tab, amma kuna da karfin hali waye ya aikeni nikam bani so" khulood tace" wlh nima bawai don ina da sha'awar hkn nakeson shiga ba saidai hkn shine nake ganin ze taimakamin wurin jeton lailah daga wannan hukunci kinsan har an kaita kurkun qasa fa" bimbii tace" kamar ya kenan" khulood tace" idan kina wannan matsayi zaki samu dama sosai wurin neman alfarma wurin babban prince don shine na biyun sarki a wannan masarauta" shiru bimbii tayi sai kuma ta dago da kanta tace" kuna ganin hkn bazai ta6a budurcinku ba" dariya sukayi gbdynsu, israt tace" tab, ai nikam idan prince akbar ya buqaceni da gudu zan miqa wuya don burina ya cika" bimbii sakin baki tayi kurum tana kallon israt da mamaki shimfide kan fuskarta, khulood tace" kaf cikin bayin da suka ta6a kula da 6angaren prince babu wacce ya ta6a nema duk kuwa wacce yau babban prince ya amshi budurcinta dole ta burge kuma dole tayi alfahari dakanta don ta isa mace" bimbii kallon khulood take da tsantsar mamakin kalamanta,gyara zama tayi tana fuskantarsu tace" toh ya akayi kksan baya nemansu" murmushi sukayi israt tace"ai al'adar wannan masarauta shine babban prince dakansa yake za6en baiwar da zata kula dashi duk wacce ta samu nasara za'a sanar a wurin za6en amma matakin qarshe na za6en idan har prince ya samu baiwar a matsayin disvirgin wato ba danyar budurwa ba toh hukunci mai tsauri ze hau kan baiwar shiyasa duk wadanda suke shiga gasar sai sun yarda da kansu, abu na gaba kuma idan ya sameki a cikakkiyar budurwa toh washegarin ranar baiwar zata fito da zanin gadon daya 6aci zuwa babbar qorama ta wankesu dakanta cike da alfahari, hkn shine shaidar dake nuni prince shine ya fara saninta diya mace kuma zata cigaba da kasancewa a matsayin baiwarsa koda ya sake sabuwa kuma sarauniyya zata mata kyautar girma sbd ta faranta ran d'anta ta bashi babbar kyauta,toh shi prince akbar har yau duk bayin da yake za6e babu wacce ta taba fitowa da wannan shaida balle sarauniyya tayi mata kyauta sannan ba'a ta6a samun wacce hukuncin rashin budurci yahau kanta ba hkn na nuni da cewa prince akbar be ta6a kusantar ko daya daga cikin bayinsa ba, kinji dalilinmu" ajiyar zuciya bimbii tayi tana al'ajabin wannan al'ada tasu tamkar ta larabawan farko, khulood tace"idan kk kasance baiwar prince kin tsira kenan don babu dan iskan dazai nemi keta miki haddi kina matsayin baiwa ga prince akbar" shiru bimbii tayi tana tunani, tabbas idan hkne gwara ta shiga gasar don tana tunanin abunda prince nasaar yace da ita yau, wai zata zama kwarkwararsa, kallon khulood bimbii tayi tace" toh su kuma sauran princes din fa suna kwatar budurcin bayin nasu" khulood tace" sukam kowacce baiwa suka za6e washegari take fitowa wankin zanin gadon daya 6aci" shiru tayi sai kuma ta dago da kanta tace"tabbas nima idan zan samu dama zan shiga gasar prince akbar kodan lailah" rumgumeta sukayi suna dariya, saidai tunaninsu yanzu shine rashin cancanta musamman bimbii da take ba balarabiyar usul ba shikansa wannan naqasu ne gareta...........



No editing pls.




WANNAN PAGE SHINE QARSHEN FREE PAGE NA WANNAN LITTAFI MAI BUKATAR KASANCE DANI CIKIN CIGABAN SAIKI TURO DA DARI UKUNKI#300 TA WANNAN ACCT..0100790419,ALHAJI SHAHIDA NASIR,UNION BANK,SAIKI TURO DA SCREENSHRT NA PAYMENT DINKI TA WANNAN LAYI...07041195806.....IDAN DA BUKATAR QARIN BAYANI GA LAYIN KIRA NAN...08080611486....



