Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Milo ta tabe baki tace "Mayyar ma bata sha shayin jiya da daddare ba, dama fa gulma ce, a gidan uwarta da ubanta ina xata samu haka, ita dai kawai ta samu d'ana sai kashe mata kudi yake a banxa a hofi, sbda ita abubuwa da yawa an daina min, tasa sai maneji muke yi, ga uban kudi xa aje a gyara kaddararrun idonta nan da kwanaki kadan, mu dai kawai Allah ya bamu lada, bafa dangin iya balle na baba" Tana ajiye gwangwanin milon taga murfin ya fadi, ta dau murfin tana kallo da mamaki, can ta ajiye tace "Ikon Allah, ni fa na hada mata shayin jiya da yamma, to wani barawo ne ya xo ya bude ya sata ya manta bai rufe ba, gashi har Milon yyi kasa, ni dai ba haka na bar sa ba wllh, sata aka fara yi gidan amadun bani da labari??" Ajiye tsintsiyar tayi ta fice daga dakin, direct parlon Abba ta nufa ta kwankwasa kofa, Mumy ce ta fito, kaka tace "Amadun fa?" Mumy tace "Yana ciki" Kaka tace "Ce masa gani a tsaye" Abba na fitowa kaka tace "Amadu wllh shigar min daki aka yi aka yashe milon Deedayah tass, ynxu ba sai ace ni ke shanyewa ba ko da ba a fito fili an gaya min ba ayi ta xagina a xuciya, toh gaskiya ni dai a san matakin da xa a dauka ynxun nan" Mumy da hankalinta yyi mugun tashi tace "Ikon Allah, toh bari in debo na wajena sai a kara mata a kai tunda yyi kasa, ba abun tada hankali bane kaka" Kaka tace "Oh oh ba wani debo naki da xa kiyi, ko ma waye ya diba sai ya maido wllh, xan fara ta kan masu aikin nan tass sai na bincike kayansu don nasan ba shan lkci daya xa ayi ma milon ba deba xa ayi a leda a boye, Kai har kayan Deedayar ma sai an bincika da nasu Rabi'ah" tana fadin haka ta nufi dakin masu aiki tana kwala ma Mami kira ita ma ta fito, kayan Sajida ta fara dubawa ta xaxxage gaba daya Ghana must go din bata ga komai ba, Kaka ta kalli Karime dake ta xufa tace "Ke ina jakarki" Karime ta nuna mata ghana must go din, ba komai ya sa hankalinta ya tashi ba sai kullin Madara da millo na Mumy da take diba a leda idan Mumy tace taje ta hada shayi, har na Mami ma tana diba, snn ga kullin soyayyen nama na jiya da ta boye a kayan, ga kuma Cornflakes a leda shima duk ta boye, kaka ta yatsina fuska tana xaro kayan kamar Kashi tana ajiyewa kasa, da ledan naman ta fara cin karo, ta kunce ledan ta saki salati ta yar a kasa tana kallon naman, Mumy ma xaro ido tayi tana kallon naman, Kaka ta ci gaba da xaro kayan sai ga ledan cornflakes, Kaka ta kara gwalo ido ta ajiye Cornflakes din, ta ci gaba da xaro kayan sai ga ledan milo sannan Madara, kaka tayi wani dariya irin na boss, Mami ma na tsaye bakin kofa ta kasa cewa komai, Kaka tace "In ji dai kun tabbatar cewar ba banxa nake ba ynxu, duk wanda Allah ya daukaka ya riga da ya daukaka sa, to a kira Amadu shi ma ya gane ma idonsa, nasan da naje na samesa nace gashi gashi a ransa cewa xai yi ohh Allah ya hadani da fitinanniyar uwa, to yau ga ranan fitinata, ni dai nasan shigar min aka yi aka debi milon nan dama" Karime ta durkusa tana matsar kwalla tace "Wllh wllh wllh kaka ba milon ki bane wnn, ki duba ki ga wnn har fa ya daskare...." Kaka ta kwala mata