An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
GAMO DA AJALI
GAMO DA AJALI
Mukhtar Kwalisa
Gamo da Ajali
amuwa mai yawa ta lulluve
zukatan xaruruwan jarumai, mafi
yawancin su suna yawo ne cikin
1
GAMO DA AJALI
fargaba da tsanain tsoro domin irin abubuwan
da suke faruwa a garesu. Hakan ya sa duk
wajen daka gansu zaka same su cikin shirin
yaqi, suna akan matsayi guda biyu mutuwa ko
rayuwa.
Amman duk da wannan shirin nasu
hakan bai hana ana yi musu xauki xaixai ta
hanyar yi musu kisan gilla, abinda yafi komai
basu takaici rashin sanin waye yake aikata
hakan daga cikin sarakuna, ifiritan aljanu ko
manya bokaye na duniya suke musu irin
wannan mugun kisan na qare dangi.
Faruwar wannan shu’umin al’amarin
ya saka manya jarumai da yawa aka rasa su a
cikin wannan qarnin.
Ganin haka ya matuqar tayar da
hankalin duk wani sadauki da yake raye a
doron duniya suka shiga cikin mayuwanciyar
damuwa duk suka rasa ina za su saka kansu
domin yawan fargaba da damuwa data lulluve
musu rai.
Masu boyake suka yi ta kai musu
kukansu domin su gano musu abunda yake
kashe zaratan sadaukai masu tumbe a fagen
fama, amman kuma qarfin tsafi da yawaitar
bincike da watsa alqaluma na tsafi yaqi nuna
2
GAMO DA AJALI
ainahin abunda yake aiwatar da kisan gillar ga
baraden sadaukai, hakan qara xaga hankalin
sarakuna da jarumai domin sun rasa madafa.
Qasar Rum ta zamto itace mai yawan
jarumai gwaraza kuma ita ce qasar datafi ko
wacce qasa qarfi a wannan lokacin, don haka
yawan sadaukanta da suka halaka a wannan
anobar data vulo tafi shafarsu, wannan abun
yasa hankalin sarki Dukuruf ya matuqar tashi,
ya kasance a cikin tsananin damuwa ya kasa
zaune ya kasa tsaye, duk sanda ka ga sarki
Dukuruf zaka same shi a cikin tsananin
damuwa, damuwarsa ta qaru ne a wannan
safiyar ta yau, hakan ya faru ne kuma
sakamakon mummunan labarin daya same shi
a safiyar yau.
Daga wajen da sarki Dukuru yake
zaune yana iya hango gawar xansa a yashe a
xakinsa anyi gunduwa-gunduwa da ita, kwana
biyu da suka gabata aka yiwa qaninsa irin
wannan mummunan kisan, duka waxan nan
‘ya ‘yan sarki Dukuruf zaratan jarumai ne
masu tsananin tumbe a fagen daga. A wannan
lokacin babu abinda ya rage wa sarki a duniya
3
GAMO DA AJALI
sai wata ‘yarsa guda xaya tilo dayake mutuwar
qaunarta.
Ta kasance gwarzuwa mai bajinta da
jajircewa a fagen fama, kamar sauran ‘yan
uwanta, tuna ‘yartasa daya yi yasa Sarki
Dakuruf ya kuma dulmiya cikin wata damuwar
domin ya ji a cikin zuciyarsa wata qila ita ma
ta rasa ranta, hakan yasa tun daga lokacin da
aka yin a yayanta duk wajen da sarki za shi
suna tare da ita, domin a ganinsa koma mene
yake kashe sadauka to shi zai iya kareta daga
garesa.
A yanzu da yake zaune ya yi shiru,
zaman jiran bokansa dake zuwa garesa duk
shekara-shekara yake yi, wanda shi kaxai ne
yake da yaqinin duk duniya zai faxa masa
wannan voyayyen abun da yake farauce
rayukan sadaukai... kafin ya kammala
tunaninsa sai ya ji wata qara ta bayyana
sannan lokaci xaya qasa tat sage wani jan
hayaqi ya fito daga cikinta ya taru a gaban
sarki Dukuruf batare da jumawa ba ya rikixa
ya koma Boka salsala.
Ya soma duban sarki Dukuruf sannan
ya qyalqyale da wata dariya mai ximautarwa
4
GAMO DA AJALI
sai daya yi ta tsawon wasu daqiqai sannan ya
tsagaita gami da faxin.
