Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

likitoci suka shigo,sai a lokacin ta kula da Mom da Aryan da Amrah a bakin ƙofa basu shigo ba,sallamar su Mama yay sannan ya shiga zuba lafiyar yaga komai ya dai² Na'oururin jikinta ya cire tare da ɗaura mata wani drip ya sanya allurar bacci a ciki,kallonsa tayi tace"dr shi yaushe ne zai farka"jinjina kai yay tare da ƙarasawa wajan Irfan ya shiga duba shi yace"koda yaushe zai iya farkawa insha Allah"yana faɗin hakan yasa kai ya fice,cikin ƙaramin lokaci bacci yay gaba da ita.



Jessica pov
Abin duniya ya isheta ga wata jaraba da take damunta sai kuma wani sauyin ya nayi sometimes ta kanji jiri da kuma ciwon kai na damunta.

A nutse take drever tayi kyau sosai tana tafe tana tauna cimgum,a haka ta ƙarasa asibitin Aminu kano parking tayi a parking space dake harabar asibitin,fituwa tayi ta nufi office ɗin dr dake dubata tana shiga ta iskeshi zaune yana duba p.c nasa,zama tayi kan kujera kafin tace"sannu fa" kallonta yay na wani lokaci kafin yace"yauwa yanzu kuma me za'ai maki?"ya mutsa fuska tayi ta shiga labarta masa abinda yake damunta,dariya yayi hadda riƙe ciki saida yay son ransa sannan ya dubeta yace"alamu na nuna bariki tayi riba ko?ke baki san ko a littafinku babu kyau aikata irin abinda kike,ko shima kun sauya shi?"bata kulashi kamar yadda shima baisa ran jin komai daga gareta ba,wata robber ya ɗauko ya bata yace taje tayi fitsari ta kawo masa,amsa tayi tare da barin ɗakin 10min ta dawo ɗauke da fitsarinta amsa yay tare da ficewa daga ɗakin bai wani jima ba ya dawo hannunsa ɗauke da papper murmushi yay mata tare furta"congratulation you have a perigenet" waro ido tayi tare faɗin "kasan me kake faɗa kowa?"jin gina yay da jikin kujera tare da faɗin"nida aikina kinga kowa zanfi kuwa fahimtar abinda nake faɗa"tsaki taja tare da amsar papper tayi waje hanyar emagency tabi tana son ganin wani likita tun daga nesa idonta ya sauka akan Aryan fuskarta fal farin ciki,ta nufi inda yake,da burcewa tayi ganin bashi kaɗai bane,murmushi tayi tare da faɗin"Sannu Aryan ina abokin naka waye babu lpa kuma"murmushin gefen baki yay mata kana ganinsa kasan na zallar mugunta ne"boddy ne da matarsa babu lpa"ya faɗa yana nuna mata ƙofar ɗakin wacce kana iya ganinsu a kwance kasan cewar ƙofar glass ce,a ɗan tsorace da kuma sakin baki tace"kut wacece mai tsautsayince ta kawo kanta"kafin Aryan yay mgn Amrah tai saurin ƙara sawa wajan Jessica tace"ohh hello Irfan ki kazu nema hala? yana da kyau kisan keda Irfan har abada,bazai taɓa zama da mace mai irin halinki ba,kada kiyi tunanin banbancin Addini yasa nake faɗa maki haka,ko ɗaya halinki shine yaja maki hakan...ya isa haka"cewar Mom,shuru Amrah tayi tare da zabgawa Jessica harara bata ƙaunarta sam halinta na dabanne dana sauran ƴan uwan masu irin addininta,Aryan shuru yay tare da jingina bayansa a jikin bango ya zubawa matar tasa he wish ya jita a cikinsa yana addu'ar yaga wannan rana mafi muhimmanci a wajan,wani killer smile Jessica tayi tare da murza ƴan yatsunta ta kalli Amrah tare dayi mata warning alamar zata gani,fasa ganin likitan tayi ta juya rai ɓace ta nufi mota,cikin motar ta faɗa tare dayi mata key tabar harabar asibitin ta nufi gidan ƙawarta Zuly.
Bata daɗe a hanya ba ta ƙara gidan,gidane babba da kuma ɗa kuna birjik da alama gida karuwar ne,wasu ƴan mata ta gani zaune suna shan shiisha,saurin shigewa ɗakin Zuly tayi tana fitar da numfashi,ɗaya daga cikin ƴan matanne tace"wannan fa mai zafi ce,da alama ba ƙowa ce,nidai tayimin yaseen"harara Hariri ta watsa mata tare da miƙewa tsaye tace"ban gaya maki indai ina tare dake babu ruwanki da sha'awar wata ƴar mace ba,nice taki kema kece tawa har abada"tana faɗin hakan ta shige ɗan ƙaramin ɗakin dake kusa dasu.

