Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 10
ni me iya biya ne ayi miki komai ba tare da ko sisinki ba". Na sauke ajiyar zuciya na ce"to yanzu nawa ake buk'ata?" "Dubu d'ari biyu" Ya fad'a kai tsaye. Na dafe k'irji tare da zaro ido na ce"haba Nazifi! Ko sata na fara ai ba na jin zan had'a dubu d'ari biyu nan da kwana bakwai". Ya yi dariya ya ce"wa ma zai aike ki sata? Ki na mace,macen ma buduruwa,buruwar ma me kyaun suffa irinki Zinatu amma ki dinga tunanin ta inda za ki samu dubu d'ari biyu acikin kwana bakwai? Wallahi sai dai rashin niyya!" Cikin son gano inda zancen sa ya dosa na ce"ban fa gane ba,ka yi min dalla-dalla". Bai yi magana ba ya d'akko wayarsa a aljihu,kafin na ankara ya k'yasta min hoto,sannan ya ce"ba ni minti biyar ki gani". Ya cigaba da danne-danne a waya,kafin ya kalle ni ya ce"na fad'a miki ba ni kad'ai zan yi aikin ba,dole sai mun had'a da direban sa,duk da ma na ji ance bai fiya son tafiya da direban ba,sai in mahaifinsa ya matsa masa.Sannan wanda zai kula da abinci da kuma abun sha a wurin,shi ma dole sai mun biya shi,ke megadin gidansu ma sai mun biya shi,sannan shi ma abokina da za a yi aikin tare da shi sai an biya shi,ni kuma na yafe, na miki saboda Allah". Na ce"ni fa duk ba wannan ba,so na ke na fara jin yanda aikin zai wakana,idan na ji ba mai yiwuwa bane gwara na hak'ura kawai". Sai ya duba wayarsa da na ji shigowar sak'o ya ce"kin gani ko!? Dama na fad'a miki ai ki na da kadara" Ya yi maganar ya na murmushi Cikin rashin fahimta na ce"wai mene?" Ya ce"yanzu na turawa wani gaye hotonki,na ce masa haja ce sabuwa dal,nawa zai siya? Shi ne ya ce ya siya dubu d'ari biyar kwana biyu". "Nazifi ni ce hajar!?" Na fad'a da k'arfi,zuciyata na zafi Ya yi shiru ya na kallo na. Na d'ora"tun farko sai da na fad'a maka zan yarda da sharad'in ka ne kawai idan babu sab'on Allah a ciki..." Ya katse ni"wannan ba ya cikin sharad'i ai,idan ki na da hanyar samun kud'in an wuce wurin". Na ce"Nazifi,ban tab'a Zina ba,kuma ba zan fara ta ba saboda Salim,idan na bada kaina ka na da tabbacin abun da za mu shirya d'in zai yiwu? Idan ba mu yi nasara ba fa? Na yi biyu babu kenan fa,ko kud'in za su siyo min wani mutuncin? Idan ma aikin ya yi kyau,da wane ido zan kalli Salim bayan ya aureni? Me zan fad'a masa?" "Gaskiya ne!" Ya fad'a da d'an rauni a muryarsa Sannan ya ce"ni dama na yi tunanin ba ki da hanyar samun kud'in ne,shi ya sa na yi hakan". Na yi huci me zafi na ce"tabbas! Ba ni da wata hanya da zan samu dubu d'ari biyu,amma hakan ba zai sa ni aikata zina ba.Mutuncina na mijina ne in sha Allah, ba ma Salim ba,duk wani namiji da ya aureni ko da ba na son shi shi kawai zan mallakawa kaina.Zan dai nemi wata hanyar ba wannan ba,zan yi shawara". Ya ce"to,amma ki yi da wuri,kin ga lokaci ya na k'urewa" Na ce"in sha Allah! Sannan maganar get fas,na samu guda biyu, anjima zan k'arb'o a wurin Baby". Ya ce"yawwa! Ya yi kyau,idan na dawo da daddare sai ki taho min da shi sashenmu". Ranar haka na wuni ina ta tunanin ta inda zan samu wannan