ledan milon da ya daskare a fuska tace "Ke dai bakya tsoron Allah, to kin saka sa cikin jaka duk wari ya baxai daskare ba?? Ai da kyau tunda ba tsutsa ya fitar ba, ni dai a kira min Amadu ya xabi ko ni ko kazamar nan, don in har xa a yafe mata ta ci gaba da xama a gidan nan gwara in tafi duk inda Allah yyi" Mami ta sauke ajiyar xuciya tace "Yau kwana nawa da biyanki kudin watan aikin ki?" Karime ta fashe da kuka tace "Sati daya" Mami tace "Toh ki hada kayanki, ki taho ki sameni in baki kudin aikinki na sati daya da kudin mota kiyi tafiyar ki, Allah ya bamu alkhairi" daga haka Mami ta fita dakin, Karime ta kara rushewa da wani matsanancin kuka ta daura hannu a ka tana kallon Mumy tace "Don girman Allah Hajiya ki taimakeni wllh aiki wahalan samu yake yi ynxu, ki saka baki a maganan nan don Allah a barni in ci gaba da aikina" Mumy ta ki kallon ko da Inda take, can ta juya kamar munafuka ta fita, kaka tayi wani shewa tace "Aje can wani gidan kuma ayi tayi masu naso ana wari amma ba gidan d'a na ba" daga haka ita ma ta fice daga dakin, Dubu goma Mami ta ba Karime kudin mota dubu biyar, dubu biyar kuma na aikin sati daya da tayi, sai kuka Karime take tana cewa "Don Allah Hajiya kiyi hakuri kar a koreni, wllh sharrin shaidan ne" Mami tace "Da ni ce kika debar ma abu na kamaki, sai dai in maki nasiha kuma in gargadeki da cewar kar ki kuma, amma kinga ya fi karfina ynxu, kinsan yanda tsofaffi suke lamarinsu, don haka kiyi hakuri ki tafi, Allah xai kawo maki wani hanyar" tana kuka sosai ta fita, Tsaye ta ga kaka da gwangwanin madara da milon a hannunta, tana ganin ta fito ta nufeta ta ajiye mata su tace "Ga nawa gudunmawar, a gaida mutan Doguwa" Mumy dake tsaye bakin kofarta ta shigo parlon da sauri kuma a rude tace "A'a kaka ya xa ayi haka? Ki bata tayi me dasu kuma???" Kaka ta katseta tace "Toh Ina ruwanki, so kike in ba Jikata gaibu ta sha, nasan barbadin da ya shiga ciki a yayin satar? Kazama ce fa bata wanka, to Deedayar xan ba ma sauran milon da ta jagwalgwala ta sha kamar uwata tace min je ki kya gani, kawai wani cutar ya kamata Amadu da Rakiya su kullaceni?? Aa wllh ta tafi da su tayi ta shan shayi a kauyen nasu" Karime sai kallon Mumy take tana hawaye, Mumy na rawar baki tace "Aa kaka idan ba xa a bata ba ni a bar min xan yi amfani da su wllh" kaka tace "Toh banyi niyya ba, ita dai barauniyar xan ba ta tafi da su, kinga dai ai baxata kullaceni sosai ba tunda na sallama mata sauran kayan shayin" kaka na fadin haka ta jawo katon Ghana must go din Karime ta xuge ta xuba gwangwanin biyu a ciki sannan ta rufe tana kakkabe hannu tace "Gudunmawata kenan, anjima kuma sai a kira min Junaidu in sa ya siyo mata wani bbu ruwana da wahala" Karime ta dau Ghana must go din ta nufi kofa tana matsar kwalla, Kai kana ganin Mumy kasan duk a rude take don hakan ya fito kiri kiri a fuskarta, Mami kuwa sai kallonta take, Mumy ta koma part dinta da sauri ta dauko Hijab sai ga ta ta fito ta bi bayan Karime tana cewa "Mu je in raka ki ai baxa ayi rabuwar tsiya ba...." Hada idon da suka yi da Mami yasa tace "Au to ai ba sai na raka ki ba ma...." Sai