Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 2
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels GAMO DA AJALI GAMO DA AJALI Mukhtar Kwalisa Gamo da Ajali amuwa mai yawa ta lulluve zukatan xaruruwan jarumai, mafi yawancin su suna yawo ne cikin  1 GAMO DA AJALI fargaba da tsanain tsoro domin irin abubuwan da suke faruwa a garesu. Hakan ya sa duk wajen daka gansu zaka same su cikin shirin yaqi, suna akan matsayi guda biyu mutuwa ko rayuwa. Amman duk da wannan shirin nasu hakan bai hana ana yi musu xauki xaixai ta hanyar yi musu kisan gilla, abinda yafi komai basu takaici rashin sanin waye yake aikata hakan daga cikin sarakuna, ifiritan aljanu ko manya bokaye na duniya suke musu irin wannan mugun kisan na qare dangi. Faruwar wannan shu’umin al’amarin ya saka manya jarumai da yawa aka rasa su a cikin wannan qarnin. Ganin haka ya matuqar tayar da hankalin duk wani sadauki da yake raye a doron duniya suka shiga cikin mayuwanciyar damuwa duk suka rasa ina za su saka kansu domin yawan fargaba da damuwa data lulluve musu rai. Masu boyake suka yi ta kai musu kukansu domin su gano musu abunda yake kashe zaratan sadaukai masu tumbe a fagen fama, amman kuma qarfin tsafi da yawaitar bincike da watsa alqaluma na tsafi yaqi nuna 2 GAMO DA AJALI ainahin abunda yake aiwatar da kisan gillar ga baraden sadaukai, hakan qara xaga hankalin sarakuna da jarumai domin sun rasa madafa. Qasar Rum ta zamto itace mai yawan jarumai gwaraza kuma ita ce qasar datafi ko wacce qasa qarfi a wannan lokacin, don haka yawan sadaukanta da suka halaka a wannan anobar data vulo tafi shafarsu, wannan abun yasa hankalin sarki Dukuruf ya matuqar tashi, ya kasance a cikin tsananin damuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye, duk sanda ka ga sarki Dukuruf zaka same shi a cikin tsananin damuwa, damuwarsa ta qaru ne a wannan safiyar ta yau, hakan ya faru ne kuma sakamakon mummunan labarin daya same shi a safiyar yau. Daga wajen da sarki Dukuru yake zaune yana iya hango gawar xansa a yashe a xakinsa anyi gunduwa-gunduwa da ita, kwana biyu da suka gabata aka yiwa qaninsa irin wannan mummunan kisan, duka waxan nan ‘ya ‘yan sarki Dukuruf zaratan jarumai ne masu tsananin tumbe a fagen daga. A wannan lokacin babu abinda ya rage wa sarki a duniya 3 GAMO DA AJALI sai wata ‘yarsa guda xaya tilo dayake mutuwar qaunarta. Ta kasance gwarzuwa mai bajinta da jajircewa a fagen fama, kamar sauran ‘yan uwanta, tuna ‘yartasa daya yi yasa Sarki Dakuruf ya kuma dulmiya cikin wata damuwar domin ya ji a cikin zuciyarsa wata qila ita ma ta rasa ranta, hakan yasa tun daga lokacin da aka yin a yayanta duk wajen da sarki za shi suna tare da ita, domin a ganinsa koma mene yake kashe sadauka to shi zai iya kareta daga garesa. A yanzu da yake zaune ya yi shiru, zaman jiran bokansa dake zuwa garesa duk shekara-shekara yake yi, wanda shi kaxai ne yake da yaqinin duk duniya zai faxa masa wannan voyayyen abun da yake farauce rayukan sadaukai... kafin ya kammala tunaninsa sai ya ji wata qara ta bayyana sannan lokaci xaya qasa tat sage wani jan hayaqi ya fito daga cikinta ya taru a gaban sarki Dukuruf batare da jumawa ba ya rikixa ya koma Boka salsala. Ya soma duban sarki Dukuruf sannan ya qyalqyale da wata dariya mai ximautarwa 4 GAMO DA AJALI sai