Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
baiyi ba yasa bai kula da shigowarsu ba sai a kurarrwn lokaci. Da hanzari yai kokarin kaucewa. Itacen kanshi na watsewa kan motar su fu.ad din da ko ina. Wani mugun birki fu.ad ya taka daya razana su anti fati. Motar ya bude a fusace ya takasa wajen mutumin daya fadin kasa. Ya tashi yana kakkabe jikinshi. Dai dai fitowar su anti fati daga mota ji kake wani. Tas! Fu.ad ya dauke mutumin da a haife ya haifi irin fu.ad din uku da mari. "Baka ganin motane? Wanne irin jahilci ne wannan?" Daga anti fatima har su lukman suka karaso wajen da salati. Marin fu.ad anty fatima tai tana salati da girgiza kai da danyen aikin da fu.ad yayi. Mutumin ta kalla da yake rike da kunci yana kallon fu.ad da mamaki a fuskarshi. Hannu fu.ad ya daga lukman ya rike shi a tsawace yace. "Haba mana fu.ad ya isa haka. Wanne irin masifa ne wannan" "lukman daka kyale shi ya rama marin. Dan wallahi ba wata rashin kunya dazai nunamun kuma" Kallonsu fu.ad yai a kyamace ya wuce ya koma mota yana huci. Har kasa anty fatima ta tsugunna tana ba mutumin hakuri. Su duka suka hada baki har da lukman. Mutumin ya jinjina kai. "Bakomai yata. Kuje kawai Allah ya shirya" Mota ta koma ta dauko kudi a jakarta ta dawo inda mutumin ke tattara itacen shi. "Baba ga wannan" Ya dago ya kalleta. Ya girgiza kai yace. "Nagode 'ya ta amman bazan karba ba" Wasu hawayen takaici suka zubo ma anty fatima. Ta goge su ta tsugunna murya na rawa tace. "Badan abinda kanina yai maka ba baba. Kyautatawa ce dan girman Allah ka karba" Ya jima yana kallonta kamun yasa hannu ya karba yace. "Nagode" Ta juya ta shiga mota. [6/10, 9:53 AM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ πŸ“šπŸ“š_* [6/10, 9:55 AM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: AKAN SO 7 *πŸ’˜πŸ’–AKAN SOπŸ’–πŸ’˜* ~Written by~ :Luβπα SufyΞ±Ο€ 07 "Fu.ad yaushe ka kara lalacewa haka? Wancan mutumin bai isa ya haifeka ba har zaka iya daga hannu ka mareshi?" Anty fatima ke fadi rai a bace. Wani numfashi yaja da alamun relief. Yace "Thank God bashi ya haifeni ba. And karki sake dagamun hannu ba yaro bane ni" Wani abu ya tokare mata wuya. Anty maryam tace. "Fu.ad rashin kunya ko?" Juyowa yai daga inda yake zaune ya watsa mata wani kallo hadi da fadin. "Mind your own fucking business" Fu.ad ke rashin kunyar amman lukman dake zaune shi yake jin kunya. Gabaki daya ji yake daman motar su pha.iza ya shiga da baiga wannan bacin ran ba. "Ka wuce muje fu.ad. And do us a favour kayi shiru muji da abu daya" Lukman ya fadi ya juya ya kalli anty fatima dake sharar hawaye. Anty maryam kuma tayi tsuru tsuru a gefe yace. "Dan Allah anty kuyi hakuri. Abar maganar nan. Muji da abu daya" Kai kawai anty fatima ta daga. Fu.ad ya wani fizgi motar duk yana gwara su da jikin motar. "Maza kashe mu to" Lukman yace rai bace. Ko kula shi baiyi ba. Kawai tafarfasa yake a ciki. Kaman shi anty fatima zata daga hannu ta mara akan wani tsohon daqiqin talaka. Ya tabbata da basu hada jini ba saiya rama marinshi. Kuma sai yasa an kulle masa ita. Suna karasawa ya samu waje yai parking. Mutane ne cike unguwar kaman zata fashe. Anata alwala