kuma ta koma bangarenta da sauri, Mami ta bi bayan Karime da har ta fita, Karime ta juyo ganin Mami ta tsaya tace "Hajiya kiyi hankali da kishiyar nan taki, bata sonki bata son yar da kike riko, wnn milon da kaka ke batu a kai ita ce ta xuba abu a ciki don da farko ni ta ba in xuwa ban samu nayi hakan ba shine taje tayi da kanta amma ta mance bata rufe murfin ba...." Tana fadin haka ta ciro milon ta mika ma Mami tace "Gashi don tana iya biyoni tace xata amsa idan na bar gidan nan" amsa Mami tayi tana kallon milon, Karime ta nufi gate da sauri tana goge idonta, sai ga Mumy ta fito, Mami ta mayar da gwangwanin bayanta, Mumy tace "Lahh har ta wuce? Canji na fa na jiya da yamma na wajenta bata bani ba, har dubu uku fa...." tana fadin haka ta nufi gate kusan da gudu, Mami tayi wani murmushi ta juya ta koma ciki, parlonta ta shiga ta bude milon tana kallon content din, ta girgixa kai ta wuce bandaki nan ta xubar da gaba daya a Bathtub ta bude ruwa ta juya ta fita rike da gwangwanin. Mumy ce xaune dakin Sadiya sai rusa kuka take, Sadiya tayi tagumi ta kasa cewa komai, Can tace "Kai kema dai wllh sai kace dakikiya, toh garin yaya ma xaki bar murfin gwangwanin a bude, ke meyasa baki yin abu da hankali, ynxu da ace abun nan na backfiring fa? Sannan uwa uba ga kudin da aka kashe, Kai ni dai wllh idan abun nan bai bata min rai ba shegiya nake" Mumy na Shessheka tace "Wllh kakan nan mayya ce kawai ki yarda" Sadiya ta ta6e baki tace "Toh ita na Rakiyan fa?" Mumy na goge idonta tace "Aa dama cewa nayi bari in fara gamawa da na yarinyar tukun, gashi kuma komai ya tashi a aikin banxa" Sadiya tace "Toh Karimen ke kina tunanin a layin ta jefar da gwangwanin milon?" Mumy tace "Wllh kaf bbu flawan da ban duba ba a layin amma banga komai ba, rashin kunya fa sosai yarinyar ta min har tana neman dambe da ni a titi xata tara min jama'ah, har da kirana shaidaniya, toh ni kuwa ai bana biyeta ba sum sum sum na juyo, amma sai da na bincika jakar banga komai ba wllh sai gwangwanin madaran" Sadiya ta sauke ajiyar xuciya tace "Ikon Allah... Yanxu dai sai ki saka rana mu koma Zarian tunda haka Allah yyi da mu" Mumy ta marairaice tace "Toh amma ynxu ya xanyi da na wannan Rahinar, ni kinsan ba shiga bangarenta nake ba haka yarana, dama da kariman na nan ne nasan idan na bata xata yi ynda nace to gashi bbu ita ynxu" Sadiya tace "Toh aikuwa dole a san yanda xa ayi a shiga bangarenta kawai..." A hankali Mumy tace "Toh shkkn, Yau laraba ranan juma'ah sai mu koma Zarian" Sadiya tace "Toh Allah ya kai mu" Kaka na yanke ma Heedayah farce a dakinta sai mita take ita an maida ta boyi boyin yarinya duk wa enda suka tsintota darewa suke su barta da ita tayi ta wahala har dare, Heedayah dai sai turo baki take tana sauraronta, kaka tace "Toh bakya turo baki ba dama tunda gani naynny ki, ni kenan kullum a wahale inyi ta fama da maki bauta bakya gani balle ki gode min, bari Rakiyar ta dawo ayi ta takare yau, xanji amfanin aurota da Amadu yyi" Bude kofar parlon aka yi Salima ta shigo da sallama tana kas kas da cingam, kaka ta kalleta ta ci gaba da abinda take, Salima ta xauna