Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kan kujera tana murmushi Khalil kuma sai yanufi Hakiman yasaka hannu ya'amshi Aamir yana faɗin "a'a my Daddy Kai da zan zo in ganka akan gado ya naganka anan?" Yaron na washe haƙora cike da murna cikin tsamin maganar sa yace "Ankul ai na waice". "Haba dai?". Sai yagyaɗa masa kai yana tsalle a jikin sa kafin yace "wayyayi". Dariya gaba ɗayan su suka yi Zama Khalil yayi yaɗaura sa a jikin sa A lokacin ne Saleema suka gaisa da Hakima tana tambayan ta jikin Aamir ɗin "Ai gashi nan yaji sauƙi sai rigima". Khalil yace "wai haka Daddy kana rigima?" Cinno baki yayi gaba yana maƙe kafaɗa yace "kayya ne Ankul". Yanzu kam dariya sosai yaba su, har Khalil sai da yadara duk da be cika son yin dariya ba Hakima tace "iyeee Ni nake maka kayyan?" Sai yawaigo yana kallon ta yana ƙyafta idanu, kafin kuma yagirgiza mata kai alamun "a'a". Murmushi Saleema tayi tace "My son Ni baka ganni bane?" Sai yamayar da idanun sa kan ta, dasauri kuma yazamo a jikin Khalil ɗin yanufo gaban ta yana faɗin "Auncy.." "Na'am ɗan Aunty". Tafaɗa tana ɗaukan sa cike da fara'a Hakima miƙe wa tayi tana cewa "kunga na barku haka ban kawo muku komi ba kuma". Khalil yace "ina Bro ne ban ji motsin sa ba?" "Wlh ya koma Hospital yana da Patient". Hakima taba sa amsa tana ciro drinks cikin Fridge Sai kuma tajuya tana nufan wani ɗan ƙaramin table da aka jera plates da Spoons tare da Cups akai anyi danki dashi "Caa nake kunyi waya ai?" Tatambaye sa tana zaro plate ɗaya "No ban Kira sa ba". Zubo drinks ɗin tayi saman plate ɗin takawo musu, sannan takoma tazauna "Saleema tace "Aunty Ina Abida yau ban ji ta ba?" "Ai kam tana school bata dawo ba". "My Daddy zo muje mu yawata". Khalil yafaɗa yana miƙe wa tsaye Hakima kallon sa tayi tace "ya haka kuma zaka tafi baka ci komi ba?" Ɗaukan Aamir yayi yana bata amsa da "A ƙoshe nake ai, bari mu fita waje". Tunda yafice kuma sai sukai ta hira da Saleema. ***** Lokacin da suka dawo tare da Sameer suka shigo gidan Khalil nan yace "Saleema tatashi su tafi". Hakima sai tsiya take mishi wai yanzu suka zo har zasu tafi baza su kai musu dare ba Shi kuwa be ce komi ba Saleeman ce take ta dariya tana faɗin "zasu biya ɗauko Halwa ne". Sannan ne fa Hakima tayi shiru da bakin ta Har waje suka rako su suka hau mota suka bar gidan A lokacin ne Khalil yaƙyalla idanu yaga saƙon da Mom tabashi yaba Saleeman, shaf ya manta shiyasa yabar shi cikin motan, don haka ya ɗauka yamiƙa mata yana faɗin "Gashi in ji Mom ɗazu na manta ban Baki ba". Amsa tayi tana kallon ledan, sai kuma tabuɗe jaka tasaka tana cewa "Allah Sarki Mom ɗina, Allah yasaka da alheri, zan kira ta in mata godiya". Shi dai be ce komi ba illa murza sitiyarin da yake yi, ahaka har suka shiga cikin makarantan Saleema takira ta awaya tasanar da ita inda sukai parcking motan Don haka babu ɓata lokaci Halwa tafito cikin holl ɗin da suka gama karatu ta tunkari inda zata same su, tana sanye da niƙab da tasaka yanzu da zata fito har ta'isa wajen motan tayi Nocking Da farko da suka kalle ta basu gane ta ba, sai kuma Saleema tasaka dariya tana zuge glass ɗin tace "Kaii sis Wai dama kina saka niƙab ne idan zaki zo?" Murmushi Halwa tayi wanda basu san ma tana yi ba, idanun ta tasauke akan Khalil da shima yazuba mata nashi, tayi saurin lumshe wa tana buɗe su sannan tabuɗe bayan tashiga tana faɗin "Saboda ƴan saka idanu ne shiyasa nake saka wa, sannu Yaya". Taƙarishe maganar tana rufo ƙofan Jan motan yayi yana amsa mata da "yauwa, ya makarantan?" "Alhmadulillah". Tace ataƙaice Saleema tace "gaskiya ne Sister kuma yayi miki kyau fa wlh". Cire niƙab ɗin Halwa tayi tana saka wa ajaka tace "ko Ƴar uwa?" "Eh mana ki tambayi Yaya Khalil". Kallon gefen sa Halwa tayi sai suka haɗa idanu ta mirror, tayi saurin ɗauke kanta batare da tace uffan ba Shi kam be ɗauke idanun sa akan ta ba, kallon fuskarta kawai yake yi, a ransa kuma sosai yaji daɗin ganin ta da niƙab ɗin Saleema ce kaɗai take ta faman surutun ta Halwa na bata amsa a taƙaice Har yanzu bata iya sakin jiki a gaban sa, sabida yanda take ji a game dashi duk da kuwa sun ɗan saba ba kamar da ba. [12/2/2020, 3:13 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Twelve* ________🎓 Koda suka isa gida Halwa wanka tasoma yi tasauya kaya zuwa riga da skert na kanti me ruwan bula, sannan tafito tasami Saleema a kichen tana ɗaura musu abincin dare Fita tayi tanufi kan dainning taɗibo abinci tasake dawowa cikin kichen ɗin tazauna akan Kujeran Robber dake ajiye gaban Freezer, Saleema na girki tana taya ta hira. Khalil kuwa ɗakin sa yawuce kai tsaye, cire kayan jikin sa yayi yasauya da farar jallabiya da gajeren wando sannan yafito parlour, Kallo yakunna yaɗau Remote yana sauya Channels, ya saka wannan yasaka wancan har sanda Halwa tagama cin abincin tafito don taƙara wani Tana fitowa suka haɗa ido dashi, ɗauke kai tayi tanufi kan dainning, tana cikin zuba abincin tatsinkayi muryan sa yana cewa "Maman Husna kawo min ruwa". Lumshe idanun ta tayi tana sauraron bugun zuciyarta dake fita dasauri-sauri, ware idanun tayi kansa wanda shima yazuba mata nashi idanun, dasauri taɗauke kanta tana nufan Fridge tabuɗe taciro masa sannan tahaɗo da cup tanufo sa, akan Centre table ta'ajiye masa tajuya da ninyan tafiya, batayi aune ba sabida yanda duk natsuwar ta yabar jikin ta sai ji tayi tay karo da Centre table ɗin ta tafi yarab ta faɗa kansa, sai gata ɗare-ɗare a jikin sa Kunya tsoro duk su suka taru mata lokaci ɗaya wanda hakan yasaka takasa tashi bare taɗago kai takalle sa, in banda gudun da zuciyarta ya ƙara kamar yafaso ƙirjin ta Shi kuwa abin ma dariya yaba sa, haka kawai yatsinci kansa cikin wani irin farin ciki mara misaltuwa, sai kawai yazuba mata idanu yana murmushi me sauti Lokacin ne kuma tasamu ƙwarin jikin da har ta'iya yunƙurin tashi, har a time ɗin bata iya kallon sa ba illa miƙe wa da tayi tana shirin barin wajen "Maman Husna halan baki gani ne kike son ki karya Ni?" Yafaɗa still yana murmushi Ɗago kai tayi takalle shi, sai kuma taɗauke kai tana murmushi bata iya cewa komi ba tanufi hanyan kichen dasauri Tana shiga Saleema ta ɗan kallo ta kafin tamaida kanta taci gaba da aikin ta Zama Halwa tayi tana sauke ajiyan zuciya har da dafe ƙirjin ta tare da lumshe