Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 5
matsalar babba ce, shisa ya daga, aikuwa kuka takeyi kamar anyi mutuwa, har saida gabanshi ya fadi, bai ma fahimci abinda take fada ba, ya daiji Haris ya kuma ji Mustafa, sai yace mata gashi nan zuwa gidan. Ya kuwa karya mota yana nufar hanyar Tudun Wada, da yake akwai 'yar tafiya, makarantar yaran na wajen Rabah Road. Yana isa, baima shigar da motarshi ciki ba, ya dai juyata yanda in yazo tafiya ba sai yayi hakan ba, kanshi tsaye bayan ya shiga gidan ya wuce bangaren Alhaji Mustafa, ya kwankwasa da sallama a bakinshi, da kanshi ya taso ya bude masa kofar yana dariya "Yanzun nake zancenka a raina fa" Cewar Alhaji Mustafa, sukayi musabaha, suna kara gaisawa kamar wadanda sukayi shekaru basu hadu da juna ba, kallo daya zakayi musu ka fuskanci irin shakuwar da take tsakaninsu "Yanzun dinma kararka aka kawomun" Alhaji Mustafa yaja tsaki mai karfi "Karma ka fara shiga maganar nan Sa'idu, na riga na rantse saiya koma inda ya fito, in taga ba zata zauna ba itama zata iya tattara nata kayan ta bishi" Ya karashe maganar yana haki saboda yanda ranshi ya kara baci lokaci daya "Azumi uku dai, ai bansanka da raki ba" Hararashi Alhaji Mustafa yayi "Bafa wasa nakeyi ba..." Ido ya dauka ya sakawa Hajiya Rumanan, daman jiranta yakeyi daga ita har Haris din. Tun lokacin da ya aureta ya fara gane halinta na jin kai da nuna isa, sannan da ace shi din namiji ne mai sanyi, ba karamin raini zatayi masa ba. Halinshi na kin daukar da yawa daga dabi'unta yasa ta dinga kokarin sauke kadan daga ciki, musamman akan danginshi da take ganin basu kai su rabesu ba. Duk da haka in sunzo din ba dadinta sukeji ba, akace shimfidar fuska ma wani abune, to harsu tafi in ba magana takeyi ba, babu wanda zaiga hakoranta. 'Yan uwanshi basu fara jin dadin kawo masa ziyara ba sai bayan daya kara aure, sai kuma ta tsiro da wani abu na kai masa korafi cewa yanzun duk wani nashi ya juya mata baya, basa ma sauka bangarenta saboda ya auro tasu, kuma suna ganin ita bata haihu ba, wani zubin ma kuka take sakashi a gaba ta dingayi, ai sunzo gidan taga sunayi mata dariya akan rashin haihuwarta, bai huta da wannan fitinar ba sai da ta samu cikin Munira, sai kuma bayan ta haihu ya zamana hankalinta kacokan ya koma kan yarinyar, kamar shi dinma bata da wani lokacinshi saina yarinyar, da yake yana samun duk wani abu da yake bukata a tare da Fadime sai bai wani damu ba. Gwarne tayi tsakanin Munira da Anisa, duka shekara daya da wata hudu ne tsakaninsu, har a danginta saida aka nuna a dauke mata Munirar sai taji da rainon Anisa, in yaso idan tayi kwari sai a dawo da ita, tace bata bukata duk zata iya hadasu tayi rainonsu. Sun fara samun matsala da ita ne akan yaran, lokacin Munira na da shekara biyar, ta dauki kofin shayin data gama sha tana bugawa a jikin TV, yana zaune sai yayi mata tsawa, yanda Hajiya Rumana ta karaso ta dauke yarinyar da ta fashe da kuka, idan wani ya hango daga nesa zaiyi zaton makami ne a hannun Alhaji Mustafa "Ya za'ayi kayiwa yarinya karama irin wannan tsawar? Ai saika firgitata" Kallon mamaki kawai ya dinga binta dashi a lokacin saboda yama rasa abinda zaice mata, a hankali kuma saiya kula da itafa akan yaran nan harshi bai isa ba, baisan