Alkalamin Bintuu ne...
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔



Written By Bintuu Seer



10


*Zinariyar mace mai ado da tagullah,jinjinar ban girma nk miki uwargida sarautar mata, kece uwar gd kuma kece amarya a gdn Dr. usman bukar*......a jima anayi sai uwar kissa mai ado da k'amshi dake nk......Hjy Hafsatu Usman Bukarâ¤ï¸ina yinki irin totally din nan, wannan page naki ne kiyi yadda kkso dashi🌺



*When I feel boring staring at you comfort me,when I feel hopeless your words give hope,when I feel weak your smile give me strength*.......My luv to you is pure,pls accept me dear💕



Washegari suka tashi kamar yadda suka saba kullum kowacce tayi 6angaren da aikinta yake,6angaren lailah kuwa kai tsaye gdn hukunci aka wuce da ita inda alkali ya zartas da hukuncin kisa akanta amma sai ta haife cikin dake cikinta tukun, kurkun qasa suka kaita ta raini cikin nata a wurin, bimbii kullum tana cikin tunanin lailah ta rasa hanyar da zata iyabi ta taimaketa daga wannan hukuncin na zalinci amma kuma kalaman su khulood har yanzu suna yawo akanta wato idan ta kasance babbar baiwa ga prince akbar zata iya samu alfarmar ku6utar da lailah kenan daga wannan danyen hukunci, zama tayi bisa wani farin dutse tana tunanin hanyar daya dace tabi wurin samun cancantar shiga wannan gasa kuma gashi ranar gabatar da za6en yana kusantowa, miqewa tayi a hnkli ta dauki kwaryar data cika da nonon raqumi ta dora akanta ta wuce dashi babban kitchen,ranar dukkaninsu sun kammala aikin nasu da wuri suka dawo 6angarensu,israt ta zaunar da bimbii tana koya mata wasu baitoci cikin wata waqar larabci, tace" tunda kince baki iya ko baiti daya daga cikin waqoqinmu na larabci ba toh ki gwada wannan ko zata shiga da kalar rawarki" miqewa bimbii tayi ta soma rera baitocin waqar tana yar rawa sai dariya suke gbdynsu, israt ta miqe tace" ku tsaya ku ga yadda zanyi a gaban prince idan na samu shiga za6en nan" sexy dance ta soma irin nasu na larabawa tana kada cikinta da kirjinta ita suke kira raqas sharqi, dariya sosai suke mata bimbii tace" baki da dama israt kuma zaki iya irin wannan rawar a gabansa baza kiji kunya ba" tace" wacce kunya idan har xe za6en" khulood tace" amma fa bana bayin da suka shirya shiga wannan za6en suna dayawa" tsaki israt tayi tace" haushi suke bani ai" khulood tace"kayy israt a gaisheki da qoqari kice muma muna baki haushi kenan" dariya tayi tace" ku idan kune ai kamar nice na samu amma sauran bayin suna samu suna matsawa zasu soma sha mn qamshi dubi fa lenah yadda take yiwa su zainah kamar ba rukuni daya suke ba da" murmushi bimbii tayi kawai tace" toh yanxu meye abunyi kunsan dai banda rukunin a tsarin gasar" israt tace" satar jiki zamuyi kawai mu shiga" khulood tace" wacce irin shawara ce wannan kina tunanin bazasu gane rukuninmu bane" israt tace" nidai ranar tsinke wannan sarqar kafan zanyi na tafi wurin za6en" shiru bimbii tayi sai tace" gsky dole su gane mu" khulood tace"kawai mu gwada yin hkn" bimbii tace" toh Allah ya kaimu ranar" da wannan shawarar a zuciyoyinsu suka kwanta bacci kowacce tana mafarkin ta samu nasara a wannan za6e........