Wata dariya Zuly tayi tace"hhh keman yaya akai kikai sake har Black man ɗinki yay aure soon haka?"ya mutsa fuska Jessica tayi kafin tace"nidai meye mafita?"..mafita guda ɗaya ce zuwa biyu idan kin amince.."wacce amincewa kike mgn kinsan akan abinda na keso bana waisting time right?"tashi Zuly tayi ta nufi dressing mirrow ɗinta ta ɗauki wata ƙaramar kwalba tare da dawowa wajan Jessica ta miƙa mata kwalbar tare da faɗin"wannan shi ake kira da *Flibanserin* over feelings yana haukata namiji fiye da tunaninki har yafi wanda na baki aiki uhm zaki sha mamaki domin bazai tsallake maki 5min ba kiyi ƙoƙarin sanya masa cikin abin sha wannan shine hanya ta ɗaya,hanya ta biyu kuma zansa a ɗauko min matar tasa a asibiti in kawota nan na haɗata da Harira nasan zata kawo huta ya kika gani🤨?"wata muguwar dariya Jessica tayi tare da miƙewa tsaye ta juya faffaɗan wais ɗinta tare rolling eye ball ɗinta tace.


Hospital pov

Misalin ƙarfe 10 na dare kishin giɗe take jikin gadon asibitin bayan ta gama kammala duk wasu sallolin da suke kanta,ware idonta tayi tare da watsatsu kan Amrah tace"waishi yaushe zai farka ne?"ta faɗa idota na cicciko da hawaye alamar zatai kuka,kafin Amrah tayi mgn na'ourar jikinsa ta fara ƙara gaba ɗaya suka maida hankalinsu kansa,a hankali ya shiga buɗe blue eyes ball ɗinsa wanda eyes lashis suke kwance saman idonsa,ya mutsa face yay yana jin jikinsa babu daɗi gaba ɗaya brain ɗinsa ta tsaya da aiki,shuru yay yana tunanin a ina yake nan ɗin,zare drip ɗin yay da bakinsa😳jini ya fara zuba,cikin sauri Amrah ta ƙarasa wajansa tare da faɗin"bloody yaya jikin naka?"sauri tattare jikinsa waje guda yay idonsa ya shiga zubar da hawaye,ware ido Jiddah tayi cike da tsoron abinda Irfan ɗin yake wasu hawaye ne itama ya shiga zubuwa daga cikin idonta tana jin wata zazzafar ƙaunarsa na ratsa ko ina na jikinta,ƙara matsawa Amrah tayi tare mai² ta abinda tace "blood yaya jikinka?"murmushi tayi tace"ka tsora tamu da yawa"shima murmushi yay yace"ka tsora tamu da yawa..




*Afuwa for the late update 2days bana da lpa ne wlh yan zuma na gaji da tambaya*


Ina jiran jin ra'ayinku akan wannan page ɗin duk da bashi da yawa.


