Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka tura ta qasarban don isar da wannan saqo ga sumayya" miqa masa wata farar takarda yyi, rissinar dakansa yyi ya amshi takardar sannan yaja da baya ya juya ya fita, wurin qorama ya wuce ya tsaya can nesa ya hango su israt da khulood suna wanki, kamar ance israt ta juya ta hango shi tsaye ga dukkan alamu su yake son gani, shikam ubaid yana ganin sun ganshi a wayance ya soke musu wata takarda a jikin wata bishiya yyi saurin barin wurin, khulood na ganin hk tayi saurin tashi da niyyar zuwa wurin israt ta dakatar da ita suka cigaba da wankinsu suka basar sai bayin dake wanki wurin suka watse sannan israt cikin dabara taje wurin bishiyar ta zare takarda suka wuce abinsu, wurin da babu koma suka samu suka warware takardar, dayan takardar itace wacce zasu kai ga sumayya dayan kuma takardar shaidar fita ce da sanya hannun ummu nana don basu basu mai sanya hannun babban prince ba kar a zargi wani abu sai ubaid ya samu ummu nana ta sanya hannu itama kanta bata fahimci komai ba don ubaid kamar qani yake a wurinta shiyasa ta bashi sa hannunta batare da wani tunani ba, israt ta kalli khulood tace"kece zakije koh sbd shaidar fitan mutum guda ne wannan" murmushi khulood tayi tace" kece zaki iya wannan aiki sbd kin fini qarfin hali da dabara" wucewa sukayi babban kitchen suka dauki kwandunan debo kayan marmari suka nufi lambu basu jima ba suka dawo kawunansu dauke da kwanduna cike da tuffa suka kai musu babban kitchen, cikin dabara israt ta saci jiki ta nufi babban kofar fita daga masarauta, ganin bayi tayi jere masu shaidar fita suna nunawa ana basu hanyar su fita, layin yyi tsawo dayawa haka take ta Allah Allah a iso kanta har masu tsaron kofa suka iso kanta ta nuna musu shaidar fita suka bata hanya ta wuce, cikin izinin Allah tana fita saqon sarki abdallah ya iso ga masu tsaron dukkan kofofin masarauta su rufe kofar shiga da fita, batare da sun sake barin kowa ya fita ba suka hade kofa suka rufe ruf,israt kuwa qarar rufe kofan da taji ne yasa ta juyawa, farin ciki tayi da Allah ya bata damar fitowa lfy, tfy take sosai tana qetarawa ta siraran hanyoyi da suka ratsa ta gefen gidajen jama'a kunsan yanayin ginin larabawa yadda yake hk har ta qarasa qasarban, rufe kanta tayi sosai har da gefen fuskarta, tsayawa tayi tana hangen kofar shiga wurin ta ganta da qaton kwado, kofar shiga wurin be nuna mata akwai wani mahaluki sake rayuwa a cikin wurin ba, hkn ya ankarar da ita lalle karta qarasa kofar shiga wurin ta shiga wurin ta wani wurin, 2kalle take ta babu kowa don wurin bayan gari ne sosai,tsalle tayi ta haye katangar shiga wurin ta dire ciki, ko'ina yyi qura har ta soma jin tsoro anya kuwa da wani abu mai numfashi a cikin wannan gd,shiga dai take tana danna kai cikin gdn dayake da zurfi, tuntu6e tayi da wani dutse ta fadi ta riqe kafarta, sumayya kuwa tana nesa kadan da wurin ta jiyo motsin mutum, miqewa tayi da hanzari ta isa inda israt take ta bayanta sai ji tayi an saka mata wuqa a wuya, bude idanu israt tayi tana kallon sumayya tace" kiyi hkr ki sake ne don nidin isar da saqo nazo yi" sauke wuqan sumayya tayi, israt ta kalli sumayya sosai ta ganta yadda ubaid ya kwatanta kamanninta cikin takarda, ciro takardar tayi daga jikinta ta miqa mata,saurin warware takardar sumayya ta ga sanya hannun babban prince sannan ta soma krt abunda ke ciki, tana gama krtw tayi ciki da sauri, israt tabi bayanta don tana son sake ganin bimbii, kai tsaye suka shiga inda bimbii take, bimbii na dago dakanta taga israt tsaye da gudu ta taho suka rumgume juna cike da farin ciki, sumayya kuwa saurin kama hannun bimbii tayi, jaririn na hannunta shiga dasu wani wuri, wata kusurwa suka shiga ta