Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kula tace.
"Toh haka ma yayi koma me nene, duk ciki Yaran maryam kece me shegen taurin kai kamar ganda, baki jin ko fiɗis, da wasu soyayyun idanunki nan kamar soyayyer gyaɗa, kik cika fitina bana wasa ba, gaji duk hakurin irinta Badaru sai da kika sashi yaƴi miki biɗibiɗi, haka kawai kin zauna ana jibgarki kamar wata lusara. Shashashar wofi"
B'antara goronta tayi cikin nutsuwa tana taunawa, Umma tace.
"Wallahi Alhaji ka bani mamaki yadda, ka ware karfinka akan safinatu, yarinyar da tun tasowarta muke zargin aljanu ne da ita, shine zaka ware karfinka akanta dan wannan abun ya faru. A cikin gidan nan har kake zargin yarka dan kaddara ta faɗo mata, toh kasheta."

Ummi kan falon ta bari, bai kulasu ba ya nufi dakin Ummi, wacce ta fito ban ɗaki zatayi sallar azhar, cikin bala'i yace.
"Kice ta bar min gidana kafin na dawo."

Ko kallo bai isheta ba tasaka hijab ɗinta ta tadda sallah,
"Na gaya miki ta fita tabar min gidana"
Banza tayi da shi, har ya fito ya dawo cikin zafin rai yace.
"Idan kika fita, dan kareta ban yaf."
Mika alamuranta tayi ga Ubangiji ta cigaba da sallarta, tana idarwa ta shiga zuba kayanta a cikin babban a kwatinta, sannan tafito zuwa falon ta kalle ni yadda nake kwance na takura guri guda ina kuka, tace.
"Ki shiga ɗakinki ki kwaso kaƴanki."
Mikewa nayi na kalleta naga ta kauda kanta, girgiza kai nayi cikin tashin hankali nace.
"Ummi!!!"
Yatsar hannunta ta ɗaura bisa bakinta alamar nayi shiru.
Mikewa nayi naje nayi yadda tace,
Ina gama hada kayana najanyo akwatin na fito dashi, dai dai shigowar Nannah, a firgice tace.
"Ina zaki Binti"
Sunkuyar da kaina naƴi nace.
"Ummi ce tasani na fito da kayana!"
Riko hannuna tayi, na ɗago tare da kallonta, kwantaccen gashin dake gefen fuskarta sak da nashi, har ɗakin ta kaini tace.
"Maryam lafiya?"
Murmushi me ciwo tayi sannan tace.
"Yace tabar mushi gidansa, toh meye amfanin zamana a gidanshi tunda bai yarda da kaddara ba. Ni yanzun damuwata Safinatu ce, ko zata gaya min cikin waye."

Jingina a jikin bango na zame a hankali tare da sake kuka mara sauti nace.
"Allah na na cuce kaina ko na gaya muku cikin waye bazaku yarda b.."

Ji nayi an shure ni da kafa, tare da ɗago ni a zafaffe akayi waje dani, har bakin get ya cillani na zuɓe a gun.
Ummi naga itama tafito tare da Nannah, sam Abba kamar wanda ya fita hankalinshi, ranar wanda bai san meke faruwa ba ya sani, a gaban ɗinbu mutane Abba yace min.

"Kisaka a ranki ke matacciya ce, kin jima da mutuwa a cikinmu, bamu da ke a cikinmu, karki kuma takowa cikinmu kije duniya ta isheki riga da wando, kamar yadda kika kwarar min da mutuncina naki sai yafi nawa zuɓewa, kuma idan baki bar min kofar gida ba yan sanda zan kira miki, bana son ganinki."

Yana gama gaya min haka yasa key ya rufe gidanshi, ya kalle Ummi yace.
"Idan kika saka kafarki kiƙa tsallakw bakin get ɗin nan a bakin aurenki."