“Ka gama kanka da wahala ya kai
wannan maxaukakin sarkin domin ka sakawa
zuciyarka tunanin da duk duniya babu mai
yarje maka shi” Jin maganar Boka Salsala ta
kuma tayarwa da Sarki Dukuruf hankali domin
haka cikin azama ya zube gaban Boka Salsala
yana faxin.
“Kayi min rai ya shugaban bokayen
duniya,ka ceci rayuwata data ‘yarta da sauran
zaratan sadaukaina daga halaka ka taimake ni
ya bokan bokayen duk duniya” Ganin haka
yasa Boka Salsala ya qyalqyale da wata dariya
kana daga bi sa ni ya tsagaita ya kalli sarki
Dukuruf gami da faxin.
“Duk duniya babu wani mahaluki daya
san abinda yake kashe mazaje sai ni xaya, to
amman kayi sani yakai wannan sarki abu guda
biyu ne kawai za su zamto mafita gareku” Ya
tsagaitawa da magana yana kallon fuskar Sarki
Dukuruf dake faman naso kamar an kara waina
a jikin tanda ya ci gaba da magana.
“Dole sai an xauko kayan yaqin sarki
salmanu da suke ajiye akan tsuburin Duf,
wanda jarumai ashirin suke da alhalin zuwa,
5
GAMO DA AJALI
suma guda goma sha shida sun fito ne daga
qasa daban-daban, su za su tafi xauko kayan
babu tabbas akwai wanda zai dawo da ransa.
Sai kuma abi na biyu matuqar za a fita
sai an kamo sauran sadaukai talatin da suka
rage a duniya an gamasu wuri xaya a qone su
da wuta sun halaka, wannan ita kaxai ce mafita
ya kuma zama dole a yi haka” Boka Salsala ya
qare maganar yana miqawa sarki Dukuruf
wasu takardu guda biyu masu xauke da sunaye.
Sarki ya saka hannu ya amsa ya soma
dubawa ganin sunan ‘yarsa daya yi shi ne ya
qara xaga masa hankali cikin sauri ya xago da
kansa da zumar magana amma kafin yace wani
abu Boka Salsala ya ci gaba da magana.
“Zan haxaku da wata rundunar aljanu
da za su zamto masu kamo muku duk wani
sadauki da yake cikin wannan doguwar
takarda, sune za a qona da wuta, sannan akwai
waxanda za su xauki ‘yan aikenka su kai su
zuwa sauran qasashen inda za a tattaro sauran
sadaukan da za su tafi tsaunin Duf domin
xauko kayan yaqin sarki salmanu”.
Sarki Dukuruf ya yi shiru kawai yana
sauraron maganar Boka Salsala wace duk ta
gama hautsina masa qwaqwalwa, amman
6
GAMO DA AJALI
kuma yasan bashi da ikon canza wani abu daga
cikin abubuwan da suka shafi maganar Bokan
na sa, duk da haka sai daya yi qarfin hali ya
dubi Boka Salsala cikin wata murya da yake
tunanin kamar ba tashi bace yace masa.
“Ya kamata a nemar mani afuwa wurin
abin bauta Gunki Zukuq daya taimake mu a
cire sunan xiyata tilo data yi saura tunda ya
xauke min sauran ‘ya ‘yan nawa”.
Boka Salsala ya daka masa tsawa,
wacce sai data rikita Sarki Dukuruf.
“Baka isa ba, baka da wani zavi daya
wuce abinda abin bauta ya bayyana, kar ka yi
masa butulci ka saka ya yi fushi daku ya
hanaku samun nasara, shi kasan mafita ne
game da abinda ya riqa faruwa daku tsawon
lokaci ba sai yanzu da aka sanar dakai ba?”
Yana gama faxa masa haka ya rikixe ya koma
hayaqi qasa ta tsage ya shige cikinta cikin
azamar Sarki Dukuruf ya miqe domin bashi
haquri amman ya makara ganin haka yasa ya
xora akai ya taqarqare duk qarfinsa ya kurma
wani uban ihu.
‘yarsa ta bankaxo xakin ta shigo da
gudu duk da zamtowar dokace babu wanda
7
GAMO DA AJALI
yake shiga cikin xakin, ta tsaya suna kallonkallo ita da mahaifinta.
“Lafiya Baba?” Tayi masa tambayar
tana kallonsa.
