Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 3
masa karya ya tafi ya barmu, kinga da bai tafi ba da sai ya nuna muna hanyar fita wannan daji, anan meenat tayi murmushi tana mai cewa, ai tafiyarsa nada amfani garemu, kaga yanzu sai mu cigaba da binciken wannan littafin har sai mun ganshi, anan bafferh ya harareta, ya za ayi muga wannan littafi, bayan mun barosho cikin kogo, kuma hanyar da zata kaimu wurin ta lalace balantana mu bita. inji bafferh. To naji, yanzu sai kazo muje wancan gidan da muka hango, domin shine naga fotonsa a cikin wannan littafin, daga nan suka fara tafiya xuwa wannan gida, suka manta da gargadin mafarauci. To bayan sun kawo gidan, sai sukaga an ajiye motoci kala kala, bayan sun zo gaf da motocin, sai sukaga mutane na fitowa cikin motocin, daga ciki harda aunty balkisu da daddy, anan mamaki ya kamasu meenat, koya akayi sukazo wannan daji?to me ya kawosu? Aunty balkisu ce ke tafiya cikin rangwada har ta kawo wurinsu, marin meenat tayi har sau biyu, sannan ta jawo kanta ta buga ga glass din mota, har sai da glass din ya fashe. KU DAURE MIN SU!!! Taba wasu samudawa umarni, anan aka daure meenat da bafferh, wata kaca ce aka dauresu da ita yadda ko motsi basa iya yi, daga nan sai ta fara tambayarsu, ina littafin da kuka sace? Anan meenat ta kalli bafferh, daga nan suka done kai kasa ba tare da cewa uffan ba, cikin fushi aunty balkisu ta amso wata karamar bindiga daga hannun masu tsaronta, "pistol" halbawa tayi sau uku domin ta nuna musu cewa akwai harsashi ciki "bullets" daga nan sai ta aza bindigar saman kan bafferh, zakiyi magana ko sai na fasa kan saurayin naki!!! inji aunty balkisu, shi kuma daddy kallonsu yake ba tare daya ce kome ba, daga nan sai meenat ta fara magana, haba daddy ka taimake mana, kana ganin abunda aunty ke shirin yi? daga nan sai daddy ya fara magana, bazan iya taimakwanki ba meenat, face idan zaki fada muna inda kuka aje wannan littafin, domin nima ina bayan auntin ki. Wani kallo aunty balkisu tama meenat, ke, ki sani ni ba mahaifiyar ki bace, kije can ki bidi mahaifiyarki ta gaskiya, wannan magana tasa hawaye sun zubo a idanun meenat, haka shima bafferh tausayinta ya kamashi, to wacece mahaifiyata ta gaskiya? meenat tambaya, yauwa, kinga sai ki fadamin inda kuka ajiye littafin kafin na baki wannan amsar, inji aunty balkisu. Kusan minti sha biyar meenat batayi magana ba, daga nan sai daddy ya bada umarni a kaisu cikin wannan gidan a kulle, hako ko akayi, ita kuma UMMI sai kallonsu take, wani matsiyacin duhu ne a cikin gidan, daddy da aunty balkisu na a cikin daki daya, haka suma mutanen da akazo dasu duk an basu masauki. To bayan kowa yayi bacci a cikin gidan, meenat ita kadai ce cikin wani wuri mai mugun duhu, gashi ba wuri guda ne aka ajesu tare da bafferh ba, saman kujera take daure da kaca, kawai sai taga an bude kofar dakin, ashe ummi ce rike da yuka, anan ta bada yukar tana mata umarni data yanke kacar ta gudu, anan meenat ta shiga yanke kacar, ita kuma ummi sai ta fita a guje domin kada a ganta, to bayan meenat ta yanke kacocin, sai taga duhu yayi yawa, saboda haka sai ta fara kiran ummi domin ta kawo mata mata fitila. UMMI,UMMI, UMMI, wai ko batanan, anan taji shiru, cikin sauri meenat ta mike,a hankali ta fara takowa kasan benen domin ganin ko meke faruwa, tsoro ya dabaibaye zuciyarta, kuma matsanancin duhu daya mamaye wurin gaba daya, takawa