Zuwa nayi nayita buga get ɗin ina kuka tare da cewa..
"Don Allah Abbana karka kore ni, daga gareka don Allah ka rufa min asir..."
Ji nayi an riko hannuna, na juya a sannu Abdul ne idanunshi sunyi jajjur, yaja hannuna a har cikin motarshi, zanyi magana ya rufe min bakina da yatsar hannunshi.
"Ya isa muje gidana."
Gidanshi muka nufa wanda yake can doctors quarts, muna shiga get ɗin gidan Matarshi Sophia, ta fito fuskarta a murtuke ta tare kofar shiga gidan, wani irin kallo take mishi. A sani na Abdul yana da matuƙar hakuri da rashin son magana, kuma ban taɓa tsamani a kaina zai iya zarta da hukunci har haka ba sai da naji yace.

"Ko ki bani hanya na shige ko kuma ki wucce gidanku na sake ki sa..."
"Abdul!!!"
Na kira sunanshi a raunane, na girgiza mishi kai cikin kuka nace.
"Don Allah karka ka rasa, ni na hakura zan nime wani gurin tunda bata son zama dani, duk nice na fara. Kabarni na amshi hukuncina daga makusantana."

"Koda za a hukuntaki, bata wannan hanyar ya dace ba a nemi wani mana."

Tunda taji ya saketq jikinta ya fara rawa, ta shiga kuka. Ɗakinta ta koma tare da ɗauƙar wayarta ta kira Layin babanta ta gaya mishi, shi kuma ya kira Abba. Ina zaune Abdul na gefe muka ga Abba a kanmu, a razane nayi bayan Abdul, cikin faɗa yace.
"Zo ki ficce musu makira kawai zaki kashe masa aure tunda ke bakiyi ba bari ki raba na kaninki ko kunya baki ji ba kin ɗiɓo jiki kinzo gidan mutumin kirki zaki lalata masa gidanshi zoki fita."

Rike rigar Abdul nayi tare da kifa kaina a bayanshi ina shashekar kuka, maganar da Abdul yayi shi ya kashe ni da mamaki, yace.
"Idan Safina tabar gidan nan wallahi Sophia tabar gidan kenan har abada, kuma gabaki ɗaya fa, ba wai zata dawo bane. Can gidanka ne kana da ikon koran kowa nan kuma Abba nawane, ina da ikon zama da kowa. Dan haka da safina da cikinta su zauna a nan hae inyi nawa na kaina. Sannan ni a yanzun son cikin nake tana haihuwa zan haɗa da nawa baki ɗaya na rike su."

"Abdul!! " na girgiza shi tare da kiran sunanshi...........

Chaiiiiiiii Yasin nagaji Anya Book 2 bazan saka shi a kasuwa ba😒.......
#MJ#HZƘ# Vote......


Oum Muwaddah....
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITERS ASSO_*

*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*

  *Wayyo Feena na tausaya miki ina Ashraf kazo😂 Team Sulfee2020 ko😉*

KYAUTAR SHAFIN NA KU NE MATAN QUARTS MUCH LOVE❤


Page.١٩

    "Ni kake gayawa Magana Abdullahi! Ni da nayi wahalarku. Dan na nuna ɓacin raina zaka saki matarka, ni Abdullahi!"
 

"Abba yadda kabi ba haka kowani dattijon Uba yake yi ba, sam abinda ka aikata tamkar a zamanin da ilimi bai wadatu kowa ba, kai...."
  
   "Kafito kace min Jahili mana! Sai masan kaji haushin abinda naiwa Yar uwanka, kuma dole tabar gidanka yau ɗin nan" ya faɗa a zazzafe,
        "Indai Safinah zata bar gidan nan toh wallahi Yar abokinka zata bar gidan nan ba makawa, dan gidana ne ina da iko akan kome na gidan, tunda fa shigo me fidda ita sai ya shirya."