janye center carpet din dake shimfide wurin sai ga kofa ta bayyana ta bude kofar tayi da hannunta suka hangi matattakala data shiga qasan wurin, takawa suke a hnkli sumayya na haska musu hanya da wata qatuwar fitila har suka qarasa qasan wurin, cikin qasan wurin yana da fadi sosai, rumbii tara dukiya ne sbd ta kowanne gefe diamond ne a jere sai kyalli yake da daukar idanu, dukkaninsu sake baki sukayi suna kallon wannan tarin arziqi tamkar ba za'a mutu ba,zaunar da bimbii sumayya tayi israt ta zauna kusa da ita, fita sumayya ta sakeyi taje tayi clearing komai wanda ze nuna akwai mutane a gdn sannan ta dawo ta shiga ta maida kofar wurin ta rufe kamar yadda yake a baya, befi awanni uku da faruwar hkn ba, dakarun sarki abdallah suka shigo wannan gd don bincike, sumayya kasa kunne tayi ta jinsu suna bincika kowanne lungu da saqo na wannan gd don suna tunanin nan prince ya kawo bimbii, har suka gama bincikensu ba bimbii babu alamarta, har zasu juya su tafi wani daga cikinsu ya hangi mayafin mace a saman gado, nuna ma sauran yyi suka dawo, daukan mayafin sukayi suna qara kallon ko'ina, binciken qurulla suka cigaba dayin cikin gdn har kusurwar da dakin qasan nan yake suka shiga suka gama bincikensu basu ga komai ba hk suka koma suka sanar da masarauta,sarauniya mar'atussaliha kuwa lkcin data ji wannan abu daya faru ba qaramin tashi hnklinta yyi ba bata ta6a tsammanin wannan baiwa na raye ba har kuma wai ta haife cikin jikinta, tsoron da take yanzu kar sarki abdallah bin jabal ya kuma fishi da prince sam bata fatan hk, tashi tayi cikin sauri ta nufi turakar sarki ta nemi iso, uxair ya shiga ya fito ya sanar da ita sarki bazai ganta ba, dole ta hkr ta koma 6angarenta cike da rudani,sarki abdallah bin jabal be sake fitowa ba sai washegari ya nufi fadarsa, umarni yyi kan a kawo masa abram, batare da 6ata lkci dakarun tsaron fadar suka gabatar da abram gaban sarki abdallah bin jabal, prince shima yana fadar beyi shakkar zuwa ba, yana tsaye daga gefe kansa a sunkuye har lkcin da aka gabatar da abram gaban sarki, abram kallo daya zaka masa kasan ya jigatu abunka da jar fata tuni jigatuwa da wahala ta bayyana a tare dashi, fada tayi tsit kowa na jiran yaji hukuncin da sarki abdallah ze yankewa wannan bayahude tare dansa, daga kai sarki abdallah yyi ya kalli abram yace" kamar yadda na mk alqawari na amshi buqatarka zan cika mk sbd bana alqawari na saba wannan itace nasarar da kayi saidai da kyakykyawan sharadi, shine na amince zan aurawa d'ana baiwa mara asali dalilin alqawarin dana dauka saidai aure ne dazai wakana batare da masarautarmu ta gayyaci kowa ba kuma ba za'ayi wani sha'ani ba"prince dake gefe yyi saurin dago dakansa cike da mamaki yana kallon mahaifin nasa, don be ta6a zaton mahaifin nasa ze amshi wannan buqata ta abram ba, shiru yyi yana tunani anya sarki abdallah be shirya wani tuggu ba kuwa shi yasa yyi hkn,kallon prince sarkin yyi yace" ina son daren yau ka gabatar da wannan baiwa da kk 6oye da ita ga ahlinka" rissinar dakai prince yyi alamar biyayya da amsar umarni,sarki yyi umarni da dakarin nan su saki abram, daga nan zaman fada ya watse, prince ya qarasa 6angarensa cike da tunani kan manufar sarki abdallah kan wannan batu gani yake kamar da wata a qasa kar fa sarki ya shirya masa shigo shigo ne ya samu damar damqe bimbii da dansa dake tare da ita ya aikasu lahira, zuciyarsa ta kasa nutsuwa har yanxu, lbrin wannan hukunci da sarki abdallah ya yanke tuni ya isa ga sarauniya itama dai mamaki abun ya bata, gimbiya hindu kuwa da bata jima da dawowa daga habasha ba baqin ciki da takaici ne ya cikata itama batayi zaton har yanzu bimbii na raye ba don akan idon kowa bimbii ta afka wannan dogon rami........






Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419, alhaji shahida nasir,union bank, saiki tura screensht na payment dinki a whatsapp ta wannan layi...07041195806....






Alkalamin Bintuu ne....
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔



Written By Bintuu Seer




40


*I give you my heart,I give you my blood,I give you my soul*............I sacrifice everything to you my beloved💕💕




Prince dakansa ya nufi qasarban ya taho da bimbii, ranar duk inda ka zauna cikin bayi tsegumin wannan zancen suke wai tsohuwar baiwar babban prince ta dawo tare da sabon jariri, mafi yawan masu tsegumin basu aminta cewa wannan d'an na babban prince bane, sarauniyya mar'atussaliha dakanta ta bada umarnin a shiga da bimbii 6angarenta, bimbii kam zuciyar cike take da tsoro musamman yadda taga fuskar wadanda suka tare ta, ummu nana da wasu kuyangi biyu suka kama hannun bimbii suka shige da ita,ummu nana ta amshi jarrin dake hannun sumayya ta wuce dashi ciki, wanka aka yiwa jarrin aka sanya masa kaya na alfarma sannan ta fito dashi ta wuce dashi ga sarauniyya, tana shiga ta sunkuya ta miqa mata jaririn, miqa hannu tayi ta amshi jaririn, qurawa jaririn idanu tayi tana kallon ikon Allah don wannan jariri babu ta inda ya baro kakansa sarki abdallah hatta idanunsa na kakansa ne, kasa dena kallon jaririn tayi tana qara jaddada mulkin ubangiji wato dai zakaran da Allah ya nufa da chara ko ana muzu ana shaho sai yyi, yaro dai kakansa ya dauko, miqewa tayi dakanta hannunta biyu riqe da jaririn ta nufi 6angaren sarki abdallah ummu nana da sauran kuyaginta na take mata baya, uxair ne ya shiga ya nema mata iso sarki abdallah ya bata damar shigowa ta shigo, yana zaune a wata kujera ta sarauta tunda ta shigo yake kallonta, rissinar dakanta tayi a gabansa sannan ta miqa masa jaririn dake hannunta, qin miqa hannunsa yyi ya amshi jaririn ya daga mata hannu alamar ya sallameta, shiru tayi tana kallonsa sanin halin taurin kai da kafiya irin nasa yasa taja da baya jikinta a sanyaye ta juya ta fita, komawa tayi sashinta ta tarar itama bimbii ta shirya tsaf, itakam sarauniya ta zubar da makaman yaqinta tunda ta dora idanunta kan jaririn nan, bayin gdn gbdy sun saka idanu har sun gaji amma basu samu damar ganin bimbii ba bare jaririn dake tare da ita,shi kansa prince ganin bimbii ya gagare shi,kamar yadda sarki abdallah ya alqawarta hkne ya faru, safiyar alhamis al'ummar fadar masarautar burham suka shaida daurin auren bimbii da prince akbar, wurin wannan daurin aure tamkar wurin makoki babu mai annuri ko walwala, a dai daura, sarki abdallah ya tabbarwa al'ummar duniya shi sarki ne mai mgn guda da tsayawa kan alqawari, wannan rana baqa take qirin ga sarki abdallah da dukkanin wani jini na sarautar burham idan muka dauke babban prince da ranar take fara qal a wurinsa, a tarihin masarautar burham yarima akbar shine d'an sarki na farko daya karya tsaurarriyar dokar