takeyi guda guda cikin tsoro, tana cikin wannan tafiya sai ta hango wani abu kamar mutum, a lullube cikin bakaken kaya, anan jikin meenat ya dau rawa, ta rasa abunyi, juyawa tayi da nufin komawa, cikin mamaki sai ta kara ganin irin wannan halittar a bayanta, to a wannan lokaci tsoron dake jikinta ya ya harzuka mutuka,batasan lokacin data fadi ba, a haka ta cigaba da mirginowa kasan benen har ta kawo kasa, a wannan lokaci dakyar take nishi, to bayan ta tashi, abunda ya daure mata kai shine bataga wadannan halittun bakake ba. Anan ta cigaba da tafiya a hankali tana kiran ummi, tana waige waige saboda tsoro,bata ganin ko tafin hannunta, sannan abunda ke ke damunta shine me yasa duk fitillun gidan sun mutu? kuma ita ummi inata shiga ne? a haka ta cigaba da tafiya har ta shigo wani daki, shogowarta keda wuya sai taga fitila, anan ta kunna, jin dadi tayi saboda ganin wani fanfo,cikin sauri takunna fanfon domin shan ruwa, ihu tayi domin jini ne ke fitowa maimako ruwa, juyawa tayi da nufin fita, kawai sai taci karo da karamar yarinya, laa ummi, ina kikaje ina neman ki, anan taji shiru, kuma gata rike da wani gatari, kuma idanunta duk sun juye zuwa ja, da karfi meenat ta kaucema saran data kawo mata, anan ta fitabdakin a guje, cikin wannan gudune sai taci karo da wani abu, anan ta fadi, ahankali ta dago kanta domin ganin ko meye, anan ta gane cewa wadannan halittun ne bakake data gani dazu, ihu tayi sannan ta nufi wani daki a guje, kullewa tayi tana nishi, shigarta keda wuya sai ta kara ganin wannan halittar baka kirin, a guje ta nufo kofa da nufin guduwa, to kafin ta kawo ga kofar, sai taji anan bugunta da gatari, wato anaso a ballata da karfin tsiya a shigo ciki, taga ta leka da nufin guduwa, sai taga duk itatuwan dake dajin sun zagaye gidan yadda ba wurin gudu, a wannan lokaci wannan halittar ta kusa cimmata, haka kuma kofar dakin ta kusa karyewa saboda bugun da tasha da gatari, anan ta hango watarijiya a cikin dakin rufe da marfi, kawai sai taga an budeta, ashe bafferh ne, to anan ya mata umarni da ta shigo ciki, rijiyar kamar hanya take, wai ya akayi ka kubuta bayan da suka daureka anan, inji meenat, anan ya bata amsa da cewa ai ummi ce ta kawomin yuka domin in taimaki kaina, anan taji mamki to meyasa ummi keson kasheta? suna cikin gudu sai suka hadu da aunty balkisu tare da jama arta, wato kunaso ku gudu ko, to ku sani bazaku tona sirrin da muka binne shekaru da dama ba, anan ta bada umarni da aka masu, to kafin a aiwatar, kawai sai kasa ta fara girgiza, tana tsagewa, anan wadannan mutanen suka fara fadawa ciki, sai kuma wasu kibiyoyi da ba asan inda suke fitowa ba suka fara kashe jama.a, idan kibiyar ta shiga jikin mutum, sai dai aga yayi kunburi ya fashe. MEYE KARSHEN WANNAN LABARI? ZAMU CIGABA.... GIDAN FATALWA 3 kashi na uku Written by abdul king article TUNATARWA DAGA NA BIYU: A cikin littafi na biyu, mun tsaya inda bafferh da meenat suka hadu da aunty balkisu tare da jama arta wato matsu tsaronta a cikin wannan rijiyar mai kamar hanya, a inda ta bada umarni a kamasu, to kafin a aiwatar sai kasa ta fara girgiza, haka kuma wasu kibiyoyi da ba asan ta inda suke fitowa ba suka shiga kashe jama a, wanda idan kibiyar ta shiga jikin mutum, sai dai aga yayi kunburi ya fashe. CIGABAN LABARIN: Bala i yayi bala i, domin ta koina kibiya fitowa take, saboda haka hanjin mutane sun yawaita a kasa, jini sai malala