idanu "Me yafaru ne Sister wannan murmushi haka?" Tatsinkayi muryan Saleema tana faɗin hakan Dasauri tabuɗe idanun ta suka haɗa ido da Saleema wacce tajuyo gaba ɗaya a yanzu tana kallon ta "Babu komi". Halwa taba ta amsa cike da sanyin muryan ta Sai kuma tamiƙe tana nufo ta "Da me zan taya ki?" Saleema tace "ai na gama, sai dai ki kwashe min zuwa dainning". "Ok". Tare suka fito kichen ɗin har a lokacin kuma Khalil na zaune a Parlour yana kallon sa Kallo ɗaya Halwa tayi masa taɗauke kai ganin sun haɗa idanu Kan dainning ɗin suka kai suka jera, sannan Saleema tanufi parlour'n tazauna gefen sa Halwa kuma sai tayi ɗakin ta dasauri "Sis Ina Zaki kuma?". Halwa da har ta buɗe ƙofan zata shiga tatsinkayi muryan Saleeman, sai tajuyo tana kallon ta tace "kawai zan ɗan kwanta ne kafin a kira sallah". "Kwanciya kuma yanzu? Ki dawo ki zauna anan zuwa anjima kya shiga ki kwanta". Gaba ɗaya kallon sa suka yi wanda kamar ba shine yayi maganan ba, don hankalin sa na kan t.v yana sake sauya Channel Takowa tayi tadawo tazauna can gefen su Su biyu kaɗai suke hiran su yayinda Halwa tamaida hankalin ta kan t.v amma tana sauraron su, idan Saleema tasako ta kuma tana bata amsa, har sanda aka kira sallah Khalil yatashi yashige ɗakin sa Su ma tashin suka yi don gabatar da farali. ****** ******** ******* Tunda Zainab tayanke shawaran fid da miji ko ta samu sauƙin nacin Nura hakan kuwa tayi, akwai wani saurayi Aliyu da suke makaranta tare, anguwan su ɗaya dashi sai dai ba layin su ɗaya ba, to shi yana degree ɗin sa ne a school ɗin, suna yawan haɗuwa a makarantan shiyasaka suke ɗan gaisawa har idan Zainab tana da assignment ko wani abinda bata gane ba kai tsaye wajen sa take zuwa, tunda dama sun san juna sosai a anguwan su magana ce kaɗai be haɗa su Wannan dalilin ne yasaka shaƙuwa yasoma shiga tsakanin su, har dai Aliyu yazurma son ta lokaci ɗaya, ahankali-ahankali dai bayan shaƙuwar su ta sake nisa sai yasanar mata da sirrin zuciyar sa Zainab bata wani ja aji ba ta amince don dama itama tana son sa aranta, komi nasa yayi mata, bare kuma dama neman saurayi take yi tayi aure ta huta. Aliyu na zuwa wajen ta, a school kuma koda yaushe suna tare hakan yaƙara ƙarfafa soyayyar su da shaƙuwar su, kuma a gidan su babu wanda be san Aliyu ba Umma ko kaɗan hakan be mata daɗi ba tunda Aliyu ko ƙwaƙƙwaran sana'a bashi dashi, iyakan dai karatun sa yasaka agaba sai kuma ɗan jiran shago da yake yi, sosai ran Umma yasake ɓaci musamman da tasan ko shi wanene don haka tasoma rura ma Zainab wuta dole tarabu dashi takoma ma Nura tunda shi yana da sana'ar sa Zainab ita kuma ta nuna mata sam ita Aliyu take ƙauna, hakan yajawo har sai da Umma tayi mata tsinannen duka Ba ƙaramin ɓaci ran Abba yayi ba, a ranan shima sai da yayi kamar zai duke Umma akan abinda tayi, wannan dalilin ne yasaka yanemi Aliyu yabashi damar yaturo idan har zai iya auren Zainab Duk da Aliyu be da wani abun yi sosai wanda ke kawo masa kuɗi, sai dai yana da ƴan uwa waɗanda ciki ɗaya suka fito su ne kuma suke taimaka masa a fannin karatun sa sabida suna da hali sosai, jiran shagon da yake yi yana yi ne kawai don rage