Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 5
fara magana "Yaro hakika mun yarda da soyayyarka ga haseena, duk munga irin halin daka shiga sakamakon ta, shakka babu ka cancanci auran budurwan sirri," Tacigaba bayan taja gauron numfashi "Kai sani cewa Haseena ita kadai ce ta tsira da rayuwarta a yayin da ka dasa makaminnan, a garin bulzum ita kanta haseena abu daya ne ya taimaketa, Ta kasance a cikin kwayoyin halittar jikinta , rabin kwayoyin halittar na Aljanu ne rabi kuma na Bil'adama ne, Toh a yayin da wannan makami ya fashe, sai ya kasance kwayoyin jikinta na Aljanu sun mutu, da shike ALlah yasa tana da sauran kwana sai kwayoyin bil'adama suka maye gurbin wajen kwayoyin halittan, Yanzu kam haseena ta zamo bil'adama sak irinka Hakan ne ma yasa Zaikid ya dauketa daga duniyar nan ya kaita duniyarku ta bil'adama domin ta samu kyakyawawan kulawa," , Bakina bude nake dubansu na kasa bambance shin farin ciki zanyi na kasancewar haseena a matsayin bil'adama ko kuma bakin ciki zanyi na komo wata duniyar da babu Bil'adama, , Tsoho zaikid yayi murmushi a karo na farko yace "ina sane na sanar dakai cewa haseena ta halaka, na kuma koma da kai izuwa duniyarku, saide yanzu da kwai matsala daya" "Wata matsala kenan" Na tambaya Tsoho zaikid yace "matsalar shine haseena ta manta dukkan wani abun daya faru da ita lokacin da take duniyar nan, shi yasa ma da kuka hadu kaga bata shaida ka ba" , "Amma mai yasata faduwa dazunnan" Na tambaya ina kallon tsohuwar nan "Dogon tunani ko kuma son tunano abun daya faru lokkacin daya wuce" , "Ban fahimta ba" "Aduk lokacin da haseena tayi yunkurin tunano rayuwarta na baya toh hakane zai runga afkuwa da ita, zata iya Suma, izan kuma abun ya yawaita zai iya shafan lafiyanta, sai ka kiyayi yi mata duk wani abun da zai sanya tayi kokarin tunano rayuwarta na baya" Tsoho zaikid ya bani amsa Tsohuwar nan ta dubeni da kyau tace "Nasan kana tunanin koni wacece? Toh nice kakar haseena, dun kuwa ni na haifi mahaifiyarta Kafin Nuridden ya aureta alokacin mahaifinta ya rasu, kuma ni bansan cewa nuriddeen Aljani bane, har ya auri yata, suka samu karuwa da juna biyu, saide a yayin haihuwar yata ta koma ga mahaliccinta, Tun daga wannan lokaci ban sake ganin nuriddeen ba bare har na gana da haseena, sai a kwanakin baya wannan aljanin ya kawota wajena ina ganinta na ga fuskar yata a tattare da ita , shine yayi mani bayanin dukkan abun da ya faru " Ta karisa zancen tana mai duban tsoho zaikid 'Baba yanzu a ina haseenan take" 'Tana cikin bukkata" , Na mike tsaye na dumfari bukkar wacce tun dana fara zuwa Dajin har wa yau ban taba shiga ciki ba , Batarre da fargabar komai ba na tura kai cikin bukkar Yadda nai tsammani hakan take babu komai cikin bukkar sai wata tabarmar karau, sai wasu tarin tarkace a wani saqo, Idanuwana suka kai ga inda haseena take kwance a saman tabarmar karau dinnan tana barci , Kallonta nake bana ko kiftawa har na kariso inda take nakai hannu da zummar na taba saman goshinta cikin mamaki sai gani nayi ta bude idanunta, Da sauri na kauda hannuna , ta mike zaune tana dubana sama da kasa tace "Wanene kai ? Yanzu a ina nake" "Zaki iya kirana da masoyi yake abar qaunata," "Masoyi!" Ta nanata sunan a bakinta "Amma ina ji tamkar na taba ganin ka a wani waje daban" , Ta fadi tana kallona Nayi murmushi nace "eh tabbas kin sanni domin kuwa mun sha haduwa dake cikin mafarki a matsayin Masoya, masu begen juna, bazan