abinda ya kamata dasu ba sai ita, kowanne irin hukuncine akansu in dai ba ita ta yanke ba to baiyi ba. Cikin danginta ma kafarta kafarsu, haka gidan iyayenshi, in dai ba tare da itaba, to yaran basa zuwa, yaran Fadime ma da yake tsoranta sukeji basa shiga bangarenta sam, saiya zamana tashin hankalin da Alhaji Mustafa ya dingayi akan ganin yaran sun shaku ya tashi a banza, shi dai ba wuni yakeyi dasu ba, wani zubinma sai yafi satika biyu baya garin. Sannan akan yaran Hajiya Rumana dai duk wata tufka da zaiyi yana barin gidan zatabi ta warware. Da ta haifi Haris kuma sai abin ya kara ninkuwa, saboda soyayyar da take nunawa yaron ya wuce yanda za'a misalta. Haka aka cigaba da rayuwar, ya rasa yanda zaiyi da ita akan yaran, ga abin yana damunshi sosai, ko yanda su Munira suke mu'amala da danginshi a darare kadai ya isa abin takaici a wajenshi. A hankali kuma ya yarda Hajiya Rumana na daga cikin kaddararshi ne da babu yanda zaiyi da ita, abinda ya faru gaban idonshi dai zai tsawatar, shisa babu ma wata shakuwa a tsakaninshi da yaran, da yawan lokutta in suka gaishe dashi duk sai su bar falon, musamman Haris da yafisu sangarta, sai rashin jituwarsu yafi yawa da Alhaji Mustafa, tunda su Munira in fada yayi musu zasuyi shiru, harma su bashi hakuri. Amman Haris sai yayi magana, sai yayi kokarin yin bayani ko dai ya fadi wani abin, duk zafin Alhaji Mustafa akan Haris ya fara dukan yaranshi, sukayi wata rigima da Hajiya Rumana har tayi yaji ta kwashi yaran ta tafi Maiduguri, rigima akayi sosai, tunda danginta sun goya mata bayane a fadan, dakyar Alhaji Sa'id yayi ruwa yayi tsaki ya shawo kan aminin nashi sannan aka samu dai-daito. Da yake a lokacin ma Haris din ya kammala primary dinshi, sai kawai ta nuna masa wata makarantar kwana ta kudi take so Haris din ya tafi, makaranta ce mai tsadar gaske da take a garin Kano. Da yaki amincewa dan yana ganin alamar kangara a tare da Haris din. Yana gudun idan yayi nisa da idanuwanshi abin zai iya fin haka, da taga alamar kamar yana neman yaki amincewa, ya tafi Abuja, ya dawo ya samu Haris baya gidan, taje da kanta tayi masa duk wani abu daya kamata ta kuma biya kudin. Suka sake wani rikicin kamar zai saketa, nan ma dai Alhaji Sa'id ta samu, ya lallaba mata shi, sai dai har kasan ranshi bayason wannan makarantar kwanan da aka kai Haris, tunda ga 'yan uwanshi nan a Kaduna suke karatunsu, Mukhtar da Haris din ya ba shekara biyu, alamu sun nuna ma lokaci daya zai hada da gama primary din da kuma haddar Al-Qur'ani. Kuma yawan misalin da Alhaji Mustafa yake yiwa Haris da Mukhtar idan yanayi masa fada ko yayi laifine abinda yasa Haris din baya kaunar ya bude ido yaga Mukhtar, saiya zamana in zai hadu dashi sau goma saiya kwade shi sau goma, ko da kuwa Alhaji Mustafa zai karyashi ne, Mukhtar dinma daya hangoshi yake neman maboya, babu jituwa ko kadan a tsakaninsu. Mukhtar bai samu salama ba sai bayan tafiyar Haris makarantar kwanan nan. Kuma duk wani tsoro da Alhaji Mustafa yake dashi akan nisan Haris shine yake faruwa acan makarantar. Tun satin da aka kaishi, maganar da Hausawa sukayi na sai hali yazo daya ake abota ta tabbata akan Haris, da yake aji dayane su dukansu sababbin dalibai ne, lokacin ake kokarin fahimtar juna. A satin ya hadu