zaman banza Koda Abba yayi masa zancen yaturo hakan ya faranta masa, kai tsaye sai yanufi gidan Babban Yayan su yasanar masa, dayike su ma suna son yayi aure sai Yayan nasa yace "yatafi zai neme sa idan suka yi shawara da Umman su". A cikin sati ɗaya har an nema wa Aliyu auren Zainab kuma Abba ya basu ita, sai aka saka ranan nan da wata uku bayan ta gama final exams ɗin ta da sati biyu, dama ƴan uwan sa zasu yi masa komi na bikin don haka basu wani damu ba koda aka saka ranan babu yawa. Fannin Nura kuwa yayi baƙin cikin hakan sosai, ya tabbata ya rasa Zainab bazai taɓa samun ta ba tunda yasan bata son sa, amma kuma har yanzu yaƙi ba ma zuciyar sa haƙuri be dena zuwa wajen ta ba. Sai mu ce Allah yakyauta maka. . _kuyi haƙuri da wannan babu yawa._ _sai kun ji Ni a next page._ _kar ku manta plz Vote and share 🙏_ [12/2/2020, 3:31 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._ *SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._ *BOOK TWO* . _______________________________ *CHAPTER Thirteen* ________🎓 *AFTER THREE MONTHS* "Wai jikin ne Sister?" Halwa tafaɗa lokacin da take zama gefen gadon Numfashi Saleema taja tana sake jan bargon da tarufe jikin ta dashi a lokaci ɗaya tana bata amsa "Wlh kuwa sis, gaba ɗaya bana jin daɗi yau, dama tunda naga a kwana biyun nan jikina ya soma kumbura na san akwai matsala". Cike da tausayin ta Halwa tace "eyya ko dai in Kira Ya Khalil mu je asibiti, don bana son wlh ciwon ki yatashi da tsananin nan". Ɗan guntun murmushi Saleema tasaki tana kallon ta cike da nuna jarumta tace "kar ki damu babu abinda zai faru, bari dai insha magani na sai in kwanta in ɗan samu barci insha Allahu zan ji daɗi domin barcin nake buƙata a yanzu". "Tom bari in ɗauko miki Maganin". Dasauri tamiƙe tazagaya side ɗin gadon tabuɗe drower taɗauko mata, tanufi Fridge tahaɗo mata da ruwa sannan tadawo tazauna "Tashi kisha". Tayi maganar tana ajiye goran ruwan da maganin ajikin ta Sai da tataimaka mata tatashi zaune kafin tabuɗe mata maganin taba ta tasha ta'ajiye ruwan a ƙasa "Ki ɗan tsaya yanarke tukun sai ki kwanta". Murmushi Saleema tayi tace "to Nagode sis, Ina jin daɗin kula dani da kike yi Allah yabiya ki da mafifin cin alkhairin sa.." "Ya isa don Allah duk abinda zan miki be kai kwatankwacin taimakon da kikai min ba, kar ki damu sister insha Allahu Allah zai yaye miki duk wani damuwar ki, Allah maji roƙon bawan sa ne kuma yana jin mu". Cikin jindaɗin maganar ta Saleema tace "Sister to ki je ki ƙarisa assignment ɗin naki mana ko kin gama ne?" Gajeren tsaki Halwa taja tana shafa gefen fuskarta tace "wlh na kasa ƴar uwa, duk wani searching da zan yi ban samu abinda nake so ba, na dai ƙoƙarta nayi biyu a cikin biyar ɗin, kuma gashi Lecturer ɗin nan yace mana shine Test ɗin mu na rasa ya zan yi". Saleema tace "to ki kai ma Yaya Barrister mana zai taimaka miki, tun farko ma na manta wlh da shi kika kai ma wa". Halwa dai batace komi ba illa jinjina zancen da take yi aranta, ba wai kai mishin bane bata so kusancin su ne ko kaɗan bata so.. "Kin yi shiru Sister?" Saleema takatse mata tunanin ta "To". Kaɗai ta'amsa mata dashi kafin