Gdy ta musamman ga *Haleemerht Muhammand Umar* ina jinjina maki sosai ina ƙaunarki😘
[12/9, 5:55 PM] +227 99 46 01 51: ```💞HEARTBEAT💞```
*JIDDAH*

NIMCYLUV

```CHAPTER 36-37
POLICE```

```Wattpad@nimcyluv```


Chapter


Waro ido Jiddah da Amrah sokai domin abin ya fara basu mamaki,kallon Jiddah Amrah tayi tare da faɗin"Zonan Jiddah yau ina kallon ikon Allah"idon Jiddah fal hawaye sai ƙifƙitasu take zuciyarta cike da rauni ta ƙarasu bed ɗin da yake zaune ya cure waje guda ko mutsi ba yayi,zama tayi kusansa tare da kama hannunsa lokacin hawayen idonta ya gama wake mata fuska,lumshe manyan narkakkun idonsa yay tare da taune red lips ɗin masu ɗan tudu gaba ɗaya ya jiƙe da sliver ɗinsa,yana jin yadda ɗumin hannunta amma baisan wace itama bai san tayaya zai fara magana da ita ba,gaba ɗaya kallonsu yake kamar ba mutane ba amma su kaɗai ya sani cikin rayuwarsa dasu ya fara tozali bashi da wanda ya fisu,ƙoƙarin zare hannunta tayi daga cikin nasa yay saurin damƙe hannunta ba tare daya buɗe idonsa ba,kafin suyi magana dr ya shigo cikin saurin ya ƙarasu wajan Irfan ɗin, Irfan yana ganin zaika mutsa yay saurin miƙewa tsaye tare nufar wajan da Jiddah take yana ya maƙale jikinta daga baya ya shiga girgiza kanta,kuka Amrah ta fara tare da faɗin"wai dr what is going on ne,na kasa fahimtar komai kada abinda nake tunani ne ya rabb ka kawo mana ɗauki"yarfe gomi dr yay tare da faɗin"Madan dole sai munyi bincike akan brain ɗinsa zan iya fahimtar abinda yake faruwa,kuma naga da ƙyar zai yarda a duba lafiyarsa"kuka Jiddah ta fara tare da ƙoƙarin cire Irfan daga bayanta amma yaƙi yarda,muryarta na wara ta juya gabansa sukai parcing ɗin juna kallonsa take shima ya shiga kallonta a hankali ta shiga magana dai² kunnansa tace"Ir..fan"kwaɓe fuska yay tare da langwaɓar da kansa a shoulder ta shima yace"Irfan"damm zuciyarta ta bada sauti mai ƙarfi hawayen fuskarta ya ƙaro ta rasa abinda za tace sai kawai ta faɗa jikinsa ta saki kuka ta shiga mgn"no kada hakan ya faro dakai Ni Anty Amrah Twinst Buddy Mom Dad duk muna buƙatar rayuwarka da tunaninka kada kayi mana haka ba zamu jure ba"lamu yay jikinta yana sauraran abinda take cewa amma babu kalma ɗaya daya fahimta kamar yadda itama bai fahimci wacece ba,da wannan damar dr ya samu damar bashi injection lokaci kaɗan jikinsa ya saki numfashinsa ya fara fita a hankali alamar bacci zai ɗaukesa,cikin dr ya kamashi tare da kwantar dashi a kan bed ya bawa su Amrah umarnin barin ɗakin,dake Jikin Jiddah da sauƙi sai rashin ƙwarin jiki babu musu Amrah ta kama hannun Jiddah suka fita waje.
Suna fita dr ya junawa Irfan wani abu a kansa ya shiga bincikensu na likitoci,lokaci kaɗan ya kammala murmushi dr yay tare da cire masa abinda ya juna,wayarsa ya ciro daga aljihu wata number ya shiga ringing biyu tayi a kai picking call ɗin,shuru dr yay yana sauraran abinda ake faɗa daga can ɓangaran,gyara tsaiwa yay tare da faɗin"Madam inaga basai anyi masa wannan Allurar ta hauka ba,da alama yay loosing memory kinga aikin zaizu da sauƙi"shuru yay da alama ana masa mgn daga can ɓangaren kafin ya numfasa yace"gsky Madam abinda Irfan yake ya huce ace masa pretending kawai dai kushirya plan ɗinku kafinsu bar asibitin"daga haka sukai sallama ya kashe wayar.