Yau itace ranar wannan za6e, kyawawan yan matan bayin sun jeru sahu sahu kowacce cikin sutura mai kyau a farfajiyar 6angaren prince akbar suna sauraron fitowarshi, bayin dake kula da wannan gasa kuwa sai kai kawo suke a wurin, y'ay'an sarakunan nan duk suna wurin sun hakimce, gimbiya hindu itama tayi ado sai walwali take da daukar idanu tana daga gefe a zaune itama,kofar fitowa prince kawai suke kallo suna tsammanin fitowarsa, ba jimawa kofar 6angaren nasa ta bud'e ya bayyana, sanye yake cikin wata doguwar farar jallabiya da farin rawani ya dora irqa baqi a saman rawanin sai baqar alkyabba, sajensa sai daukar ido yake sbd sheqi, gefensa ubaid ne yake take masa baya sai kuma babbar baiwarsa wacce ze musanya wato lenah,fuskarta babu annuri ko kadan sai hararar jerin yan matan take don ita tafi son kullum ta kasance da babban prince tana masa hidima,tsayawa yyi yana qarewa jerin y'an matan nan kallo, caraf idanunsa suka sauka kan bimbii dake ta faman rissinar dakanta qasa,duk cikin yan mata ita kadai ce mara hasken fata sosai,dauke idanunsa yyi akanta ya kalli ubaid yace" ku fara jarrabasu" batare da 6ata lkci ba aka soma jarrabasu,farko baiwa kowacce abun girki akayi ta canki abinci da prince yafi so ta girka ta kawo masa ya dandana, bimbii tana can baya don batason prince nasaar ya ganta shiyasa take ta sunkuyar dakanta, bimbii bata iya irin girkinsu ba tayi tsuru tsuru, kowacce sai aikinta take don ana tfy ne da lkci, ganin idanu yana zuwa kanta ne yasa ta soma aikin nata cike da tunanin abunda ya kamata tayi, tashi tayi taje ta tatso nonon raqumi ta dawa ta soma aiwatar da abunda ya kamata,chugui tayi na nonon ragumin sannan tayi green tea irin wanda ta koya a wurin maheer, daya bayan daya kowacce take miqewa taje gaban prince ta sunkuya ta riqe abunda ta girka shi kuma ya dandana yaji, bimbii itace ta qarshe cikin sanyin jiki ta qaraso don ita gani take kamar za'a mata dariya abunda ta girka, sunkuya tayi a gabansa ta riqe dan qaramin plate din data saka chuguin da small mug na green tea, sai da yadan dakata sbd ganinta da yyi mai duhun fata yana kyankyamin dandana abun nata sai kuma jan dai ya dauki small spoon din dake faranta ya debi green tea din nata ya dandana sau biyu yana dandanawa sannan ya dauki chugui kadan ya dora a saman le6ensa cike da shakku, kallon ubaid yyi tuni ya fahimci abunda yake nufi, ubaid ya kalli bimbii yace" prince yana son sanin da mene kk had'a wannan abun"ya nuna mata chugui din dake saman plate din hannunta, dago da idanunta tayi tace" da nonon raqumi na hada" komar da ita wurin nata akayi ta kuma hada chuguin yadda ta hada na farko, hk dai aka cigaba da jarrabawar har akazo fagen rawa shima bimbii ta birge kowa don komai nata fita yake daban,komai irin na al'adarta take hkn shine ya dauki hnkli kowa da prince shi kansa, prince nasaar dake gefe kuwa wani irin bala'in haushi yakeji, be ta6a tunanin zata iya shiga gasan nan ba, sauran yan matan dake wurin suma mugun