kasancewar yamma tayi sosai. Dan a hanzarta akaita makwancinta. "Ku nemi wani ride din home" Fu.ad ya fadi bai jira amsarsu ba ya fice ya doka murfin motar da karfi har wasu dake gefe suka juyo suka kalle shi. "What?!!!" Ya bukata a tsawace. Suka sadda kansu kasa. Yace yan sa idon banza kawai a ranshi. Fitowa su anty maryam sukai sunata kuka. Dan yanzun mutuwar ke kara shigarsu da wani sabon yanayi. Basu bi takan fu.ad ba suka wuce abinsu. Lukman yazo ya raba zai wuce shima fu.ad yace. "Ina kuma zakaje? Aika tsayani ko?" Cikin idanuwa lukman ya kalle shi. "After abinda kai wallahi kunya nakeji ace tare muke" Yana gama magana ya wuce abinshi. Wani mutum yai ma sallama suka gaisa ya karbi butar hannunshi da fu.ad ke jin ai ko wajen zai hade bazai iya wanke ko takalmi da ruwan ciki ba. Ballantana har azo ga jikinshi. Allah kadai yasan daga inda butar ta fito da kuma kalar germs din dake jiki. Motarshi ya bude ya dauko robar faro daya sabuwa. Ya rufe motar. Wajen ya karema kallo dan baiga inda zai tsaya yai alwala ba. Da alamar tsantsar takura a fuskarshi ya hango wani dutse. Ya karasa wajen ya zauna ya kwance takalmin kafarshi. Alwala yai sannan ya mayar da komai ya daure takalmin. Haneef ya hango ya karasa wajen shi. Wani kallo haneef yai masa daga samanshi zuwa kasa. "Ka cire wannan glass din" Haneef yace yana dauko mukullin motarshi daga aljihu. Ya mika masa. "Car dina yana bayan can. Kaje ka dauko takalmi ka cire na kafarka" Kabar mukullin motar yai daga hannun haneef muryashi can kasa yace. "Bana so ana fadamun abinda zanyi. And menene matsalar takalmina?" Wucewa haneef yai ya kyale shi. Gaba daya gidansu haneef ne baya jurar rashin kunyar fu.ad. Bashi bane babba amman har su anty fatima suna ganin girmanshi. Saboda yanada hankali. Magana ma sai dole yake yinta. Baya shiga harkar kowa. Kuma sunfi shakuwa da fu.ad. Ko a yarinta in fu.ad ya janyo rigimar data fi karfinshi haneef din yake shigar masa dole. Shi da kanshi yakan rasa ta ina haneef yake bullowa sanda yake bukatarshi. Wucewa yai ya dauko takalman haneef din yan zire. Ya saka da alkawarin suna dawowa jana.iza zai sake su. Dan sun bala.in bata mishi shiga. Badon haneef bane bama bazai sake ba. * Suna dawowa yaje ya sake takalmanshi. Bai nemi lukman ba. Shima yai zuciyar kowa yai harkar shi. Haneef ya lalubo dakyar saboda taron mutane. Ya mika mishi mukulli yana fadin. "Saikun taho" Da mamaki haneef yace. "Meaning?" "Gida zan tafi. Yunwa nake ji like sosai fa" Jinjina kai haneef yai. "Wai yaushe zakai hankali? Will you go and remove that shoe ka dawo a zauna dakai. Kama ga abba? Ka mishi gaisuwa?" Kaman fu.ad zaisa ihu yake kallon haneef. "Abba gaisuwan me zan mishi? Bana zo ba anyi jana.iza and dare yana yi fa" Wani murmushin takaici haneef yai. Muryarshi da alamun gajiya yace "Anan zamu kwana har sai anyi sadakar ukku" Wani pale fuskar fu.ad tai. Ya kwana uku a ina? Wannan garin da tun daya mallaki hankalinshi zai iya kirga zuwansa. Ya bude baki ya tabbatar ma haneef da cewan ya samu matsala inhar yana tunanin zai kwana daya ma ba uku ba a wannan kauyen. Kaman daga sama sukaji muryar abba yace. "Yawwa