daya yi ta tsawon wasu daqiqai sannan ya tsagaita gami da faxin. “Ka gama kanka da wahala ya kai wannan maxaukakin sarkin domin ka sakawa zuciyarka tunanin da duk duniya babu mai yarje maka shi” Jin maganar Boka Salsala ta kuma tayarwa da Sarki Dukuruf hankali domin haka cikin azama ya zube gaban Boka Salsala yana faxin. “Kayi min rai ya shugaban bokayen duniya,ka ceci rayuwata data ‘yarta da sauran zaratan sadaukaina daga halaka ka taimake ni ya bokan bokayen duk duniya” Ganin haka yasa Boka Salsala ya qyalqyale da wata dariya kana daga bi sa ni ya tsagaita ya kalli sarki Dukuruf gami da faxin. “Duk duniya babu wani mahaluki daya san abinda yake kashe mazaje sai ni xaya, to amman kayi sani yakai wannan sarki abu guda biyu ne kawai za su zamto mafita gareku” Ya tsagaitawa da magana yana kallon fuskar Sarki Dukuruf dake faman naso kamar an kara waina a jikin tanda ya ci gaba da magana. “Dole sai an xauko kayan yaqin sarki salmanu da suke ajiye akan tsuburin Duf, wanda jarumai ashirin suke da alhalin zuwa, 5 GAMO DA AJALI suma guda goma sha shida sun fito ne daga qasa daban-daban, su za su tafi xauko kayan babu tabbas akwai wanda zai dawo da ransa. Sai kuma abi na biyu matuqar za a fita sai an kamo sauran sadaukai talatin da suka rage a duniya an gamasu wuri xaya a qone su da wuta sun halaka, wannan ita kaxai ce mafita ya kuma zama dole a yi haka” Boka Salsala ya qare maganar yana miqawa sarki Dukuruf wasu takardu guda biyu masu xauke da sunaye. Sarki ya saka hannu ya amsa ya soma dubawa ganin sunan ‘yarsa daya yi shi ne ya qara xaga masa hankali cikin sauri ya xago da kansa da zumar magana amma kafin yace wani abu Boka Salsala ya ci gaba da magana. “Zan haxaku da wata rundunar aljanu da za su zamto masu kamo muku duk wani sadauki da yake cikin wannan doguwar takarda, sune za a qona da wuta, sannan akwai waxanda za su xauki ‘yan aikenka su kai su zuwa sauran qasashen inda za a tattaro sauran sadaukan da za su tafi tsaunin Duf domin xauko kayan yaqin sarki salmanu”. Sarki Dukuruf ya yi shiru kawai yana sauraron maganar Boka Salsala wace duk ta gama hautsina masa qwaqwalwa, amman 6 GAMO DA AJALI kuma yasan bashi da ikon canza wani abu daga cikin abubuwan da suka shafi maganar Bokan na sa, duk da haka sai daya yi qarfin hali ya dubi Boka Salsala cikin wata murya da yake tunanin kamar ba tashi bace yace masa. “Ya kamata a nemar mani afuwa wurin abin bauta Gunki Zukuq daya taimake mu a cire sunan xiyata tilo data yi saura tunda ya xauke min sauran ‘ya ‘yan nawa”. Boka Salsala ya daka masa tsawa, wacce sai data rikita Sarki Dukuruf. “Baka isa ba, baka da wani zavi daya wuce abinda abin bauta ya bayyana, kar ka yi masa butulci ka saka ya yi fushi daku ya hanaku samun nasara, shi kasan mafita ne game da abinda ya riqa faruwa daku tsawon lokaci ba sai yanzu da aka sanar dakai ba?” Yana gama faxa masa haka ya rikixe ya koma hayaqi qasa ta tsage ya shige cikinta cikin azamar Sarki Dukuruf ya miqe domin bashi haquri amman ya makara ganin haka yasa ya xora akai ya taqarqare duk qarfinsa ya kurma wani uban ihu. ‘yarsa ta bankaxo xakin ta shigo da gudu duk da zamtowar dokace babu wanda 7 GAMO DA AJALI yake shiga cikin xakin, ta tsaya suna kallonkallo ita da mahaifinta. “Lafiya Baba?” Tayi masa tambayar tana