yake tamkar ruwa, to a wannan lokaci aunty balkisu ta rude, domin mafi yawan masu tsaronta sun mutu "security agents" to ana cikin haka sai wasu daga cikin mutanenta suka zo da wata shawara, cikin sauri suka fito da garkuwa domin kare wadannan kibau, "protector" cikin dubara suka hada wani sahu, daga nan sai su aunty balkisu suka koma bayansu, meenat ko magana bata iya yi saboda tsoro, haka suka cigaba da tafiya cikin wannan sahu, duk kibiyar da tazo sai dai ta tsaya ga garkuwar, an dauki lokaci wadannan kibiyoyin na fitowa kafin daga bisani su dauke gaba daya, to bayan kibiyoyin sun dauke, sai dakarun suka aje garkuwowin, suna duban inda kibiyoyin ke fitowa, basa ganin kome face tsananin duhun daya karwade wurin gaba daya, anan wasu daga cikinsu suka fara yadiya da fitila " torchlight" sai dai fitilar batada haske sosai, saboda haka duhun ya rinjayi fitillun, daga nan sai suka fara jin wani ruri marar dadi, wanda hakan yasa kowa ya like kunnuwansa, kuma abun mamaki basa ganin mai yin rurin, da sun haska wurin sai dai suka ga duhu, gaskiya ni bazan iya zama a wannan gida ba, tsoro nakeji!!! inji meenat. Yi shiru, banza, ai duk kece kikaja, yanzu zamu cigaba da tafiya domin mu samu hanyar fita, aunty balkisu ta fadi cikin fushi, to daga nan sai suka cigaba da tafiya cikin wannan rijiyar "underground" suna waiwaye waiwaye, kowanensu idanunsa sun fito saboda tsoro, domin ji suke a kowane lokaci za a iya kawo musu hari, to suna cikin tafiyar sai suka kawo wani wuri da anyi zane zane a bangon wurin, anan suka fara kallon zane zanen domin da fenti ja aka yishi, wasu kwarangwal din mutane ne aka zana, sai kuma wata mata mai siffar dodanni tana kalaci da naman mutum, anan suka cigaba da kallon wadannan zane naban mamaki, shi kuma bafferh kome ya kaishi, hannunsa yasa ya shafi wani zane, yin haka keda wuya, sai suka fara jin wani rugugi, kamar ana magana amma basajin abunda ake cewa, cikin rashin tsammani sai sukaga wani abu mai kamada maciji, sai dai jikinsa dauri gareshi, kuma bayada kafafu balantana idanu, cikin sauri wannan abu ya laulaye daya daga cikin dakarun aunty balkisu, haka wannan mutumi ya fara ihu yana neman taimako, amma ba mai iya zuwa wurinsa, kafin kaceme wannan abu ya wuce da wannan mutumi, cikin minti biyu sai aka jefo musu gangar jikin wannan mutum, kai daban, hannaye daban, kuma kafafuwa daban, duk an masa guntu guntu ba kyan gani, wannan abu ya mutukar tayar musu da hankali, anan suka fara gudu, kowa na ta kansa, aunty balkisu ce ke basu umarni inda zasu shiga sai kace tasan gidan, wannan abu yaba meenat da bafferh mamaki, anan suka fara tunani wai ko batada nasaba da wannan gida? To suna cikin wannan gudu ne sai wannan abun ya dawo, cikin sauri ya kara laulaye wani daga cikinsu ya wuce dashi, abokin wanda aka laulaye ya kasa hakuri, saboda haka ya bi shi domin cetoshi, anan su aunty balkisu suka rikeshi suna bashi hakuri, amma ina ya kasa jurewa, sai kuka yakeyi yana kiran sunansa, AL AMEEN, ihun al ameen din sukaji tare da ganin guntattakin jikinsa, anan suka tashi kowanensu yacigaba da gudu, suna cikin gudu sai suka kawo ga wani wuri mai matattakala, a can saman wurin akwai wata kofa wadda zata fiddasu daga cikin rijiyar, cikin sauri kowanensu ya fara tattakawa yana kokarin fita, turanni in tureka suke, suna cikin wannan hali sai wannan abun ya kara dawowa, wani ya laulaye sannan