Aryan pov
Hankali tashe ya ƙarasu asibitin domin Amrah ta gama gaya masa komai a waya,yana zuwa ya gansu zaune lokacin hadda Dad da Abu suna zaune suna tattaunawa,bai tsaya ko ina ba sai office ɗin dr a zaune ya sameshi yana waya,katse kiran yay ya miƙawa Aryan hannu suka gaisa ya bashi wajan zama"no thank basai na zauna ba inason ta kaddar sallama yanzun nan"da mamaki dr yake kallon Aryan kafin yace"a wannan conditon ɗin da Irfan ke ciki kakeson a baka sallama kayi tunani kowa?"cije baki Aryan yay tare da kallon dr yace"ni bana tunani ai abinda na yake shi nake aikatawa tunda nace kabani kawai kabani tun kafin fushina ya kufce a kan ka"dr baice komai ba ya shiga rubuce² a papper saida ya gama sannan ya ɗaga kai yace" ga sallama nan as long as your wish"daga haka bai kuma cewa komai ba yaja P.c ɗinsa yaci gaba da latsawa,Aryan na karɓar takaddar yay waje hankalinsa kwace ya nufi wajansu Dad ya durƙusa har ƙasa ya gai dasu tare dayi masu bayanin komai amma a nan zasu bar Jiddah zuwa gobe ta ƙarasa karɓar drip ɗinta,gaba ɗaya sukai na'am da abun duk da Irfan ɗin ba wani lafiya garesa ba,nan suka shirya tafiya Dad da kansa ya ɗauko Irfan tare da sashi a bayan mota shima ya shiga Abu kuma ya shiga gidan gaba Aryan ya zauna mazaunin drever,suka bar Amrah da Jiddah acan itama anjima zata koma gida a hankali yaja motar suka bar harabar asibitin suka nufi jan Bulo gidan Dad.






Hospital pov
Misali 11 na dare wata mota tayi parking a bakin asibitin,mutane uku ne suka fito daga motar cikin manyan kaya na alfarma,babu inda suka tsaya sai emagency a ƙofar wani office suka sami dr da alama jiransu yake cikin sauri yay masu jagora zuwa room ɗin da take ciki,baka ganin komai a ɗakin sbd hasken ɗakin da aka kashe,kwance take flat numfashinta na sauka a hankali hannunta ɗauke da drip sauranne suka tsaya a harabar ɗakin guda ɗaya kuma ya nufi bed ɗin da take kwance hannu yasa da nufin ɗaukanta yaga an kunna fitila bai kawo komai ba dan haka yaci gaba da ƙoƙarin ɗaukanta kamar daga sama yaji ance"don't toch her"sauri ɗaga kai yay tare da juyawa nan yay tozali da samari guda 2 Irfan ne tsaye sanye t.shirt ash colour sai wando three gauter ya zuba hannayensa cikin aljihun wando haɗi da lumshe idonsa haiba da ƙiba da izzarsa sun ƙara fitow idan ka ganshi ba zakace shine yay magana ba,gefe guda kuma Aryan sanye da jallabiyi black colour mai ƙaramin hannu,ƴan sanda ne suka shigo tare da kama mutane sannan sukayo kan dr cikin tashin hankali yace"ni...ni kuma me nayi?" Irfan ne ya taka zuwa inda dr yake kallonsa yay sosai tare faɗin"kaga nai maka kama da wawa ne,a zahiri na riga 4eyes farkawa amma