fu.ad ka kira lukman kuzo zan aike ku" Juyawa yai da fara.a a fuskarshi yace. "Abbah ..." Fu.ad ya fadi da farin cikin ganin mahaifin nashi. Dan tunda yazo yau sati daya kenan bai saka shi a ido ba. Da sassafe ya tafi wajen training kamun ya dawo kuma ya fita. "Fu.ad lemuka zaku siyo da ruwa. Sai nama kadai samu mamanku ko ka kirata a waya saita lissafa maka" ATM baba yake kokarin daukowa a aljihu fu.ad yace. "No abba. Zan siyo kome ake bukata. Kabarshi kawai" "Allah yai maka albarka. Ya kara daukaka kaji" Ya amsa da amin. Abbah ya maida hankalinshi kan haneef. "To kai muje ko da za.ai wani abun" Lukman ya kira harta yanke bai dauka ba yai mishi text. "Idiot. Abbah ne ya aikemu to mu hadu mota" Momma ya kira ta fada mishi abubuwan da suke bukata. * Har suka gama siyayyarsu tas lukman bai kula shi ba. Suka koma gida dan su dauko kayan sakewa. Gaba daya fu.ad ji yake an takura ma rayuwarshi. A ina zai kwanta ma? Me zaici a ina zai wanka? Cake ya kwasa leda biyu ciccike ya dibi cincin da yoghurt da yawa. Zaka rantse sati biyu zaiyi. Yawan training din da yake yi yana burning mishi energy da wuri. Yasan abinda ya diba ya masa kadan. Balle ba wani abincin kirki bane. Ko kaya kala takwas ya diba dan baya iya wuni da kaya daya a jikinshi. A mota ya samu lukman zaune. Lokacin anata kiran sallar isha.i. "Ko muyi sallah mu sauke nauyi?" Fu.ad ya bukata. Kallon shi lukman yai ya fito daga mota sannan yace. "Da ace yanda kake kyautata sallah haka halayyarka take da kaji dadi" Dariya abin yaba fu.ad sosai. "Halina is just fine dan rainin hankali. Ka gama fushin kenan" Yamutsa fuska lukman yai. "You disgust me. Ewww" Da gudu fu.ad ya bishi ya ruga yana dariya. * Waje suke zaune har wajen tara da wani abu na dare. Haneef na kallon yanda fu.ad ke sosa hannuwa alaman sauro ya ishe shi. Dariya yai kasa kasa. Tabararren banza ya fadi a ranshi. Gani yai abun yai yawa dan shi kanshi sauron ya dame shi. Balle kuma fu.ad da kwata kwata bai saba shiga irin wannan wajajen ba. Kallon shi yai shida lukman yace. "Ku tashi muje in kaiku inda zamu kwana ko?" Ba musu suka tashi. Gidan wani dan uwan baban sukaje bayan gidan hajiya babba. Saboda cikin gidan hajiya babba mata ne kawai. Kasancewar daga ita sai yan aikinta da take da rai. Sai wasu yayan dangi da take rikewa. Gidan ba wani babba bane can. "Tafdi" Fu.ad ya fada ganin gidan da suka tunkara. Wani saurayi da zai kai tsaran haneef da sai lokacin fu.ad ya kula dashi. Ya karasa ya bude wani shago jikin gidan da kyauren langa langa. Hannun haneef yaja gefe. Kaman zai kuka. "Kasan bazan iya kwana anan ba ko?" Ya karasa yana nuna shagon da hannu. Hannun haneef ya kama ya sauke kasa yace. "Last i check baka da wani option. Inkuma zakaje kace ma abbah ba zaka kwana bane saika dawo" Kasa ya kara yi da muryar da yakanyi amfani da ita ya samu abinda yake so wajen haneef din da suna yara. "In tafi gida. Da sassafe in dawo" Kallon baka da hankali haneef yai masa. "Please..... " Yanda haneef ya zaro ido zai tabbatar maka da fu.ad fadin please din nan da fu.ad yai abune mai bala.in wahala a wajen shi. Numfashi ya sauke. "Ka hakura fu.ad dare yayi