wannan masarauta ya auri baiwarsa, wannan aure ya zamto tamkar faruwar mugun abu ga jinin sarautar burham, dayake abun duniya baya 6uya kafin giftawar ido wannan aure tsakanin d'an sarki da baiwa ya karad'a sauran masarautun larabawa, sarakai dayawa idan suka ji wai duk qarfin mulki da izzah irin ta sarautar burham magajin masarautar ya bige da auren qasqantacciyar baiwa kuma baqar fata, hkn yasa sarki abdallah ya dena halartar taron sarakuna na nahiyar larabawa sbd wannan abun kunya da d'ansa ya janyo masarautarsa,bimbii har yanzu tana 6angaren sarauniyya daren yau za'a miqata 6angaren prince akbar, sun shirya sosai albarkacin hada jini dasu da tayi, prince yasa matakan tsaron sirri masu sanya idanu kan duk wani motsi na masarautar burham kan iyalinsa,keken doki na musamman aka kawo don daukar bimbii zuwa 6angaren babban prince, dakarun tsaro da yan matan bayi kewaye suke da wannan keken dokin, fuskarta rufe take da jan mayafin kayan dake jikinta, ta wata siririyar dake saman gada suka bi,hanya ce da dawakai ke ratsawa zuwa 6angarori daban daban na gdn, tfy suke zabiyoyi dake biye da keken dokin na rero waqoqi na masoya masu dadi har suka kai tsakiyar hanyar, suna tsakiyar wannan siririyar hanya sai gani sukayi kawai an tsagayesu, wasu mutane ne sanye da baqaqen kaya, fuskokinsu ma a rufe suke batare da wani 6ata lkci ba suka soma fada da dakarun dake janye da keken dokin da amarya ke ciki, sunyi masifar iya fada kafi kwabo sun soma kwantar da dakarun, burinsu kawai su qarasa wurin wannan keken doki su dauke amarya da jaririn dake tare da ita, ihu kawai kkji, jini duk ya 6ata keken dokin, yan matan bayin nan qoqarin fito da amarya suke su gudu da ita kafin wadannan mutane su qaraso, tuni suka gane nufin kafin suyi wani yunquri wani cikin mutanen ya yarfa musu wani sai ga wasu kananan allurai masu guba sun fita sun sossoki jikinsu suka zube a wurin, sai da suka gama da kowa suka bude keken dokin suka janyota waje wani daga cikinsu yasa hannu ya wafce jarrin dake hannunta, jin jikin jaririn yyi wani iri, saurin bud'e kyakykyawan farin towel din da jaririn yake ciki yyi,tirrqashi! kunsan me ya gani qatuwar teddie, kallon juna sukayi cike da tsantsar mamaki, aikuwa tamkar hadin baki su duka suka sanya hannu suka yaye mayafin da armarya ke rufe dashi sukaci karo da wata baiwa itama duk a tsorace take, batare da wata wata ba babban cikinsu ya daga takobi ze fille kan wannan baiwa a fusace,wani mahayi fuskarsa rufe da baqin kyalle ya bayyana bisa farin doki tunkan ya qaraso yake harbinsu da kwari da baka har ya qaraso wurin, hkn yasa hnklinsu gbdy ya tafi ga wannan mahayin doki suka gyara riqon takubban dake hannunsu hkn ya bawa wannan baiwa daman barin wajen don tsira da rayuwarta, wani irin fada suke gwabzawa tsakaninsu da wannan mahayin dokin burinsu kawai suyi masa illah saidai salon fadansa yyi masifar basu mamaki sbd fada yake irin na cikakkun