“Wannan shekarar akwai masifa,
jama’a za su zamto a cikin bala’i duniya zata
zama cikin qunci” Abinda ya iya cewa kenan
ya juya a fusace ya fice daga cikin xakin.
Tun lokacin data mallaki hankalinta
tasan kanta har tayi wani abu da zai taimaketa,
ta ji tana matuqar son mahaifinta irin son da
bata tava yiwa wani mahaluki ba. Saboda irin
yanayin kulawar da yake nunawa akanta hakan
yasa take ji a cikin ranta zata iya yin komai
domin kare martaba da qimar mulkin
mahaifinta.
Azima kyakkyawa mai matuqar kyau
da cikar halita wacce duk zamanin babu mai
kyawunta, gata jaruma mai matuqar yawan
bajinta da dauriya bata ko shayin wani gwarzo,
amman ganin irin kisan da ake yiwa gwarazan
jarumai ba tare da sanin ko waye mahalukin ba.
Babban abun baqin cikinta zata mutu
ba tare data aikata wata bajinta ba da zata
zamto tarihi ga ‘yan baya domin haka da
8
GAMO DA AJALI
maganar da mahaifinta ya gaya mata da
lamarin dake damar mata qwaqwalwa suka
taru suka zamto wani babban ruxani gareta.
Daga wurin da take a zaune akan
shimfixar ta alfarma a xakin alfarma a waje
barada birjik cikin kayan yaqi sonata faman
rarraba idanuwa domin ganin wanda zai kawo
farmaki zuwa gare su. Itama da take cikin
xakin tana cikin shirin yaqi ne tana riqe da duk
wani na’u’in makami kamar yadda sauran
sadaukan suke.
Azima tayi shiru ita xaya lokaci zuwa
lokaci takan zaro takobinta tax an shafeta
amman hankalinta ya yi nisa wurin yawaitar
tunani, bayan tsawon lokaci ta miqe ta xauko
wani xan mulmulallen qarfe ta doka a jikin
wani xan sanho, ai kuwa bata gama bugawa ba
wani tiririn hayaqi ya turniqe a cikin xakin, a
sannu a hankali hayaqin yana raguwa a lokacin
wani matashin saurayi ya baiyana tsaye da
jakar bokanci ya na yiwa Azima murmushi
idanunsa akanta.
“Meye ka qura min ido kana kallona
kamar kaga wata halite da baka saba ganinta
ba?” Da Gadara irin ta jarumai ta yi masa
tambayar.
9
GAMO DA AJALI
Boka hamad ya yi wani marayan
murmushi gareta, tun tsawon lokaci mai tsawo
yake tare da ita har ta mallaki sirrin kiransa
bata tava yi masa irin wannan kiran ba cikin
gaggawa sai yau, ya qara shagala zuwa ga
kallonta kafin daga bisani ya sunkuyar da
kansa domin yasan sai dai gani ya qyale.
Ya jima yana qaunarta a cikin
zuciyarsa, amman kuma ya rasa hanyar da zai
bi domin ya bayyana mata.
Ya dakatar da tunaninsa gami da kuma
kallonta, kafin ya xauke kansa daga gareta ba
tare daya bata amsar tambayar data yi masa ba
a hankali ya motsa fatar bakinsa da zumar yi
mata magana.
‘Me yasa kika yi min wannan kiran
gaggawar a cikin wannan talatainin daren, a
lokacin da nake kan aiwatar da wani bincikena
mai matuqar muhimanci”.
Ta gyara riqon data yiwa takobinta.
“Ina son sanin abinda aka faxawa
mahaifina har naga hankalinsa ya xaga?” Boka
Hamad ya kalleta kallon tsawon lokaci kafin
ya kauda kansa gefe guda a hankali ya soma
faxa mata duk abinda ya faru.
10
GAMO DA AJALI
Itama jin labarin ya matuqar tayar
mata da hankali ya birkitatta, hakan yasa ta
kuma kallonsa da wani kallo na tsananin
ruxani tace masa.
“Yakai maxaukakin boka mai daraja
mai girma xan saurayi matashi mai kyawu
abun kwatance...” Ta xan dakata da maganarta
ta kuma kallonsa domin gano tasirin da
lafazinta ya yi a gareshi.
“Gaskiya kinyi min yabo da tunda
nake a duniya babu wanda ya tava yi min shi,
saboda haka na yi miki alqawarin zan taimaka
miki akan komai idan kika nema daga gare ni”
Da kwantar da murya yace mata.