wallahi. Gobe in Allah ya kaimu saika koma gida" Yanda yai da fuska yaba haneef tausayi. Dan yasan bai saba ba sam. Kama hannunshi yai kaman yaro. Yaja shi zuwa cikin shagon. Ko ina share yake tsaf. Da leda a shimfide sai katifa an lailayeta da zanin gado. Kusurwar dakin jakunkuna ne da wasu kaya a rataye jikin kusa. Sai takalmansu can gefen wni bango kan siminti wajen da alamu ledar dakin bata kai ba. Haneef ya karasa ya cire takalminshi ya ajiye inda yaga masu shagon na ajiye nasu. Ya koma kan katifar kusa da lukman ya zauna. Fu.ad suka kalla tsaye kofar dakin. Idanuwan nan nashi kalar na turawa sun wani yi haske. Suka bushe da dariya. Baice musu komai ba dan ya kusa kuka. Ya fara takawa da takalmin bai ko kula haneef dake mishi magana ba. Wani farin hanky ya dauko daga aljihunshi kato ya shimfida kan zanin gadon dake jikin katifar sannan ya zauna kaman wanda zai hau k'aya. "Kai da zakai birkida kan katifar. Meye na saka hanky kuma. Ko kan leda zaka kwana?" Cewar lukman da ya sake bushewa da wata irin dariya. "Fuck you and damn your mouth" Fu.ad ya fadi yana kai mishi duka. "Manners fu.ad. Kamata yai ace momma na wanke maka bakinka da sabulu" Haneef da yake dariya shima ya fadi. Pillow din dake gefe fu.ad ya dauka ya jefa masa a fuska ya kauce pillow din ya samu lukman. Dauka yai ya rama suka soma hauka cikin dakin haneef ya musu ihu. "Dan kaniyarku mutuwa akai mana fa. Kuma ba a gida kuke ba. Ku nutsu please" Dakyar haneef ya samu fu.ad ya cire takalminshi yabar socks. Ga katifa daya su uku. Ga sauro. Tashi fu.ad yai ya hada kanshi da gwiwa kawai yana jira gari ya waye. [6/10, 9:55 AM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ πŸ“šπŸ“š_* [6/10, 9:56 AM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: AKAN SO 8 *πŸ’˜πŸ’–AKAN SOπŸ’–πŸ’˜* ~Written by~ :Luβπα SufyΞ±Ο€ 08 Lukman ne ya zo gyara kwanciya yaga mutum a zaune. Idanuwanshi ya ware sosai. Ya lalubo wayarshi ya haska. "Fu.ad?" Ya kira muryarshi cike da bacci. Dagowa fu.ad yai ya kalle shi da idanuwanshi cike da bacci. "Ka kwanta mana" Ya yatsine fuska. "Bazan iya bacci anan ba lukman. Ga zafi ga sauro. Wajen kuma ya matse da yawa. Just go back to sleep i will manage" Girgiza kai yai alamar eh. Haneef dake bacci gefensu ya motsa saboda yanajin maganganu sama sama. "lafiya?" Ya tambaya yana kare idanuwanshi daga hasken fitilar wayar lukman. "Fu.ad ne wai bazai iya bacci ba" Cewar lukman. Wani guntun tsaki haneef yaja. Matsalolin fu.ad yawane dasu. Pillow kawai ya ja ya sauka daga katifar zuwa kasa. Lukman ma pillow ya dauka ya sauka kasa kan leda. "Ku dawo bacci ne bazan iya ba. Zafi ga sauro" Fu.ad ya fadi irritated. "Ka kwanta malam" Inji haneef. Girgiza kai yai. Yasan taurin kan fu.ad kaman yunwar cikinshi. "Lukman tashi mu koma. Dan ubanka karka kwanta" Baccinsu suka koma suka kyale shi. Shikam daya fara baccin ma farkawa yake. Ga kanshi na wani irin ciwo. Kan kunnenshi aka kira sallar asuba. Ya tashi su haneef. Abu dayane matsala. Bandakin dazai shiga. Haneef suka bari dakin suka fita zuwa motar fu.ad din cewarshi zai dauko ruwan dazai alwala. Suna hanyane yace. "Damn. Wallahi nabar brush dina. Ban