kallonsa. “Wannan shekarar akwai masifa, jama’a za su zamto a cikin bala’i duniya zata zama cikin qunci” Abinda ya iya cewa kenan ya juya a fusace ya fice daga cikin xakin. Tun lokacin data mallaki hankalinta tasan kanta har tayi wani abu da zai taimaketa, ta ji tana matuqar son mahaifinta irin son da bata tava yiwa wani mahaluki ba. Saboda irin yanayin kulawar da yake nunawa akanta hakan yasa take ji a cikin ranta zata iya yin komai domin kare martaba da qimar mulkin mahaifinta. Azima kyakkyawa mai matuqar kyau da cikar halita wacce duk zamanin babu mai kyawunta, gata jaruma mai matuqar yawan bajinta da dauriya bata ko shayin wani gwarzo, amman ganin irin kisan da ake yiwa gwarazan jarumai ba tare da sanin ko waye mahalukin ba. Babban abun baqin cikinta zata mutu ba tare data aikata wata bajinta ba da zata zamto tarihi ga ‘yan baya domin haka da 8 GAMO DA AJALI maganar da mahaifinta ya gaya mata da lamarin dake damar mata qwaqwalwa suka taru suka zamto wani babban ruxani gareta. Daga wurin da take a zaune akan shimfixar ta alfarma a xakin alfarma a waje barada birjik cikin kayan yaqi sonata faman rarraba idanuwa domin ganin wanda zai kawo farmaki zuwa gare su. Itama da take cikin xakin tana cikin shirin yaqi ne tana riqe da duk wani na’u’in makami kamar yadda sauran sadaukan suke. Azima tayi shiru ita xaya lokaci zuwa lokaci takan zaro takobinta tax an shafeta amman hankalinta ya yi nisa wurin yawaitar tunani, bayan tsawon lokaci ta miqe ta xauko wani xan mulmulallen qarfe ta doka a jikin wani xan sanho, ai kuwa bata gama bugawa ba wani tiririn hayaqi ya turniqe a cikin xakin, a sannu a hankali hayaqin yana raguwa a lokacin wani matashin saurayi ya baiyana tsaye da jakar bokanci ya na yiwa Azima murmushi idanunsa akanta. “Meye ka qura min ido kana kallona kamar kaga wata halite da baka saba ganinta ba?” Da Gadara irin ta jarumai ta yi masa tambayar. 9 GAMO DA AJALI Boka hamad ya yi wani marayan murmushi gareta, tun tsawon lokaci mai tsawo yake tare da ita har ta mallaki sirrin kiransa bata tava yi masa irin wannan kiran ba cikin gaggawa sai yau, ya qara shagala zuwa ga kallonta kafin daga bisani ya sunkuyar da kansa domin yasan sai dai gani ya qyale. Ya jima yana qaunarta a cikin zuciyarsa, amman kuma ya rasa hanyar da zai bi domin ya bayyana mata. Ya dakatar da tunaninsa gami da kuma kallonta, kafin ya xauke kansa daga gareta ba tare daya bata amsar tambayar data yi masa ba a hankali ya motsa fatar bakinsa da zumar yi mata magana. ‘Me yasa kika yi min wannan kiran gaggawar a cikin wannan talatainin daren, a lokacin da nake kan aiwatar da wani bincikena mai matuqar muhimanci”. Ta gyara riqon data yiwa takobinta. “Ina son sanin abinda aka faxawa mahaifina har naga hankalinsa ya xaga?” Boka Hamad ya kalleta kallon tsawon lokaci kafin ya kauda kansa gefe guda a hankali ya soma faxa mata duk abinda ya faru. 10 GAMO DA AJALI Itama jin labarin ya matuqar tayar mata da hankali ya birkitatta, hakan yasa ta kuma kallonsa da wani kallo na tsananin ruxani tace masa. “Yakai maxaukakin boka mai daraja mai girma xan saurayi matashi mai kyawu abun kwatance...” Ta xan dakata da maganarta ta kuma kallonsa domin gano tasirin da lafazinta ya yi a gareshi. “Gaskiya kinyi min yabo da tunda nake a duniya babu wanda ya tava