Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
10 / 10
Hafeeza? Kuma Yaya akai har kikasan gidan su? kede nasan wannan layin ba wajan zuwan ki bane" Hafeeza tayi shiru itade kanta yana qasa, shi kuwa Kawu Hamza har lokacin baice komai ba, Inna ta Kalle shi tace"kayi Shiru Hamza" Ajiyar zuciya ya saki yace" Ta Rasulu bakisan gidan Hajiya Rabi'atu ba?" Inna tayi shiruuu sai can tace" nagane ta, tabbas nagane ta,wadda take zaune tareda jikokin ta ko?" Kawu Hamza yace"tabbas,ai abinda zanyi magana akai kenan,yaron nan da Hafeeza take maganar sa dan gidan ne, shima jikan Hajiya Rabin ne,kuma ni dashi mun zauna nayi masa tayin auren Hafeeza amma yaron nan firr yaqi,ya nuna min baya sonta, qarshe ma cemin yayi idan yarinyar tawa tanada ma nema to in batasu, shine yaron danake baki labarin sa kwanaki" Cikin sauri Hafeeza ta dago kanta ta kalli kawun nata,kanta ya daure,yaushe akai haka? Kuma Hafeez din? To menene amfanin zuwansa wajan ta kenan? inde yariga ya fadawa kawun ta haka dama yaudara ce ta kawo shi wajanta kenan? Kafin tagama tunanin da take Inna ta Rasulu tace"to kode bashi bane qaninsa ne?"(😂) Cikin tabbatar wa kawu Hamza yace"Shine" Inna ta gyara Zaman ta sannan ta kalli Hafeeza da kanta ke qasa har yanzu,ta dawo da kallon ta wajan Kawu Hamza sannan tace" tonikam Hamza tun farko ma dakace min kaje wajan sa da maganar Auren Hafeeza nake ta tunanin dalilin zuwanka wajansa? yaron da ake yawo dashi agari ana cewa baya mu'amular kirki shida iyayensa?" Kan Hafeeza ya Sara,tafara tambayar kanta da gaske baya mu'amular kirki da iyayen nasa? tatuna lokacin da suka hadu a Saudia, agabanta mahaifiyar sa takirashi yakai sau uku,amma baya dauka, sannan lokaci daya taga yanayin fuskar sa ya sauya saboda ganin kiran, tayi tunanin ko me mutum yake muddin mahaifiyar sa takirashi to dole zaibar abinda yake ya saurari kiran mahaifiyar sa. Inna ta kalli Hafeeza sannan tace"to kinji de anyi masa tayin aurenki yace bayaso,sannan Nima shaida ce kaf layin unguwar nan babu wanda baisan cewa yaron nan anyi masa shedar baya mutunta iyayensa ba,to wanda bai bawa iyayensa mutunci ba tayaya kike tunanin ke Zaki samu girmamawa daga wajan sa? me zaki dashi ?" Kawu Hamza yace"to nima de abinda nagani kenan, ban duba wannan surutun ba nataka qafa ya qafa naje har inda yake nayi masa tayin auren ta, amma yaron nan yace bayaso" Inna tayi ajiyar zuciya tace"to ai shikkenan,dama Bansan inda ta debo Shiba,kasan Allah Hamza, Allah daya ne bansan inda Hafeeza ta hadu dashi ba, saboda ita ba yawo take ba" Tamaida kallon ta wajan Hafeeza tace"wanne irin aiki yake ne? ko shima a Habujan yake?" Kan Hafeeza aqasa tace"a a Inna,awata qasa yake aiki" Cikin sauri Inna ta dafe qirjnta sannan tace"wata qasa? a a Hamza, ina ganin asake tsananta bincike akan halin yaron nan"(😲😂🤭) Kawu Hamza yace" Ta Rasulu nifa bazan bashi 'yata ba,nabashi da bakinsa yace bayaso ya watsamin qasa a'ido" Inna daga Jin zancen qasar waje lokaci daya ta rikice tasake gyara zamanta tace"to gata nan a zaune, tunda kaga haka son abinta take, kasa a bincika muji gaskiyar lamari, halayen sa dakuma abinda yake faruwa tsakanin sa da iyayensa" Kawu Hamza ya qeqashe idonsa ya kalli Inna yace" zan'iya bincikawa kam amma badon in had'ashi aure da'ita ba, zan bincikane domin inyi masa iyaka da Hafeeza" Hafeeza tanajin haka ta tashi da