dauko komai ba" "Karka damu. Sanin halinka yasa na dauko extra" Numfashi fu.ad ya sauke. Sukaje suka dauko. Suka koma. A bakin shagon sukai brush dinsu. "haneef fitsari fa nake ji" "zo ga bakina. Kayi a ciki" Lukman ya bushe da dariya. Wani mugun kallo fu.ad ya watsa mishi kamun yace. "wallahi da gaske. Lokacin sallah na wucewa" Cikin shagon haneef yakoma ya kira khalid mai shagon. Ya tambaye shi ko da akwai bandaki kusa sannan ya fito. "Saika taso" Ba musu ya tashi ga mamakinshi cikin shagon suka koma. Haneef ya bude wani kofa da duk zatonsu wadda zata kaika cikin gida ce. Ban dakine dan matsakaici. Shafe da siminti. A bushe yake tsaf. Bokitin karfe a gefe sai kwandon soso. Sai masai irin namu na gargajiya da murfi a rufe. Wani baya fu.ad yai yana bata fuska kaman zaiyi amai. "Karka cemun anan zanyi fitsari" Takaici ya hana haneef magana. Fita yai yabar masa shagon. Ya fito ya samu lukman yace. "Seriously kana kokari. Ya kake baka fasa bakin fu.ad ne?" Dariya lukman yai ya girgiza kai. Suna nan fu.ad din ya fito fuskarshi a yamutse. "Allah ya kiyaye in ban kwashi infection ba. Ina komawa gida zance asibiti a mun check ups" Fu.ad ya fadi yana samun wani dutse ya zauna zaiyi alwala. "Asibitin murtala ka kwasa ba infection ba" Haneef yace yana masa kallon ka kure rainin hankali. Wannan karon harshi fu.ad din saida ya dara. Tare sukaje asuba suka dawo. Fu.ad nason yadanyi gudu ko ya yake. Nan fa shi dole saiya cire dogon wandon shi yabar gajere da singlet. Ba yanda haneef baiba tunda baizo da kayan gudu ba. Ko yaje dana jikinshi ko ya hakura yaqi. "Idan baka kwashi infection a bandakin nan ba. Zaka makalo a jikinka ne" Lukman ya fadi. Ai ba shiri ya dauki kayanshi ya maida yace ma lukman suje. Tare suka fita gudun. Sun sami wajen awa daya. Dan gari ya fara wayewa. Mike hanya kawai sukai. Dan ma lukman na dan taba kwallo lokaci lokaci. Duk da haka s yana ce ma fu.ad yadan rage gudu. Fu.ad yaji takalminshi yadan kwance. Dan haka ya tsaya ya gyara. Lukman yake ma dariya dayai ma nisa. Tsayawa yai yana jiranshi. Kaman daga sama yaji saukar wani ruwa mai danqo danqo tun daga wuyanshi har bayanshi. Wani numfashi yaja na mamaki. Lokaci daya wani bacin rai ya maye gurbin mamaki. "What the hell!!!......" A fusace ya juya ya sauke idonshi kan yarinyar dake tsaye kofar gida da wata tukunya da bayanta ya gaji da yin baqi. Yanayin fuskarshi kawai ta kalla tace. "Na shiga uku ni safiyya. Wallahi banganka ba" Ta fadi tana zaro idanuwanta. Baisan me ya kamata ya fara yi ba. Gaba daya gefenshi a jike yake. Ruwan koma menene har cikin sumarshi da yake bala.in ji da ita. Har gefen fuskarshi. Da tashin hankali lukman ya karaso yana rike baki. "Fu.ad......" Ya kira da alamomi da dama. Ban hakuri. Tsoro da jimamin abinda zai auku tun kamun faruwarshi. Takawa fu.ad ya soma yi zuwa inda yarinyar take. Numfashi yake ja yana fitarwa. Yana kokarin calming kanshi. Idanuwanshi harsun kara hasken nan da sukanyi idan ranshi yakai karshe wajen baci. Lukman ya riko masa hannu yana fadin. "Please fu.ad......." Kwace hannunshi yayi. Ganin datai ya tunkaro ta har yana gab da ita yasa ta tura masa