tace "Ina yini kaka?" Kaka tace "Lafiya lau, ke dai har yau bbu matayi ko Salima? Toh Allah ya fiddo maki da na gari" Salima ta d'an harareta bata ce komai ba, kaka tace "Toh ai Ina jin Maryam din ma bata nan ta fice" Salima tace "Ehh na sani" Kaka tace "Ayyo, to tafiya xakiyi sai ta dawo ki dawo kenan?" Salima tace "Aa xan d'an kwana biyu a nan" kaka ta kalleta da sauri tace "Kwana biyu kuma? Toh... Allah dai ya ba Amadu ladan ciyarwa, amma ynxu ai abinci ya xama abinda ya xama a kasuwa, ynxu fa mun kusa mu ashirin a gidan nan" Mikewa Salima tayi tana taunar cingam dinta ta fita, kaka tace "Karuwanci dai a sarari ni 'ya su" A hankali Heedayah tace "Kaka wacece?" Kaka tace "Kanwar Maryam uwa daya uba daya, ai bin otal take tana kwana, kinsan uwarta ta rasu haka ma ubanta to bata da wani mafadi ynxu sai makwabta, Maryam ita ma da ba don auren dake kanta ba xata yi fiye da haka ina tsammani, kinsan kafin Amadu ya aureta har xuwa Abuja take wai yawon bude ido a can ma suka hadu da Amadun...." Heedayah tace "Meye yawon bude ido" Kaka tace "Toh ke ina ruwanki da xancen manya kina 'yar yarinya da ke" Heedayah ta turo baki Kaka ta ci gaba da yi mata yankar farcen tana cewa "Banda lalacewa ma ina ni ina hiran nan da ke" Bayan La'asar Salima na kwance parlor tana kallo aka bude kofa, Junaid ne ya shigo parlon da sallama, ta mike xaune a hankali tana kallonsa, Tunda suka hada ido ya dauke kai, ta bi sa da kallo tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau, ya gida?" Tace "Alhmdllh, nima yau na xo" yace "Ohk" parlon kaka ya shiga, ko gama gaisawa basu yi da kaka ba sai ga Saliman ta shigo, ta d'an xauna gefen kujera tace "Kaka bbu abinda xa ayi maki?" Kaka tace "Ehh to wankin bayi ne, daxu ban yrda da wanki Sajida ba, kinsan na sa an Kori dayar me aikin, ta saci milon Deedayah ni ko na sa aka sallameta, shine aka kira min Junaidu yanxu ince masa ya tafi ya siyo mata wasu...." Salima tace "Toh bari a wanke" cire karamin mayafinta tayi ta ajiye nan kan kujera ta nannade skirt dinta har saman Gwiwa, duk fararen kafafuwanta a waje, shi dai Junaid tunda ya kalleta sau daya ya dauke kai, ta nufi cikin bathroom din, kaka tace "Ae Salima yar albarka ce, ga haxaka wajen aiki, da fa idan ta xo gidan nan har kwaleman dakina tana min, kwana biyu ne kawai ta guji gidan nan, kasan yayartata bata da hali tsangwamarta kawai take shi yasa bata son xuwa ma" Junaid ya kalli kaka yace "Wacece yayarta?" Kaka tace "Kishiyar uwarka mana Maryam" Junaid bai ce komai ba, Heedayah tace "Kaka ko xaki basa ya yanke min kina min da xafi" Kaka ta jefar da nail cutter din a jikinta tace "Algunguma sai kije yyi maki da sanyi, yarinya sai sharrin jaraba kawai" murmushi Junaid yyi ya dau nail cutter din yana kallon Heedayah da ta 6ata fuska xata yi kuka, ya ja hancinta a hankali yace "Don't Lolly...." kaka ta mike tana kakkabe jikinta tace "Ni idan ta bata min rai ma sai ince ma Amadu na fasa xuwa gyaran idon da ita sai in ga ta tsiya"




Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....



Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096.....

Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍



Murmushi Shuraim yyi ya gyada kai yace "Toh Allah ya tsare" Kaka tace "Atoh yanxu kayi magana, Ameen dai..... Allah ya kai mu lafiya ya dawo da mu lfya kawai" Juyawa yyi ya fita dakin still smiling ya kulle kofar, Baffa dai na ta xaune bai iya yace komai ba, lkci lkci yake kallon wayarsa waiting for his son Sudais don kafin ya iso gidan sai da ya kirasa yace ya samesa gidan Abba, Kaka na kakkabe jakarta ta tabe tace "To su matan naka basu da niyyar xuwa yi min sallama ne Umaru?" Baffa yace "Dama ba wanda xai yi tafiya ake xuwa yi ma sallama ba Baaba, amma ai xa su xo sallaman" kaka da bata tsaya ta fahimci farkon maganansa ba tace "Toh kar ma su xo mana, xuwansu da rashin sa duk daya ai a wajena, meye hadina da su banda kai da ka auro su, matan da suka kusa kashe ni da kwai duk karni Allah yyi da sauran kwanana a gaba" Baffa na kallon Heedayah yace "Baaba meyasa ake bari tana baccin yamma haka?" Kaka ta daga hannu sama tace "Haka aka saban mata tun daga gun iyayenta wllh, sakakku ne iyayen nata duk sun sangartata sun lalatata, Banda haka katuwa kamar yarinyar nan ace tana tashi shan shayin dare, baka ga gwangwanayen kayan shayin da na tara ba xan ba 'yan gwan gwan, wllh xa su siya dubu biyu ko uku kila, kana maganan baccin yamma ai ko xaka shekara kana tashinta magagi kawai xata yi ta maka, to ni baxan iya wahala ba shi yasa nake barin ta, kuma bana rabo da tofa mata addu'a ba don halinta ba" Baffa ya gyada kai yace "Hakan na da kyau ai" Bude kofar dakin aka yi Sudais ya shigo da sallama, Kaka tayi tagumi tana kallonsa tace "Ta janye tsinannen bakin da tayi maka na xuwa gidan nan kenan, Kai dai kam baka yi sa'ar uwa ba Sudess, yau kusan wata daya kenan rabona da kai fa" Sudais da idonsa ke kan Heedayah ya xauna ya cire face cap din kansa, Baffa ya fara gaidawa sannan ya kalli kaka yace "Ina yini kaka" tace "Lafiya lau Sudess muna ta shirye shirye ashe da rabon xa mu hadu, kai ma ka xo sallaman kenan?" Yace "Sallama da wa?" kaka tace "Ni mana, gashi har na gama hada kayana" Yace "Hada kaya xuwa Ina?" Ta ja tsaki tace "India mana, ko baka da labari ne? Au da yake uwarka ta hanaka xuwa gidan kilan shi yasa baka da labari, ae ni da Rakiya xa mu kai ta indiyan" Ya wara ido yace "Toh ai naga ba da ke xa aje bane Hajiya Kaka? ko wani ya bude baki yace maki har da ke ne a tafiyar kika hada uban kaya haka?" Kaka tayi shiru tana kallonsa bayan ta hadiye wani yawu da kyar, ya danne dariyar sa yana xare mata idanuwansa yace "Mami da Shuraim ko Junaid ne ai xa su yi tafiyan ai, ko mafarki kika yi xa a je da ke ne baki ba mu labari ba kika tsiri hada kaya" Kaka ta juya a hankali tana kallon Baffa dake danna waya, Sudais yace "To ba a ma barin tsofaffi su shiga asibitin, don su ma tsoffin kansu ai cutane...." Baffa ya jefa masa wani kallo, ba shiri yyi shiru trying hard not to laugh, kaka dai magana ya makale mata sai 'yan idanuwa, Baffa yyi gyaran murya yace "Kina ji kaka, kece baki fahimci abun nan ba tun farko, kinga dole ana son a samu masu ilimi sosai su je tare da ita, sannan kin san ynda xaman asibiti yake kuma a gaskiya baxa ma su barki ki xauna ciki ba tunda kin manyanta, shine muka yanke shawara da Amadu cewar Hajiya Rahinah da Shuraim ko kuma Junaid su tafi can din tare da ita don shi Sudais baxai je ba yace, Kinga ai duk masu ilimi ne, komai xuwa xai yi da sauki tare da su, ke kuma daga baya ko kafin a sallame su ne sai a kai ki ki sauka hotel a dinga kai ki asibitin kullum kina dubata...." Kaka ta sauke ajiyar xuciya a hankali tace "Toh daga kai har Amadun da duk wanda ya kawo wannan shawaran ku je na bar ku da Allah...." Sai kuma ta fashe da matsanancin kuka ta