haushin bimbii suka soma ji tun kafin a bayyana sakamako, gani sukayi komai nata ya dauki hnklin prince akbar saidai kafin a fadi sakamako rahoto ya shigo musu cewa bimbii tana cikin rukunin bayi ne na farko kuma suna da shakkun asalinta, prince yace" duk da hk su saki sakamakon a gaban kowa" batare da 6ata lkci ba aka bayyana bimbii a matsayin wacce ta lashe wannan za6e don prince ya yaba da salon dandanon abunda ta hada da kuma yanayin rawarta,israt wani irin tsalle tayi ta qanqame bimbii cike da farin ciki don sukam riqima ce kawai ta kawo su basu ta6a zato daya daga cikinsu zata samu nasara ba, musamman ma bimbii da take jinsin baqar fata,bimbii kuwa ta kasa dago idanunta sbd fuskoki daya aika mata da harara suke cike da hassada wasu kuma zallar qiyayyace kawai irinsu gimbiya hindu da ba shiri tabar wurin cike da mamaki babban prince fal ranta tayaya ze karye dokar gdn nan ya za6i baiwa mara cikakken asali kuma wani abun takaicin ma gata baqar fata a tarihin masarautar babu dan sarkin daya ta6a za6en baqar fata a matsayin babbar baiwa don yawancinsu basu da asali don ba jinin larabawa bane, bimbii kuwa saida aka gama za6en kafin aka gane rukuninsu amma tunda prince ya riga ya za6eta a matsayin babbar baiwa ta wuce wurin, 6angaren ummul shukri kuwa abun ya bata mata rai sosai na wannan za6en da prince yyi taya ze za6i babbar baiwarsa daga qasqantattun bayi rukunin farko wannan ai tamkar zub da qimar gdn ne, za6en bimbii a matsayin babbar baiwa ya kawo gutsiri tsoma sosai a wannan masarauta wanda hkn yakai kunne sarauniyya mar'atuusaliha ta kira ummul shukri don jin yadda akayi rukunin bayi na farko suka shiga za6en shiru ummul shukri tayi don tabbas tasan laifin kowa ze gani don su bimbii a qarqashin kulawarta suke itace tun farko tayi sake, ranar ummul shukri tasha fada a wurin sarauniya mar'atussaliha har takai da an dakatar da ita daga matsayinta na wasu kwanaki, hargitsi aka samu sosai cikin wannan gdn don mafi yawan jama'ar gdn na ganin rashin cancantar bimbii a wannan matsayi, 6angaren prince kuwa ko a jiknsa don halinsa kusan daya da mahaifinsa sarki Abdallah bin jabal akwai taurin kai da kafiya musamman akan abunda suka aminta akansa, babu wanda ya isa ya sanyashi sauyawa baiwa tunda har ya riga ya za6a, ummu sumayya ita ta wuce da bimbii wurin gyara aka gyarata kamar yadda ake yiwa duk baiwar data samu nasarar samun wannan matsayi, wani tamkamemen daki aka kaita a matsayin dakin kwananta sannan ummu sumayya ta soma sanar da bimbii abunda prince yakeso da kuma wanda baya so don mugunta sai tace mata prince baya son qamshi kuma yana son mace ta din ga yawan sanya baqaqen kaya, Allah sarki bimbii duk ta dauka hkne tace"toh" daren ranar bimbii zata soma ziyartar fadar prince,bimbii cike take da tsantsar fargaba da faduwar gaba sosai harta soma dana sanin shiga wannan gasar, maqiya da mahassada kuwa kawai jiran wayewar gari suke su ga ko bimbii zata fito wankin budurci bakin qorama.....