       Wallahi ban taba shiga matsananci tashin hankali a rayuwata irin na yau ba, rigima ta kaure tsakanin Uba da D'a, ba zan iyace na fahimci kome ba. Sai dai n daina jin kome da kuma ganinsu sannu sannu duhu ya mamaye idanuna na zuɓe a kasa.

   Kaɗa rigarshi Abba yaƴi ya fita tare da kashedi zabga min rashin mutunci idan na mutu kar  a qawo mishi gawar karuwa gidansa, sannan ya bawa sophia dama da zaran na mata iskanci ta min tijara, karta raga min.

       "Wannan ikon a gidanka zakayi ba a gidana ba, kuma koda wasa kika taɓa min ran Yar uwa zawarci ya aureki."

Yana gama gaya mata haka ya ɗauke ni zuwa gun motarsa, buɗe masa motar me gadin gidan yayi. Shi kuma ya sakani sannan ya koma ma zaunin drive ya tadda motar muka fita bayan an buɗe masa,

     ***
"Maryam! Har kin haifi d'an da zai gaya min magana ko? Toh na zare hannuna akan Abdullahi da Safinah, suje su nemi wani  uban bani ba,"
    Cikanka Ummi bata ce mishi ba, tayi cikin da sauri ɗakinta dan taji karar wayarta.

       D'auka tayi ta kanga a kunne.
"Ummi na kawo Feener asibiti! An bata gado."

  "Toh Abdul zan duba na gani ko zan sami zuwa. Koda ban zo ba Nannah da Hajja zasu zo"
   Ta gaya mishi cikin wani irin murya me cike da sanyi da tarin damuwa. Kashe kirar yayi
      
    ***
Tunda muka isa su uku har dashi huɗu suka rufa min, jini na yayi masifar hayewa. Kusan ɗari biyu da 220. D'aya daga cikin abokan aikinsa yace.
"Dr Kyari! Wannan mara lafiyar ta tsallake rijiya da baya sabida jikinta da ya haura, ya taɓa zuciyarta amma sakamakon bugun zuciyar babyn cikinta jinin dake zuciyarta ya sauka, sannan cikin jikinta yana cikin koshin lafiya, sai dai dole ta rage damuwa dan zai iya tab'a zuciyarta"
    
        Shiru Abdul yayi kawai dan bai da abinda zai iya cewa, haka suka gama ceto rayuwata, sannan nurse suka turoni zuwa ɗakin da zan kwanta.
 
         ***
*Ko ina labarin Sultan Ashraf*

       Da misalin karfe huɗu na asuba suka sauka a king Abdul Aziz international Airport... Har suka son inda za ɗauki kayanshi.
   
      Yan sandar saudia suka kewaye shi, cike da mamaki ya kalle su kafin yace.
"Wani abu ne?"
       "Musamu labarin kashigo mana da bom daga kasar jordan aka turo mana."

        Gyara tsayuwarshi yayi cike da mamaki bakinsa a sake, jakarshi suka janyo tare da buɗewa, sai ga bindigogi kirar ak47, kananun bindigo gi biyar. Sai wani waya ɗauke da numbers tada bom, gefe guda kananun bom ne masu zubin abun wasan Yara,
           D'ago kanshi yayi a rikice yana kallonsu, cikin ko in kula suka buga mishi ankwa.

       (Grp ɗin matan quarts da fatan zaku hararo gaba)

        Hukumar saudia ta kama Ashraf da mugun laifi, kuma hukuncinsu ba kamar na kowacce kasa bane domin su shika suke (😂 ) kuma abune daga hukumar kasarshi suka turo da sanarwa.

