Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 2
hannun ki sannan kije yanason ganinki" Dubansu tayi sama zuwa ƙasa tace “Ku kuma don taɓewa iyayenku suka barku kuka taho Bauta ga ɗaki can na baƙin da basusan aikinsu ba idan na dawo kowacce zataji aikinta amma kafin wannan ga kayana can a ninkemin su kan na dawo" ficewa tayi suka kalli juna Rumah tace “Asma'u a haka zamu rayu?" Numfashi Asma'u ta sauke tace “Rumasa'u jikina yayi sanyi Nikam wannan rayuwa Nima dauriyata ta kusan ƙare wa" Kamar yanda ta umarcesu haka suka ninke kayan Asma'u tace “Rumasa'u yunwa nakeji kinsan fa ko karyawa bamuyi ba" sauke taguminta tayi tace “Nima haka har amai ne yake tasomin bari jakadiya ta dawo mu roketa ta sammana abinda zamuci" kafin Asma'u tayi magana Jakadiya ta shigo ta dubi Rumah tace “Ah Ni Sahura Jakadiya wannan yarinya da Sa'a kike Ki tashi muje na nuna Miki aikinki a ɓangaren masu garin" batayi musu ba ta miƙe ta riƙo hannun Asma'u Sahura Jakadiya ta harareta tace “An faɗa Miki ɓangaren ubanki zaki shiga da zakiyi gayya dalla saki hannunta ita munanan da ita" a sanyaye ta saki hannun Asma'u zatayi magana Asma'u tace “Kije insha Allahu alkhairi ne zai biyo baya ƴar'uwata. [12/15/2022, 1:12 PM] OUM HAIRAN: *RUMAH!...* _Labarin sarauta me taɓa zuciya_ *Oum Hairan* Masu son karanta wannan littafi zaku tuntuɓe Ni ta wannan number a WhatsApp 09013718241, 300 ne PC 600 babu VIP ko ku tura ta acct 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko katin MTN. *Page 7-8* Cikin matuƙar mutuwar jiki tabi bayan Jakadiya sukabi wata siririyar hanya sunyi doguwar tafiya kan hanyar da babu mutane sosai a kanta sai haske daya cika ko ina kamar ka jefar da allura ka ɗauka itadai Rumah bin Jakadiya kawai takeyi har sanda suka fara hango wata ƙofa babba wadda aka matuƙar karar da fasaha wajen ƙerata. Tun a ƙofar Rumah ta ƙare ƙauyancinta duk da abubuwan ƙyale-ƙyale na duniya basu cika wani burgeta ba tabbas wannan ƙofa tayi masifar jan hankalinta har Saida takai hannu ta taɓa tunaninta gold ne akayi kofar dashi. Wani ƙarfe dake jikin ƙofar Jakadiya ta taɓa ba'a bata lokaci ba aka buɗe ƙofar tuni gaban Rumah yayi kwance² ya faɗi ganin wani gabjejen mutum sanye da kalar kayan dogaran da suka taho dasu daga gidan marayu. Cikin muryarsa mara daɗin sauraro yace “Sahura kutungwila meye ke tafe dake da maraican nan?" Tana wasa da hannun rigarta ta bayi tace “To Allah ya taimaki uban gidana sarkin ƙofa kaima kasan inba da sahalewar Mai Martaba ba babu kirinki da karambanin da zai kawoni wannan sashi yanzu dai bani guri na wucce" Kaucewa yayi yana kai hannunsa ya riƙo hijjabin Rumah yace “Uwar ɗaki wannan zumar fa farar saƙa..." Saurin rufe masa baki tayi tace “Uffararan kar kayi shuka a idon makwarwa wannan aiken Mai Martaba ne kasan banza bazatasa yace a kawwame masa ita anan ba" duk da cewar Rumah da Hausa take magana hakan baisa tana gane ma'anar kowanne lafazi ba amma Saida ta ɗago ta kalli Sahura Jakadiya itakuwa gaba tayi tana sakin doro tace “Fulanin Sokoto nake matuƙar tausayawa domin ta kasa sabawa da rayuwar gidannan duk da cewar itama tanada jiɓi da sarauta...." Itadai Rumah bata da bakin magana tunda ba abune daya shafeta ba ganin yanda sukaci gaba da zurara tafiya suka hari wani gini da take hangowa can nesa yasa ta gane tabbas can za'a kaita ita kuma nata aikin bautar a ƙarshen duniyar gidan zatayishi, ta