Littafin na kudi ne ki siya ki karanta cikin yanci ba satar fage ba, idan kin shirya siya ga trasaction detail nan, zaki tura #300 ta wannan acct..0100790419,alhaji shahida nasir,union bank,saiki turomin da screesht na payment ta whatsapp through wannan layi...07041195806, idan da neman qarin bayani ga layin kira nan..08080611486......





Alkalamin Bintuu ne.....
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔



Written By Bintuu Seer




11


*In the middle of the night when the stars scattered at the sky the moon become shiny I keep thinking at you*.......Your voice are the sweetest thing I ever.......




Dare yyi sosai amma gdn akwai yalwar fitilu ta ko'ina suna haske kowacce kusurwa ko allura ce ta radio take za'a ganota sbd wadataccen haske daidai lkcin bimbii ta fito sanye da wata doguwar riga bak'a qirin hkm mayafin rigar tfy take a wani dogon corridor hannunta dauke da wani faranti na azurfa da qananan kofina da kuma wani jug mai kyan gaske a tsakiya, green tea ne aciki kuma wannan dogon corridorn shine zai sadata da babbar k'ofar inda prince akbar yake wato sashinsa,jikinta rawa yake sosai don duk a tsorace take sbd batasan meze faru ba, tana qarasowa bayin dake tsaron kofar suka bata hanya,kofar ta bude da kanta ita kuma ta danna kanta ciki kanta a sunkuye tamkar wata munafika, tana sanya kafafunta ciki wani sassayan qamshi tare da sanyi yyi mata maraba, qasan wurin tamkar glass yake sai daukar idanu yake da kyalli, dakin qaton gaske ne kuma kusurwa kusurwa yake,kowacce kusurwa tana da kofa kamar ta masallaci an kame wurin da curtains na alfarma ga kuma shimfida na manyan royal center carpets masu ado, curtains din da aka kame kowacce kusurwa zaka gansu sharara,komai na cikin wurin abun kallo ne, 6angare guda kuma wasu kujeru ne irin royal chairs din nan kalar golden, kusurwar tsakiya idanunta suka kalla inda ta gano kusurwar tafi kowacce girma an kameta da wani qasaitaccen curtains shara shara milk colour, wani gado ta gano a cikinta tafkeke yasha bedshit na wawayen kudade shima bedshit din milk colour, bimbii tsayawa tayi kalle kalle tamkar yar qauye cikin ranta tana mamaki wai nan duk wurin kwanan mutum guda ne, tunda ta shigo yana zaune a wata kujera yana karanta wani littafi na tarihi ko dago da kansa beyi ba sai yanzu, ita kuma sai lkcin idanunta suka sauka a 6angaren da yake take taji wata faduwar gaba ta tsaya qam a inda take batare data qaraso ciki ba, miqewa yyi ya soma takowa a hnkli har ya qaraso inda take fuskarsa babu yabo babu fallasa kamar dai yadda yake kullum, tsayawa yyi yana qarewa shigarta kallo ya tsayar da kwayar idanunta akan fuskarta ita kuwa sai tayi saurin yin qasa da guiwowinta a gabansa, bata ta6a tsammanin zeyi magana ba taji muryarsa cikin tsadadden larabcinsa yace" kije ki sauya wannan kayan dake jikinki" abunda ya fada mata kenan ya juya cike da takun qasaita ya koma inda yake zaune ya cigaba da abunda yake, ita kuwa bimbii miqewa tayi da sauri ta juya da niyyar ficewa daga dakin har tana hard'ewa ta rasa dalilinsa nacewa taje ta sauya kayan jikinta sai ta soma wani tunani nata na daba take hnklinta ya qara tashi cikin ya duri ruwa hk ta koma dakin da take, tana ta cika da mamakin ganin su israt da suka sato jiki suka zo wurinta suka tarar bata nan suka bararraje a saman gadonta suna baccinsu, motsin shigowarta ne da farkar dasu suka tashi suna binta da kallon mamaki, khulood tace" bimbii daga ina kk badai daga 6angaren prince kk ba cikin wannan kayan" kallon kanta tayi ta dago ta kallesu tace" me kayan yyi" israt ta sakko daga saman gado ta iso gabanta tace" waye ya fada miki prince yana son baqin abu komai nashi