gudu tashige dakinsu,zama tayi agefen gado ta rafka uban tagumi,yanzu kenan batada mafita data wuce auren wannan dan siyasar kenan? Cikin sauri shawarar kiran Maman Fadila ta fad'o Mata, cikin sauri kuwa ta doka Mata Kira, ta kwashe komai tafada mata, Maman Fadila tace"gaskiya Hafeeza Nima bana miki sha'awar auren wannan dan siyasar, abinda za'ai yanzu ki kira shi Hafeez din kifada masa komai, karki ji shakka, ki kirashi kuyita ku qare idan ma bada gaske yake ba Zaki gane" Hafeeza tayi mata godia ta kashe wayar sannan tafara qoqarin kiran wayar Hafeez. Acan tsakar gida kuwa, kawu Hamza miqewa yayi zai tafi, Inna tace" nikam Hamza mezai Hana kakira mana abokin shi Hafeezun muji ta bakinsa akan abinda mutane suke rade-radi akansa?" Kawu Hamza yace" Ta Rasulu, yaron nanfa babu abinda ba'a fadamin akansa ba,duk abinda kikaga shedar mutane tayi yawa akansa toda gaske ne,tayi haquri ta cire shi aranta kawai" Inna tace"banqi taka ba, amma karka manta tunda har Hafeeza ta ajiye kunya agefe tace shi takeso, ina ganin munemi ba'asin yaron muji dalilin abinda yake faruwa tsakanin sa da iyayensa, idan har abinda mutane suke fada gaskiya to Hafeeza ko zata fad'a cikin rijiya saboda soyaiyar sa saide ta haqura dashi, domin duk mutumin dabai girma ma iyayensa ba to bazai ga daidai ba a rayuwar sa" Kawu Hamza yadawo ya zauna, sannan ya dauko wayar sa daga cikin aljihunsa ya dokawa ma'aruf kira. Acan daki kuwa bayan Hafeeza takira Hafeez awaya kira biyu yayi caraf ya dauka,yana fatan ace tabashi dama yazo gidan su kamar yanda ya nema awajan ta. Cikin nutsuwa ta gaida shi sannan taci gaba da fadin"dama inaso zamuyi magana ne" Cikin wata irin kasalalliyar murya Hafeez yasake narkewa yace"duk abinda kike buqata daga gareni Umarni kawai Zaki bani,ba buqatar ki nemi iznina, inajin ki" Hafeeza tayi ajiyar zuciya tace"kayi haquri akan maganar dazan fadama, nayi wa kawuna maganar ka,amma yacemin auren mu bazai iyu ba" Hafeez dayake kishingide afalo cikin sauri ya tashi zaune tareda bude idonsa yace"what!" Hafeeza ta gyada kanta kamar yana ganin ta, sannan taci gaba da fadin "yacemin yayima maganata yana so yabaka aure na kai kuma kace bakasona, shiyasa yanzu yake son hadani da wani sanata" lokaci guda Hafeez ya lumshe idonsa,wani irin zufa yafara wanke masa fuska, ahankali yafara furta kalmar ''innallillahi wa Inna ilaihirraji'un, dama kawunki ne?'' Cikin tsananin mamaki Hafeeza tace"da gaske ne kunyi hakan?" Hafeez ya runtse idonsa yakasa magana sannan kuma yakasa bude idon. Ganin yayi shiru hakan yasake tabbatar wa da Hafeeza cewa tabbas anyi hakan,cikin sanyi jiki dakuma sanyin muryar tace" kayi haquri, alaqarmu bazata iyu ba, domin kuwa koba wannan kawuna yace anfada masa cewa baka shiri da iyayenka,sannan nima shaida ce,a gabana MAMANKA takira waya naga yanayin ka ya sauka,kuma...." Cikin wani irin yanayi da dacin zuciya Hafeez ya katseta yace"ina shiri da iyayena Hafeeza" Abinda Hajiya Kaka taji kenan tagama gane anzo wajan,anzo wajan da batason azo,hakan yasa batasan lokacin da flate din dake hannun ta yazame ya fadi batare data sani ba har qaran faduwar flate din ya janyo hankalin 'yanbiyu. Hafeeza tace"to amma meyasa mutane suke fadar haka? meyasa Mamanka ta kiraka kayi rejecting kiran,kana nufin nafita muhinmanci ne kome?,kazo ka fuskanceshi kuyi magana, idan har kawuna bai