ya wuce dashi, ganin haka yasa kowanensu ya kara himma ganin cewa ya fita daga wurin, cikin kuzari meenat ke kutsa kai ganin cewa ta fita, amma a duk lokacin data tunkaro wurin sai wani yasha gabanta ya wuce, haka meenat ta cigaba da kokari amma duk a banza, kafin kaceme kowa ya haye ya barta, anan ta fara kokarin hawa cikin tsoro tana waige waige, fara takawarta keda wuya sai sukayi ido biyu da wannan halittar mai kashe mutane, anan jikin meenat ya dau rawa, sukuma wadanda suka samu damar hawayewa sai suka fara yi mata magana, suna bata umarni da tayi sauri, haka meenat ta cigaba da takawa jikinta na rawa, shi kuma wannan halittar kokarin cimmata yake, anan yayi wani tsalle ya riko rigar meenat, to a wannan lokaci tana gab da fita, shi kuma bafferh yana ganin abunda ke faruwa sai ya zaro wata karamar yuka, rigar meenat ya fara yankewa har sai da katse wurin da wannan halittar ya rike rigar, daga nan sai ya jawota da karfi, tana fitowa suna kulle kofar, ji kake baaaam. Anan sukayi tsaye suna nishi, kai da gani kasan sun gaji, daga nan sai suka cigaba da tafiya har suka shigo wani daki, inda sukaga daddy da ummi na bacci, wannan abu yaba meenat mamaki, anan ta tuno lokacin da ummi ke binta tana kokarin kasheta, kuma gashi yanzu ta sameta tana bacci, to ya haka? Aunty balkisu ce ta matsa da bugunsu har sai da suka tashi, ku bakuji abunda ke faruwa damu neba? anan suka amsa da basuji komeba, anan meenat taja ummi gefe tana tambayarta, ke da kika bani yuka nida bafferh ina kikaje? meenat ta tambayeta, anan ummi ta amsa da cewa, bayan na baku yuka domin ku kwance kanku keda bafferh, anan dakin na shigo na tarar da daddy na bacci, daga nan sai na kwanta nima na fara bacci, daga nan ban dan abunda ke faruwa ba sai yanzu da kuka tasheni, inji ummi, anan meenat ta shiga mamaki, kenan waccan ummi data gani tanason kasheta bata gaskiya bace, wannan itace ta gaskiyar. Bayan kamar minti goma, sai aunty balkisu ta dauki fitila da niyyar zuwa ban daki, anan ta fita, cikin tsoro take tafiya tana waige waige, kamar ana tafiya bayanta takeji, anan tayi tsaye cif ta kasa motsi, rike take da fitila jikinta na makarkata, kuma ta kasa juyawa baya balantana taga ko meye, ana cikin haka sai taga jini na zuba ga kafafunta, anan ta juyo a hankali, ihu ta buga, wani hannu ta gani duk kassa, ba tsoka a ciki, a guje tayar da fitilar ta nufi dakin data baro, anan ta fara kwankwasar kofar domin a bude mata, amma ina basaji, can kuma sai ta hango wani haske, wata mata ce a cikin hasken sai dai bata ganin matar da kyau, domin dushi dushi take gani, anan ta cigaba da kwankwasar kofar domin a bude mata, shi kuma wannan hasken mai dauke da matar ya cigaba da nufota, wata juwa ta fara gani, kafin kaceme ta fadi, batasan inda take ba. Mutane ne kewaye da wani gado, a saman wannan gado aunty balkisu ce, fita ake mata domin ta farfado, daganan sai ta fara bude idanu a hankali, can sai ta budesu gaba daya, da karfi ta tashi. INA TAKE? abunda ta tambaya kenan. HALA WACECE? daddy ya tambayeta, anan aunty balkisu ta kankane jikinsa tana kuka, ashe bata mutu ba, dama tana raye, ta fadi cikin kuka, ki gayamin wacece mana? MUHIBBAT!!! inji aunty balkisu. Ina bazai yiwu ba, inji daddy, domin ni na turbudeta da kaina, kuma yanzu an fi shekara goma da mutuwarta, anan dai aunty balkisu ta kara kankane jikinsa tana kuka, nidai na tuba, kuma yanzu inaso