da, Idris, Sulaiman da Yakub, kuma sai aka hadasy daki daya, haka suka samu sukayi musayar gadaje da wasu a cikin dakin yanda suka koma makotaka da juna. Basu hada wata a makarantar ba duk wani Malami daya kwana ya tashi saida ya sansu, shugaban makaranta ya haddace fuskokinsu, suka kafa tarihin kasancewa 'yan aji daya da suka gagari seniors dinsu. Idan wani laifin suka aikata, makaranta bata da contact din kowa saina Hajiya Rumana, idan ma aka nemi ganin mahaifinshi sai tace baya kasar. Ita kuma ba fada take iya yiwa Haris din ba, duka yaran bakar fatarta suka biyo, gara Munira ita kai tsaye ba zaka kirata da baka ba, sannan fuskarta sak irin ta Alhaji Mustafa ce, hakama Anisa duk da bakinta dashi take kama, Haris ne duk yanda ake cewa ba'a gane kamannin jariri, a asibiti ma Nurses suka fara maganar yanda yake kama da ita. Hasken fatar da jarirai sukanyi Haris baiyi ba, da duhunshi ta haifoshi, kunnuwanshi bakikirin, aikuwa kafin ma ayi arba'in yayi baki, irin wannan duhun fatar Hajiya Rumana daya hadu da hutu yasa take wani irin kyalli, da yake tana da cikar gashin gira, sannan gashin kanta ma duk da bamai tsayi bane sosai a cike yake, ya kwanta luf har gaban goshinta, haka gashin idanuwanta ma, tana da irin kyawun da idan wasu manyan fashion houses din zasu ganta zasu kafa mata nacin zame musu model. Wannan kalar fatar Haris ya biyo, cikar gashin da kuma kyan daga kallon farko. Yanda idanuwanta suke haka nashi suke, kamar da ruwa a cikinsu, in yayi dariya zaka ga ta isa har cikinsu, haka idan ranshi ya baci zaka ga kyallin bacin ran nan a cikin idanuwanshi, yana da irin idanuwan nan na kalilan mutane, idanuwa masu tonon asiri, wanda zasu haska maka har kasan zuciyarshi inka natsu a cikinsu. Shisa ko yayi kokarin kama bakinshi sai su fada maka duk wata kalma da bai furta ba. Wani irin so Hajiya Rumana takeyi masa da ita kanta bata san iyakarshi ba. Sone daya makantar da ita daga ganin laifukanshi, a wajenta kome Haris zaiyi kuruciya ce, zai bari idan yayi hankali. A wannan bigiren ya kammala ajinshi uku, ya kuma shiga aji daya inda ya zabi bangaren Art, tunda bason karatun yakeyi ba, yama fara kokartawa ne tun wani zagi da aka hadu akayi musu a staff room. Wata Malama ta kirasu da "Dakikai" Kalmar nan tayi masa ciwo matuka, da yayiwa su Sulaiman magana kan ya kamata su fara maida hankali sai abin ya basu dariya, shi dai ya kyalesu ne tunda ba'a dole, ya dai fara canzawa ta bangaren karatun, shisa ya zabi Art din, a tunaninshi zaifi mishi sauki tunda akwai saukin lissafi a duka subjects din. Wannan shekarar itace tazo musu da sauyi daga shi har abokanshi, Idris duk yafisu girma, suna kiranshi da Barde, sai Yakub da soyayyar da yakeyiwa wani sanannen mawaki 2Pac yasa lakabinshi ya koma haka. Sulaiman daman ana kiranshi Lalaye ne tun suna aji daya. A lokacin Haris ne bashi da wani sunan banza. Lokacin da suka dawo hutun first term na aji hudu a Sakandiri ne suka ga canji mai yawa tare da 2Pac, da yake su mahaifiyarsu bata tare da Babansu, tun suna primary suka rabu, gallazawar da mahaifinsu ya kula suna fuskanta ne ma yasa duk ya daukesu yana rarrabasu a makarantun kwana, sai dai babban wanshi da aka tura kasar Amurka, haka ya dawo ya zama rikakken dan shaye-shaye, yanzun