Hmmm idan baka mutu ba, makiya bazasu taɓa barin ka ba........
           ***
Nannah tazo asibitin tunda tashigo take kallon yadda na koma, jikinta ne yayi sanyi dan idan hasashen da take gaskiyane tabbas Safina Jordan ta fito. Dan taga takardan da Ashraf ya turo min kafin jirginmu ya tashi tare da zobe da ya bata. Ta fahimci haka ne bayan ta tsinci takardan da kuma stamp ɗin masarautar... Tabbas a can binti ta ɗauko cikin jikinta.
   "Ya Allah kasa binti tasan waye ya mata wannan aika aikan, tabbas sai sun biya abinda suka aikata bazan taɓa kyale su ba, abinda sukayi na shekaru shirin da shida bazai tafi a iska ba, kodan binti zan koma gida."

                  Haka tayita magana ita ɗayarta har lokacin sallar magrib yayi ban tashi ba, sallah ta gabatar tana zaune Abdul ya shigo da abinci, karɓa tayi fuskarta kawai zaka kalla kasan a dame take.
"Abdul!"
  D'ago jajjayen idanunsa yayi, ya kalleta a hankali yace.
"Na'am, Nannah."

       "Binti Jordan taje fa..."
Zaro idanu yaƴi waye zuciyarsa ba daɗi, kafin yace.
"Taƴa haka ya zai kasance,"
   Mika mishi takardan tayi, a hankali ya warware. Sannan ya karanta abinda yake jikin takadan.
  *_Nasan bazan biyaki abinda kika rasa ba, bansan me yasa haka ya faru ba amma ina me baki hakuri da ki yafe min dan na zalince ki na rabaki da kimarki na Y'a mace ina kara baki hakuri , idan kin isa ki sumbaci goshin Ammina ina nan zuwa gareta_*

    "Nannah baki karanta wasikar bane?" ya tambayeta,
   yana tsareta da idanu. Girgiza kanta tayi cike da damuwa tace.
"Bansan me zan gani ba, ina tsoron abinda ke rubuce a cikinsa."  

          "Ina kyautata zaton Ashraf ne ya rubuta mata."
    Karɓa takardan yayi dai dai da farkawata.
   "Ruwa Dudu.!" na faɗa a hankali, goran faro da yake cikin kwalinsu ya ɗauka tare da buɗewa ya tsiyaya a cup ya kawo min tare da ɗ'agani ya bani sai da nasha, sannan ya jinginar dani a jikin bangon yasa min pillow.

Shafa kaina yaƴi tare da cewa .
"Sannu kinji! Ina ke miki ciwo?"

Idanuna ne ya sauka kan takardan dake hannun Nannah, kallonta nayi tare da sunkuyar da kaina, kwalla na saukar min daga idanuna. Mikewa taƴi ta zauna a kusadani,
"Bansan da can zaki ba! Da bazan taɓa barinki zuwa can ɗin ba, me yasa da zaki baki gaya mana ba."
D'ago manyan idanuna nayi cikin dishashiyar murya nace.
"Nannah! Bansan me yasa naji ina son zuwa ba, kodan kaddarar da zata ribta dani ne yasani zuwa can ɗin, Nannah nasha wahala. Amma ya zama a banza tunda gashi na dawo gida babu abinda naje samowa sai sheg."

Rufe min bakina taƴi cikin tsananin damuwa tace.
"Yanzun cikin waye, zaki gane me cikin dan zan tsaƴa miki har a sama miki adalci."

Girgiza kai nayi kuka ya kuma kwace min, sosai sai da nayie isata sannan na ciro kaina a hankali ina jan zuciya nace.
"Cikinsa ne!"

"Waye shi ɗin!"
Lumshe idanuna nayi, kwalla masu xafi suka sauƙa da mugun gudu dakyar na haɗiye yawun bakina nace.
"Nannah sorry!!"
Rike hannuna tayi sosai, cikin kulawa tace.
"Gaya min waye shi.?"

Sake girgiza mata kai naƴi na zame tare da kwanciya na lumshe idanuna, yau na janyowa kaina abinda yafi karfina, na faɗi sunanshi abun ya gaggara.
Shigowar Fatimah da Khalila. Da kuma Ƙhalil sai mijin Nana Asma'u, da itama tare da babynta da ta haifa bana nan.