jarumai masana sirrin takobi, gashi da zafin nama da iya gociya, suna ganin hk sukayi wani irin alkafira suka fada qasan gada su dukka, sauka yyi a hnkli daga saman dokinsa yana kallon irin 6arnar rayukan da sukayi sbd kawai son zuciya, shikam taurun kai wannan sarki na bashi mamaki besan sai yaushe ne ze ajiya wannan kiyayyar da taurin kai ba, qara jinjina kaifin basira na prince yyi daman yasan hkn na iya faruwa shiyasa ya bawa sumayya kayan da bayi ke sanyawa yace ta bawa bimbii ta saka ta fito da ita a sace ya tura mata wannan baiwa ta zama a madadin bimbii, saida sumayya ta bari an gama shirya bimbii daga ita sai ita tayi saurin sanyata ta cire wannan kayan dake jikinta sannan ta shigo da wannan baiwa ta cire kayan jikinta sukayi musaye, ita baiwa ta zauna a madadin bimbii ta rufe fuskarta da mayafi, sumayya sanya jaririn cikin kwando bimbii ta fita dashi batare da kowa ya ankara ba ta nufa inda sumayya ta fada mata don daman tasan ko'ina cikin gdn, sai qasa take da fuskarta kar wani ya ganeta hk har ta samu ta fice daga 6angaren sarauniya ta nufi daidai gdn magani wurin da sumayya ta fada mata ta hangi inuwar mutum tana waigawa ta hangi ubaid ta qarasa, batare da wata doguwar mgn ba ya samu ya qarasa da ita 6angaren prince akbar ta shige, wannan shine zahirin abunda ya faru a 6angaren sarauniyya, lkcin da bimbii ta shiga ta tarar da prince tsaye yana sauraron qarasowarta don ya aminta da hikimar hadiman dayasa wannan aiki yasan dakyar ne a samu kuskure, yana ganin bimbii ta shigo yyi murmushi tare da bude mata hannayensa, tsayawa tayi don kunyarsa take ji, murmushi yyi ya qaraso ya amshi yaron dake hannunta ya rumgume shi a qirjinsa itama ya janyota ya rumgumeta suka qarasa bakin gado suka zauna hannunsa yasa ya dago da fuskarsa data 6oye a saman kafadarsa yace" kin zama sarauniyata nafi kowa farin ciki da hkn kefa?" shiru tayi masa ta qara 6oye fuskarta a kafadarsa, juyawa yyi ya kwantar da babyn dake hannunsa a saman gadon ya dawo ya zauna ya sake janyota jikinta suna fuskantar juna, numfashinsu na haduwa, bakinsa ya matso dashi daidai da dan mitsitsin bakinta ya dora saman nata a hnkli kuma ya soma kissing nata cikin wani salo mai saurin rikita lissafi, bimbii kam idanunta na lumshe, sun yi nisa cikin wannan yanayi suka ji qarar kukan babynsu yana wani irin kakari, a rude suka saki juna suka juya don ganin me ya same shi................






Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank,saiki tura screenshrt na payment ta whatsapp ta wannan layi...07041195806.....






Alkalamin Bintuu ne......

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


2 Comments On DAREN GOMA SHA HUDU
avatar
abubakar-sunusi

1 year ago

Reply

I want to read the novel

avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Replying to abubakar-sunusi

Click The READ THIS NOVEL button

Please Login or Register in order to submit comment