amince dakai ba,bazan iya auren ka ba,saboda shine amatsayin mahaifina yanzu" Runtse idonsa yayi, jijiyar Kansa tafuto sosai,gumi ya wanke masa fuska,idonsa yayi jajir kamar me ciwon ido,tashin hankali guda biyu suka taru suka hade masa waje daya,batun iyayensa dakuma hanyar da zaibi ya'iya kallon kawun Hafeeza bayan irin rashin kunyar da yayi masa. yan'biyu suka tsaya cirko cirko atsaye, ahankali Kaka tayi qarfin halin dafa kafadar sa, cikin tsananin damuwa yadago idonsa ya kalleta. *** *** *** Acan gidansu Hafeeza kuwa ko minti talatin ba'a yiba Ma'aruf yayi sallama a qofar gidan, kawu Hamza ya tashi yaje yashigo dashi,lokaci daya qamshin turarensa yacika qaramin tsakar gidan nasu. Kawu Hamza ya kalli Ma'aruf yace"bawani abu bane yasa nakira ka,ta inda aka hau tanan ake sauka,nabawa abokin ka yata yace bayaso,anyi haka ko ba'a yiba?" Ma'aruf ya jinjina Kansa alamun tabbas hakane anyi haka, saide shi aransa yana mamakin dalilin wannan Kira, tunda Hafeez din yace bayaso dole ne? ana soyaiya dole ne? Yanzu shi daya kirashi har gida mezai yi masa? ko tunda Hafeez bayaso yanzu kuma shi zai liqawa 'yar tasa? (🤭🤔) Zancen kawu Hamza ne ya katse masa tunanin sa, kawu Hamza yaci gaba da fadin"to Yanzu ya lalla6o zai hurewa 'yata kunne,kafada masa yafita idona in rufe,bashida hurumin magana da Hafeeza" Cikin sauri Ma'aruf yadago idonsa ya kalli kawu Hamza, gabansa ya fadi, nan take wayar sa da Hafeez ta fad'o masa,kenan de akan Hafeeza ake maganar,innallillah...,anyanka ta tashi kenan. Cikin tashin hankali Ma'aruf ya cire hular dake Kansa yafara firfita da'ita. Shi Kansa wata irin kunya ce ta rufe shi, daqyar yadago Kansa yace" Dan Allah Baba kuyi haquri,ku taimaka ku bashi ita, shi din abun tausayi ne, yana buqatar Hafeeza acikin rayuwar sa, Baba karka duba laifin da mukayi" Inna ta Rasulu tace"kaga ba wannan ba yaro,fada mana menene yake faruwa tsakanin sa da iyayensa?, shin da gaske ne baya jituwa shida iyayensa? " Ma'aruf ya kalleta yakasa cewa komai. wacce irin amsa zai bata? tayaya zai bata amsar gaskiyar magana batare dashi Hafeez din ya amince masa ba? Inna ta Kalle shi tace" kayi shiru,ya kamata kayi mana bayani ka cire mu aduhu'' Ma'aruf ya saki Ajiyar zuciya sannan ya sake sunkuyar da Kansa yana tunani, daga qarshe yace" ina zuwa" Kai tsaye ya dauko wayarsa daga aljihunsa, yadokawa Hafeez Kira,adede wannan lokacin Hafeez baya cikin yanayin daukar waya,yanaji wayar tana qara yakasa dauka,Hajiya Kaka da take zaune agefensa tana shafa Kansa dake kan cinyarta itace ta dauki wayar, bayan sun gaisa Ma'aruf yace"Hajiya Kaka,ina gidansu Hafeeza, kawun ta yakirani akan nayi wa Hafeez magana yadena kula yarsa, inaso keda Hafeez kubani izni,idan kun amince zan sanar da iyayen Hafeeza komai" Hajiya Kaka cikin sanyin murya tace"Mun amince, Kafada musu Ma'aruf..." Ma'aruf yadago Kansa ya kalli Inna da kawu Hamza sannan yace"Yau zan fada muku wanene Hafeez, yau zan fada muku dalilin da dayasa mutane suke cewa baya mu'amula da iyayensa" Inna ta Rasulu data zaqu da son Jin abinda yake faruwa cikin sauri tace"muna jinka" Ma'aruf yace"Shekarun baya...." Complete document 1k 8621296018 Amina Muhammad fcmb kokuma Katin Mtn ta wannan number 08033300034, tareda shedar biya ta wannan number 08033300034💃 Amnah El Yaqoub✍🏻 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 10 of 10