Ta yi matuqar jin daxin haka, wannan
karon cikin qwarin gwiwa tace masa.
“Waye makashin jarumai?”
Tambayar ta tayar masa da hankali,
domin lokaci xaya fuskarsa ta sauya kamar
yadda zabibi yake sauya ruwa idan aka zube,
ba qwarin gwiwa a muryarsa yace mata.
“Tabbas babu wata mafita data wuce
bin maganar Boka Salsala na xauko kayan
yaqin sarki salmanu dake tsubirin Duf wanda
jarumai ashirin za su kuma a kamo talatin a
qonasu da wuta har su halaka, game da
11
GAMO DA AJALI
tambayarki kuma wane makashin sadaukar,
amsar ita ce har zuwa yanzu babu wani
mahalukin daya gano wane makashin kawai
dai ana zargin-zargi ne har yanzu an kasa gano
gaskiyar lamarin” Maganar shi ta matuqar
tsuma zuciyar Azima tayi shiru kawai tana
tunanin mafita ga lamarin can bayan tsawon
lokaci taja numfashi tare da faxin.
“Babu wata mafita bayan wannan?”
Boka Hamad ya kalleta wannan karon
da xan murmushi akan fuskarta.
“Sai dai mutuwa”.
Azima ta tsaya tsai kawai tana kallonsa,
tabbas ta aminta ya zama dole tayi shirin
tunkarar abinda yanzu yake gabansu.
“Zan baki kariya amman da sharaxi
idan kika aminta za ki aure ni idan kun dawo
daga tsuburin Duf”.
Maganar tashi tayi wa Azima wata irin
shiga, tunda take a rayuwarta wani mahaluki
bai tava faxa mata wannan maganar ba sai shi,
wannan dalilin yasa ta ji ya burgeta dahar ya yi
jarumtar sanar da ita abinda yake cikin
zuciyarsa, duk kuwa da ruxanin data kasance a
ciki.
12
GAMO DA AJALI
Ta yi masa wani marayan kallo daya
saka tunaninsa tsayawa na wucin gadi.
“Duk zamanin nan babu wata mace da
zaka nunawa qauna ta tsere daga gareka
musamman idan har kunyi kallon-kallo da ita”.
Boka Hamad ya ji matuqar daxin
maganarta haka kuma bai tava tsamanin zai
shawo kanta cikin ruwan sanyi ba.
“Zan kareki duk nisan da kika yi da ni,
zan tsumaki ki zamto gaggara gasa ko wane
mahaluki a duniya kuma ke za ki zama mai
nasara a lokacin zuwa tsubirin Duf” Wannan
maganar daya faxawa Azima ta qara bata
qwarin gwiwa haka kuma hankalinta ya
kwanta.
**
A lokacin da sarki Dukuruf bai tava
tsamani ba ya samu nasarar kamo gwarazan
jarumai talatin da aka lisafa waxanda sune za a
qone su a cikin wuta, sannan aka gayato
sauran da za su tafi xauko kayan yaqin sarki
sulaiman, hakan ba qaramin mamaki ya baiwa
sarki Dukuruf ba.
Hakan yasa suka tsaida rana ita yau a
matsayin ranar da za qone sadaukan domin
cima umarnin Boka Salsala, kuma za su yi
13
GAMO DA AJALI
haka ne domin kar waxanda aka gayato su zo
suka abinda yake faruwa na zallunci
musamman domin sato su aka yi ba tare da
sanin iyalansu ba.
Bayan tsawon lokaci da xumbin
dubatar jama’ar birnin rum suka xauka suna
jiran fitowar sarki daga bisani suka soma jiwo
tashin algaita da bugun tambura hakan ne suke
nuni garesu sarki yana gab da fitowa, bayan
wasu ‘yan sakani suka hango sarki tafe tare da
‘yarsa Azima a vangaren sa tana cikin wata
shiga ta alfarma sai qyalqyali take yi.
Jama’ar qasar suka varke da sowa da
ihu gami da yawan iface-iface bayan tsawon
lokaci sarki ya xaga musu hannu lokaci xaya
wurin ya yi shiru kamar babu wata halita mai
numfashi a wajen.
Sarki Dukuruf ya qurawa yawaitar
sadaukan da jama’arsa idanu na wani taqin
lokaci, sai yaji wani irin alfahari ya lulluve
masa rai don haka da tsananin girman kai ya
soma magana.