raya a ranta. Ita wannan ƙofa a buɗe take turawa kawai sukayi suka shiga wani babban falo ne mai girman gaske zubinsa zubin fada duk an zaneshi da hotunan wani kyakkyawan farin matashi dogo da shekarunsa bazasu gaza arba'in ba, wani bangaren kuma hotunan wani dattijo ne an rubuta late Sarki Abbas bin Ridwan Rahimahullah, tsayawa tayi cike da matsanancin tsoro razani da kuma mamaki ashe dai da gaske rabo ajali ne yau gata a gidan sarauta matsayin baiwa ajiyar zuciya ta sauke ta kai dubanta ga Jakadiya, Jakadiya ta figi hannunta tace “nan fadar hutawar Mai Martaba ce ya umarceni dana umarceki da nan gurin ya zama ƙarƙashin kulawarki muje na ƙarasa nuna miki na kama gabana ruwanki kiyi masa aiki me kyau tunda shi ke yaga kin dace da kula masa da wannan ɓangaren, yo bandama yaro burmin yaro ne yanzu saboda Allah ace duk girɗa girɗan yammata bayin da muke dasu a gidannan sai wata ke da kema baki gama sanin ya zaki kula da kanki ba" Shiga sukayi ta nuna mata ko ina sannan ta kama kunnenta ta murɗe tayi ƙasa da murya tace “kuma nasan ana kwasar daɗi a nan duk abinda akaci aka rage idan baki ƙullo min nawa ba saina shaƙeki" Juyawa tayi ta fice ta barta ita kaɗai a wannan sashi Ta jima kafin ta ƙarfafi jikinta ta fara aikin tana matsar ƙwalla iya sharar falukan akabar mutum dashi an haɗashi da babban tashin hankali bare ƙalƙale²n da Jakadiya ta lissafa mata ba ita ta gama aikin ba sai Bakwai na maraice itadai ko mahaukaciyar kasuwa ce ta cijeta bazata iya kwana a wannan guri ita kaɗai ba gashi Jakadiya tace duk wanda ke kula da wannan ɓangare anan yake kwana saboda idan Mai Martaba yayi shigowar dare akwai abubuwan da ake yi masa. Can baya ta koma ta zauna ta haɗe kai da gwiwa bayan tayi sallah tana tunanin halin da ƴar uwarta take ciki itadai a yinin yau ko ruwa bata sanya a cikinta ba share hawayenta tayi tace “Yanzu haka zamu rayu Asma'u ko kinci abinci ke?" Batada me bata amsa taji wata murya a bayanta tace “ki amsa kira a Mai Martaba yana buƙatar abin sha zumbur ta miƙe ta nufi ciki har tana tuntuɓe taja ta tsaya da sauri ganinsa tsaye hannunsa zube cikin aljihun alƙabbarsa ya zuba idanunsa da suke cikin farin Glass akanta zubewa tayi ya ɗaga mata hannu ya zauna saman kujerar ta mike da sauri ta nufi wani bangare da aka jera ma'adanar sanyi ta buɗe tana tunanin meye ma ya kamata ta bashi a wannan lokacin, tire tire ta ɗauka ta jera fruit ta sake ɗaukar wani ta zuba kayan sha ta ɗauki na kayan shan takai ta ajiye a saman wani teburin Glass dake gabansa ta ɗauki wani kyakkyawan kofin glass ta tiyaya ruwan tataccen tuffa ta miƙe da abin a hannunta Jakadiya tace a baki ake basa ita yanzu ta ina zata fara basa abinci a baki? _Manege_ *Share please* *Oum Hairan* [12/15/2022, 1:12 PM] OUM HAIRAN: *RUMAH!...* _Labarin sarauta me taɓa zuciya_ *Oum Hairan* Masu son karanta wannan littafi zaku tuntuɓe Ni ta wannan number a WhatsApp 09013718241, 300 ne PC 600 babu VIP ko ku tura ta acct 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko katin MTN. *Page 9-10* Kansa a ƙasa yake shirun da yaji tana neman yin tsayi ya sanyashi ɗagowa ya sake sauke idanunsa kanta cike da mamakin yanda ta riƙe cup ɗin jikinta yana karkarwa tana kallon ƙasa, itama motsin motsa ƙafarsa yasata dawowa hayyacinta tayi ƙasa da kanta tace “Ka gafarceni Allah ya taimake ka na kasa iyawa" ba ma'abocin son magana bane saboda izzar