haka wannan komawa hutun da 2Pac yayi ma an kai yayan Rehab saboda kwakwalwarshi ta fara samun matsala. Wani abu da iyayen 2Pac da ma abokanshi basu sani ba tun yana aji daya ya fara sha, daga maganin tari, saiya koma sato kwayoyin daya ke gani wajen yayan nashi, kuma sai kowa yayi bacci yake dauko daya ya rabata wajen gida takwas, saiya totse kashi daya yake iya samun bacci. Kamar yanda dabi'ar masu shaye-shaye take, suna girma abin yana gaba, saiya zamana a hankali yake kara dosage din, wannan hutun daya koma kuma ya hadu da wasu abokan da suka girmi kanshi sai suka koya masa shan wiwi, da yake Baban 2Pac na tunanin zai cike musu gurbin rashinshi da na mahaifiyarsu hadi da gallazawar matarshi sai yake sakar musu kudi sosai da sosai, harma baisan abinda zaiyi da kudadenshi ba lokutta da dama, sai yanzun daya fara amfani dasu yana siyan wiwi. Itace yayi sneaking dinta da yawa, da yake abokan sun koya masa yanda ake boyonta, kasan takalman makarantarshi. Sai dare ya raba in ya nada saiya boye da lighter dinshi ya tafi bandakin makaranta ya zuqa. Haris shiya fara kamashi, da farko ya tsorata, har saida sukayi fada da 2Pac din, amman abu na kuruciya, sai yanda 2Pac din yake nada wiwin ya kuma kunnata yana zuqa ya fara burge Haris, harya gwada shima, ranar farko kara daya ya zuqe bayan tarin daya dingayi a zuka wajen biyar kamar zai shide amman yaki hakura, sai dai maimakon cajin da yake ta kwadaita masa, sai yaji kamar kawai wani abune yake dan yawo a kanshi, bai bugu yanda ya kamata ace yayi ba. Kafin term ya kare saiya zamana sun janyo Barde da Lalaye sun fara wannan muguwar ta'adar. Waje suka gano ma cikin makarantar inda suke zuwa susha kayansu, data kare sai 2Pac ya kwanta ciwon karya, ya dingayi kamar wanda jinnu suka shafa, dole aka mayar dashi gida da permit na kwana uku zuwa sati daya in har bai samu sauki ba. Kwananshi uku yayo musu kayanta ya dawo musu da ita makaranta, har shayi idan aka basu sai Haris ya faki ido ya marmasa ganyen a ciki, lokacin ne ya samu sunanshi na Ganja, dan ba karamin burge abokanshi yakeyi ba, sunce babban kai yake dashi. Kuma Hajiya Rumana ta kara kankaro masa mutunci data siya masa wata tsadaddiyar waya, haka yayi sneaking dinta zuwa makaranta, aikam ranar ko wani dan sarki ba zai nuna ma Haris jin kai ba. Inda ace Hajiya Rumana ta nutsu ta saka idanuwa akan Haris, data kula da canjin da ya samu, a lokacin kuma data ga duhun da labbanshi sukayi fiye da sauran fatarshi saboda yawan hayakin da yake bankawa cikinshi. A lokacin yazo hutu, wanda daga shine zasu shiga aji shidda, Alhaji Mustafa ya jima bai saka shi a ido ba, kamar boye masa Haris din yakeyi, sannan Hajiya Rumana ma tana tayashi wannan boyon. Idan da yamma ya dawo gidan sai tace masa Haris na Islamiyya inya tambaya, idan da daddare ne kuma ace ya tafi sallar isha'i, ko kuma ya riga ya kwanta, shi dai bai karyata ba, amman basu taba haduwa da Haris a masallaci ba, duk da unguwar cike take da masallatai, amman ai na kusa shi duk suke zuwa. Sannan yaushe rabon Haris da wata Islamiyya? Ya kan leka dai in ance ya kwanta, har dakinshi, kuma yana samunshi a kwance din, ya dan tsaya sai yayi masa addu'ar shiriya da neman kariya kawai yaja masa kofar. Sai ya yanke hukunci