“Yaku jama’ar birnin rum nasan kuna
da masaniyar irin abinda yake gudana ga
gwarazan sadaukan mu na salwantar
rayukansu, bama mu kaxai ba duk duniya tana
14
GAMO DA AJALI
cikin wannan barazanar hakan shi yasa fargaba
ga zukatan jarumai. Amman da muka nemi
taimako an sanar da mu hanyar samun nasara
wacce a cikinta dole sai mun qone sadaukan
nan guda talatin, sannan kuma mun tura guda
ashirin zuwa tsibirin Duf dan xauko kayan
yaqin sarki salmanu, wannan saqo ne daga
abin bautar mu” Ya kammala maganar yana
kallon jama’arsa koda suka ji haka sai suka
varke da ihu da iface-iface.
Sarki ya koma ya zauna, sannan ya
bada uwarni domin qona sadaukan da za a
saka a cikin wutar da aka kunna tana ci gangaganga, cikin gaggawa aka soma janyo
sadaukan da suke xaure cikin wasu manyamanya baqaqen sarqoqi kana kallonsu za ka
ga duk sun sauya kama saboda wahala da suka
sha, idan ka kalle su zaka ga tsoro bayyane a
idanun wasu daga cikin su, wasu kuma saboda
tsananin jarumta ko gezau basu yi a haka aka
riqa kai su ana jefawa a cikin wani rami mai
tsayin zura’i goma.
Wanda aka xauki tsawon kwanaki ana
hura wutar.
Duk sadaukin da aka cila a cikin wutar
sai dai kaji ihunsa zuwa wasu ‘yan sakani sai
15
GAMO DA AJALI
ka ji shiru wuta ta qone shi, haka aka riqa jawo
sadaukai xaya bayan xaya ana cillasu cikin
wutar suna halaka a haka har ya zamana
sauran wani sadauki guda xaya a tsaye shi
xaya jal, wannan sadaukin ya kasance tsufa ya
kamashi amman duk da haka akwai zubin
jarumta a tattare da shi ya kasance jarumi daya
wanda ya gagari duniyar sarakuna, bokaye da
sadaukai duk lokacin daya fito yaqi aljanu ma
guduwa suke yi.
Amman a yau ya zama cikin sarqa ana
shirin halaka shi.
Aka jawoshi da qyar yana tafiya cikin
isa da izza kamar ba halaka zai yi ba, a haka
aka qaraso wajen da sarki Dukuruf yake zaune
suna qarasowa sarki da kansa ya miqe domin
girmamawa ga wannan tsohon sadaukin.
Yaja ya tirje yana duban sarki ido
cikin ido sannan cikin wata murya wacce
amonta yake hauhauwa yace masa.
“Tabbas munyi wa qasar nan bauta tun
daga quruciya har zuwa tsofa, mun xaga
darajarta har ta gagari duniya, amman da
wanna sakamakon aka saka mana, sai dai ka yi
sani yakai sarki Dukuruf kun bar baya da qura
saboda matashin jarumi ya bayyana kuma zai
16
GAMO DA AJALI
binciko duk wani voyayyen matsoranci daya
zamto yana halakar da sadaukai” Yana
kammala maganar ya sunkuyar da kai ya yi
gaba abinsa ya nufi wajen da wutar take ci tana
toroqo.
Maganar daya faxa ta tsaya a zuciyar
sarki Dukuruf saboda bai fahimci abinda yake
nufi ba, ya kuma san halin sadauki bangu indai
ya yi magana akwai abinda take nufi, kuma
duk abinda ya faxa babu makawa sai ya faru”
Da yana da iko hana aiwatar da kashe shi da
tuni ya hana, amman yana kallo aka cila shi
cikin wutar amman abin mamaki babu wanda
ya ji ihunsa.
Jama’ar dake gurin suka yi shiru suna
kallon-kallo a tsakaninsu suna masu qara
jinjinawa jarumtaka irin ta sadauki Bangu,
tabbas ya bar abin tarihi wanda za a sanar da
‘yan baya.
Daga nan sarki Dukuruf bai kuma
cewa komai ba ya juya cikin kasala ya nufi
gida Azima ta rufa masa baya.
Suma jama’ar birnin kowa ya watse
aka shiga harkokin yau da kullum.