ka nemo muna hanyar fita cikin wannan gida. Wannan magana taba meenat mamaki, domin kaka zuwaira ta taba yin magana akan muhibbat, a lokacin da daddy yazo mata da labarin cewa guguwa ta kashe mutum dari biyar, kuma ta taba ganin an rubuta sunan MUHIBBAT a wannan littafin data tsinta cikin akwati, to tambaya anan shine wacece muhibbat? haka wannan tambaya ta cigaba da damun meenat, anan ta kasa samun sukuni sai da ta gabatar da ita gaban daddy. Wato ki sani meenat bazan iya amsa miki wannan tambaya ba, sai yanzu zan kira kaka zuwaira domin ta bayyanar dake abunda ke damunki na daga wannan tambayar, anan daddy ya dauko laptop dinsa, kunnawa yayi, daga nan sai ya kira aunty zuwaira, fuskarta ce ta bayyana ga screen din laptop din, daga nan sai daddy ya fada mata abunda meenat ke son sani, murmushi kaka zuwaira tayi, su kuma sai kallon fuskarta suke, daga nan sai ta fara labari kamar haka: Tun kafin a haifeki meenat, babanki wato daddy ya sayi wannan gida da kuke ciki a yanzu, domin yasa amaryarsa a ciki, wannan amarya tasa itace mamarki, kuma itace ake kira MUHIBBAT, na masa fada a lokacin da ya sayi wannan gida, domin gidan ya kasance tilo a tsakiyar daji, amma haka babanki ya kanne akan yanason gidan, to bayan an daura aurensa da muhibbat, bayan wani lokaci, sai ya hadu da aunty balkisu, wadda suka far soyayyar boye da ita, ita kuma balkisu batasan yanada mata ba, wata rana sai ta kawo masa ziyara, a wannan lokaci kuma bayanan, to anan taci karo da muhibbat, daga nan ta gane cewa yanada mata, rikici ne ya kullu tsakaninsu harda buge buge, to a cikin wannan fada ne balkisu ta samu nasarar buga ma muhibbat tangaram, anan muhibbat tace ga garinku, to bayan daddy ya dawo, anan ya rasa abunda ke masa daddy, ke kuma lokacin kina jaririya, domin kwananki hudu, to anan daddy ya yi kokarin turbude muhibbat a cikin wannan gidan, haka ko akayi, a nan ya gina mata kabari cikin gidan, daga nan kuma sai ya auri aunty balkisu, to wannan shine takaitaccen labarin muhibbat, inji kaka zuwaira, wannan labari yasa meenat ta mutukar bayyana haushinta ga aunty balkisu, domin ji take kamar ta kasheta. To menene ke bamu tsoro a cikin wannan gida? meenat ta tambaya, daga nan sai kaka zuwaira ta bata amsa da cewa, idan aka rufe gawar mutum a gida, to hadari ne zaman wannan gida, domin ruhin mutumin kan iya zamar muku matsala, sannan wannan gidan da kuke gani, na dade inajin labarinsa, yafi shekara dari gine, asalinsa na wani mai kudi ne, shi ya gina shi, amma saboda yawan tsoron da ake bashi, dole yabar gidan, haka wani ya saishi, shima dakyar yasha, dole yabar gidan, daga nan sai mahaifinki shima ya saya, kinga tun asali wannan gidan ba mai kyau bane, daga nan sai laptop din ta dauke saboda rashin caji, daga nan sai daddy ya basu umarni dasu tashi su samu hanyar fita daga gidan, gaba dayansu suka tashi, anan suka fara tafiya cikin tsoro, basuyi nisa ba sai wannan halittar ta dawo, cikinsu ta dauke wani, yana karaji ta wuce dashi, to a wannan lokaci sun kawo daf da kofar fita, amma kuma taki budewa, to anan aunty balkisu tayi tsintuwar wata takadda wadda aka yi rubutu da jini kamar haka: SAI NA KASHEKI. hankalinta ya tashi, amma haka ta daure, wani irin mugun bugu daddy yama kofar, daga nan sai ta bude, budewar kofar keda wuya sai wannan halittar ta fito, anan ta laulaye mutum biyar ta wuce dasu, wato saura daddy, aunty