yi min shi, saboda haka na yi miki alqawarin zan taimaka miki akan komai idan kika nema daga gare ni” Da kwantar da murya yace mata. Ta yi matuqar jin daxin haka, wannan karon cikin qwarin gwiwa tace masa. “Waye makashin jarumai?” Tambayar ta tayar masa da hankali, domin lokaci xaya fuskarsa ta sauya kamar yadda zabibi yake sauya ruwa idan aka zube, ba qwarin gwiwa a muryarsa yace mata. “Tabbas babu wata mafita data wuce bin maganar Boka Salsala na xauko kayan yaqin sarki salmanu dake tsubirin Duf wanda jarumai ashirin za su kuma a kamo talatin a qonasu da wuta har su halaka, game da 11 GAMO DA AJALI tambayarki kuma wane makashin sadaukar, amsar ita ce har zuwa yanzu babu wani mahalukin daya gano wane makashin kawai dai ana zargin-zargi ne har yanzu an kasa gano gaskiyar lamarin” Maganar shi ta matuqar tsuma zuciyar Azima tayi shiru kawai tana tunanin mafita ga lamarin can bayan tsawon lokaci taja numfashi tare da faxin. “Babu wata mafita bayan wannan?” Boka Hamad ya kalleta wannan karon da xan murmushi akan fuskarta. “Sai dai mutuwa”. Azima ta tsaya tsai kawai tana kallonsa, tabbas ta aminta ya zama dole tayi shirin tunkarar abinda yanzu yake gabansu. “Zan baki kariya amman da sharaxi idan kika aminta za ki aure ni idan kun dawo daga tsuburin Duf”. Maganar tashi tayi wa Azima wata irin shiga, tunda take a rayuwarta wani mahaluki bai tava faxa mata wannan maganar ba sai shi, wannan dalilin yasa ta ji ya burgeta dahar ya yi jarumtar sanar da ita abinda yake cikin zuciyarsa, duk kuwa da ruxanin data kasance a ciki. 12 GAMO DA AJALI Ta yi masa wani marayan kallo daya saka tunaninsa tsayawa na wucin gadi. “Duk zamanin nan babu wata mace da zaka nunawa qauna ta tsere daga gareka musamman idan har kunyi kallon-kallo da ita”. Boka Hamad ya ji matuqar daxin maganarta haka kuma bai tava tsamanin zai shawo kanta cikin ruwan sanyi ba. “Zan kareki duk nisan da kika yi da ni, zan tsumaki ki zamto gaggara gasa ko wane mahaluki a duniya kuma ke za ki zama mai nasara a lokacin zuwa tsubirin Duf” Wannan maganar daya faxawa Azima ta qara bata qwarin gwiwa haka kuma hankalinta ya kwanta. ** A lokacin da sarki Dukuruf bai tava tsamani ba ya samu nasarar kamo gwarazan jarumai talatin da aka lisafa waxanda sune za a qone su a cikin wuta, sannan aka gayato sauran da za su tafi xauko kayan yaqin sarki sulaiman, hakan ba qaramin mamaki ya baiwa sarki Dukuruf ba. Hakan yasa suka tsaida rana ita yau a matsayin ranar da za qone sadaukan domin cima umarnin Boka Salsala, kuma za su yi 13 GAMO DA AJALI haka ne domin kar waxanda aka gayato su zo suka abinda yake faruwa na zallunci musamman domin sato su aka yi ba tare da sanin iyalansu ba. Bayan tsawon lokaci da xumbin dubatar jama’ar birnin rum suka xauka suna jiran fitowar sarki daga bisani suka soma jiwo tashin algaita da bugun tambura hakan ne suke nuni garesu sarki yana gab da fitowa, bayan wasu ‘yan sakani suka hango sarki tafe tare da ‘yarsa Azima a vangaren sa tana cikin wata shiga ta alfarma sai qyalqyali take yi. Jama’ar qasar suka varke da sowa da ihu gami da yawan iface-iface bayan tsawon lokaci sarki ya xaga musu hannu lokaci xaya wurin ya yi shiru kamar babu wata halita mai numfashi a wajen. Sarki Dukuruf ya qurawa yawaitar sadaukan da jama’arsa idanu na wani taqin