Zama sukayi a kafet ɗin da Nannah tazo dashi aka shimfiɗa.
Koda suka zo sama sama muka gaisa, tunda na amsa musu na rufe idanuna. Ban kuma buɗewa ba har suka fita bawai nayi barci bane kawai bana jin na amsa musu ne, sai da safe suka mana, har Abdul shima ya tafi . Bayan tafiyarsu na tashi tare da shiga ban ɗaki nayi alola tare da watsa ruwa na fito. Sallar da ake bina nayi koƙarin saukewa sannan na koma na kwanta. A hankali kome yake dawo min, babu inda yaki tafiya kamar inda Ashraf ke gwada karfinshi ya shiga jikina, a nan kuka ya kwace min. Tabbas nayi kuskure amma bata wannan hanyar ya dace a hukuntani ba, yadda naga rana haka na ga dare. Kawai ina tuna irin azabar dukar da nasha a hannun Ghaniyu kafin mu shirya. Da irin hidimar da nasha a gun Ashraf.

Ni da yadace nayi murna yau nice na dawo gida da guzirin me albarka, ehmana cikin da na dawo dashi waye zai yarda cikin Ashraf ne, sannan idan sun yarda Abba bazai yarda, tunda an gama masa ingiza me kantu ruwa..
***
*JORDAN*
"Ni nafi dacewa a bani sarkin jordan na biyar."

Wani irin kallo Amir Ukshe yabi d'anshi da ita, cike da ɓacin rai ya kuma watsawa Marhum wani banzan kallo,

"Baba baka ce kome ba. Sai bina kake da idanu, kuma nasa a sake min mutane na da wancan jakin ya saka aka kama min, su."
Tura keken Amir Ukshe yayi cikin jin takaici da kuma tuna wahalarshi na shekaru, ya tashi a banza knn.

A fizge kamar yadda kullum idan zai magana yace.
"Marhum, mulkin jordan bana ka bane sabida tun fil azal akwai me faɗa akan kujerar kum......"

Duƙar glass Marhum yayi cikin d'aga murya yace.
"Waye ne shi? Ni nafi dacewa da jordan ba wani jaki ba."

"Wanda ya dace da jordan shi yake yadda yaso da Jordan ba kai ba.......

*_Hmmm! Anayinta Feener Abba ya koreta! Ashraf Saudia sun kama shi! Jordan akwai me juyata inji Amir! Wannan chakwakiya ya min tsauri Anya ban ɗibo da zafi ba, Ana Dara ga dare..... toh Akafta mana_*😂😉



#MJ#HZƘ#Vote....

Oum Muwaddah......😂
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITERS ASSO_*

*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*

   INA JI DAKU ZAUREN MAI_DAMBU FANS CLUB MUSANMAN, AMMYN KHAIRAT, SAMEERA,MAMAN DADDY, MRS YUSIF...GA KYAUTARKU nan bayawa.....😹😎 Sai dai na fahimceku ai kodan  Albarkacin Binti Nannah zata ɗ'aga musu kafa..... Amma wata tace.yadda tasan larabawa da kaunar y'ay'a. toh ba asan maci tuwo ba......

ZAUREN MAI_DAMBU NOVEL GRP ga tukwaicinku nan Yan amincin Sultan Ashraf
@Mom Sayeed @Smartzeezee @Ummulkhairi Muhammad Sani @Maryam Kolo @Oum Nawal @Naja'atu Sani
@Meelat Ib
@My Meerah
@Maman A3 and M2 @M Muhammad
@Hafsat Abubakar
@Aichatou Mani Kane
@lubabatu shehu shayi
@Fatima Madaki