kud'in,to ni kam indai ba kayan lefena zan siyar ba ta ina kud'in za su fito? Ga shi sai hanya-hanya ya ke min,ya k'i sanar min yanda aikin ya ke,da dubu hamsin ne ma da tsaf zan shafawa idona toka na tambayi Habib,don na tabbata zai bani,amma gaskiya dubu d'ari biyu ya yi yawa,da me zai ji? Ga duka ga tsinka jaka! Dab da magriba na tambayi Anti zan je gida na d'akko wasu kayana,sai da ta yi min fad'a kafin ta bar ni,wai meyasa tun safe ban je ba sai da magriba? Haka dai na shirya na tafi shagon Baby,sai dai ina zuwa na tarar ba ta nan,wai lokacin tafiyarta gida ya yi.Na kirata a waya na sanar mata na zo mata nan,ta ce sai dai na k'araso gidansu tunda babu nisa,ta kwatanta min na kama hanya. WANI KUSKURE... Ban san zuwa na gidan su Salim a lokacin kuskure bane sai daga baya,da na je na tarar da megadi,amma bai hana ni shiga ba,ina dai tunanin Baby ta sanar masa za ta yi bak'uwa,lokacin har an shiga masallaci ana sallar magriba,a tsakar gida na tadda Baby,ta tareni da farinciki,mu ka k'arasa ciki,ta na ta murna Mu na zama sai ga wata matashiya ta zo ta kawo min abun motsa baki,na tambayi Baby wace ita? Ta fad'a min me taya su aiki ce,sunanta Habiba. Na sha lemon da ta kawo min,sannan mu ka gaisa da Baby na ce"yi sauri ki d'akko min,kin ga magriba ta yi". Ta ce"Tabb! Ai ki tashi ki yi sallarki,yau sai kin ci abincin dare a gidan nan". Na ce"rufa min asiri Baby,kunyar Ammi na ke ji wallahi". Ta kwashe da dariya,har da rik'e ciki ta ce"wato ga surukarki ko? Aikuwa dole sai kun gaisa,don ta san da zuwanki,sallah take yi shiyasa ba ta fito ba" Na tashi tsaye na ce"don Allah Baby ki rufa min asiri,wallahi sauri na ke yi". Ta yi murmushi ta ce"to bari na nuna miki abun d'ebe kewa". Kafin na yi magana ta ja hannuna,ta nufi wani d'aki da ni,ta tura k'ofar ta bud'e mu ka shiga,ni na yi zaton ma d'akinta ne,amma ina shiga sai na ji irin k'amshin da nake ji a jikin Salim ya daki hanci na,ga wani k'aton hotonsa a bangon d'akin,ya yi kyau sosai yana sanye da k'ananun kaya,a d'ayan bangon kuma na shi ne,shi da Baby,ta rirrik'e shi su na dariya,sun yi kyau sosai,kamar rak'umi da akala haka ta ja ni har kan gadonsa. Ta ce"ga d'akin angon ki nan,na san ba za ki gaji da jiran Ammi ba ". Na zauna a bakin gadon,kamar wata amarya,tuni na ji wata kasala ta rufeni,k'amshin sa duk ya cika d'akin,har na fara zargin ko dai ya na ciki? Na kalli Baby na ce" k'amshin Salim duka ya cika d'akin,ko dai ya na nan?" Ta yi dariya ta ce"turarukan shi dai su na nan,ko na ba ki d'aya?" Na zare ido na ce"rufa min asiri,idan ya tambaye ki Wanda ya d'auka fa?" "Sai na ce ke ce" Ta fad'a ta na d'age kafad'a.Na yi murmushi na tashi, na ce, "Don Allah mu fita,ni dai gida zan koma". Ta d'akko wani turare a gaban mudubi ta damk'a min a hannu ta ce" ni ce na ba ki kyauta". Na karb'a na ce"na gode". Da mu ka fito ba Ammi ba ta dawi falon ba,sai ta ce bari ta kira ta mu gaisa,ni dai duk sai na ji kunyar matar tun kafin na ganta,haka dai na zauna don kar Baby ta ji babu dad'i Wayata ta fara ringing na