lokaci, sai yaji wani irin alfahari ya lulluve masa rai don haka da tsananin girman kai ya soma magana. “Yaku jama’ar birnin rum nasan kuna da masaniyar irin abinda yake gudana ga gwarazan sadaukan mu na salwantar rayukansu, bama mu kaxai ba duk duniya tana 14 GAMO DA AJALI cikin wannan barazanar hakan shi yasa fargaba ga zukatan jarumai. Amman da muka nemi taimako an sanar da mu hanyar samun nasara wacce a cikinta dole sai mun qone sadaukan nan guda talatin, sannan kuma mun tura guda ashirin zuwa tsibirin Duf dan xauko kayan yaqin sarki salmanu, wannan saqo ne daga abin bautar mu” Ya kammala maganar yana kallon jama’arsa koda suka ji haka sai suka varke da ihu da iface-iface. Sarki ya koma ya zauna, sannan ya bada uwarni domin qona sadaukan da za a saka a cikin wutar da aka kunna tana ci gangaganga, cikin gaggawa aka soma janyo sadaukan da suke xaure cikin wasu manyamanya baqaqen sarqoqi kana kallonsu za ka ga duk sun sauya kama saboda wahala da suka sha, idan ka kalle su zaka ga tsoro bayyane a idanun wasu daga cikin su, wasu kuma saboda tsananin jarumta ko gezau basu yi a haka aka riqa kai su ana jefawa a cikin wani rami mai tsayin zura’i goma. Wanda aka xauki tsawon kwanaki ana hura wutar. Duk sadaukin da aka cila a cikin wutar sai dai kaji ihunsa zuwa wasu ‘yan sakani sai 15 GAMO DA AJALI ka ji shiru wuta ta qone shi, haka aka riqa jawo sadaukai xaya bayan xaya ana cillasu cikin wutar suna halaka a haka har ya zamana sauran wani sadauki guda xaya a tsaye shi xaya jal, wannan sadaukin ya kasance tsufa ya kamashi amman duk da haka akwai zubin jarumta a tattare da shi ya kasance jarumi daya wanda ya gagari duniyar sarakuna, bokaye da sadaukai duk lokacin daya fito yaqi aljanu ma guduwa suke yi. Amman a yau ya zama cikin sarqa ana shirin halaka shi. Aka jawoshi da qyar yana tafiya cikin isa da izza kamar ba halaka zai yi ba, a haka aka qaraso wajen da sarki Dukuruf yake zaune suna qarasowa sarki da kansa ya miqe domin girmamawa ga wannan tsohon sadaukin. Yaja ya tirje yana duban sarki ido cikin ido sannan cikin wata murya wacce amonta yake hauhauwa yace masa. “Tabbas munyi wa qasar nan bauta tun daga quruciya har zuwa tsofa, mun xaga darajarta har ta gagari duniya, amman da wanna sakamakon aka saka mana, sai dai ka yi sani yakai sarki Dukuruf kun bar baya da qura saboda matashin jarumi ya bayyana kuma zai 16 GAMO DA AJALI binciko duk wani voyayyen matsoranci daya zamto yana halakar da sadaukai” Yana kammala maganar ya sunkuyar da kai ya yi gaba abinsa ya nufi wajen da wutar take ci tana toroqo. Maganar daya faxa ta tsaya a zuciyar sarki Dukuruf saboda bai fahimci abinda yake nufi ba, ya kuma san halin sadauki bangu indai ya yi magana akwai abinda take nufi, kuma duk abinda ya faxa babu makawa sai ya faru” Da yana da iko hana aiwatar da kashe shi da tuni ya hana, amman yana kallo aka cila shi cikin wutar amman abin mamaki babu wanda ya ji ihunsa. Jama’ar dake gurin suka yi shiru suna kallon-kallo a tsakaninsu suna masu qara jinjinawa jarumtaka irin ta sadauki Bangu, tabbas ya bar abin tarihi wanda za a sanar da ‘yan baya. Daga nan sarki Dukuruf bai kuma cewa komai ba ya juya cikin kasala ya nufi gida Azima ta rufa masa baya. Suma jama’ar birnin kowa ya watse aka shiga harkokin yau da kullum. 