Fatan Alkhairi HZƘ FANS musamanku.....
@🌹Maryama🌹
@🍇MOMYN ILHAMA🍇

Page.٢١
      A hankali bakina ke motsawa ina son kiran Sophia, amma ina numfashina yabar gangan jikina, ina cikin wannan halin sai ga Abdul ya kawo min, rake dake tunda na dawo yake kirana da Mommyn Littil dan haka yana shigowa da abinda ya fara cewa kenan.
   "Mommyn Littil boy!!!"
Ya buɗe kofar kawai yayi mugun gani, watsar da abin hannunshi yayi ya shigo da gudu kuma duk sai ya ruɗe, ya koma da baya yaje ya buɗe motarshi ya dawo ya ɗauke ni jikinshi na rawa, sai cewa yake.
"No..no..no, Safina buɗe idanunki. Ga Dudunki nan don Allah karki rufe gani nan zan kaiki asibiti kinji Yayata buɗe don Allah."
Duk ya birkice sakani yayi cikin motar sannan ya koma mazaunin driven yaja motar da mugun karfi yakure motar duk wanda yaganshi sai ya matsa mishi a hanya, sabida gudun da yakeyi. Allah kaɗai ya kaishi asibiti, yana shiga yayi wani irin parking ya fito da mugun sauri ya cinciɓeni ya shige cikin dani yana kiran "Dr!!! Nurse ku kawo min agaji jininta zai kare."

Dake ansanshi, kuma ana ganin mutuncinsa, da sauri aka kawo gadon ya ɗaurani. Aka wucce dani ɗakin yan ɓari. Rike dr Muhsin yayi cikin tashin hankali yace.
"Frnd! Ina son dukkansu a raye, don Allah."
Rike hannunshi Dr Muhsin yayi cikin kwantar da hankali yace.
" Insha Allah zanyi iya kokarina."

Haka ya janye hannunshi har likitan ya shiga, zama yayi akan bencin da yake gurin...

*OMAN*
Zaune take tayi kuka har ta godewa Allah, Yayanta sarkin daular Oman ya sata a gaba sai taci abinci kamar magani take haɗiya, kallonshi tayi cikin kuka tace.
"Akkhi haka zan cigaba da rayuwa makiya suna galaba a kaina, da shi Muh'd ɗin."
Gyara zama yayi cikin rarrashi yace.
"Tun ranar da naji kasar saudia takama shi, na tura lauyoyina da kuma wasu daga cikin aikatan sirrin da na tura Amman dan lura da lafiyarshi, a yanzun haka ana bincike ne, idan aka same shi da laifi toh Allah ya kare."

Share kwallarta tayi, sannan tace.
"Naso komawa Nigeria amma zan zauna a nan har Allah ya fitar dashi sai muje baki ɗaya."

Sun tattauna sosai, sannan tabar gun yayanta zuwa shashinta..
(😂 Nannah ta makale😉)
*SAUDI*
Tunda hukumar saudia ta kamashi, bata azabtar dashi ba sabida ya fidda passport ɗinshi da lasisin zamanshi a kasar, kasancewa yayi karatunsa na degree a nan saudia a fannin Islamic law, yaje Germany ya karanci law har na tsawon shekara huɗu. Sannan ya dawo saudia degree dinsa na uku a fannin law ɗin.

...... Ashraf a idanun masarautar jordan karatun boko yake. Amma a zahirin gaskiya karatunsa ta fannin musulunci ya zurfaffa. (ku biyo ni a sannu dan ji waye Ashraf ne)