sai yaga Haris a ranar zai ma fita daga gidan, da yake girkin Hajiya Rumana ne, yayi zamanshi a falo, fushi take tayi masa da baima san dalili ba, yara ne suke yawan hadasu fada, kuma ai ya gaji ya hakura, ya yarda tafi karfinshi akansu, tunda da yace ba zai biyawa su Munira su tafi kasar waje ba, sai tace ita zata biya, nan ne ma ya nuna bata isa ba, sai dai in ya yafe mata su gabaki daya, dole ta hakura, amman yanaji yana gani duk sukayi applying Jami'ar Maiduguri, suka koma wajen danginta, sai dai suzo hutu, a lokacin ma ana maganar auren Munira dinne da wani abokin wasanta na bangaren Hajiya Rumana din, wanda haihuwar kasar Ingila ne, kasancewar mahaifinshi yana aiki acan, akwai 'yan uwan Hajiya Rumana da yawa a kasashen waje. Yaron yanzun haka Likita ne, yana aiki a Birmingham ta kasar Ingila, can dinma zasu tafi, itama sai ta cigaba da karatunta dan ta kusan kammalawa inda take karantar fannin magunguna wato Pharmacy. Lokacin da Haris ya shigo falon, wando ne dogo a jikinshi, ruwan toka mai cizawa, sai farar t-shirt, sumar da ya dan tara kadan bakikirin da ita, tasha gyara sai daukar ido takeyi, kallo daya Alhaji Mustafa yayi masa yaji gabanshi yayi mummunar faduwa, ya kafe shi da ido bayan sun gaisa yana dorawa da "Zo nan Haris" Bai musa ba ya karasa, da yake akan doguwar kujera Alhaji Mustafa yake, shi Haris saiya zauna akan hannun kujerar "Ya makarantar?" Ya tsinci kanshi da tambaya "Alhamdulillah" Cewar Haris, wata irin rashin natsuwa ce take ta shigar Alhaji Mustafa game da Haris din, bai kawo wani abu guda daya a ranshi ba, ya dai tabbatar akwai wani abu da ba dai-dai ba a tare da yaron nashi, anya kuwa Allaah ba zai kamashi akan sakaci da 'ya'yan Hajiya Rumana ba? Ya kamata ma ace ya gaji ya hakura ya bar mata su? To ta ina ma zai fara yanzun, inda Mukhtar ne ko wani a cikin yaran Fadime da yanzun sun zagaye shi kowa nason bashi labari, amman kalli yanzun yanda kalamai sukayi musu karanci tsakaninshi da Haris, kamar wasu bakin juna. "Yaushe zaka koma makaranta?" Haris din ya dan numfasa "Ranar Monday" Saiya jinjina kai, kudi yake sakawa Hajiya Rumana na duk wata hidima data danganci yaran, amman yau sai yace "To ka shirya gobe sai muje muyi siyayyar komawa makarantar ko?" Cike da mamaki Haris ya kalle shi, saboda abune da bai saba ba, "Mami ma ta gama saimun komai da nake bukata" Sukayi shiru na wani lokaci "Karfe nawa zaku wuce ran Monday din?" Haris yasan basa wuce karfe goma, direba ne yake kaisu shi da Hajiya Rumana "Wajen tara da rabi zuwa goma haka muke fita" Kafin ma Alhaji Mustafa yace wani abu Haris din ya mike "Ina dan shirya kayana ne Baba, saida safe" Bai kuma jira amsar shi ba ya wuce abinshi, Alhaji Mustafa yaji wani abu ya takure a cikin kirjinshi, haka ya kwanta da wannan rashin natsuwar, itace kuma ta zame masa wata abokiya a kwanakin har zuwa Monday, da saida su Haris din suka ganshi a shirye tsaf, kallo daya zakayiwa Hajiya Rumana kagane bataji dadin wannan bazata na mijin nata ba. Akan dole akayi tafiyar dashi, har makarantarsu Haris, duk wani report card dinshi da take fada masa wai a makaranta ake ajiyewa sun dai fada mata grade dinshi yasa aka dauko, yaji dan sauki ganin Haris din ya fara kokari, ko a term din da aka fita na