17 GAMO DA AJALI A hakankali awani suka rikixa suka zama kwanaki, su kuma kwanaki suka zama kwana bakwai a cikin kwanakin kullum sai wani sabon abu ya faru na zuwan wani jarumin sadauki daga wata nahiya a haka suka taru har baqin sadaukan da aka gayyata suka taru suka zama goma sha tara ya zamana sauran sadauki xaya ake jira. Mafiya yawa daga maqwabtan birnin rum suka zo, sai tsiraru da suka zo daga wata nahiya ta daban hakan ya saka aka samu bambanci addini da kuma al’ada, wasu suna bautar gunki, wasu rana suke bautawa yayin da wasu zaka samu wuta suke bauyawa sai kuma masu yin bauta ga ubangiji wanda ya yi umarni da bin tafarkin tsira. Har kwanaki biyar suka qaru akai amman xaya sadaukin da ake jira bai zo ba, hakan ba qaramin xagawa sarki Dukuruf hankali ya yi ba, amman hankalinsa ya fi tashi ne idan ya tuna da rabuwa da ‘yarsa Azima wannan ne yafi komai xaga masa hankali. Ganin lokaci yaja sadaukin bai zo ba sai ya soma tunanin ko qaddarar da take hawa kan sadaukai ko ta same shi ne? don haka aka fitar da ranar tafiya ko ya zo ko bai zo ba. 18 GAMO DA AJALI A lokacin da aka fitar da tsamani a lokacin matashin jarumin ya bayyana, yana haye bisa wani baqin doki mai nagarta, kamar yadda mahayinsa shima ya zama nagartace ma’abocin kwarjini yana da doguwar fuska da manyan dara-daran idanu da jerarun fararen haqora kamar gonar auduga, gashin kansa ya zuba har baya ya warwatsu sashe zuwa sashe. Ya kasance mai yawan tambaya akan duk abinda ya gani bai sani ba, ya kasance ma’abocin bin tafarkin addinin musulunci. Bai san tsoro ba kuma baya shayin kowa saboda duk da wannan kisan da ake yiwa sadaukai shi ko kaxan bai xaxa shi da qasa ba sabida yasan mutuwa da rayuwa tana hannun Allah idan lokacinka ya yi babu makawa sai ka mutu, hakan yasa yake gudanar da rayuwarsa cikin walwala da jin daxi. Wannan shi ne jarumi Salman. Kai tsaye ya nufi fada ba tare da fargaba ko shayin wani abu ba, duk da kasancewar yamaci ya yi rana ta tafi faxuwa ya qarasa qofar fada yaja dokinsa ya tsaya yana kallon dogarawan da suke tsattsaye a tsube cikin shirin kota kwana. 19 GAMO DA AJALI Cikin sauri wasu daga cikinsu suka kama mishi ya sauka, sannan aka yi masa jagora zuwa wajen sarki a haka suka qarasa wata turaka inda suka samu wasu mafiya yawa daga cikin dakaru suna gadi, a hankali suka qarasa suka yi wata magana da Salma bai ji abinda suka ce ba sai ganin sun juyo gareshi suka yi masa alama daya qaraso. “Sarki yasan da zuwanka?” Wani dogari mai kai kamar qoqo ya tambaye shi. Salman bai bashi amsa ba sai kawai ya sa kai cikin xakin inda ya samu sarki Dukuruf a zaune yana bincike a cikin wani qaton littafi da Salman ya gaza gane rubutun dake jikinsa, face wani xan hoto daya gani anyi na wani xan mulmulallen abu da hoton gunki kan saniya. Ya nemi gefe guda ya zauna yana kallonsa har ya kammala ya xago da qananun jajayen idanunusa masu kama dana maciji suka yi kallon-kallo. Duk duniya babu abinda sarki Dukuruf ya tsana sama da ma’abota addinin musulunci, hakan ya saka babu abinda yake shiga tsakaninsa da duk ma’aboncin musulunci sai kisa. 20 GAMO DA AJALI Yana da masaniyar wane Salma, yasan ma’aboncin musulunci ne wanda ya fito daga yankin masu tsattsauran ra’ayi da riqo da addinin musulunci hakan yasa bai samu wata tarba sosai daga