abinda naji kana faɗe a waya lokacin daka shigo zaka duba ni shine ya tayarmin da hankali,kasu ganin baya nan sannan ta dalilin hakan a ɗaukemin mata wanda da alama duk wanda ya saka hakan yana da wani plan ne,shi yasa dana farka nayi wannan abinda kaga nayi hakan yasa ka fasa yimin wannan allurar daka shirya yimin ita,nine da kaina nasa Buddy yazu ya amshi sallamar kuma ni nace abar 4eyes nan ta hakan zan kama wanda sukeson raba zuciyoyinmu"yana faɗin hakan ya nufi bed ɗin Jiddah da take kwance tattausan hannunsa ya saka ya ɗauketa zuwa jikinsa,ajjiyar zuciya ta sauke ta ƙara shigewa jikinsa tana fitar da numfashi da alama bacci yay mata nisa,a hankali yakai bakinsa saitin kunnanta cikin lion voice yace"i'm sorry jerryn no mattet what we are to getter"ƙara mannata da ƙirjinsa yay tare juyawa suka bar room shi da Aryan,dr kuma ƴan sanda suka tisa keyarsa zuwa mota inda sauran suke,a hankali Aryan ke juya kan motar kallon titin yay yaga saho duk ya ɗauke hakan yana nufin dare yay sosai dan sha biyu saura,"Buddy nifa an cugeni yaseen"cewar Aryan taɓe baki Irfan yay kamar bazai magana ba sai kuma yace"like how"lumshe ido Aryan yay kafin ya buɗe baki yace"Amrah a gida zata kwana ita da twinst fa nida nasu jin ɗumin matata"banza Irfan yay masa ba tare daya tanka saba gaba ɗaya hankalinsa nakan Jerrynsa wacce take bacci hankali kwance"mtwws wai kana jin ina mgn"still idonsa na kan Jiddah yace"to ubanka kakeson nace ma,daman aikai manyan mata ne"wani wawan birki Aryan yaja a tsakiyar titi wanda yasa Jiddah tsorata harta ƙanƙame Irfan ta kwaɓe fuska da baki zatai kuka,naushi Irfan ya kaiwa Aryan ya goce shima kamar zai kuka yace"Allah yasa bamu yafe ba ko Jerryn ka firgitamin matana haka nan,sleep well my jerry kina jikin mijinki notin happen"saida Aryan yay dariya mai isarshi sannan yaywa motar key yaci gaba da dreving suna tafe yana mitar an masa kwacan mata a wannan lokacin yayinda Irfan yay masa banza,a haka suka ƙarasa jan Bulo a parlo suka tarar da Mom da kuma Dad hadda Amrah twinst kam sun daɗe dayin bacci,da sallama suka shiga parlon babu inda Irfan ya zarce sai ɗakin Amrah yana zuwa ya shimfiɗeta saman bed kayan bacci ya ɗauko ya sauya mata tare dayi mata addu'a yaja mata balget ta ƙaro gudan A.C sannan yay waje yana zuwa yaga babu Aryan shima sallama sukai da iyayen nasa ya nufi flat ɗinsa na gidan,a nan ya sami Aryan harya kwanta tea ya haɗa mai zafi tare da matsa lemon tsami wajan biyar a ciki ya shanye,ruwa ya watsa jikinsa sannan ya ɗaura bathrop ya faɗa bed bakinsa ɗauke da addu'ar bacci tunaninta fal zuciyarsa bacci ya ɗaukesa.. Asuba ta gari kwarzun namiji inji Jiddah😂