mulki dake addabar rayuwarsa amma bai san sanda bakinsa ya furta kalmar “Me?" Ba cikin in...ina da shirme na ƙuruciya tace “Cewa fah tayi a baki zanke baka kuma ina matsa maka yatsun ƙafarka Allah ya taimake ka wlh kunya nakeji kuma ma ai babu halacci a cikin hakan.... Sosai yanda take maganar yayi masifar bashi nishaɗi yayi murmushin da bata iya gani ba yace “Kinsan halacci da haramci?" Ɗaga kai tayi tace “A gidanmu an fayyace mana halacci da haramci" “Tsakanin baiwa da ubangidanta fah?" Ya tambaya yana kafeta da manyan idanunsa daya zare tabarau ɗin dake saye dasu. Girgiza kai tayi ta miƙe jikinta a mace ta durƙusa tayi zaman raƙuma hannunta na rawa ta ɗaga cup ɗin ta nufaci bakinsa dashi tana furta bismillah.... Yanda hannunta ke rawa yasashi saurin rikewa don kada ta ɓata shi ya karɓi kofin hannunta ya aje saman teburin yace “kina iya tafiya" miƙewa tayi kamar yayi mata bushara har taje bakin kofa taji yayi gyaran murya ta juya ya nuna mata wata kula yace ta fita da ita, ɗauka tayi ta fice batasan ina zata kaita ba hakan yasata nufar asalin ɓaryar bayin tana wuccewa batare da tana sauraron kowa ba can nesa Asma'u dake zaune cikin bayin suna gyaran agushi ta hangota ta tashi ta tarota sukayiwa juna kallon tsaf Rumah tace “Har sun baki kaya? Me lokaci?" A raunane tace har yanzu banci komai ba ke fah ina Jakadiya takaiki naji ta dawo tanata masifa" Numfashi ta sauke tace “Muje kular nan akwai abinci a ciki mu rage zagi amma meye yasa ba'a baki abinci ba?" Suna zama a wata kusurwa Asma'u tace “Masu kula da madafin ne sukace ba'a faɗa musu da sabbin bayi a gidan ba shiyasa basuyi girki damu ba wai saidai ƙarshen wata tunda wata yazo ƙarshe zasu sanyamu a jadawali" Buɗe kular Rumah tayi da sauri suka zubawa farfesun naman kajin dake ciki idanu Asma'u har lashe baki takeyi saboda ƙamshin daya bugeta tace “Wayyoh daɗi Rumah ina kika samo?" A ɗan tsorace Rumah tace “kodai ba ita yake nufin na ɗauka ba?" Da sauri Asma'u tace “Waye?" Rausayar dakai tayi tace “nikam naga rayuwa Asma'u Mai Martaba ne ya nunamin yace na taho da ita kuma naga wannan abincin ba irin namu bane irin nasu ne inajin tsoron kar naje ba ita yake nufi ba" “Eh algungumai biyu wato ɗan ragowar kalacin da Mai Martaba yace ki kawomin shine kika ja ƴar'uwarki gefe zaku cinye shegiya me suffar aljanu...." Jakadiya na maganar tana warcewa zaro idanu waje tayi tace “Ƙundun ubannan yau da danasha a gidannan yanzu yarnan da munafurtata zakiyi ki cinye wannan daɗin amma Allah ya isa tsakanina dake ƴar jakar uba me kan taɓarya" Kinkimar kular tayi zata tafi Asma'u tace “Don Allah Jakadiya ki taimaka mana wlh yunwa mukeji Rumasa'u tanada ulcer idan bata sami abinda tasa s cikinta ba ciwonta zai iya tashi Ni Ko bazaki sammin ba ita ki sammata" Bige bakin Asma'u Jakadiya tayi tace “Innaƙi fa gulum" tafiya tayi ta barsu tsaye sake da baki tsabar takaici tuni Rumah me arhar hawaye idanunta ya kawo ruwa ta dafe cikinta tace “Ita kuma wannan rayuwar da haka ta ɗofu" kowa zuciyarsa babu daɗi haka suka bi bayan Jakadiya ɗakin da aka saukesu nan suka shiga sukayi sallah Rumah ƙarfinta ya fara ƙarewa shiyasa dole tana sallah ta kwanta itakuwa Asma'u tashi tayi ta fita domin tasan yanzu zata galaɓaice. Wasu matasa tagani su biyu da kwanon abinci a gabansu ta ƙara sa ta tsugunna suka dubeta a tare ɗayan yace “Yadai ƴammata buɗe baki tayi tace “Don Allah