tamiƙe tanufi kan kujera taɗau Hijabin ta tana ƙoƙarin saka wa "Wlh Sister ban taɓa ganin wanda ciki yake masa kyau ba kamar ke, Ni har na fi ganin kyan wannan cikin akan wancan, kinga yanda kika yi kuwa?" Cewar Saleema tana dariya ahankali Itama Halwan dariyan tayi tana ƙarisa saka Hijabin sannan taɗau Peppers ɗin ta tana kallon Saleeman "Ke dai Sister kin fiye saka idanu, ina wani kyau anan kina ganin yanda yaƙara min muni ya mayar dani sai kace wata uwa". Dariya suka yi gaba ɗaya kafin Halwa tafice Ita kuma Saleema tagyara kwanciyar ta. Tana fita tatarda Khalil ɗin zaune saman sofa yana latsa wayan sa Ƙarisawa tayi ahankali tayi masa sallama Hakan yasa yaɗago kai yana kallon ta at the same time yana amsa mata sallaman tare da ɗaura murmushi a fuskar sa "Maman Husna". Yafaɗa idanun sa akan ta Murmushi tayi tana Sad da kanta ƙasa don bata son ko kaɗan suna haɗa idanu, sai taji kamar wasu abubuwa suna fita ta cikin nasa idanun su shiga cikin nata "Dama yaya Khalil nazo ne kayi min wannan assignment ɗin". Gyara zaman sa yayi yana ajiye wayan yace "mu gani". Miƙa masa tayi Ya'amsa yana duba wa, ya ɗau tsawon mintuna biyu yana duba wa kafin yaɗago kansa yana kallon ta yace "ina Bairo ɗin?". Miƙa masa tayi dasauri Ya'amsa yaci gaba da dubawa kafin yasoma rubutun Ita kuma tana tsaye tana kallon sa "Baki gaji ba? ki zauna mana". Tatsinkayi muryan sa yana faɗin hakan batare da ya ɗago ya kalle ta ba Babu musu tazauna kan hannun kujeran Tsawon mintuna goma yaɗauka yana mata kafin yagama yakalle ta yana cewa "matso in yi miki bayani yanda zaki fahimta koda nan gaba". Hakan kuwa yayi mata daɗi don babu ita akai karatun shiyasa duk bata wani fahimta ba Zama tayi kan kujeran sosai, shima kuma yamatso ta yanda zata iya ganin rubutun sannan yasoma mata bayani Sosai tatsayar da hankalin ta waje ɗaya tafahimce sa duk da kuwa yanda take ji sabida kusancin su da yayi yawa Sai da yagama sannan yaɗago kai yana kallon ta da murmushi yace "yauwa to na gama saura biya ko?" Itama kallon sa tayi tana fid do idanu waje tace "ba kyauta kayi min ba?" "Laa ba kyauta nayi miki ba, ki duba ai nayi ƙoƙari Yakamata ace kin biya Ni" yayi maganar yana shafa suman kanshi yana dariya ƙasa-ƙasa "To nawa ne sai in biya ka?". "Duk yanda kika ba da babu matsala, amma meyasaka kike son karantan Low?" Kanta tasauke ƙasa, batasan me zata ce masa ba illa jujjuya Bairo ɗin hannun ta da take yi "Kinyi shiru". Yace mata a hankali idanun sa ƙyam akanta Ɗago kai tayi takalle sa, ganin sun haɗa ido tayi saurin maida kanta ƙasa tana jin gabanta na sake matsanancin bugawa "Ina so ne kawai". Tafaɗa a matuƙar sanyin murya Shiru yayi be yi magana ba, illa kallon ta kawai da yake yi cike da ƙauna, wannan kusancin nasu ya saka sa matuƙar nishaɗi da wani irin farin ciki ainun Miƙe wa tayi ta ɗan saci kallon sa kafin tace "na gode yaya Khalil, Allah yasaka". Murmusawa kaɗai yayi be ce komi ba Har ta juya kuma sai yace "ina Saleema?" "Bata jindaɗin jikin ta shine takwanta". "Subhanallah.." yafaɗa yana miƙe wa "Muje in duba ta". Ɗakin suka nufa Suna shiga sukai wajen gadon, zama Khalil yayi yana