ga Nazifi ne me kira,kamar kar na d'aga sai dai na d'aga,get fas ne ya ke tambaya ta,na ce ya ba ni mintuna ina cikin gidan Ina gama wayar Ammi ta na k'arasowa tare da Baby,babbar mace ce y'ar gayu,fara ce tass! Don da gani ma hasken ta Salim ya yi Ta k'araso da murumushi a fuskarta ta zauna a d'aya daga cikin kujerun Na ji ta yi min wani kwarjini,na sakko na zauna a k'asa,kaina a duk'e na gaishe ta "Lafiya lau Zinatu,ta shi ki koma kujerar" Ammin ta fad'a Bam koma ba,kuma ban d'ago na kalle ta ba Baby ta ce"Ammi sauri take yi,bari na raka ta". Ta ce"to! Rowa za ki ma k'awar taki,ba za ta ci abinci ba?" Na yi saurin fad'in"na k'oshi Ammi,na gode". Na tashi na yi hanyar fita,ina ta wasa da kwalbar turaren ta cikin hijjabina. Kafin Baby ta fito daga d'akinta har na fice tsakar gida,bayan na yi wa Ammi sai da safe.Baby ta fito hannunta rik'e da leda,ta mik'o min,sannan ta ba ni get fas d'in guda biyu. Na amsa na ce"ke! Wannan ledar ta meye?" Ta ce"Ammi ta ba ki". Na ce"to ki taya ni godiya,Allah ya saka". "Ameen" Ta fad'a, ta na murmushi.Sai da ta raka ni har k'ofar gida sannan ta koma Ina tsaye a bakin titi ina jiran adaidaita sahu,na ga hango wani mashin tun daga nesa ya dalle min fuska da hanke,ni ma shi na ke kallo don ina son sanin ko waye,amma hasken ya kashe min ido har na kasa gane shi,ya zo ya wuce ni.Na shiga adaidaita,bayan na zauna na bud'e ledar,da kud'i na fara cin karo,na yi mamaki don haka na yi saurin d'akko su,na k'irga dubu biyar ne cif,sai wata atamfa me kyau,da mayafi,sai wani saitin turare a kwali,na ji dad'in kyautar sosai,na kai kwalbar turaren Salim hancina,na shak'a har da lumshe idona,sai na ji kamar ina tare da shi ne,na jefa shi jakata tare da kud'in,na kuma fara tunanin yanda zan yi idan Anti ta tambaye ni wanda ya ba ni. Ina shiga gida mu ka had'u da Nazifi,ya tare ni da fad'in"yawwa kin samu abun?" Na ce"an samu" Na d'akko get fas d'in na ba shi duka,sannan na yi masa bayanin kayan da Ammi ta ba ni Ya ce"tab! Aikuwa Anti ta na falo, don yanzu haka daga can na ke". Na ce"yanzu me zan ce mata?" Ya yi dariya ya ce"ai kawai ki bar min,dama yau zan je zance,kin ga sai ayi kyauta akan kyauta,ita ta ba ki,ke kin ba ni,ni kuma na bawa wata". Na harare shi na ce"kyautar surukar tawa? Ina so ni ma" Allah ya taimake ni hijjabi ne a jikina,na saka saitin turaren cikin jakata,na soke sauran kayan a jikina,na shiga d'akin. Washegari da safe sai ga sak'on Salim a wayata,hannu na rawa na bud'e,duk da na san ba ya nema na sai na yi masa wani laifin,ko sallama babu a sak'on,tambaya ta kawai ya ke yi,wai da fatan dai jiya ba gidansu na je ba. Na maida masa da amsa _"idan na je gidanku zai zama matsaka ne?_ Ina ta jiran amsa na ji shiru,na tashi na d'akko turaren da daga jiya zuwa yau na shinshina shi ya fi sau shurin masak'i. *MATAR SHIGE...!* _(Ba ta daraja)_ BY *SADIYA ABDUL* _(Maizafafa)_ *&?FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION&?* Page 16 *O'o! Fans=??,ni fa ba matar shege sunan littafin nan ba>?&?

Chapter 7 of 10