17
GAMO DA AJALI
A hakankali awani suka rikixa suka
zama kwanaki, su kuma kwanaki suka zama
kwana bakwai a cikin kwanakin kullum sai
wani sabon abu ya faru na zuwan wani jarumin
sadauki daga wata nahiya a haka suka taru har
baqin sadaukan da aka gayyata suka taru suka
zama goma sha tara ya zamana sauran sadauki
xaya ake jira.
Mafiya yawa daga maqwabtan birnin
rum suka zo, sai tsiraru da suka zo daga wata
nahiya ta daban hakan ya saka aka samu
bambanci addini da kuma al’ada, wasu suna
bautar gunki, wasu rana suke bautawa yayin da
wasu zaka samu wuta suke bauyawa sai kuma
masu yin bauta ga ubangiji wanda ya yi
umarni da bin tafarkin tsira.
Har kwanaki biyar suka qaru akai
amman xaya sadaukin da ake jira bai zo ba,
hakan ba qaramin xagawa sarki Dukuruf
hankali ya yi ba, amman hankalinsa ya fi tashi
ne idan ya tuna da rabuwa da ‘yarsa Azima
wannan ne yafi komai xaga masa hankali.
Ganin lokaci yaja sadaukin bai zo ba
sai ya soma tunanin ko qaddarar da take hawa
kan sadaukai ko ta same shi ne? don haka aka
fitar da ranar tafiya ko ya zo ko bai zo ba.
18
GAMO DA AJALI
A lokacin da aka fitar da tsamani a
lokacin matashin jarumin ya bayyana, yana
haye bisa wani baqin doki mai nagarta, kamar
yadda mahayinsa shima ya zama nagartace
ma’abocin kwarjini yana da doguwar fuska da
manyan dara-daran idanu da jerarun fararen
haqora kamar gonar auduga, gashin kansa ya
zuba har baya ya warwatsu sashe zuwa sashe.
Ya kasance mai yawan tambaya akan
duk abinda ya gani bai sani ba, ya kasance
ma’abocin bin tafarkin addinin musulunci. Bai
san tsoro ba kuma baya shayin kowa saboda
duk da wannan kisan da ake yiwa sadaukai shi
ko kaxan bai xaxa shi da qasa ba sabida yasan
mutuwa da rayuwa tana hannun Allah idan
lokacinka ya yi babu makawa sai ka mutu,
hakan yasa yake gudanar da rayuwarsa cikin
walwala da jin daxi.
Wannan shi ne jarumi Salman.
Kai tsaye ya nufi fada ba tare da
fargaba ko shayin wani abu ba, duk da
kasancewar yamaci ya yi rana ta tafi faxuwa
ya qarasa qofar fada yaja dokinsa ya tsaya
yana kallon dogarawan da suke tsattsaye a
tsube cikin shirin kota kwana.
19
GAMO DA AJALI
Cikin sauri wasu daga cikinsu suka
kama mishi ya sauka, sannan aka yi masa
jagora zuwa wajen sarki a haka suka qarasa
wata turaka inda suka samu wasu mafiya yawa
daga cikin dakaru suna gadi, a hankali suka
qarasa suka yi wata magana da Salma bai ji
abinda suka ce ba sai ganin sun juyo gareshi
suka yi masa alama daya qaraso.
“Sarki yasan da zuwanka?” Wani
dogari mai kai kamar qoqo ya tambaye shi.
Salman bai bashi amsa ba sai kawai ya
sa kai cikin xakin inda ya samu sarki Dukuruf
a zaune yana bincike a cikin wani qaton littafi
da Salman ya gaza gane rubutun dake jikinsa,
face wani xan hoto daya gani anyi na wani xan
mulmulallen abu da hoton gunki kan saniya.
Ya nemi gefe guda ya zauna yana
kallonsa har ya kammala ya xago da qananun
jajayen idanunusa masu kama dana maciji
suka yi kallon-kallo.
Duk duniya babu abinda sarki Dukuruf
ya tsana sama da ma’abota addinin musulunci,
hakan ya saka babu abinda yake shiga
tsakaninsa da duk ma’aboncin musulunci sai
kisa.
20
GAMO DA AJALI
Yana da masaniyar wane Salma, yasan
ma’aboncin musulunci ne wanda ya fito daga
yankin masu tsattsauran ra’ayi da riqo da
addinin musulunci hakan yasa bai samu wata
tarba sosai daga gare shi ba, mai makon haka
sai wani kallon hadarin kaji daya yi masa.