kallon fuskarta Har ta samu barci, gaba ɗaya jikin ta a rufe yake ruf sai fuskarta dake waje, a yanda take fitar da numfashi da ƙarfi zaka san jikin ta be mata daɗi, gashi fuskarta ya jiƙe sharkaf da zuba, gaban goshin ta sai tsatstsafo da gumi yake yi Hannun sa yaɗaura a saman gashinta kasancewar ɗankwalin ta ya zame, shafa gashin kawai yake yi yana kallon ta cike da tausayi Haka zalika Halwa dake tsaye itama kallon Saleeman take yi cikin tsananin tausayin ta Babu wanda ke magana cikin su kowa da tunanin dake ransa, tsawon wasu mintuna kafin Khalil yamiƙe yafice a ɗakin Yana fita Halwa takoma inda yatashi tazauna, tasaka hannun ta itama kamar yanda yayi tana shafa mata gashin Bata tashi a wajen ba sai da taji kiran sallan Asar, kafin tashiga Toilet taɗauro alwala tafito, sallah tayi tacire Hijabin tana zama kan sofa, sai tabuga tagumi kawai tana kallon Saleema, sai dai abaɗini tunani kawai take yi Daga ƙarshe tashi tayi tafito parlour, sai tayi hanyan kichen tana tafiya a hankali, tana shiga sai tatsaya tana tunanin abinda zata yi Ta ɗan jima a tsaye kafin ta'isa wajen kanta tasoma kiciniyar ɗaura musu girkin dare, duk da dama girkin ranan Khalil ne yayi musu Take-away, ita taje yin test a makaranta, Saleema kuma rashin jindaɗin jikin ta yasaka bata girka ba, da Khalil ɗin yadawo sai be ma tambayi ba'asi ba yakoma yasiyo musu Motsin da taji a bayan ta ne yasaka tajuya dasauri Khalil ne tsaye ya harɗe hannayen sa akan ƙirjin sa ya zuba mata kyawawan idanun sa masu tsananin kaifi da burge wa, fuskarsa kuma yalwace da murmushi Duƙar da kanta tayi tana jin matsanancin kunya ya kamata kasancewar ta bata da Hijab a jikinta, duk da riga da sani ne na atamfa a jikin ta, amma kuma duk da haka cikin ta yafito sosai ga kuma ƙiba da yasaka ta tayi "Me zaki yi?" Yatambaye ta yana kallon ta yana ji kamar yahaɗiye ta sabida tsananin ƙaunar ta da yake ji a ransa Halwa taba shi amsa batare da ta ɗago kai ta kalle sa ba "Dama zan yi mana girki ne". Khalil yace "a'a ki bar shi kawai, idan na fita anjima zan siyo kar ki wahal da kanki uhmm?". Kaɗa masa kai tayi kamar ƙadangaruwa, bata sake ɗago kai ba sai da taji tafiyar sa kafin taɗaga kanta a lokaci ɗaya kuma tana sauke ajiyan zuciya me ƙarfi har da dafe ƙirji Bata san meyasa take zama wata daban ba a gaban sa, sai takoma kamar ba ita Halwan da tasani ba Murmushi tayi a fili tace "wlh na sauya sosai kamar ba Ni ba". Sai kuma tasaki dariya tana juyawa tanufi wajen Freezer bayan ta ɗau ɗanyen naman da taɗauko tamayar cikin Freezern, sai kuma tatsaya tana tunanin abinda zata girka taci, sosai take jin kwaɗayi tana son ta ɗan saka wani abun da zai mata text a baki "Ko dai inyi ɗan wake ne?" Tafaɗa tana juya ido alamun tunani Sai kuma tagirgiza kanta "A'a bari in yi dai kalallaɓa, yeessss shi zan yi". Taƙarike maganar da dariyan farin ciki a fuskarta Kasancewar suna da komi sabida haka cikin ƙanƙanin lokaci tayi tagama sannan taɗauki Plate ɗin da tazuba tanufi hanyar fita, har ta kai bakin ƙofa sai tadawo taɗau Robbern yaji tafice A Parlour tazauna taɗaura plate ɗin saman cinyan ta, tana ci tana kallon ta