kwantar da kanta saman katon akwatinta, Baffa ya bude baki yana kallonta ya kasa cewa komai, Sudais duk irin yanda yake dakewa bai san lkcn da ya fashe da dariya ba har da kyakyatawa, Baffa ya juya fuska daure yana kallonsa, Mikewa yyi da sauri yana kokarin hadiye dariyar sa yace "Meye kuma abun barin jama'ah da Allah kaka?? Daga fadin gaskiya?" Cikin rawar murya ta dafe kirjinta tace "Ae sun cuce ni ne sun toxarta ni sun kunyata ni Sudess, yanxu da wani idon xan kalli duniya ince masu ba da ni xa aje ba? Dama ashe Deedayah na da wani me muhimmanci bayan ni a rayuwar nan bani da labari? Ashe dama Rakiya munafuka algunguma ce ita ma bani da labari?" Wani kukan ta kuma rushewa da kai kace yarinya ce, Sudais yace "Toh ai ba ace baxa ki je ba fa kaka, cewa aka yi su fara yin gaba daga baya sai ke da Abba ku bi su" Kaka ta dakatar da kukan da take yi ta daga hannu sama da sauri tace "Aa wllh na yafe suyi ta tafiya har bangon duniya idan da matsallaki su tsallake bangon duniyar ma bbu abinda ya sha ma Patuu kai, dama ai ban hada uban komai da shegiyar makauniyar ba karambani na ne" Mikewa Baffa yyi ya fita dakin gaba daya ransa a bace, Sudais na nunata yace "Ke dai kin fiye wahala da neman fitina, tsofe tsofe da ke ina kike son a kai ki? Jinyarki xa aje india ayi ko na Heedayah?" Kaka na nunasa ita ma tayi fici fici da ido tace "Wllh tllh idan ka bari na maka baki sai ya bi ka, uwarka ce tsohuwa ba ni ba, to sae me don su Umaru da Amadu sun munafurce ni? Ae dama munafukan ne tun suna yara, Ga dai gari da yawa maye ae baya ci kansa ba, dama yanxun nan xan bar gidan nan inga shegen da xai hanani in tsine masa bbu ruwana" Tana fadin haka ta mike ta fara neman gyalenta tana matsar kwalla, Sudais sai kyalkyala dariya yake yace "Sai ki fi ruwa gudu ai, mu ba mun huta da wahalar ki ba ma, dama duk kin addabemu kin dame mu" Kaka ta juya tana kallonsa ta nufesa ta cakumosa tana huci tace "Don kaza kazan ka nice wahalalliya??" Gwalo yyi mata ta kara rushewa da kuka ta sakesa ta xauna nan kasa tana rera kuka, suka yi ido hudu da Heedayah da hayaniyar kaka ya tasheta ta mike xaune tana bin ko ina da kallo, a mugun fusace kaka tace "Munafuka maxa sauko min saman gadon kar in jefar da ke" Turo baki Heedayah tayi xata sauka, Sudais ya karasa yana dariya ya kama hannunta ta sauka, kaka tace "Dama duk a xo a fitar min da kayanta daki na kada in konasu wllh wllh" Sudais ya nufi kofar fita da Heedayah yace "Baxa dai kije India ba idan xa ki sa ma ranki salama ki saka, ance maki tsofaffi na fita India ne, ke a dole xa a hau jirgi, to sai a dau na annabawa dai" Daga haka ya fice da sauri kafin ta ce komai, ya nufi part din Mami. Baffa na tsaye compound tare da Shuraim da ya ki shiga dakin kaka shi dai, Baffa ya kalli Shuraim yace "Me yasa baxa ka bi su Shuraim? Barrister ya ce min da junaid xa su tafi" Shuraim ya shafa kansa yace "Haka nan kawai Baffa" Baffa yace "But you need to go as your father's representative tunda shi baxai samu xuwa ba, shi Junaid can go anytime" Shuraim yayi murmushi kawai bai ce komai ba, Muryar Mumy suka ji ta leko tace "Ni na hanasa tafiya Doctor, tunda ba a maida uwarsa bakin komai ba a gidan uban me xai je yi masu India?" Baffa ya juya yana kallonta, can yace "Wnn ba girman ki bane Maryam" bata tanka sa ba ta juya ta koma, Baffa ya girgixa kai bai ce komai ba, Suna tsaye har Abba ya dawo ya samesu wajen, Abba na ganin yanayin yayan nasa dama bai ce komai ba duk suka shiga cikin gidan, parlor suka tadda kaka tana jan akwatin ta fuska a tsuke, Mumy na daga dining tana dariya kasa kasa dadi kamar ya kasheta, Abba yace "Ina kuma xa ki Baaba?" A mugun fusace tace "Rufe min

Please Login or Register in order to submit comment