gare shi ba, mai makon haka sai wani kallon hadarin kaji daya yi masa. “Barka da zuwa cikon sauran jaruman” Sarki Dukuruf yace masa. “Har an gayyato sauran kenan, mu dai mun sadaukar da rayukan mu domin na baya su rayu” Yana kammala maganar ya miqe domin barin xakin, a lokacin daya miqe ne sarki Dukuruf ya samu ikon qare masa kallo a yanzu ya tabbatar da cikar jarumtaka a tattare da shi. Wani sadauki ya yi masa jagora zuwa masaukinsa wanda aka ware a cikin wani vangare daga gidan sarki, anyi hane sakamakon sauran su kenan a duniya, kuma sune ake saka ran za su zama mafita a duniyar jarumta. A haka suka qarasa har zuwa masaukinsa ya shiga ya tarar da an shigar masa da ragowar kayansa ya zauna, zaman shi ke da wuya ya gano kwanikan abinci waxanda aka ajiye masa ya miqe cikin sauri ya xebi wanda 21 GAMO DA AJALI ransa yake so ya zauna ya soma ci har sai daya qoshi, ya shiga wajen wanka ya yi wanka ya sako wasu kayan alfarma ya fito da zumar ya xan tattaka domin miqe qafafunsa da kuma baiwa idonshi abinci na daga kallon tsarin gidan sarautar Rum. A lokacin daya fito itama Azima ta zo daidai wurin domin shiga vangarenta, suka yi musayar kallo a tsakaninsu, su duka suka ja suka tsaya kamar an tirsassa musu yin haka, suka qurawa juna idanuwa suna duban juna kowa yana mamakin kyawun xan uwansa. Ta kawar da kanta gefe tayi gaba da zumar barin wajen, a lokacin shima ya motsa ya shiga gabanta ya tsaya wanda hakan yasa ya tsare mata hanya kafin tayi wani yunquri yace mata. “Ko zan iya sanin ko ke wacce ce yake ma’abociyar kyawu? Azima ta kauda kai gefe tace masa. “Bani da suna” Ya yi murmushi. “An tava yin mutumin da bashi da suna? Da za ki daure ki sanar da ni domin na yi gaggawar sanar dake wani sirri” Ta xago idanu ta dube shi cikin wani sirrin kallo, ya sauke numfashi kafin ya daidaita tunaninsa sai 22 GAMO DA AJALI yaga ta tunkaro shi gadan-gadan kamar zata shiga jikinsa. “Kar ki haxa jikin ki da shi, ke yanzu tamu ce kina soyayya ne da matashin boka” Wata siririyar murya mai kama da raxa tace mata. Hakan shi ne ya tilastawa Azima tsayawa cak kamar an kafeta a wajen daga wajen da take tsaye tana iya jiyo bugun numfashin Salman, ta dubi wajen data ji murya tana mata raxa amman bata samu ikon ganin Boka Hamad ba. Ganin kallon da take yi yasa wani hayaqi ya tashi a wajen lokaci guda, suka dubi wajen su duka biyu a lokacin Boka Hamad ya bayyana a gabansu fuskarsa a murtuke kamar an sassaqo daga katako. Ya jefi Salman da wani mugun kallo sannan yace masa. “Kai yaro wargi waje ya ke samu, wannan Gimbiyar tafi qarfin yaro sai dai baban yaro” Salman ya yi murmushi. “Lallai yanzu ne na yadda cewar ita ce wacce ya kamata na nemi aurenta don fafatawa da jahilai irin ku” Idon Boka Hamad ya kaxa ya yi ja. 23 GAMO DA AJALI “Ahir! Xinka kar gigiwa ta kai ka ta baro, domin yanzu nan na saka a naxe maka qafafu” Salman ya buga masa harara. “Yaro bai san wuta ba, sai ya taka” Yana gama faxa mata haka sai ya sunkuya a hankali ya kamo hannunta ya sumbata ya yi gaba abinsa. Hakan daya aikata ba qaramin qonawa Boka Hamad zuciya ya yi ba, ya ji zuciyarsa ta soma raurawa tana azalzala a cikin qirjinsa, a haka ya bi bayan Salman da kallo har sai daya vace masa. Ku min afuwa ci gaban labarin yana littafi na biyu. Na

Chapter 1 of 2