tukunyar. Da sauri ya rike tukunyar da ta rigada ta gama lalata masa gaban riga. Cikin gida ta kwasa da gudu. * "Innaaaaaa!" Take kira da tashin hankali. Sanin cewar safiyya bamai kwaramniya bace ba. Yasa inna fitowa da sauri dan taga ko lafiya. Bayanta safiyya ta labe tana sharar hawaye. "Ke wai lafiyarki. Meya koro ki?" Inna ke tambaya tana kokarin janyo safiyya daga bayanta. * Ganin fu.ad rike da tukunya a hannu yana danna kai gidan mutane yasa lukman riko shi. "Fu.ad gidan matan aure ne fa. Dan Allah kayi hakuri kazo mu tafi" Juyowa yai da tukunyar a hannu. "wallahi ko ka sakeni ko in kafta maka tukunyar nan. Like hell inyi hakuri" Ganin ran fu.ad ya gama bi yasa lukman sakinshi. Yasan ba.a tempting maganar shi. Tsaf zai kafta masa wannan bakar tukunyar. * Inna nata kokarin banbaro safiyya daga bayanta amman ina. A banza sake makalewa take tana share hawaye. Tafiya inna taji data sata kallon shigowar fu.ad rike da tukunya da hannuwa duka biyu. Ga rigarshi da take fara kal ta gama tashi daga aiki. Jikinshi daga gefe rabi a jike. Dafe kirji inna tai. "Na shiga uku ni lami. Safiyya badai ruwan dan waken bane kikai masa wanka dashi???" Tukunyar fu.ad ya ajiye a kasa. Yana kare ma gidan kallo. Gidan kasane na asali ma kuwa. ko shafe babu a kasan gidan. Kaurayen langa langa. Duk da tsaf yake babu shara. Akwai komatsai cikin gidan. "Dan Allah dana kayi hakuri" Inna ta fadi a raunane. Dan kallo daya zakaima fu.ad kagane hutu da kudin dake tattare dashi. Ga wata isa da gadara dake fita daga jikinshi kaman hayaqi. Daga ma inna hannu yai. "Karki sake hada sunanki da nawa a waje daya. And bake kikaimun laifi ba. Yarki ce da take labe bayanki. Hakurin daga bakinta nake son ya fito" Kallon shi inna take baki a sake. A ranta tace safiyya ta janyo musu bala.i. Wannan tsageran kuma ko daga ina ya fito oho. Da alama dai bako ne a garin dan ko kala kalarshi bata taba gani ba. Safiyya ta fisgo. "Bashi hakuri...." Hawayenta safiyya ta share. Ta sauke idanuwanta cikin na fu.ad. Ta kasa magana saboda tunda take sau daya ta taba ganin mai irin idanuwanshi. Shima aikenta siyan ruwan sanyi akai da azumi gidan malam.mudi ta samu suna kallo. Aka nuno wani bature har tana mamakin kallar idanuwan. Kallon da take masa yasa shi yaji wani iri. Lokaci daya yaji abinda bai taba ji ba a zuciyarshi. Wani squeezing yaji tayi har numfashin shi na son tsayawa. Idanuwanshi ya lumshe dan wani abu dake fizgarshi cikin nata. Dai dai shigowar lukman dayaga shirun yai yawa kar ace wani danyen aikin lukman yayi. Dan yasan kadan da aikin shi. Inna lukman yace ma. "Ina kwana" A mutunce ta amsa ta dora da. "Yaro dan Allah kuyi hakuri. Wallahi safiyya bamai kwaramniya bace na tabbatar da kuskure ne" Hannun fu.ad da yake tsaye kamar an dasa shi lukman yai. Tunda har Allah ya tsare baiyi wani rashin mutuncin ba. Fu.ad kam duk wani rashin mutuncin dayai niyya yanajin shi yana narkewa. Saidai koma menene ba.a masa laifi a tafi a banza. Fisge hannunshi yai yace. "Sai tabani hakuri. Wallahi sai taban hakuri" Da sauri safiyya ta sauke idanuwanta daga cikin nashi jin maganar dayayi. Wani yanayi take ji. Kaman zazzabi