cike da nishaɗi da jindaɗin kalallaɓan Bata san sanda Khalil yazo wajen ba sai tsinkayan muryan sa tayi "Ashe dai hanci na be jiyo min ƙarya ba". Dasauri taɗago kanta a tsorace tana kallon sa Hakan yasa yayi dariya yana zama yace "sorry na tsorata ki ko? Menene wannan kuma?" Yaƙarike maganar yana kallon cikin Plate ɗin Tana murmushi taba shi amsa da "kalallaɓa ne, bismillan mu". Taɗago Plate ɗin tana ajiye wa a tsakiyar su "Ai kuwa zan ci, wannan abun tun daga ɗakin karatuna na jiyo ƙamshin sa". Yayi maganar yana dariya Sai kuma yasaka hannu yagutsira yakai bakin sa Duk tana kallon sa tana murmusawa Taunawa yasoma yi a hankali yana ɗan yamutsa fuska, sai kuma yasoma gyaɗa kansa yana wani lumshe idanu "Waiii wannan abun daɗi yake dashi, me kika ce ma sunan sa?" Dariya tayi tace "kalallaɓa". "Uhmm kalallaɓa yayi daɗi fa, Ni ban taɓa cin abun da yakai wannan daɗi ba, so texting". Murmushi tayi me fid da haƙora tace "ko dai santi kake yi?" Saurin girgiza mata kai yayi yana taunan wanda yasaka a baki, a kuma time ɗin yake bata amsa da "a'a dagaske nake miki". Halwa dariya kawai take mishi, shi kuma sai zuba santi yake yi cike da barkwanci Be cire hannun sa ba sai da suka cinye gaba ɗaya Halwa ƙoƙarin miƙe wa tayi zata maida Plate ɗin kichen Yayi saurin cewa "no koma ki zauna bari in Kai". Ya'amshi plate ɗin yakai kichen tare da wanke hannun sa yafito "Gaskiya yayi daɗi, kinga daɗin sa ya saka na cinye miki ban rage miki ba, Allah yasa dai ya ishe ki?" Yayi maganar bayan ya dawo wajen ya zauna Murmushi Halwa tayi tace "sai yanzu kenan zaka tuna bayan ka gama cinye min? To ya zan yi haka nan zan haƙura ai tunda ba wani". Shafo kansa yayi yana dariya yace "sorry na manta ne wlh". "Babu komi ai". Tafaɗa cike da nishaɗi "Wai yaushe ne zaku soma Exams ɗin nan ne, naga time na ƙure wa?" Halwa tace "jibi ne insha Allahu". Zai sake magana wayan sa yasoma ƙara, ciro wa yayi cikin aljihun wandon sa yana kallon screan ɗin wayan, be ɗaga ba sai yamaida kallon sa gare ta yana faɗin "Bari inje Tahir na jira na, idan Saleema tatashi jikin babu daɗi Please ki kira ni kinji? Bazan daɗe ba ma zan dawo". "To sai ka dawo Allah yatsare". "Ameen na gode". Yafaɗa alokacin da yake miƙe wa yayi hanyan fita yana ɗaura wayan a kunne sa bayan yayi peacking call ɗin Bin bayan sa tayi da kallo har yafice "Yana da matuƙar kirki". Tayi maganar a fili tana murmusawa tare da kwanciya kan kujeran, lumshe idanun ta tayi cike da tsantsan farin ciki tare da tunanin Khalil ɗin Yau dai baza ta iya hana kanta tunanin sa ba, don haka tabaje zuciyarta tana tariyo duk wani abu da yataɓa shiga tsakanin su, har da ma wanda be faru ba sai da zuciyar nata takawo mata tunanin tare da ƙawata mata abun ta yanda zai saka ta nishaɗi. _kun san dai zuciya 🤣🤣🤣🤣__ [12/3/2020, 5:34 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️ *Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_ *بسم الله الرحمن الرحيم* ⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓``` *JIKAR LAWALI CE*✍️ *Wattpad: UmmuDahirah*👈 *\F.W.A📚/* ```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH

Chapter 23 of 34