*Afuwa Afuwa Afuwa nima ba a sanraina hakan ba,amma lafiya tafi komai gaba ɗaya bansa inda kaina yake ba,bana da ƙarfin yi maku typing kunsan da ai ba haka nake baku ba kuci gaba da hƙr a ƙara sani cikin addu'a i luv u all😍🥰ina gdy da addu'ar kuma inajin daɗi sai mun haɗe a next page...*
[12/9, 5:55 PM] +227 99 46 01 51: ```💞HEARTBEAT💞```
*JIDDAH*

NIMCYLUV

```CHAPTER 38-39
EVENT

Wattpad@nimcyluv```




مشا ألله 🙌🏻الهمدلله رب العالمين 🥰🥰👏🏻الله ءبن غديي ان غديي ءدخخن مسين ء دج اندسك 😘


Chapter


Washe gari da safe gidan yay shuru ba kajin komai sai ƙara a kicin masu aiki na ƙoƙarin kammala breakfast,Mom ce ta fito cikin shigar baccinta sai a baya data ɗura a sama, cikin kicin ɗin da shiga nan ƴan aikin suka zube suna gaisheta amsa masu tayi cikin fara'a da sakin fuska,Irfan da Aryan ta shiga yiwa breakfast kasan cewar basa cin na ƴan aiki,fatan dan kalin turawa tayi wanda yasha kayan lambu da kifi,sai agada data soya masu tare da kunun gaɗa,daga ƙarshe ta dafa coffee mai daɗi ta joye a flask ta gama jerawa a daining table sannan tayiwa su Hansai sallama ta koma flat ɗinta domin shiryawa,misalin 10 ya shiga buɗe idonsa ganin ya makara yasa yay saurin tashi ya miƙewa ya nufi bathroom cikin saurin ya sutale kayan jikinsa kasan cewar garin da alamun hadari tunda damuna ta fara tsananta yasa ya kunna hiter ya samu ruwan zafi dai² da yadda fatar jikinsa zata iya ɗaukan ya fara wanka a gaggauce,bayan ya gama yay brush sannan ya ɗaura bathrop a jikinsa ya fito daret wajan dressing mirrow ya nufa ya shiga gyara sumar kansa da take ɗigar ruwa saida ya gyara tsaf sannan ya ɗauki cream mai ɗan zama a jiki ya shiga gogawa dark black skin ɗinsa turare ya ɗauka body spray ya fesa a jikinsa wajan wadrop ya nufa ya buɗe tare da zubawa kayan nasa ido yama rasa wanne zai ɗauka,ana haka Aryan ya shigo tare da faɗin"mai hali baya fasa halinsa ana tunanin kayan sawa ne?" ..uhm"shine abinda ya fito daga bakin Irfan ganin haka yasa Aryan ciro masa wani cofie ɗin yad mai laushi da kuma manyan zafi shara²,ɗago kai yay yaga ashema irinsa Aryan ɗin ya saka,cikin sauri ya zura riga tare da saka wandon ɗinkin yay kyau sosai mai ƙaramin hannu ne rigarma irin ƙaramar nance iya gwiwa tashe sumar kansa ya ƙarayi ta kwanta luff har wuyansa sai sheƙi yake,Ohud mood ya ɗauka ya shiga fesawa a jikinsa saida ya gama laƙe² ƙensa ya ɗibi wayoyinsa da kuma keys ɗin motocinsa"oya muje"cewarsa dry Aryan yay yace"yaron nan wai mekayi da lemon tsami ne jiya?"ya tsuna fuska Irfan yay kafin yay murmushinsa wanda yake tafiya da tunanin duk wacce tayi arba dashi yace"feeling pain ya kamani jiya so i don't have any choice wanda ya huce nada lemon"kafaɗarsa Aryan ya daka tare da faɗin"eyee duk saurinka saina rigaka" ...caf and so what kuma ka zama ayo mana zanfi gane hakan😂and wlh saina riga ajjiya yara matasa bama mata ba niɗin ba lusarin namiji bane i'm telling u za kace na faɗa maka"shida Aryan banda dry babu abinda yake shima Irfan murmushi kawai yake wanda yake ƙara ƙawata fuskarsa a haka suka nufi waje,a parlo suka tarar da familyn gidan wajan Mom ya nufa yace"mrng mom"mrng too son ya ƙarfin jikin naka?"..felling better Mom"ɗan hug ya bata tare dayi mata peak a goshi ya nufi wajan Dad,tsaye yaywa Dad sai turo baki yake gaba kamar zaiyi kuka yace"mrng"murmushi kawai Dad yay yasa hannu ya jawoshi zuwa jikinsa tare da faɗin"i'm sorry my luv i knew i'm hurt u i don't have any choice daya huce hakan brain ɗina ya gaza aiki am sorry zuwa yanzu na gama fahimtar komai jibi zamu shiga court"ajjiyar zuciya Irfan ya sauke ya ɗanyi hug ɗin Dad ɗinsa cikin muryarsa mai Amoo yace"sorry Dad" ...lallai ƴan samarin nan nice baku gani ba kenan ko?"cewar Amrah taɓe baki Irfan yay kafin yace"aikin makaro babu batun gaisuwa yanzu tunda kika auri under age"dariya aka fashe da ita duk wajan harsu twinst da suke jikin Aryan kwaɓe fuska tayi tare da kallon Mom tace"mom kin gansa ko?"