Daga saudia an tura masarautar jordan domin su san halin da yake ciki, kin saurarra dan sakon sukayi karshe ya dawo da bakar magana. Haka ya harzuka jami'an jakadancin Saudia a nan Amman, inda suka fara yunkuri yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya. Saiga sako daga kasar Oman. Wannan dalilin yasasu hakura da yanke hukunci aka fara sabon bincike.
***
*Nigeria*
Wasa farin girki, dr Muhsin ya zata zai iya ne, sai da abin yashiga bashi tsoro dan tsakani da Allah suka min alluran da zai tsayar da jinin, amma yaki tsayuwa asalima jinin sake zuba yake, a gigice ya fito yana zare glass ɗinsa ya kalle Abdul.
"Dr Kyari sisternka zata iya mutuwa fa, wallahi jinin yaki tsayawa, duk da mun mata allurai amma kamar karashi ake."
Shiga ɗakin Abdul yayi ji yake kamar zuciyarsa zata buga, shigowar wasu likitoti guda uku yasashi juyawa, biyu bakakken fatane, ɗayan kuma ɗan kasar india ne. Yana zuwa kaina ya ɗauki takarda ya rubuta sunan magani, ya mikawa Abdul da sauri ya fita. Kallon sauran likitan yayi bayan yasaka handglove ya shafo jinin da yake ɗiga a kasa ya kallesu. Shinshina jinin yayi, ya kaɗa kanshi yace.
"Tayi amfanin da maganin zubda ciki da karfin tsiya, ko kuma an bata taci bata sani ba. Ga jinin yana karnin maganin kuma idan ba ayi da gaske ba mahaifarta zata iya samun matsala dan maganin tayiwa jininta karfi."

Abdul na shigowa ya mika mishi maganin, buɗe kwayar yayi ya yaye zanin da aka rufa min ya kauda kanshi ya saka min maganin a cikin jikina, sannan ya ɗago hannunshi ya kalle Abdul yayi masa bayani, janyo machine ɗin scanner yayi ya ɗiga min luquid ɗin sannan ya shiga dubawa yana musu baya yace.
"Toh cikin yafita fa!"
Cigaba yayi da dubawa karshe ya ɗaga daga jikin cikina yace.
"Dr Kyari am so sorry we lost the baby"
Gyaɗa mishi kai Abdul yayi cikin jin zafina, wanke hannunshi likitan yayi yace.
"Idan ta farka za a mata wankin ciki."
Gyaɗa kai kawai Abdul yayi, sannan ya fita, suma fita sukayi. Nana Asma'u yayi ya gaya mata halin da nake ciki, ta kira mijinta ta gaya mishi.
Ummi ya kira ya faɗa mata, ita kuma ta kira Fatima akan tazo ina asibiti kafin gobe tazo.
Gidanshi ya wucce yasami gidan yadda ya barta cire kayanshi yayi yasaka a cikin machine din wanki, ya saka Ariel. Tare da ruwa sannan ya komo ɗakina ya gyara tare da goge ko ina yasaka room fresh.
Yana fitowa yaga Sophia da kayanshi da yasaka a cikin machine ɗin wanki. Ta watsar dama a tafashe yake niman abokin taƴi yake, sai akayi dace itace ta taro match ɗin, ba faɗa ba zagi ya kwashe kayanshi ya zo ɗakinshi ya wanke sannan yaje ya shanya, ban ɗaki ya shiga yayi wanka sai cizon lips ɗinsa yake, dan ya lura hatta yaranshi ta kwashesu takai gidan iyayenta, wai kar a lalata mata tarbiyansu.
Yana gama shirƴawa ya nufi masalaci daga can ya shige asibiti. Yasame Nana da Fatima suna ɗakin jum, ajiye take away ɗin da yazo da ita yayi sannan yace.
"Bata farka ba ko?"
"Eh Baban Affan har yanzun ga abinci nazo maku dashi. Wallahi tausayi Didi take bani, daga wannan sai wannan, kasan da nacewa BABAN Sabir dukanta Abbanmu yayi,kamar ya rufe ni da duka. Karshe har kaurace min yayi wai abba bai kyauta ba,tuntuni bata

2 Comments On MASARAUTAR JORDAN
avatar
halimat-6

2 years ago

Reply

Happy love

avatar
halimat-6

2 years ago

Reply

Happy love

Please Login or Register in order to submit comment