ya kamata. Muryarta a sarke ta tsugunna gaban fu.ad tace. "Ka...ka kayi hakuri dan Allah" Sanda ya shigo gidan yai niyya ta ja ma kowa. Duk sai an kulle yan gidan. Saiyai rashin mutuncin da basu taba tunani ba. A karo na farko a rayuwarshi dayaji ya kasa abinda yai niyya ya kuma rasa dalili. Hannu yasa yadan daki goshin shi. Yana son koma menene ya same shi ya warke. Dan ji yai tsugunnawar da safiyya tai mishi baya so. Har lukman ya zaro wayarshi daga aljihu zai kira haneef. Fu.ad ya kalle shi yace "Muje please" Ba musu lukman ya dauki hanyar waje. Dan gaji yake idan ya tsaya fu.ad zai iya sake shawara. Suna fita ya mike hanyar da suka biyo da gudu ba tare da ya waigo yaga ko lukman na biye dashi ba. Wata hamdala lukman yake jerowa dan har ya gama hango su ana rikici a police station. Shi kanshi mamakin abinda ya faru yake. Sai kuma ya tuna yanda fu.ad yake rike da tukunya. Mai zaiyi inba dariya. Hanya ya mika yana sassarfa yana shan dariya. * Babu ko sallama haneef yaji an turo kofar shagon. Kallo daya yaima yanayin fu.ad ya mike da hanzari yana fadin. "Ya Rabb. Fu.ad me ya same ka haka?" Cikin wani sanyin murya ya tsinci kanshi da fadin. "safiyya ce ta watsamun ruwan dan wake" "Ruwan dan wake? Safiyya?" Haneef ya tambaya yana son ya gane ma.anar maganar fu.ad. Sake kallonshi yake daga sama zuwa kasa. "Gaban rigarka kuma fa?" Ya tambaya yana kallonshi sosai. "Tukunyar dan waken ce ta mikomun" Abin yai yawa. Wata irin dariya haneef ya kwashe da ita harda hawaye. Sai da ya samu waje kan katifa ya zauna ya dafe ciki yana dariya. Lukman ne ya shigo da sallama. Kallon fu.ad da yake tsaye yai cuku cuku yake. Ya maida kallonshi ga haneef da ya kasa controlling dariyar da yake. Gefe ya zauna ya tusa tashi. Da sun fara dainawa suka sake kallon fu.ad sai su kwashe da wata dariyar. Tsaye yake yana kallon su. Abin ma ya wuce na takaici. Murmushi kawai yai ya juya musu baya yana kwance takalmin shi. Dakyar fu.ad ya iya controlling kanshi yace. "Wanne police station yan gidansu suke?" Yana mikewa dan yasan dole yaje solving rigima. Girgiza masa kai lukman yai yace. "Ba abinda ya faru fa......." A nutse ya gaya masa duk yanda sukai. Da tsananin mamaki ya kalli fu.ad da yake tsaye daga shi sai boxers yasa rigar daya cire yana goge gashin kanshi yace. "Who are you and ina ka kaimun kanina?" Rigar dake hannunshi ya jefa ma haneef daya cabe ta yana dariya. "But guess what. I am proud of you. Like sosai little one. Yau kaine da hakuri?" Murmushin da ba ko yaushe yake yi ba yaima haneef saboda wani rawa zuciyarshi take yi har yanzun. "In kun gama dariyar wanka nake sonyi. And lukman ka dauko mun kaya a mota" Lukman da yanayin maganar fu.ad bai dame shi ba ya daga kai kawai alamar yaji. Dan inda sabo ya saba da yanda yake magana cikin gadara. "Yan gidan nan suna da karamci. Ga ruwa nan ansa an jawo mana. Kai amfani da bokiti daya kabar ma lukman daya" Haneef yai masa bayani. Wani kwalo idanuwa yai waje. Ya taka a hankali ya tura bandakin yaga ruwa a bokiti. Tunda yake a rayuwarshi banda dazun da asuba baima taba shiga irin wannan bandakin ba. Baima san yazai fara wanka da ruwa a bokiti