bakwai yazo. Ya dai kalli Hajiya Rumana da yaji cewa duk sanda za'a nemeshi yana kasar waje, da alama shugaban makarantar yaji dadin zuwanshi. Sukayi musayar Lamba, Hajiya Rumana na sakawa a ranta, suna koma gida zata faki idon Alhaji Sa'id ta rufe lambar ta yanda shugaban makarantar ba zai iya kira ba, shikuma ta sauya lamba daya a ciki yanda inya kira ma sai daiya samu wani. Ba zata bari Haris na gab da gama makarantar nan sujawo mata wata fitina da Alhaji Mustafa ba, so takeyi akan Haris ta shawo kanshi ya fitar da yaron kasar waje, a gaban idonta yake maganar watakila Mukhtar na da rabon komawa Madina, tunda su kananun duk sunje Umra, manyan kuma sun hadane harda Hajj, acan zaiyi karatunshi, da tayi magana sai yace mata "Bafa ni zan kaishi ba, kwakwalwarshi ce zatayi masa sanadi" Wai ita zai ninke a bai-bai, ta dauki idone ta saka masa, dan ba karamin tashin hankali za'ayi ba ace wani a cikin yaran Fadime ya tsallaka wata kasa da sunan karatu, in har ya nuna mata ba zai fitar da Haris ba, sannan ta riga tayi rantsuwa sai dai yayi abinda zaiyi, amman ko da yardashi ko babu, Haris ba zaiyi karatu a Najeriya ba, haka suka dawo gida. Aikuwa abinda tayi niyya shi tayi data samu ta dauki wayar Alhaji Mustafa. Sai dai har ranta bataso a kirashi ne akan irin rashin ji da rigimar da Haris yakeyi Ko a mugun tunani batayi hasashen kiran da za'ayi ma Alhaji Mustafa har akan Haris har ita saiya girgiza... [24/08, 7:21 am] +234 903 572 3778: #LubnaSufyan ✨ #WomenOfWords #09035723778 (WhatsApp) Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram ne kawai 20/06/2025 In Shaa Allaah, bayan mun kammala shafukan dandano. Zaku iya biya ta: 9035723778 Opay, Lubabatu Sufyan. NAGODE. * LABULE...Asirin mai daki 3 Wata tafiya ce mai matukar muhimmanci ta kamashi zuwa jihar Lagos, saboda dole sai yana wajen komai zai tafi dai-dai, da ya sake komawa makarantarsu Haris tunda ya kira lambar da Shugaban makarantar tasu ya bashi sai wata mace ta dauka, haka ya bata hakuri yana rayawa a ranshi cewar an samu kuskure wajen shigar da lambar, wannan rashin natsuwar da yaji tun ranar da yaga Haris ne yake kara girma duk rana, yana darsa masa wata irin fargaba da tafi karfin fassara. Wani abu na fada masa cewar danshi na bukatarshi, yana bukatar yaja shi a jiki ya gano menene matsalarshi. Satinshi biyu a Lagos kafin ya gama ya dawo Kaduna, sai ya sake shiga wata sabgar bayan ya tambayi Hajiya Rumana ta bashi lambar da take da ita na daya daga cikin Malaman Haris din tace masa babu. Ranar ta kama Lahadi ce, ya kamata ace kuma ya wuni a gida, ko da ba zaiyi bacci ba yana hutawa, sai ya fita wata dubiya, a hanyar dawowa nema kira ya dinga shigowa wayarshi da wata bakuwar lamba, da yake bai cika daga lambar da bai sani ba, amman yanda ake kiran babu kakkautawa yasa shi ya daga hadi dayin sallama. "Alhaji Mustafa ne?" Aka tambaya daga dayan bangaren bayan gajeruwar gaisuwa, ya amsa, sannan aka sanar dashi daga makarantarsu Haris ne, haka kawai yaji zuciyarshi ta buga, musamman da aka sanar dashi ana nemansu ne da gaggawa washegari da zata kama Litinin, jiki da murya a sanyaye ya amsa, tunda ance idan yaje din zaiji koma menene, haka kawai daya koma gida, duk da ba dakin Hajiya Rumana yake ba, sai daya