fari ne shiyasa bayinsa basu sanya duk abunda ya danganci baqi" shiru bimbii tayi sai lkcin ta gano manufarsa ta kuma fahimci mugunta ummu sumayya taso mata tace ta sanya baqin kaya, zama tayi a bakin gado ta zabga tagumi, israt ta sanya hannu ta cire mata tagumin da tayi tace" mene ya faru yar uwa" murmushi tayi tace" wlh nikam tsoro nk gbdy nayi dana sanin shiga wannan za6en" israt tace" me kkce? sake fada naji, yanzu bimbii baqin ciki kk mana don gashi dai silar cin za6en nan da kkyi har muma mun samu arzikin shigowa wannan wuri har da kwana akan gado mai taushi shine kk cewa kina dana sani, toh meye abun dana sani anan" kwantar dakanta tayi ta kafadar israt, khulood ta matso ta zauna kusa dasu ta dafa bimbii tace" tashi ki cire wannan kayan dake jikinki ki shirya cikin masu jan hnkli" harararta bimbii tayi suka bushe mata da dariya, hk suka sake shirya cikin wata milk colour din doguwar riga mai cike da kwalliya sannan israt ta mata 6arin turare har sai da tace" israt wlh ya isa hk" sannan suka qara taje mata gashi suka tufkeshi da wani band shima milk colour, suka sanya mata wani mai kyalli a le6en bakinta, le6en ya soma shiny, suna cikin shiryata lenah ita da wasu bayi su hudu suka bankado kofar dakin suka shigo ta soma binsu da wani matsiyacin kallo sai ta bushe da dariya suma sauran dake biye da ita suka bushe da dariya, tace" idan kun sauya mata baqin kaya ai baku isa ku sauya mata kalar fatar jikinta ba koh" israt tana shirin maida musu da martani bimbii ta riqeta, matsowa lenah tayi kusa da bimbii tana mata wani kallon wulaqanci tace" basu sanar dake babban prince bashi son baqin abu bane toh bawai baqin kaya ne kawai baya so ba har ma da baqar fata" khulood tazo iya wuya ta kallesu itama a wulaqance tace" dadin abun dai shiya za6eta kuma cikin gayyar fararen fatan yace ita ta dace ta hidimta masa wannan kadai abun alfahari ne" israt tace" idan ma ba naci da neman fada na wasu matan ba yace ya dena yayinki toh meye kuma na farkar jeji hk" kalaman nasu sun fusata lenah sosai amma sai ta dake tayi wani murmushin yaqe tace" toh muna nan muna jira muga ko iskar tusa zata hure wuta" dariya sauran bayin dake biye da ita sukayi suka juya suka fice abinsu,bimbii tayi tsuru tsuru da ita saida su khulood suka din ga binta da kalamai na qara qarfin guiwa,khulood tace" karki mance lailah tana nan tana jiran gudummawar mu gareta komai rintsi kiyi mn alqawarin ba zaki gjy ba" tashi tayi ta rumgumesu gbdy sannan suka mata rakiya har kofa ta fice ta doshi komawar 6angaren babban prince, tana shiga ta tarar dashi sanye da wasu kayan bacci farare qal, gashi kansa ya sauko masa har kafada yana zaune a wata kujera ta alfarma yana hada wasu takardu, shigowar ta ne yasa shi dago dakansa yana kallonta sannan ya dauke kansa ya cigaba da abunda yake, rasa abunyi tayi sai ta koma gefe ta sunkuya akan guiwowinta tana jiran umarninsa, kallonta yyi yace" wannan abun da kk kawo ni kkson na zuba dakaina" mgn yake yana abunda yake batare daya kalleta ba, tashi tayi da sauri ta matso wurin ta dauki qaramin jug din ta tsiyaya masa green tea din data kawo a daya daga cikin qananan cups din dake saman farantin ta rissinar dakanta tare da sanya hannu biyu ta miqa masa cup din, kallonta yyi sannan ya miqa hannunsa fari tas dashi ga yalwar gashi zarara ya amshi cup din daga hannunta ya komar dakansa ya kwantar jikin kujerar dayake

2 Comments On DAREN GOMA SHA HUDU
avatar
abubakar-sunusi

1 year ago

Reply

I want to read the novel

avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Replying to abubakar-sunusi

Click The READ THIS NOVEL button

Please Login or Register in order to submit comment