ku taimakemu ku ceci rayuwar ƴar uwata wlh tun jiya rabonmu da abinci ita kuma tanada matsalar ulcer zata galaɓaita idan bata samu abinda taci ba" Cikin mamaki ɗayan yace “Meye yasa bakuje madafi kun karɓo abinci ba?" Muryarta na rawa tace “Naje sunce ba'a faɗa musu za'ayi baƙi ba nidai don Allah ku taimakemu" ɗaya cikin matasan ne ya miƙa mata abincin tayi musu godiya ta tashi da sauri ta nufi inda ta baro Rumah ta tura mata tace “kici zakiji ƙarfi" kallon abincin tayi babu laifi da yawansa tace “ina kika samo?" Murmushi tayi tace “kedai kici abinci kawai" bata kuma tambayarta ba tasa hannu suka fara ci tana bata labarin aikinta itama tana bata labarin nata da haka suka gama suka kwanta sau da yawa Rumah ba bacci takeyi ba takan ɓata tsayin dare tana tunanin yaushe zasu samu ƴanci suyi rayuwa me daɗi, shin wai suna ma da rabon samun tagomashin nishaɗin ko kuwa a haka zasu ƙare rayuwarsu?. To yau ɗinma kamar kullum ta jima tana juyi gashi batason fita bare tayo alwala tayi nafila ko ta samu sanyin zuciya, haka daren ya shuɗe sai gaf da asuba bacci ya ɗauketa asuba ta tashi sukayi sallah gari na haskawa aka fara rabon abinci ana zuwa kansu aka tsallakesu sunaji suna gani sai Jakadiya ce taji ƙansu ta basu nata sukaci su biyu kunu ne da ƙosai bayan sun gama Rumah ta tafi Ɓaryarta ta fara aikinta kamar jiya ta gabatar da komai duk abinda aka nuna mata sau ɗaya takan haddace hakan yasa batasha wahala ba ta kammala ta fice ta koma gurinta na jiya ta zauna yauma sai bayan la'asar ya shigo ba kamar jiya ba yau doguwar riga ce a jikinsa babu naɗi hakan ya bayyana asalinsa kyakkyawa ne sosai daka yanda kaga bafulatanin asali a asalin falonsa wata hadimarsa Shema'u ta kaita yana kishingiɗe saman kilishi da magazine a hannunsa yana dubawa suka iso suka zube Shema'u tace “Ran adalin Sarki ya daɗe ga Rumasa'u ta gabata gareka" jinjina mata kai yayi tare da kallon hanya ta miƙe tunda ta saba da maganarsa da ido. Tana tafe tana zuba masa gdy har ta fice ya aje magazine ɗin ya ɗora manyan idanunsa da tsabar mulki da jin isa da izza yakesa ya mayar dasu ƙanana akanta, ƙasa tayi da kanta tace “Allah ya taimake ka me ake buƙata?" Ta faɗa a dole don tambayar ta zame mata dole ya sauke numfashi yace “Rumah!" Bata amsa ba sai ɗan ɗagowa da tayi tace “Na'am" tashi yayi zaune yace “Jakadiya tayi Miki bayanin ayyukanki?" Ɗaga masa kai tayi ya sake saita idanunsa yace “Kin iya tausa?" Da sauri ta ɗago kai tare da cewa “inayiwa Baba Lami a gidanmu" murmushi yayi yace “Ok tana cikin aikinki na dole kibar shara mopping da cleaning na part ɗin nan Mudi zaikeyi ke aikinki kula da abinci na da ciremin gajiya banida wani tsayayyen lokaci da nake shigowa nan don hutawa shiyasa nake umartarki da ki dawo nan da kwana saboda ɓaryar bayi tayi nisa da nan ɓaryar idan buƙatar ganinki da dare ta kama komai zai iya faruwa kafin zuwanki" *Share please* *Oum Hairan* [12/15/2022, 1:12 PM] OUM HAIRAN: *RUMAH!...