balkisu,ummi,bafferh, da meenat, sauran security agents duk sun mutu, kusan su hamsin. Suna fitowa daga gidan, sai wani haske ya bayyana a kofar gidan, wata mata ce a cikin hasken, kawai sai aunty balkisu ta tsaya tana kallon hasken, a wannan lokaci wannan halittar ta dawo, kafin kaceme ta laulaye aunty balkisu, ita kuma ummi ta fasa wata irin kuwa ganin mahaifiyarta cikin wani hali, anan ta sheka a guje da nufin kai mata dauki, meenat ce ta riketa don kada taje ta halaka, kiyi hakuri meenat, bazan iya rayuwa ba idan bada momina ba, injita, daga nan ta kubce ta nufi wurin halittar, aiko tana zuwa itama aka laulayeta, shi kuma bafferh zuciyarsa ta kawo, anan yayi wani tsalle da nufin kai dauki, halittar ce ta cabe shi, daga nan sai halittar ta shiga dasu cikin gidan suna ihu, ita kuma wannan matar a cikin haske murmushi tama meenat kafin daga bisani ta bace, anan meenat ta gane cewa matar tayi kamada wannan data gani cikin littafi, bako shakka itace muhibbat, wato mahaifiyarta, anan meenat ta nufi gidan a guje, tana zuwa kofar gidan na kullewa, haka ta duka tana kuka, gashi kuma tanajin ihun su bafferh a ciki, anan daddy yazo wurinta yana lallashinta, daga nan sai yaja hannunta suka shiga cikin mota, wato su biyu kawai suka rage cikin taron jama a, a haka daddy ya fara tuka motar yana fita kokarin fita daga dajin, to bayan sun isa gida ne, sai kaka zuwaira ta fara lallashinta, su bafferh basu mutu ba, kada ki damu meenat, anan meenat ta fara kallonta cikin mamaki, daga nan sai kaka zuwaira ta cigaba da bayani, wannan littafin da aka rubuta labarin muhibbat ta dauko, laa ya akayi kika sameshi? meenat ta tambaya, ai ali sarki baka ya kawo min shi, wato ki sani meenat, a binciken da nayi da nayi, na gano cewa mahaifiyarki muhibbat bata mutu ba, domin a lokacin da a lokacin da aka turbudeta, ashe wannan hakittar ce ta tona kabarinta ta cinyeta, saboda haka sai ruhinta ya fita daga gangar jikinta, to wannan ruhin ne ke baku tsoro, kuma shine kuke gani matsayin haske, akwai wasu ruwa da ake cema RUWAN SIRRI, da zaran an ba halittar wadannan ruwan, to ba ko shakka zata amayo duk abunta ta hade, to a cikin wannan amai ne zamu gansu, sai dai ruwan basu cikin wanan duniyar da muke takawa, suna can wata duniya daban, aiko duk inda suke sai na nemosu, inji meenat, daga nan sai kaka zuwaira ta bata wata sarka, wannan sarkar tsari ce, ki riketa sosai, kuma da itace zaki iya dawowa wannan duniyar, daga nan sai kaka zuwaira ta bude wannan littafi, anan ta fara karanta wadansu kalmomi marar ma ana, wani bacci ne mai nauyi ya dauki meenat, daga nan kuma sai wata guguwa ta fito ta dagata sama, anan wannan guguwar ta cigaba da tafiya da meenat sama domin kaita wannan duniyar da zata nemo RUWAN SIRRI. kaka zuwaira da daddy sai daga mata hannu suke har ta bace suka bar ganinta. WANNAN SHINE KARSHEN LABARIN GIDAN FATALWA, SAI DAI ZAMU HADU A WANI LABARI MAI SUNA ( RUWAN SIRRI ) WANNAN LABARI SHINE CIGABAN GIDAN FATALWA, KUMA A CIKINSA NE ZAMUJI GWAGWARMAYAR DA MEENAT TASHA DOMIN SAMO RUWAN, DA KUMA YADDA SU BAFFERH ZASU TASHI, MUNA BAKU HAKURI DOMIN LITTAFIN BAZAI FITO BA SAI BAYAN SALLAH, AMMA YANA FITOWA ZAMUYI POSTING DINSA, MUNA GODIYA. abdul king article To be continue in ( RUWAN SIRRI).... An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __ An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your

Chapter 2 of 3