..ke rabu dashi shida ya auri adult fa ƴar yarinyar ƙarama zaiga tarin shirme fa"nan dry aika shikam gogan ko ajikinsa sai wayarsa yake dannawa Dad ne yace"yaran aisu ake yayi yanzu sunfi shiga rai nima ina nan ina laliban ƴar 15 na ƙara da ita"kafin suyi magana Jiddah ta fito ƙamshin turarenta daya daki hancinsa shine ya tabbatar masa da haka cikin nutsuwa ta ƙarasu wajan sanye take da milk ɗin lass mai red ɗin flower ɗinkin ya amsheta dake tana da faɗin hips shiya saka ɗinkin Bubar ya zauna a jikinta babu ɗan kwali kanta sai red vail data yafa akanta haka ya bawa gashinta damar bayyana cikin sauƙi,a hankali ta shiga gaisar da mutanan wajan muryarta a raunane kamar wacce yake shirin kuka,kallon ɗaya tayi masa ta ɗauke kai kamar daga sama taji yace"baki iya gaisuwa ba ko?"saurin lumshe ido tayi ta shiga taune lips ɗinta tare da ƙoƙarin ware laɓɓanta taɓe baki yay tare da miƙewa ya nufi wajan daining,ɗaya baya ɗaya suka miƙe zuwa daining ɗin hannu Mom tasa ta ɗaga Jiddah tace"rabu dashi beb yau faɗa ya keji naga alama basai kin kulashi ba"sadda kanta ƙasa tayi tabi bayan Mom zuwa kan daining saida akai saving ɗin kowa sannan Mom tace"gobe akwai event dana shirya maku get ready after event ɗin za'a kai maku matanku gida janku wanda kuka gini Amrah zata bar gidan da take ciki son zaibar wannan gidan na Farawa misalin 10 na dare za'a Meena event nasan baku na matsalar kayan sawa sai kuyi anko"gdy sukai mata itakam Jiddah kanta a ƙasa take mamakin event ɗin da za'ai to waye yay aure kasan cewar bata da amsa yasa tayi shuru da bakinta,coffee ɗin kawai take sha haka nan taji gabanta na faɗuwa duk abinda take yana lura da ita yay mata ban zane sbd su Mom a haka suka kammala shida Irfan sukaiwa su Dad sallama kubar gida,Mom kam suna fita ta miƙe ta fara haɗa kayan gyara Amarya Jiddah domin Mom gwanace ta iya komai na gyaran jiki ita dai Jiddah da shuru kawai tayi sbd kunyar Mom.







Police pov
Bayan sun gama criminal ɗin babu inda suka tsaya sai police station gaba ɗaya suka sakasu a bayan kanta suka rufe,an tambayesu waya sakasu amma fur sunƙi magana ganin hakan suka saka aka fara dukansu kamar za'a kashesu ɗaya daga cikinsu daya sha wahala a galabaice yace"oga Zuly ce ta bamu kuɗi masu yawa tare dayi mana bamu kanta sannan kuma zata haɗamu da wasu ƴan matan"tsayawa yay da sukan nasu mamaki fal ransa jin macace tasa akama matar wani ko meye nufinta ohuu"wacece Zuly a ina take?"numfashi wani guy ya sauke yace"oga sheɗaniyace fa kuma ƙaruwa ce gidan kanta ne tana tara ƴan mata kala² gidan nan a Saban gari"a.c.p bai ƙara cewa komai ba yasa yaransa suka shirya suka nufi Saban gari.


Basu daɗe a hanya ba suka ƙarasa gidan,a bayan gidan sukayi parking motarsu tare da fitowa suka nufi cikin gidan,tun daga waje su kaga alamar gidan karuwai ne sanin hakan yasa suka danna kansu cikin gidan kowa yana ɗaki dake dare ne baka jin sautin komai saina fitar numfashi mutane😂ɗaya bayan ɗaya suka dinga fito da mutanan gidan wata da namiji wata kuma da mace abun babu kyan gani sai wanda ya gani(ubangini ka kiyayemu da kiyayewarka,Allah ka tsare dukkan musulmi da aikata abinda addini ya hanemu dashi,sharrin mutum sharrin ƙawa sharri aljani Allah ka kiyaye zuƙatanmu آ مين ياربل ءلمين ).

Oga Zuly na tsaka da juyi akan bed sbd da jaraba ta kama lodawa kanta drugs sbd wani guy da sukai alƙawari zaizo kuma shuru bai zuba hakan yasa take ta malele kowa akan bed ɗin nata,banko ƙofar ɗakin da akai shine

Please Login or Register in order to submit comment