* _Labarin sarauta me taɓa zuciya_ *Oum Hairan* Masu son karanta wannan littafi zaku tuntuɓe Ni ta wannan number a WhatsApp 09013718241, 300 ne PC 600 babu VIP ko ku tura ta acct 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko katin MTN. *Last Free Page 11-12* Wani Gwauron numfashi ta sauke me huci tare da jinjina girman wannan aiki lamarin ya girmi ƙwaƙwalwarta tausa, kwana a wannan shatareren part ɗin ita kaɗai? Ta tambayi kanta da son bawa kanta amsar da bata da ita “Ko kinada abin cewa ne Rumah bancika son takurawa mutum ba idan akwai abinda kikeson faɗa ki faɗi" Jin ya bata dama yasata sosa kanta tace “Nidai inajin tsoro Allah ya taimake ka..." Kafe tan da yayi da ido shine yasata katse furucin nata yace “Tsoron me?" Sunkuyar da kanta tayi tace “Kwana Ni kaɗai bazan iya ba zanke jin kamar wani abun zai kamani" murmushi yayi yace “Shikenan kike komawa part dinku idan an kwana biyu kin saba da sassan gidan sai ki dawo" godiya tayi me yawa ta fara haɗa masa abinsha kamar yanda aka karanta mata yauma karɓa yayi da hannunsa yakai bakinsa ya lumshe idanunsa yace “Rumah anayi muku tatsuniya a makaranta" Dariya tayi tace “Lahh! Mai Martaba dama kasan tatsuniya ne?" Ɗaganta kai yayi yace “Nasanta kakata Hajiyan Loko kafin ta rasu tanayi mana nasan kema kin iya ko?" Jinjina kai tayi tace “Malamin Hausar mu yanayi mana lokacin muna primary school" murmushinsa ya faɗaɗa yace “zaki rinƙa yimin?" Kunshe bakinta tayi da dariya tace “Ai manya kamarka baayi musu tatsuniya saidai ƴaƴanka" hannunsa yakai ya tsinki Ƴaƴan inibi guda biyu yasa ɗaya a bakinsa ya miƙa mata ɗaya yace “Shekararki nawa?" Dafe kuncinta tayi tace “Uhmm sha bakwai" iska ya furzar yace “Ok nima shekara ta sha bakwai banda yara har yanzu yaro ne Ni" langwaɓar da kanta tayi tace “Allah sarki kai ai babanka da mamanka duk suna kusa dakai Ni kuwa banma sansu ba.... Maganar ce ta sarƙe kuka na neman ƙwace mata yayi saurin kai ɗaukar handkerchief ya miƙa mata yana girgiza mata kai yace “karki rinƙa yawan zubar da hawaye Rumah kinsa damuwa a zuciyarki akan abinda bazaki iya canza shi ba ko kinsan saboda ke yasa na buƙaci sabbin bayi a gidanku..." “Ni?" Ta faɗa tana dafe ƙirji ya ɗaga kai yace “Zuwa na na farko gidanku kinyi bayani akan haƙƙin marayu akan al'umma yanda kike bayani ya tabbatar min akwai kwantacciyar damuwa a ranki tunda na taho na kasa samun nutsuwa shine dalilin da yasa wannan satin muka koma nayi bincike sosai akanki an tabbatar min da abinda na gani a fuskarki naso daukoki ke kaɗai Chief na gidanku ya bani dama gudun shigarki kaɗaici yasa muka hadoki da yan uwanki. Meye yasa kina sanya damuwar da tafi ƙarfin brain ɗinki a ranki babu wani bawa dake wuccewa ƙaddararsa so ki saki ranki kiyi rayuwa kamar kowa zaki samu dacewa insha Allahu, tashi kije magrib tayi ki ɗauki abincin nan ki tafi dashi, yauwa abinda nakeson sanar dake kiyi mu'amala dani kamar mahaifinki yayanki kuma abokinki idan mun samu keɓancewa Ni dake saidai inaso ki ɓoye kusanci ko sabon dake tsakanina dake a idon jama'ar gidannan kinji kyakkyawar ƴata" Fitar furucin yana murmushi tare da kai tafin hannunsa kuncinta yasata murmushi me ɗauke da hawaye karon farko a rayuwarta da ta sami arziƙin kalma me daɗi daga wani mutum bayan Asma'u tabbas yau rana ce ta musamman kuma ta daban a rayuwarta mamaki al'ajabi da tambayoyi sune narke cikin ranta saidai bazata iya sake furta masa komai ba domin ya gama bawa rayuwarta ta yau farin ciki. Tashi tayi ta ɗauki basket ɗin da aka aje abincin ta shiga kitchen na bangaren ta juye a leda farfesun kayan ciki ne da farfesun kifi sai tuwon alkama miyar kubewa ɗanya murmushi tayi ta kulle kowanne ta kurbi lemon me daɗi ta lumshe idanu a ranta tana raya masu dukiya da masu mulki sunajin daɗinsu wata miyar sai a maƙota, dake lemon babu yawa zuƙe abinta