ba. Juyowa yai ya kalli haneef. "Dame zanyi wankan?" Daure fuska haneef yayi yace. "Wannan ruwan na bokiti. Ka watsa kawai tunda bamu dauko sponge dinmu ba. Yau zanje gida nima in dauko kaya sai in taho dashi" Girgiza kai fu.ad yake alamar ai shifa bai yarda ba. "Ni momma nake son magana da" Ya fadi yana kallon haneef da lukman a lokaci daya kaman wani yaron da akaima laifi yake neman mamanshi ya gaya mata. Ganin sun banza sun kyale shi yasa shi shiga bandakin yana doko yar kofar langalangar kaman zai karya musu ita. Hada idanuwa sukai shida lukman suka sake bushewa da dariya. [6/10, 9:56 AM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ πŸ“šπŸ“š_* [6/10, 9:57 AM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: AKAN SO 9 *πŸ’˜πŸ’–AKAN SOπŸ’–πŸ’˜* ~Written by~ :Luβπα SufyΞ±Ο€ 0ο»Ώ9 "A mikomun towel dina" Fu.ad ya fadi yana daga cikin toilet din. "waya hanaka shiga dashi?" Lukman ya fadi. Haneef kam tabe baki kawai yai. "Wallahi zan fito haka" Da sauri lukman ya dauki towel din ya kwankwasa ban dakin. Ya mika masa. Yanayin dariyar da yake. Yasan halin fu.ad babu kunya a idanunshi tsaf zai fito in basu mika mishi towel din ba. Yana fitowa lukman ya shiga. Jakarshi ya dauka. Banda comb da man gashi bai dauko komai ba. Sai kayan sawa da takalma. "bani manka indan shafa ma hannuwana" Vaseline haneef ya mika mishi. Dan shima bai dauko mai ba yace. "Ga dai na masu dakin" Ai da sauri ya janye jikinshi kaman ya miko masa miciji. Ajiye robar haneef yayi yaci gaba da latsa wayarshi. Kaya ya dauka ya sake ya gyara gashin shi da yake ta daukar ido. Kallon shi haneef yai yaga crazy jeans din dake jikinshi. Yaga duk a gwiwar zuwa kwauri. Har jikin cinya yaga ne. Sai riga fara data bala.in kamashi shi ba wani jikin kirki ba. Yasan inya masa magana ma fitsara zai sha ranshi ya baci a banza dan haka yai masa fatan shiriya kawai a ranshi. Dai dai sallamar khalid. Haneef ya amsa da fara.a a fuskarshi. "Ina kwananku" Khalid ya fadi yana ajiye kwanan shan daya shigo dashi a hannu. "Khalid ka tashi lafiya? Ya hidima kuma?" Haneef ke tambaya yana mikewa daga kwanciyar da yai. Khalid ya amsa shi da. "Alhamdulillah" Yana ficewa da sauri. Ya sake dawowa da leda a hannunshi. Kamshin kosai ya cika dakin. Fu.ad dake tsaye ya wani yamutsa fuska. Dan kamshin koma menene aka shigo dashi yana shirin saka shi amai. "Ga abin kari" Haneef yai masa godiya ya sauko ya bude ledar kosan. Gasu manya manya ya dauki daya ya gutsura. Rabon shi da kosai tun wani azumi da atika tayi musu shi. Hada idanuwa sukai da fu.ad dake masa kallon 'Me kake yi haka?' Share shi yai ya ci gaba dacin kosan shi suna dan hira da khalid din dake kallon fu.ad lokaci lokaci. Kayan daya cire ya daga a kyamace yace. "Ina za.a yadda wannan?" Idanuwan khalid ya zaro yana kallon kayan da fu.ad ke kira da a zubda. "Me ya same su?" Ya tambaya sanin fu.ad bazai kula khalid ba balle har ya amsa mishi tambayar dayai yasa haneef saurin cewa. "Yadan fita wata ta watso ruwa ya same shi" "Ayya bara sai na wanke masa su" Cewar khalid. Rolling idanuwanshi fu.ad yai. Ko ance ma wannan dan kauyen zai iya saka kayan da

Chapter 3 of 36