sake shiga ya fada mata kiran da akace anayi masa, taji ranta yayi mugun baci, akan me zasu kirashi? Ai kam dole ne zata kora musu kashedi idan taje "Ba zai wuce kare-karen kudinsu da suka saba bafa, ko kuma kan maganar jarabawar da zasu zana, meye zasu wahalar dakai kai da kake da hidindimu a gabanka, kabarsu kawai goben sai in shirya akaini inji menene" Ya girgiza mata kai, yanajin ya daina bar mata yaran da hidimarsu, koya ne zai dinga kokarin shiga rayuwarsu da sanin me take ciki "Zanje din tunda har suka bukaci hakan, banajin akan karamin dalili ne" Tasan shi, yanayin da yake fuskarshi kuma ya nuna mata babu abinda zata fada da zai sauya masa ra'ayi "Sai in shirya muje tare" Wannan ba laifi bane, shisa ya amsata, suka dan kara taba hira kafin ya fice. Baiyi wani baccin kirki ba saboda tunanin daya cunkushe masa, washegari kuwa tun karfe bakwai na safe daga shi har Hajiya Rumana sun gama shiryawa tunda direbanshi ne zai kaisu. Kuma bayaso ace tara na safiya tayi basu karasa ba shisa yayi mata magana ta shirya da wuri, ta fara janshi da hira taga yana amsata dai-dai, sai kawai ta kama danna wayarta ta kyaleshi. Haka suka karasa makarantar kamar wasu bakin juna, a tunanin Hajiya Rumana ba zai wuce Haris yayi fadan daya saba bane, ya kama wani abokin karatun nashi ya jibga. Ko daya wuce aji daya, babu ruwanshi da duk wani yaro na kasa dashi, wannan seniority din da akeyi a makarantar kwana baya cikin lissafin Haris. Yanda yaran basa shiga hanyarshi haka baya shiga tasu, a aji ma inka cire abokanshi sauran in zasu fita sabgarshi zaiso haka, to fadanshi a tsakanin sa'anninshi ne, sune zai kama ya jibga in wani abin ya hadosu, ya taba jibgar wani Malaminsu dan bautar kasa, ko da yake yace ma ba Malaminshi bane dan Junior section yake koyarwa, shisa baiga dalilin da zaisa ya daga bulala da sunan dukanshi ba, da yake ance matsalar da kudi basa magancewa kalilan ce, dasu Hajiya Rumana ta kashe wannan case din, aka ja masa kunne da suspension din sati biyu kacal. Yau ma ta tabbata Alhaji Mustafa ne zai kwafsa mata, haka suka shiga ofishin shugaban makarantar hancinta a sama, fuskar nan kamar bata taba fara'a ba. Ko gaisuwar da yayi musu ma, a shaqe ta amsa, tanajin shi yanata koro bayani da wani turancin shi da yake kara shakar da ita, sai ga kunnuwanta sun jiyo mata abinda yake neman sakata fadowa daga kujerar da take zaune "Ina mai dana sanin fada maka cewa yaranka na daya daga cikin wanda muka kama suna shaye-shaye a cikin makaranta, ansha kawo mana kara, sai dai abune da yake bukatar bincike shisa bamu dauki wani mataki ba mukayi amfani da wasu hanyoyi wajen zurfafa bincike yanda zamu kamasu da laifin..." Cikin tashin hankali Hajiya Rumana ta katse shi da fadin "Karya ne, ba dai Haris dina ba, shaye-shaye? Karya ne" Ai dan shaye-shaye baya boyuwa ko? Ba haka zaka gansu ko a labarai firgai-firgai ba? Duqu-duqu dasu, Haris dinta da zai shigo dakinta ya fita yana bar mata kamshin  turarenshi na Addictive ambergris, Haris din da yake tsaf-tsaf dashi ko da yaushe, sau nawa suna wuni a gidan bata taba ganinshi yana marisa ba? Ko ana nufin har yayi hutu ya gama baya sha saiya koma makaranta? "Karyane wallahi" Ta sake fadi, Alhaji Mustafa banda "Inalillahi

Chapter 2 of 5