tayi sannan ta fice ranta wasai wani farin ciki takeji yau wanda bata taɓa jin irinsa ba a rayuwarta har tuntuɓe takeyi saboda sauri a hanya suka haɗu da Asma'u saboda tace hanyar tayi jeji bazata iya bari ta rinƙa tahowa ita kaɗai ba. Riƙo hannun Asma'u tayi suka koma gefe tace “Ma'u zo mu cinye naman mukaiwa waccan masifaffiyar matar abincin da kifin" hakan kuwa sukayi suka cinye farfesun naman sukaci tuwon sukayi hani'an suka tashi suka ƙarasa suna shiga Jakadiya ta karɓe ledar hannunta ta buɗe ta haɗiyi yawu tace “Yau abinda sarakin yaci kenan muma bari muci ko mayi mulmul mu rinƙa sheƙi" Taɓe baki Ma'u tayi tace “Muma saiki fitar mana da rabonmu" duka takai mata tace “Shegiya me kan kwakwa ungo gunduwa ɗaya" murmushi Rumah tayi tace “kema ungo makira Allah yasa ba idanu kike kafa masa yake kasaci yake baki ba" kwantar dakai tayi tace “Kai Jakadiya naga Bama fa yaci yake cemin na dauko" nan suka shantake Jakadiya da son zuciya sai gashi ta fara jan Rumah a jika saboda ta lura yarinyar da sa'arta ta shigo gidan tunda har tayi aikin yini biyu a Sashen Sarki Ridwan bai kirata yace karta ƙara zuwar masa ba tabbas zasu kwashi arziƙi kafin gayyar ta watse. “Gafaranku dai" Indo ta faɗa tare da shigowa tace “Ranki ya dade Jakadiya Ki amsa kiran Mai Martaba a lambu" miƙewa tayi tace “Na shiga uku Ni Sahura kwarankwatsa banason kiran Mai Martaba yanzu kar yayi mana baƙin cikin wannan rikitiɓa da muke kwasa ke dan ubanki me kikayi masa?" Ta kama kunnen Rumah ta murɗe ta fasa ƙara tace “Wlh banyi masa komai ba Ni...." Ficewa tayi tace “Allah yasa dai kar wani abu ya biyo baya yasin saina yankaki" Tana maganar tana ficewa a ɗakin bata jima ba ta dawo ɗauke da ledoji niki² ta aje tace “Ni Sahura ji da gani baya ƙarewa sai ranar da kurman bebe ya makance ke Indo nifa kaina ya kulle me wannan bawan Allah yake nufi ne?" Da sauri Indo tace “Uhm ai Sahura na rasa bakin magana tunda naji sharruɗansa akan yarinyar nan “zazzage ledar tayi ta tafa hannu tace Shikenan tazo a bayanmu ta fimu fada Kinga wasu tsala²n riguna da y bayar a kawo mata wai kar ya kuma ganinta da tsummokara kuma ya haramta mata sa kayan bayi ke Rumasa'u kiji tsoron Allah waye bokanki a ƙasar nan?"....... Tun daga wannan rana Rumah ta samu sauyin rayuwa wata shaƙuwa ce take shiga tsakaninta da Ridwan a fakaice shine ya fara aikenta ɓangaren Fulanin Sokoto ganin farko taji yarinyar ta shiga ranta ranar a wannan ɓangare ta wuni saboda dama cewa yayi taje ta taya Fulanin Sokoto hira a hankali cikin hikimarsu ta manya ta rinƙa janta dake batada duhun kai ta saki jiki sosai ita ce harda yima Fulanin Sokoto kitso sunata hirar su tana cewa da Fulanin Sokoto hausarta ba irin tasu ba, a wannan yanayin yazo ya ishesu idanunsa akan Rumah yace “Ke dama kinanan" ƙasa tayi da kanta Fulani tace “Nice nace in ba abinda zatayi tazo ta ɗauke min kewa" zama yayi yace “hakane kije akwai saƙonki wajen Jakadiya" tashi tayi tace “Mu kwana lfy Fulani" bin bayanta yayi da kallo har Saida ta ɓacewa ganinsa sannan ya sauke numfashi yace “Tasa damuwa da yawa a ranta Fulani bantaɓa jin tausayin wani mutum kamar yanda nakejin tausayinta ba saidai na rasa meye ya kamata nayi mata na bambanta ta da bayin gidannan amma zuciyata taƙi nutsuwa ohh God kaina ya kulle meye zai hanata damuwa ne......." *Share please* An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 2 of 2