taba mantawa da ranar da kika furta cewa kina Sona ba, " , A dan firgice ta zazzaro idanuwa tace "da gaske ni na fadi hakan" ' "Eh kin fadi haka kuma har ma kika bani zobe a matsayin Alkawarin aure a tsakaninmu, tun daga lokacin danai arba dake a cikin mafarkina rayuwata ta sauya, a kullum bana da buri sai na in sake yin mafarkinki, nakan raba dare ina mai tunano da kyakkyawann fuskarki , abun dayafi jamin hankali dangane dake shine murmushinki, aduk lokacin dana tunaki sai inji farin ciki ya baibayeni, duk irin kuncin dana ke ciki da zarar na tunaki sai ya yaye, Akullum addu'ata shine ubangiji ya bayyana min ke a zahiri, da shike Allah maji roqon bawansane, sai gashi Allah ya hadamu," Haseena tayi shiru tana kallona ga dukkan alamu kalamaina sun ratsa jikinta, Cikin sanyin jiki ta kwantar da kanta kas "Haseena" na kira sunanta Ta dago kai a hankali batare data amsa ba "Ina sonki, ina kaunarki, shin kina Sona" Bakintane ya fara kokarin motsi alamar tana son furta wani abun sai kuma ta fasa , Ta mike tsaye tsam ta fara tafiya cikin sanyin jiki , har ta isa bakin kofan bukkar sannan ta juyo muka hada idanuwa da ita Duk da bana iya jure kallon cikin kwayan idon haseena, a wannan lokaci sai na tsinci kaina ina mai kallonta batare da kiftawa , , Murmushi tayi yayin da gefen kumatunta suka lotse wushiryarta suka fito, hakan yayi matukar kara fidda kyawunta, daga nan sai ta fice daga bukkar a guje , Koda naga haka sai nima na tashi na fice daga cikin bukkar........ ALHAMDULILLAH Anan na kawo karshen Littafin BUDURWAN SIRRI Sai kun jini cikin sabon littafi , Duk wani kuskure dana tafka Allah ya yafeni Gefen ADABI kuwa, Ashirye nake don karbar gyararraki, shakka babu ni kaina nasan da kwai kurakurai da dama dana tafka, A kullum burina shine na ga na kware wajen rubutun hausa na adabi, DAlibi nake ba gwani ba , Dan koyo nake ba dan iya ba Wannan shine takena , (c) Shuraih 99% 2018 BUDURWAN SIRRI Publisher : (c) Shuraih 99% Author : Shuraih Usman Year : 2018 . Wannan littafin na BUDURWAN SIRRI an fara kasuwancinsa Okadabooks akan #300 , Wayanda suke son karantawa sai su duba facebook ko kuma su duba shafin Shuraih 99% , Masu neman Ebook sai suyi marmaza su garzaya shafinmu na ebook mai taken Hausaebooks.cf . Nagode wa Allah mai kowa mai komai daya bani dama na kammala littafinnan , Matukar godiya da jinjina ga ahalin ; _____ PAGE _____ Shuraih 99% Triple Abubakar Hausa Books Littattafan Hausa Dandalin Abduluk hausa books Zauran Labarai Home of Littafan Yaki And Hausa Novels Hikayoyin Yaki Hausa ebooks - pdf,txt and doc _______ GROUP _______ KINGBOY ISAH HAUSA NOVELS FILIN LITTAFAN HAUSA NEW TSANGAYAR MARUBUTA "TASKAR GIDAN LITTAFI" HAUSA BOOKS HAUSA NOVELS Chakwakiyar Soyayya Hausawa DA Pulani Donated By www.Hausazone.Com KUZO MUYI NISHADI Samee khairah novels group DANDALIN HAUSA NOVEL DUNIYAR MAKARANTA LITTATAFAN HAUS 360 Hausa Novel Books FEENAT JA'AFAR NOVEL'S HAUSA BOOKS NOVELS Just Hausa Novels kingarticle novels of abdul$bafferh Zumunci Hausa NoveLs [ÝäzèèÐ] HAUSA NOVELS ONLY *FATIMA ZARAH NOVEL GRP(HAUSA)* Hausa Novels by ASK (GREAT HAUSA NOVELS BOOKS) SOYAYYA RAYUWA CE ZAINAB MUHAMMAD AND NUHU ALIYU GUSAU NOVEL GROUP Nagode sosai da yadda kuka nuna kulawarku gareni da kuma bibiyar littafin budurwan sirri Allah ya barmu tare Nine dai nakunnan shuraih Usman inkiya 99% An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 5 of 5