“Barka da zuwa cikon sauran jaruman”
Sarki Dukuruf yace masa.
“Har an gayyato sauran kenan, mu dai
mun sadaukar da rayukan mu domin na baya
su rayu” Yana kammala maganar ya miqe
domin barin xakin, a lokacin daya miqe ne
sarki Dukuruf ya samu ikon qare masa kallo a
yanzu ya tabbatar da cikar jarumtaka a tattare
da shi.
Wani sadauki ya yi masa jagora zuwa
masaukinsa wanda aka ware a cikin wani
vangare daga gidan sarki, anyi hane
sakamakon sauran su kenan a duniya, kuma
sune ake saka ran za su zama mafita a duniyar
jarumta.
A haka suka qarasa har zuwa
masaukinsa ya shiga ya tarar da an shigar masa
da ragowar kayansa ya zauna, zaman shi ke da
wuya ya gano kwanikan abinci waxanda aka
ajiye masa ya miqe cikin sauri ya xebi wanda
21
GAMO DA AJALI
ransa yake so ya zauna ya soma ci har sai daya
qoshi, ya shiga wajen wanka ya yi wanka ya
sako wasu kayan alfarma ya fito da zumar ya
xan tattaka domin miqe qafafunsa da kuma
baiwa idonshi abinci na daga kallon tsarin
gidan sarautar Rum.
A lokacin daya fito itama Azima ta zo
daidai wurin domin shiga vangarenta, suka yi
musayar kallo a tsakaninsu, su duka suka ja
suka tsaya kamar an tirsassa musu yin haka,
suka qurawa juna idanuwa suna duban juna
kowa yana mamakin kyawun xan uwansa.
Ta kawar da kanta gefe tayi gaba da
zumar barin wajen, a lokacin shima ya motsa
ya shiga gabanta ya tsaya wanda hakan yasa ya
tsare mata hanya kafin tayi wani yunquri yace
mata.
“Ko zan iya sanin ko ke wacce ce yake
ma’abociyar kyawu? Azima ta kauda kai gefe
tace masa.
“Bani da suna” Ya yi murmushi.
“An tava yin mutumin da bashi da
suna? Da za ki daure ki sanar da ni domin na
yi gaggawar sanar dake wani sirri” Ta xago
idanu ta dube shi cikin wani sirrin kallo, ya
sauke numfashi kafin ya daidaita tunaninsa sai
22
GAMO DA AJALI
yaga ta tunkaro shi gadan-gadan kamar zata
shiga jikinsa.
“Kar ki haxa jikin ki da shi, ke yanzu
tamu ce kina soyayya ne da matashin boka”
Wata siririyar murya mai kama da raxa tace
mata. Hakan shi ne ya tilastawa Azima
tsayawa cak kamar an kafeta a wajen daga
wajen da take tsaye tana iya jiyo bugun
numfashin Salman, ta dubi wajen data ji murya
tana mata raxa amman bata samu ikon ganin
Boka Hamad ba.
Ganin kallon da take yi yasa wani
hayaqi ya tashi a wajen lokaci guda, suka dubi
wajen su duka biyu a lokacin Boka Hamad ya
bayyana a gabansu fuskarsa a murtuke kamar
an sassaqo daga katako. Ya jefi Salman da
wani mugun kallo sannan yace masa.
“Kai yaro wargi waje ya ke samu,
wannan Gimbiyar tafi qarfin yaro sai dai
baban yaro” Salman ya yi murmushi.
“Lallai yanzu ne na yadda cewar ita ce
wacce ya kamata na nemi aurenta don fafatawa
da jahilai irin ku” Idon Boka Hamad ya kaxa
ya yi ja.
23
GAMO DA AJALI
“Ahir! Xinka kar gigiwa ta kai ka ta
baro, domin yanzu nan na saka a naxe maka
qafafu” Salman ya buga masa harara.
“Yaro bai san wuta ba, sai ya taka”
Yana gama faxa mata haka sai ya sunkuya a
hankali ya kamo hannunta ya sumbata ya yi
gaba abinsa.
Hakan daya aikata ba qaramin qonawa
Boka Hamad zuciya ya yi ba, ya ji zuciyarsa ta
soma raurawa tana azalzala a cikin qirjinsa, a
haka ya bi bayan Salman da kallo har sai daya
vace masa.
Ku min afuwa ci gaban labarin yana
littafi na biyu. Na